Showing 1 words to 3000 words out of 104857 words

Chapter 1 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

22 Feb 2025

4185

   UWATA CE SANADI




©Maimunah Tijjani Iyam








Bismillahir rahmanir rahim ina Mai farawa da sunan Allah mahaliccina Wanda cikin ikonsa,amincewar sa,yardar sa tare da Aron numfashin daya bani na rubuta wannan littafin nawa UWATACE SANADI.ya Allah ka tsare min hannaye na wajen rubuta abin da zai zama cutarwa ga al'umman musulmai tare da tarbiyarsu.


GARGAƊI
Ban yadda wani ko wata suyi ƙoƙarin sauyamin littafi ba,ba tare da iznina ba Duk Wanda yayi ƙoƙarin aikata hakan ALLAH YA ISA BAN YAFE MASA BA.




UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


______________________________


Page 0⃣1⃣




Littafin ƙaddarar rayuwa ta cike yake da babi-babi na ƙuncin dana taso,na tsinci kaina a cikin tun kafin nasan kaina.
Kamar yanda jini yake yawo cikin duk wata sassan jikin ɗan adam misalin yanda ƙunci yayi kane-kane cikin rayuwa ta.
Kowani ɗa yafi kusanci da mahaifiyar sa saɓani nida ta wa uwar take ƙoƙarin nisan ta kanta dani,rashin dace da samun nagartacciyar uwa shi yaja ragamar rayuwa ta izuwa ga ƙunci da baƙin ciki.
Bansa menene farin-ciki ba,bansan ya ake yinsa ba,bansan inda ake samun sa ba,wasu lokutan nakan zauna nayi kuka da hawaye anya akwai mai irin ƙaddara ta kuwa?.




Tabbas kowani bawa da irin tashi salon ƙaddarar da kuma yanda take zuwa masa amma tawa ta fita daban.
Suna na Hibba labarin rayuwata Mai matuƙar girgizarwa ne,firgitarwa,gami da kiɗimarwa.
Duk wata zuciyar da Allah ya dasa imani acikin ta sai ta raunana domin jin labarina,yayin da idanuwa da yawa zasu zubda hawaye yayin da suka saurari labarin rayuwata.
Nice ɗiya ta farko a wajen mahaifina ta bangaren mahaifiyata kuwa ta kasance, ta taɓa aure kafin mahaifina ɗanta ɗaya da tsohon mijin nata YAYA FAWAS,amma duk tare muke zaune dashi.
Mahaifiyarmu haj.Juwahir ba inda munanan halayyarta basu jeba kowa ya shaideta da rashin ta ido wato kunya,ta bangaren Abbana kuwa juya shi takeyi son ranta kasancewar ta fishi abin duniya.
Duk dawainiyar gidanmu ita takeyi,Abu daya daya ke rushe mata wannan aikin alkhairin shine gori domin ko ruwa.
Ta saya a gidan nan sai ta wuni tana yiwa Abba gori,ta gaza fahimtar nauyin igiyoyin aurensa uku dake kanta, ta wofantar da nauyin tarbiyanmu dake kanta ta zaɓi duniya sama da inganta lahilarta.
Yanda ake dama koko a cikin kowani gida na kirki haka Umman mu ke dama giya a tsakar gidanmu wai da sunan Sana'a.
Safiya ce datake cike da sanya nishaɗi yayin da faffaɗan bishiyar tsamiyar dake dashe,a madaidaicin filin tsakar gidan mu ke kaɗa iska ko'ina.Yanayi ne mai tafiyar da zuciya kasancewar daren jiya kwana akayi ana zabga ruwa,hakan ya sanya garin ƙara sanyaya.
Zaune nake a madaidaicin ɗakin yake mallaki na,katifa ce wacce take yashe a ƙasa sai kuma bahon kaya daga can gefe guda su kenan a cikin ɗakin.
Shirin tafiya makaranta nakeyi ina saka safa yaya Fawas ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, da fara'a a saman fuskata nake amsa sallamar.A gefena ya zauna tare da karɓan safan dake hannuna ya fara ƙoƙarin sanin yana cewa.


