Showing 84001 words to 87000 words out of 178062 words

Chapter 29 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

a qarshe mutun d’aya na aura wanda ya kasance d’anuwana auren gida aka mana sakamakon matsalolin da akayita samu akan aurena .”




Numfashi da ajiyar zuciya ta sauke atare tana kallonsa “bansan ina sonshi ba sai dana rasashi acikin duniyar nan ,na rasa yaya sadam amman na rasa dalilin dayasa a kullum nake jin tamkar yana raye acikin duniyar nan amman Allah yafini sanin daidai kuma na barwa Allah komai ,duk hukuncin da ya yanke akaina daidai ne “gyara zamansa tare da riko laulausan tafin hannunta "yanzu dai babu kowa sai sultan?”wani kallo ta sake binsa dashi mai d’auke da tambayoyi “yaushe ne kuka fara soyayya dashi ?”shi wa kenan ?itama ta aika masa da nata tambayar “karki rainawa kanki hankali mana amsar tambayata kawai zaki bani “ya qarasa mgnr yana matse hannunta cikin nashi wanda yasa ta dan saki qara mara sauti “ouch!” ahankali ta motsa lip’s tana yatsina fuska tace “yau dai muka fara magana “okay kinji zaki iya fara son shi ?ya sake tmbyrta yana jin mummunar faduwar gaba ”babu wannan maganar araina akwai tarin abubuwa dayawa agabana wanda aure ne zai zamo last .”




Wani boyayyen ajiyar zuciya ya sauke yana cewa “Okay Idan kin san baki tashi aure ba a yanzu kar na qara ganin kin kula sultan ,magana ma ta fatar baki kar ya qara shiga tsakaninku dashi ya qarasa mgnr yana mata tafiyar tsutsa a tsakiyar tafin hannunta tayi saurin zare hannuna daga cikin nasa tana yarfarwa kamar wadda wuta ta kona saboda wani blood rush data ji ya taso daga hannun nata cikin seconds ya zagaye duk sansar jikinta cikin sarkewar murya tace "okay, okay naji "ya lumshe tsumammun idanunshi na second biyu sannan ya bude yana kallon yadda take yarfe hannunta, sake miko mata hannunsa yayi yace "let's shake on that" ta boye hannunta a cikin qaramin hijab dinta tace"na.."na yarda ai, no need to shake kuma" ita fa mugun tsoron maza take bata qaunar nmj yana kai hannunsa jikinta a kullum tahirin mahaifiyarta yana tasiri arayuwarta ta kyamaci rayuwar kuma tana neman tsari da irin rayuwar shiyasa a kullum take jin bazata iya soyayyar waje ba gara tayi aure taso mijinta daga baya .”




“let's shake!”ya sake maimaitawa tai saurin girgiza masa kai ya dage mata girarsa d'aya yana cewa "tsorona kike ji?" ta gyara zaman tace "goodbye sir ta yunkura zata bude kofar stll ta kasa bai san sanda yayi murmushi yace "till we meet tomorrow ".ta fahimci baka ya fad'a mata ba ."shiru yayi yana tunanin aransa anya kuwa maryama tasan nmj kuwa ?” domin duk wasu alamomi na mace ta ta’ba having sex da wani bai gansa à tattare daita ba “kai soko ko tasani taya zata nuna maka wa zai samu kamarta ya tsaya kallon ruwa “amman kuma yadda zawaran wannna zamanin suka da kwarewa a yadda yake mata ai ta saki jiki dashi “sai daya gama jan aikinsa sannan ya bud'e mata murfin kofar ta fita da sauri daga motar tana harhada hanya, but she felt as if gangar jikina ce ta fito daga cikin motar ta bar zuciyata a cikin motar. sai dai tayi kokarin calming down .”






