Showing 69001 words to 72000 words out of 178062 words

Chapter 24 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

anji cewar oga amar "ai soyayyar yarinyar nan tana wujijjjiga rayuwata ,ni yanzu kiran da nai maka nace mu hadu anan shawara zamuyi ina son naje nema aurenta "
“waya fada maka barno gabas take ,suka kwashe da dariya "suka samu waje suka zauna alokacin da karfe takwas ta buga wanda zuwa wannan lokacin wasu daga cikin maaikata sun fara zuwa "ina jinka abokina wannan labari yafi kowani irin labari dadi domin ina matukar son na g maryama a qarqashinka ."




Mr ata ya numfasa kana ya cigaba da magana a natse "ina son naje neman aurenta koma nace ina son tazama mallakina acikin tsukukun lokacin nan dan sai nafi samun kwanciyar hankali idan na aureta ahankali kuma sai na shigar da soyayyata sai dai kasan wani abu bana son sweetheart da kowa nawa su san da wannna auren zai tsaya ne a tsakaninmu dagani sai kai ita kanta yarinyar bana son tasani yanzu “ya qarasa maganar tare da yin shiru ya zuba ma oga amar idanu yana son yaki me zai ce "Ko me yasa ka zabi kayi haka ?bayyana maryama a halin yanzu zai iya janyo min abubuwa da yawa. abu na farko idan sweetheart da sauran yan’uwana suka san mafarkina ce zata fuskanci mummunar tsana daga garesu kasamcewar naki zama da zabinsu abinda ka rigada kasani ne bazan d'auki raini ga matar danafi so ba haka zalika bazan wulakanta yanuwana da Mahaifiyata akanta ba,shiyasa nake son na aureta a boye ,muyi rayuwarmu dagani sai ita da yaran da zata haifa min ".






numfashi oga amar ya sauke "amman kace itama maryama din baka son tasani ?"a yanzu ba amman daga baya ai dole zata sani idan lokacin da ya kamata tasani yayi, zan aureta a yanzu na dinga janta ajikina ina d’an rage zafi "tunda ita shasha ce da zata yarda ka dinga ta'bata batare data san meye matsayinta ba "wannan kuma matsalarta ce tunda ni nasan matsayinta ai shikenan."kai dai wallahi mugun jarababbabe ne “sosai kuwa number one ma ni kad'ai nasan irin dauriyar da nake akanta wallahi amar ina da mugun karfin shaawa akanta idan shaawarta ta taso mun kwana nake gabana a mike duk na rasa yadda zanyi ,inga ya maka jijiya ta bata kwanciya har sai asuba tayi wata rana ma haka zan yini kaga gara nasan abunyi.” naunayen ajiyar zuciya oga amar ya sauke yana cewa "ni dai gsky kayi tunani sosai akan wannan raayi naka gara ka fahimtar daita idan yaso sai abar maganar daga kai sai ita sai kuma ni da zan zamo sheida saboda halin rayuwa ".




“kai ma kazo da magana mai kyau amman kasan wani abu ?oga amar ya girgiza masa kai "bazan iya fahimtar daita da bakina ba "akan wani dalili ?i don’t know,kai dai kace tsoronta kake ji “wani irin tsoro kuma amar yarinyar da loma d'aya zanyi daita na gama daita ni kawai damuwar sweetheart ne data yanuwana ce banaso, sun dade suna tautaunawa a qarshe suka ajiye ranar da zasuje su samu baba gali ."qarfe goma daidai oga amar yayi masa sallama ya wuce yayinda maryama ke ta faman kuka surayya wacce ta shigo ta isketa tana kuka ta fara rallashi tana tambayarta dalilin kuka sai dai bata ce mata kalallahu ba dan haka taje ta kira yusura itama dai tmbyrta dalilin kukanta tayi a qarshe tace "ko dai mr ata ne ?"maryama ta gyada mata kai alamun eh me ya had’aki dashi ?tayi shiru dan bazata iya fad'a ba ,da kyar yusura ta rarrasheta ta tsaida sheshekar kukanta tana cigaba da tmbyeta "aikin banza kawai kuna damun kanku akan wannan figaggar yarinyar kuma tunda kukaga tayi shiru har yanzu taki cewa da ku komai saboda munafunci da shegen zurfin ciki irin nata ai sai ku rabu daita haka ".sultana dake tsaye a bakin kofa ta fadi haka tana mazurai yusura kam ta yarda maryama tana da zurfin ciki sosai "ban wani d'auki lokaci mai tsawo daita ba amman na karanci maryama din nan tana kafiya da zurfin ciki maryama ta kalleta da idanunta da suka canza kala "kina kallona kamar karya na fad'a akanki “tana gama fadar haka maryama ta d'auki jakar aikinta ta rataya a kafad’anta ta fita ta bar office din da idanu suka bita da kallo ."




