Showing 171001 words to 174000 words out of 178062 words

Chapter 58 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

na second goma bai iya aikata komai ba ta cigaba da magana “dan Allah sir kayi hakuri da sultana ka barta ta cigaba da zuwa aikinta dan ni na yafe mata coz I think she’ll not do it again in sha allahu .”haushi yaji har cikin zuciyarsa ”.bai sanda yayi magana a harzuke ba“Idan ke sha sha ce ni bashi bane idan ke sallamamiyar zuciya gareki ni ba itace dani ba nasan me nakeyi kuma nasan ciwon abinda aka min okay “.duk naji abinda kace amman kayi hakuri dan Allah dogon tsaki taja yana watsa mata harara yace “kin wani damu kanki ita datai laifi kinji ta bud’e baki ta bada hakuri !?“ya tambayeta yana sake jan tsaki “idan ta baka hakuri zaka hakura ?dan nasan dai dole zata ..”!
”shiiiiiii !”
Yayi mata alamar tayi masa shiru nan take tayi tsit ta shiga taitayinta tun kafin itama ta samu nata marin sai daya numfasa kana yace “idan kina da abunyi je kiyi dan ni bani da lokacin ‘bata wa akan wannan nonsense girl din” ya fad’a tare da mikewa tsaye ya shige d’akin dake cikin Office dinsa .”






ahankali tabi bayansa da kallo dole bata yadda ta iya ta fito anan suka ci karo da madam some ta qarasa kusa daita tana gaisheta tare da fad’a mata an gano wanda ya d’aukesu hoto sai dai bata fad’a mata ko wacece ba “kai marayama amamn gaskiya naji dadi sosai da’aka gano ko waye ,wallahi mr ata yayi min qoqari sosai banida abinda zance masa dan allah ki tayani masa godiya” ai ke din tabance a zuciyarsa sau nawa zan fad’a miki matsyainki a wajensa ?mutane nawa ne sukai aiki dashi amman ban ta’ba ganin wacce ya damu da damuwarta ba kamarki wanda hakan ke nuna alamun yana matukar sonki ne “haka dai kike fad’a amamn ni walalhi bazan ta’ba yarda ba, dan maganarki ma mamaki take bani ta yaya hakan ma zai kasance gara ma idan kince tausayina yake ji zan fi yarda da hakan amman batu na maganar so kam babu alamunsa saboda shi kulkum yayi min wani taimako cewa yake akan baya son ya samu matsala ne da aikinsa sai dai ban ta’ba jin ya burgeni ba kamar yau dan ya kwantar min da hanakali sosai .”




“da fari yasa naji zan iya cigaba da rayuwata ko babu kowa ,yasa na daina kwana ina kuka akan damuwa .” “ke dai kinyi sa’a ko babu so kinsamu matsayin kulawa a wajensa wannan ma kawai abun godiya ne bare kuma mu musan akwai so wanda kema kinsan da zaman haka mryama tayi murmushi ta juya tana cewa “a’a ni dai gaskiya bansan da zaman komai ba tana daf da shigewa office dinsu madam some ta biyota “maryama waye ya d’auke hotunan?.”maryama tai shiru na second goma sannan tace “gaskiya ban so na fad’a ko waye ba dan duk wanda ya rufa wani danuwansa asiri ,to fa asirin kansa ya rufa kawai Abar magana kamar zai fi “okay shikenan amman jikina ya bani kamar sultana ce amman Allah ya Kyauta ta fad’a tare da juyawa ta koma mazauninta .”