kafin ta karasa gida ta dinga jiyo kamshin sanyayyen turarensa bata kawowa zuciyarta shi bane kasance war taga daga cikin motarsa ta fito wani sanyayyen ajiyar ta sauke kwakwaluwarta na hasko mata kyakkyawar fuskarsa kamar ance ta juyo bayanta kawai taga mutun abayanta juyowa tayi gabad’aya qirjinta na dokawa tayi tsaye Kmr wata mutun mutumi har ya qaraso daf daita yace “muje ko ?da mamaki akan face dinta take kallonsa “muje ko ?ta sake maimata abinda ya fad’a yanzu “suje ina kuma ?ganin bata da niyya ya kai hannu zai rikota tayi saurin janye hannunta tana cewa “dan allah sir ka barni hk zan qarasa gida da kaina nama yi kusa da gidan “nasani ai !”kasani kuma “? ta fad’a fuskarta da mamaki ita kam mutun ne shi ko aljani ?shiru tayi tana kallonsa acikin duhun unguwarsu”yayi kusa daita kamar zai shige jikinta “muje maryama !ya sake fad’a,ahankali ta tattara jarumta tasanyawa jikinta tace “no sir dan… “ke malama banason hauka muje .”ya fad’a yana nuna mata hanya da yatsan hannunsa .”


Mmn sudais[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 24


"Saurin 'bata fuska maryama tayi "dan me zai dinga dangatata da kalmar hauka alhalin ita ba mahauka ciya ba ?"kuma ta lura daga lokacin daya ganta da sultan ne ya sake shigo da wani sabon salon wula kanci ,mr ata yayi bala'in tsareta da ido duk da suna cikin duhu ne amman idanunshi suna iya karantar halin da take ciki sakamakon maganar da yayi mata a yanzu ,cike da tsananin tsoro tace"please sir ka daina dangantani da kalmar haukan nan ina jin kamar na munzanta dayawa " bai ce daita uhm ba bare uhm uhm kawai sai ji tayi ya riko tsintsiyar hannunta da qarfin ya soma tafiya daita, nan take ta turje amman yaki sakar mata hannu dole tasa tace "ka sakar min hannu nayi tafiya da kaina ."yana jinta yayi mata banza tamkar ba dashi take magana ba ."
"acikin unguwarmu muke idan wani ya ganmu haka wata fassara daban za'a mana "ta fad'a tana 'dora hanunta a saman shi a qoqarinta nason zare hannunta, shareta yayi batare da yace mata kala ba sai ma sake damke tsintsiyar hannunta yayi ya cigaba da tafiya "shi ina ruwansa da wasu , ita din tashi ce kuma kome zaa ce akanta zuciyarsa bazata d'auka ba ."








"jin yaki sakar mata hannu yasa jikinta ya fara rawa dan tasan tunda ta bari ya tunzura sai abinda yaga dama zai yi." alhankali muryarta ta fito "please sir kayi hakuri wallahi bazan sake jayayya da kai ba ka sakar min hannu"dogon tsaki yaja yace "wannan kuma problem dinki ne ".bai tsaya daita akoina ba sai daf da bakin get din gidansu sai dai yaki sakar mata hannu ,inda zuciyarta ta shiga tashin hankali mai tsanani da jin tsoron abinda zai biyo baya, dan bazata so wani acikin 'yan unguwa ya fito ya gansu haka, bare wani daga cikin 'yan gidan su. shi kuwa tsura mata ido yayi acikin duhun yana kallonta yana jin kamar ya janyota jikinsa ya rungume tsam tsam!!
maryama bata gama tunaninta ba sai ga fitowar husna diyar aunty hassana daga cikin gida tana waya tana waige waige da alamun wani ta fito nema jin sautin muryarta yasa maryama ta d'an juyo cike da tsoro ,ganin husna yasa wani bakinciki ya tokare mata kahon zuciya wanda yasa hawaye zuba daga idanunta ,da sauri ta dawo da kallonta garesa muryarta can kasa cike da shagwa'ba tace "ka gani ko ."






