Showing 174001 words to 177000 words out of 178062 words

Chapter 59 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

iri ajikinsa bare ita da zuciyarta take jin wani abu akanshi .”har ga Allah da tasan zai zo ya samesu a wajen data shiga cikin motar alhj mansoor dan kwata kwata bataji dadin ganinsa ba koda bai furta mata kalmar so ba ai ya furta mata kalmar aure kenan gansu yanzu haka ya zama cin fuska ne .”






bayan kamar second goma alhj mansoor ya kira sunanta a tsanake yana jin wani irin mummunar tsoro a zuciyarsa “my princess lafiya ko akwai damuwa ne naga duk yanayinki ya canza daga farin ciki zuwa damuwa ?”ba tace masa komai illa ta d’ago kwayar idanunta ahankali still dai tsumammun idanun mr ata suna kanta ya sake tsareta da idanunshi masu sata shiga taitayin ta ,kuma duk sanda zai d’aura mata su,wani irin sinadari ne ke fitowa daga cikinsu suna shiga cikin kwayar idanunta tare caccakar duk wani sashi na jikinta most especially idan suna cikin damuwa dole ne ka dabarbarce sai kayi da gaske ka samu ka dawo da natsuwarka,”






so take ta maida kanta kasa amman ta kasa dan wani irin mummunar fad’uwa gaba take ji ahankali ta lumshe idanunta dan kallon da yake mata ya saukar mata da jin kasala hakan tasa ta sake tsura masa ido tana tunanin mafuta dan bata san yadda zata bullo masa ba shi kuma banda kallonta babu abinda yake “my princess !”ta jiyo sautin muryar alhji mansoor ya sake kiran sunanta a karo na biyu ,still dai shiru tayi masa tana cigaba da kallon mr ata up and down wanda zuwa wannan lokacin ya kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa yana shafawa ahankali dan baa maganar irin zugi da kuncin data shiga alokacin “Ina ganin ya kamata ki shiga mota na saukeki a gida nima na qarasa gida ko.”ahankali maryama ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tana duba agogon dake d’aure da tsintsiyar hannunta tare da gyad’a masa kai alamun taji duk dai lokacin tashi bai yi ba amman itama a ganinta gara ta wuce gida zai fiyye mata kwanciyar hankali muryarta a sanyaye tace “habibi bani minti biyar bari naje na d’auko jakata na dawo “murmushi ya sakar mata tare da cewa “an baki ranki shi dade.”






Mr ata yana kallonta ta soma taku batare data kalli inda yake tsaye ba dan yi tayi ma tamkar bata san da tsayuwarsa a wajen ba tana daf da shiga lifter wasu abokan aikinta suka qaraso suka gaishesa cike da girmamawa sannan suka qarasa gareta suna mata magana atare suka shiga lift gabad’aya hankalin mr ata baya kansu yana kan maryama ne dan har lokacin ya kasa daina mamakin ta.” yana nan tsaye ta dawo ta wucesa tana latsa wayarta still tayi tamkar bata san da tsayuwarsa ba tun kafin ta qaraso wajen motar alhj mansoor ya bud’e mata gidan gaba yana sakar mata murmushi, ahankali ta d’an rage tafiyarta tana qoqarin shiga motar taji an fixge wayar hannunta ta baya a firgice ta juyo,nan take kwayar idanunta ya sauka akan mr ata yana huci tamkar wanda yayi gudun tsare ahankali ta rausayar da kwayar idanunta cikin nashi wanda hakan ya haddasawa zuciyarsa tsalle da shiga rud’ani “lafiya sir !” ya zaka amshe min wayata !?
”tayi masa tambayar ajere tana hura masa hanci wani mummunar kallo ya d’auketa dashi mai had’e da harara “lallai ma yarinyar nan ta mugun rainashi sai da tayi qasa da muryarta sannan tace “dan Allah sir ka bani wayata gida zani !”tayi maganar cikin salon jan hankali.”




