Showing 162001 words to 165000 words out of 178062 words

Chapter 55 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

sauke masa hucin numfashin Wanda dole tasa ya d’an lumshe idanunshi yana cewa “na fuskanci maryam kina son ganin iyakar taurin kaina ko“?”kayi hakuri amman ai na fad’a maka bazan ci..”oh my god wai me na fad’a miki ?”banace lallai kizo yau ba “kayi hakuri sir ni aikin ne gbdy ya fice min arai kar na dawo ayita samun matsala dani “da sauri ya mike tsaye tare da dunkule hannunsa ya naushi iska sannan ya dinga Kai kawo a filin office din inda idanun madam some da hankalinta yake kanshi sosai taga ya shiga damuwa maryama kuwa tana can rike da waya tana zance zuci “dokar daya kamata yayi akan matarsa ko damuwar daya kamata yayi akan matarsa ya tsaya yana yin abinda bai shafesa ba on expecting taji saukar muryarsa “karki ga na damu akanki ki d’auka wani dalili ne amman kisani zuwanki aiki gobe shine kwanciyar hankalinki wallahi muddin kuma kika yarda na tako gidanku zan miki abinda zai miki illa.”








Mmn sudais[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




45




zaro idanuwa maryama tayi jin furucinsa”tunda nemo miji zaki yi to ki aureni”ta maimaitawa kanta furucinsa na qarshe mai cike da tsarkakki ya da shiga tashin hankali,kai tsaye mgnrsa ta ta’ba kwakwaluwarta sannan ta samu kyakkwan mazauni a zuciyarta ,sai dai maganar tayi mugun gigitata ahankali ta kai hannunta ta murza idanuwanta domin tabbatarwa kanta gskiya ne ko kuwa mafarki take,bata gasganta a zahiri taji ya fad’i kalmar ba sai data d’an ciza yatsanta taji wani irin rad’adi sannan ta tabbatarwa kanta da shi din ne yayi maganar“.a matukar gigice take kallonsa hannuwansa duka zagaye da kungunta ya mugun tsareta da tsumammun idanunshi tamkar bashi yayi furucin ba “.






“ban ta’ba expecting ko da wasa irin wannan mganar zata fito daga bakinka ba ,plese sir can you say what you said again Ina son na sake tabbatar da naji abinda ka fad’a da kyau kuskure ne, ko kuwa da gaske ka furta wanan kalmar agareni ”tayi maganar jikinta na sake d’aukar rawa tamkar mazari ahankali ya lumshe tsumamun idanunshi tare da motsa lip’s dinsa “nace muddin kinsan baki da wanda kike so wallahi ni a shirye nake zan aureki.”sake ware idanunwanta tayi tana mai fuskantarshi sosai tasan ba da wasa yayi maganar ba tunda gashi har ya rantse .”
”maryama !”
Ya kira sunanta wanda yasa tsigar jikinta suka mike yrrrrr “ki aureni .”ya sake share mata tantamar dake damunta, bata san lokacin da ta saki murmushin yake ba tare da girgiza masa kai.”jikinta na rawa ta fara qoqarin zare jikinta daga nashi ya sake riketa da kyau ta sake girgiza masa kai a sanyaye alamun ya sakar mata jiki “.






“ki natsu maryama ki bani amsa zaki aureni ?”
Wannan karon da sauri ta girgiza masa tana waigen bayanta.” Sosai tayi kasa da muryarta
“ dan Allah sir ka sakar min jiki kar ummah ta fito ta ganmu haka “kinsan Allah ki bud’e baki ki amsa min zaki aureni ko a’a if not anan zan kwana.” “what !”ta furta a rud’e hankalinta na sake tashi ya d’age girarsa d’aya alamun”eh!”tayi Imani zai iya aikata abinda ya fad’a din dan haka cike da karkarwa tace “Ka kwana anan akan me zaka kwana anan ?”dan Allah sir Ina rokanka tare da girmamawa ka tashi ka tafi gidanka gun matar ka,dan wallahi idan ka qara wasu mintuna anan zan iya had’iyar zuciya .”tayi maganar tana sake waiga bayanta .”






