Showing 63001 words to 66000 words out of 178062 words

Chapter 22 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

jikina ya kama rawa.” taso ta fad'a masa idanunsu ne yayi mata yawa amman sai ta tsinci kanta da kasa fad'ar haka dan batasan me hakan zai haifar ba tunda ta rigada tasan halinsa abu kad’an ke hassalashi "idanun maza yayi miki yawa kina gani bai kamata kiyi aure anan kusa ki huta ba "?tayi shiru tana cigaba da kallonsa yayinda qararrawar zuciyarta na kad'awa da sauri sauri sakamakon kusancin da suka samu na haifar mata da shiga cikin wani yanayi "ya dai kamata kiyi tunani ko sanin cewar ke matar aure ce zai saukaka miki wasu abubuwan ."numafshi ta janyo ta sauke da kyar tana sake sunkuyar da kanta gabdaya ta sake neman natsuwarta ta rasa rawar da jikinta keyi ta qaru ".






“Maryama ki tsaida miji kiyi aure zai fiye miki kina aure kina aikinki , dan bai dace ki dinga kula kowani kare alade da jaki ba "idan dai kema din ba irin hallitarsu gareki ba ."ya qarasa mgnr yana jan tsaki tabi shi da wani irin kallo zuciyarta na tsinkewa idan ta fahimcesa da kyau" idan halittartata ba irin ta jaki kare da alade bace ta daina kula kowa kallonsa take fuskarta da bayananen mamaki “to shi da yake kulata take kulasa fa ?”kenan shima ya kasance d’aya daga cikin abinda ya lissafa kare da alade da jaki ne ?”tayi maganar a can kasan makoshinta ta yadda ko shi da yake zaune a gabanta bazai iya fahimtar komai .ya juya ya d'auki kwalin sigari ya bud’e ya zari d’aya ya kai bakinsa ya kai hannu ya dauki abun kunnawa tana ganin haka ta zabura ta mike ranta a matukar bace ta nufi kofar fita tana jan tsaki da kallo yabi bayanta yana ta'be fuska "abinda zaki qarasa tsawon rayuwarki daita itace abar gudu ai gara ki fara sabawa daita sannna ya lumshe idanunshi lokacin guda kuma ya budesu yana cewa "ke dawo ki zauna ."!








Maryama taki tsayawa bare ta dawo kamar yadda ya bukata "idan kika kuskura kika bar office din nan ki tabbatarwa kanki kin tafi kenan har abada bazaki sake da aiki a AGC ba ".cak taja qafafuwanta ta tsaya tana sauke wani wahalallen numfashi daga inda yake zaune yana kallon yadda kafad’unta suke d’agawa sama alamun tana kokuwa da numfashinta Ahankali ta juyo tare da sunkuyar da kanta kasa dan bazata iya cigaba da kallonsa a yanayin da yake ba saboda yayi mugun tsareta da ido yana kallonta tana takowa ahankali har sanda ta qaraso ta tsaya "set "! ya fad'a yana kunna sigarinsa muryarta sanyaye tace "sir kayi hakuri ka kashe wannan abar bana son warinta "daga yau ki koyi son warinta set !ya sake maimaitawa" inna ilaihi ita kam ta shiga ukunta da wannan mutumin ta sake yin kasa da muryarta sosai kmr zatayi kuka "sir kada kamin haka dan Allah "me nayi miki ?"ya tambayeta yana dage mata girarsa d’aya “sigari ce fa kawai ?meye illarta?" set and don't let me repeat my seif again ".






babu yadda maryama ta iya da rayuwarta haka tayi shiru ta toshe hancinta da hannunta d'aya dayan hannun kuma taja kujerar baya kad'an domin rage kusancinsu ta zauna sai dai duk a rud'e take .
tunda ta zauna bata d'ago kanta ba yayinda shi kuma kwayar idanunshi ke kanta yana zugar sigari yana zance zuci "ta d'ara duk matan duniya a idanunsa ita kadai zuciyarsa take so ,kuma bazai ta'ba son wata bayanta ba ,sai dai duk runtsi bazai d'auki raini daga gareta ba farar takadar ya janyo ya ajiye mata sannan ya janyo wata roba da kayan zane yake ciki shima ya ajiye mata "ki zanani ahaka .
"what ?" !
ta furta à matukar razane tare da d'ago fuskarta ta tsura masa yana rike da sigari yana zuga muryarta a raunane tace "sir kayi hakuri bazan iya zanaka kana shan sigari ba ka canza min da wani aikin na yarda "okay ! zana min mata da miji rungume da junansu suna kissing din juna a bakin kofa "oh my goodness god ya rabbi ka taimakeni akan wannan mutunin ta furta a can qasan makoshinta sannna ta sake tsura masa idanunta gbdy ta rasa natsuwarta ji take kamar zuciyarta zata buga haka ne ma yasa ta cigaba da kallonsa ko dai a buge yake ne ?sai dai tsaf yake abunsa idan ma baa a gabanka yake shan sigari ba bazaka ta'ba cewar shi din dan sigari bane dan babu abinda ya nuna ko ya sauya ajikinsa "Kina 'batawa kanki lokaci domin kuwa babu inda zaki har sai kinyi abinda nake bukata."