wani bakinciki ne ya tokare masa kahon zuciya wanda yasa ya soma ganin dishi dishi yayinda zuciyarsa ta soma tafasa yana jin duk laifinsa ne daya biyewa girman kan zuciyarsa da bata mahimmanci akan komai gbdy qasa magana mr ata yayi sakamakon ‘bacin ran daya tsinci kanshi ciki dan shi a ganinsa ta fahimcesa ta kuma tasan yana sonta so kawai take taga qarshensa so take sai ya furta mata mouth to mouth sannan zata fahimcesa .”ganin bashi da niyyar bata wayarta yasa ta juya a natse ta kalli alhj mansoor dake tsaye yana dubansu zuciyarsa cike da jin haushi da tsananin kishi tace “habibi shiga mota muje “what !?mr ata ya furta a tsawace alhj mansoor dake qoqarin yin magana cikin farinciki wanke masa zuciya da tai bakinsa ya rufe jin mr ata yana cewa “karka sake kayi wata magana anan salin alin ka shigar motarka kai kad’ai ka wuce ka kama gabanka ,and you ki koma ciki”. ya juya kanta kamar wani nmjin zaki duk wani matsayinsa da miskilancinsa da jin kanshi ya nema ya rasa saboda tsananin kishin dake dawainiya dashi .”






da mabambamnta idanu maryama da alhj mansoor suka bishi dashi .” alhj mansoor ya tsaida hankalinsa da natsuwarsa sosai akan maryama yana lashe lip’s dinsa wanda ya zame masa miji kafin ahankali cikin tsananin fushi yace mata “waye shi !?”tace please kayi hakuri me gidana ne “mai gidanki !”?ya sake furta wa idanunshi na kan mr ata wanda cikin Kankani lokaci ya fahimcesa baya raba dayan biyu kishi ne ke dawainiya dashi abun tambaya anan shima mai gidanta na sonta yake kenan ?”
“Mintu biyu!” minti biyu kawai na baki maryama ki fad’a masa kin fasa aurensa“ idan ba haka ba zan shayar dake mamaki.” nan take rauni ya lullubeta ganin yadda yake shirin tujarata agaban alhj mansoor mutumin da yake shirin zama miji gareta “wai mai yasa mr ata yake son wulaqanta ta a bayanan nasi ?




katse mata tunanita yayi ta hanyar sakin wata tsawar yana mai cewa “wai ba dake nake magana ba kin tsaya kina kallon wannan banzar mutumin “maza maza ki fad’a masa kin fasa aurensa kuma a yanzu .”turo masa qaramin bakinta tayi tana cewa “haba yallabai wai me yasa ..”stop !” yayi saurin katseta ta hanyar fad’ar haka “I don’t want to hear anything from you maryama just tell him and let him leave this company right now “
“Wai a yanzu kake nufi na fad’a masa na fasa aurensa “?matsota yayi yana kallonta yana Jin yadda zuciyarsa ke kutememiyar bugawa fiyye da Kaida “tambayata ma kika tsaya yi kenan bazakiyi abinda na sakaki ba ?”ya tambayeta a hassale “naji shikenan zan dai fad’a masa ya wuce shima tare zamu wuce tunda ma’akatan takace amman gasky bazan iya fasa aurensa ba tunda Ina son shi washe baki alhj mansoor yayi yana Shafa kanshi,shi kam ata tsoro da matsanancin firgici ne ya bayyana a fuskarsa yyinda zuciyarsa ta dinga bugu numfashinsa ya soma baraza nar daukewa cikin zafin zuciya yace “malam ka d’auke wannan akwalar motartaka ka bar nan yanzu tun kafin nasa ayi maka abinda zai fi komai muni gareka.”ya qarasa mgnr ahankali tmkr ba acikin fushi yake ba .”