gyara zama yayi sosai kamar yana parlour’sa ko na mami tare da sake mata riko mai kyau wanda ko maza biyu sun qaru akanta bazata iya kwace wa a hannunsa ba “dan girman Allah sir ka tashi ka tafi gidanka ka rufa min asiri Ina ni ina aurenka zan dai samu takala daidaini na aura …”maryama ta fad’a cikin marai raicewar murya tamkar zata fashe masa da kuka .”ganin idan batayi wani abu ba umma zata iya fitowa ta gansu haka idan kuwa hakan ta faru ta shiga ukunta dan bata san da wani ido zata cigaba da kallon umma ba ,idan tace abinda ya faru a hoto kuskure ne wannan dake faruwa yanzu fa “?.
a wani matsaya za’a kirasa dashi ?”dan haka cike da tashin hankali ta fara masa alamun kuka domin tasan shine kawai mafutar da zata kubutar daita daga hannunsa .”






ahankali ta cigaba da rokonsa tare da mutsumutsun kwacewa daga jikinsa tana furta masa kalmar” ka rufa min asiri idan umma ta fito ban san da wani kalma zan kare kaina ba .”
ganin haka yasa ya zare hannunwansa ajikinta ta mike da sauri tana sauke numfashi tmkr wacce tayi gudun tsere .”ya gyara zamansa sosai tare da jingina jikinsa da kujerar da yake zaune yayinda tsamammun idanunshi wad’an da suka fara canza kala ne tsaye a kanta, ya mugun tsura mata ido sai dai fuskar nan tashi a had’e take kwata kwata babu wani alamun annuri “kina rikon na rufa miki asiri kmr wanda zai yi wani abu dake byn taimakonki zanyi .“cewa nayi kawai ki aureni ba cewa nayi zan kwanta a mararki ba .”yayi maganar tsumammun idanunshi kyar acikin kwayoyin idanuwanta ba kunya ba alkunya ko alamun yaji nauyin fitowar kalmar daga bakinsa bai yi ba .”






nan da nan maryama ta qara shiga tashin hankali sai dai ta had’e fuskarta dan kar ma ya sake samun damar sake furta mata wata maganar iskanci dan ta fahimci ba kunya garesa ba duk abinda yaga dama shi yake yi ,haka duk mgnr datai masa dadi yake fad’awa mutun “.ni zan wuce ki fara shirin zuwa aiki monday “da sauri tace “nifa na fad’a maka babu wani aiki da zan cigaba da zuwa na hakura da aiki nan zan cigaba da zama a gida har zuwa lokacin da Allah zai fito min da miji “ki bar wannan maganr dan bazaki samu wani miji kina kunshe a gida ba , ni kuma da nace zan taimaka miki kince baki sona dan haka ki shirye ki fara zuwa aiki dan zai fiye miki samun kwanciyar hankali …..”






“nifa babu wani aiki da ..”wani mugun kallo ya d’auketa dashi wanda yasa da sauri ta datse harshenta zuciyarta na wani irin bugawa da sauri sauri .”anatse ya yunkura ya mike tsaye bisa qafafunsa yayi taku biyu ya tsaya a gabanta yana tura hannunwansa duka cikin aljihunsa .”amatukar firgice take kallonsa yayinda qamshin turarensa ya dinga Kai wa hancinta ziyara yana kashe masa sansar jiki lumshe idanunta tayi kamar mai jin bacci dan gabadaya yau din sai take ganin ya sake sauya mata daga mr ata din datasani zuwa wani mutun dabam “yaushe muka fara haka dake ?”tayi shir tare da sunkuyar da kanta tana Jin wata irin fad’uwar gaba mai qarfi from no where na shigarta wanda bata ta’ba jin irinsa ba a tun tsawon rayuwarta.”






