Showing 153001 words to 156000 words out of 178062 words

Chapter 52 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

zugi akan rashin d’aga kirana damuwarki tana maseefar d’aga min hankali ,a yanzu haka ina jin kamar ana zarar raina ne idan kinga sakona ki kirani ina son muyi magana dake ina son nasan halin da kike ciki_




shiru tayi kawai tana sake karanta sakon shi”zuciyata na min zugi akan rashin d’aga kirana damuwarki tana maseefar d’aga min hankali ,a yanzu haka ina jin kamar ana zarar raina ne idan kinga sakona ki kirani ina son muyi magana dake ina son nasan halin da kike ciki ta karanta sakon yafi sau biyar duk da ba sako ne na kwantar da hankali ba amman ta rasa dalilin da yasa taji kalmomin sun tsaya mata arai .numfashi ta sauke sannan ta tashi ta shige bayi ta dauro alwala ta fito ta fara gabatar da nafilflii .”




washegari ma kiransa ne ya soma shigowa wayarta amman taki dagawa sai ma kashe wayar tayi gabad’aya ta fita wajen umma ta cigaba da tsabgogin gabanta sai wajen tara na dare ta kunna wayar tana kunna wayar sakonsa ne ya shigo “maryama zan miki rashin mutunci idan baki kirani ba, ko idan na sake kiranki baki daga ba ko kuma naji wayarki a kashe .”shiru tai tana karanta sakonsa tana mamakinsa rashin mutunci kuma idan dai rashin mutuncika ne wanene sabon abu a wajena kayi duk abinda zakayi tunda ba qarqashinka nake ba mai zai dameni ta fad’a a fili tana yatsuna fuska .”
Ko minti biyar batayi da shigowa ba kiransa ya shigo tsaye tayi tana kallon sunansa qirjinta na wani Irin luguden bugu da qarfi kira uku yayi mata ajere bata daga ba haushi yasa yayi wurgi da wayar yana jan tsaki tare da cewa bazai sake kiranta ba sai dai baya jin zuciyarsa zata iya hakura daita jiki a sanyaye kamar wanda Kwai ya fashe aciki ya samu waje ya zauna yana huci shi kadai yasan yadda yake ji a sansar ajikinsa .”




Yau kwana biyu mr ata bai kira maryama ba wanda yayi daidai da kwanaki bakwai kenan bai sakata acikin ko danunshi sai dai yayi balain jin jiki adaddafe mr ata yayi kwanaki nan batare daya sanya maryamarsa a ido ba, jinsa yake kamar wanda yayi shekara ba lafiya har zubewa yayi ya qara zamowa silent kullum tunaninta ne ya zame masa aikinyi ,kullum yaje office idanunshi na kan kofar shigowa ko zai ganta daga sama still shiru dan haka ya tura some gidansu domin ta dubo masa ita babu bata lokaci taje sai dai labarin data zo masa dashi yayi mugun girgiza shi dan haka ya kudurce aransa gobe Jumma’a zai je gidansu maryama ,ya kira m.b yace yazo su had’u gobe yayi masa rakiya zuwa gidansu kasancewar amar baya qasar tun kafin mr ata ya dasa aya yace “kar dai har yanzu baka fad’a ma yarinyar nan kana sonta ba ?
ya gyada masa Kmr yana gabansa “wallahi har yanzu mb yanxu ma wata matsala ce ta tso iyayenta sun hanata zuwa aiki ,to kai mai yasa baka fad’a mata ba ayita ta qare idan aure zai yuwu ayi idan bazai yuwu ba ka saukakawa kanka “bare ma zai yuwu ai maryama bata da wani miji sai ni haka nima bani da wata mata sai ita kasan komai sai lokaci yayi may be akwai abinda Allah ya boye yasa har yanzu ban fad’a ba amman fa ina shan wahala sosai ya fad’a yana dafe goshinsa sun jima suna hira kafin daga bisani sukai sallama.”