alhj mansoor ya kalli maryama ya juya ya kalli mr ata yana jiran taji mai uwar gayya zata ce maryama kam kallonsa kawai take batai mamaki ba dan tasan zai iya aikata fiyye da haka mr ata ya sake tsare gira “muje ciki !”cikin sanyi jiki tace “please sir bana son irin abinda kake min domin kuwa barazana ne ga rayuwata idan ma wasa kake ka daina dan gsky sai da kayi hakuri dan ban zan koma ciki ba zan bi zabina kuma mijin da zan aura habibi muje ko .”kamar jira alhj mansoor yake ya sauke ajiyar zuciya ya zagaya ya bud’e murfin mota ya shiga ya zauna mr ata kuwa ya sake d’aure fuska ya fara mgna cikin fad’a da jin haushi “look at me maryama kinga alamun wasa atattare dani ?”babu wasa acikin maganata yaushe kika hadu dashi da har kika amincewa aurensa “?ba gara ni ki aureni ba at least kin sanni kinsan halina, maryama ta girgiza masa Kai cike da tsoro sai dai bata bari tsoron yayi tasiri ba ta shige motar alhj mansoor ta zauna ta rufe murfin kofar da qarfi yayinda shigarta keda wuya alhaji mansoor yaja motar ya fice daga ma’akatan inda mr ata yabi bayan motar da kallo mai cike da tashin hankali.”






Ahankali motar alhj mansoor take guda akan titi sai dai zuciyar maryama bata cikin natsuwa gabad’aya ta rasa meke damunta “tabbass tasan ta baro wani bangare na rayuwata a AGC sannan tasan tsananin kishinta mr ata yake amman mai yasa bazai fito da abinda ke cikin zuciyarsa ba?” shin darajarta ce bata kai haka ba ko kuwa kasancewarta daga tsatson talakawa ne yasa haka ?”wannna abu yasa zuciyarta ke tsananin bugawa da matsanancin qarfin gaske “my princess da alamun shima wannna mai gidan naki sonki yake yi “kunnuwanta suka jiyo mata maganar alhji mansoor kai tsaye tace “ba so bane haka yanayinsa yake ,shi mutun ne mai tsananin son wulaqanta duk wanda yake qarqashinsa “no my princess wannan mutumin akwai so atattare dashi sai dai idan bai furta miki ba amman tabbas akwai so idan ba haka ba ,ba rami me ya kawo zance rami “.yayi mgnr yana qoqarin riko hannunta wanda taji tmkr garwashin wuta yake barazanar konata da sauri ta zame hannunta tana cewa “ka yarda dani habibi babu wani abu makamancin haka atare dashi ,shi dai haka rayuwarsa take bama akaina ba akan kowa ne.”






Gyad’a kai yayi kafin ya cigaba da magana”na fara wani tunanin !ta waigo a natse ta kallesa sannan tace wani tunani kenan ?“bana Jin zaki cigaba da aiki a qarqashin wannan mutumin zan nemar miki aiki a wani guri dan kwata kwata zuciyata ta kasa samun natsuwa da mutumin kar yaje yayi min illa, numfashi ta sauke tace “shikenan idan har hakan zai samar maka da natsuwa da kwanciyar hankali fine anything for you habibi khairan in sha allahu” na gode sosai shiyasa nake qara sonki akwaiki da biyayya a natse yake janta har suka qaraso ikeja sun kusan jara mall yace”my princess let me order diner for us ko kuma muci anan tace “okay ba dan ranta ya so ba dan ba dabiarta bace cin abinci a waje yanzu ganin girmansa da kuma ganin shi zata aura yasa ta amince .”








Suna isa jara mall sai ga wata budurwasa khairat wacce take mutuwar son shi sun dade tare suna bin juna dashi har da alqawarin aure a tsakaninsu sai dai shi har ga Allah baya sonta kawai jikinta yake so tazo ta wuce taganshi tare da maryama ,haba nan zuciya ya debeta ta d’aga hannu zata zabgawa maryama mari kenan ya rike hannunta ya wanke ta da mari gudu biyu masu kyau “in your life don’t ever I said don’t ever see me with a girl and act like a fool banza sha sha this girl you seeing here tafi min dubu akanki kina jina mara kamun kai maryama kam baki bud’e take kallonsa ya dawo ya gaban maryama yace “sorry my princess kiyi hakuri I caused all this let just take a way muje nayi feeding dinki a mota plse I’m sorry.”




