Showing 144001 words to 147000 words out of 178062 words

Chapter 49 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

masa sunanta hakan nan ya tsinci kanshi cikin tsananin shaukinta yana tuno yanayin daya barota.”








Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.






Page 42






Mr ata ya kasa tashi daga zaunen da yake yana cigaba da tunanin maryama kukanta na d’aya daga cikin abinda yake matuqar d’aga masa hankali da tsuma zuciyarsa ,dauriya kawai yake, kasancewar soyayyar da yakewa maryama yafi wanda yakewa kanshi fatan shi Allah yasa ta so shi fiyye da komai.”sosai yayi zurfi cikin tunanin maryama yayinda mami take zaune tana kallon kyakkywan fuskar tilon d’an nata .”ahankali mr ata ya ajiye hannunsa mai ciwo a saman cinyarsa yana jijiga qafarsa d’aya wanda hakan ya bawa mami damar ganin bandage din dake hannunsa .”a matukar tsorace take kallonsa jikinta har rawa yake gurin kiran sunansa ”adamcy!” a natse ya bud’e idanunshi ya zuba mata yana dubanta a tsanake “me nake gani haka a hannunka?ko kuma nace me ya sameka a hannu?”tayi masa tambayar ajere cikin tsananin tashin hankali ahankali ya sake lumshe idanunshi yana tunanin abinda yayi sanadin jin ciwon nashi .”






“Cikin tsananin tashin hankali mami ta mike tsaye ta soma taku tana dubansa da ciwon nashi har ta qaraso inda yake zaune ta zauna kusa dashi tana kallon bandage din dake nad’e ahannunsa kafin ahankali tace “adamcy garin yaya kaji ciwo a hannunka?”shiru yayi mata tare da kamo lip’s dinsa na kasa ya soma cizawa yana tunanin abd zai fad’a mata “kamin magana mana ?”numfashi ya sauke yana bud’e idanunshi sai daya d’an fito da harshensa kad’an ya lashi lip’s dinsa sannan ya fara magana a kasalance “wani abu ne ya faru yau a office kin san halin naki shine fa bansan yadda akayi ba kawai naji na samu wannan ciwon “kai da wa?”yaji tai masa tambayr ta qasan idanunshi ya d’auki kallonta “nace kai dawa kukayi rigima? ta tambayesa tana mai tsaresa da kwayar idanunta hakan nan ya tsinci kansa da cewa “.maryama .”!
“Maryama .” mami ta furta sunan sai da mami ta furta sunan sannan ya fahimci yayi kuskuren ambatar sunanta dan haka ya kai hannunsa ya shafa sumar kanshi yana cewa “wani suna na kira yanzu ?”maryama kace !”numfashi yaja da qarfi ya sauke yana kawar da kanshi gefe “.wni irin yanayi mami ta tsinci kanta ciki na tsananin damuwa “amman me faru tsakaninka daita haka ?”.
ba wani abu bane sweetheart kawai dai ….“sai dai yayi shiru ya kasa qarasa maganarsa “ban gane ba wani abu bane kawai dai ?”yarinya tayi maka illa haka amman kace ba wani abu bane ?”mami tayi maganar cikin tsananin ‘bacin rai “wallahi adamcy kasan abinda kakeyi na fahimci kana boye min abubu wa akan yarinyar nan abinda baka saba min ba aman yanzu duk shi kake min kuma duk akanta ne .yanzu data kasheka fa ?”d’an zaro idanunshi yayi “eh !”mana ai na d’auka tana da hankali she dai bata dashi idan ba haka ba komai zaka mata yanzu ya dace ta ji maka ciwo?”
”yanzu daya zamo silar mutu warka fa “no sweatheart karki yi wannan tunanin kawai dai tsautsayi ne amman kwata kwata bata da laifi idan akwai mai laifi to ni ne domin ni jiwa kaina ciwo .”yana gama fad’ar haka ya mike ya nufi hanyar step mami tabi shi da kallo tana jin zafi aranta dan kwatakwata
Bata qaunar abinda zai ta’ba lafiyar yaranta most especially shi .”








