Showing 15001 words to 18000 words out of 178062 words
Chapter 6 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt
meet tabawa idan zamu wuce zan kaiku ku ganta shikenan tashi sukai suka wuce rike da hannun juna yayinda ata ya bisu da kallo yana lumshe ido yana jin ina ma yaransa ne .”ahankali ya bude idonsa yana motsa lips dinsa “shikenan sweetheart komai ya wuce amman gsky ban so na sauko hk da wuri ba har sai bayan shekaru masu yawa “Au yanzu nan ka sauko da wuri kenan wajen wata biyar ?ya lumshe mata tsumammun idanunshi kawai kallonsa zabiba tayi cike da tausayawa tace “allah dai ya huci zuciyar babban yaya in sha allahu bazamu sake ba “kuma sake ya fad’a tare da mikewa ya nufi kofar fita yana cewa “sweet heart sai nã dawo “bazaka karya bane ?bana jin cin komai sai dai na dawo kawai “to a dawo lafiya Allah ya tsare “Ameen !” ya amsa ya nufi kofar fita .”
kai tsaye hanyar kamaninsa aka nufa dashi yana zaune hannunwansa rike da jaridar daily trust yana karantawa yana son wani abu ya d’auki hankalinsa na son kawar da tunanin maryama acikin ransa amman aikin banza yayi domin duk shafin da zai bud’e sai fuskarta sai ta bayyana aciki wani dogon tsaki yaja ya ajiye jaridar hannunsa ko da yake shima yasan dole abun zai damesa kuma zai hana rayuwarsa sukuni har suka qarasa office dinsa tunaninta ne fal acikin zuciyarsa bai dade da zama ba sai ga some ta shigo bayan ta nemi izinin shigowa wasu file ta ajiye agabansa cike da girmamawa tace "sir ana bukatar saka hannunka anan” bai ce mata komai ba ,ya kar’bi biron data miko masa batare da bata lokaci ba duk ya sign ta kwashe file din ta fice tana satar kallonsa dan da alamun yana cikin damuwa duk da dai ko yaushe fuskar nan tashi a hade take amman na wannan karon ya zarta na sauran lukuta har tayi taku biyu sai kuma ta juyo ahankali ta dawo inda yake zaune ya d’an d’aga kwayar idanun shi ya kalleta sannan ya d’auke idanunshi “sir ko zan iya cewa wani abu ?shiru ya biyo bayan mgnrta na second biyar sannan yace “zaki iya “sir yau yanayinka yayi wani iri Kmr akwai wani abu dake damunka “yes akwai abinda ke damuna wanda nake jin kamar na kashe kaina .”
”what ?ta fad’a tana zaro ido kafin ta sake mgn yace “you can leave shiru tayi tana dubansa rike da file ganin haka yasa ya janyo wasu file gabansa ya shiga dubawa duk a qoqarinsa nason ya manta da komai alokacin amman ya kasa duk shafin daya bud'e still dai hoton fuskarta yake gani tana hawaye cikin mummunar tashin hankalin data bar office dinsa jiya ."tsaki yaja yana dukan table din gabansa da karfi “what’s all nonsense ya fad’a yana mai rike goshinsa da hannunwansa duka yana jin wani irin zugi from no where”ke kuma tsayuwar me kike yi ?yayi mgnr a tsawace da sauri ta nufi kofar fita cikin zafin zuciya ya zabura ya mike tsaye ya fara zariya acikin office kafin ahankali ya tsaya cak a tsakiyar office yana dogon nazari kusan minti goma yana tsaye yana qoqarin nemawa kansa mafuta domin dole ya nemowa kanshi mafutar da zai rabu da tunaninta gabad’aya ya huta saurin waiwayowa yayi sakamakon jin sautin muryar ammar a bayansa .”
