Showing 75001 words to 78000 words out of 178062 words

Chapter 26 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

shiru itama shiru tayi tsaye tana jiran izininsa yayinda zuciyarta ke dokowa gashi tana hangosa zaune daga cikin amman yaki cewa komai sai tayi kamar ta bude kofar ta shiga sai ta fasa tasan yayi haka ne dan ya samu hanyar da zai kamata da laifi tana tsaye qirjinta nata faman Lugudan bugu dum!dum!”sake knowking tayi da neman izinin a karo na biyu still shiru yayi mata lokacin ma ya soma waya taji zuciyarta ba zata jure ba sai kawai ta bude Kofar ta shiga ta qarasa gabansa ta tsaya still juyi ya cigaba da yi yana waya har kusan mintuna talatin bai kalleta ba ,ta duba agaogon hannunta taga ta bata lokaci a tsaye kawai ta juya tana Kokarin saka kafafunta dan fita daga cikin office din taji sassanyar muryarshi mai tsananin kashe sansar jiki “ke dawo nan "tayi shiru tsaye tana jin zafin abinda yayi mata a yanzu, tasan da mutane sunzo da yanzu hankalinsu da idanusu yana kansu, most especially sultana da bata da buri da wuce taga ya wulakantata sai data rarrashi kanta sannna ta dawo ta tsaya agabansa ta sunkuyar da fuskarta kasa dan wani irin take ji a gabad’aya ilahirin jikinta “.






“Maryama ." ya kira sunanta cikin wani salo mai kashe sansar jiki dagowa tayi ahankali tana kallonshi da shayayyun idanunta masu narkar masa da zuciya sai dai kallo daya tayi masa tavi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta dan bata iya jurar irin kallon da yake mata dan kallo yake mata mai dauke da ma'anoni iri iri daga inda yake zaune yake jin kamar ya mike yaje ya d’ago fuskarta damuwar fuskarta ta damesa matukar baya son ganin fuskarta hk “maryama “!ya sake kiran sunanta a karo na biyu ta dago ta zuba masa shayyyun idanunta tana shirin sake sunkuyar da kanta kasa yace “karki kuskura ki tsaya a yadda kike koni sirinki ne ?”numfashi kawai ta sauke ta cigaba da tsayuwa a yadda yake bukata “to yau kuma me yake nufi daita ?da wani sabon iskanci yazo mata dashi ?”tayiwa kanta tambayar ajire tana sake tsuke fuska “shi daya zo da zumar zuba mata ruwan bala’i amman ya kasa sai ma ya qare a tsura mata kwayar idanunshi masu sata shiga taitayinta ,duk sanda zai daura mata su a jikinta wani irin sanadari ne akwai cikin idanun TARIQ ADAM ABDULLAH masu hargitsa lissafin dan adam kallo daya zai yi maka ka dabarbarce sai kayi da gaske kake samu ka maido natsuwarka so take ta maida kanta kasa dan zai fiyye mata zaman lafiya amman yaki bata damar sai ma hannunsa d’aya ya kai ya dafe gefen fuskarsa yana taune lip’s dinta still kuma kwayar idanunshi na kanta.”






Mmn Sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 22


Mr ata ya tasa maryama gaba da kallo tamkar wani tsohon maye ido cikin ido yake kallonta dan sosai ya sanya kwayar idanunshi cikin nata ai ko tana lumshe idonta sai hawaye sharrr ..”suka shiga gangarowa akan kuncinta,bai san sanda ya mike tsaye ba ya soma taku ahankali har ya qarasa inda take tsaye Ya tsaya yana qoqarin kamo laulausar tafin hannunta cikin nashi tayi saurin zame hannunta cike da jin haushinsa amamn sai da yayi nasara riko yatsun hannunta yana murzawa a hankali tare da hura mata iskan bakinshi a saman fuskarta.”
sun kai minti goma a haka tana hawaye shi bai rarrashinta ba ,shi bai sakar mata hannu ba har sai data gaji dan kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya a jere murmushi yayi aciki yana cewa “kin d’auaka d’an wannnan hawayen zai sa na tausaya miki ,”?” “yarinya baki san adadin hawayen dana zubar akanki ba ,baki san kalar wahalar dana sha akan zafin soayyarki ba ,baki san tashin hankalin da dana shiga akanki ba, nayi kuka nayi hauka duk akanki a qarshe har aka so a d’aukeni mahaukaci alokacin da nake jin cewar kina cikin duniyar nan amamn aka nuna min ke din iya mafarki ce ,wannan wahalar kad’an ce daga cikin wahalar dana sha akanki maryama dan kukan dadi kike yi a yanzu tunda kina dani .”






