Showing 66001 words to 69000 words out of 178062 words

Chapter 23 - MAR ADAMS BOOK 3 COMPLETE BY AYSHA BAGUDU.txt

ta dinga massaging qafafunta tana mata sannu umma tayi shiru tana jin tsananin qaunar maryama aranta amman wani lokacin sai ta dinga jin tamakar zata juya mata baya wata rana ,domin d’an wani da uwar wani sai Allah duk da dai tana mata kyakkyawan zato haihuwa na dadi amman haihuwar da tafi kowace dadi itace haihuwar diya mace tasan koda sadam dinta yana raye watan wata rana sai taji kewar rashin haihuwar diya mace sheshekan kukan umma ne yasa maryama ta bar abinda take ta dago a gigice tana cewa “umma lafiya ?” ai sai umma ta fashe mata da kuka hankalin maryama yayi matukar tashi duk ta rude ta sake bajewa daga tsugunon da take a gaban umma ta riko hannunta cikin nata itama idanunta sun cika da hawaye dan haka kawai bata ta’ba ganin umma tana zubar da hawaye ba lallai duk abinda ya sakata zubar da hawaye abu ne mai girma “dan girman allah umma kiyi hakuri ki daina kukan “ko kin tuna da yaya sadam ne ?”






Umma ta sauke wani ajiyar zuciya tana damke hannun maryama cikin nata cikin muryar kuka ta soma magana “ba akan sadam bane maryama”to akan menene haka umma kike min asarar hawayenki ?”ina jin araina kamar wata rana zaki gujeni alhalin bani da kowa daga Allah sai ke maryama zuciyata tana tsananin qaunarki maryama rashin sadam ya tabani matuka amman rashin ki shi zai fi komai damuna “numfashi da naunayen ajiyar zuciya maryama ta sauke sannan ta yunkura ta mike ta zauna kusa da umma tana goge mata hawaye tana cewa “a gsky umma baki ta’ba min abinda ya ‘bata min rai ba irin wannnan lokacin ba domin baki d’aukeni kamar yadda na d’aukeki ba nan take umma ta soma girgiza mata kai “umma nifa yar halak ce kuma nasan hallaci kuma zuciyata tana qaunarki fiyye da tunaninki bana tunanin akwai wata ranar da ni maryama zan juya miki baya ba duk runtse duk wuya umma nah tare ban ta’ba jin cewar bakece kika kawoni duniya ba zan kasance dake muddin rai mutuwa ce kawai zata rabamu dan Allah ki daina wannan tunanin ki daina tunanin zan gujeki ni amarki ce haka kema amanata ce ta qarasa maganar tana zubar da hawaye .”






Umma ta rungume maryama ajikinta umma kuka maryama kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani acikinsu sai dai har ga allah umma ta samu natsuwar zuciya domin bata son abinda zai nisantata da maryama idan ba aure bane .kuma a kullum tana mata fatan samun miji na gari sun d’auki sama da mintuna talatin suna kuka sannna umma ta soma shafa bayanta tana cewa “kukan ya isa haka maryama kiyi min afuwa yau ummanki ta sakaki kuka sheahekan kuka kawai maryama take tana narkewa ajikin umma “dan allah umma ki daina wannan tunanin aranki “in sha allahu maryama bazan sake ba kuma na gode matuka da qaunarki allah ya barmu tare allah yayiwa rayuwarki albarka Allah ya azurtaki da samun miji na gari wanda zai kular min dake ya kuma rike minke amana addua sosai umma tayita mata tana shafa bayanta har maryama ta samu natsuwa .”






Parlour’n ya d’auki shiru har na tsawon minti goma sannna umma tace “tashi muje ki kwanta gobe zaki office ta fad’a tana mikewa tare daita ajikinta ta d’aukar mata jakar aikinta da d’ayan hannunta suka nufi d’akin maryama umma na sake kwantar wa maryama da hankali ,ta ajiye mata jakar akan table sannna ta kwantar daita akan katifa ta zauna a gefenta tana tofe mata jiki da addaua tana cigaba da shafa bayanta tamakar wata yarinya qarama maryama tace, umma kije ki kwanta ki huta kema “to maryama sai da safe, Allah ya tashemu lafiya ta mike ta fito ta shiga dakinta ta hau Kan gadonta ta kwanta “.bayn fitar umma da kusan awa uku amman maryama ta kasa bacci sai faman juyi take kwance ta mike zaune ta duba wayarta taga lokaci ya wuce sosai dan d’aya ta kusa jin idanuwanta basa jin bacci ta janyo jakar aikinta ta cigaba da aikinta ahankali ahankali ta dinga jin kamar motsin shigowar mutun tayi tsam da ranta tare da dakatar da aikin da take na wani lokaci ta kasa cigaba aikinta ta kasa kunneta sosai ko zata ji takun tafiyar mutun sai dai bataji komai ba har tsawon wasu mintuna dan haka ta maida hankalinta kan takardar gabanta ta cigaba da aikinta .sai dai haka nan ta dinga jin zuciyarta na tsinkewa tare da jin mummunar faduwar gaba .”




