Showing 150001 words to 153000 words out of 178062 words
Chapter 51 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
kaina kawai ma kowa ya huta da ganina a duniya.“da sauri umma ta fito daga kitchen din dan bata jin zata sauko cikin sauki haka.”a parlour maryama ta isketa kai tsaye ta isa inda alqurani yake ajiye akan abun tv tsand ta d’auka “umma na rantse miki da girman allah da da girman wannan alqurani mai tsarki.. ..”tun kafin ta kai ga fad’ar abinda zata fad’a umma tayi zumbur ta mike ta kwace alquranin a hannunta tana cewa “qul !na sake ganin kin d’auki qurni kinyi rantsuwa dashi .”
nan take maryama ta zube gaban umma tana wani irin kuka mai ta’ba zuciya tana rokon umma ta yafe mata “hakika maryama kinyi kuskure kuma tun tuni ni na yafe miki dan bazan iya cigaba da fushi dake ba, na dai barki ne kisan mahimanci laifinki “kiyi hakuri umma bazan sake ba aikin ma na ajiyesa bazan sake taka qafafuwa na acikin AGC ba “ta fad’a tana sheshekan kuka.
umma ta tsura mata ido kawai tana kallonta kafin ahankali tayi taku biyu ta qaraso gareta ta mikar daita tsaye ta rungumeta tsam ajikinta tana shafa bayanta .maryama kam banda kuka babu abinda take “kukan ya isa haka maryama dan ga jikinki har ya d’auki zafi ta fad’a tana numfasawa “hakika naji bakinciki yanayin danaganki ban san haka nake sonki da kishinki ba wallahi sai dana ga wad’an nan hotunan duk kwanakin nan bana iya runtsawa sai dai banji digo daya daga cikin so da qaunar da nake miki ta ragu ba,wallahi ni kad’ai nasan irin radadin da ciwon da naji a zuciyata ke macece bai dace ace kina biye masa kina zubar da mutuncinki da qimarki a gurinsa ba, idan kuma kuna son juna ne ai gara kuyi aure kamar zai fiyye maku irin wannan rayuwar .”
maryama tayi saurin zare jikinta ajikin umma tana girgiza mata kai “ni babu abinda zanyi dashi kamar yadda nasan shima babu abinda zai yi dani” kece kike ganin haka maryama” Allah umma babu abinda zanyi dashi babu abinda zakiyi dashi mai ya kaiki jikinsa ?wallahi umma tsautsayi ne amman na rantse miki da girman Allah babu abinda ya ta’ba shiga tsakanina dashi ,umma jawo hannunta ta zaunar daita bisa kujera cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da Jin tsoron abinda zata furta ta kalli cikin idanun maryama tare da yin kasa da murya tace “kina nufi wannan mutumin bai ta’ba sanki ‘ya mace ba ?”numfashi kawai maryama ta sauke da ajiyar zuciya sannan tace “umma zaki iya duba jikina idan kina so, nasan zaki iya fahimtar macen data ta’ba sanin d’a nmj da kuma wacce bata sani ba.” ajiyar zuciya umma ta sauke idan kuma baki yarda dani ba wallahi zan iya miki rantsuwa da alqurni .”abinda ya faru a ranar da har ta kai mu ga shiga wannan halin shine “nan ta fara zayyanowa umma komai tun daga farko har qarshe tana kuka.shiru umma tayi tana sauraronta tana mai gamsuwa da maganar maryama “ni dai fatana ayanzu umma ki yafemin kuma ki rokar min aunty da habib su yafemin bazan sake ba.” cike da kulawa umma ta riko hannunta cikin nata tana cewa kukan ya isa haka kije ki bata hakuri da kanki ganin nan zuwa yanzu .”
