Showing 39001 words to 42000 words out of 178062 words

Chapter 14 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

maryam zaune .”




Kai tsaye gadon baby ya zarce ya tsaya shiru yana kallon baby kwance cikin showel haka zalika maryam shiru tayi tana kallonsa yana ta’ba qirjinsa yana murmushi kafin yaya hisham ya kai hannu ya d’auki babyn ya kai masa sumbata a goshi ya mika masa ya karbi baby ya nufo wajen mami ya zauna kusa daita “sweetheart!”ya kira sunanta “naam adamcy nah ran my prince ya dade yayi murmushi jin dadi har dimples dinsa ya lotsa “an dade baa min abinda ya faranta raina ba “haka ne kasan baby da shiga rai ai na lura tunda aka haifi yaron nan kake son shi kai ma allah ya baka naka masu albarka shafa fuskar babyn ya cigaba dayi yana murmushi “babana ,my prince ,my averything cikin murmushi ya kalli mami “sunan babana hisham yasa bansan yadda zan misalta farincikina ba.”






nan take fuskar nana hauwa’u data sauran yanuwata ta bayyana tsantsar farinciki daman burinta kenan sunan babanta amman duba ga shi kad’ai iyayensa suka haifa yasa tayi tunanin sunan abbansa zai sa allah sarki ashe ita zai wa suprise
ta kalli yaya hisham tana masa kallo mai dauke da murna da godiya“maryam kuwa ji tayi jikinta yayi mugu mugun sanyi sai taji inama ace nmj zata haifa ba mace ba kai wannnan mutumin ko me zata haifar masa bazai nuna farincikinsa haka ba “ta fad’a a kasan rabata “hisham ya tsallake sunan kowa a dangi yasa na babana bansan yadda zan kwatata murnata ba yau “. hankalin mami gabadaya ta maido kan ata dake zaune rike da baby “lallai wannan abu yayi kyau Allah yayiwa rayuwar ishaq albarka koni naji dadi sosai kuma nasan hajiya zulfa’u ma zataji dadin wannna alamarin kai kowa ma nasan zai ji dadi yaya hisham ya mike ya fita yana dariya byn Kmr second biyar nana hauwa’u ta kwashe kayan baby daaka kawo wa mami tabiyo mijinta d’akin da take jego suka shiga tare ta nufi wordrobe din baby ta bude ta soma qoqarin ajiye kaya .”




Ahankali ya tako zuwa inda take ji tayi kawai ya hadeta da jikinsa ta baya ta juyo a tsorace suka hada ido fuskarsa a sake “meye na wani tsorata bayan kinsan mu kadai ne a dakin “ ?a ganinka bai dace naji tsoro ba?ya daga mata girasa daya lumshe masa idanunta tayi tace “yau ne fa na cika kwana shida da haihuwa “matsota ya sake yi sosai ya hadeta jikinsa “an só !? sai akace kar naji dumin jikin matata ?numfashi ta sauke alokacin da taji ya zame hular kanta ya fara shafa sabon kitson daaka mata kamar wata sokuwa haka ta dawo yayi kamar zai warware mata zani tayi saurin rikewa tana kallonsa ganin yadda ta tsorata ya saki murmushi yana cewa “malama babu abinda zan miki wani naunayen ajiyar zuciya ta sauke “nayi missing dumin jikinki da lip’s dinki bari na rungumeki na rage zafi yana gama fad’ar hk ya hadeta da jikinsa ya kai hannusa ya taro byn kanta ya hade bakinsu waje daya .”






***
Da misalin karfe shad’aya na daren ranar bayan maryamta taga ma komai nata ta dawo parlour’n ta zauna akan kujera hannuta rike da littafin zane tana aikin mr ata duk da tace bazataje aiki gobe ba saboda wulakancisa amman zatayi iyakar qoqarinta taga ta zana masa abinda yake so sai ta mikawa yusura gobe da sassafe ta mika masa ta jima tana zane sai dai bata gama ba acikin biyar uku kawai ta samu damar yi masa a qarshe ta tattara taje ta kwanta washegari karfe bakwai a gidan su yusura tayi mata alokacin yusura na qoqarin futa zuwa aiki bayan maryama sun gaisa da iyayen yusura ta maida hankalinta kanta “ya naga kin biyo ta nan kuma cikin wata irin shiga “?bazani aiki bane yau nazo ne na kawo miki wadan nan zane ki kaiwa mr ata “what ?haba maryama so kike ya tasheni aiki kawai kije ki shirya ki kai masa da kanki ?ai ban gama bane shiyasa nake jin tsoron zuwa ,shine ni zaki tura ni dai gsky Kiyi hakuri gara kije da kanki “yanzu dai bazaki kai masa ba?” gsky ba wai bazan kai masa bane tsoro nake ji maryama ta dauki lokaci tana fama da yusura as ending dai da kyar ta karba da zumar zata bawa madam some sukai sallama