domin ta samarwar zuciyarta natsuwa ta ajiye takardar dake Kan pillow ta yunkura ta tashi ta sauko daga Kan gado ta soma tafiya a hankali cikin sand'a har ta fito zuwa babban falon gidan ta tsaya shiru tana kallon koina ta cikin hasken da bai gama haskaka falon ba, ta kai idanunta ga kofar shigowa taga kofar a kulle take dan haka ta sauke numfashi ta koma ta cigaba da aikinta bayan wasu lokaci ta soma jin bacci dan da kyar take iya bude idanunta tashi tayi tana hamma tare da cewa " gashi ina tsananin jin bacci gashi banga ma aikin dake gabana ba ."
ta fito zuwa falo ta nufi kitchen ta dauko dan qaramin prepand mai zurfi ta zuba ruwa kadan dan tea take bukata ta daura akan gas ta kunna ta tsaya har sai da ruwan yayi zafi ta hada tea ta zuba a cup ta fito tana sha a ahankali ..qarar faduwar abu taji ta daidai bangaren d’akin yaya sadam ta tsaya cak tason ta qara ji amman shiru .”




sai dai batayi tunanin komawa dakinta ba ta fara tafiya a hankali zata dakin inda taji motsin qarar faduwar abu har tayi taku biyu sai kafarta tayi tuntube da takalmin aunty hassna ta sauke numfashi sannan ta tsuguna ta dauka tana cewa "bansa sai yaushe aunty hasana zata daina shigowa da takalmi har parlour' ba, idan ya zama dole ai akwai takalmin yawo a parlour ba irin wannan ba da zai cire maka farce , takalmi Kmr katako gashi abun haushin ma sai tazo da takalmi amman idan ta tashi wucewa ta sai ta barshi ta kama gabanta haka .ta qarasa inda suke ajiye takalma ta ajiye nan ya kamata da irin wadan takalmar wannan abu ya dauki hankalinta yasa bata shiga dakin ba ta koma dakinta ta zauna ta tankwashe kafafaunta ta dauki takarda wayarta taji ta dauki qara ta lalubo wayar ta manna a kunnenta"okay yusura nima ina Kan aiki bazan kwanata ba sai na kammala byn ta kammala ta ajiye wayar wani kiran ya shigo taja tsaki waye kuma adaidai wannnan lokacin ? ta lalubo ta dauka tana duba number bata san number ba kamar bazata dauka amman sai tayi tunanin ko emergency call ne ta dauka tana cewa "hello !






Daga can bangaren taji ance "maryama hussein ce maaikaciyar AGC company “yes sir okay gobe muna bukatar ganinki a kamfanin da misalin karfe bakwai daidai ana gama fadar haka akayi discounting din kiran tayi shiru tana tunanin wanda ya kirata wannan dai ba muryar mr ATA bane ta lumshe idanunta tana cewa babu mamaki ko cikin yan'uwansa ne wani Ke bukatar yin aiki daita dan haka bata sake yunkurin tashi ba gara ta qarasa kafin wani aiki ya shigo mata gobe tana hamma tana aiki har ta qarasa ta kwanta da zumar tayi bacci amman ta kasa runtsawa har aka kira sallah ko byn daaka idar ma bata iya komawa ba dan haka ta yi wanka tayi shirin zuwa aiki ."Karfe bakwai daidai a AGC company tayi mata koda ta shigo ma'aikatan babu wasu mutane sai tsirarrun mutane dake kai kawo da securities da masu share maaikata ta kama hanya zuwa sama nan ma dai bbu kowa koina shiru kai tsaye office dinsu ta shiga tana sauke numfashi ta cire jakar kafadarta ta ajiye akan table ta ciro takardun zanenta tana dubawa ta sake duba agogon hannuta .”






“gsky yau nazo da wuri sosai ko da yake na huta da complain din madam some kullum sai tayi complain akaina to gashi itama bata zo ba tukun.” ta fad'a tana sauke numfashi tare da tuna yadda take mata idan tazo late "Mis maryama hussein why are you always late ?ta fada da irin muryarta ?tana lumshe idanunta tare da saka hannunta cikin aljihun doguwar rigar dake jikinta yayinda hannunta daya ke tokare da table din gabanta exactly yadda mr ata shi kuma yake yi har da qara taku biyu ta tsaya Kmr yadda yake yi .murmushi ya bayyana akan fuskarta sakamakon tuno mr ata datayi tana jin wani iri ajiknta shi kuma matsalarsa always complain “baki daukar aikinki da mahimanci a tunaninki ke din professional ce bana bukatar mutane da basa daukar aikinsu da daraja kullum bakya son zuwa aiki da wuri , kullum da excuse din da kike kawao wata rana zan dakatar dake aiki ta fada a fili .kamar ance ta juya bayanta tana juyo kawai taga mutun tsaye ya jingina jikinsa da kofar shigowa idanunsa kyam akanta sanye cikin kanana kaya irin shigar jiya sak yayi sai dai kalar kayan dabam yana rike da farin glass dinsa,yayinda hannunsa daya na soke cikin aljihun wondonsa kmr koda yaushe yayi shiru yana jifan da wani irin mayataccen kallo mai tsantsar kashe sansar jiki .”






Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


BOOK 3


*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 20


A matukar rikice ta juya tana mai had'e hannu wanta waje d'aya tana jin wani irin mummunar fad'uwar gaba mai tsanani "gabad'aya yanayinsa yayi matuqar tsoratata. a bangaren mr ata kuwa wani sanyi dadi ne ya mamaye sansar jikinsa sakamakon d'aura kwayar idanunshi da yayi akan sanyi idaniyansa da sanyi safiyar nan , wani tunani maryama tayi wanda yasa ta juyo da sauri tayi taku biyu ta tsaya kusa dashi muryarta na rawa tace "good morning sir"! bai amsa mata ba ya qarasa shigowa cikin office din sosai yayi kmr yadda yake
yi a duk sanda ya shigo hannunsa d'aya cikin aljihun wondonsa yayinda d'ayan hannun kuma ya d'aura akan table . shiru tayi tana ciza harshenta kamar tayi dariya dan wannan salon nasa yana matukar burgeta kuma yana sakata jin nishad'i acikin ranta sai dai ganin yadda yayi mugun had'e rai fiyye da kullum dan fuskar nan tashi sam babu annuri kirki yasa tayi maza ta sanyawa jikinta natsuwa tare da lumshe idanunta na second biyar sannan ta bud'esu fess akan kyakkyawar fuskarsa ta sake gaishesa a karo na biyu ". “good morning sir ?!






“still shiru ne ya sake biyowa baya batare daya kalli inda take tsaye ba "maganar me kike yi ?taji saukar muryarsa ta doke dodon kunnenta,a natse ta kallesa qirjinta na dokawa da qarfin gaske tace"ba maganar komai nake yi ba "!tsumammun idanunshi ya waigo ya kalli inda take tsaye har lokacin tana wasa da yatsun hannunta ,kana kallonta kasan tayi kama da mai laifi domin ko a iya haka ma rashin gaskiyarta ta nuna ,ya motsa lip's dinsa ahankali yace "ya zakice ba maganar komai kikeyi ba byn da na shigo naji kina cewa wani abu me kikeyi cewa ?"nan take hantar cikinta ya kad'a ilahirin jikinta ya kama rawa.
sosai ta firgita "kar dai yaji abinda ta fad’a?"inna lillahi!" ta furta acikin ranta ,zuciyarta cike da matsanancin tsoro take kallonsa."ya gyara tsayuwarsa sannan ya fuskanceta tare da zura hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa ya tsura mata tsumammun idanunshi masu firgitarwa “maryama kince wani abu, abinda kikace nake son na sani ".




muryarta cike da in ina tace "ina..ina.. dai magana da zuciyata ne yayi shiru still kwayar idanunshi na yawo a sansar jikinta wanda ke qara saka zuciyarta shiga rud’ani bayan kamar second goma ya sake motsa lip’s dinsa " amman kamar kina raact kmr ni ?da sauri ta fito da shanyayyun idanunta waje tana cewa "no no sir me yasa zanyi haka?" ni sam ban yi haka ba kawai dai ..."sauran design's din dana baki aikinsu last week sunyi ready "?ya katseta ta hanyar fad'ar haka yana cigaba da kallonta kamar zai cinyeta, shiru tayi ta kasa cewa komai dan tuni ta ajiyesu a gefe tana kan new desing's din da zasu gabatar ne ,wani kyakkwan shu'umin kallo ya d'auketa dashi wanda yasa take tsigar jikinta d'aya bayan d'aya suka fara mikewa tayi saurin cewa "no basu yi ready ba sir "ko zan iya sani dalili ?."tayi shiru qirjinta na lugud'en bugu da qarfi .”






