Showing 123001 words to 126000 words out of 178062 words
Chapter 42 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
daya saura a tsakaninsu wanda hakan yasa numfashinsu ya gauraye waje d'aya dan sosai suke shakar numfashin juna wani wahalallen numfashi ya sauke yace "kiyi zaki iya kiyi kuka da iyakacin qarfinki maryama wallahi muddin bakiyi ba bazaki samu kwanciyar hankali ba oya one ,two three .." ai yana gama fad'ar 3 ta kamkame jikinta waje d'aya ta soma kuka mai qarfi tun daga qasan zuciyarta kukan ke fitowa da sauti jikinta na d'aukar rawa kuka take sosai jikinata na cigaba da rawa har qafafuwanta suka kasa d'aukarta bata san sanda ta zube jikinsa ta rungumesa tsam ajikinta sauran kad'an mr ata yayi qasa amman qarfin da yake tattare a jikinsa ya bashi kariya ya tsaya bisa qafafunsa sosai batare daya kai hannunsa jikinta ba."
wani irin sanyi mai tattare da jin dadin samun nasarar da yayi akanta ya shiga bin jini da jijiyo dake aiki a sansar jikinsa lokacin da yaji ta qara kamkame shi ajikinta hakan yasa yaji wani maganadisun soyayyarta na sake shigarsa, yayinda har lokacin tana rungume tsam dashi tana wani irin kuka mai ban tausayi tana qoqarin goge duk wani abinda tasan damuwa ne acikin momery dinta sai daya tabbatar da tayi irin kukan da yake bukata kafin ahankali yasa hannunwansa duka ya zagaye kugunta dashi ya kai bakinsa daidai saitin kunnenta ya soma mata magana cikin wata irin kasalalaliyar murya mai cike da tausayawa "maryama duniya cike take da jarabawa kala kala amman idan kayi imani da Allah ,Allah yana tare da kai ,ki manta komai da duk abinda ya faru a tsakaninki da mutumin nan zaki iya samun madadinsa koma wanda ya fishi arayuwarki, kisani da kice kika mutu da yanzu yana tare da wata ko nadiya sun cigaba da rayuwarsu daga inda suka tsaya"ki mantashi arayuwarki shi zai bawa wani damar mallakarki ko baki damar mallakar wani ."
ahankali ya dinga mata magana batare da yace ta daina kuka ba , sosai maryama ta narke ajikinsa ta manta ajikin wanda take kwance inda daddan qamshin turarensa mai sanyi ya dinga shiga hancinta yana kaiwa kwakwaluwarta wani sako na musamman tare da táttaro duk wata natsuwa da
kwanciyar hankali zuwa kwakwaluwa dama gangar jikinta ."sosai zuciyarsu tai nitso cikin wata duniya inda soyayyar maryama ta sake samun kyakkywan mazauni acikin zuciyar mr ata yayinda daga can nesa hasken camera sultana ce ke faman aikin d'aukarsu hoto "bazaki ta'ba samunsa ba maryama ,yadda ban samesa ba kema bazaki ta'ba samunsa ba bayan baki samesa ba kuma kin shigar da kanki cikin matseefar da bazaki iya kwatar kanki ba sai kinyi nadama da danasani arayuwarki, idan kuma kince zaki iya wannan fad'ar lallai zan koyar dake yadda ake dandana dacin mutuwa ."kwanciya maryama tayi lamo ajikin mr ata tana kuka tana shaqar qamshin turarensa , zuban hawayenta yake ji agaban rigarsa dan duk ta 'bata masa gaban rigarsa da ruwan hawaye "tabbas duk maganganunsa gaskiya ne ya kamata ta manta komai kamar yadda kowa yake fad'a mata domin ita din macece bata da wani dogon lokacin da zata bata , wani irin dogon numfashi mr ata ya sauke yana hura mata iskar bakinsa cikin kunnenta inda maryama ta sake shigewa jikinsa yayinda sultana ta zuba masu ido cikin zallar bacin rai ganin yadda yanayin ata ya canza one time acikin kankanin lokaci ."