Mr ata na zaune yana amsa waya sultana ta shigo Office din kamar wacce aka jeho kai tsaye ta soma magana cikin wata irin murya mai karfi wanda yasa mr ata yace “excuse me just give me fiver second, disconecting din kiran yayi tare da had’e hannuwansa waje d’aya ya rike ha’barsa dashi tare da zubawa sarautar Allah ido “ban san me na kashe maka ba arayuwar nan “baka san abinda kayi a yau din nan ba sake qara min tsanar maryama kawai kayi a zuciyata .”
“amman kasani zan baka mamaki kuma lallai kasa hankalinka da kyau akanta duk abinda zai faru ,dan duk abinda ya samu maryama kasani kai ne sila ,kuma ka sawa ranka nice nan sultana na aikata ,wallahi wallahi maryama ce zata d’auki zazzafan hukuncin abinda kayi min .”




jin ta ambaci sunan maryama ce zata d’auki hukunci yaji gabansa yayi mummunar fad’uwa a sukwane ya mike tsaye yana taku yana mata wani mugun kallo mai tarwatsa zuciya kafin a natse ya motsa lip’s dinsa “look sultan bazan ce karki yi duk abinda kike so ba ,kiyi komai kike so but kisani ni ne na wulakantaki idan abinda nayi miki wulaqanci ne ba maryama ba why not ni kiyi facing dina ni da nayi miki hukunci “.
“okay saboda kinsan ni ba abokin karawarki bane shine zaki huce akan maryama we’ll go and head dan girman Allah karki fasa ki tabbatar kinyi abinda kike son kiyi karki fasa amman kasani duk abinda kike ji dashi nafiki iyashi ya fad’a a tsawace yana nuna mata kofar fita da yatsan hannunsa “leave my office.”””




da sauri ta juya ta nufi kofar fita tana wani irin haki ,kamar wata zautacciyar mahaukaciya ta sauka zuwa qasa ta nufi inda motarta take da kyar ta lalaba ta shiga motarta ta zauna ta kifa kanta akan sitiyarin mota wani irin kuka ne ya kufce mata ba dan taso ba , tayita kuka sosai dan haka ne kawai zai iya sanyaya mata zuciyarta sai datai kukan mai isarta ba mai rarrashinta tukun tayi shiru taja motarta ta wuce gida sai dai aranta ta kudurta duk runtse duk wuya sai taga bayan maryama sai tayi mata abinda har ta mutu bazata manta daita arayuwarta ba .”tana isa gida ta zayyanewa aunty abida komai daya faru a Office jin abinda tace ta fadawa ata yasa gabanta yayi wani irin mummunar fad’uwa hankalinta ya tashi sosai tace “kinga babu kyau ire item wad’an nan maganganun wani Abu yaje ya sameta ace kece maganganunki sunyi tsauri dayawa me yasa baki kirani ba ?ko me yasa bayan yaga hotunan a wayarki baki dawo gida ba ?.”






kinga irin taurin kanki tunda kika tura wa wad’an da kike bukatar suga hotunan nace ki goge kika ki ban san meye amfanin zamansa a wayar ki ba gashi kin ruguza komai dan damar data rage mana kinsa ta subuce mana tayi shiru tana jan tsaki tare da neman mafuta dan dole su samo mafuta kafin komai ya rincabe masu mikewa tayi tsaye ta shiga Kai kawo acikin parlour’n tana Neman mafuta can ya tsaya cak tace “dole ki bashi hakuri .”wa kenan zan bawa hakuri ?”adam zaki bawa hakuri “I can’t aunty duk wannan wulakacin da yayi min kuma na bashi hakuri ?”mari har biyu fa yayi a gaban wannan tsinanniyar yarinyar wallahi idan ban kashe yarinyar nan ba hankalina bazai ta’ba kwanta wa ba..”Kinga sultana dole fa yanzu ki ajiye komai ki nemi adam ki bashi hakuri dan nasan halinsa mahaukaci ne na bugawa a jarida zai iya sakawa ‘batar dake kuma babu abinda za’ayi .”