Taron suna akayi a gidan mami mai cike da tsantsar farinciki dan tsabar murna ma mr ata bai je koina ba yayinda duk wanda ya kalli fuskarsa zai san yana cikin farinciki da annashuwa sannan duk wanda yaji sunan da baby yaci sai yayi murna tare da yiwa marigayi alhaji ishaq addua kowa ka kalli fuskarsa farinciki yake banda maryam da gabad’aya tayi wani iri kallo daya zaka mata kasan akwai damuwa atattare da ita duk da mami tana cikin hidima amman hankalinta na kan maryam bini bini zata nemota taga yanayinta ,baby ishaq wanda aka masa lakabi da ashraf ya samu kyaututtuka ta bangaren dabam dabam ta bangaren yan’uwa da kaninsa da kuma bangaren qawayen hajiya zulfa’u dana mami ata ma kyauta yayi masa ta mussaman inda ya bashi takardun gidajensa biyu dake acikin runin gidajensa dake banana estate .”






Zaune maryam take akan kujera a parlour’n umma ta rungume pillow hannuta rike da littafi wanda ya kasance english novel ne tana karantawa domin so take ta cire damuwar mr ata aranta dan tun safe take cikin tashin hankali da fargaba shiyasa ma ta kasa qarasa masa aikinsa dan batasan wainar daake toyawa ba jira take biyar tayi ta kira layin yusura taji ko ta bawa madam some .”knowking din kofa taji ta ajiye littafin hannunta akan kujera da pillow ta mike ta garasa bakin kofa ta bude wata kyakkyawar budurwa ta gani tsaye abakin kofar lokaci daya taji wani mummunar faduwar gaba from know where ya diram mata “ko zan iya shigowa ? budurwar ta tambaya “sunana anifa friend din sadam ko nace tare mukayi karatu dashi haka ma wurin aikinmu daya dashi bana nan nayi tafiya na dawo naji abinda ya samesa”jin haka yasa maryama ta qara sakin fuska sosai tace sannu da zuwa ki shigo daga ciki budurwar ta shigo ta tsaya tana qarewa falon kallo” ya kika tsaya ki zauna mana babu mutsu ta samu waje ta zauna tana cigaba da qarewa falon kallo .”




“Kece matar daya aura “?maryama ta gyda mata kai alamun “eh!allah sarki wai ya wannan alamarin ya kasance ance anemi sadam an rasa amman kuma ke kina raye ?kuma kin cigaba da rayuwa batare da kin cigaba da nemansa ba ko yana raye ko ya mutu?” ya zakice hk ?kin kuwa san irin nemanshi da mukayi ?” munyi iya qaqarinmu ni alokacin bana cikin haiyacina ni dai nasan an binnesa da ransa daga nan kuma bansan komai daya faru ba “okay budurwa ta gyada kanta tana cewa “allah bayyana shi idan yana raye idan kuma ya mutu allah ya jikinsa dan sadam mutumin kirki ne kowa nashi ne sam bashi da matsala banji dadin abinda ya faru dashi ba allah dai yayi masa rahma.”ameen !maryama ta fad’a .”muryarta cike da runi.”




“Amman dai ya kamata kiyi aure zuwa yanzu tunda baya raye .”maryama tayi shiru tana dubanta hakan yasa budurwar tace “am really sorry shawara ce na baki dan naga ke yarinya ce bai dace kice zaki tsaya batawa kanki lokaci ba saboda rayuwa babu tabbas ko yana raye bare baasan a hali da yake ciki ba a mace ne ko a raye “haka ne banji zafin mgnrki ba amman dai na barwa allah komai .”gsky ne kinyi rashin miji mai hakuri da son mutane kai baqarmin sabo mukai dashi ba alokacin muna karatu koda yaushe muna tare har ma mutane suka fara tunanin ko akwai soyayya a tsakaninmu .”




Maryama tayi murmushi kana tace “Amman kuma bai ta’ba bani labari ki ba ?duk wasu abokan karatusa nasani ,haka dayawa abokan aikinsa nasani kece dai gsky ko sunanki ban ta’ba ji ba sai yau shiru budurwar tayi sannan maryama ta cigaba “bari na kira mahaifiyarmu idan zata dawo yanzu ku hadu watakilla ya taba bata labarinki ?” Oh ! bata nan ne ?eh ta dan fita amman bazata jima ba zata dawo zan so naganta dan hasalima akwai abinda ya kawoni saboda akwai aikin project din da muka fara dashi kafin nayi tafiya in fact maryam document din gabadaya suna hannunsa inda zan samu document din gaskiya da zanji dadi sai na qarasa komai idan aka biyani sai nã kawo masa nashi kason tunda tare muka fara .”