Bai ce masa uffan ba yaja wani dogon tsaki yana mai d’auke kwayar idanunshi akansa cike da jin haushinsa domin a yanzu ya gane shine ma damuwarsa ,shine mutumin daya bari ya rasa duk wani farincikinsa duk yadda yasan halin da yake ciki amman yana ji yana kallo yarinyar nan ta zama mallakin wani bashi ba .”
ahankali ata ya kasa dauke tsumammun idanunshi daga kan ammar yana jifansa da wani mugun kallo mai d’auke da fassara dabam dabam ahankali ammar ya dawo gaban ata ya tsaya yana kallonsa kamar yayi dariya amman sai ya share saboda ganin fuskar ata din har lokacin tana cikin yanayi na damuwa da tashin hankali wanda kuma yasan na rasa maryama ne shima ata kallonsa yake amman kallon tsana ammar ya saki fuska yana murmushi wanda bashi da maraba dana mugunta “mamaki murmushin ammar ata yake wato ya cucesa kuma yazo ya tasa shi gaba da murmushin mugunta ?sai da ammar ya bashi wasu mintun sannna ya fara magana “haba friend kar dai maryama ce ta gigita rayuwarka haka ?bai kulashi ba sai ma sake had’e fuska da yayi sannna ya juya ya bar wajen “cikin daga murya ammar yace “daman nasan sai tayi wuji wuji da rayuwarka tasa ka fad’i kasa warwasss cak ata ya tsaya yana cizan lip’s dinsa kamar yayi masa mgn sai km ya cigaba da taku ya nufi d’akin dake cikin office wata dariya ta subucewa ammar alokacin da ata yake qoqarin shigewa d’akin bai san sanda ya juyo a fusace yace “kai me kake nufi ne wai dani ?”
“Oho abinda kake nufi nima shi nake nufi yana daga inda yake ya girgiza kai had’e da cewa “ka shiga hankalinka ammar da wannan dariyar da kake “na shiga hankalina ko dai ka shiga hankalinka ina ta faman kiranka a waya tun jiya kaki dauka yanzu kuma nazo ina ta mgn ka min shiru sai faman cika kake kana batsewa “idan dan abinda ya faru ne kake fushi kayi hakuri amman dai yanzu abar duk wannna maganr nazo maka da wata magana ne mai mahimanci .”a wulakance ata yake kallonsa tare da cewa “bana bukatar komai daga gareka coz I hate you !I hate you ammar ganinka da maganarka babu abinda yake qara min ayanzu illa jin bakinciki da tarin tsanarka acikin zuciyata.” da sauri ammar ya matso kusa dashi yana qoqarin riko hannunsa yay saurin ja baya “don’t try me ammar! ya fad’a a matukar fusace ammar bai damu ba dan yasan halinsa ya matso sosai yana dubansa “wallahi ammar ka cuceni ,ka cuci rayuwata bazan ta’ba yafe maka abinda ka min ba sakamakon kasan duk wata damuwa dake tattare da shafukan rayuwata akan yarinyar nan amman dan mugunta irintaka ka cutar da zuciyata, yarinyar da zaka d’aukota musamman ka kawo min ita nayi tozali daita ba wai ka tsaya yi min wasa da hankali ba wallahi ka cutar dani ammar gashi har wani yayi galaba aureta “.
ka tsaya kaji mai zance maka yanzu “bana son jin komai ammar macuci mugu kawai mai bakar fuska ya fad’a yana hadashi da wani kyawawan mari. duk wannan maganar a zuciye yake yi yana cewa “get out from my office I don’t want to see your face again tare da point dinsa da hannusa kana ya cigaba da magana kamar zai zubar da hawaye” dan iska kawai da kai mai zaka fad’a ?bayan ka gama lalata min rayuwa sannna kazo kana cika ni da surutu banza da wofi “Adam ni ka mara ?an mareka wallahi idan ka cika da surutu zan qara maka kuma babu abinda ka isa kayi banza mara mutunci maci amanar abota wallahi ka gama cutata “enough ata bafa tsoronka nake ji ba na cuceka ko ka cuci kanka ?”ya fad’a tare da jan tsaki “.“Oh haka ma zakace kenan “?kenan har yanzu kana da karfin halin cigaba da bata min rai ?wai tsaya ma na tambayeka kai masoyina ko makiyina?”duk matsayin daka bani na kar’ba “okay na baka matsayin makiyina domin duk duniya kaine makiyina na farko kuma na tsaneka fiyye da tsanar da nayi maka daga yau ammar babu ni babu kai ka cire ni acikin duk wata danganta amman kafin nan zan shiga ciki dan girman allah ka cigaba da tsayuwa har na fito kaga yadda zanyi da kai yana gama fad’ar haka ya juya yana sauke numfashi sama sama .”jiki a sanyaye ammar yake kallon kofar daya shiga kamar ya shiga amman yasa shigarsa bazai haifar masu da mai ido ba kuma bazai sauraresa yaji abinda ya kawo sa ba cike da zafin zuciya ya fice .”