Sultana tayi shiru tana dubanta tana mamaki “kinyi shiru kina kallonta sanin halinsa ne danayi dan ga hindu nan ta isheni misali tunda aka ne metà aka rasa da kyar uwarsa tasa ya fad’i gaskyr inda take kuma duk da haka baa bada belinta ba ana kan bincike akanta dan haka ki kirasa ki bashi hakuri tun wuri ki kuma janye kalamanki kar wani abu yaje ya samu yarinyar yace kece kinga kin sakamu cikin damuwa .”
Bana tunanin aikata hakan ,bana tunanin zan iya bashi hakuri “ni dai ki tabbatar anjima idan ya dawo kije ki bashi hakuri idan ba haka duk abinda yabiyo baya babu hannuna”ban gane hausar babu hannunki ba ?ai kece kuwa mai hannu dumu dumu aciki ma kuwa dan Ina zaman zamana kika janyoni cikin matseefar da bansan ranar fitata acikinsa ba “sultana daga abun arziki ?ina arzikin yake ?tunda nazo wani kwanciyar hankali na samu ?”kullum daga wannan matsalar sai wannan I can’t take any more kuma zance naje na bashi hakuri bazanje na bashi hakuri komai ba bare na janye wata magana da nayi duk abinda zai faru ya faru am ready to die “ta fad’a da qarfi har sai da gidan ya amsa sannan ta fashe da kuka .”




Ganin ta fita haiyacinta yasa aunty abida ta rungumeta zuww jikinta tana rarrashinta “kiyi hakuri sultana Nima bansan abun zai zama haka ba, nayi tunanin zai amince da aurenki cikin sauki , amman kiyi hakuri “aunty Ina tsananin son ya adam akan na rasashi wallahi gara na mutu “subhanallah!”ki daina fad’ar haka bama zaki mutu ba muryarta da sheshekar kuka tace “to kiyi wani abu ko kiyi abinda zaki cire min son shi ko kuma kiyi abinda zai aureni “ki kwantar da hankalinki sultana muddin Ina raye zaki auresa ko ya aureki da girma da arziki ko kuma ya aureki da tsiya amman wannna auren babu fashi sultana sai kin auresa wani irin naunauyen ajiyar zuciya ta sauke tana sake rungume yaruwarta ajiki aunty abida tai shiru kwakwaluwarta na tunanin abun yi .”






Wunin ranar cikin farinciki maryama tayi sa cike da farinciki ta koma gida tana shiga bangaren umma ta shige tana cewa” umma nah na dawo ta fad’a tare da zama a kusa da umma ta ajiye jakarta “sannu da zuwa ya aiki”?” wayyo allah umma na gaji sosai kaina ciwo yake amman kuma alamun sun nuna kina cikin farinciki ?”
“sosai kuwa ammn wallahi kaina ciwo yake bari naje na kawo miki magani ki sha umma ta mike ta shige dakin bata jima ba ta fito rike da magani “ungo ki sha zaki ji daidai ta kai maganin bakinta saurin runtse idanunta tayi dan ta tsani shan magani umma ta dafa bayanata tana shafawa
da kyar ta amince ta sha “sannu kinji !”yauwa bari naje na kawo miki abinci umma me kika dafa ne mutuminki na dafa” shinkafa !? sosai kuwa shinkafa da miyar dayen kifi nayi “wow umma wallahi naji dadi sosai amman bari nayi fresh up nayi sallah ta mike ta shige d’akinta bayan ta gama komai ta fito adaidai lokacin da tuni umma ta kawo mata abincin ta d’aura akan qaramin table tana zaune tana jiran fitowarta.”






ahankali ta zauna kusa da umma ta soma cin abinci suna hira da umma “amm ummah ina son na tambayeki wani abu ?”ina jinki misali mutun ne yake da zafin rai sosai sai dai yana da kulawa da duk wani damuwarka, idan kana cikin damuwa shima yana tsintar kanshi ciki kuma bai ta’ba cewa yana sonka ba hassalima idan magana zata had’aku dashi maganr kaje kayi aure yake maka , amaman mutanen dake tare daku sai suna masa kallon yana sonka ne kuma umma kinsan wani abu, shi dai wannan mutumin ya dawo daga baya yace a auresa batare daya furta kalmar so ba .”ta qarasa maganar tana kallon fuskar mr ata acikin kwayar idanunta”umma tayi shiru tana saurarenta.”ahankali maryama ta numfasa sannan ta cigaba da magana “umma Ina son ki fahimtar da wani abu a cikin maganata .”?




