Showing 147001 words to 150000 words out of 178062 words

Chapter 50 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

komai “maryama bai kamata kiki bin umarnin umma ba ,meye aciki ki kai masa idan ya kar’ba fine idan bai kar’ba shikenan sai ki bawa wani amamn idan kika ki bashi idan kin koma gida ta rutsaki me zakice mata?” ko idan tace ki rantse me zaki ce ?”.
shiru tai kawai tana tunanin yadda zatayi bayan wasu mintuna ta mike ta nufi office dinsa bata iske madam some a mazauninta ba dan haka ta soma qoqarin shiga ta ajiye masa ta kama gabanta inda ahankali madam some ta kai hannu ta dafata da sauri ta juyo jikinta na wani irin rawa lafiyarki maryama me kikeyi ?sorry ma ta fad’a bakinta da jikinta na rawa kina bukatar wani abu ne ?no ..”no ma .”meye wannan rike a hannunki ?”amm daman mamana ce tayi wa mr ata custard tace na kawo masa .”
nan take gaban madam some ya bada rasa haka ma sultana dake tsaye a bayansu dan tana hankalce da duk wani motsin maryama “kutumar uba can .”sultana ta furta tana cewa” lallai ma yarinyar nan yayinda madam some tace “shikenan kije ki fara aikinki kafin yazo dan har yanzu bai qaraso ba tukun, jiki a sanyaye ta juya bayanta da zumar komawa office tana gama juyawa taga sultana tsaye tana jifanta da wani rikitaccen kallo wanda yasa hantar cikinta kad’awa bata ce mata Uhm ba bare uhm uhm hakan nan yau kallon nata ya saukar mata da mummunar fargaba mai tsanani.”sultana ta cigaba da aika mata da mugayen kallo mai had’e da harara.”








Maryama na tsaye cikin tashin hankali da tsananin fargaba sai gashi ya shigo ya iskesu tsaye “good morning sir”. ta furta da sauri qirjinta na bugawa “morning “!kawai yace tare da kallon inda madam some take yace some kije ki fad,awa duk wanda aka turawa hotunan nan su goge kuma muddin ya fita nayi bincike na gano wanda ya fitar dashi qarshen aikinsa yazo bayan na d’auki mataki akansa” okay sir yana gama fad’ar haka ya shige office dinsa yayinda maryama ta sauke numfashi tana mai Jin farinciki ta koma office da sauri sultana itama ta juya ta shiga wani office ta samu waje ta zauna tana tunanin matakin da zasu d’auka akan maryama.”




Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye acikin office din tana tunanin yadda zatayi ta bashi sakon umma tayi taku d’aya biyu sai kuma ta tsaya gabdaya ma’aikatan dake office din suka bita da kallo sultana da hankalin ta ke kan maryama tai murmu shi yayinda maryama ke sake sake “ naje na bashi yanzu ne ko kuma na bari zuwa anjima na kai masa tana kallonsa ya fito yana kiran sunan some “yes sir “! ta amsa masa dashi yayi mata magana a can kasan makoshi sannnan ya fice da idanu maryama ta bishi dashi tana sauke wani wahallen numfashi ,sultana ta kasa hakuri ta mike ta shigo office din da maryama take ta tsaya adaidai gefenta “ban ta’ba ganin yar talakawar dake shishigi irin naki ba ,wama yasan me aka zuba masa cikin custard din da ake son ya sha dan naga duk hankalinki baya jikinki alamun rashin gasky? .