numfashi maryama ta sauke da qarfi cikin sanyi murya tace “na gode umma ahankali ta fita ta nufi bangaren mahaifiyarta tana kai wa bakin kofar ta tsaya cak ta kasa shiga tana tunanin abinda zata tarar daga masoyi ya, kuma abar qaunarta sai data sanyawa jikinta jarumta sannan ta shiga inda ta iske aunty zaune ta zuba tagumi daga ganin kasan tunani take wanda bata raba dayan biyu nata ne, ta qarasa ta durkusa gabanta ta dafa gwiwar qafafu wanta cikin tsananin sanyin murya tace “aunty kiyi hakuri ki yafe min bazan sake ba nayi nadamar abinda na aikata hakika baki cancanci haka daga gareni ba. sai lokacin aunty ta dawo daga duniyar tunanin data lula. ta tsura mata ido cikin zafin rai kwanaki uku kenan da faruwar abun amman ganinta yanzu sai take jin kamar yanzu abun ya faru “ki taimakeni aunty ki yafe min ki daina fushi dani bazan iya jurar fushinku ba “just shut up! ta fad’a tana janye qafafuwanta daga gareta batare da tace mata uffan ba “dan allah aunty wallahi bazan sake ba”maryama ki tashi ki fita ki bar nan bana son ganinki dan a yadda nake jin zuciyata zan iya aikata miki komai maryama tayi shiru tana duban mahaifiyarta fuskarta da bayananen mamaki “yau itace ta zama haka ga mahaifiya kuma abar sonta ?”mahaifiyar dake qaunarta fiyye da komai arayuwarta ,mahaifiyar data sadaukar da rayuwarta da farin cikinta dan kawai suzo duniya ita kuwa wace irin baqar rana ce yau agareta?” inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta soma furta wa cikin tsananin tashin hankali yayinda gbdy ilahirin jikinta ya d’auki rawa kanta ta soma juya mata “nace ki tashi ki fita anan !aunty ta sake furtawa a matukar tsawace tana haki da sauri maryama ta mike jikinta na rawa tayi hanyar waje da sauri tana daf da fita suka ci karo da umma ta riko hannunta suka juyo zuwa ciki dan taji tsawar da aunty ta buga mata tsaye suka iske aunty tana zariya tana haki dafe da goshinta
Umma ta saki hannun maryama ta dafa kafad’an aunty tana cewa” taho nan bilkisu ki zauna ta janyota zuwa kan kujera inda aunty ta zauna tana goge hawaye da gefen rigarta” “kiyi hakuri bilkisu ki daina kukan nan haka .shiru kawai aunty tayi tana cigaba da goge hawayenta “bilkisu ki kalleni aunty ta d’ago idanunta da kyar ta tsura mata cikin tsannain damuwa “ki kwantar da hankalinki babu abinda ya faru da diyarmu maryama ki bar damuwa haka mutuncinta yana nan har yanzu ,abinda ya faru kuma tsaitsayi ne kuma zai iya faruwa da kowa bisa qaddara sam sam kada ki d’auka tana zubar da mutuncinta ne.”
“ ba wai ina tunanin haka bane umma amman ni uwa ce fa abun da ciwo ace maryamata ce na gani kwnace ajikin wani “ta fad’a tana goge hawayen numfashi umma ta sauke yayinda nan take kwalkwal warta ta shiga tariyo mata abinda ya faru a shekarun baya “nasan kema uwa ce a yanzu amman kiyi hakuri ki bar kukan hk sai dai a yau nake son kisan wani abu bilkisu ba wai zan dawo miki da abinda ya wuce bane a’a kawai dai ina son ki gane irin so da qaunar dake tsakanin uwa da d’a ne”Kinsan mai yasa zanyi mgnr tun kafin tayi mgnr kukan aunty ya qaru “bilkisu kina fushi da iyayenki especially mahaifiyarki akan rayuwarki ta baya to kisani taji zafi da radadi fiyye da wanda kike ji a yanzu .kisani ba kiyayya bace tasa mahaifiyarki ta dinga miki abinda ta miki abaya illa so ne da kuma gata da take son tayiwa rayuwarki amman soyayya da qaddara ya rufe miki ido ya hanaki fahimtarta abinda take gudar miki shi kika tsinta kanki ciki ,duk uwa ta gari baza só diyarta tayi rayuwa irin wanda kikayi da hussein ba wahala take gudamarki kuma kin shata