Mmn sudais[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 19






Zuciyar maryama cunkushe da haushi had’e da takaicin mr ata ta zari pencil din zane ta soma aikin daya sakata wanda tai masa laqabi da aikin mugunta tana zane bakincikinsa na sake ninkuwa a kasan ranta, yayinda zuciyarta ke wani irin zafi da suya .
ina ma zata iya murje idanunta tare da cire d’an burbushin tsoronsa dake ranta ai wallahi data zage kunjinta ta zabga masa rashin mutunci fiyye da wanda ya iya .amman ina bazata iya ba ,bazata iya karawa da mr ata ba ,dan ko a yanzu ya gano wani abu daga cikin rauninta domin kuwa ya fahimci aikinta yana da matukar mahimanci arayuwarta.
cikin kankanin lokaci ta zana namiji sanye da kaya wondo da riga tare da jacket sannan ta zana mace tana rungume da namiji sanye da dogon riga kanta lullu’be da mayafi,ta gama amman tsabar ‘bacin ran sigarin da yaketa faman bankawa cikinsa yana busa mata hayaki ya hanata d’agowa ta kallesa bare ta sheida masa ta gama.”shi kuwa mr ata zuba mata ido yayi ganin yadda ta gama amman tana jin wani abu aranta yasa ya sake ware qafafuwansa ya kunna wani sigari a ransa yayi murmushi ,shi ko kwana zasuyi a hk daidai ne.”






“ ganin muddin bata yi managa ba zasu kwana a haka ba damuwarsa bane dan ta tabbrwa kanta miskilancisa da jin kansa bazai barshi yayi magana ba , dan haka cike da tsinkewar zuciya da kyarma jiki ta d’ago fuskarta inda yake karaf idanunsu ya tsarke cikin juna ,ganin haka yasa maryama sake had’e ranta tamau dan bata son ya kawo mata wani sabon rainin hankali ko rainin wayo tare da d’aga masa farar takardar hannunta tana nuna masa alamun ta gama .” kina son ki zamo matsalata?” yayi mata tambayar yana tsareta da tsumammun idanunshi ahankali ta girgiza masa kai tana cewa “bazan ta’ba son na zamo matsalar kowa ba ,abinda kasani kenan sir , kuma wannan shine iya abinda zan iya yi . shiru yayi kawai yana ajiye qarshen bakin sigari acikin wani dan qaramin kwanon tangaran .”sannan ya cigaba da dubanta tare da cewa “tsarin yanayi rungumar bai min ba kasancewar babu remotic .“
ta kalleshi da tarin mamaki akan fuskarta lip’s dinta take matsawa alamun magana take son tayi masa sai dai ta kasa furta komai dan zuwa yanzu gaba d’aya a firgice take dashi .”




Yanayin zamansa ,yanayin kallonsa ,yanayin maganarsa duk sun canza dan hatta kwayar idanunshi sun canza kala yayinda shirunta ya
bashi damar kallonta son ranshi dan ko son kifta
ido ba yayi ,ga wani kalar murmushi da yake wanda shi karon kanshi bai san yana yi ba sosai itama ta shagala da kallonsa amman ita kallo ne dake tattare da tashin hankali da tsoro ,ahankali ya matso kusa daita ya hura mata iskar bakinsa da sauri tayi kasa da kanta tana jin wata irin fargaba yayinda gabad’aya ilahirin jikinta rawa yake .zuciyarta ta cika fal da matsanancin tsoronsa ,jigun sukayi daga shi har ita barin maryama wacce komai ya tsaya mata cak ,yadda bai sake yin mgn ba itama bata ko motsa ba daga inda take zaune sai dai kowannen su da abinda zuciyarsa ke saqawa acikin zuciyarsa .”
zurfa goshinta ta share tana kallon mr ata tace “sir ko zan iya wucewa “?numfashi ya sauke da kyar yana soka yatsan hannunsa a gefen bakinsa.”