Office din ya d’auki shiru bakajin motsin komai sai na saukar numfashinsu wanda ke sake haddasawa zuciyar maryama shiga tashin hankali yayinda shi kuma zuciyarsa ke narkewa akanta gabad’aya marayama a matukar rikice take dan bata qaunar kusancinsu haka, dan ma Allah ya taiamketa har zuwa lokacin sauran abonkan aikinta basu qaraso ba
batayi tsammanin zai yi magana dan a tunaninta a haka zasu tabbata sai kawai ta jiyo muryarsa a kasalance “menene dalilinki na barin office jiya ?”kamar tace masa takurawarsa ce tayi yawa sai ta share tace “am very sorry sir jiya kaina ke ciwo “tana fad’ar hk ya sakar mata hannu yana cewa” I hate lies “ya fad’a yana jan tsaki .”nan take ta diririce “shi kuma wayarki me yasa kika kashe ?“saboda matsalar wuta ne “ta bashi amsa da haka bakinsa ya ta’be “daman yaushe zaa samu natsuwa a wannan banzar unguwar taku, kiyi qoqari kiyi aure ki bar wannan banzar unguwar “kamar tace masa unguwarsu ba banza bace dan duk lalacewarta tayi wa rayuwarta amafani ,kuma ta rufawa ahlinta asiri na tsawon shekaru amamn saboda alqawarin data d’aukarwa kanta na bazata sake yin abinda zai hassalashi ba saboda abincinta dake qarqaahinsa yasa ta sauke nunfashi kawai tana jin quna aranta dan taji zafin mgnrsa amman bata da zabin daya wuce tayi shiru .”






"new design dinki sunyi ready "?new desing kuma ?ta tambayesa zuciyarta na rawa dan ta manta da wani batunsa Kallon da ya dauketa dashi ne yasa tayi saurin cewa "yes ready ready sir” good kije ki kawo min yanzu na gani yana gama fadar haka ya juya ya wuceta ya fita daga office din ta juya a natse tana kallon bayansa tana sauke wani naunayen ajiyar zuciya tare da lumshe idanunta “kai wannan mutumin zai iya kashe mutun da ransa .”
ahankali ahankali take d’aga qafafunta tana kallon tafiyarsa, tafiyarsa ma abun burgewa ne har sanda ya shiga wani office dinsa yana shiga ya d’auki wani file green ya fito ya sake shiga office din daya baro ya zauna ya d’aura kafarsa d’aya akan d’aya .”
tana fito da desing’s din tana mita “wannan mutumin mugun dan rainin wayo ne cewa yayi babu ruwansa da wani new designs din da zaayi yanzu kuma yazo yana tmby dana yagasu dana shiga uku ko kuma da nice nayi masa magana da yanzu yau ni da maseefa, takardu ta rike ta fito zuwa office dinsa ta nemi izinin shiga ya bata izini ta shiga ta qarasa daf dashi ta tsaya tana dubansa yana duba file .”can ya ajiye sakamakon kiran wayar office dinsa da akayi ya amsa kiran.”




ta cigaba da tsayuwa can ta duba agogon hannunta byn ya gama ya ajiye wayar yana dan waigo inda take fuskarta ahade da alamun jin haushi muryarta a dake tace” Mr ATA sir !” ya sake tsura mata idanu alamun yana saurarenta”a sanina baka zuwa office da wuri amman me yasa jiya da yau kazo da wuri ?a d’an tsorace yace “why are you asking me foolish question?ya qarasa fad’a tsawace yana mika mata hannunsa alamun ta bashi desing din ya gani zuciyarta a dake ta mika masa a hankali ya kar’ba ya fara budewa yana kallo zanen mace ce sanye da doguwar riga da abun hannu da sarkar wuya yayinda take tsaye a gefensa tana ciza harshenta ya dan waigo kadan ya kalleta ya dauke idanunshi ya sake maidawa kan desing din hannunsa.” byn second goma ya ajiye ya dauki dayan takardar zane zane ne masu matukar kyau da daukar hankali ta zana ta sake kai dubanta ga agogon hannun
“wannan dabia nata na mugun bashi haushi ita da bata bawa lokaci mahimanci sai yaransa uwar me take dubawa a agogo ,yaja tsaki yana shafa sajen fuskarsa sannan ya dauki pencil ya daura akan takardar zanen tana ganin hk tayi saurin cewa"sir what are you doing?