Shima muryarsa a kasalance yace "me nã gani ?
"cousing dina ce ta fito yanzu "so what ina ruwana da fitowarta ?ko gani tayi ina miki wani abu ? "ba zaka gane abinda nake jin tsoro ba, abinda zai je yazo nake gudu ".tayi maganar muryarta cike da matsanancin tsoro "ki ganar dani zan gane "ya fad'a cike da kulawa yana sake motsata so take taja baya saboda bata són kusancinta dashi amman tana gudun husna ta gane itace tsaye a wajen "menene damuwarki a gidan ?yayi maganar cikin wani irin salo "da sauri ta girgiza masa kai tana cewa "no karka damu kawai sakar min hannuna na wuce "ke matsalarki kenan kinsan bana son taurin kai da jayayya bare kafiya amman a dole sai kinyi min "ya qarasa maganar yana hura mata hucin bakinsa a fuskarta da wuyanta sakamakon kusancin da suka samu saurin lumshe idanunta tayi zuciyarta na wani irin tsinkewa ."yayinda husna tayi shiru tana duban inda suke tsaye sun yi mugun yin kusa da juna wanda bai fi taku d'aya zasu qara jikinsu ya had'e ba . "a fili tace "wacece wannan kamar maryama ?"






"aiko jin haka yasa hankalin maryama yayi matukar tashi tun da take arayuwarta baa ta'ba ganin tasamu kusanci irin haka da wani d'a namiji ba ."ganin husna na qoqarin tahowa inda suke tayi saurin jan hijab dinta ta rufe rabin fuskarta iya bakinta da rabin hancinta ne kawai a waje tun kafin ta qaraso ta ganta taje ta bazawa aunty hasana ita kuma tasamu abun zaginta dashi ."husna na gama qarasowa kusa dasu ta tsaya tana cewa "maryama !" ko ba maryama bace ?" maryama na jinta amman tayi mata banza a zuwan ba ita bace ,shi kam mr ata kallon d'aya yayi mata ya d'auke kanshi ya cigaba da kallon princess dinsa ." ganin da husna tayi ba'a kulata ba gashi wanda take waya dashi yana sheida mata inda zata zo ta samesa yasa ta juya tana taku tana cigaba da wayarta sai dai zuciyarta cike take da wasi wasi akan maryama ce ko kuma wata ce daban tsaye a kofar gidansu amman wani bangaren na zuciyarta yafi amince mata da maryama ce."






sai sanda mr ata yaga dama sannan ya sakar ma maryama hannu tana jinta free ta juya ta nufi cikin gidansu da sauri batare data waiwayo ba ,tana shiga bangaren umma ta nufa tana haki bata iske umma ba da alamun tana ciki tana sallah ta zauna akan kujera ta kifa kanta akan hannun kujera kawai sai hawaye ya soma gangaro mata kukan da bataso tayi akan shi shine ya kufuce mata ba dan taso ba dan hakan ne kawai zai iya sanyaya zuciyarta akan wulakancin da yake mata "yana son ya maida mata jiki banza, babu wani shamaki kawai daya so zai riketa, ita kam sam bazata d'auki wannan wulakanci ba gara tun wuri ta takawa abun burki bazata sake yarda ya dinga ta'bata anyhow ba ,jikinta mai daraja ne ,jiki ne data d'auki tsawon shekaru tana killace abunta bazai yuwu lokaci d'aya yazo ya dinga wasa dashi son ransa ba ,ya hanata saka hijab da nikaf ta yarda amman jikinta kam tana da rowarsa bana ta'bawa bane nã aure ne, tana kuka tana zancen zuci sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru ta shige d'akinta tun kafin umma ta fito ."