ahankali mr ata ya soma qoqarin dagota daga yadda ta kwanta a qirjinsa maryama ta sunkuyar da kanta kanta qasa tana mai tsananin jin kunyarsa "am very sorry sir maryama ta furta had'e da juyawa da sauri tana tafiya cike da kunya tamkar bata son taka qasa ya tsurawa bayanta ido most especially tsukakken west dinta wanda ya bawa bombom dinta damar nunawa kad'an"alhamdulillah ya rab ."ya furta a fili sannan ya tura hannunsa d'aya cikin aljihunsa ya biyota da sauri sultana tayi baya daga maboyarta ahankali mr ata ya kamo maryama kasamcewar bata da sauri suka jera kafad'a da kafad'a "bai ce mata komai ba dan ya fahimci kamar a yanzu take jin kunyar irin rungumar datai masa suna qarasa saukowa qasa direbansa da masu tsaronsa suka taso tare da zagayesu .da kanshi ya bud'e mata murfin mota kamar yadda ya saba mata kuma duk akan idanun sultana kuma batayi sanya ba gurin saurin d'aukarsu a hoto ,wadan nan hotunan sun isheni blackmailing dinsa ko ya amince da aurena cikin sauki ko kuma na yad'asu a social media duniya tasan halin da yake ciki a ma'aikatansa "nasani bazai ta'ba yarda mutuncinsa ya zube ba dan dole zai yi abinda na bukata."
Tun jami'an tsaronsa da direbansa a ruwa suna mamakin yadda mr ata yake ma maryama har sun zo sun daina mamaki domin dai zuwa yanzu sun gama fahimtar mai gidansu ya rufta cikin shaukin soyayyar yarinyar né ,sai dai suyi masa fatan alkhairi jiki a sanyaye maryama ta shiga motar ta zauna tare da lumshe idanunta inda zuciyarta ke bugawa da qarfin gaske ."ya d'an duka ta gefenta, hakika ran sultana baqaramin baci yayi ba sakamakon ganin mr ata durkushe yana rike da hannu rigar maryama yana qoqarin janye mata dan kar ya had'a da murfin mota wani dogon tsaki sultuna taja tana sake mamaki mutumin da tasani mara fara'a da sakin fuska mai nuna ma mata tsantsar rashin kulawa da soyayya mara son farincikin mutane ,mara damuwa da damuwar wani wai yau shine durkushe agaban wata ,watan ma ma'aikaciyarsa bayan ya gama rungumeta anya kuwa duk wad'an nan babuwan ba gizo yake mata ba ?" ta kai hannu da sauri ta murza idanunta adaidai lokacin daya mike tsaye yana aika ma maryama wani kallo wanda bashi da maraba da kallon soyayya "sannan ya maida murfin kofar a natse ya rufe ."
ya zagaya Wanda shi tuni an bud'e masa bangaren da zai zauna ya shiga ya zauna yana d'an kallon fuskarta da tsumammun Idanunshi har a ruwa ya já motar kwayar idanunshi da hankalinsa na kanta ya zuba mata ido yana qare mata kallo ."ya rasa wani irin mahaukacin so yake mata "numfashi maryama ta sauke sanda ta tuna girman taimakon da yayi mata a yau din nan ,ya daukar mata alqawarin had'ata da nadiya kuma ya cika wannan alqawarin ."
hakika ya cancanci ta yaba masa idan ma da hali ta had'a da godiya dan gabdaya wani abu daya tsaya mata a qirjinta ne taji ya fad'a zuwa cikinta wanda take jin babu tantama tarin damuwa da bakinciki da ta dade tana fama dashi na tsawon lokaci ne ya bar rayuwarta .saukar laulausar tafin hannunsa a saman hannunta yasa ta bud'e idanunta ahankali ta waigo gefen da yake zaune yana faman kallonta kamar zai cinyeta ."nan take idanunsu ya tsarkar cikin juna sukai shiru suna kallon juna cikin wani irin yanayi mai tattare da shauki kafin ahankali maryama ta maida idanunta ta runtse dan bazata iya cigaba da kallonsa ba dan wani iri take ji a sansar jikinta .”