“wato dan taji zai taimaka mata ya aureta shine har ta fara rainashi kenan ?”sosai tayi kasa da kanta dan bazata iya kallon fuskarsa ba ,sai dai jikinta wani irin kyarma yake tmkr mazari sakamakon idanunshi dake yawo a sansar jikinta .” lumshe idanunshi yayi na second biyu sannan ya bud’e su fes akanta ,sosai yaji zafin abinda tayi masa bai san dalili ba yaji ya d’aura maganartata acikin zuciyarsa daram sai dai bazai yarda tayi tasiri ba “muryarsa a kasalance ta fito
“ ki san Allah muddin banganki AGC ranar monday ba kullum sai kin gani a gidan nan kuma abinda kike gudun faruwarsa ne zai dinga faruwa dan bazan d’aga miki kafa ba .”ya qarasa mgnr batare da yasan ya fad’a haka ba kawai dai ya tsinci bakinsa ne da maganar “.






lumshe idanunta tayi tana mai sake shiga tashin hankali mai tsanani ,muryata can kasan makoshi tace “ai sai ka zo ka sani dole sai naje .”ya sake matsota yana shafa gefen fuskarta tayi saurin matsawa baya da sauri ya cafko tsintsi yar hannunta cikin nashi yana murzawa,kwayoyin idanunshi cikin nata yace “mryama speek loud !“.Ina son naji abinda kika fad’a yanzu “yayi mgnr yana sake murza tsintsiyar hannunta sai dai wannan karon da zafi yayi mata ,da sauri ta shiga girgiza masa kai tana waigen waige gab d’aya a rude take “okay zabi ya rage naki kizo ko karki zo abinda na sani ne bana magana biyu, kuma bazan fara akanki ba ,zabi ya rage naki kizo ko karki zo .”yana gama fad’ar haka ya sakar mata hannu ya juya ya fara tafiya ”




Ahankali tabi bayanshi da kallo yana taku a natse har ya fice daga parlour’n, da sauri ta dawo jikin widow parlour’n ta d’aga labule kad’an tana lekensa yana taku a natse cike da izza tamkar baya son taka kasa “ya salam !”ta fad’a tana dafe qirjinta da taji yayi mugun rike mata “.
maryama ta kasa matsawa daga jikin window tana tariyo abinda ya faru a tsakaninsu yanzu,.”duk maganganunsa babu wanda ta manta domin kuwa sun zauna mata daram kamar hadda acikin kwakwaluwarta sannan sunyi mugun tasiri a kwakwaluwarta har suna son suyi tasiri a gangar jikinta da zuciyarta .”ya rab meke shirin faruwa dani ne?mai yasa mr ata zai ce na auresa ?”me yasa nake Jin kamar ana zarar raina a duk sanda yake tare dani ?”shiru tayi tana sake nazarin maganarsa dan ta kasa bawa kanta amsa “anya mr ata ba sonta yake ba kuwa ?” wannan shine tambayar farko da zuciyar maryama ta fara yiwa kwakwaluwarta “kuma tambayar ta daki brain dinta sannan ta wuce har cikin zuciyarta “yes yes !! kamar fa alamunsa ya nuna haka!” zuciyarta ta bata amsa da hakan ta sake dafe qirjinta sosai .”




Ahankali taji tamkar ta kunno wa kanta wani emotion ne da take qoqarin dannewa acikin zuciyarta nan take taji hawaye ya fara zubo mata kan kuncinta ahankali ta fara rera kuka kasa kasa “idan har ya tabbata mr ata sonta yake kuma har ya kasa fitowa ya furta mata kuma yake son ta auresa matuqar ta auresa ba qaramin azaba da matsin rayuwa zata shiga a hannunsa ba koma tace tabani ta lalace dan tun ba’aje koina ba ya fara da taimaka mata zai yi Ina ga ta auresa ?” uwa uba yanayin da take ji akanshi ya bam bamta da sauran mazan “no no !!.” I can’t marry him ya Allah ka ji tausayina ka bani miji daidai dani dan wannan mutumin yafi qrfina kuma koda zuciyata ta kamu da sonshi wallahi sai nasa wuka na raba tsakanimu .”