maryama ta dago kanta ta kalleta da mamaki sai dai bata ce mata komai ba ta maida hankalinta akan aikinta tana zance zuci ,”da Kinsan da yaya na taho da custard din nan da bakice haka ba ,any way ma mai zai sa ayi wa mr ata wani abu mai ake nema agurinsa kawai dai kyatatawa ce irin ta umma ba komai bane”idan kuma son shi kike yi gara kiyi maza ki ciresa aranki dan yafi karfin aurenki ,sai dai ya more kuruciyarki kamar yadda muka gani a hotunan wama yasan me ya faru a tsakaninku dan a yadda nake kallonki zaki iya aikata fiyye da zina “subhallah maryama ta furta a fili tana kallonta da kwayar idanunta da suka soma canza kala tsabar bacin rai “mai yasa sultana zaki fad’a min haka ?”wallahi Allah shine shidata akan hotuna nan kuma nasan duk abinda zan fad’a bazaa ta’ba yarda dani ba amman kije na barki da Allah daman dashi kawai zaki barni dan babu abinda zaki iya min munafuka kawai “dan Allah sultana bana son tashin hankali ki barni naji da damuwata maryama ta fad’a qirjinta na Dylan uku uku gbdy taji sauran natsuwar dake jikinta ta kau mussaman a yanzu tafi Jin bugun zuciyarta yana qaruwa
duk baqaqen maganganun sultana maryama bata tankata ba ta shareta ta cigaba da aikinta sai dai zuciyarta ke mata wani irin zafi kusan mintuna talatin maryama na zaune tana aikinta batare data kalli kowa acikin office dinsu ba haka zalika bata ga dawowar mr ata ba har lokacin break yayi.”
ta ciro flaks dinta ta d’aura akan table ta soma shan custard din tana cikin sha wayarta ta soma vabriting alamun kira ta ciro ta duba sunan umma ta gani yana yawo a scren din wayar ta d’aga tana cewa “hello umma nah daga bangaren umma tace “hello maryamata ya kike ya aiki.”? “alhamdulillah umma!” kin bawa mai gidan custard din kuwa ?”
”amm umm ban bashi ba nasan kunya kike ji da tsoro Kiyi qoqari ki cire tsoron nan ki bashi kinji diyata zan ji dadi idan kika bashi sannan zanyi farinciki idan ya kar’ba ya sha.” “In sha allahu umma zanyi qoqarin na bashi yanzu ma dai baya nan tun dazu daya shigo ya fita banga dawowarsa ba amman da zarar ya dawo zan bashi tana cikin magana sai gashi ya dawo tace “yauwa gashi nan ma amman wallahi umma tsoro nake ji ban san yadda zai dubi abun ba bana son yayi react kamar cutar dashi zanyi .”




“karki damu maryama bana jin zai yi tunanin wani abu kije ki bashi “to umma kin sha naki ne Eh umma shi nake sha okay yayi sai kin dawo “ya rab ka taimakeni ban san yadda zanyi na bashi custard din nan ba gashi yau da alamun akwai rashin mutunci atare dashi kar naje ya sauke min ruwan balai tana cikin wannan halin yazo ya tsaya akanta “maryama”! yes sir !”ta amsa da haka tana qoqarin rufe flak’s din gabanta ta mike tsaye “ance kin kawo min wani abu me kika kawo min ?..”




“uhm ..” no sir bani bace daman umma ummata ce .”ki natsu ki yi min magana ta yadda zan fahimta “daman me ..”?daman ummata ce tayi maka tace na kawo maka “.ta fad’a jikinta da zuciyarta na karkarwa hakan yasa tayi saurin tsarke hannu wanta waje d’aya domin taimakawa gangar jikinta samun sausauci idanunshi ya tsura mata ta cikin farin glas din dake manne da kwayar idanunshi yana kallonta kmr zai cinyeta ,kafin ahankali ya ciro hannunsa d’aya cikin aljihun wondonsa yana kallonta yace “me ta baki ki kawo min ?da sauri ta ciro flaks din ta miko masa jikinta na sake d’aukar rawa, ya cire dayan hannunsa dake cikin wondo ya amsa ya bude flaks din data mika masa yayinda ta tsaya a tsorace tana kallonsa tare da jiran rashin mutuncin da zai mata .”




yana gama budewa ya tsaya shiru yana kallon abinda Ke ciki yayinda ta cigaba da kallonsa a matukar tsorace muryarsa a kasalance yace“meye wannan ? ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi masu matukar tsoratarwa” kayi hakuri sir ummana ce tace na kawo maka .”numfashi ya sauke tare da cewa “yakayi tasan ina matukar son fruit custard kallonsa tayi da sauri tana jin wani irin sanyi a zuciyarta wanda bai tsaya iya zuciyarta ba har ganganr jikinta take jinsa wani sanyayen dadi ne ya mamayeta” kana matukar son fruit custard ?”ya gyada mata kai kawai tare da yin shiru ya rufe flaks din ya juya har yayi taku d’aya sai kuma ya tsaya rike da flaks din “kice wa mum na gode sosai” kenan zaka sha? ya juyo tare da lumshe mata tsumammun idanunshi bana shan abun hannun kowa bayan mahaifiyata da some amman zan sha saboda mahaifiyarki ce tace ki kawo min ,”kuma kace nace mata ka gode?” meye damuwarki dan nace na gode ?ya fad’a yana hura mata hanci tace” babu “!




maryama ta waiga waje taga babu mai zuwa dan Allah Allah take ya fita ya barta kar wani ya gansu bare sultana”
”maryama kina mamaki dan na kar’bi abun hannunki” ta gyada masa kai alamun eh “ina mamaki ne sir dan na ma fad’a mata bazaka kar’ba ba saboda behavior’s dinka sai gashi ka kar’ba babu mai saka abu babu mai hanaka babu wanda kake iya yiwa godiya sai gashi kayi wa ummata,kasan wani abun ?”yayi shiru kawai yana kallon bakinta da take magana dashi daga gida har office nasan duk dabi’a daya kake yi dan allah ka canza wannan dabiar taka kowa tsoronka yake ji “.sannan kuma na gode sosai da kace kowa ya goge hotu nanmu hakan ya rage min tarin radadi da nake ji duk da ya zubar min da kimata agurin abokan aikina ,sun zargeni Akan laifin da ban aikata ba kuma suna min kallon banza gabadaya bana cikin sukuni da kwanciyar hankali ina jin kamar na bar aikina domin bazan iya jurar irin kallon kaskanci da tozarcin da suke min ba ta qarasa maganar muryarta na rawa “ban san me zan cigaba da cewa ba amman naji dadi sosai dakasa suka goge ta fad’a tana d’ago idanunta dake cike da ruwan hawaye .”




