Showing 126001 words to 129000 words out of 178062 words

Chapter 43 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

arayuwata ina mutuwar son shi amman shi ko kad’an baya qaunar sanyani acikin kwayar idanunshi .”mai yasa ya bawa maryama mahimanci haka arayuwarsa in takaita miki aunty a irin soyayyar da yakewa yarinyar nan baya iya juyata a office komai taga dama shi take yi kuma yana kallonta bai isa yayi magana ba amman kuma nasan duk yana yin haka ne saboda yana samun wani abu agurinta ka rasa ma sonta yake ko kuwa saduwa yake daita .?”ni babu ruwana sultana da ma koma menene a tsakaninsu ni dai ya barta kawai ya fuskanceki kema Kinsan dole kema kiyi closing dashi idan ya kama ki mallaka masa kanki ne duk kiyi domin dole ki zama suruka acikin gidansu dan bazan bari wata mace ta sake shigowa cikin rayuwar adam ba never .”sultana tayi shiru kawai tana duban yayarta dake tsaye cikin tsananin tashin hankali anya kuwa zata iya wannan kasadar mallaka masa kanta fa ta ina ma haka zata kasance a tsakaninsu mutunin da ko second biyar baya bata za dai ta tuntubesa akan aure idan yaki kuwa zata bashi mamaki .”




*****


Washegari




Ahankali maryama ta shigo cikin ma’akatan sanye cikin doguwar riga baka mai ratsin ash colour ajiki tayi rolling din kanta da mayafi ash yayinda qafafuwanta ke sanye da bakaken flat shoe haka jikinta wani irin sihirtaccen qamshi mai sanyi ne yake fitarwa,jikinta a sanyaye take tafiya makale da jakar aikinta sai dai kallo d’aya zaka mata ka fahimci yau din tana cikin farinciki .”a natse ta shiga lifter zuciyarta da kwayar idanunta cike da tsananin farinciki son d’aura kwayar idanunta akan mr ata kofar lifter na gama bud’ewa ta fito tare da mutane dayawa kowannensu ya d’auki hanyar office din da zashi .”kai tsaye hanyar office dinsu ta nufa a natse ta shiga fuskarta d’auke da murmushi
ta gaishe da abokan aikinta sannan ta cire jakarta ta ajiye akan table daidai saitin kujerarta sannan ahankali ta kai kwayar idanunta zuwa ga office din mr ATA ta hango kujerarsa empty da alamun bai zo ba tai shiru kawai tana cigaba da kallon office din kuma tana tunanin kalmomin da zatai amfanin dasu wajen gode masa domin ya cancaci tai masa godiya na mussaman amman gashi bai zo ba har yanzu babu mamaki yazo ya fita ne ? zuciyarta ta fad’a mata haka .”






ahankali ta tsuke qaramin bakinta kafin ahankali ta fito zuwa inda ta hango madam some zaune ta qaraso tana gaisheta “good morning ma ?”
”mornig maryama !”ta amsa mata tana dubanta da kulawa “amm ko mr ata yazo kuwa ?”no !bai zo ba amman dai zai zo yana kan hanya “okay maryama ta fad’a tare da juyawa ta koma office dinsu ta zauna zuciyarta na cigaba da tunaninsa haka fuskarta na cigaba da bayyana farincikinta.”
Ko cikakken minti shabiyar batai da zama ba qamshin daddaden turarensa ya soma karasowa inda suke ta juyo zuwa bayanta nan take kwayar idanunta suka sauka akanshi yana taku ahankali cike da izza da isa yayinda duk taku d’aya idan yayi sai zuciyar maryama ya buga da qarfin gaske sakamakon qamshin turarensa dake kusantota .”
ahankali ya shigo office dinsa na farko inda madam some take zaune hannunsa d’aya cikin aljihunsa ,yayinda jikinsa ke sanye da wani had’ad’den suit brown colour ,suma kanshi dana fuskarshi na kwance luf luf kamar ta yan india madam some na ganinsa ta mike tsaye da sauri cike da girmamawa tace “good morning sir ?.”
”morning ! ya amsa mata atakaice sannan ya nufi kofar shiga cikin office dinsa ya zauna yana juyi akan kujera .”