har yau kina kan shanta , bazan tillastaki dole ki koma garesu ba amman kisani lokaci yayi da zaki je ga iyayenki ki nemi yafiyarsu da wannna kawai zan kawo qarshen maganata .”nasani umma nasan ban kyauta masu ba, ban kuma san cewar illa nayiwa raywuta ba sai a yanzu” umma ta numfasa sanna ta mikawa maryama dake rakube hannunta alamun tazo gareta “durkusa ki bawa mahaifiyarki hakuri “cike da sanyi jiki ta durkusa tana sheshekar kuka tare da riko hannun aunty cikin nata bilkisu ki yafewa diyarki ki kuma cigaba da yi mata addaua Allah ya shirya mana gabad’aya kasa cewa komai aunty tayi illa ta rike hannun maryama da cike nata sun dade suna kuka umma na rarrashinsu kafin daga bisani umma ta fito ta basu waje”
Kwanciya lamo maryama tayi a saman gwiwowin aunty yayinda ahankali aunty take jin zubar hawayenta ,ta yadda har ta fara jika zanenita duk da har lokacin aunty najin haushi da bakincikin abinda ya faru amman data tuna abinda tayiwa iyayenta sai taga kamar maryama rama masu tayi wani dogon numfashi tare da zubawa bayan maryama ido .”
”aunty kiyi hakuri bazan sake ba, ahankali aunty ta kai hannunta saman kanta tana sheshekan kuka wanda yasa maryama ta d’ago kanta “I’m very sorry aunty !tayi maganar adaidai lokacin da aunty ta mike tsaye cike da sanyin jiki ta juya tana tafiya tamkar wacce bata da laka ajikinta da sauri maryama ta biyo bayanta tana ta faman bata hakuri atare suka shiga dakin aunty inda aunty ta samu waje ta zauna tana sauke numfashi maryama ta qaraso ta zube gabanta cikin tsananin damuwa ki hukuntani aunty ko zuciyarki zatai sanyi domin kuwa na cancanci haka “ta fad’a tana riko hannunsa ta zuba mata ido kawai babu abinda take gani illa maryamar ta kwance ajikin wani kato hannuwansa zagaye da kugunta “dan Allah aunty kiyi hakuri ki daina kukan nan muddin ba so kike rayuwata tafi haka muzanta ba ,dan allah kice kin yafe min ko zuciyata zata samu sausauci “ta fad’a tana hade hannuwnta waje wani numfashi ta sauke sannan ta goge hawayenta “na yafe miki amman abinda nake so dake ki fidda miji aure maryama bazan iya zuyar ganin rayuwarki haka ba, ina miki addua Allah ya baki mijin na kwarai wanda zai duba lamarinki .”bakinta na rawa tace am ..”ameen “amman aunty bani da wanda yake sona da au..” ki nemoshi.” ta fad’a mata haka ta hanyar katseta yayinda fuskarta ke a hade tmkr wacce bata ta’ba dariya ba .”
tun tasowar maryama wannan shine karo na uku data ga damuwa mai tsanani atattare da mahaifiyarta “wata biyu kawai na baki maryama ki fidda mijin aure dan bazan juri ganin a ta’ba min ke ba …”ji maryama tayi gabanta yayi mummunar faduwa sakamakon jin abinda mahaifiyarta ta fad’a “dan Allah aunty ki taimakeni I promise you I will be..”banason jin komai daga bakinki mryama ni dai kinji abinda nake da bukata dake ,ki tabbatar kin fito da miji a wata biyu kuma bance kije ki fad’awa umma ba dan na canza maganata ba idan kikayi haka zanyi fushi mai tsanani dake ,ki tashi kije”. inna ilaihi !”ana wata ga wata dame zataji ina zata samo wanda zasuyi aure dashi nan da wata biyu tana kallon aunty ta mike tsaye ta canza waje ,tabita da wani kallo hawaye na kwarara akan kuncinta da kyar maryama ta yunkura ta mike tsaye haka ta fito daga bangaren aunty zuciyarta cike da mummunar tashin hankali daf da maryama zata fita sukai karo da habib wanda shigowarsa kenan ta tsura masa ido tana kallonsa hawaye nabin kuncinta wani irin tausayi da qaunar yaruwarsa ya mamayesa dan yaji duk matakin da aunty ta dauka akanta riko hannunta yayi cikin zafin nama suka dawo wajen aunty .”