“eh to ni dai abinda na fahimta hakan zai iya yuwuwa ace so ne, saboda kowani d’an adam da yanayinsa da kuma yanayin yadda yake shigar da soyayya rsa,” su waye wadan nan mutane ?” “amm wasu mutane ne a office dinmu”maryama kodai kice da mr ata?umma tayi mata tambayar kai tsaye “ware idanuwanta tayi tare da cewa “kai no no haba umma ina ni ina shi wannan mutumin da bai da sakin fuska ,ai muddin ya zamo mijina to nasan kwanaki da allah ya bani a duniya bamasu yawa bane .”ta qarasa maganar tana dariya sun jima suna hira maryama tayiwa umma sallama ta shige dakinta ta kwanta zuciyarta fess babu wani alamun damuwa sai dai hakan nan zuciyarta ta dinga tunanin mr ata wanda ya zame mata jiki tana son raba zuciyarta da wannan tunanin amman abun ya citura most especially a yau din nan ahankali ta gyara kwanciyarta tana sake rungume pillow ajikinta tana jin kamar shi ta rungume .”




Bayan kwana biyu akayi ma maryama salary sannan ranar ta kasance babu wani aiki a Office dan duk wani aikin da’aka bata ta kammala dan haka tayi tunanin da zaman da take ta tashi taje tay masu siyayya abubuwan da basu dashi a gida ta mike ta fito rataye da jakarta ta fito ta sanarwa madam some sannan ta sauko zuwa qasa .”
tunda ta sauko taji gabanta yayi wani irin mummunar fad’uwa sai dai bata kawo komai ba ta biyo dogon titin da zai fito da mutun zuwa babban titi stil dai gabanta bai daina fad’uwa ba duk ilahirin jikinta yayi mata wani iri taji kamar ana mganrta a baya , ta tsaya tare da juyowa wasu mutane tagani sanye da suit suna magana wanda ke nuna alamun bama daita suke ba dan haka ta sake juyawa ahankali ta cigaba da tafiya har ta fito bakin titi kai tsaye mota ta shiga zuwa bank mafi kusa da inda take ta ciro kudi masu yawa ta shiga wani shago siyar da Kayan sakawa na mata dana maza ta siyawa aunty da umma kala biyu biyu ,habib ma haka da takalmin itama ta siyawa kanta dogayen riguna guda uku kowanne da kalar takalminsa da jaka ta biya kudin ta fito ta shiga wani super market domin siya masu kayan kwalama ,anan ne ta hadu da wani alhaji mansoor wanda ya nuna qaunarsa agareta baro baro .”




ba wani dogon turanci maryama ta aminta dashi saboda daman irin wannan damar take nema wanda zai aureta ido rufe tunda bata da wani tsayayye maganar mr ata kam shirme ta daukesa duk da tana tsananin jinsa aranta .”nan sukai musanyar number da Alahji mansoor dan zuciyarta ta natsu dashi haka zalika bugun da zuciyarta take ta kau har tai tunanin watakilla haduwarsu dashi ne yasa taji wannan yanayin ajikinta , taiwa kanta fatan Allah yasa haduwarsu ta zame mata alkhairi arayuwarta alhji mansoor ne ya biya maku kudin shopping din da tai ya kuma kawota gida bayan ta shigar da siyayyar datai ciki ta dawo inda alhaji mansoor yace mata shi fa da gaske aurenta yake so yi kuma cikin kankanin lokaci sai dai yana da mata biyu da yara takwas kai tsaye maryama tace ta amince sai dai ta fad’a masa tana zuwa aiki .”






