Showing 156001 words to 159000 words out of 178062 words
Chapter 53 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
tsananin bugawa da qarfi ”
Cike da tsinkewar zuciya tace “please sir kayi hakuri nasan nayi maka ba daidai ba na ajiye aiki da nayi batare da sanar maka ba, dan rashin maganarka a yanzu ya fara d’aga min hankli matuka fiyye da tashin hankali dana shiga.”ta fad’a tare da yin shiru stil qirjinta na dokawa .”
baba gali dake tsaye aharaban bangarensa ya janyo hannun aunty salma suka la’be duk zufa ta rufesa “salma matso kiga ikon Allah “aiko karaf idanunta ya sauka akan mryma da ata tsaye “me zan gani kamar wancan mutumin da ya rungumeta a hoto ko ?”shine kuma shine dai wannan mutmin daya zo neman aurenta a boye na hanashi“anya salma malam bai fara girba miki karya ba?“Anya ma kuwa kinsa a farraka tsakaninsu domin muddin mukayi sakacin da maryama ta auresa mun tafka babban kuskuren da bamu ta’ba yi ba a rayuwarmu “ka yarda dani ba zan ta’ba barin muyi wannan kuskuren ba,ina ganin an samu kuskuren aiki ne amman tabbas malamina ya tabbatar min bazai aureta ba sai dai su qare rayuwarsu a neman juna.”
Maryama tayi kasa da kanta sosai tace “kayi hakuri dan Allah nasan nayi maka laifi gashi na sakaka wahalar zuwa unguwarmu ”ta qarasa maganar muryarta na rawa “mryama you should know me by now mai yasa rashin magana ta zata d’aga miki hankali ?shiru tayi tana kallonsa up & down.”
shi kuwa gogan hannu ya kai yana shafa qirjinsa yana jin wani irin sanyin dadi a ilahirin jikinsa “well yanzu ma ba saboda ke nazo ba nazo ne naga ummanki ki shiga ki sanar daita zuwana .”shiru tayi tana kallonsa cike da tsannain mamakinsa “ki shiga mana kin wani tsareni da wad’an nan idanuwan naki kmr na mage “.jiki a sanyaye ta juya tana taku ahankali tamkar kazar da kwai ya fashe acikinta .”
iskar bakinsa ya furzar yana bin every step of her “Adamcy kana mugun son yarinyar nan over wallahi mb so ba kad’an ba yanzu haka ganin da nayi mata wani irin yanayi mai tsarkakkiya da wuyar misaltuwa ke shigana da ana bud’e sansar jikin mutu nasan ana bud’e nawa tsananin soyayyar maryama da qaunarta kawai zaa gani yana yawo aciki ji nake na zarta duk mazan duniya shan wahalar soyayya amaman na godewa allah da zai mallakamin ita.”
“ karka cika baki ka fara sheida mata matsayinka tukun kafin wani yazo yayi maka shigar sauri dan irin wad’an nan matan Allah ba’a sakaci dasu itama dan tana cikin lugun ne da waje take wallahi da yanzu matar wani ce.”wani murmushin yake mr ata yayi yana shafa qirjinsa cikin kankanin lokaci ya hango tahowarta tana gama qarasowa tace “muje!” tana gaba suna biye daita har bangaren umma .”
basu iske umma parlour’n ba maryama ta kallesu tace “ga guri ku zauna yanzu zata fito.” mb ne ya soma zama akan kujera mai zaman mutun daya yayinda ata sai daya kalli maryama sannan ya zauna a natse yana gyara wuyan rigarsa bayan ya zauna ya d’an kalleta a tsanake yaga duk tayi wani iri kamar a firgice take ya d’an motsa lip’s dinsa “ya naga duk kin birkice?”ta girgiza masa kai”to ki zauna!”ya nuna mata kusa dashi tayi saurin girgiza masa kanta tana sake damke yatsun hannunta .”suna nan zaune har sanda idanun mr ata ya sauka akan hoton sadam dake manne a bangon parlour’n sosai ya tsurawa hoton ido yana kallonsa kafin ahankali yace “wannna shine sadam ?da sauri ta gyad’a masa kai tana cewa “shine sadam dina sir.” wani mugun kallo yayi mata yana sauke numafshi tare da jinjina kai yana jan tsaki adaidai lokacin da umma ta fito tana masu sannu da zuwa.”