ahankali maryama ta mike ta nufi kofar office dinsa ta turo kofar ta shigo ta tsaya a gabansa tana gaishesa “good morning sir ?” a natse ya d’ago tsumammun idanunshi wad’an da suka wadatu da gashin ido dana gira ya zuba mata tare da yin shiru yana sauraronta itama shiru tai tana kallonsa tana wasa da yatsun hannunta ganin irin kallon da yake mata yasa babu shiri ta sunkuyar da kanta qasa ta cigaba da murza yatsun hannunta dake tsarke cikin juna ta sake d’agowa ahankali fuskarta d’auke da murmushi amman nan take murmushi ya d’auke a fuskarta sakamakon ganin fuskarsa a had’e tamkar yadda ya shigo ,kwatakwata fuskar nan babu alamun fara’a bare annuri akan fuskarsa ,dole tasa ta shanye dukkanin wani farinciki da take tattare dashi .”




shiru tayi tana zazzare idanu kusan mintuna shabiyar bai ce mata kala ba itama bata iya ce masa komai ba tana dai tsaye a gabansa tana kallonsa ya mike tsaye ya zagayo ya wuceta tsaye ya shige d’aya daga cikin dakun nan dake cikin office din .”qirjin maryama na wani irin dokawa ta juyo da sauri tabi shi da kallon mamaki tamkar bashi ne jiya ya dinga bata kulawa ba “karfa yayi tunanin wani abu akanta alhalin ita tazo ne dan yi masa godiyar taimakon da yayi mata ,yayinda sultana wacce idanunta ke kansu tai murmushin jin dadi yadda yayi mata wulakaci “kad’an ma kika gani dan dole yayi miki wulakanci tunda ya rigada ya gama more miki albarka jiki ,amman kuma sultana ki natsu da kyau zai iya zamowa pretending yayi dan kwayar idanunshi kad’ai idan kika kalla kinsan akwai zazzafar soyayyar yarinyar acikinsu sai dai ga dukkanin alamun bai sheida mata ba ,kamata yayi ki bari maryama tasan irin son da kike masa ta haka ne kawai zata janye jikinta daga nashi .”






Wani irin wahalallen numfashi maryama ta sauke ta soma magana da zuciyarta“ki sharesa kawai ba sai kin masa godiya ba ,no no hakan bazai yuwu ba ga mutumin daya tayaka jin pains dinka ,mutumin da yayi qoqarin cire maka damuwar dake cikin zuciyarka ai ko babu komai ya cancanci kayi masa godiya koda kuwa bazai amsa ba.jiki a sanyaye ta fito daga office dinsa zuwa nasu ta tsaya dan gabad’aya ta kasa samun natsuwa bare ta zauna tunanin abinda zata kawai take “to ni yanzu me zanyi ? ” me zanyi “?yauwa nasan me zanyi !ta furta a fili lokacin data furta hakan sai da kowa dake zaune acikin office din ya kalleta .”da sauri ta dauki jakarta ta fita daga office din inda sultana ta mike da sauri tabi bayanta tana son taga inda zata.”ganin ta fita daga maaikatar gabadaya yasa ta dawo .”