*******
Da sauri maryama ta shigo dakinta dake bangaren mahaifiyarta kunneta manne da waya ta qarasa inda kayan aikinta yake ta dauki biro da joter adaidai lokacin da mahaifiyarta ta shigo tana daukar kayansu dana habib zata hada cikin kayan wanki da sauri ta zagayo cike da farinciki ta daura joter akan gadon bayan mahaifiyarta ta soma rubutu tana cigaba da amsa kira “okay!!Ina jinka okay na fahimta shikenan zan tura muku da irin nawa kugani thank thank so much “.aunty ta mike rike kayan tana dubanta itama maryama dubanta take fuskata kunshe da dariya “Kinsan wani abu ?aunty ta girgiza mata kai itama fuskarta cike da farinciki “na samu aiki a alico insurance ta fad’a tana rungumeta ajikinta nan da kwana hudu zan fara aiki dasu “kin gani ba ai daman na fad’a zaki samu wani da yarda allah kofar allah ai tana da yawa in sha allahu daga wannan nasara kin dinga samu nasara kenan arayuwarki domin adduata tana tare daku akoda yaushe na gode sosai mumcy tana sake makale wa ajikinta tmkr yarinya.” karki damu princess maza kije ki fadawa ummanki nasan zataji dadi “okay bari naje wallahi zataji dadi sosai ta dauki qaramin hijab dinta ta saka ta fice .”
Mmn sudais
[8/31, 11:24 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 65
Numfashi ya sauke ya koma ya samu guri ya zauna a kan kujera yana jujjuya jikinsa gabansa na wani irin bugawa da karfin gaske haka nan yake jin zuciyarsa na matukar jin tsoron abinda zai faru yayinda a hankali maganganunta na jiya da sukai waya da some ya dinga dawo masa daki daki " na tsaya naji nayi miki me ?me ma kuka d'aukeni shasha wacce bata san ciwon kanta ba ?"kunsan zaku bukaceni me yasa kuka wulakan tani?"ya runtse idanunshi gam yana jin matsamanancin tashin hankali "wannan yarinyar fa da gani rigimammeya ce ."ya furta a fili qirjinsa na lugud'en bugu alokacin da maganarta ta sake yi masa kuwa acikin kunnuwansa da zuciyarsa ".sorry for what?, wallahi ko duk duniya za'a bani a wannan kamfanin babu ni babu wannan kamfanin har abada "shi wannan mutumin a wajenki yake da mahimanci amman a wurin maryama zero ne ,dan haka tun wuri ku nemi wata amman ni har abada bazan sake dawowa AGC company ba ".