Cike da girmamawa suka rusunar da kansu suka gaisheta ta amsa masu da kulawa tana murmushi ta kalli maryama dake tsaye “ya zaki bar bakinki haka batare da kin kawo masu komai ba?” akwia sobo da nayi d’azu da safe sannan akwia cinci a fridge maza je ki kawo masu “okay !” har ta juya taji mb yace “no a koshe muke wallahi mun gode sosai ya fad’a yana murmushi amman duk da haka sai data maryama taje ta kawo a gaban mb ta ajiye ta samu waje ta tsaya tana jin wani irin mummunar fad’uwar gaba .”mb yayi gyaran murya sannan ya fara magana a tsanake cike da kamala “amm daman abinda ya kawo mu akan abinda ya faru ne atsakanin maryama da adam “.
Umma ta jinjina kai sannan tace “ai nayi mamakin ma da sai yanzu biyo sawunta “mr ata najin haka yayi kasa da kanshi “kuyi hakuri da abinda ya faru
“Ala hakika gaskiya gabadayanmu bamuji dadin faruwar wannan alamarin ba kuskure aka samu daga gyara matsala abun ya dawo matsala domin shi yayi qoqrin yaga ya rabata da damuwar dake damunta ne ba wai da wata manufa hakan ta faru ba “.
“ba wai dan adamcy yana nawa ba wallahil azim shi din mutu min kirki ne .”umma ta kalli maryama tace “maryama maza kije ki kira aunty ayi komai a gabanta ahkli maryama ta juya ta fita yayinda mb ya cigaba da zayyanowa umma komai kamar yadda maryama ta fad’a mata yana rufe bakinsa aunty da maryama suka shigo bakin aunty d’auke da sallama cikin shiga ta kamala “yauwa ga mahaifiyarta nan” a sukwane mr ata ya juyo ya kalleta adaidai lokacin da take qoqarin zama kusa da umma, yayi shiru tare da tsura mata ido yana kallonta ta banga ren fuska ba tayi kama da maryamarsa ba dai dai ta yanayin jiki kasancewarta ba wata mai kiba bace duk da cikin hijab take amman yanayin ta ya nuna masa bata da kiba, yayi kasa da kanshi sosai inda idanunsa ya sauka akan yatsun qafafuwanta abun mamaki da d’aure kai irin yatsun sweet heart dinsa sak gareta ya d’ago kanshi kad’an zuwa yatsun hannunta nan ma irin yatsun maminsa ne gareta ya sake kallon fuskarta da kyau sai ma yaga kamar yasan fuskar ko kuma yace ya ta’ba ganin mai yanayin irin fuskar .”
Shiru yayi yana nazarin fuskar sosai amamn ganin ba abinda ya kawo shi kenan ba yayi qoqarin qawar da hakan acikin ransa ,sai dai aransa yana mamaki yadda yatsunta hannu dana qafa yayi kama dana sweetheart iska ya feasar yace “ kawai halittar yatsunsu ne ya zama iri d’aya bayan sun gaisa daita umma ta bukaci mb ya sake yin magana agaban aunty bai yi mutsu ba yabi umarnin umma yana dasa aya mr ata ya soma magana kanshi a kasa cike da nadama “ kuyi hakuri da abinda ya faru idan zaku d’aura laifin ku daura laifin akaina domin ni ne mai laifi if nayi shishigi acikin rayuwarta da duk hakan bata faru ba .”yana gama fadar haka yayi shiru yana jiran yaji abinda zasu ce.”numfashi umma ta sauke sannan ta gyara zamanta tace “duk na fahimceku sannna kai ma baka da laifi haka Allah ya qaddaro bawa kuma bai isa ya canza qaddararsa ba Allah yasa mu dace duniya da lahira “haka ne sai batu na gaba naji mryam tace ta daina aiki damu ?