Yace ai wannan ba matsala bane bazai hanata zuwa aikinta ba ,wannan ne abinda ya qara sa zuciyar maryama ta sakankance dashi har ma tayi tunanin zuwa satin da zasu shiga zata gabatar dashi ga iyayenta ,tun daga wannan lokacin alhji monsoor ya fara zuwa zance gidansu maryama wanda hakan yasa gabad’aya maryama ta cire tunanin wani adam aranta ta soma saka tunanin alhji mansoor aranta duk lokacin daya so ganinta yana ganinta ranar da suka cika sati biyu da haduwa ne yazo wajen aikinta suna tsaye dashi ajikin motarsa kwatsam sai ga mr ata ya fito daga masallaci tun daga nesa ya hangota tsaye tare da alhji mansoor ,gabansa ne yayi wani irin mummunar fad’uwa ganinta tare da wani Wanda bashi ba ,nan take zufa ta shiga karyo masa .”ahankali ya cigaba da d’aga qafafuwansa ya zagayo ta bayansu ya tsaya ta yadda bazasu gansa ba sai dai qirjinsa ne ke wani irin bugu da matsanacin qarfin gaske “cike da tashin hankali ya zuba duka hannunwansa cikin aljihunsa .”




Tunani yake anya kuwa ba mafarki yake ba ?”maryamarsa ce tare da wani kato tsaye tana washe masa baki ?to ya bazaka ganta da wani ba tunda Kai ka kasa furta mata kana sonta ai dole ka ganta tare da wani “to kuma ai duk alamunta sun nuna tana sonka “okay kenan jira kake tace kana sonta ?”yayiwa kanshi tbayar yana sake shiga rudani da tashin hankali “adam kaga irin abinda zaka janyowa kanka ko?“ka bud’e baki kace mata kana sonta ne matsala to ai gashi nan wani zai maka shigar sauri ?”yayiwa kanshi magana yana datse harshensa da qarfin .”ahankali ahankali yake jiyo duk hirarsu da suke sai dai zance auren da yaji suke har da tsare tsare yadda komai zai guduna shine yafi komai daga masa hankali “aure kuma maryama “?






Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.






Page 49




jijiyar kansa ne ya amsa har zuwa kan babban d’an yatsansa, ahankali ya zura hannunwansa duka cikin aljihun windonsa ya shiga d’aga qafafuwansa da kyar, qirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin qarfi ya zagayo gabansu ya tsaya nisa kad’an da inda suke tsaye tare da tsura mata kwayar idanunshi dake cike da tashin hankali .”cikin sa’a shayayyun idanun maryama suka sauka akanshi gabanta ne yayi mummunar fad’uwa yayinda gbad’aya annurin dake kwance akan fuskarta ya d’auke cak ta daina murmushi da jin maganar da alhaji mansoor yake mata .”
nan take jikinta ya kama kyarma komai na duniya ya tsaya mata ,ba wanda yace ma d’anuwansa komai daga maryama har mr ata da alhaji mansoor wanda ya dawo tamkar mutun mutumi tsaye yana kallon yadda one time yanayin maryama ya sauya sakamakon ganin mutumin dake tsaye a gabansu .”






zufar data tsatsafo a saman goshinta ta share tana cigaba da kallon mr ata dake tsaye tamkar mashi kafin ahankali tayi kasa da kanta tare da kamo yatsun hannunta tana wasa dasu dan bazata jura irin kallon da yake mata ba mai d’auke da ma’anoni iri iri ,tasan waye mr ata kuma tasan halinsa tamkar yunwar cikinta wannan kallon da yake mata bana banza bane“.
sosai take jin wani iri a gbdy ilahirin sansar jikinta “ai dole duk wanda mr ata ya tsurawa wad’an nan tsumammun idanunwan nashi masu firgitarwa dole sai yaji wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login