Tsaye mr ata yayi a wajen gidansu maryama tamkar wanda aka dasa tsabar mamakin kansa da yake duk yadda yake son ya boye tarin soyayyarta da qaunarta acikin zuciyarsa abun ya cutura har yau gashi tsananin kishinta da son kare lafiyarta da mutuncinta ya kawo shi kofar gidansu a karo na biyu har sai daya ga shigarta cikin gidansu sannan ya samu natsuwa da kwanciyar ahankali ,yana tsananin qaunarta ita kuma tana tsnanin qaunar waninsa . "
"wasu hawaye masu zafi da ciwo ne sukayi nasarar biyo fuskarsa a lokacin daya tuna tun sanda ya fara ganinta a mafarkinsa wanda shine asalin lokacin daya fara jin zazzafar soyayyarta acikin zuciyarsa haka rayuwar take cike da tarin abin mamaki da fari ya d'auka komai da sauki ake samusa ashe abun ba haka yake ba ,abun ba kamar yadda ya taso bane da duk abinda yace yana so ya zama dole ayi masa, idan kuma babu dole sai an nemoshi a duk inda yake an bashi."






Ahankali mr ata ya d'auke kwayar idanunshi akan kwara'babben get din gidan su maryama ,ya juya cike da sanyin jiki, ya soma tafiya zuciyarsa na sake nitso cikin tafkin shaukin qauna da tunani da kyar yake iya d'aga qafafuwansa tamkar wanda bashi da laka haka yake ji a sansar jikinsa inda zuciyarsa ke wani irin bugawa da karfin gaske "wai shine yau acikin irin wannan kwarababbiyar unguwar a karo na biyu ?" a tun tasowarsa idan aka fad'a masa cewar a irin wannan unguwar zuciyarsa zata mace zai karyata wata killa ma sai anyi mugun rigima dashi."
sannan duk tsawon shekaru da yayi yana nemanta bai d'auka daga irin wannan family zata fito ba ,ya d'auka daga gidan mulki ko gidan wani shararren attijira ko d'an siyasa da duniya tasan da zamansa sai gashi zuciyarsa ta tsallake tarin mata bilaadadin masu tarin arziki mulki tattare da boko soyayya tayi wuji wuji dashi ta wullosa cikin wani ahli da ba kowa bane ,bama kowa ne ya sansu ba a iyakar agage ma yayi imani ba kowa ne yasan da zamansu ba ."




a natse ya cigaba da taku yana cigaba da zance zuci still yana jin dinga hawayensa akan kuncinsa shi ba gudun ahlinta yake ko kyamar ahlinta yake ba a'a tsantsar mamaki ne kawai cunkushe a zuciyarsa da tarin iliminsa da tarin dukiyarsa da tarin nasabarsa da tarin nuna isarsa amman Allah ya nuna masa shi din ba kowa bane face bawansa kuma wanda yake qarqashin ikonsa ,ya nuna masa wannan itace irin kalar qaddarar da zai d'aura masa kuma bai isa ya canzata ko ya gudarwa qaddarar dake biye dashi ba ko akan maryam ya kamata ace ya fahimta duk yadda ya kai ga kin yarinyar yadda ya dinga gudun aurenta babu irin qiyayyar da bai nunawa yarinyar ba amman a qarshe sai da allah ya nuna masa shi din bakowa bane ya aura masa ita ya kuma zauna daita a qarshe ga ciki "ya rabbi " ya furta a fili alokacin daya tsoma qafarsa d'aya cikin ca'balbali ai bai tsaya dubawa ba dan yasan zuciyarsa bazata d'auki kallon inda ya sanya qafarsa ba gara ya cigaba da tafiya zai fiyye masa alkhairi da kwanciyar hankali ."