Bangaren maryama tsayuwa ta cigaba yi cikin matsanancin tashin hankali “maryama shiga mota muje ko.”! “madam some tace daita tana qoqarin bud’e mata gidan gaba dan ita kam ta gaji da tsayuwa madadin maryama ta shiga sai ma ta juya ahankali ta soma tafiya tana cewa “bari naje na d’auko jakata.” madam some tabi bayanta da kallo batare da tace mata koma ba sai dai zuciyarta cike take fal da jin tausayinta .
maryama bata wani jima ba ta dawo makale da jakarta ta shiga gaban mota ta zauna tare da takure jikinta waje d’aya tana goge hawaye idanunta inda tuni madam some ta shge mazaunin direba.”hankali suke tafiya hawaye kawai maryama take gogewa yayinda madam some take faman sauke ajiyar zuciya akaro na barkatai had’e da sake rike stearing mota tana kallon agogon dake d’aure da tsintsiyar hannunta.”a fakaice madam some ta kalleta ta gefen ido sannan ta maida hankalinta akan tuki “Ina ganin ya dace ki bar kukan nan haka idan ba haka ba mutanen gidanku zasu fahimci akwai damuwa atattare dake .“kamar kar madam some ta fad’a haka hawaye suka shiga turereniyar zubowa daga cikin idanunta “shine babban tashin hankalina ma.” “bana son yan gidanmu su san halin da nake ciki “ai kuwa babu abinda zai hana basu fahimta ba da wannan kukan da kike “nasan kina wannan kukan ne dan kar su ga hotunanku da mr ata to fa ba lallai su gani ba tunda ni a fahimtata iyamu kawai ake son mu gani “dan Allah ma ki taimakeni kar hotunan nan su fita idan suka fita bansan ya zanyi da rayuwata ba, tun farko na fara rayuwata ne acikin qunci ban san wani abu wai shi farinciki ba sai daga bayan nan ne na d’an samu sausaucin rayuwata ki taimakeni banason na koma baya “is okay maryama ki bar kuka ki bar komai a hannun sir da sannu zai gano komai dan nasan bazai bar abun ya tafi haka ba, ko babu komai dole zai qare mutuncinsa dan haka ki kwantar da hankali ki share karki nuna alamar akwai wata matsla ,maryama ta gyad’a mata kai tana qoqarin saisaita kanta .har suka isa unguwarsu maryama madam some na kwantar mata da hankali .”









“Tunda maryama ta isa gida ta kasa aiwatar da komai duk da tana ta qoqarin kawar da damuwar dake tattare daita sai dai kallo d’aya zaka mata ka tabbatar da bata cikin natsuwa da kwanciyar hankalinta minti minti take sauke naunayen ajiyar zuciya ,kuma irin wanda yake fitowa daga kasan zuciya umma sarai ta fahimceta dan haka ma ta isketa ta tamvayeta amman tsananin zurfin ciki irin na maryama ta kasa cewa daita komai ,ganin tunani zai mata yawa kuma hakan zai iya barin hankalin umma yaki kwanciya yasa ta d’auko littafi ta dawo parlour ta zauna tana dubawa wanda hakan bai rage mata komai daga cikin d’igon damuwar da take cunkushe a zuciyarta ba.”
ahankali take bin littafin tana goge hawayen dake tsiyaya a gefen idanunta ta d’auki kusan mintuna talatin tana zaune tana duba littafin da babu abinda take fahimta aciki idanuwanta sukai mata nauyi sosai saka makon abu biyu da suka had’e mata waje d’aya bacci da kuma damuwarta. anan ta zame ta kwanta akan kujera tare da yin shiru tana zance zuci “ko a wani hali mr ata yake ?”ko me ya iske a gidansu ?”haka nan take jin ya dace ace ya kirata yaji halin da take ciki, ko tana tare da matsala ko akasin hk?” dan tabbas ya kamata ya kirata yaji yata qare ta iske an turo hotunansu gidansu ko kuwa amman ya shareta “wato kowa yaji da damuwarsa.”