“Okay wannan ba matsala bane wani suna ne ajiki sai naje dakinsa na duba miki uhm zakiga sunana da sunanshi maryama ta mike itama budurwar ta mike da sauri “ammm ko zan iya biyoki dan ba lallai ki gane document din ba maryam ta tsaya jim tana mata kallon mamaki kafin tace “tunda akwai suna ai komai zai zo da sauki amman dai muje tayi mata alamar ta biyota da hannunta “maryama tana gaba budurwar data kira kanta da anifa ta biyota basu tsaya akoina ba sai a bakin kofarsa .”




Tsayawa tayi cak qirjinta na bugawa a hankali ta tura kofar dakin ta sanya kafarta daya tana mai jin faduwar gaba tunda aka nemesa aka rasa bata qara shigowa dakin ba ta shigo sosai haka ma anifa abubuwa dayawa sun dawo mata yadda a farko kamar bazai karbi soyayyarta ba daga baya ta juye soyayyar gaskiyar daya dawo yana mata sadaukar wa da yayi a gareta aranar daurin aurensu murmushinsa tabbas matar tayi gsky shi din mutumin kirki ne .”a hankali ta sauke naunayen ajiyar zuciya tana kallon koina a dakin komai nashi yana nan kamar lokacin da yake nan dakin babu dotti da alamun umma na kula da dakin sosai .”




Ahankali suka fara duba wuraren da takardu suke sai dai duk document din da maryama ta nuna mata sai anifa tace bashi bane can ta kalleta “ammmm ko akwai key din wordrobe dinsa a hannunki ?maryama daukowa tayi ta mika mata tare suka bude wani jaka suka gani dan haka suka fito dashi tare suka bude suka fito da takardun ciki gbdy sai dai basu gani ba tarasa yadda zatai can tayi wani tunani dan haka ta kalli maryama “ko zan iya samun ruwa ?ta dafe kanta maryama tayi tana cewa “sorry wallahi na manta ban baki ruwa ba akawo miki juice ko ruwan Kika fi bukata ?kawo min ruwan ma ya isa ok bari naje na kawo miki ta mike ta fita wanda hakan ya bawa budurwa damar kira a waya .”




byn an dauka ta soma magan kasa kasa “na fa duba inda kace amman banga komai ba sai wasu takardun dabam can bangaren data kira akace “ki dai duba da kyau zaki gani anan suke ,wa kika samu a gidan?”
“ wannna sakariyar yarinyar , okay shinkenan naji na daina ta fad’a tana ajiye wayar akan gado ta cigaba da dubawa har tagani naunayen ajiyar zuciya ta sauke da karfi ta dauki abinda ya kawota tana mgnr a fili “ya allah na gode maka da baka bari na sha wahala ba “kin gani ne taji sautin murayar ta cikin waya ?eh ! nagani bari nayi masa kyaywan ajiya ajikina kafin ta dawo ta daga rigarta daman akwai bodyhug data saka domin aiwatar da shirita ta nade takardun ta saka acikin rigarta ta maida rigarta ta sauke da sauri sannan ta cigaba dadduba sauran takardun zuwa sanda maryama ta dawo dakin tana qaqarin mika mata cup din ruwa taji sautin magana “me kik jira ne ?ga ruwa taji muryar maryama a gigice ta dago da sauri ta mike tana duban wayarta da mgn ta fito “kina jina Kiyi sauri mana ina kiranki please “budurwa tayi sauri ta dauki wayar tana rage volume ta gefe “wannan muryar fa ? Maryama ta furta a matukar rikice .”




Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 11




"Ke babu ruwana da wani aiki da kike son Kiyi dashi ku biyoni kawai har ya juya da sauri maryama tace "excuse me sir ! ya juyo ya tsaya a natse yana dubanta "sir ka za’beni ka bar sultana da surayya tunda su suna bukatar aiki dashi ya juyo qare mata kallon tsam yana murmushin mugunta “ai shi baya son wad’an da basa son zama tare da ATA yafi qaunar masu bukatar kasancewa akarkashina fuskarsa a sake yace "bana bukatarki ki barni da wad’an da na za’ba ya fad'a yana sake juyawa lokacin tuni su surayya sunyi hanyar waje .”ta sake qoqarin bud’e bakinta zatayi magana da sauri tayi shiru sakamakon yatsun qafarta da taji mr ata ya take da takalmin kafarsa yana jifanta da wani mugun kallo mai d’auke da gargadi lumshe idanun tayi cikin jin rad’ad’in azaba .”