Maryama bata d’auki wani lokaci ba ta dawo still dai ta kasa samun natsuwa dan ko aikin da madam some ta ajiye mata bata bi ta kansu ba babban burinta tai masa godiya sultana ta kalleta a tsanake “meke cikin zuciyar maryama yau kamar tana son furta wani abu mai mahimanci ga yaya adam I most find what’s the matter maryma ta sake kallonsa alokacin daya fito yana waya “ni na rasa ma me zanyi gabad’aya yanayinsa yau ya bani tsoro ta fad’a a zuciya inda sultana tazo ta tsaya a kusa daita tana cewa “lafiyarki kuwa maryama “?“me kika gani ?maryama ta tambayeta fuskarta babu yabo babu fallasa “abubuwa dayawa na gani !” “sultana abubuwa dayawa kuma ?”maryama ta tambayeta, ta gyada mata kai alamun eh “amman kuma babu komai ai,” amman me yasa kika kasa zaune kika kasa tsaye kike ta zariya office din d’anuwana bayan nasan babu aikin daya baki ?”am babu komai sultana kawai dai Ina son na gode masa ne saboda ya taimakeni.” tayaya akayi ya taimakeki ki fad’a min dan ina son sani “?mr ata yayi min taimakon mai girman da wani dan adam ya kasa min a jiya na d’auki tswon lokacin ina cikin damuwa sakamakon mutuwar mijina amman a jiya yayi silar yaye min wannan damuwar ya taimakeni wajen dawo min da farincikina shiyasa nake son ganinsa na gode masa .”




murmushi sultana tayi tana cewa “wannan bashi ne asalin gaskiyar abinda ke ranki ba akwai wani abu dabam acikin zuciyarki da kika boye .”ta fad’a tana kallon tsakiyar idanun maryama “no sultana babu komai acikin raina bayan wannan karki manta mr ata matsayin mai gidana ne kawai dai godiya zan masa bayan haka wallahi babu komai acikin zuciyata “lallai ya tsaya amatsyain babu komai sultana ta fad’a mata hk cike da gargadi har maryama zatai magana sai kuma tayi shiru ta fasa cewa komai ta zaro takardar zanenta tana mamakin maganr sultana ”lallai ya tsaya amatsayin babu komai ta sake maimaitawa kanta maganar sultana na qarshe tana mata wani irin kallo mamaki to me take nufi daita ?.”






can bangaren mr ata kuwa kawo qarshen wayar da yake yayi da cewa “okay zan duba thank you sannan ya ajiye wayar ya maida tsumammun idanunshi zuwa ga glass din office dinsu maryama ,ya d’an kalleta yana jin wani irin magadisun sonta na shigarsa ,kafin ahankali ya mike yasa hannunsa d’aya cikin aljihunsa ya bud’e kofar ya fito yana cewa madam some “ina mukalan motocin da’aka kawo “?gasu anan sir !”okay biyoni dasu “okay sir ta bud’e doruwar data ajiye ta kwaso “kai tsaye office dinsu maryama ya shiga ya tsaya yana cewa “guy’s!gabad’ayansu suna ganinsa duk suka natsu suka tattara hankalinsu garesa cike da girmamawa madam some ta tsaya kusa dashi inda hankalin maryama da idanunta suke kanshi tana qare masa kallo tsab tare da nazarinsa tana son gano wani abu atattare dashi cikin tunanin da take ta soma jiyo sautin zazzakar muryarsa mai bugar da zuciya tare da sanya natsuwa a zuciya “some ki fara raba masu”. d’aya bayan d’aya some take mika masu keyn din motar benz new model “lokacin data kawo kan maryama yace “bani nata !”babu musu ta mika masa ya jefa cikin aljihunsa hakan bai damu maryama ba kamar yadda taga yanayinsa mutum kamar hawainiya kamar bashine jiya yay silar cire mata damuwa ba .”wannan shine kyautarku na presentation din da kuka gabatar “.nan take office din ya kaure da hayaniyar godiya ,yayi saurin dakatar dasu ta hanyar d’aga masu hannu “bana bukatar godiyarku sannan bana son ganin kowa yau din nan a office dina duk wanda yake da wata bukata ya samu some yana gama fad’ar haka ya juya ya fita inda maryama ta mike ta biyosa da sauri tana cewa “sir !”go back to your office …”