sannu ahankali bacci ya d’auketa da tunanin mr ata acikin ranta ,acikin bacci ne taji ana shafata ana mata massagin jikinta ana mata magana cikin wani irin salo.”ahankali ta bud’e idanunta ganin mr ata tayi manne ajikinta,ya d’aura kanta adaidai damtsen hannunsa yayinda bakinta ke daidai nipples dinsa ,ta d’ago kanta zuwa fuskarsa, janyota yayi jikinsa sosai yana cigaba da shafa sansar jikinta “kina dani ki daina damun kanki too much duk wanda ya ta’ba min ke zanji dashi “zare jikinta tayi daga nashi ta tashi zaune tana girgiza masa kai tana share hawaye tace “kai din ba nawa bane taya zan yarda da Kai ?”
ya janyota zuwa jikinsa yayi mata kyakkwan runguma a faffad’an qirjinsa“ki yarda dani“!
ya fad’a yana d’aura lips dinsa akan nata cike da shagwaba tace “ni dai kataimakeni “ya cusa kanshi a qirjinta yana cewa “zanyi komai dan bana son ganinki kina kuka.” ahankali ta dinga jin yana sarrafata cikin mafarki ita dai bata san ya’akayi taje d’akinta ba sai farkawa tayi da misalin qarfe hudu na dare da wasu mintuna ta ganta kwance a d’aki .”




ahankali ta mike zaune bakinta dauke da addaur tashi a bacci tana sauke numfashi ta godewa da mafarki tayi ba gaske bane komawa tayi ta kwanta lamo tana tariyo abubuwan da suka faru acikin mafarkinta tana kwance tana juyi har aka fara kiran sallah ta tashi ta matso kad’an ta zuro qafafuwanta duka qasa sannan gangar jikinta ya biyo baya kai tsaye bayi ta shiga tai wanka ta d’auro alwala ta fito ta sanya doguwar riga da hijab ta qarasa inda daddamar sallarta take shimfide kamar koda yaushe ta soma gabatar da raka’atani fajiri byn ta idar ta mike tai sallah bayan ta idar sallah bata mike ba ta soma azkar sannan ta janyo alqurani ta soma karatu cikin surataul ahraf har zuwa karfe shida daidai sannna ta rufe alqurni ta samu waje ta kwanta a kasa kasance war har lokacin akwai bacci acikin idanunta,nan take wani bacci yayi awon gaba daita kusan yadda baccin safe yake bare ya hade mata da gajiyar zuwa aiki da tarin damuwa bata dade tana bacci ba ta tashi tana miqa tana duba lokaci “takwas da wasu mintuna da sauri ta soma shirin zuwa office bata wani jima ba ta fito kai tsaye falo ta wuce inda ta iske umma zaune .”