Ahankali taji an dafa kafad’anta ta baya ,ta jiyo da sauri ganin umma yasa ta sake dafe qirjinta gam tana goge hawayen dake shirin sake gangarowa bisa kuncinta “har mr ata din ya wuce ne ?”ta gyda mata kai da sauri tana cewa”eh ya wuce “ya naga kmr kuka kika yi?numfashi kawai ta sauke dan bazata iya mutsa mata ba tunda tasan kukan take ,umma ta sake tambayarta amman taki bata gamsashiyar amsa “.to akan zuwanki aiki ne kike kuka ko wata magana ya fad’a miki “? still dai girgiza mata kai tayi “to me yasa zaki tsaya kina kuka ?” umma babu komai !”ta fad’a tana shesheka.”numfashi umma ta sauke tare da cewa “ikon allah haka kawai mutun ya zauna yana kuka to Allah ya Kyauta to amman idan kinji har cikin zuciyarki baki son zuwa aikin nan ki hakura babu lallai babu dole dan babu wanda zai takura miki shi yasa ma kikaji nace ya tuntubeki .”tana gama fad’ar haka ta juya ta barta ta shige kitchen tana tunanin me ya sakata kuka ?”Umma ta jima tsaye a kitchen tana qoqarin had’a masu abincin dare koda ta fito bata ganta ba dan haka ta wuce d’akinta .”








Acikin mota mr ata ya iske mb ya shiga ya zauna suka kama hanyar komawa gida mb ya d’an kallesa yace aboki hankalinka ya kwanta zuciya taga abincin ruhinta ”ya qarasa mgnr yana kallon gabansa yana murmurshi “babu laifi hankalina ya d’an kwanta tunda har na d’aura kwayar idanuna akanta “ata kana son maryama..” sosai mb ina sonta ina mata son da idan babu it acikin rayuwata rayuwata zata kare ne cikin garari da tashin hankali amman na rasa dalilin da yasa na kasa fad’a mata kai tsaye kuma wallahi ina son na fito na fad’a mata amman sai naji zuciyata ta kasa “girman kai da rashin son arainaka ne ya hanaka fad’a mata amman dai ya kamata ka d’aure at least tasan irin mutu war son da kake mata tunda ga dama ta samu ance aure za’a mata”friend do something before everything could have mess up to you .”




in sha Allahu i wil try dan ko yanzu nayi mata mgnr ta aureni !”yayi maganar yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa “kai Kai masha Allah mutumina ai an gama magana ,an gama wasan kawai game over sai mu fara shirin shan biki “tsaki ata yaja yana cewa “bata amince ba fa “yayi mgnr muryarsa a sanyaye kamar mai koyon magana” kamar ya bata amince ?” .
“am telling you!” yarinyar nan so take sai taga qarshena hankalinta zai kwanta mb ya saki dry mai qarfi yana cigaba da murza stearing “kar dai tayi wuji wuji da adamcy mami ?”ya qarasa maganar yana sake kwashewa da dariya numfashi kawai mr ata ya sauke tare da kamo lip’s dinsa na kasa yana cizawa a hankali “ka bita a hankali da sannu zata amince kasan ganin abun zatayi wani iri kmr shirin drama ne ace mutun kamarka zaka aureta batare da kuna soyayya ba ”yanzu dai mu ajiye wannna maganar in sha allahu komai zai zo da sauki maryama rabonmu ce da izinin Allah.”Allah yasa”ya amsa masa jiki a sanyaye .”