cak ta tsaya qafafuwnata na d’aukar rawa “me ke faruwa dashi ne yau ?” tayiwa kanta tambayar tana mai jin wani irin tashin hankali mai tsanani yana shigarta “bayansa ta cigaba da kallo har sanda ya qarasa shigewa office dinsa ya zauna jikinta a sanyaye ta dawo ta zauna inda sauran abokan aikinta ke cike da tsannain murna.”yusura ta matso kusa daita ta dafa kafadarta tana cewa “lafiya maryma meke faruwa mr ata ya bawa kowa kyautar mota amman ya hanaki ?”I don’t know yusura ban san meke faruwa ba bansan dalilinsa ba but is like sir his not in good mood today ki natsu sosai maryama kiyi tunani baki yi masa laifin komai ba dan bazai yuwu ace ya bawa kowa kyautar mota ya hanaki ba ?”tai shiru kawai tana tunanin mutumin da suka wuni dashi jiya kuma lafiya lafiya suka rabu dashi babu wata matsala kawai dai tafi tunanin miskilancinsa ne ya motsa. numfashi ta sauke da qarfi tana cewa” yusura kije kiyi abinda ke gabanki ni ban damu da kyautar motar da ya baku ba dan ko bai bani ba inada niyyar zan siya lokaci kawai nake jira ta qarasa maganar tana hura hanci tare da runtse idanunta tana mai jin zafin abinda yayi mata.”






Yana zaune rike da file yana dubawa maryama ta shigo office dinsa batare data tsaya neman izininsa ba ta tsaya a gabansa tare da goya hannunwanta duka abaya yayinda kwayar idanunta ke kansa muryarta a sanyaye tace “sir !”ya d’ago tsumammun idanunshi ya zuba mata sai data ji wani irin mummunar fad’uwar gaba sannan taji wani abu ya caki zuciyarta sai dai tayi qoqarin danne abinda taji a zuciya da sansar jikinta ta motsa lip’s dinta ahankali ta soma magana a natse “thank you for yesterday sir .”daman shine dalilin zuwana d’azu office dinka ba wani bane kawai ina son na gode maka ne bisa qoqarinka akaina domin ka dawo min da farincikina” shiru yayi kawai yana kallon kyakkyawar fuskarta da qaramin bakinta da burinsa a yanzu ya jisa cikin bakinsa yana sarrafasa tana gama fad’ar haka ta juya a natse ta nufi kofar fita batare datai masa maganar keyn motarta ba .”




ya ajiye file din hannunsa yana ya cigaba da kallon bayanta yaji kamar ana zarar ranshi ne a zaune da yake ,idanunshi na kanta har ta shiga office dinsu ta samu waje ta zauna ta soma aikinta batare da wata damuwa ba ,can bayan wasu mintuna duk abokan aikinta suka fita zuwa break ,office din ya saura ita kad’ai, ta mike a natse taje inda aka tanada masu ruwan zafi ta tara cup ta tsiyaya ruwan zafi ta had’a shayi ta soma sha ahankali tana lumshe idanunta ahankali mr ata ya tashi daga mazauninsa ya fito har zai karya kwana sai ya hango bayanta tsaye shiru bata ko motsi dan haka ya shiga office dinsu har lokacin tana tsaye hannunta rike da cup qamshin daddaden turarensa ne yasa ta juyo da sauri aiko taji tayi karo da mutu tsaye a gabanta da sauri ta d’ago shi din ta gani tsaye yana dubanta da tsumammun idanunshi gashi har ruwan tea ya d’an ta’ba masa gaban rigarsa a rikice ta soma cewa so..” sorry sir ban..”bansan kana tahowa ba.”




ya tsura mata ido kawai yana kallon yadda duk ta rikice tana faman furta masa “sorry sir “what happened maryama ?” ya sorry yaki qarewa haka ?”.maryama why are you so distracted ?” Sorry sir am ..” bai tsaya jin mai zata sake cewa ba ya fita ya koma office dinsa ya d’auki kwalin tissue ya ajiye akan table ya zari kwaya d’aya ya soma goge jikinsa.” oh Allah meke shirin faruwa dani ne yau ?” ta ajiye cup din hannunta da karfi akan table ta biyosa alokacin daya zauna yana goge saman takalmin qafarsa dan ruwan tea ya sauka akansu muryarta a sanyaye tace “kayi hakuri dan Allah ba da gangan nayi ba “is okay “.
ya fad’a yana lumshe ido .”Jin haka yasa ta juya tana mai jin sanyi aranta dan tafi son taji muryarsa da yanayinsa haka bata son ganinsa cikin fushi ko miskilanci domin hakan yana rikitata sosai if kar yayi wani tunani kamar yadda sultana tayi ai data bashi flowers din data siyo danshi ko hakan zai qara sanyaya zuciyarsa amman tasan halinsa bahagon mutun ne kuma gara ma da sultana tai mata gargadi dan shima haka zai fassara ta ,ta shigo office dinsu da niyyar ciro flower din da niyyar ta yar a shara sai dai taga wayam babu jakarta a inda ta ajiye babu alamunta ta sake dubawa taga babu, ina jakata yake kuma anan fa na ajiye jakata ?”ta fad’a tana duddubawa tana sake tambayar kanta, nan take ta rikice tana sake dubawa alokcin mr ata ya fito ya nufi qasa .”