Ahankali ta zauna akan hannun kujerar da umma take zaune tana cewa “umma ina kwana !”ta gaishe da umma tana daukar littafinta na jiya .umma ta amsa mata muryarta cikin wani irin yanayi maryama ta dubeta a tsanake qirjinta na bugawa so take ta gano ko akwai wani abu dan haka jikina a matukar sanyaye tace “umma ya naji muryarki tayi wani irin ?”me murya ta tayi maryama ?ta tambayeta tana dubanta “ai umma ji nayi muryarki tayi wani irin ba kamar yadda na saba jinta ba sannan yanayinki kmr kinyi kuka .”ta qarasa maganar tana jin wani irin mummunar fad’uwar gaba.murmushi umma ta sakar mata tana cewa “ke fa matslarki kenan saurin rud’ewa babu abinda Ke damuna kece ma zance yanayinki kmr kinyi kuka bama kamar bane kinyi kuka dan ga sheida nan a little danunki bata da ja domin ita kanta tasan tabbas a irin kukan datai dole za’a gane ba “tabbas nayi kuka umma amman acikin mafarki .”umma bata mutsa mata ba amman tasan ba’a mafarki bane azahiri tayi kuka amamn tunda ta zabi ta fad’a haka shikenan “na had’a mana tea mai dadi bari naje na kawo miki jirani ina zuwa .”umma ta mike ta nufi kitchen inda maryama tabi bayanta da kallo mai tattare da tsantsar qauna tana zaune umma ta fito ta dawo gabanta ta tsaya tana mika mata cup din tea “ga naki tea tasa hannunta ta kar’ba cike da girmamawa tace “na gode sosai ummata umma ta kai nata cup din baki ta kur’ba tana cewa kai tea din nan yayi dadi sosai hakan yasa maryama ta kai nata cup din bakinta ta soma kur’ba tana lumshe ido “gsky ne umma yayi dadi kuma ya sha bambam da sauran tea “kuma kinga bashi da wata wahalar yi ba idan zaki yi ki samu kanufari,lipton tafarnuwa mint leave da gayen nahna’a shikenan ina son ki koya dan bamu san wani irin mutun zaki aura ba, idan allah yasa mai yawon sha tea ne shikenan sai ki dinga masa irinsa” kai umma duk maganarki bata wuce ta aure nifa ynzu ba aure bane agabana kamar yadda na sha fad’a miki burina a yanzu mu bar gidan nan “nasani amman kibi komai ahankali” umma ta fad’a tana dubanta a natse kafin ahankali ta cigaba da magana ina son ki bani aron hankalinki jin haka yasa zuciyar maryama ta fara tsinkewa ina son nayi miki magana akan wani abu zuciyarta ce ta cigaba da tsinkewa yayinda ilahirin jikinta ya d’auki rawa babu shiri ta ajiye cup din hannunta ta tsura mata ido “muryarta a sanyaye tace “ina sauraronki umma “ina son Kiyi aure maryama bazan so ki cigaba da rayuwa haka ba wani irin ajiyar zuciya ta sauke mai qarfin saka makon ba abinda tayi tunanin bane “ muddin ban baki shawa rar kiyi aure ba lallai ban cika mai adalci ba ,aure yana daraja kuma zai kareki daga dukkanin wata matseefa “in sha allahu zanyi umma amman ba yznu ba dan ahalin yanzu babu wanda yace yana son maryamarki ko da yake kin dai san maryamarki da bakinjini .”ta fad’a tana dan murmushi “.




“ni maryamata bata da wani bakinjini kisa niyya sai Allah ya taimakemu ,shikenan umma naji bari na wuce aiki lokaci na tafiya .”har tayi taku biyu ta kira sunanta “maryama !ta tsaya cak batare data juyo ba ki tsaya bari naje na kawo miki custard lokacin data juya alokacin maryama ta juyo tana duba agogon hannunta, lokaci ya soma tafiya umma bata wani jima ba ta fito hannuta rike da wasu flaks guda biyu kanana
ta miko mata daya maryama ta kar’ba tana murmushin jin dadi “kai gaksy umma kina ji dani shiyasa nake sonki fiyye da komai kamra Kinsan kwana biyu nayi missing custard dinki ai shiyasa nayi miki dan nasan kina so ga naki ,wannan d’aya kuma na mai gidanki “what !”
Maryama ta furta da karfi jikinta har rawa yake tsabar rudewa “umma wa kenan kike magana akai wa custard ?wa kuwa bayan mai gidanki mr ata shi zaki kaiwa nasan bai ta’ba shan custard irinsa ba “what !” wai mr..”mr ata kike nufi ?ta fad’a murayarta na rawa me zai yi da wani custard umma?” ke kike tunanin mai zai yi dashi ke dai ki kai masa ki gani “murmushi maryama tayi tana cewa “amman dai umma da wasa kike ko ?” idan ba haka ba ta yaya zan kai wa mr ata custard?”