kallon da yake mata ma ayanzu da tana da hali zata iya hanashi domin kallo ne dake nukurkusa mata
garkuwa jiki ,ahankali ya tsarke yatsun hannuwan su waje d'aya ya fara murzawa a tare suka ji wani abu ya tsarga masu a gabad'aya ilahirin jikinsu da sauri ta sake bude idanunta ." gani tayi ya mugun tsareta da idanunshi masu firgita mutum Iokaci daya tayi saurin kawar da kanta gefe tana jin wani irin fad'uwar gaba kmr tasa masa kuka tace masa stop touching my body amman ta kasa aiwatar da komai ."
Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
38
A kaikaice mami ta kallesa sannan tace “maganata ta tabbata kenan ?ATA ya bala’in tsurawa mami Ido yana kallonta fuskarsa d’auke da mamakinta yayinda kwakwaluwar sa ta shiga maimaita masa abinda ta fad’a yanzu “maganata ta tabbata kenan “.to me hakan yake nufi?” “adamcy!“ ta kira sunansa tare da riko tafin hannunsa cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da jin tsoron abinda take son fad’a ,shi kam kallonta ya cigaba dayi cike da rauni tare da yin kasa da murya yace “sweetheart ina jinki “da gaske adamcy son yarinyar nan kake tunda gashi kace zata zo? numfashi ya sauke yana cigaba da kallonta “itace fa ta matsa masa da batun tana son ganin maryama yanzu kuma ga abinda take fad’a “wai meyasa sweetheart take masa haka ne ?numfashi ya janyo da kyar ya fesar sannan ya motsa lip’s dinsa yana cewa “sweetheart nifa ban fahimceki ba?” ya qarasa maganar yana mai kawar da kanshi daga kallonta “adamcy nasan ka fahimceni sosai ba iya zargina ba ,hatta zuciyata ta aminta da son da kake ma yarinyar nan abida naso ya faru akan mar…” .“sweetheart abar maganar nan .”ta sake bud’e baki har ta soma magana ya juyo da sauri yace “dan Allah sweetheart karki sake cewa komai akan yarinyar nan ,itama maryama baza tazo ba shikenan “ya qarashe maganar cikin ‘bacin rai da rauni a fuskarshi ,ya rasa dalilin da yasa take masa haka idan ma son yarinyar yake me ye laifi aciki tunda shi ba yaro ne da zaa dinga masa irin haka?.”tace tana son gani yariya yace yaji sannan kuma ta shigo masa da batun wata maryam abinda ta rigada tasani ne ko maganarta baya son ana masa,wannan matsalar na cikin abinda yasa yake son ya auri maryama a boye sai bayan sun haihu sannan ya fad’a mata dan yasan kota amince ya auri maryama to fa kullum sai tayita masa mitar rashin kasancewarsu da wannan banzar maryam din ”.
“Me yasa?kuma saboda me za’a bari “?me yasa zaka d’auki zafi daga ‘yar wannan maganar har kace baza tazo ba ?”tayi masa tambayar ajere tana dubansa cikin tsananin tashin hankali duk da dai tafi son shi da maryam dinta amman kuma hakan bazai sa taki son abinda yake so ba dan arincikinsa shine nata “kayi shiru kana jina kayi magana mana,sarkin zuciya. “Kai dai ba’a ta’ba yin hirar arziki da kai batare da ka shigo da zafin zuciya ba ,kanshi ya juya tare da zare hannunsa cikin nata ya had’e waje d’aya ya fuskanci mahaifiyar tashi cikin sanyi yace “ba maganar zuciya bane kawai dai gani nayi rashin zuwan nata zai fi zuwanta samun kwanciyar hankali”amman dai kasan kana son yarinyar nan “inna lillahi ya furta yana runts ido “babu wani batun inna lillah gskyr dake cikin zuciyarka nake son nasani “dan girman Allah sweetheart ki bar maganar nan kuma maryama bazata zo ba dan nasan zuwanta ba zai kwantar miki da hankali ?
