Showing 36001 words to 39000 words out of 178062 words
Chapter 13 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
aiki ko kar nayi dole kuma abiyani saboda mahaifiyata tanada karfin iko acikin wannna kamfanin dan haka daga yau ido ne naki akaina dan ko mr ATA bai isa ya koreni daga wannan ma’aikatanr ba dan banyi aiki ba okay.”
Some bata ce mata komai ba har sultana ta qarasa inda maryama take zaune ”uhm Ke dai bagajiya da aiki kamar ba d’azu kikayi wani aikin yanzu kuma kin dukufa yin wani “me ya kawo ni ?”ai aikin ya kawoni kinga dole nayi”sultana tayi shiru can ta cigaba da mgn “duk aikin da mr ATA ya kawo bakya sallakewa ?”taya zan tsallake me ya kawoni idan ba aiki ba kuma dai ai shi din mai gidana ne dole nayi masa duk aiki daya sakani sultana ta cigaba da surutu mara ma’ana “maryama tace “kinga sultana kin dameni ni fa ina son aikina “ ko ma dai menen bazaki ta’ba burge mr ATA ba “banzo dan na burge kowa ba nazo dan nayi aiki ne oky sultana taja tsaki da numfashi sannan ta fita “.
Some ta tsaya akan maryama !tana kiran sunanta “yes ma ta tsaya kusa daita rungume da file “duk cikin masu aiki a kamfanin nan daga manya har kana babu wanda Ke iya maidawa sir magana saboda tsoro amman naga ko kad’an bakijin tsoron komai kina iya mutsu dashi kina iya magana dashi kai tsaye tun shekaranjiya hankalina a tashe yake sai gashi naga sir yayi shiru bai ce komai ba “Eh ! nima nayi tunanin zai ce wani abu sai naga bai ce ba sai abu na gaba nima ina jin tsoronsa kamar kowa “really!?” yes ma !ta fad’a tana sakar mata murmushi “na danne nawa tsoron ko nace so nake na cire tsoronsa dan naga alamar kowa najin tsoronsa shine nake son na cire kaina ya zamo ban dani sannan kuma na rufe damar da zai fad’a min abinda ya ga dama, no chance for him “shiru some tayi tana sauke numfash.”sannan tace “ki dai bi ahankali “okay ma .”
Cikin yanayin na tashin hankali sultan ya shigo office din mr ata yana huci tmkr zaki ya soma magana “yana cewa wai me ka d’auki kanka ne komai kai sai ka nuna wa mutane isa da mallaka , kayi iko akan kowa ,kayi iko akan komai, Ka dinga abu da d’agawa naga alamun so kake ka mallakemu gbdy da kamfanin “mr ata bai ce masa uffan ba illa ya fesar da numfashi mai zafi kana ya mai da jikinsa sosai akan kujera tare da lumshe idanunsa inda sultan ya cigaba da fadar magana son ransa idanunshi ya bude a hankali cikin yanayin tashin hankali ya ci gaba sauraronsa “kamfanin IGA mu suke bawa aiki amman dan rashin godiyar allah irin naka sai da kayi munafurcin da suka kawo maka aiki “ me muka tsare maka me ala dole so kake ka malleke kamfani .”
“Mallakar kamfani kuma na nwa ?ai tun tuni na mallake ,kuma babu wanda ya isa yayi abinda yaga dama matsawar ina cikinsa ,kai kanka kasan nafi karfin na tallata sanaata ga kowa bare IGA “ abu na farko bansan ku kuke masu aiki ba sun bukaci aiki daga gareni kuma nayi masu abinda suke so amman kawai saboda burika kullum ka ci min mutunci ko kayi abinda zan bar kafanin nan ka maye gurbina ka zama MD na wannan ma’aikatar shine zaka zo kana fad’a min mgn kana son matsayina sai dai baka da wannan kokarin sannan baka da talent din sannan daga yau idan kana son ka zo wurina ka dinga amfani da common sense din kafin kazo okay yayi maganar a tsawace .”
“Adam kana wuce gona da iri acikin kamfaninmu ka tattara kwararu masu aiki a wurinka ka hana kowa ya dinga sakasu aiki sai kai kad’ai “mr ata ya kallesa a kaskance jin ya shigo da wata maganar bai kai ga cewa komai ba yaji ana neman izini “ko zan iya shigowa ? aka fad’a daga bakin kofa”kullum kana jin dadin ganinmu cikin damuwa kullum burinka kaga komai namu ya tsaya .” shi dai mr ATA bai ce uffan ba dan daman tuni ya maida idanuwanshi kan system.“daga yanzu zan fad’awa gabadayan family’s dake aiki acikin kafanin nan kada wanda ya sake bin umarninka ko bin wata dokarka acikinmu dan baaajiyemu kayi ba “ maryama taji shiru ba’a bata izini shiga ba tace “sorry sir ! ta juya da sauri ta koma kasancewar taji kamar alamun fad’a “sultan kana damuna alhalin kasan bana son damuwa dan Allah zaka iya tafiya please .”