“to ke mai yasa kike mamaki ke dai nace ki kai masa kuma kice inji mamanki “no no umma karki damu kanki wallahi baki san waye wannna mutumin ba shiyasa ,mutumin da bashi da bambamci da hawainiya mutunin da zuciyarsa bata da bambamci data dutse kai zuciyarsa tafi ta dutse karfi mutumin da babu abinda yasani sai wulakanci da tozarci shine mutumin da kike tuannin na kaiwa custard?” ina bazan iya ba umma ba,” tsaya maryama ina son ki fahimceni kema na rasa gane kanki wata rana kice mutumin kirki ne wata rana ki canza magana ,ni wanne zan dauka aciki maryama tai shiru kawai cikin tsnanin damuwa dan tasa aiki ja umma take son bata ,duk abinda kike fad’a akansa ni dai abu daya nasani zuciyata tana son shi a haka duk rashin kirkinsa shine yayi nasarar dawo miki da farinciki da walwalarki dan haka ki amsa ki masa idan na isa dake idan kuma ban isa dake ba nasani.” lumshe idanu maryama tayi “.
“na fahimceki umma amman walalhi mutum ne shi mai wuyar shaani”nasani !wallahi umma da wahala ya karba ki fahimceni ba wai ina jayayya dake bane halinsa nasani “nace miki zai amsa ki kar’ba to ni yanzu idan na kai masa mai zance masa ?”
tai maganar tana dafe goshinta umma tace “ bazanki bin umarnina bane ?”babu shiri maryama tasa hannu ta kar’ba “yauwa sai kin dawo Allah ya tsareki “ ahankali ta juya ta bar bangaren da sauri inda ta bar umma tsaye tana kallonta “maryama kenan bazaki gane abinda wannna mutuminn yake nufi dake ba sai nan gaba kin kasa fahimtar mai yasa ya damu dake, me yasa yake yawon fushi akanki ,mai yasa ya damu matukar sai kinyi aiki akarkashinsa ,ni dai nayi imani akwai wani abu acikin ransa akanki, koma dai menene Allah kasa mu dace Allah yayi miki kyakkywan zabi mafi alkairi arayuwarki da addininki.”






Ahankali maryama ta shigo ma’aikatan tana gyara zaman jakar dake kafad’anta tare da rike qaramin jakar da umma ta sako mata flaks ciki duk ilahirin jikinta yayi wani iri yayinda zuciyarta ke cike da tsannain fargaba “maryama ki sanyawa jikinki jarumta sannan ki karkafa zuciyarki, yanayin yadda kike damun kanki akan abinda bai kai ya kawo ba, yanayin ne damuwa zata miki yawa.”
ki samu natsuwa ba dole sai kin bashi sakon umma ba zaki iya bawa wani ya shanye a madadinsa tana tafiya tana zance zuci a natse ta shiga office dinsu ta gaishe da mutanen data iske ,sai dai babu wanda ya amasa mata bare ya kalli inda take, sai yusura kad’ai ta amsa mata sa’banin jiya tana kallonta cike da tsananin tausayi da mamakinta dan har lokacin bata daina mamakin hotunan jiya da’aka tura masu ba .”




Maryama tana tsaye madam some ta shigo ta wuce ta gabanta tana kallonta tana zance zuci tare da nazarin maryma har a wannan lokacin zuciyarta bata bar mamakin mami da dalilin da yasa ta tambayeta tsakanin maryama da mr ata ba ,da kuma dalilin mr ata na cewa lallai ta tabbatar maryama ta shiga motarta kuma lallai ta kaita har unguwar su “amsarki itace mr ata yana tsananin son maryama haka ma mahaifiyarsa ta fahimci irin son da yake mata shi yasa ta kiraki jiya domin ta tabbatar
Numfashi ta sauke adaidai lokacin da maryama tace “good morning ma !” madam some ta amsa mata ,inda maryama ta samu waje ta zauna ta ciro littafinta tana dubawa sai dai bata fahimtar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login