“aunty …..”karka ce min komai habib domin maryama bata canci ta cigaba da zama damu haka ba data dinga janyo min magana gara tayi aure kowa ya huta daman yarda da kalar tarbiyar dana mata ne yasa taga na barta tana yin yadda taso bansan shashancin banza da wofi zata dinga yi a wajen aiki ba “nasani aunty hakika heartbeat bata kyauta miki ba ni kaina naji ciwo abun har cikin raina amman ya zamuyi dole hakuri zakiyi ?wani dogon numfashi aunty ta sauke kana ta cigaba da magana “maryama ta manta tsatsonta, ta manta halin da muke ciki acikin gidan nan ,ta manta irin rayuwar da muke ciki acikin gidan da abu kad’an ake jira akanmu ya zama abun mgn ta manta bata da galihu sai nã allah duk ilar da mutumin nan yyi miki yaci bulus tunda shi yana takama da kudi mufa ?bamu da kowa bamu da gata sai Allah shine gatanmu shi yasa wata biyu kawai na bata ta fito da miji tayi aure “.
“Naji tace babu komai tsakanin su amman sau tari idan ta dawo daga aiki ta shigo wajena Ina Jin qamshin turare ajikinta wanda ba nata ba kuma turare ne mai qarfi sai dai yarda da nayi mata yasa naji kunyar tmbyrta sai da wannan abu ya faru na fahimci daga wannan mutumin ne idan ma bai ta’ba yin komai daita ba zata iya rantsewa kafin wannan abun ya faru bai ta’ba sanyata ajikinsa da sunan runguma ba .”
Maryama ta sake rudewa ta gigice tana zazzare ido jikinta na wani irin rawa umma da habib suka zuba mata ido alamun tunhuma ita kuma Maryama alamun rashin gaskiya ya bayyana atare daita “kagani habib duk ta rude alamun rashin gaskiya nan take maryama tayi kasa da kanta tana zubar da kwalla numfashi habib ya saki yana cewa “duk abinda kika fad’a aunty da alamun gsky ne amman dai kiyi hakuri ki yafe mata ki barta har zuwa sanda allah zai kawo mata miji idan kika matsa mata taje ta shiga wata rayuwa fa sam sam zuciyata bazata lamunci haka ba dan haka ki janye maganarki akanta .
ido aunty ta zuba masu ganin yadda yanayin habib ya canza one time ahankali maryama ta d’ago kanta idanunta cike da ruwan hawaye “aunty kiyi hakuri bazan sake ba,kuma babu abinda ya shiga tsakanina da mr ata kawai dai nasan tsautsayi ne yasa na sakar masa jikina amman shima mutumin Kirk ne “aunty ba tace masu uhm bare uhm uhm ta fice daga dakin ta barsu.”
tana fita maryama ta zube jikin habib tana wani irin kuka tana cewa “habib karka qara saka bakinka cikin maganar nan kar laifina ya shafeka ka dai ka tayani da addua Allah ya kawo min mafuta na rabu da mahaifiyarmu lafiya.” sun dade a dakin suna tautaunawa inda maryama ta zayyane masa komai daya faru a wancan ranar wanda ya zamo silar ganin da suka mata da mr ata sai bayan ishai maryama ta dawo bangaren umma tana shiga d’akinta wayarta na soma alamun kira ta qarasa ta d’auka idanunta ya sauka akan screen din wayar sunan mr ata tagani yana yawo akan screen din wayar numfashi ta sauke tare da d’auke idanunta ta samu waje ta zauna bakin gado tai shiru tana tunanin halin da take ciki aure kuma nan da wata biyu “wa take dashi da zata kawo a matsayin miji ?”ta sauke naunayen ajiyar zuciya tana bleming din kanta akan duk abinda ya faru daita itace sila da bata nace akan sai tasan wani abu akan nadia ba da tabbas da yanzu bata tsinci kanta cikin halin da take ciki ba .”