kallonta mr ata ya cigaba dayi ransa nayi masa quna muryarsa a tsarke yace "wato kin so ya zabeki ba ?ya fad’a yana zabga mata wata katuwar harara tayi shiru tana jin tamkar yana zarar ranta ne dan har lokacin bai dauke qafarsa ba dan mugunta irin tashi ganin idan batayi wani abu ba zai sabauta mata yatsu yasa ta soma kokarin mgn yayi saurin dakatar daita "ki min shiru ana karki ‘bata min lokaci kiyi qoqari ki gama aikin dana baki nonsense girl kawai.”ya qarasa fad’a yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa yayinda zuciyarsa ta dinga bugawa da qarfi Ahankali ya dinga saisaita numfashinsa da yayi barazanar daukewa sakamakon wasa da rayuwarsa da maryama taso yi ,shi kad’ai yasa bala’i da zai faru da sultan ya zabita dan dai yasan muddin ya zabeta bazai janye qudirinsa ba shi kuma bazai bar masa ita ba .”






yafi mintuna ashiru yana fama da zuciyarsa batare da yace qala ba yayinda duk wani ma’aikaci dake tsaye a wajen, shi yake kallo fuska cike da tsananin mamaki ”some ya d’auke kwayar idanunshi akan maryama ya maida kanta byn ya kira sunanta "yes sir! ta amsa cike da girmamawa .”ya juya cikin hanzari sectary ta biyosa da sauri maryama kam dukawa tayi tana duba yatsunta ko basu samu matsala ba yayinda sauran ma’aikatan da sultan bai za’besu ba suka shiga murna suna godewa allah domin kuwa aiki akarkashin mr ATA akwai samu ba iya albashi bane kawai duk sati akwai kyauta ta musamman da yakewa ma'aikatansa ."






“Maryama tayi kasa da muryarta sosai tace “na kasa fahimtar me yasa suke bukatar kasancewa da wannan mugun mutumin wallahi ni dai naso sultan ya za’beni na huta da takuramin da yawon kallon da yake min “ maryama ta fad’a tana kallon fuskar yusura dake tsaye kusa daita itama yusura cikin yin kasa da murya tace “ke yanzu da sultan ya zabeki sai kiyi aiki dashi ?sosai kuwa zai fiyye min kwanciyar hankali akan aiki da wannan mugun mutumin “ke ki godewa allah wallahi dama kika fahimci yana kallonki mata nawa ke son ya kallesu bai yi ba ?”wannan matsalarsu ce ni dai wallahi banason wannan kallon yusura tayi murmushi tace ta kai bakinta daidai kunnen maryama “kodai oga ata ya kwasa ne ?tsaki maryama taja tana janye kunnenta bata sake yunkurin cewa komai ba .duk ma’aikatan suka watse suka barta ita kad’ai acikin office tana aiki tana zance zuci sosai tayi ta qoqarin taga ta kammala da aikin daya bata har kusan karfe hud’u bata gama ba wanda zuwa lokacin ma'aikata sun fara watsewa daydaykun mutane ne ke kai kawo ita kuwa tana nan ta dukufa gurin qarasa masa aikinsa ."






a matukar gajiya ta d’ago daga abinda take tare da yin shiru tasa pencil a bakinta tana cizawa fuskata da alamun gajiya “ina ma wannan mutumin zai min uzuri dana wuce gida na qarasa masa a gida tunda baa gobe zaa kar’bi aikin ba dan wallahi na gaji dayawa “.ta fad'a tana lumshe idanunta. bayan Kmr minti biyar ta mike da sauri hannu rike da farar takarda tana tafiya tana duba aikinta ta nufi office din mr ATA har a lokacin yana tare da sectary dinsa suna tautaunawa kai tsaye ta shigo batare da neman izini ba ta soma mgn "sir! "bata kai qa fad’ar abinda ya shigo daita ba taji sautin muryarsa a tsawac"out !tsaye tayi sororo tana dubansa cike da mamaki da jin haushi disgin da yayi mata gabadaya jikinta yayi mugu mugun sanyi ya waigo inda take tsaye rike da farar takarda gbdy ta kasa kwakwaran motsi a waje .”






"nace out dan kin wani tsaya da wad’an banzayen idanun naki kina kallon mutane .”ya fad'a a tsawace bata san sanda ta juya a fusace ba har ta kusan kai bakin glass door din ta sake jin sautin muryarsa " ki koma bakin kofa Kiyi knowking idan an baki izini sai ki shigo “oya leave."wani irin kunya taji ya kamata ta juya tana sauke numfashi da ajiyar zuciya tunda take arayuwarta bata ta’ba jin kunya irin na ranar ba ,har ta kai bakin kofa ta d’an juya baya har lokacin idanunshi na kanta ya hura mata hanci yana watsa mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login