Har qarfe biyu da wasu mintuna maryama bata dawo office ba, yayinda mr ata ya shiga office din yafi sau babu adadi amman bai ganta ba ya yi mamakin inda ta shige har zuwa wannna lokacin dan ya lura tun shabiyu bai sanyata acikin kwayar idanunshi ba kuma shi bai ga fitarta ba dan hk ya kira layinta bai shiga ba ,hankalinsa ya dan tashi ya kira madam some zuwa office dinsa bayan ta shigo ya kalleta atsanake yace "ko maryama tana ina ne ?na ganta dazu da safe ,”yanzu nake magana "eh gsky bansan inda taje ba amman yau din dai kamar bata da lafiya dan naga yanayinta wani iri kamar ma tayi kuka amman naga su surayya suna ta rarrashinta nafi tunanin ko akwai matsala daga gidansu ne sir "numfashi da ajiyar zuciya ya sauke atare yana cewa "you can go "!ta juya a natse ta fita .”




Ya mike ahankali ya nufi d’akin da camerar cctv suke masu kula da bangaren wajen suna ganinsa suka mike cike da girmamawa domin dai duk lokacin da zasu ganshi da kansa abu ne mai mahimanci ya kawosa ,mr ata ya zauna a mazauninsa na musam man wanda an tanadi wajen ne dan shi kad’ai camera mai kula da bangaren office dinsu maryama zuwa first flow ya bukaci gani tukun, da sauri suka fara tariyo masa wanda zuwa wannnan lokacin ya hade hannunwansa duka waje d’aya ya tokare habarsa yana duban screen din tv ahankali ya fara kallon d’aukar yau inda mutane da suke shiga da fita har yazo kan shi da maryama yayi shiru yana kallon shi daita sosai yaga yanayinta cikin tsananin damuwa d’aukar tayi gaba zuwa inda su surayya da yusura ke tsaye akanta da sanda sultana tayi mgnrta ta juya ta bar office din kuma at the same time alokaci maryama ta mike tana goge hawaye ta fice daga ma’aikatar gabad’aya .




"me yarinyar nan take nufi dashi ?"yasan duk akan abinda ya faru ne da safe ta kama hanya ta wuce gida abunta ahlin lokacin tashi bai yi ba yayi kwafa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ."bayan ya gama ganin komai ya mike ya fito daga office din cike da jin kai ya koma office dinsa ransa a matukar bace dan ganinsa maryama tayi mugun mugun rainashi babu wani maaikaci ko maaikaciyar da zata masa haka ya d’auka itama dan matsayinta ne yake d’aga mata kafa yaja tsaki yana rike kugunsa da hannu d’aya,bangaren maryama kam kai tsaye gidansu ta wuce abunta, ta zarce zuwa bangaren aunty tayi kwanciyarta akan doguwar kujera tare da kashe wayarta nan da nan bacci ya dauketa sakamakon daman daren jiya bata runtsa ba ."




******


Qarfe takwas na dare da mintuna ashirin mr ata ya tako cikin parlour'n Mami wanda babu motsin kowa sai na na'urori da kuma hasken qwayaye, samanshi ya nufa kai tsaye yana furzar da hucin iska daga bakinsa yana tuno gamuwarsa da maryama d'azu da safe sannan zuciyarsa na tafasa akan barin office da tai batare da neman izininsa ba gamuwarsu a gobe kawai yake jira dan lamarinta na matukar 'bata ranshi ya tabbatar da cewa ta tafi ne dan musguna masa ta nuna masa iyakar shi wanda hakan ya sake tabbatar masa da bai isa daita ba kamar yadda ya isa da duk wanda ke qarqashinsa ,shima kuma yana nan akan nashi qudurin da raayi bai ga abinda zai sanya shi daga mata qafa ba koda kuwa suma zai dingayi akanta ko mutuwa zai yi sai ya juyata ya tankwasata ya laddatar daita, qarfin soyayyarta bazai sa ya juri iskanci ba haka zai aureta ya kasa zama tsayayyen nmj acikin gidansa "never maryama dolenki ki bini sannan ki zauna lfiya."






Tsab tsab ya iske dakinsa koina neat sai kamshi turare yake wannan kuma yasan aikin sweetheart dinsa ne ita ke tsayawa akan masu gyara masa daki
A natse ya qarasa bakin gado ya soma fidda kayan jikinsa byn ya gama cirewa bandaki ya shige yana niyyar hada ruwan wanka,yaga an had'a masa tsayawa yayi cike da shakku yana tunani ta ina aka samu haka? , cikin kokwanto ya sanya hannunshi cikin ruwan, anya ba jinnu ke neman yi masa wasa da hankali ba,dan tun da yake sweetheart bata ta'ba sawa an masa haka ba ,share mamakinsa yayi yayi wankan ya fito ya saka kayan shan iska farare sol ya fito yana taka step da kyar turus yayi sakamakon ganin maryam da sweetheart tare da aunty shahida zaune suna magana ganinsa yasa duk sukai shiru ya qaraso ya gaishe da mami da aunty shahida duk suka amsa masa ".maryam tayi karfin halin gaishesa duk da tasan bazai amsa mata ba "ina yini yaya ?"shareta yayi kamar yadda ya saba “ adamcy maryam na gaisheka ".