"My cute angle har yanzu baki gama shiryawa ba ko so kike muyi latti?".


Cikin murmushi nace"A'a yayaa Fawas ai nakusa gamawa ma fa ka shigo".


"Ba wani kin kusa gamawa bayan kullum sai nazo na taya ki shiryawan".
Yana gama sanin safan ya riƙo hannuna muka fito,A kwance akan tabarma muka hango Umman mu ta lumshe idanunta kamar mai bacci, a hankali muka ƙariso inda take cikin ƙasa-ƙasa da murya yaya Fawas ya kamo kunne na yana cewa,


"Ƙanwata mu tashe tane ko kuma mu tafi?".




Nace "yaya Fawas inmuka tashe ta faɗa zata mana gwara mu tafi kawai".


"To".




Kawai yaya Fawas yace tare da ƙara riƙo hannu na muka dauƙi hanyar fita daga gidan.
Kamar daga sama muka ji muryan Umma ta daka mana tsawa a firgice dukkaninmu muka juyo yayin,da lokacin ɗaya jikinmu ya ɗauki rawa bansan sanda nasaki wani razanannan ƙara ba saboda duk na tsorita inda abin dayake saurin gigitani to tsawa ne.
Kamoni yaya Fawas yayi sosai cikin zubda ƙwalla yace "kin nutsu ƙanwata kinji".
Cikin wani tsawan umma ta cigaba da magana tana cewa,"Munafukan banza ina da kuke shirin tafiya yan iska jarababbu salon kujawa mutum abin magana a gun wannan sakaran uban naki ko?".
Cikin raunanniyar murya yaya Fawas ya shiga faɗin "Umma dama munga kina bacci ne kuma bamason mu tashe k......"


Wani tsawan ta kuma dakawa yaya Fawas Wanda yasa shi yayi shiru ba tare da ya ƙarisa maganar da yakeyi ba.
Cikin zafin rai Umma take maganan tamkar zata kaiwa ya Fawas duka take cewa"Dalla rufe min baki munafikin banza, Ku wuce kuje Ku ɗauko abinci kuci kafin Ku tafi".


A hankali na wuce kitchen naje na ɗauko mana abincin, hawaye tunin ya fara wanke min fuska muka fara cin abincin.
Ai kuwa kamar jira Umma takeyi mu fara cin abincin.Muna kai spoon ɗin farko ta fara zazzaga mana gori.Wani dariyar ƙeta tayi sosai har sai da idanunta suka kawo ƙwalle kafin tace,"Uhm abin da kuka iya kenan daga Ku har lusarin uban naki shine ci kudai sai dai infita innemo muku,in dafa,in baku Ku zauna Ku hau ci ko? daman shine aikin.ba komai ai Allah yana ganin duk abin da sule yakemin a cikin gidan nan duk ɗawainiyar gidan nan ya gibge shi a kaina tsabaragen lusaranci irin nasa".




Sai data numfasa sannan ta cigaba da faɗin"Bashi da aikin sai yawo a cikin unguwa daga wannan masallacin sai wancen".
Da hawaye fal a idona na takaicin furcin Umma na miƙe daga cin abincin cafko hannuna yaya Fawas yayi shima idonsa cike da hawaye yace"A'a ƙanwata ki zauna mugama cin abincin kar ki ja mana wani abin maganan".
Tabbas akwai wata irin so da shaƙuwa tsakani na da yaya Fawas,a lokuta da dama nakan mance dacewa ba mahaifinmu ɗaya da shi domin ko Kaɗan Abba baya nuna bambamci a tsakaninmu.


A hankali na dawo na zauna tare da ɗaura kaina akan cinyar yaya fawas ina kuka.Mukam wacce iriyar uwa Allah ya bamu,kullum tinani na shine wani irin laifi muka aikatawa umma datake nuna mana wannan zallar kiyayya tamkar ba ita ta haife muba.