“Bazan tafi ba sai lokacin dana ga dama dan ba kai kad’ai kake son yin abinda ka dama ba wai har kamar ni zan sa akira min yara zan sakasu aiki suki bin umarnina wai suna maka aiki “rashin tunaninka bazai bari ka fahimci komai ba kai kasani babu wanda zan hana yayi maka aiki sai dai idan suna min aiki amman tunda idanunka yanzu sun dawo Kan ma’aikatan dake karka shina saboda a tunaninka sune nasarata muje ka zabi duk wacce kake son tayi aiki da kai .”wani farinciki ya kama sultan saka makon burinsa ya cika sai dai yaki bayyana hakan dan kar mr ATA ya fahimta ya canza ra’ayinsa dan yasan halinsa .”
Mr ata ya mike ya fito sultan ya biyo bayansa cike da farinciki kai tsaye office din su maryama ya shiga akayi saa duk kusan wadan da yake aiki dasu suna gurin har maryama tunda ya shigo gaban maryama ke fad’uwa sakamakon idanunshi dake kanta “ya numfasa sannan ya soma magana “acikinku wa yake son yayi aiki akarkashin sultan ?gabadaya office din yayi shiru babu wanda yayi magana wanda hakan ya nuna basa bukata ,maryam kam taso tace zatai aiki dashi tunda shi wannan balainsa yayi yawa amman har sanda mr ATA ya gama maganarsa ya shiga wata bata iya cewa komai ba “duk wanda yake bukatar yayi aiki akarkashinsa ya daga hannu? nan ma shiru maryama ta kalli gabadayansu ma’aikatan wurin taga babu alamun akwai wanda Ke bukata dan haka tayi qoqarin daga nata hannun wanda hakan yasa cikin hanzari mr ATA ya cigaba da magana wanda kuma yasan zai kasance akarkashina ya daga hannu ?gabadaya suka daga hannu banda maryama alamun bata tare dashi .”
sultan yaji zafi sosai kenan duk matanka iko da kaidodin da yake masu da balain da hantararsa sun fi bukatar kasance akarkashinsa akan shi lallai sai ya tashi tsaye akan ATA .”wani kallo mr ATA yayi wa maryama ganin har lokacin taki daga hannunta yayinda kowa hannunsa Ke sama d’auke idanunta tayi cikin nashi tana hura hanci “ka gani sultan babu ruwana kawai ni business dina ne agabana bani da burin shiga hakin kowa idan kamfani ne kasan ina dashi masu tarin yawa anan ma ku nake taimakawa da rayuwarku domin idan na barshi barayin cikinku zasu karyar da kamfani qarshe ku dawo kuna bara a wurina which’s very bad .”ya fad’a yana kallonsa a dage ,yanzu ko zaka iya tafiya kasa a nemo maka wasu maaikatan da zasuyi aiki da kai dan wadan nan nawa ne ?”
Tun bai kai ga rufe baki ba maryama tace “sir ko zan iya cewa wani abu ?yayi shiru yana dubanta cikin tsananin fad’uwar gaba yana fargaban bata damar yin mgn d’an bai san me zatace ba hakan nan ya tsinci kanshi cikin tashin hankali da fargaba dan dai shi din miskilin kanshi ne da gabadayansu zasu iya fahimtar yanayin daya shiga “kayi shiru sir ko zan iya cewa wani abu ?ta sake maimaitawa sai daya sauke naunayen ajiyar zuciya a boye sannan yace “yes!.ta rausayar da kwayar idanunta cikin nashi sannan ta bude baki a natse ta soma mgn “sir dayawa daga cikinmu suna jin tsoron su amince da wannan da bansan ko waye shi ba sbd da kai koda kuwa suna só , haka zalika suna jin tsoron suki amincewa da zama kusa da kai duk dai saboda tsananin tsoronka .”sultan ya gyada alamun ya gamsu da maganarta domin daí gsky magana ta tsage ta fad’a kuma ta burgesa sosai kawai ka barshi ya zabi wadan yake so acikinmu .”
gabansa ne yayi wani mummunar faduwa nan take fargaba da tashin hankali da yake ciki ya qaru ya tsura mata tsumammun idanunshi sosai yana jin wani iri a ilahirin jikinsa shi da yake burin matso daita kusa dashi sosai idan ya kasance sultan ya zabeta fa ya zai yi ?muryarsa a kasalance yace “me kika ce ?karka yi kamar baka jita ba alhalin kaji abinda ta fad’a,wannan yarinyar gsky ta fad’a domin ta kawo mana masalaha dan haka zan zabi wadan da nake son suyi aiki akarkashina cewar sultan ,mr ATA bai ce uffan ba illa ya runtse idanunshi qirjinsa na wani irin luguden bugu dan dai itace ta kawo wannan tsarin da wani ne da shi kad’ai yasan irin azabar da zai yi masa amman ko yanzu bazai barta haka ba sai ya hukuntata .”