“kwarai kuwa haka tace ammn bisa tsarinta ne ban sani ba ko dan mahaifiyarta tace ta fito da mijin aure nan da two month ne yasa ta yankewa kanta wannan hukunci bansani ba, amman kuma aganina hakan da tayi shine daidai agaremu gbdy domin tsare mutuncinta da kuma namu,duk da ina da yarda da kuma yakinin maryama ba mutuniyar banza bace a gabana aka haifeta in fact ma nice nayi mata tarbiya nasanta ciki da bai macece data san ciwon kanta duk dai ba’a sheidar d’an yau amamn maryama she’s the best kuma ina mata kyakkwan zato .”umma fad’a haka tana tsaresa da ido domin son gano wani abu atattare dashi ita dai tun bata ganshi azahiri ba take ma maryama shaawar aurensa bare yanzu data ganshi Allah yasa hasashenta ya zamo gaskiya mutumin son maryama yake kuma da aure .”
shiru adamcy yayi yana kallon umma da aunty wacce aka kira da mahaifiyar maryama yana tunain yadda gabad’aya take son rayuwar diyarta ta lalace idan ba haka ba mai zai sa dan mutun yayi kuskure kankani ace ya fito da mijin aure nan da wata biyu ba’a jin tsoron abinda zai biyo bayan auren ,” nasan kuna da gaskiya akan hukuncinku a matsayinku na iyayenta sai dai ina jin kmar ni ne na aikata laifin ita kuma ta dauki hukuncin mai tsanani .”ya fad’a yana furzar da numfashi sanan ya cigaba da magana cike da natsuwa da kamala “nasan ko ni ne naga diyata a wannan yanayin zan yi iyakacin bakin qoqarina na kare diyata amman bata hanyar tillasta mata ta fito da mijin aure acikin tsukukun lokaci nan ba saboda yadda rayuwar nan ta zama yanzu .”
shiru sukai gabad’aya suna sauraronsa da kunnen baseera “nasan abinda ya faru ba daidai bane amman kuma wannan hukuncin da kuka yanke mata yayi mata tsauri dayawa a matsayinta na diya mace mai qaranci shekaru nasan babu wanda yake son yaga rayuwar iyalinsa ta tagayyara tunda nake d’aukar masu aiki ban ta’ba d’aukar mai aiki irinta mai tattare da basera da kamaun kai ba, wallahi na yarda kuma na amince kunyi qoqri sosai akan tarbiyarta .”
wani sanyayen numafshi aunty ta sauke tana jin natsuwa acikin zuciyarta karon farko data gansa sai dai taji natsuwa dashi ,”tsannain yadda na damu na tsanata bincike akan abinda ya faru ina son na gano wanda ya d’aukemu hoto kuma dole zan gano kuma dole zai amshi hukuncinsa dan ba dan maryama aka yi wanan tozarcin ba saboda ni ne ,ni ake son tozartawa ba ita ba .duk suka jinjina kai ya lashi lips dinsa ya dan kalli inda maryama take tsaye tana wasa da yatsun hannunta sannan ya d’auke idanunshi ,ya tsurawa umma da aunty ido kafin ahankali maganarsa ta fito “ina rokon alfaram ku bar maryama ta cigaba da aiki tare dani nayi maku alqawarin zan kare mata mutuncinta ,zan kula maku daita zan tsaya mata km zan iya zuwa kowani irin mataki akanta nasan zaku yi tunanin ina da son kaina dawa wallahi ba haka bane ita kanta bazata cigaba da rayuwa mai dadi ba kasancewar tana son aikinta.”