Shafa kaina yaya Fawas yayi cikin Ƙarfi hali yace"Ya isa haka Hibba ki tashi mu tafi kinga ma munyi latti".




Tashi nayi na fara tattare kwanukan abincin na kai kitchen.Umma nake kallo yayin da ita kam ma hankalinta ba'a kanmu yake ba sai al'amuran gabanta takeyi.
Wasu hawaye ne naji sun shiga ambaliya a fuska na wato ita kukan damukeyi ma bai dameta ba,.kitchen na shiga domin ajiye kwanukan daidai lokacin daxan fito daga kitchen din najiyo muryan yaya Fawas yana cewa."Umma xamu tafi".




Cikin ɗaga murya Umma tace" to Fawas Dan zaku tafi me kakeson namuku kenan?na goya Ku nakai Ku makarantar ko kuma yaya kake son na muku?".




Cikin sanyin murya yaya Fawas yace" A'a Umma dama kuɗin nafef zaki bamu kinga munyi latti".


Harara Umma ta watsa masa sannan tace" nizan baku kuɗin nafef ɗin? Ai da niyyar ficewa kukayi daga gidan ba tare dakun sanar dani ba indai sai nabaku kuɗin nafef sai dai, Ku fasa zuwa makarantar ai dama ba dole bane".




Tana kawowa nan ta cigaba da abinda ke gabanta.Fitowa nayi daga kitchen ɗin na nufi inda yaya Fawas ke tsaye riƙo hannun shi nayi ina cewa"Yaya na mu tafi kar muyi latti".


Durƙusawa yaya Fawas yayi tare da ƙara riƙo hannu na dukka biyu hawaye nabin fuskar sa yake cewa"Hibba ko zamu haƙura yau da zuwa makarantar,kinsan da nisa in mukace zamuje da ƙafa bazamu isa akan lokaci ba,gashi kuma Abba baya nan balle inyana dashi ya bamu".


Wani marayan murmushi nasaka Wanda iyaka cinsa fuska dan baikai har ga zuci ba kafin nayi ƙarfin halin furta.




"A'a yaya Fawas muje kawai".




Shima murmushin ya saka yana cewa" Ƙanwata mu tafi da ƙafa bazaki gaji ba?".kaina na ɗaga masa alamarar e.




Share hawaye fuskan shi yayi tare da riƙo hannu na muka tafi.A hankali muke tafiyar kamar babu laka a jikin mu,tunda muka fito daga gidan cikinmu ba Wanda yayi magana.
Kowa da abinda yake tinani acikin ransa.Muna cikin tafiya muka hangi Abba zaune a bakin wani masallaci,ya zabga tagumi hannu bibiyu.




Hannunsa riƙe da carbi yana tasbihi amma kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar wa kanka,cewa hankalinsa ba akan tasbihin daya ke yi yake ba.




Ina hango Abba nasaki wani nauyayyan ajiyan zuciya nasan wahalar mu ta ƙare matuƙar yana da kuɗi zai bamu.
Mu ƙarisa makarantar ƙafafuna har jinsu nakeyi tamkar ba'a,jiki na suke ba dan tsabar gajiya kawai,daurewa nake har ya fawas ya gane hakan.
Da sallama muka iso inda Abba ke zaune,a hankali ya ɗago kansa daga tagumin da yayi yana binmu da kallo yace"Hibba Fawas me kuke yi har yanxu Baku tafi makarantar ba?".
Tunin idanuna sun kawo ruwan ƙwalla nace "Abba wallahi Umma ce tace bazata bamu kuɗin abin hawa ba wai sai dai mu tafi da ƙafa,Ko kuma mu fasa zuwa makarantar".
"inna lillahi wa inna ilaihir raji'un!wannan wani irin rashin tausayi ne haka,tun daga nan zaku tafi har makarantar kuma da ƙafa?".
Jijjiga kansa yayi tare da ciro naira ɗari biyu daga aljihunsa,ya miƙawa yaya Fawas tare da faɗin"Ga wannan Fawas ko hau nafef,Ku tafi makarantar".Karɓa yaya Fawas yayi tare da yi masa godiya sannan muka tafi.