******




Wayewar garin ranar jumaa mr ata bai fito daga samansa ba da murna yayi shirinsa kamar wanda akayi masa albishiri da gidan aljanna shigar farin kaya yayi na wani had’ad’den danyen yadi mai azabar kyau wanda tsayawa fad’ar kudinsa ma bata lokaci ne, yasa takalmi da hula baki haka zalika agogon rolex din dake d’aure da hannusa baki ne , kana kallonsa zaka d’auka zashi d’aurin aurensa ne ahankali cike da natsuwa yake qarasa saukowa yana taku kamar baya son taka kasa hannusa d’aya soke acikin aljihunsa sai zuba qamshi yake tunda ya sauko idanun mami yake kanshi babu abinda take sai kallonsa sai kace wanda zashi biki yayi mata kyau sosai cike da farinciki ta soma mgn “kai adamcy nah irin wannan kwaliya ai sai ka firgita yammata “ta fad’a cike da tsigar zolaya d’an murmushi yayi wanda bai wuce iya labbansa ba “ina zuwa ne haka ?kai tsaye yace mata “zanje gidansu maryama ne.”“gidansu maryama !ta furta ahankali ya gyad’a mata kai yana ciro wayarsa ya soma neman layin mb “wai kana ina ne ko d’an na bukaci kamin rakiya shine zaka ‘bata min lokaci daga can bangaren mb cewa yayi “malam karka dameni dan sai na fasa maka rakiya wajen budurwarka ai kafi kowa ‘batawa mutane lokacin ko dan wajen maryama za’aje ka wani shirya da wuri .?”




“minti goma kawai na ba”dan Allah karka dameni idan ma ka dame ni sai naje massalaci na dawo na had’a da ziyara gidan yanuwa da abokan arziki daga nan sai nazo” inji cewar mb “shikenan karka zo ka tafi duk inda zakaje nonsense”mr ata ya fad’a yana cika yana batsewa shi a dole mb ya bata masa rai sosai ransa a ‘baci ya kalli mami wacce Ke zaune tana kallon sarautar allah “sai na dawo sweetheart “yana gamar fadar haka ya juya itama ta juyo tana kallon kyakkywan d’an nata dake faman zuba qamshi kamar shagon turare killama wanka yayi da ruwan turare wayasani




Cigaba da kallonsa tayi yana taku yana gyara zaman hullarsa har sai data daina hangosa sannan ta lumshe idanunta .mr ata yana gama fitowa idanunshi da m.b suka soma cin karo tsaye kamar had’in baki shima farin yadi ne sanye ajikinsa “ya sakar masa murmushin yana cewa “yi hakuri abokina sarkin zuciya ai kasan bazanki rakaka gurin gimbiya kuma sarauniyar mata ba ,muje ko !”ya fad’a yana mika masa hannu bayan sun gaisa mb yace” muje masaalaci muyi sallah tukun sai muje dan lokaci sallah ya kusa tsaki mr ata yaja yace “ai kai wallahi baka da mutunci sai ka gama batawa mutun rai ka dawo kana bashi hakuri “naji dai ai gara ni tunda zan iya bada hakuri muje amamn fa abokina kayi kyau sosai wannan sai kasa maryama ta furta kalmar só batere data sani ba .”


wani irin kallon iskan yayi masa “allah baqaramin kyau kayi ba wallahi duk inda muka bi dole sai an kalleka saboda uban wanka turaren da kayi ko mace sai haka nifa ina ganin kamar har da hoda ka shafa ko ?shi dai mr ata bai tanka masa ba har suka isa massalaci yana koda kyawun da adamcyn mami yayi wanda shi bai ce masa komai ba qarshe dai yayi shiru yana cigaba da sauraronsa .”




Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




45




Daga masallaci basu tsaya koina ba sai akan titin unguwar su maryama, bayan sun samu guri sunyi parking suka fito ahankali inda m.b ya tsaya shiru yana karewa yanayin tsarin unguwar kallo ,”titin unguwar tasu babu laifi sai dai cike take da jama’a ‘yan cirani da ‘yan sikiraf “mr ata tsab ya fahimci inda hankalin m.b ya dosa dan haka tun kafin yace masa wani abu ya tsosa keyarsa yace “kaga malam ban son gulma da iskanci muje!”.wallahi wannan yarinyar bancin a mafarki ka fara ganinta da nace asiri ta maka, dan irin wannan unguwar sai dai aikin asiri ne kawai zai kawo mutun .”
a natse mr ata ya wucesa ya d’auki hanyar dogon lungun da zai shigar da mutun zuwa kofar gidansu maryama.ganin haka yasa m.b ya biyosa da d’an sauri suka jera suna tafiya acikin lungun mamakin m.b ya sake qaruwa dan duk yadda ata ya fad’a masa yanayin unguwarsu geto area ne bai d’auka haka yake ba dan har gara kan titi akan wannan lungun da suka shigo. m.b dai ya kasa hakuri yace “lallai wani abu sai aikin syya idan ba soyayya ba mai zai kawo mutun irin wanan ungu war ?”ko da yake wannan shine abinda yafi dacewa ga attajirai irinku masu jin kai soyayyarku ta qare akan yaran talakawa wanda ba kome bane.”madadin mr ata yaji zafin maganarsa sai ma yace“ashe dai kana da raunin imani kasani nasani babu wani abu da zai gagari Allah kawai zai fi kyau kace qaddarar aurena tana cikin wannan unguwar kuma ban isa na gujewa qaddarata ba ko tazo ta sameni a inda nake ko kuma ni na biyota inda take kamar dai yadda ya faru sai dai in sha Allahu da zarar na d’auke maryama daga unguwar nan daga ni har ita mun bar shigowa cikinsa”mr ata yana gama fad’ar haka ya ciro wayarsa ya soma neman layin maryama domin ya sanar mata isowarsa da kuma katse duk wata magan da zata fito daga bakin m.b sai dai akayi rashin sa’a layin nata a kashe yake .”








Har suka qaraso kofar gidan kiran bai shiga kira biyar yayi mata anace masa layin switch off yayi shiru yana tunani yayinda nan take moon dinsa ya sauya zuwa damuwa.”mb ya kallesa yace “ya’akayi ne mutumina naji kayi shiru ko akwai matsala ne?layinta ne wai akashe “okay sake kira may be matsalar network ne kasan yanayin network din yanzu bai fiyye kyau ba bare a irin wad’an nan unguwannin,sake kira idan bai shiga ba sai mu samu yaro mu tura cikin gidansu take yabi shawarar m.b ya sake kira layin cikin sa’a layin ya soma ringing sai dai bata d’aga ba sai da yayi kira biyu a karo na uku ne ta d’aga tare da yin shiru taki cewa komai illa numfashin data dinga sauke masa acikin kunnensa wanda ya haddasa masa shiga cikin wani yanayi mai tsarkakkiya da wuyar musaltuwa wani iri naunayen ajiyar zuciya mr ata ya sauke da qarfi shima .”
kamar yadda maryama tayi shiru haka shima yayi shiru har kusan mintuna sha takwas babu wanda ya cewa d’anuwansa uffan.” maryama ta sauke wayar daga kunnenta ta duba ko ya sauka akan layin ne sai dai gani tayi har lokacin yana kan layi magana ne dai bazai ba ta kalli inda umma ke zaune a kusa daita wacce ta kasa kunne domin sauraron abinda zata ce .”