kallon da yayi mata yasa tayi kasa da muryarta sosai "sir idan akwai abinda bai yi maka ba kamata yayi kabari na gyara da kaina ba sai ka wahalar da kanka ba ,ta fad'a tana kokarin kwace takardar ya hana akwai abinda bai min ba a desing din kuma zan gyara any problem?"No sir !ta fad'a ba dan ranta yaso ba can tace “amman shekaranjiya da mukayi magana akan plan dinmu kin amincewa kayi amman kuma me yasa yau kayi mgn akanshi "bana son yin mgn akan abinda ya wuce yanzu zamuyi aiki ne ko kuwa tmby zaki kasheni daahi ?numfashi ta sauke tace “ muyi aiki “ta fad'a am tana d’auke kanta .”
"your design are very nice but there's something mistake kina bukatar taimakon irinmu kafin ki zama expect, nan take ya shiga mata bayanin abinda zatai tasa hannunta acikin bakinta ta dan ciza tana lumshe idanuwa wanda kadan ya rage mr ATA bai sume ba gabadaya yanayinsa ya sauya hatta tsigar jikinsa sun tashi, allah dai ya tamaikesa sanye yake da suit da babu abinda zai hana bata gani ba ."






Yadda yake mata bayani itama batayi sanya agwiwa ba ta shiga yi masa bayani tana juya hannuta da kwayar idanunta ta a qarshe ta saka yatsan hannunta cikin bakinta duk sanda tayi haka sai yaji wani iri yerrr ajikinsa kuma ya lura dabiar ce haka ya mike tsaye daga mazauninsa ya qarasa inda wasu manya takardun zane suke ,ya dauki guda daya ya bude yana dubawa har ya taho gareta ya tsaya kusa daita yana nuna mata kokuwa tashiga yi da numfashinta dan kamshin turarensa mai tsuma zuciya da gangar jiki ne irin turaren da nmj yayi amfani dashi yazo gareka babu tantama zaka iya sakar masa ragamar rayuwarka ,ta dan kallesa tana yatsina fuska bayan wani lokaci ya rufe ya ajiye ya amshi takardar hannunta ya bude yna nuna mata bayanin abinda zatai wanda zai sake sakawa ta dauki hankalin client yana gamawa ya nuna mata kofar fita da hannusa sannan ya koma mazauninsa.”




ta fara tafiya a hankali tana cigaba da kallon takardar hannunta yayinda aranta tana sake mamakinsa wani irin juyayyen hali garesa idan mutun bai da tsananin hakuri bazai ta’ba jin dadin zama dashi “Ko me ta tuna sai ta juya ahankali nan take kwayar idanunsu ya tsarke cikin juna dan shima bayanta yake kallo dayar takadarta dake kan table dinsa ta nuna masa ,ya dauka ya mika mata ta sake juyawa shi kuma ya gyara zama yana cigaba da kallon yadda take bada step ."bayan kmr minti goma ta sake shigowa "sir dan allah ko zaka taimaka min ina son nayi aiki amman kayan aikin duk suna cikin wancan durowa din nayi nayi na bude na kasa ko zaka taimaka min dan Allah ?shiru yayi yaki cewa komai "please sir !"okay ya mike yayi gaba ta biyo bayansa har zuwa office dinsu ta nuna masa durowan da hannunta ya qarasa cike da kwarin gwiwa yaja sai dai ya kasa budewa.”




ya waigo ya kalleta ta hade fuska tamau tmkr wacce bata ta’ba dariya ba tana ciza harshenta dan daman tana sane ta bashi aiki ,shi kullum bashi da aiki sai zama Kan kujera yana amsa waya da zarar kayi mistake ya kiraka da nonsense,stupid ,ko sai gama shan wahala kayi aiki yace bai masa ba .”ya sake ja still the same ya saka iya karfinsa ai ko yana já durowar ya bude shi kum yayi baya zai fado kanta itama tayi baya luuuuu yasa duka hannuwansa yayi mata riko mai kyau batare daya sani ba hannuta ya sauka akan daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da mahaukacin qarfi shima hannunsa daya ya rike tsintsiyar hannunta dake rike da zane dayan hannunsa kuma ya zagaye kungunta dashi .”




ido cikin ido suke kallon juna yana kallonta cike da tsananin soyayya yayinda ita kuma abun ya zame mata bakon alamari dan tunda take hakan bai ta faruwa daita ba, hasalima kullum cikin hijab da nikaf take shine silar canza mata rayuwa sun dade tsaye suna kallon juna yana kwakume daita jin saukar tafin hannunsa a gefen fuskarta yasa ta dawo haiyacinta da sauri ta zare jikinta tana juya masa baya tare da rungume takardar aqirjinta tana jin wani irin kasala ajikinta numfashi ya sauke yana kallon bayanta kafin ahankali ya tura hannunwansa duka cikin aljihunsa muryarta a matukar sanyaye ta furta "am sorry sir ?babu abinda yaji hakan ma dadi yayi masa .”