”girgiza masa kai tayi alamun a’a.”karka damu ka kawo min ita Ina son naga ka sake ajiye iyali a karo na biyu, zaka auri yariyar nan kuma anan kusa idan ma bazaka iya sheida mata kana sonta bane ni zan sheida mata da kaina karyata taki amincewa ,dan banga macen duniya da zaace mata ga miji kamar d’ana tayi rejecting ba gara ma ka natsu ka kawo min ita ni na sheida mata d’ana yana sonta tunda kai girman kan tsiya bazai barka ka iya sheida mata ba.”numfashi da ajiyar zuciya ya sauke atare still idanunshi na kallonta .mami ta jima zaune suna hira irinta d’a da mahaifiya sannan tai masa sallama ta sauko qasa ta shige bangarenta .”
Bayan fitar mami tashi yayi ya shiga bedroom dinsa ya qarasa inda system dinsa yake ya d’auka ya dawo kan bed dinshi ya kishingid’a akan gadonsa had’e da tokare hannunsa d’aya a gefen kungunsa sannan a hakan ya kunna system ya soma daddana keyboard din system dinsa yana amsa sakonin abokan kasuwancinsa yayinda bangaren maryama itama zaune take a tsakiyar gadonta ta rungume pillow a qirjinta tana tunanin abinda ya faru yau atsakaninsu sosai take tunanin abinda mr ATA yayi mata a yau din nan ,ahankali komai daya faru tsakaninsu yake zuwan mata daki daki har zuwa sanda ya kamo hannunta yace“tayi jump !”jump maryma” ya fad'a hankalinsa a matukar tashe yana sake hura hanci “wannan shine best solution agareki ,shine kawai abinda zai kawo miki qarshen kuncin da kike ciki ,kuma shi zai kawo qarshen rayuwarki .”
”kina zubar da hawayenki a banza bayan Kinsan mutumin nan ya mutu baya raye "wani irin tsoro da matsanancin firgice taga ya bayyana akan fuskarsa alokacin "oya jump!”har sanda ta soma kuka mai tsanani wanda ya zamo sanadiyyar kawar da tarin damuwarta wani irin naunayen ajiyar zuciya ta sauke mai qarfi tana cewa “duk rashin kirkinka da nake gani still kai din mutu min kirki ne ,ban ta’ba tunanin zaka zamo silar yayewar damuwata ba sai gashi acikin awanni ka zamo silar kawar da tarin damuwar da nayi shekara da shekaru ina dawainiya dasu.” “hakika kai din mai kyakkywar zuciya ne ,kawai da nice da wasu daga cikin mutane muke maka wani irin kallo ,duk da kana da wasu dabi’u marasa kyau amman dai kana da kyakkyawar zuciya .”ta furta a fili fuskarta bayyane da murmushin farinciki ta matse pillow dake makale a qirjinta tana cewa .”maryama tana godiya bisa qoqarin da kayi mata na gode sosai daka canza min rayuwa .”
ahankali mr ata ya d’auke kwayar idanunshi akan system zuwa wani bangare dabam tare da rufe system din gaba daya“ya d’aga kanshi sama kallon saman d’anki tunanin maryama yake yana jin kamar ya kirata “idan ka kirata kace mata me?”ai ita ya kamata ta kiraka no kai ya kamata call her and tell her how much you loves her dan idan ka bari wani ya sake sace zuciyar yarinyar nan zaka iya mutuwa for real you’re so much in love with her .”ya fad’a yana runts tsumammun idanunshi .a natse maryama ta sauko daga kan gado ta soma tafiya tana magana a fili muryarta cike da matsanancin farinciki “na gode sosai mr ata Allah saka maka da mafificin alkhairi.”