"wai mai yasa kika rainani har haka ?"sake fito da idanuwanta tayi sosai tana kallonsa zuciyarta na sake shiga tashin hankali "na shiga uku ta fad'a acikin ranta “wallahi ta d'auka bazai nemesu da wuri ba yasa ta tattara ta ajiyesu "yaushe zaki fara bin umarnina?" yayi mata tmbyr yana qara taku d'aya zuwa gareta "yaushe ne idan na baki aiki zakiyi min shi cikin dad'in rai batare da 'bata lokaci ko jayayya ba "?ya qarasa maganar yana sake yin taku d'aya ya matso daf da inda take sosai yana mata wani wahalallen kallo." tayi saurin ja da baya tana furta kalmar "inna lillahi !”yau na bani me ya kai ni shiga wani aikin bayan ban qarasa masa nashi ba "?lallai maryama kin tarp match dan kin fara wuce limit dinki ,amman duk abinda nake ai ina yi ne domin shi ,ina yi dan na wanke masa zuciyarsa akan kuskuren da nayi masa, ya sake matsota sosai "ina jinki ki bani amsar tmbyoyina "saboda kin rainani yasa kike aikata min haka ko?






takure jikinta tayi waje d'aya tana wata irin kyarma tace "wayyo allah tsigar jikina " gbdy ta kasa motsi duk ta rikice sakamakon kusancinsu da yayi yawa dan har suna iya jiyo bugun zukatansu da saukar numfashinsu "wannan shirun ma kanshi cikin rainin da kika min ne ko ba haka ba ?"da sauri ta girgiza masa kai "alamun a’a!”idan ba haka bane taya ina magana kina jina amman kiyi min shiru?" kayi hakuri sir sabon aikin dana nemi izininka na fara "wa ya sakaki ?"wa ya baki izini ?yayi mata tambayar ajere yana sauke mata zazzafan numfashinsa a fuskarta da wuyanta ,ta firxgo numfashi da kyar sannan ta d’ago ta kallesa zuciyarta na karkarwa “banace bana supporting ba ?"kayi hakuri kace but .."but what ?wannan karon a matukar tsorace yayi maganar wanda yasa tasa hannunwanta duka ta toshe kunnenta tana durkushewa qasa a gabansa.”




wani dogon numfashi ya sauke yana binta da kallo ganin yadda ta gigice ta rikice ta mugun bashi dariya kasa rike dariyar yayi har sai data bayyana akan fuskarsa ,inda ya kamo gefen lip’s dinsa na kasa ya fara cizawa ahankali ahankali,suna cikin wannan halin sai ga oga amar tun daga nesa ya hango bayan mr ata kuma nan take jikinsa ya bashi maryama ce durkushe a gabansa domin dai yayi imani babu wannan macen a duniya da ata zai tasata gaba irin haka ."Jin shiru yasa maryama d'ago idanunta sha'be sha'be da ruwan hawaye ta zuba masa tana “kayi hakuri nayi kuskure sir,amman zan ‘bata komai na aikin ,haka zalika zan dakatar da kowa kuma in sha allahu gobe zanzo maka da desing’s dinka .”ta qarasa maganar wasu hawaye masu zafi suna gangarowa akan kuncinta adaidai lokacin oga amar ya samu qarasowa wajen. ya tsaya yana kallonsu da bayyana nen mamaki akan fuskarsa kafin daga bisa yace "ya haka ata ?".






Mr ata ya juyo ya kallesa alokacin da oga amar ya bud’e baki zai sake cewa wani abu nan take mr ata yaja hannunsa suka fita daga office din dan yasan zai iya masa ' baran 'barama a gaban maryama shi kuma bai shiryawa hakan ba tukun, yana da plan akanta suna shiga office dinsa oga amar yace "ata ka dinga jin tsoron Allah fa “me nayi?!” dan ubanka ya kake tsoratar da yar mutane kaga yadda yarinyar nan ta fita haiyacinta tana zubar da hawaye wallahi zaka ballowa kanka ruwa ,kai yanzu soyayyar ma sai ka nuna mata seniority?"mr ata yayi bayyana nen murmushi mai d’an sauti kad'an abinda bai ta'ba yi ba kenan a tsawon rayuwarsa sannan yace "yarinyar nan wallahi bazaka ta'ba gane rashin kirkinta ba bugani take kamar ta samu kwallon kafa ga rashin bin umarnina ka shigo min da kaidodin na babu gaira babu dalili ." karya kakeyi ata " kai dai wallahi mugu ne sam maryama bata haka kawai dai kayi niyyar kasa yarinyar mutane kuka ne da sassafe "ai daman nasan haka zakace tunda kai ma sonta kake yi ."




Oga amar ya kyalkyace da wata dariya yana kaiwa kafad'ansa duka "gsky ata ka gama dani amman kasani da son maryama nake da tuni an wuce gurin da sai dai ka bud'e idanunka ka ganta a gidana a matsayin matata "da kuwa anyi burouba!"ya fad'a yana zabga masa wata qatuwsr harara "sorry friend maryama taka ce kai kad’ai daman kace babu macen da zaka bi sai ita kuma naga hk sauran ka zama bita zai zai ko da yake shima ka fara zama "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login