da kyar maryama ta sanyawa jikinta jarumta tace “ina wuni sir….” “fito gani a kofar gidanku!” ya fad’a atakaice “what ?!ta furta a d’an firgice tana sake kallon umma kafin ahankali ta daidaita natsuwarta “ko ba zaki fito bane ? kwantar da murya tayi sosai tace “sannu da zuwa gani nan fitowa “.ta fad’a tana sauke numfashi tare da zubawa umma ido ,gabadaya duk sai yanayinta ya canza daga d’an farinciki data fara samu zuwa bakinciki ,dan a yanzu bata qaunar duk wani abinda zai zame mata damuwa arayuwar ta .“kallon tsanake umma tayi mata kafin ahankali ta motsa bakinta tace “bako kikayi ne ?cike da damuwa ta gyd’a mata Kai tare da cewa “mr ata ne yazo” mr ata sai yanzu zai nemeki ?” umma ta furta hakan
dan batayi tsamanin zai d’auki lokaci har haka batare daya kawo kansa ba dan har ta fara cire ranta akan son maryama yake .maryama tayi mamakin jin furucin umma “to yanzu mai km ya kawosa ?nima bansani ba amman may be ayyukan daya bani ne yazo kar’ba ganin kwana biyu banje aiki ba haka nan ta tsinci kanta da shara rawa umma karya “inda umma tace “ai shikenan sai kije ki samesa kiji abinda ya kawosa bata mike tsaye alokacin ba sai data d’auki kusan minti biyar zaune har sai da umma tace” ki tashi ki shirya kije mana kin bar mutun tsaye sannan ta mike da kyar ta shiga d,akinta .”






A can kofar gidan kuwa tun daga nesa baba gali ya hango tsayuwar mutane biyu a kofar gidansu cikin shiga ta alfarma tun bai qaraso ba yaji gabansa yana wani irin bugun tara tara ahankali ahankali ya dinga taku har ya kusan qarasowa inda suke tsaye , nan idanunshi ya tabbatar masa da ko waye tsaye, a fili ya sauke ajiyar zuciya had’e da kare masu kallon tsab cike da mamakin ganinsa yace “duk lalata da kayi a wajen aiki bai maka ba har sai ka biyota gida ai kuwa bazata sa’bu ba bindiga acikin ruwa nan take baba gali ya soma tunanin irin qalar wulaqancin da masu sai dai yana qarasowa gabansu yanayin yadda yaga fuskar gogan naku babu wasa bare alamun d’aukar nonsense yasa baba gali ya had’e abinda ke cikin ransa, ya ‘bige da yar gyaran murya kana yace “ashe kaina tsaye ?”m.b ya kalli baba gali sannan ya kalli mr ata sannan ya gaishesa .”baba gali ya amsa yana washe masa baki yace “sannuku da zuwa .”
”yauwa !”inji cewar mb shi kam mr ata sai da ya d’auki lokaci kafin yace masa “ina yini!” kuma daga nan bai qara ba sai ma sake had’e fuskarsa da yayi yana kallon wani banngare dabam “ku shigo daga ciki mana “ba wajenka muka zo ba ata ya fad’a yana fesar da iska mai zaki daga bakinsa jiki baba gali a sanyaye ya nufi cikin gida yana wai wayensu sauran ka d’an ya tuntsura da hannu mb ya nuna baba yana cewa ”halan waye wannan mutumin?”ban san shi ba “mr ata ya fad’a atakaice shiru m.b yayi kafin ahankali ya cigaba da magana “baka san shi ba amman kuma shi da alamun yasanka “kai ma kasan sanina ba abu ne mai wahala ba acikin kasar nan mb yaja bakinsa yayi shiru .”