Shiru sukai daga ita shi kafin ahankali ta d’ago idanunta nan take idanunsu ya tsarke cikin juna ,ido cikin ido suke kallon kwayar idanun juna suna cikin wannan yanayin sai ga sauran ma’akatan sun shigo da sauri maryama ta d’auke kwayar idanunta acikin nashi ta maida wani bangaren turus sukayi suna kallonsu daya bayan daya kallo daya yayi masu kowannen su ya kama gabansa madam some ta shigo itama kallo daya tayi masu ta d’auke idanunta ta wuce a natse ya soma tafiya rike da flaks din hannunsa cike da jin haushin abinda sukai mata yana zance zuci baku sani bane,akanta zan iya korar kowa acikinku, amman zan d’auki mataki akai dan babu wanda ya isa ya tozarta min rayuwata.”






Bayan wasu mintuna ya bude kofar office dinsa da qarfi ya fito yana waya ya isa a gaban madam some tare da cire wayar a kunnensa ya nuna mata hotunansu shi da maryama “ kinsa sun goge hotunan nan ko kuwa ?”yes sir sun goge ya qara taku daya ya isa inda take zaune yana cewa “zan yiwa kowaye ya tura maku hotunmu rashin mutunci domin ba maryama ake son tozarta wa ba ni ake son tozartawa ko ba haba,” haka ne sir wannan abu ba wai da gaske bane nan ya shiga kora mata dalilin da yasa hakan ta faru batare da yasan ma yana mata bayani ba yana dasa aya tace “I will explain everything to them sir “ bana bukatar some amman na rantse da girman allah bazan d’agawa kowaye kafa ba kuma zan yi komai akan duk wanda zai ciwa maryama mutunci acikin ma’aikatar nan ya qarasa fad’ar haka a tsawa ce kallonsa take cike da tsananin tsora da mamaki yana gama fadar ya wuceta ya shiga office dinsu maryama sakamakon hangosu da yayi suna tautaunawa a tsakaninsu sun ware maryama .”






shiru kowannensu yayi alokacin da suka gansa “why everybody quiet?a tsawace ya tambayesu yana had’e rai fiyye yadda yake yi “oh ashe kunyi shiru ne saboda kunsan cewar ni ne shugaba anan ba .”?ai bai kamata kunyi shiru ba ku cigaba da tautaunawa ko bakuna tautaunawar ne akan abinda ya faru tsakanina da maryama ba ? daya bayan daya ya kira sunansu tare da cewa ku cigaba da tautaunawar mana “speak up let me hear you “. “wato kun d’aukemu amatsayin mazinacita ba?shiru sukai gabad’aya sai yusura ce ta samu damar cewar “kayi hakuri sir ai bazamu ta’ba fad’ar abu makamancin haka ba,dan mun san bazaka ta’ba aika haka ba .”taya kuke tunanin bazan iya aikata haka abu makamancin haka da maryama ba ?ai ni mutun bane kamar kowa kuma zan iya “! a matukar tsorace suke kallonsa yayinda mryama ta kasa d’ago idanuta ta kallesa a tun sanda ya soma magana iska mai zafi ya fesar daga bakinsa ya cigaba da magana kusani babu wanda ake jin tsoronsa anan ,saboda daku da ma’aikatan nan abun ikona ne sannan yadda naga dama zanyi daku kuma ko barin aiki kukayi nan sai naga dama zan baku damar yin aiki da kowani ma’aikatan amman bazan nuna maku qarfin ikona ba ,abinda nake son kusani maryama ba mazinaciya bace, ba yar iska bace, hassalima ta fiku kamewa da natsuwa dasanin ya kamata.”




cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa maryama ta d’ago idanunta tana kallonsa tana sauke naunayen ajiyar zuciya zan iya korar kowa acikin kamfanin nan na zauna daita kad’ai ,sannan da zaa tara min duk matan duniya wad’an da zan sheida ita kadai zan cire wani sabon mamaki ya bayyana akan fuskarsu maryama maryama mutuniyar kirki ce and she have especial talent yayi maganar tare da matsowa kusa daita sosai, ban dauka zaku iya mata wannan tunanin ba domin kuwa nayi imani da itace wani acikinku ya samu kanshi cikin halin data tsinci kanta tabbas bazata so taga ya wulakanta ba ,kuma bazaa ta’ba hade kai daita dan a musgunawa wani ba .”
shiru sukai gabad’aya farko tunani ya kamata kuyi mai yasa maryama ta rungumeni mai ya faru daita ba wai ku dauki wannan damar ba dan kuyi mata wulakacin ko kuci mata matunci ko tozarci ba ,kallonsa kawai maryama take babu abinda yake faru haka kawai batare da dalili ba ,kuma nasan kusan haka dan ku ba yara bane ni mai yasa baku canza min ba ,ko dan ita ta kasance mace ne shiyasa kuke jin haushinta har kuje bleming dinta ?ai ni ma yakama kuyi bleming dina kamar yadda kuke bleming dinta . kallosa kawai maryama takeyi har bata son kifta idanunta.”








Mmn Sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.






Page 44




maryama na kwance lamo duk abun duniya ya isheta ahankali ta soma jiyo sautin magana daga parlour’n umma ta yun kura ta mike tsaye daga kwance da take ta soma taku cike da natsuwa tana kusanto parlour’n tana sake jiyo abinda suke tautaunawa akai “na gode maku sosai da yadda kuka mutuntani ,kuka nuna min cewar ina da darajar da zan nemi alfarma a wajenku kuyi min,na gode sosai allah kuma ya shirya mana zuria ,”
babu komai dan wallahi kin wuce haka a wajenmu dan data shegiyar yarinyar nan ce ko uwarta da wallahi komai za’ayi sai kowa acikin dangi yaga wad’an hotun , bama iya nan kawai zai tsaya ba dan hatta jama’ar unguwar nan sai sun gani , duk wani mai ganinta da kima ya daina ganita dashi amman taci darajarki”.inji cewar aunty hasana “na gode sosai sai dai hasana kisani duk abinda kikawa maryama kasani kanki kika yiwa saboda idan sunan maryama ya lalace dole za’a zageki saboda jininki “a’a aunty karki had’ani da wannan mara kunyar yarinyar da bata san ciwon kanta ba .”a qalla sun d’auki mintuna sama da shabiyar suna tautaunawa.” maryama ta fito gbdy daga d’akinta adaidai lokacin da umma ta kar’bi duka hotunan hannunsu ta had’esu waje d’aya su kuma suka mike suka nufi kofar fita ,inda umma ta shiga kitchen ta d’auko ashana duk maryama tana tsaye tana kallonta ta fito ta nufi hanyar kofar baya da alamun kona hotunan zatayi .”bayan wasu mintunan ta dawo inda tayi turus sakamakon ganin maryama tsaye dan kwanaki uku kenan rabon data sanyata acikin kwayar idanunta bata ce mata komai ba ta sake shigewa kitchen ta soma qoqarin d’aura girki .”






Jin motsin umma yayi yawa a kitchen yasa maryama ta fahimci wani aiki take dan haka ta taka ahankali ta shiga a bakin kofar kitchen din ta tsaya tana kallon bayan umma dake wanke tukunya ,numfashi ta sauke ahankali sannan ta soma taku ahankali har ta qaraso cikin kitchen din sosai ta tsaya a gafenta tana cewa “umma sannu da aiki “yauwa !kawai ta amsa mata atakaice kana ta cigaba da abinda take bayan ta gama ta zagaya ta gefenta ta d’aura tukuyar akan gas jikin maryama a sanyaye ta d’auki wuka ta soma yanka mata karas din data gani dan ko bata fad’a mata ba tasan mai zata girka alokacin.”






“ shiru dukkaninsu sukayi sai dai kowannensu zuciyarsa da abinda take tunani ,maryama ta d’an saci kallon umma inda ta fahimci ta d’an soma saukowa daga fushinta, jikinta da muryar ta amatuqar sanyayye ta motsa la’bbanta“umma!maryama ta kira sunanta. umma na jinta amman tayi shiru taki cewa komai duk da tana son amsa mata” umma nah !” ta sake kiran sunanta a tsanake wanan karon sai da tsigar jikin umma suka mike “kiyi hakuri ummah ki yafe min abinda nayi wallahi nayi nadama bazan sake kuskure aikata abinda nayi ba ,nayi miki wannan alqawarin bazan sake ba .”ta qarasa maganar tana danne kukanta tare da juyowa ta fuskanci umma dake tsaye a gabanta bata san sanda ta durkushe kasa bisa gwiwowinta tare da had’e hannuwanta waje d’aya tana kuka tana rokonta “ ki taimaikeni umma bazan iya jurar fushinki gareni ba ,ina jin kamar na kashe kaina bazan iya jurar fushinki ba kina fushi dani haka ma aunty zuciyata tana bani shawarar na kashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login