UWATACE SANADI




Tsarawa/rubutawa




©Maimunah Tijjani Iyam




__________________________


Free page






Page 0⃣2⃣




Asalinmu


A jahar yobe muke da zama ƙaramar hukumar potiskum, unguwar tandari.


Asalin sunana Fatima naci sunan kakata ta wajen abba shiyasa Abba yake ƙirana da Ummul-khair.


Abba Dan asalin kano ne cikin ƙauyen gano, kasuwanci ya kawo shi potiskum.A lokacin ya mallaki komai najin daɗin rayuwa kafin Allah ya jarabce shi da karayan arziki,auren soyayya sukayi da Umma amma tun daga lokacin da karayan arziki ya sameshi komai ya canza na daga zaman dasuke yi.




Anan garin potiskum suka haɗu da Umma lokacin ta fito daga gidan mahaifin yaya fawas.A wajen kakarta take saboda iyayenta sun daɗe da rasuwa,bayan wani ɗan lokaci ma Allah yayiwa kakarta ta rasuwa.


A haka Abba ya aure ta ya kuma riƙe yaya fawas tamkar ɗan daya haifa.


Abba baya wasa akan duk wani lamarin daya shafi harkan karatunmu tun muna nursery school suke private school har kawo yanzu,duk da halin dayake ciki na babu bai taɓa gajiyawa,ba ko nuna gazawa wajen biya mana kuɗin makaranta ba.


Burinsa ɗaya ne a duniya shine muyi karatu ta yanda zamu tsaya Da ƙafafunmu ko bayan bashi.Ina jss 3 ya Fawas yana ss 2 a unity model school dake nan cikin potiskum.




Yau kam idan nace na gane abinda aka mana a makaranta to nayi ƙarya,dan tun da muka isa hankali yake ga tinani,har aka tashi muka dawo.




Tun daga nesa muke hangi mutane keta shige da fice a gidanmu,wani baƙin ciki ne naji ya tsaya min a raina dana tino mummunar sana'ar Umma na sayar da abinda da Allah ya haramta.


Manyan mutane,yan siyasa da ma'abota dukiya suke siyan giyan da umma keyi da sunan Sana'a.


Da sallama muka shiga cikin gidan amma ba,Wanda ya kula da shigowarmu cikin gidan balle musa rai ga za'a amsa sallamar da muka shigo da ita.Gidan cike yake da mata da maza, karuwai da kuma ƴan daudu kowa abin da ke gabansa shi yakeyi.




Ga wani mummunar shigar da matan sukayi,Umma na zaune a kan garduma tare da wasu mutane biyar uku maza biyu mata.Suna buga caca riƙo hannuna yaya Fawas yayi sosa tare da rufe min idona da tafukan hannunsa wai dan kar na kalli abin da Umma keyi.




Muka wuce muka shiga ɗaki yaya Fawas yace."Kiyi wanka kihuta kafin lokacin islamiya yayi kinji ƙanwata "






"To yaya Fawas".


Fita yayi ya nufi daƙinsa,wanka nayi sannan nayi salla na kwanta ina kwanciya yaya Fawas ya shigo.




A gefena ya zauna yana cewa" Hibba kinci abinci kuwa?".




"A'a yaya Fawas kaima ai nasan baka Ciba"na faɗa ina tsaida idanuna akan fuskar shi.


Ajiyan numfashi yasaka kafin yace,"Hibba inason muyi wani magana dake".


Gyara zamana nayi ina cewa" to yayana inajinka".


Cigaba da magana yayi yana cewa "ƙanwata kinga irin rayuwar da mahaifiyar mu ta zabawa kanta ko?" jinjina kaina nayi alamar ina fahimtar maganan tasa,sannan ya ɗaura da faɗin.