Haka sukai take a way yana bata hakuri a zuciyarta kam sam bata ji dadin yadda ya mari mace haka ba, kuma menene tsakaninsu “? ya bud’e mata ta shiga mota ya mika mata farar ledar hannunsa ya zagaya ya shiga mota ya zauna yana cewa “sorry my princess ko zamu shiga quest house din can ne saboda kici abinci muyi hira before I drop you tace “no tana girgiza masa Kai “wai da Ina son ki samu natsuwa ne kafin kije gida “wacece wannan yarinya “.karki wani damun kanki akanta “khairat sunanta tana masifar sona haka zalika duk sanda ta ganni da wata haukacewa take kuma fa wallahi ni bana sonta”.yayi maganar yana Shafa sumar kanshi “da fari dai mata ababen girmamawa ne bare mutumin da yake sonka gsky ni dai banji dadin abinda kayi ba .”






“Kenan kina nufin na bari ta tozarta min ke kamr yadda ta saba no no impossible I can take it hakan da nayi shine daidai kema yanzu kika nunawa wani darajata ni me yasa zan bar wata banza mara kanmu kai ta ta’ba min wannan kyakkwar fuskar taki da nake kallo tmkr lu’u lu’u never ai sai inda qarfina ya qare haba sonka fa take “to ni wallahi bana sonta ke kad’ai nake so kece madubina kuma zabina nifa da ke na fara haduwa bazan auri matana ba domin kece irin type dina “ni dai gsky banji dadi ba kuma hakan bai burgeni ba marin mace yaruwata akaina wallahi naji zafin marin ina jin kamar ni akawa “okay am sorry my princess da wannan hirar suka qaraso unguwarsu alokacin da qarfe shida saura ta buga ya sauketa ya kama gabansa .”




Jiki a sanyaye maryama ta d’auki hanyar gidansu inda zuciyarta ke wani irin bugawa kai tsaye bangaren umma ta nufa sai dai taga kofar a rufe ta duba inda take ajiye key ta d’auka ta bud’e ta shiga ta ajiye ledar hannunta a fridge ta fito tare da maida kofar ta rufe ta ajiye key a inda ta d’auka ,kanta na mata wani irin mugun sarà ta shiga bangaren aunty bata ganta a parlour’n ba akan kujera ta zauna jagwba tana rufe shayayyun idanunta tana tunani abinda alhj mansoor ya aikata mutumin da takewa kyakkwan zato da kuma halin data baro mr ata zame wa tayi kwanciyarta akan doguwar kujera tana sake zurfafa tunani yadda zatayi da mr ata gobe dan tasan dole yayi fushi sosai daita wasu hawaye ne masu azabar zafi suka taru a kwarnin idanunta alokcin tai nasarar fashe wa da kuka sai datai mai isarta sannan ta tashi ta shige d’akin aunty bayan wasu mintuna ta fito ta nufi bangaren umma har lokacin bata dawo ba tai shiru tana tunanin inda taje .”