Maryama ta d’aura after dress akan kayan jikinta tayi rolling mayafin after dress din ta dauki turarenta mai sanyin qamshi ta feshe ilahirin jikinta sosai tayi kyau ta fito zuwa parlour qamshin turarenta yasa umma ta waigo inda take tsaye tana qoqarin saka takalmi umma tai shiru kawai tana kallonta ,sai kace mai zuwa zance ko wani biki amman dai tayi kyau sosai Allah yasa mr ata ya furta mana yana sonta dan hakan nan take ji mutumin son maryamarta yake ,maryama ta qaraso ahankali ta tsaya kusa da umma tana cewa “sai na dawo umma” adawo lafiya amman kinyi kyau sosai maryama ta d’an murmusa tana cewa” na gode umma nah sannan tasa kai ta fice .”
ahankali take taku kamar bata son taka qasa yayinda zuciyarta ke wani irin tsinkewa tana tunanin abinda ya kawosa gidansu, har ta fito zuwa kofar gidansu ta tsaya inda idanunta suka sauka akan mr ata nata da kuma wani da bata san ko waye ba .”wani abu taji yana shigarta wanda take yawon jinsa ailahirin jikinta a duk sanda zata d’aura kwayar idanunta akanshi sai dai ta rasa gane komenene wannan abun dake shiga jikinta yana yawo acikin jini da tsokar.”
sosai taga yayi mata kyau acikin shigar da yayi looking extra ordinary mr ata ba dai kyau ba his nose is so pointed har baki ga gashin fuskarshi baki sitik kamar an ratsa golden brown aciki sai shining yake yi kamar ya zuba oil gashin yana cikin abinda yake mugun qara masa kyau ,”masha Allah ta furta ahankali.”






Numfashi da ajiyar zuciya ta sauke atare sannan a natse ta cigaba d’aga qafafunta.” tun daga nesa mr ata ya d’auki kallonta har ta qaraso ta tsaya a gabansu tana masu sannu da zuwa “sannuku da zuwa”! mb ne kawai ya amsa mata cike da kulawa shi kuwa mr ata yayi gum da bakinsa ya cigaba da kallonta wanda yasa tayi kasa da kanta ta kamo yatsun hannunta ta tsarke cikin juna tana wasa dasu.gabad’aya sai ta jita a takure sakamakon tsumammun danunshi dake yawo a sansar jikinta “bayan kamar minti biyar ta d’ago nan take kwayar idanusu ya tsarke cikin juna ,wani irin yanayi mai bugar da zuciya ya farmakesu atare ,da sauri maryama ta janye idanunta daga cikin nashi tana gaishesa “ina yini !?”har sai da dimple dinta ya lotsa kmr an saka nail da hammer anyi nailing cheeks dinsu norma normal ko bata tayi magana ba ana ganin alamun lotsawarsu still mr ata bai amsa mata ba ya cigaba da kallonta yana hukuntata da kwayar idanunshi masu firgitarwa tare da qara d’aure fuska tmkr wani zaki .”
mb yayi kusa dashi sosai tare da yin kasa da muryarshi yace “kayi mata magana mana ko za’a bamu izinin shiga ciki “still shiru yayi yaki cewa komai har sai da maryama ta sake d’ago idanunta, sosai ta tsorata da ganin yanayin yadda ya d’aure fuska yake kallonta,muryata na rawa tace” mu shiga daga ciki”still shiru yayi yaki motsawa har sai da ta sake yin magana “kayi hakuri ka shigo baza kuji dadin tsayuwa anan ba.” tana gama fad’ar haka ta juya .






Wani irin naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da qarfi “kaga malam ka saki fuska mu da muka zo zance da ban hakuri zaka wani had’e wannan fuska tare da takure yarinyar mutane wannan fuskar zakin taka ai sai ka firgitata .” iska ya fesar mai zafi daga bakinsa sannan ya soma taku ya biyo bayanta shima mb ya biyosu sosai mr ata yake kare mata kallo yana furta masha Allah yarinyar ba dai diri ba she has the best figure kyawunta sirri ne ya godewa Allah da zai mallaketa ,kusan atare suka shiga gidan a haraban gidan suka tsaya mr ata yaki yin magana haka zalika maryama da mb babu wanda yace komai gabdaya marayam ta rasa meke mata dadi “wanna shirun nasa yasa zuciyarta Ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login