tayi shiru kawai tana tunani inda jakarta ya shiga kafin ahankali ta jiyo sautin muryar sultana abayanta “kalli nan maryama !”maryama ta juyo da sauri tana kallonta, sultana ta nuna mata kan makeken table din mr ata jakarta dake makale da takada mai ruwan kasa data makala flower ta gani ajiye akai ,har ana iya hango flowers din dake ciki da sauri ta zaro ido waje tana cewa “mai yasa zaki min haka sultana ?”ai gode min ya kamata kiyi domin na saukaka miki “na sakaki ?me yasa zaki min haka “?no no !! yanzu me kike tunani idan mr ata ya gani ?”ta fad’a cikin tsannain tashin hankali gani nayi kina so kina jin tsoro har qarin taimako nayi miki ta yadda zaki samu shiga a wajensa ba dai bazakiji gargadin da na miki ba ai..”kafin sultana ta sake cewa wani abu da sauri maryama ta ra’ba ta gefenta ta nufi office din mr ata inda sultana ta tsaya tana kallon bayanta tana murmushin mugunta. “




cak maryama taja ta tsaya daga tafiyar saurin da take sakamakon jiyo qamshinsa datai ta d’an juyo ahankali shi din ne yana taku cikin yanyanayi na jin kai ,fuskar nan tashi a had’e ta gefenta ya ra’ba ya wuce yana satar kallonta hannu ta kai saman goshinta ta dafe tana kallonsa ta rasa meke mata dadi can tayi wani tunani dan haka ta matsa gaban kofar tace “sir may I coming ?”ya kalleta a natse daga inda yake yace “are you okay ?kayi hakuri ina distoping dinka over daman na manta jakar aikina ne ko zan iya shigowa na d’auka?” da hannunsa ya bata umarni ta shiga ahankali tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki ta kai hannunta ta d’auki jakarta ganin idan ta tsaya tura flower din sosai cikin jakarta zai iya fahimtar wani abu tayi tunanin boye jakar abayanta alokacin da ya juyo da saurin idanunshi suka sauka akanta .”kallo daya yayi mata ya fahimci alamun rashin gaskiya atattare daita .”




Muryarsa a kasalance yace “me kike boyewa ? muryarta cike da in..ina tace “amm ..”umm no babu komai “show m your hands zaro idanunta tayi tana cewa “babu komai sir jakata ce”.uhm nasan jakarki ce but let me see .”gabad’aya maryama ta rikice tayi fuska kalar tausayi ta ciro jakar ta rike a hannunta tana nuna masa a tunaninta ganin jakar kawai zai yi ya barta ta wuce kawai sai taga ya kawo hannunsa zai kar’bi jakar.”ta sakar masa jikinta na rawa ,ya tsurawa jakar ido da takardar dake jikin jakar makale yana kallo yana jin wani irin zirrrr a gabdaya ilahirin sansar jikinsa yayinda qararrawar soyayya ta buga a zukansu .ahankali maryama tasa gefen mayafinta tana rufe fuskarta cike da jin tsananin kunya gabdaya a matukar tsorace take da irin kallon da yake mata yana wa flowers din hannunsa, ta sake kai hannunta daya ta rufe fuskarta saboda tsannain kunyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login