"To Hibba banason koda wasa ne koda ace ni da Abba bamu numfashi cikin duniya,wataran kiyi sha'awar irin rayuwar da kikaga umma nayi,my cute angle kinga ke macece".


Cikin nutsuwa nace" In sha Allah yaya Fawas zan nisanta kaina daga dukkanin ɗabi'un da umma take aikatawa.Amma abinda yake damuna shine in har tasan baza ta so mu ba to meyasa ta haifemu?".


Gyaran murya yaya Fawas yayi kafin yace "Hibba Umma tafi karfin musata acikin jerin maƙiyanmu,ita tayi silar zuwanmu duniya ta nuna mana dukkanin ƙauna tinda har ta haifemu kuma bana son na ƙarajin,ki furta cewa Umma bata son mu kinji my cute angle?".


" To ya Fawas in sha Allahu bazan ƙara ba".




Shafo kaina yayi yana cewa" yauwa my cute angle nizan tafi shago in lokacin islamiya yayi ki shirya ki tafi kinji ko".




Turo baki nayi kana nace" yaya Fawas ban iya hadda ba bazan jeba".




Murmushi yayi Wanda sa ka fararen jerarrun hakwaran sa suka bayyana, yaya Fawas badai kyau ba dan mahaifinsa buzu ne ɗan nijar.


"To shikenan amma in Abba ya dawo yasame ki a gida ba ruwa na" yana gama faɗin haka ya fice.


Kallo nabishi dashi yayin da take ficewa daga daƙin,ina ƙara jinjina irin shaƙuwar dake tsakaninmu da yaya Fawas komawa nayi kwanciyata.


Sai dab da magriba sannan na tashi nan naji gidan gaba ɗaya yaɗau kiɗa ta ko'ina sauti ne kawa ke tashi.


A hankali na buɗe ƙofan ɗakin na fito wajen,dan gane ma idano na meyake faruwa.Maza da mata ne sun haɗe sai tiƙar rawa suke babu ko kunya,gefe guda masu shan taba sunayi,masu sha wiwi sunayi,mai shan shishi nayi.
Can gefe kuwa masu caca ne suma sun haɗa nasu daban sunayi.




Umma kuwa tana ta dama giyarta ga masu saya sun mata cirko-cirko akanta,sai sauri take taga ta sallame su lokaci ɗaya muka haɗa ido da ita.
Sauri nayi na kawar da kaina gefe tare da share hawayen dake shirin zubowa daga idona.






"Yauwa Hibba zo ki sallame waɗannan".


Tunin ƙwalla suka fara bin fuskata nace"Umma alwala zanyi fa an ƙira salla".


Ashar Umma ta shiga ɗuramin masu nauyin maimaitawa sannan tacigaba da cewa"Ƴar iska Mai halin ubanta ni zaki cewa salla? zakiyi ko muɗin ce miki akayi bama sallan,zaki yi gadon tsiya matuƙar kikace zaki gado halin ubanki wuce ki bani waje shashasha".


A hankali nake daga ƙafata na wuce naje nayi alwala sannan na koma daƙi nayi salla.


Ina iddarwa na kwanta akan sallayar wani azababban yunwa nakeji har sai da naji kamar zazzabi yana neman rufe ni,lokaci ɗaya jikina yaɗau rawa tashi nayi nashiga banɗaki nayi wanka sannan na dawo kan sallayata na,kwanta bansan sanda wani baccin wahala ya ɗauke ni ba.


Sai bayan sallan isha'i sannan Abba da yaya Fawas suka shigo kamar night club haka gidanmu yake a kowani dare,suna shigowa suka hango Umma ta zage sai buga caca yakeyi,ga wani sautin daya ke tashi cikin ko wata kusurwa acikin gidan.


Kai tsaye Abba ya nufi inda Umma take yace."Juwahir taso innason magana dake".


Ko ɗago kai batayi ta kalle shi ba balle tasan da mutum awajen ta cigaba da cacan ta.