“ya kukayi daita batun cigaba da zuwanta aiki “ta amince ko kuwa “uhm ai yarinyar nan akwai d’agawa mutun hankali shiyasa wallahi nake jin bazan iya tunkararta da batu na soyayya ba gara kawai na aureta a aikace zata gane son da nake mata”Kai dan Allah kana ganin yarinya kmr mummuna inji cewar m.b “ya fad’a yana masa dariyar mugunta “Ai kana ganinta wallahi muguwar yar rigima ce ta bugawa a jarida.”
“ ai na lura da yadda take girgi zawa iyayenta kai alamun karsu amince” aikuwa zata janyowa kanta sabon tashin hankali domin kuwa bazan barta ba na dinga zuwa kenan Ina d’aga mata hankali har su fahimceni a qarshe su aura min ita kaga shikenan na huta .”mb yasa dariya yana sake dukan stearing motar “wallahi tunda nake ban ta’ba maganin mutun da girman kai da miskilanci mai cutar da kanshi ba kamar kai wai ka fito ka fad’a wa yarinya kana sonta ne abun kunya ko me ?ata ya girgiza masa kai “mb me yasa ka kasa fahimtata ne “ .?




“babu wani na kasa fahimtar ka,kawai kace tsoron yarinyar nan kake ji,kai yanzu a tunanin ka akwai halittar da zanji tsoro? ” gata kuwa na gani tsoron maryama kake ji “mb ba tsoro bane akwai dalilai sannan kuma wannnan yarinyar da kake kallo rikitacciyar yarinya ce shiyasa ma ta kasa fahimtata inda na dosa ko da yake har da kuruciya ke damunta ko nace irin matan nan ne da sai an fito an fad’a masu ana son su suke fahimta if not ko acikin kalamaina ya dace ta fahimceni .”






“Taya kake son ta fahimceka?”kai ma fa da naka kana da son takurawa rai dayawa tsoro ma zai sa ta kasa gane inda ka dosa da wannan tautauna war suka isa abdullahi estate mb ya sauke ata ya wuce gida.”koda ya shigo parlour’n mami babu kowa dan haka ya haye samansa ya kirata ya sheida mata dawowarsa .
bayan sallar Ishai bayan yayi wanka ya sanya Jallabiya brown colour mai gajeren hannu mami ta nufi samansa tare da d’aya daga cikin masu aikinta dake rike da trayn wanda ke d’auke da kayan marmari da hadin salad da qaramin flaks na ruwan zafi abayanta ta same mr ata zaune a parlour’n sa akan kujera hannunsa rike da remut yayi shiru yana kallon tv sai dai hankalinsa baya kan news din daake gabatarwa .har mami ta shigo bai san ta shigo ba mami ta umarci mai aikinta data ajiye trayn ta wuce cike da girmama wa mai aiki taja dan qara min table din glass din dake tsakitar parlour’n ta daura masa akai ta Kama gabanta inda mami ta qaraso inda yake ta girgiza shi sannan ya dawo haiyacinsa .”




Muryarta a sanyaye tace “adamcy me kake tunani haka ?”ya soma in ina yana cewa” babu komai ta zauna kusa dashi tana cewa “kace babu komai ?”ya d’age mata girarsa d’aya yana shafa sumar kanshi “ka fita cikin tsananin farinciki amman kalli yadda ka dawo kamar wani mara lafiya tayi mgnr tana kamo hannunsa cikin nashi inda nan take idanuwanshi suka sauka akan yatsun hannunta masu tsananin Kama dana mahaifiyar mryama “ya ka baro maryama fatan tana lafiya?”tana lafiya!”ya fad’a atakaice tayi shiru tana nazarinsa har tsawon minti biyar ta sake cewa “halan da kaje gidansu maryama wani abu tayi maka ?”ya girgiza mata Kai da sauri sannan ahankali yayi qasa da idanunshi ya zubawa yatsunta na qafa ido ya jima yana kallon yatsun kafafun mami da kuma hannunta yana son yayi mata magana amman yana tunanin yadda zata fahimcesa .”






yana kallonta ta mike ta soma zuba masa abinci tana magana cikin sanyayye yar murya “adamcy banason kana boye min matsalarka dan baka da wacce tafini kuma na jaka ajikina ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login