“haka ne sai dai wannna hukuncinta ne ba namu ba itace bata bukatar cigaba da aiki “inji cewar umma “umma ki bar maganarta fatana ku bani dama ni zan mata magana ta yadda zata dawo aiki .”
duk suka yi shiru suka kasa cewa komai umma ta kalli maryama taga tana girgiza mata kai alamun karsu yarda karaf idanun mr ata ya sauka akanta da sauri tayi kasa da kanta tana jin wani irin mummu nar fad’a uwar gaba .”Mb ma bai yi sanya ba ya fuskanci wacce akace itace mahaifiyar maryama yace “aunty kiyi hakuri munyi miki alqawarin babu abinda zai sameta da izinin Allah duk abinda ya sameta ki d’auki duk matakin da yayi miki dadi akan mu.” numfashi aunty ta sauke ta kalli ata dake zaune shiru ,ta waiga ta kalli umma sannan tace duk naji bayaninku sai dai ni bani da abinda zance sai abinda umma tace idan ta yarda ta amince shikenan idan kuma bata amince ba sai ku hakura ,sai batun aure wannan kam bazan janye maganata ba bawai na gaji da zamanta haka bane ,amamn ta fito da miji dan aure shine darajar duk wata diya mace “ku yarda dani bazan ta’ba cutar da maryama ba “shikenan .”inji cewar umma “mun gode sosai shima mijin nan kusa zata samu da iznin Allah koma nace ta samu “wani irin kallo ata yayi masa” mb ya hararesa yana fuskantar umma inda itama umman cewa tayi “ shikenan Allah ya shige mana gaba amamn kuyi magana daita idan ta yarda babu matsala allah yasa haka ne abinda yafi zama alkhairi agaremu.”Umma na gama fadar haka ta mike auny ma ta mike tai masu sallama ta fice haka ma umma ta shige d’akinta mb ma ya yunkura ya mike tsaye yace “bari naje na jiraka a mota “.
adamcy ya gyad’a masa Kai ya fice ya barsu parlour’n ya saura daga ata sai maryama dake tsaye shiru taki zama har kusan mintuna goma tana tsaye daga gefensa on expecting maryama taji ya fixgota zuwa gefen jikinsa saurin d’auke numfashi tayi sannna ta waigo a gigice tana kallonsa cike da matsanancin tsoro.” iskar bakinsa da hucin numafshin ya dinga sauka a gefen fuskarta tayi saurin lumshe ido ahankali ya dawo daita ta gabansa still tana kwnace ajikinsa yayi mata kyakkyawan rikon da bazata iya kwacewa ba ya kai bakinsa daidai saitin kunnenta ya soma rad’a mata magana cikin sanyayyar murya shi mai tsananin kashe jiki da tsuma zuciyar wanda akayi dominsa “maryama ni zaki wa butulci ?” wani bugu qirjinta yayi yayinda jikinta ya d’auki rawa “ina kallonki kina girgizawa umma kai alamun karsu yarda ki sani bazaki ta’ba iya gujewa adam ba domin shi din mai nasara ne
Duk abinda yasa a gaba sai yaga qarashnsa kuma duk abinda yake bukata sai ya zama mallakinsa duk inda nake dole ki kasance anan bare a halin yanzu da zuciyata take cikin garari “inna lillahi! ta furta a kasan zuciyarta tsigar jikinta na mikewa “.