Cikin zafin rai Abba ya sake magana a karo na biyu" Juwahir wai ba magana nake miki bane".


A harsale Umma ta juyo tana cewa,"Haba!sule wai ya kake son nayi da rai nane kazo ka tarar dani ina Abu to ba sai kayi wucewar ka ba".


Ɗaga hannu Abba yayi da nufin zabga mata mari,cikin sauri yaya Fawas ya riƙe hannun Abba cikin muryar kuka yace."Dan Allah Abba kayi haƙuri taci alfarma mu".




Cike da takaicin daya gama cika Abba yace,"Juwahir Allah ya shiryeki" sannan ya wuce daƙin sa.


Yaya Fawas ya shigo daƙi na kwance akan sallaya ya tarar dani a hankali ya zauna gefe na,mafici ya ɗauko ya fara min fifita gani yanda naketa haɗa gumi.




Wani wahalallan ajiyan zuciya na saka lokacin,dana ji iskan na ratsani hijabin dake kaina ya fara ƙoƙarin ciremin.


A hankali nafara buɗe idona ganin yaya awas ne yasa na fara,sakin murmushi yayin da nake ƙoƙarin tashi.




Da fara'ar sa yace "my cute angle yunwa ce tasaki baccin nan ko?".






UWATACE SANADI




Tsarawa/rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


________________________________________




Free page




Page 0⃣3⃣




Sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina cewa"A'a yaya Fawas naci abinci".


Ɗago kaina yayi yana cewa,"Hibba ko wani motsi kikayi nasan me hakan yake nufi baki ci abinci ba ko ƙanwata?".


A hankali nace" e ya Fawas ban Ciba".




Wata Leda ya miƙo min wacce ya shigo da ita yace."Gashi kici Abba ne ya taho mana dashi".


Jawo ledan nayi gaba na na buɗe ƙosai ne a ciki Wanda baifi guda bakwai ba,tunin na fara hawaye na buɗe baki zanyi magana kenan yaya Fawas ya dakatar dani ta hanyar cewa.


"Nasan bazai ishemu ba kici ke ɗaya kinji my cute angle".


Bai jira amsar dazan bashi ba ya fice daga daƙin.


Inaci ina hawaye haka har na gama na tashi naje nayi alwala sannan nazo nayi sallar isha'i,ina iddarwa yaya Fawas ya shigo yace Abba na ƙira na.




Cikin sauri na miƙe nabi bayansa muka nufi daƙin Abba.Yana zaune akan sallaya muka sameshi wuri muka nema muka zauna,gyaran murya Abba yayi kafin yace "Ummul-khair da Fawas".


Cikin nutsuwa dukkaninmu muka amsa sannan ya cigaba da maganar.


"Kunsan halin da muke ciki a wannan gidan abinda yake damuna yanda ƙiyayyar da juwahir kemin har ya shafeku,amma bana son kusa wannan damuwar a ranku har akai ga wataran kun ɓata mata rai,a cikin ko wani yanayi kar Ku na mantawa da cewa ita ce silar ku nazuwa duniya babu abinda zaku yi mata Wanda zai biyata wahalar nishin naƙudar ku datayi.Tsakanin Ku da ita sai addu'a Allah ya shirya mana ita".




"Amin "duk kaninmu muka amsa dashi.


Nasiha Abba yake mana sosai akan irin girman hakkin da umma take dashi akanmu.




Muna cikin haka umma ta bankaɗo labulen daƙin tare da shigowa daƙin tsaki ta saka kafin tace.




"Haka dai ka iya sule baka da aikin yj sai dai ka tara yaran nan kana tusa musu ƙiyayya ta a cikin ransu.Wa kai a hakan kafi kowa son su bayan ba ɗaya daga cikin ɗawainiyar, su Wanda kakeyi sule kai kam ka tsoraci ranan da Allah zai tambaye ka irin kulawar daka bawa iyalinka".




A hankali Abba yace"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login