" ya d'auki tsawon shekara shatakwas yana tsnanin sonta shi kad'ai yasan irin wahalar da zuciyarsa ta sha akanta ,babu dare babu rana kullum muradinsa da rokonsa ya ga ko mai kama daita ne a zahiri sai gashi allah ya amsa rokonsa ya had'asu a gaske ai duk yadda maryama take ya amsa koda kuwa zata kasance bata da kowa ,bata da komai bata da galihu kai koda kuwa acikin tsatson bayi ta fito zai 'yantata da ko nawa akace ya maidaita mallakina take wani bangarensa na zuciyarsa yace "tabbas adam kai din masoyi ne tunda kana sonta a duk yadda take "wallahi ina matukar son maryama ya bawa zuciyarsa amsa da haka .bayan mahaifiyata itace abinda nafi só a kaf duniya yana tafiya yana ciza lip's dinsa yana ganin hanya da kyar kasancewar unguwr nada mugun dubu. naunayen ajiyar zuciya ya sauke yayinda soyayyar maryama ke cigaba da kutime meniya da zuciyarsa da gangar jikinsa qaunar maryama ya dinga bin dukkanin sansar jikinsa ji yake kamar ya zarta duk mazan duniya saa da allah ya kwatota a hannun wani ya dawo masa da farinciki rayuwarsa."






" hakika Allah yana son shi domin daya had'u daita da aurenta da lallai zaayi gagarumin tashin hankali dan ko ta kashe auren ta dawo garesa ko kuma ta kasance mai maza biyu amman bazai ta'ba yarda ya barwa wani ita ba ,amamn dake Allah yana son shi da rahma kuma had'uwarsu tana cikin qaddararsa sai ya kashe masa tsohon mijinta saboda shi ya sameta ."Allah kenan yadda yaso haka zai yi inda yayi parking din motarsa ya qaraso da kyar yana kakkabe qafarsa data fad'a cikin cabalbali ".
Mr ata ya iske tarin samarin unguwar dake zaman banza a bakin titi kamar safiya haka yaga wajen kasancewar zuwa wannan lokacin an kunna street light suna ganinsa duk suka matso suna sara masa a hakan ma basu san ko waye shi ba kawai dai kyawun motar daya zo daita ne yasa sukai masa kyakkyawan zato, bud'e motar yayi ya shiga ya zauna sai daya saka seat belt sannna ya d'auko bandir din yan dubu d'aya d'aya guda uku yayi warning glass din motar kad'an ya miko masu yace su raba . nan take ihunsu ya karad'e unguwa wad'an da ya bawa kudin suka shiga bashi hanya suna korar mutane a guje ya figi motar ya hau babban titi yana tunani"yana son dauke maryama daga wannan unguwar amman yana tunanin soyayyarsa ."




"Zai so ya fito mata da zahirinsa amamn kuma jin tsoron tace bata son shi "kai kuwa adam akwai macen da zatace bata sonka ?" Wani bangaren ba zuciyarta ya tambayesa .zata iya cewa bata sona mana tunda zuciyarta da hankalinta yana kan matacce tunda gashi tna mata maganar aure amamn ita ba wannan maganar bane arainta “akwai tarin abubuwa dayawa agabana wanda aure ne zai zamo last .”kwakwaluwarsa ta tariyo masa maganrta tsaki yaja yana sake ganin aurenta a boye shine kawai mafuta agaresa idan yaso ahankali zai koyar daita yadda zata shi fiyye da wancan mataccen ."qarfe shadaya na dare da mintuna ashirin ya tako cikin babban parlour'n mami wanda babu motsin komai da kowa acikinsa sai nã makeken tv bango da ac nan dake aiki ,kai tsaye samansa ya nufa yana furzar da hucin iska daga bakinsa yana shiga ya fad'a bedroom dinsa ya fad'a kan makeken gadonsa yana sauke wani wahalallen numfashi."






Yana kwance mami ta shigo har cikin bedroom dinsa ta tsaya akanshi tana qare masa kallo tsab dottin data gani tun daga step har parlour'n kenan a takalminsa ya kwaso ?” to ina yaje ma har ya kai by this time ?shi da matukar yana gari duk tsanani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login