Ya fesa mata iskan bakinsa “bama haka ba har cikin zuciyata bana son yin nesa dake zan kulawar ummanki da auntynki ke.” yayi maganar yana sake damke jikinta dake rawa kamar mazari saboda tsananin tsoro “zuciyata na tsananin jin tausayinki bazan bar wani abu ya sameki ba ,addu’at da fatana Allah ya bani ikon cika alaqawa rin dana d’aukar masu ,sosai ya sake janyota jikinsa ta shige masa wanda hakan yayi mugun mugun d’aga hankalinta yanzu fa ya gama magana zai kula daita”kenan irin wannan kula war zai mata ?”muddin irin tace gsky bazata ta’ba kasancewa dashi ba ,ya sake Kai bakinsa daidai kunneta “ance baza’a d’aga miki qafa ba lallai sai kin fitar da miji aure “?ta lumshe masa ido tana sauke numfashi dan wani iri take ji a gabad’aya ilahirin jikinta “.ya sake sauke mata numfashin bakinsa a kunnenta “kinsan na ta’ba miki mgn akan ya dace kiyi aure? “muryarta cike da in ina tace “eh zanyi qoqarin na fitar da miji kafin lokacin da aunty ta bani “kenan kina da Wanda kike so ?”bani dashi amman zan nemo “zaki nemo ki auri wanda bakya so ?”to zanyi dole zan bi umarnin mahaifiyata ta qarasa maganar hawaye na cika mata ido yayi shiru na second biyu sannan ya cigaba da magana “tunda nemo mijin zakiyi to ki aureni ”
Mmn Sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
45
zaro idanuwa maryama tayi jin furucinsa”tunda nemo miji zaki yi to ki aureni”ta maimaitawa kanta furucinsa na qarshe mai cike da tsarkakki ya da shiga tashin hankali,kai tsaye mgnrsa ta ta’ba kwakwaluwarta sannan ta samu kyakkwan mazauni a zuciyarta ,sai dai maganar tayi mugun gigitata ahankali ta kai hannunta ta murza idanuwanta domin tabbatarwa kanta gskiya ne ko kuwa mafarki take,bata gasganta a zahiri taji ya fad’i kalmar ba sai data d’an ciza yatsanta taji wani irin rad’adi sannan ta tabbatarwa kanta da shi din ne yayi maganar“.a matukar gigice take kallonsa hannuwansa duka zagaye da kungunta ya mugun tsareta da tsumammun idanunshi tamkar bashi yayi furucin ba “.
“ban ta’ba expecting ko da wasa irin wannan mganar zata fito daga bakinka ba ,plese sir can you say what you said again Ina son na sake tabbatar da naji abinda ka fad’a da kyau kuskure ne, ko kuwa da gaske ka furta wanan kalmar agareni ”tayi maganar jikinta na sake d’aukar rawa tamkar mazari ahankali ya lumshe tsumamun idanunshi tare da motsa lip’s dinsa “nace muddin kinsan baki da wanda kike so wallahi ni a shirye nake zan aureki.”sake ware idanunwanta tayi tana mai fuskantarshi sosai tasan ba da wasa yayi maganar ba tunda gashi har ya rantse .”
”maryama !”
Ya kira sunanta wanda yasa tsigar jikinta suka mike yrrrrr “ki aureni .”ya sake share mata tantamar dake damunta, bata san lokacin da ta saki murmushin yake ba tare da girgiza masa kai.”jikinta na rawa ta fara qoqarin zare jikinta daga nashi ya sake riketa da kyau ta sake girgiza masa kai a sanyaye alamun ya sakar mata jiki “.
“ki natsu maryama ki bani amsa zaki aureni ?”
Wannan karon da sauri ta girgiza masa tana waigen bayanta.” Sosai tayi kasa da muryarta
“ dan Allah sir ka sakar min jiki kar ummah ta fito ta ganmu haka “kinsan Allah ki bud’e baki ki amsa min zaki aureni ko a’a if not anan zan kwana.” “what !”ta furta a rud’e hankalinta na sake tashi ya d’age girarsa d’aya alamun”eh!”tayi Imani zai iya aikata abinda ya fad’a din dan haka cike da karkarwa tace “Ka kwana anan akan me zaka kwana anan ?”dan Allah sir Ina rokanka tare da girmamawa ka tashi ka tafi gidanka gun matar ka,dan wallahi idan ka qara wasu mintuna anan zan iya had’iyar zuciya .”tayi maganar tana sake waiga bayanta .”
gyara zama yayi sosai kamar yana parlour’sa ko na mami tare da sake mata riko mai kyau wanda ko maza biyu sun qaru akanta bazata iya kwace wa a hannunsa ba “dan girman Allah sir ka tashi ka tafi gidanka ka rufa min asiri Ina ni ina aurenka zan dai samu takala daidaini na aura …”maryama ta fad’a cikin marai raicewar murya tamkar