“Ba wai kai mai wayo ba ,yasan yayi hakan ne dan yasan babu mai zabarsa acikinsu sai gashi acikinsu din dai wata ta kawo masu masalaha sultan yayi mgnr aransa Ahankali ya soma zaba ya nuna surayya da sauri tace “sir ni yanzu haka ina Kan wani aiki ne ban gama ba “shiru tunda na zabeki ki shin ga cikin list, jin hk yasa mr ATA ya bude idanunshi da kyar tare da tsintar kanshi da yin adduar kar ya zabi maryama yayinda maryama ta matsu bai yi pointing dinta ba ya nuna wasu maza guda biyu sannan ya nuna sultana da sauri itama tace “haba yaya me yasa zaka min haka ni dai ka barni nafi son nayi aiki tare da ya Adam .”
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 12
“Har mr ata ya fito haraban ma’aikatan zuciyarsa tafasa take . da wannan d’acin rai ya qaraso gida duk wani d’aga hannu da securities suke masa bai kalli inda suke ba ,hakan yasa duk suka shiga hankalinsu alokacin da jerin motoncinsa suka paka babu wanda yayi kaud’in isa inda yake dan duk lokacin da yanayinsa yayi haka to gagarumin bala’i ne zai biyo baya.haushinsa ba’a iya kan wanda ya ta’bosa yake tsayawa ba har akan wanda bai da ruwa da tsaki yake saukewa , dan a irin wannan lokacin yake korar mutun daga aiki ko kuma ya bawa mutun hutun satittika.” tun kafin yasa kai cikin babban parlour’n gidan ya soma jiyo hayaniyar mutane sai lokacin ya tuna ashe gobe ne zaayi sunan auta.” a dake ya sanyo kai cikin parlour’n fuskarsa babu digon annuri bai tsaya ba kai tsaye samansa ya nufa batare daya kalli tarin matane dake zaune a parlour’n mami ba, ita kanta mami bai nemita ba sakamakon kansa dake masa mugun sara .
“Ahankali ya zauna akan daya daga cikin kujerun cushions din parlour’n sa kanshi na cigaba da sara gabadaya ya kasa samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali.”ji yayi muddin bai kira maryama ya mata bala’i ba bazai ji dadi aransa ba sannan zuciyarsa bazata samu kwanciyar hankali ba dan haka ya soma neman layinta. shigowar maryama kenan tana yiwa umma sannu da gida inda umma Ke tako wa zuwa inda take tsaye tana tambayarta “yau kin dade a wajen aiki .muryarta a gajiye tace “wallahi wannna boss din namu ne sai ahankali nan ta shiga korowa umma abinda ya faru da yadda suka rabu dashi “ikon allah shi kuma haka nashi tsarin yake ?” “ke dai bari umma mutane na mugun shan wahala a hannunsa amman fa duk da wannan takurawar tasa wai haka suke son aiki akarkashinsa nifa ina ganin zan soma neman wani aikin dan bazan jura ba“Allah ya zaba miki abinda yafi zama alkhairi ko cigaba da aiki akarkashinsa ko samun wani aiki “amen umma “! maryama ta fad’a tana cire jakarta tana qoqarin ajiye jakarta kenan wayarta ta d’auki qara ta d’auka tana duba screan din wayar suann “sir ! ta gani wato sunan mr ATA ne yake yawo a screen din wayar tayi shiru tana jin kamr ta d’auka sai kuma tayi tunanin kar ta d’auaka dan batasan me kiran nashi zai haifar mata ba gara ta sharesa dan haka ta kashe wayar gabad’aya gaban ta na fad’awa ta shige d’akinta .”