shima bangarensa mikewa yayi tsaye tare da yin shiru ya saka hannunwansa duka cikin aljihunsa
wondonsa yana magana a fili “lallai soyayya ya zautar da kamilar yarinya mai tsananin baseera da sanin kan aikinta yana matukar son furta mata cewar yana sonta amman soyayyar wannan mataccen da yake hangowa har yanzu acikin kwayar idanunta shine dalilin da yasa ya kasa fad’a mata ,hakazalika itama karon kanta shine dalilin da yasa ta kasa fahimtar inda ya dosa ina ma zata bashi damar daya d’an d’ana mata gard’in soyayyarsa.”amman zan yaki zuciyarta.
“ zan yi duk yadda zanyi na raba zuciyarta da tunanin kowa sai nawa ,zan dasa mata qaunata ta yadda zata kasa samun kwanciyar hankali sai tana tare dani.”cire hannuwansa yayi duka yaje ya bud’e wordrobe dinsa ya d’auko wani takarda ya rufe wordrobe din ya tsaya sosai rike da takardan yana kallo yana cigaba da tunanin maryama sosai yake jin tsananin soyayyarta na sake ratsa dukkanin sansar jikinsa kai kawo ya shiga yi acikin d’akin shi kad’ai yasan irin azabar da yake ji ajikinsa .”
Hotonsu maryama aunty abida ta tsaya tana kallo jikinta na wani irin rawa tmkr mazari “meye haka sultana? meke faruwa haka ?”mafarki nake ko kuwa gaske ne abinda nake gani adam ne rungume da wannan yarinyar ?shine aunty ai ba wannan bane karo na farko da suke lalatarsu a office sai dai wannan shine karo na farko da nayi qoqarin d’aukarsu batare saninsu ba bama fa AGC wannan abu ya faru ba d’aukar ta yayi taka nas suka bar kamfani zuwa ATA company .” “aikinsu fa kenan sai dai idan basu had’u da juna ba.” nan take gaban aunty abida yayi wani irin bugawa da qarfi tamkar wata matarsa “aunty da alamun yaya adam yana tsananin qaunar yarinyar nan “ai wannan ma ba abu ne mai yuwu ba sultana kinji yadda nake ji kuwa “ta mika mata wayar tana cewa” ai kallon wadan nan hotunan zai iya sa mutun yayi loosing temper dinsa .”wallahi aunty haka nake fama da wannan bakinciki kullum zuciyata kamar ta fashe ni nasan bazan ta’ba samun auren yaya adam ba kinsa zuciyata ta kamu da tsananin soyayyarsa .”ta qarasa mgnr tana dafe goshinta
“aunty kece kika dasa min soyayyarsa a zuciyata gashi nazo ina masa wani irin mahaukaci so da bazan iya rayuwa babu shi ba “sultana ta qarasa maganar cikin zafin rai “ki natsu sultana duk runtse duk wuya ina tare dake kuma zaki auresa sannan soyayyarsa da wannan yarinyar ba abu ne mai yuwuwa ba kamar ma ya lalace ya gama “me zaki iya yi aunty akai ?zanyi komai akai sultana “sultana ta matso kusa da auntynta tana cewa “aunty kibi komai a hankali karki yi bakin jini ki barni dashi “no no sultana gara ni nayi saboda kinsan halinsa bazai ta’ba d’aga miki qafa ba “yadda bazai ta’ba d’aga min qafa ba haka kema bazai d’aga miki ba amman da sannu ni zanyi maganinsa sai na watsa hotunan nan zuwa social media kowa ya san halin da yake ciki sai dai kafin nayi haka sai muyi da wajewa dashi zai aureni ko kuwa na yad’a idan ya amince fine idan kuma yayi taurin kai nima zan nuna masa kalar nawa taurin kai ta fad’a idanuwanta na kawo ruwan hawaye “.
“mai na rasa aunty da yaya adam bazai soni ba ?wallahi aunty ina tsananin son yaya adam yana da matukar mahimanci