“ kamar yace mata “a’a sai kuma yayi mata alama da hannunsa dan ya tabbatar muddin yace zai yi taurin kai zata maimata masa abinda tasaba ,dan yana ji kuma yana gani zata wuce abunta ta barshi zaune ” ahankali ta mike ta biyo ta raba gefensa zata wuce har jikinta na zozon jikinsa saurin d’auke numfashi yayi yana jin kamar ta jona masa wutar lantarki ne
ta juya a natse ta soma daga qafafuwanta da kyar gyara zama yayi tare da ware qafafuwansa yana bin every step of her tafiyarta kad’ai aka bar mutun dashi wani abu ne mai tsayawa arai bare akai ga samunta gabad’aya .”ahankali ya dinga bin kugunta da wani mayataccen kallo cikin salon magana yace “wannnan kugun zai sha wuya a hannuna domin kuwa bazan ta’ba saurara masa ba haka zalika wannna bakin rashin kunyar zai sha kissing har sai yayi kukan neman sausauci.”sai bayan la’asar maryama ta soma shirin tafiya gida taso kwarai ta sake yi masa magana akan sabon aikinsu amman sai taga gara kawai ta rabu dashi idan ranar ta kusa zata sake nemansa da maganar wata killa zuwa lokacin ya amince suyi .” wucewa tayi abunta tana tunani hali irin na mr ata “tsarin yanayi rungumar bai min ba kasancewar babu remotic girgiza kai tayi tana murmushi.”


******


Da daddadre da misalin karfe takwai yana zaune atsakiyar gadonsa hannusa rike da remut ya canza channel zuwa breaking news yana kallo sai dai hankalinsa baya wajen kallon labarai yana gurin tunanin yadda zai mallaki maryama ne cikin sauki har sanda mami ta shigo hannunta rike da cup din coffee'nsa bai sani ba ta tsaya shiru tana kallonsa tana nazarinsa kafin ahankali ta kira sunansa "adamcy "! yayi firgigib ya dawo haiyacinsa yana kallonta "kar’bi !" ta mika masa cup tana cewa "wai meye matsalarka madadin naga lapto agabanka kana Kan aiki amamn kayi busy kallo kana tunani ".
"na gaji ne sweetheart !"ba maganar ka gaji bane what's wrong with you?" ta tmbyesa tana kallonsa " me kake tunani yanzu koda yaushe cikin tunani kake , meye matslarka"? babu !"ya fad'a atakaice yana kai cup bakinsa "akwai gskyar ko damuwar da zaka iya boye min duk yadda mami tayi dashi yaki fad'a mata damuwarsa abinda bai saba mata ba Kenan ya ajiye cup din hannunsa ya koma Kan kujera ya zauna ya dafe goshinsa."





ta dawo kusa dashi ta zauna" abinda kake min wani lokaci yana damuna "ya d’ago ya kalleta kawai kuma zai iya kashe ne tun kwanakina basu kai ba .”ta fad'a tana dubansa shi fa duk saboda wannna yarinyar maryam ne yasa baya jin zai iya fad'a mata damuwarsa domin dai ya fad'a yaga mafarkinsa a yanzu zai iya janyo masa damuwa bugu da qari shi karon kansa bai san takamaiman makomarsa ba ta yaya zai fito da damuwarsa yana cikin zance zuci ya cigaba da jin maganarta "idan ka kamu da soyayyar yarinyar nan dake aiki a qarqashinka fine let me know?" ya sake d'agowa ya kalleta atsanake amman still bai ce mata komai ba dan ba maganar kamuwa bane magana ce tsananin qauna kuma jin zai iya hakura daita duk runtsi duk wuya sai ya mallaketa kuma acikin wannan lokaci zai organizing wasu mutane dabam su nema masa aurenta ."






“Adamcy boye abu acikin zuciya yana saurin cutar da dan Adam,sannnan boye abu shi da kyau a zuciya yana da kyau mu samu wadan da zamu dinga sharing secret dinmu dasu. wannna shine karo na farko da ka boye min damuwarka .dan haka zaka iya tsintata cikin damuwar datafi taka .sam baya ma jin maganr da mami take masa dan hankalinsa gabaday baya ga mami yana ga yadda zai mallaki maryama ne, tunanin hanyar da zai bi ya bayyana mata matsayinta da kuma su wa ya kamata ya saka zuwa neman aurenta da yake bukata arayuwarsa yake .
Mami ta kallesa taga hankalinsa da natsuwarsa baya gurinta shima wannan ne karo na farko da take masa magana hankalinsa baya gareta ba dan haka ta mike ta fito daga d’akinsa sai dai zuciyarta ta tsayu ne akan danta ya kamu da son wannan bazawarar yarinyar ita ko zata so tagansu tare domin kasancewarsu waje d’aya zai tabbatar mata da zarginta “bazawara!”zuciyarta ta furta hakan a fili .”