Ahankali ta shiga d’akinta ta cire kayan jikinta ta d’aura towel ta shiga bayi tayi wanka tare dauro alwala dan alokacin sallah yayi ta fito tana goge jikinta da gefen towel bayan ta gama ta saka wasu Kayan marasa nauyi adaidai lokacin aka Kira sallah ta qarasa inda daddumar sallah take ta Kai hannu ta d’auki hijab dinta dake ajiye a gefe ta zira ta tada sallah .”bayan ta idar bata mike ba ta cigaba da zama tana zikirin la ila a illa anta subuhanaka inni kuntu minal zalim tana zaune haka nan ta dinga Jin fad’uwar gaba jifa jifa km tana jiyo sanayayyin kamashi turaren mr ata ta lumshe idanunta kawai tana tunanin gezo qamshinsa yake mata tmkr yadda kammaninsa yake mata gizo acikin kwayar idanunta tana zaune har aka Kira ishai ta mike ta gabatar bayan ta idar ta cire hijab dinta ta daura hulla akanta ta fito zuwa parlour’n tana gama fitowa idanunta ya sauka akan mr ata zaune akan kujera mai zaman mutun d’aya gabanta ne bada wani irin ras rass !! har bata san lokacin data Kai hannu ta dafe qirjinta ba .kallo d’aya tayi masa ta fahimci ranshi a matukar bace yake sai furzar da iska mai zafi yake daga bakinsa sosai tayi mamaki da ganinsa dan bata ta’ba tunanin zai biyota ba tamkar mai shirin yin kuka ta qarasa bakin kofar umma tare da ta’ba kofar ta zuge labulen kad’an ta hangota zaune akan dadduama hannunta a sama tana addua.”




Ahankali ta saki labulen tare da janyo kofar kamar yadda take ta dawo kusa dashi tace “lafiya sir ?”me kazo yi km ?”yayi mata banza tamkar bada shi take ba ya cigaba da furzar da iska yana girgiza qafarsa d’aya babu alamun zai mata magana qara matsowa tayi tace “I’m talking to you sir “?what the fuck do you want “?ya fad’a a hassale“ganin yanayinsa da kum yadda yyi mgana yasa tayi kasa da muryarta tace “dan Allah sir kayi magana ahankali kar umma ta fito koma nace ka tashi ka wuce karta fito ta iskeka anan tayi shiru tana dubansa kamar yadda yake dubanta “ban san me zance mata ba idan ta fito and bansan me yasa kake damun kanka akaina ba alhalin ba sona kake ba ..”




“Zaki iya kasheni ?”tai shiru kawai tana dubansa gabad’aya yanayinsa ya sake canzawa “kill me maryama I no you have already hate me so it’s normal if you can kill me. ya qarasa maganar yana sake tsura mata tsumammun idanunshi sauke numfashi tayi tana kallonsa ranta a dan bace tace “be serious sir please ka tashi ka wuce yanzu da da ba d’aya bane a yanzu Ina daf da zama mallakin wani” tai maganar tana Jin fad’uwar gaba mai tsanani tsaki yayi sannan yace “ni me na kashe miki da zaki auri wani ki barni ?”ajiyar zuciya maryama ta sauke “wannan shine kuskuren da zanyi arayuwarta na amincewa aurenka batare danasan matsa…”saurin dakatar daita yayi a fusace yace “look maryama if you’re here to joke or talk about some useless issues just stop “ya qarasa maganar yana zaro mata ido kallonsa ta cigaba da yi da mamaki “leave this useless man and marry me” ya fad’a a zafafe .”




Hawaye ne ya gangaro daga idanunta yayinda bakinta ya kasa furta komai sai kallonsa data cigaba da yi “ taya zan fasa aurensa byn mun gama tsara komai “wannan kuma ya rage naki amman lallai komai ya rushe zuwa gobe ki kirani a shirye nake da aurenki yana gama fad’ar haka ya mike ya nufi kofar fita da sauri ta biyo bayansa alokacin har ya fito haraban gidansu ta riko hannunsa “ka tsaya muyi mgn .”a fusace a juyo “me kuma zaki ce min ?”bana bukatar Jin komai baya ga kin fasa aurensa dan ko kin auresa sai dai kiyi aure akan aure .”inna lillahi wa inna ilaihi rajiun “bansan me zan fadawa iyayena ba “dont be stupid maryama yadda kika fad’a masu zaki aurin wancan usuless din haka zaki koma ki fad’a masu kin fasa ni zaki aura “.




“this is complete no mr ata I can’t betray him bai jira me za tace ba ya juya ya cigaba da tafiya sake tare hanyarsa tayi tace “why mr ata why you al ways huts me ?”amman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login