Bangaren mr ata kuwa tsaye yake acikin d’akinsa sanye cikin farar riga mai gajeren hannu da gajeren wondo blue black iya gwiwarsa kanshi sanye da facing cap golden colour ya hard’e hannuwansa waje akan qirjinsa yana kallon hotunan da mami ta zube masa agabnasa “me zakace akan wannan ?akan me zakayi min haka adamcy? a she daman irin sha shancin da kake yi kenan a wajen aiki yasa ka kasa zama da matarka sannan ka kasa yin wani auren ?”wallahi adamcy kayi matukar bani mamaki sam banyi tunanin wannan shashan cin banza daga gareka ba wallahi ka bani mamaki.”
shiru yayi kawai yana jin mami shi sam ba hotunansu rungume da juna da mami ta gani ne damuwarsa ba kmr yadda yaga hankalinta ya tashi matuka da kuma son sanin halin da maryama take ciki ,yana son yasan a wani hali maryama take ciki adaidai wannnan lokacin domin kuwa bai san dalilinta na rashin zuwa aiki ba gashi ya kikkirata wayar bata shiga ba sai yau kuma shina taki d’auka.”
sosai yaga mami ta firgice masa tanata zuba ruwan fad’a “wallahi adamcy ka cuceni .”kuka mami take sosai numfashi ya sauke sannan ya isa wajenta ya zaunar daita akan kujera alokcin kukanta ya ragu” mai yasa sweetheart?” mai yasa zaki min haka kinfi kowa sanin koni waye “mai zan tsinta a isknaci kuma idan ma shashan ci zanyi a irin wannan wajen zanyi ,”ki kalli hotunan nan da kyau zaki fahimci anyisa ne cikin yanayi na damuwa ba wai anyisa dan son rai bane .”akwai guraarr da dama acikin ma’aikatan da zanyi komai da nake so batare da wani yasan halin da nake ciki ba mai yasa sai irin wannan wajen zanyi wani abu .yarinyar nan kamar yadda na fad’a miki tana da matsla a kwakwaluwarta sakamakon abinda ya faru da mijinta ahankali mr ata ya faiyacewa mami komai babu abinda ya rage mata aciki kuma ta fahimcesa” ni bazan cuci rayuwar diyar kowa ba idan kuma har shashncin zanyi wallahilzim bazan yi da maryama ba”. ya fad’a a zuciye yana gama fad’ar haka ya tashi ya shiga d’akinsa cikin tsannain fushi.”
mami tabi bayansa da sauri tana kiran sunansa tsaye ta iskeshi a juyawa kofar baya ta dafashi tana cewa “kayi hakuri adamcy nayi saurin daukar zafi batare da naji ta bakinka ba .” Mami tayi magana sosai amman sam ata bai ce mata Uhm ba bare uhm uhm tasan halinsa tunda yayi shiru irin haka to fa komai zatace bazai yi magana ba dan haka ta juya ta bar masa d’akin daren ranar mr ata bai runtsa ba duk byn awa sai ya kiran layin maryama amman bata d’auka a qarshe dai ya tura mata text amman babu amsa “.
Sosai zuciyarsa tayi nauyi dan ko ya kwanta da zumar bacci baccin bai zuwa bangaren maryama kuwa ko ajiknta tana kallon kiransa amman taki d’agawa dan tasan qarshe dai ruwan bala’i zai mata ya ma barta taji da damuwarta ba sai ya qara mata wani ba qarfe uku daidai tayi wani juyi ta kai hannunta inda wayarta take ajiye shigowar sakonsa ta gani da kamar bazata duba ba sai kuma tayi tunanin ta bude taga wani irin cin mutunci ya turo .”
_Slm zuciyata na min