Wani irin zufa ne ya shiga tsatsafo masa akan hancinsa da ilahirin jikinsa ,ahankali ya kai hannu ya lalubo wayarsa ya soma binciken unguwar da take domin dai yana bukatar yaga yanayin tsarin unguwarsu "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ya furta a fili yana mai sake tsurawa wayarsa do tagumi yayi da hannu d'aya yana tunani irin rayuwar da mutun zai yi a irin wannan bazar unguwar numfashi ya janyo da kyar ya sauke sannan ya soma neman layin mb yana d'agawa yace "kazo yanzu yanzu ina AGC yana gama fad'ar haka yayi discounting din kiran ya kira salim da ammar."yayi baya da kujerar da yake zaune yana ciza lip's dinsa da qarfi babu abinda yake gani acikin kwayar idanunshi sai kyakkyawar fuskarta mai mugun kyaun gaske da yanayin jikinta tana rayuwa acikin unguwarsu imagenation dinta kawai yake tun daga qarancin shekarunta har zuwa sanda ya fara daura kwayar idanunshi akanta ,yanayin tsayinta da dogon hancinta shine yafi komai fito da ainihin sahihin kyawunta da Allah yayi mata ya numfasa yana sake lumshe tsumammun idanunshi "hakika maryama iyayenki sun iya haihuwa tunda suka haifa muradin zuciyar Adam .”yana cikin wannan halin sai gasu ammar sun bayyana a gabansa ."
SALIM ,AMMAR ,M.B duk suka zuba masa idanu suna kallonsa fuskarsa a sukwane kuma d'aure take kamar ko wani lokaci sai dai kallo d'aya sukai masa suka fahimci akwai abinda ke damunsa duk suka samu gurin suka zauna sukai shiru suna jiran suji abinda zai fad'a masu."ahankali ATA ya lumshe tsumammun idanunshi tare da sanya hannunsa d'aya adaidai saitin qirjinsa yana murza daidai inda zuciyarsa take beating very fast bayan kamar second goma ya ware tsumammun idanunshi sosai akansu yana kokawa da lamarin princess dinsa saka makon matsayinta daya fahimta domin duk a tunaninsa bai d'auka zata fito daga irin area daaka fad'a masa ba ,ya d'auka zai ganta acikin royal family ne ko wani babban attajirin ne mahaifinta sai a yanzu ne ma ya fahimci bayan mugun abinda take rufe fuskarta dashi har da ma unguwar da take rayuwa aciki ya janyo rashin had'uwarsu .wani abu ya had'iye mai d'aci daya tsaya masa a mak'oshinsa kafin ahankali ya mike tsaye ya tsaya ajikin bangon office din tare da tura hannuwansa duka cikin ajihun wondonsa ya tokare qafarsa d'aya da bango yana cigaba da dubansu kamar zai yi kuka cikin kasa da murya ammar yace "Adam ya'akayi ne ?ka taso mu daga kan ayyuka masu mahimanci meke faruwa ?meye dalilin taramu dakayi ?ammar yayi masa tamvayoyin a jere duk da jikinsa ya bashi akan maryama ne dan idan akan kasuwancinsu ne bai zai nemi har da mb ba dan meye had'in soja da kasuwanci ."
"kasani ammar! "ata ya fad'a yana kokawa acikin ranshi "kasan dalili kiranku ammar amman kafin nan nasa some ta kira yarinyar nan jiya amman gabad'aya kalamanta sun nuna bazatayi aiki dani ba, amman ni ba wannan bane damwta ." meye damuwarka ata ?"mb ya tambayesa cike da kulawa "sai da ata ya sauke wani naunayen ajiyar zuciya sannan ya motsa lip's dinsa "wai princess dinace tayi rayuwa a irin wannan banzar unguwar ."yayi maganar cike da tsananin fushi yana zare hannuwansa daga cikin aljihunsa yayi taku d'aya biyu sannan ya tsaya cak atsakiyar office din tare da juya masu baya "gyaran murya salim yayi kana ya fara magana cike da sanyin murya "to meye aciki Adam kowani bawa ai da irin tasa kalar qaddarar "a ina take zaune ne ammar ?"inji cewar mb yayi tmbyr yana duban fuskar ammar ". "tana zaune ne a unguwar gwagulori "ina ne haka kuma ?""wata geto area ce acikin agege local government "cewar ammar "kunji abinda naji kuwa acikin zuciyata kamar ni Adam tariq Abdallah ace matar da nake haukar so ce tayi rayuwa a irin wannan banzar unguwa wani irin rayuwa ma tayi ?"gidansu ne ko haya suke yi ? Ata yayi masa tamvayar yana dungule hannunsa ya kaiwa bango naushi .da mamaki gabad'ayansu suka mike tsaye cikin tsananin tashin hankali suka qaraso inda yake suka rikesa suna kiran sunansa "what's wrong with you Adam ?" gabad'aya suka had'a baki wajen fad'ar haka."ka natsu mana ."