“lafiya!” ya fad'a atakaice sannan ya zauna mr ya daura kafarsa daya akan daya ya dauki remut ya kunna tv ya Kure volum alokacin da aunty shahida da maryam suka mike "to mami mu mun wuce sai an kwana biyu kuma "Allah ya kaiku lafiya zan lekoku in sha allahu maryam ki kula da kanki ki dinga shan maganinki akan lokaci Allah ya sauke min ke lafiya bai ji abinda suke tautaunawa ba shi dai yaga sun fice ko cikakken minti goma basuyi ba sai ga baba qaramin ya shigo kamar wanda aka jehosa kai tsaye kan mr ata yayi yana nunasa da dan yatsa yana cewa "duk tsarinka ne bana wacce sabuwar maaikaciyar bace maryama akace sunanta ko me ,to kasani na samu labari komai kuma bamu yarda ba bamu amince ba ayi wani aiki a boye sai dai a bari lokacin da kowa ya hada nashi sai ayi atare" .




Baba qarami ya kalli inda mami take zaune yana sauke numfashi “ki gaya ma danki dan nasan yana da matukar taurin ka idan kuma yayi Kuskuren yin yadda nace zai hadu da mummunar bacin raina da bai ta'ba gani ba ."wai meke faruwa ne baba qarami kai da danka kullum sai a jiku "karki qara cewa dana dan ba dana bane nasan ya'yana shima yasan ubansa numfashi mami ta sauke kana tace "shikenan Allah ya kyauta karka damu baba qarami zai ji maganata in sha allahu company AGC din ma zan sa ya bar maku tunda shi allah ya rufa masa asiri yafi qarfinsa " okay haka ma zaki ce ?to me kake son nace wannan yaron danka né halak malak kace a'a ."adamcy danka ne banga amfanin idan zakayi mgn dashi ba ka dinga daukar zafi ,idan kabi shi a hankali zai yi abinda kake só ta juya inda mr ata yake zaune wanda yayi kamar tunda akayi duniya bai san da wani halitta baba qarami ba bare ma yasan me yake cewa .”




"adamcy tashi kaje dakinka zan kawo maka abincinka "zazzafan numfashi ya sauke sannan ya yunkura ya tashi ya wuce cikin zafin zuciya saka makon bai samu damar fadawa baba qarami mgn ba kuma daman mami tayi haka ne saboda gudun abinda zai biyo baya ."da kyar mami ta sauko da baba qarami akan lallai adamcy zai janye akan komai suyi duk yadda suke so jin haka ya hakura sai dai tafiya yayi yana bambame yayinda mr ata ya shiga zariya a parlour'nsa goye da hannuwansa duka abayansa tunanin wanda ya fad'a ma baba qarami shirin maryama yake." tabbas ko waye yasan bai wuce sultana ba saboda da ita aka shirya komai . tafiya ya fara yi acikin parlour'n lallai tayi haka ne dan ta janyowa maryama mummunar tsana daga garesa amman shi hakan ba damuwarsa bace dan zai iya karawa da kowa most especially akace za'a ta'bo masa zuciyarsa , abarshi shi a karon kanshi yayi mata duk abinda yaga dama amman wani yayi mata he can't take it sai inda qarfinsa ya qare,da fari bai yi suppoting din plan din maryama ba amman a yanzu zuciyarsa ta yarda kuma ta amince bazai karyar mata da gwiwa ba zai yi supporting dinta da dukkanin karfinsa da rayuwarsa.”