ta juyo ta sake bude bakinta zata sake furta masa am sorry "ki zauna Kiyi aiki dake gabanki “ ya fad'a yana juyawa ta lumshe idanunta, ta zauna masa dariyar mugunta ai taso ya kasa ne ,tana cikin aiki ya sake shigowa hannunsa rike da cup biyu ya ajiye mata a gabanta ta dago ta kallesa a natse da shayayyun idanunta "coffe !
"Thanks “. kawai ta fad’a atakaice taso tace masa bata sha sai dai tayi shiru zuciyarta cike da mamakinsa yau din kamar bashi ba ta cigaba da aikinta a natse ya dinga tafiya acikin office din yana kurban coffe yana lumshe idanun har zai wuce yaga bata da alamun shan coffe "me yasa bazaki sha coffe ba ? ya fad’a domin a tunaninsa tunda tazo da sanyin safiyar nan ba lallai ta karya ba sai data yatsina fuska tace “ bani da raayin shan abu a waje bare abun hannun nmj ba kuma dan rashin yarda bane raayi ne kuma ma I don't like drinking coffee ai kamar na fad’a maka last time .”




shiru yayi yana kallon qaramin bakinta komai nata dabam ne da sauran mata ya koma bakin kofa ya tsaya yana rike da kugunsa yana kallonta ta maseefar burgesa "maryama !ya kira sunanta cikin wata irin murya mai kashe jiki” yes sir !” ta amsa ko zan iya sakaki wani aiki ?why not sir “ta fad'a ya ajiye cup din hannuna yace biyoni ya fita zuwa office dinsa ta biyosa ya mika mata wani jaka mai shegen kyau "ta karba ta bude taga kaya ta tsaya tana dubansa da jakar hannunta "ki bude ki gani?”




batai mutsu ba ta bude ta fito da kayan ciki doguwar riga ce wacce akayiwa aiki da stone tun daga sama har kasa "ko zaki gwada naga yadda zai yi ajikinki ?da sauri ta tsura masa ido tana kallonsa da mamaki"
Muryarta cike da tashin hankali tace “but sir !"Kar dakikiyar kwalkwaluwarki ta kawo miki wani abu matata na siyawa "sir tunda matarka ka siyawa ai kamata yayi ka kai ma.."Ke nake son ki gwada ajikinki na gani so kije kiyi abinda na sakaki ga daki can ki shaga karki bata min lokaci jiki sanyaye ta wuce tana yatsina face ta murda handle ta shiga .
"shi kuma ya dauki cup din coffee dinsa ya shiga sha yana kai kawo .”




Byn wasu mintuna ta bude kofar ta tsaya batare data fito sosai ba ta hade hannunwanta waje daya tana jin faduwar gaba kafin daga baya ta soma taku a hankali ya ajiye cup din hannunsa tun daga sama ya dauki kallonta har kasanta ahankali ya zuba hannuwansa cikin aljihunsa yana cigaba da kallonta kafin a natse ya qaraso ya tsaya abayanta yana sauke numfashi sannan ya cire hannunsa daya acikin aljihunsa ya ta'ba kayan a hannunsa yana dubawa can taga ya dauki takarda yana rubuce rubuce yana mata bayani ina bukatar zanen mace da irin wannan kayan har komai da komai exactly ta tsura masa ido tana masa wani irin kallo "ko bazakiyi ba ?.




Jikinta a sanyaye tace “zanyi!” só sai kije ki fara ya gbdy ta kasa magana kai kawai take gyada masa dan yanayin da take ji ajikinta babu sauki yanayin da bata ta’ba jin irinsa bane ,ya sake yin taku biyu yayi kusa daita sosai ya kai kansa daidai saitin wuyanta yana sauke mata numfashinsa a wuya ya motsa bakinsa a hankali "mar ..."sautin muryar sultana ta katse masa hanzari ..."cak ta tsaya mamaki qarara kwance akan fuskarta tana dubansu , jikin maryam yayi sanyi sakamakon matsananciyar kunyar data rufeta, ta dan saci kallon sultana ta kasan idanunta taga irin kallon tsanar da take mata mai cike da tsantsar kishi ."






mr ATA bai kalli inda sultana take tsaye tana kallonsu da mamaki ba ya bawa maryam umarnin kije ki cire kayan "good morning sir “! amman me Ke faruwa haka ?ya lumshe mata tsumammun idsnunshi yana sauke numfashi sai maryama ce tayi mata bayani dan shi bashi da lokacinta "you could have called me ya Adam I can do more than this for you ,ita nayi raayi ta min any problem?amman me yasa sai ita bayan gani dana kasance jininka ?ya ma akayi kuka kasance tare adaidai wannan lokacin ko tare kuka zo ne? gaban maryama ta rikice ta dinga jin wani irin mummunar fad'uwa gaba yayinda jikinta ya dauki rawa ta kasa motsi bare taje ta cire kayan jikinta shi kuwa wani irin mugun kallo yayi ma sultana sannan ya wuceta zuwa mazauninsa batare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login