Yayinda adaidai wannan lokacin mami na zaune agefen gadonta kusa da maryam tana cewa"haba maryam banason ina ganinki shiru , yawan tunani ko saka damuwa a zuciyarki shin zai miki maganin halin da kike ciki ne? "Jin haka yasa maryama fashe mata da kuka dan daman danne kukan take tana yinsa a cikin ranta “subhallah !”mami ta furta tana riko hannunta cikin nata “haba maryam daga magana meye kuma abun kuka ?”tunanin ne banaso bare ganinki cikin damuwa “akwai abinda aka miki ne kika dawo nan ke kad’ai ki baro yan’uwanki ?cikin muryar kuka maryam ta girgiza mata kai tana saka hanu ta rufe bakinta saboda wani kukan da yake kuma tahu mata suna cikin wannan halin sai ga nana hauwa’u ta shigo bayanta aunty khadija ce rungume da baby da sauri suka qaraso suna tambayar mami “lafiya mami me kuma faru maryam take kuka ? .”
“nan mami ta fad’a masu tsaki aunty khadija tayi sannan ta soma yi mata fada cikin zafin rai “ki zauna kashe kanki abanza ki cuci abinda zaki haifa dan wanda kike damuwa akanshi bai san kina yi ba wai shin dole ne da bazaki rabu dashi da tunaninsa ba ?”a’a khadija banaso haka dame kike son taji ?ke daya kamata ki rarrasheta ki kwantar mata da hankali tunda Kinsan ba'a son tana yawan shiga damuwa da tunani saboda cikin jikinta “.Allah mami maryam din ce da kayan haushi mutumin ko kallon inda take ba yayi bare ya duba situation din da take ciki amman ita kullum cikin damuwa take ,yanzu ki duba kiga kowa tsabgar gabansa yake cikin walwala amman ita ta dawo nan tana damun kanta da tunanin banza da wofi ta qarasa maganar tana jan tsaki sannan ta juya ta fice .”
nana hauwa’u zama tayi kusa daita suka saka maryam a tsakiyarsu .ita kam maryam kuka kawai take dan bata da abinda ya wuce kuka most especially idan ta tuna abubuwan da tayi duk akan adam amman babu abinda yayi tasiri akanshi da kyar suka samu tayi shiru ta share hawayenta tare da zabga tagumi still dai tunanin da basa son tayi shi ta sake lulawa ahankali mami ta dinga mata nasiha .” yayinda mr ata yake can bangarensa bai fito ba sai dai zuwa lokacin yayi wanka ya sauya kaya zuwa na shan iska .”wayarsa ya d’auko ya sake kiran number maryama sai dai amsa daya ake bashi wayar is switch off…..Oh my godness god wai me yake faruwa dani ne? komai ya zama worst a gareni? me ma yarinyar nan ta take nufi dani ?“anya kuwa yarinyar nan bazata haukata ni ba ? wannan shine tambayoyin da ya cigaba dayi a zuciyarsa yana jin zafi mai quna a ransa .”
Zaune yake shiru a parlour’nsa rike da waya layin maryama yake nema amman still a kashe ya duba agogon wayarsa karfe goma ta wuce tsaki yaja “may be tayi baccinta ya furta a fili yana rufe bakinsa aka turo kofar parlour’n aka shigo saurin waiwayowa mr ata yayi,ahankali kuma ya d’auke kanshi yana fesar da iska ganin yaya hisham ne ahankali yaya hisham ya dinga takowa har ya qaraso inda yake ya tsaya gaban Mr ata yana kallonsa kawai, rasa abun cewa yaya hisham yayi saboda yadda yaga fuskar mr ata alokacin tana cikin wani yanayi daya kasa fassarawa ko da ganin haka sai ya samu waje ya zauna ya zuba masa ido kamar yadda yayi masa, a hankali yaya hisham ya saki fuskarsa zuwa yanayin mur mushi, yace” ATA nazo maka da wani albishiri mai dadi mr ata yayi shiru yana kallonsa yana jiran yaji wani irin albishiri ne duk da baya tunanin akwai abinda zai wanke masa zuciya ahalin da yake ciki .”
“babynmu yaci sunan abbanku muhammed tariq ga mamakin yaya hisham murmushin ata ya fara daga yanayinsa sai daya bashi wasu mintuna sannan ya bud'e baki ya cigaba da magana ! Mr ata what this smile ?" wani sabon murmushin ya sake yi cike da tsananin farinciki mara misaltuwa cike da murya Ata Ya furta "ya Allah.! Amman gskiya naji dadin wannan alamarin allah kuma ya raya min ya kuma shirya ma mai sunan babana albarka “Ameen yaya hisham ya furta a fili fuskarsa cike da tsananin murna. yayi mamaki Kwarai da gaske domin bai dauka zai ji dadi har haka ba shikenan fad’a ya qare atsakaninsu a natse ata ya mike ya nufi hanyar fita waje fuskarsa dauke da murmushi yaya hisham ma ya biyosa kai tsaye dakin mami ya shiga anan ya iske mami da yaranta kaf har da