Mmn Sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 21


Mr ata na zagaya parlour’nsa mami ta turo kofar parlour’n ahankali ta shigo tare da mai aikinta tabawa wacce ke d’auke da madaidaicin tray mai d’auke da kular abinci da flak’s sai qaramin cup da spoon nacin abinci dana shan tea, ahankali ta ajiye tray din akan qaramin stood, cak mr ata ya tsaya daga zagaya parlour’n da yake sakamakon shigo warsu,ya tsura ma mami tsumammun idanunshi yayinda ta’bawa ta juya ta bud’e kofa ahankali ta fita, idanunshi na kan mami har sanda tayi taku uku ta qaraso inda yake tsaye zuciyarsa cunkushe da haushin baba qarami “tsayuwar me kake yi ?tayi maganar cike da tausasawa bai ce mata uhm ba bare uhm “kamata yayi ka zauna.“sweetheart bazan iya zama ba saboda wani irin zafi da suya zuciyata ke yi min “shiyasa nace ka zauna domin ba’a son mutun yana tsaye tattare da fushi dan komai zai iya faruwa dashi “madadin ya zauna kamar yadda mami ta ce masa sai ya cigaba da magana cikin zafin zuciya “sweetheart baba qarami yana son yaga kalar nawa rashin mutunci ,so yake na murje idanuna nayi masa rashin kunya fiyye da nashi “ban yarda ba kuma ban amince maka ba kada naji kuma kada na gani ina mai umartarka daka kiyaye harshenka akanshi .”








“Sai data numfasa kana ta cigaba da magana atsanake “bazan daina fad’a maka ba, baba qarami uba ne agareka, indai zaka iya masa rashin mutunci tabbas zaka iyawa tariq mahaifinka da yana raye “.da sauri ya shiga girgiza mata kai yana mai runtse idanunshi gam dan jin zafi da ciwon abinda ta fad’a ya d’auki mintuna goma idanunshi na runtse sannan ahankali ya bud’e tsumammun idanunshi ya tsurawa mami dake tsaye a gabansa tana faman fad’a masa mahimanci baba qarami agaresa “sweetheart nasan mahaifina “ mahaifina bazai ta’ba aibantani ba .”bazai ta’ba min irin abinda baba qarami yake min ba “ya qarasa maganar kwayar idanunshi na canza kala tamkar wanda aka watsa garwashin wuta acikinsu .”Shiru mami tayi tana dubansa a tsanake domin dai gaskiya ya fad’a amman kuma duk da hakan baba qarami yana da qarfi iko da mahimanci arayuwarsa
Numfasawa tayi irin nasu na manya sannan ta riko tafin hannunsa cikin nata tayi taku biyu tace “zauna ka samu natsuwa “!cike da zafin zuciya ya zauna yana dafe goshinsa da hannunsa d’aya “adamcy !”Mami ta kira sunansa “yana jinta amman bai amsa ba dan ko yace zai yi magana a halin da yake ciki maganar ba fitowa zatayi ba .”






“Adamcy ka qara hakuri da yan’uwan mahaifinka “ka cigaba da ganin girmansu sannan kayi masu biyayya albarkasu albarka mahaifinka ce .”sai lokacin ya samu damar sarrafa harshensa “sweet heart ki daina fad’ar haka ki daina bani umarnin most especially akan baba qarami dan bazan iya ba kuma ko yanzu darajanki yaci .“ya qarasa fad’ar haka yana cire hannunsa daga goshinsa ya cigaba da magana “aiki kuma da yake magana a kanshi wallahi wallahi sweetheart sai anyi aikin nan kuma kafin time din presentatoin day in yaso yayi duk abinda zai yi bazan bi umarninsa ba dan ba ubana bane kamar yadda ya fad’a nasan mahaifina shima yasan ya’yansa.” shiru mami tayi kawai tana kallonsa har sanda ya dasa aya sannan tace “da farko dai na gode daya ci darajata kuma naji dadin yadda kayi masa daman kullum mutun yana girma yana qara hankalina ne a duk sanda zai zo maka da fad’ansa na umarceka da kayi qoqari ka danne zuciyarka wata sai labari Allah kuma yayi maka albarka .”






“Sai magana ta biyu zan so ka hakura da aikin nan kai idan ma da hali ka bar masu kamfanin gbdy.” “a’a sweetheart karkiyi min haka dan girman allah ki cire bakinki acikin lamarin nan ki barni dashi tunda abayan ya’yansa yake mutane sai son zuciya kullum basa duba cigabanmu sai abinda zasu samu “.ya fad’a yana jan tsaki tare da fesar da iska mai zafi .”
“Nasani adamcy nasani baba qarami baya maka adalci akan ra’ayinsa dana ya’yansa amman duk da haka hakurin shi yafi ka bar masu ba dan komai ba sai dan a zauna lafiya ”hankalinsa amatukar tashe ya zamo jikinsa ya durkushe a gaban mami ya risinar da kanshi sosai yana cewa “sweetheart kiyi hakuri kiyi min fatan alkhairi in sha allahu wannan aikin shine aikin da zanyi na qarshe a AGC na tattara na bar masu kamfanin gabad’aya tunda haka kike so kike buqata ,daman wahalar abbana nake duba ba akan kamfanin nan ya sha matuqar wahala akanshi kuma mutanen dake amfana da kamfanin nan suna dayawa idan nã barshi baba qarami da ya’yansa zasuyi hamdame komai tare da yin babakeri amman tunda kince na hakura nayi amman dan allah ki barni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login