Shiru yayi kawai yana fesar da numfashi da iska mai zafi daga bakinsa gbdy yanayinsa ya canza zuwa na tsananin damuwa, fixge hannunsa yayi yana shafa daidai qashin hannunsa daya bugu yana watsa ma ammar wani mugun kallo .da sauri ammar ya d'auke idonsa saboda mugun tsoro daya kamasa ya koma ya zauna ."mb ya kallesa cike da tausayawa domin dai ya fahimci tausayi ne mai tattare da tsananin son da yake mata yasa shi shiga damuwa janyosa yayi ya zaunar dashi yana cewa "ka kwantar da hankalinka Adam haka rayuwa take kai a tunaninka zata zamanto diyar wani kamar yadda ka kasance to shi Allah ba haka yake son ganinta ba sannan ba hk tsarinsa yake ba ,ganin damarsa ne ya hada masoya masu wadata waje d'aya haka ganin damarsa ne ya hada talaka da mai arziki ." nasan kasan dukkanin rayuwa rubutaccen lamari ne daga rabbi yadda yaso haka zai yi ,saboda haka kasan duk wannan mai sauki ne a wajen Allah fatan mu yarinyar ta amince da soyayyarka tun da ka rigada ka gano Inda take .”
shiru ata yayi ya fad'a kogin tunani sosai hankalinsa ya bar duniyar da yake ya lula dashi can duniyar maryama inda zuciyarsa ta shiga hasko masa ita tare da wani tana rayuwar aure daahi . wani dogon tsaki yaja yana sake taune gefen bakinsa da qarfi saboda zafin kishin da yake ji hakika idan yace yaji dadin kasancewarta a bazawara yayi wa kanshi karya yaso ace shine mutun na farko da zai fara muamula ta aure daita bawani katon bazan can ba "Adam ka daina zurfafa tunani da yawa akanta tunda already kasan ta ta'ba aure ,tunda ta ta'ba aure kasan dole wani abu zai shiga tsakaninta da wanda ta aura ita kad'anta kake so kuma ko a wani hali take zaka kasance daita ." "jin an dafa kafad'ansa yasanyashi sauke kwayar idanunshi akansu "ba shiga damuwa ko dogon tunanin zaka tsaya ba abinda ya kamata kayi yanzu ka gaugauta aurenta domin ka inganta rayuwata kayi ma iyayenta duk abinda kasan ya dace ."inji cewar mb "Allah kad'ai yasan irin rayuwar datayi acikin wannan banzar unguwar mb ku duba map kuga yanayin tsarin unguwar datai rayuwa aciki inna ilaihi "ya sake furtawa yana yarfe hannu alamun abun na masa ciwo ".kai yanzu meye damuwarka da unguwarsu ? unguwarsu kake so ko ita ?"salim ya tambayesa wani kallo yayi masa yana fesar da huci yana sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri." rabu dashi salim dan ma bai shiga lungun unguwarsu bane yasa yake fad'ar haka ."wani sabon zufa ne ya karyowa ata yayinda salim ya barke da wata irin dariya yana cewa "ai daidai kenan kamuwa da soyayyar yar talakawa zai sa wasu abubuwa su..."wani mugun kallo ata ya watsa masa wanda yasa salim yayi shiru yana kunshe sauran dariyarsa "ba hararar mutane ya kamata kayi ba kayi maza kayi abinda ya dace ku fahimci juna da yarinya ka aureta kafin wani yazo yayi maka shigar sauri "wannan duk ba matsala bane zan yi duk yadda zanyi ta dawo