Yau ma kamar jiya maryama bata qaraso gida ba sai daf da sallar isha’i a gajiye ta shiga bangaren ummah tayi mata sannu da gida “sannu maryama ya aiki ?”naunauyen ajiyar zuciya ta sauke tana cewa “ummah aiki da mr ata sam babu dadi amamn a haka zamuyita lalla’bawa ,ta fad’a tare da shigewa d’akinta murmushi umma tayi tace “ke dai da wannan mutun allah ya d’auraki akanshi idan ba haka ba bazaki ji dadin aiki dashi ba “maryama tana shiga daki ta fad’a bayi tayi wanka tare da dauro alwala ta fito daure da towel orange tana goge sansar jikinta byn ta gama ta d’auki terry dream’s ta feshe ilahirin jikinta sannna ta zura doguwar riga baka ta gabatar da magrib da isha’i dan zuwa lokacin an kira sallah byn tayi sallama ta ‘daga hannuwanta zuwa sama ta soma addua ta kira allah da sunan daake kiransa yake amsawa, kuma idan an rokesa dashi yake amsawa “allahumma as alukal bi anna lakal hamda laila ailla anta ,wahdaka lasharika laka ,al mannan ya badi’us-samawati wal ardi ya zal jalalu wal ikram ya hayyu ya qayum inni as alukal janna wa auzubika Minan nar har da mr ata tasanya cikin adduarta allah ya shiga tsakaninta dashi .”






Bayan ta kammala ta mike tare da daddumar sallah tana nadewa ta fito zuwa parlour inda umma take zaune ta d’auki jakar aikinta tana cewa “umma zan shiga wajen aunty idan goma tayi baki ganni ba ki rufe gida “to shikenan abinci fa bazaki ci ba ?ko zaki turo habib ya kar’ba miki ?”ko da yake ba abincin da kike so nayi yau ba .maryama tayi murmushi tana tambayarta “umma me kika dafa ?”tuwon samoviter ne da miyar kuka nan take maryama ta kwa’be fuska dan gaskiya bata qaunar tuwo da duk wani abu daya zamo loma bata só sai dai tsananin yunwa tasa taci dole “umma bari naje Allah yasa aunty ba tuwon tayi ba itama ”to shikenan yasa ki samu abincin da yayi miki idan itama tuwon tayi ki aiko habib ko ki kirani sai na dafa miki ko indomi ce “shikenan umma nah na gode .”tasa kai ta fito ta wuce part din mahaifiyarta inda ta samu abinda take so .”






Jollof din rice and beans aunty tayi wanda yaji busashen kifi da vegetable taci sosai kasancewar tana matukar so duk wani abu da zaa sarrafashi da wake bayan ta gama cin suka shiga hira da aunty da habib tana aiki habib ya dameta sosai da tambaya “daman kusan hayaniyarsa ke hanata zama a bangresu idan tana da aiki dan baya barinta tayi “heartbeat dan Allah ki bar aikin nan muyi hirarmu ta tsaida abinda take ta zuba masa ido “ance wannan mai kamfanin AGC din yana matukar takura miki dayawa ?Injiwa yace maka yana takura min ?yayi murmushi yana shafa fuskarsa “abakin lancin kanin yusura naji maryama tayi murmushi dan tasan tabbas a bakin yusura yaji “dan Allah ki bari naje naci miki ubansa mana ?yayi maganar cike da zolaya maryama ta zaro waje duk da tasan da wasa ya fad’a,can kuma kwashe da dariya “ai kuwa daga ranar na daina aiki dashi bayan yasa anci masa ubanmu,after dad ai wannan mutumin ya wuce da tunaninka shegen kanshi ne duk abinda mutun yake ji dashi zai sauke masa shi cikin isa da miskilanci shiyasa yanzu har cikin addua nake saka shi .”






“Ai kuwa kin kyautawa kanki gara ki dinga hadawa da addua kuma ki dinga binsa ahankali banson a cutar min dake “inji cewar aunty wacce ta mike ta nufi hanyar d’akinta ta barsu suka cigaba da hirarsu maryama lumshe idanunta ta soma tattara takardun zanen dake watsewa akan kujera ta mike tsaye tana cewa “gara na tattara na koma inda na fito dan bazaka barni nayi aiki ba ta leka dakin aunty tana cewa "aunty zan wuce part din umma "a can zaki kwana mu kulle gida ?eh ! aunty a can zan kwana halan habib ya hanaki aiki? maryama ta rausayar da kwayar idanunta kawai “to shikenan allah ya tashemu lafiya Ameen ta fad'a tana juyawa tare da kiran habib yazo ya rufe gida ta wuce part din umma,ta iske kofa a bude dan haka turawa tayi kawai ta shiga inda iske umma tana massaging kafafunta tana runtse ido da sauri ta qaraso ta ajiye jakarta ta karbin man aboniki dake rike a hannunta tana cewa”ummah sannu bari nayi miki “to maryama nã gode allah yayi miki albarka “Ameen umma maryama ta fad’a tana mai tsananin jin tausayin umma aranta kuma tana tsanani qaunarta kuma zata kasance daita muddin rai zata maye mata gurbin komai arayuwa .”






Ahankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login