Showing 45001 words to 48000 words out of 104857 words

Chapter 16 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7295

banida shi wani maganar sukayi da Granny wanda ya jefashi cikin wannan yanayin,ajiye flask ɗin tea ɗin dake hannu na nayi akan dinning ɗin.Sannan na wuce part ɗinmu na ɗauko masa maganinsa sannan na dawo,nan inda na barshi na same shi sai dai izuwa yanzun ya buɗe idanunsa yana kallon rufin falon da yazamto shamaki tsakanin sa da sararin samaniya.
Kusa dashi na zauna na ɓalla masa maganin sannan na miƙa masa,idanunsa dasukayi jajir ya zuba mini sosai abin ya bani tsoro dan gani nayi kamar baya numfashi.Hannu nasa a ƙirjinsa na tabbatar da zuciyar sa na bugawa sannan na sauƙe wata zazzafar ajiyan numfashi.


Ganin baida niyyar amsar maganin yasa nasa masa a bakinsa saurin riƙe hannu yayi tana faɗin"Nasha maganin tunda asuba yau azumi nakeyi".


Da mamaki na nace"Azumin meye?".


"Azumin kare kaina daga faɗawa izuwa ga halaka".Wani abu ne wanda bazan iya fasalta shi ba naji ya ratsa dukkan jikina baiɗaya.Miƙewa nayi yayi sauri kamo hannu na tare da faɗin"zauna inason muyi wata magana".


Ba musu na komo na zauna ƙara kareni da rikiɗaɗɗon idanusa yayi har izuwa lokacin da Iya da Yasira suka fito,saurin tashi daga kusa dashi nayi na miƙe na nufi part ɗinmu domin ajiye maganin.


Koda na dawo duk sun gama hallara akan dinning table ɗin,banda Habib dayake har yanzu zaune cikin falon duk yanda naso sakar jiki na kamar ba abinda ke damuna kasa hakan nayi,banci abincin sosai ba na tashi na koma part ɗin mu.Akan bed na zube ina sakin wani kuka dayake fitowa kai tsaye daga ƙasan zuciya ta.


Koda suka gamayin breakfast ɗin ɗakinta Granny ta wuce bayan tacewa Yasira ta same ta a ɗaki,Tana zaune bakin gado tana kaɗa ƙafafunta data saƙale su wuri guda Yasira ta same takusa da ita ta zauna.


"Yasira wata tambaya zan miki kuma inason kiyi mini alƙawarin,cewa zaki sanar dani gaskiyar abinda kika sani dangane da lamarin".


"In sha Allah Granny zan sanar dake komai game da tambayar dazaki min gwargwadon masaniyar danake shi akan abun".


Cike dajin daɗin furcin Yasira Granny ta ɗaura da faɗin"inason ki sanar dani abun dakika sani game da irin zaman da babban mutum sukeyi da matar sa Hibba,nasan dole zakisan wani abu dan kice kike zaune dasu".
Wannan tambayar ta sanya canjin cikin Yasira kaɗawa sai data basar kana tace"Granny wani abun kika ji ko kika gani daya sa kike zargi wani abu a tsakaninsu?".


Sanar da ita duk tattaunar Habib ɗin dataji sunayi da Bashir tayi sannan ta ɗaura da faɗin"Tabbas akwai wani abun dasuke ɓoye mana wanda nakeson ki sanar dani yanzu".




Jin wannan maganar ta Granny yasanya Yasira ganin ba amfanin ta ɓoye mata,komai tunda ta riga da taji rabin bayanin gwara kawai ta sanar da ita ko zata nemawa Hamma Habib ɗin masifa.
Sai data gama wannan tinanin kafin tace"Granny tabbas abinda kikaji haka ne,Basu taɓa haɗa gado da Hibba ba hasalima a mabambamtan ɗakuna suke kwana,Hamma ya ɓoye muku hakan ne a tinanin sa zai iya yiwa tufkan hanci sai dai kuma abin na neman yaci tura.Dan bana raba ɗayan biyu azumi da yakeyi yau bana Allah da annabi bane sai dai ganin da yayi lamarin na neman fin ƙarfinsa".


Tabbas abinda Granny ke hasashe ne ya tabbata tace"Tashi kije zamuyi maganar da suraj".riƙo hannunta Yasira tare da marairaice murya ta shiga faɗin"Granny dan Allah duk hukuncin dazaku ɗauka kar ku raba Hamma da matar wallahi yana sonta dukkanmu shaidane".
Kanta kawai Granny ta ɗaga mata alamar taji,sannan Yasira ta tashi ta fice daga ɗakin kamar yanda Grannyn ta umarce ta da hakan.
Wayar ta Granny ta ɗaga ta ƙira Suraj bugu ɗaya ya ɗauka,ko gaisuwa kirki bata bari sunyi ba ta wuce kai tsaye ga maganar dake bakinta.Ajiyan zuciya Suraj ya sauƙe bayan ya gama sauraron Granny sannan yace"Hajiya yanzu meye abunyi,dan bazamu zuba ido mu cigaba da ganin Habib a cikin wannan halin ba gudun kar hakan ya haifar maba da ɗa marar ido".


Itama ajiyar zuciyar ta sauƙe kana tace"Zan tarasu na musu magana idan har bata gyara ba,sai mu aura masa ƴar-uwarsa YASIRA na tabbatar ita zata bashi kulawa yanda ya dace tunda ƴan uwa suke".


Sosai Suraj yayi na'am da batun Granny sannan sukayi sallama,Ina kici cikin part ɗin mu ina haɗawa Habib abin ɓuda baki Yaya Fawas ya ƙirani bayan mun gaisa yake sanar dani yazo gano wajensu Baffa.Nan ya basu muka gaisa hadda Inna mun daɗe muna hira kafin mukayi sallama.
Ina gama haɗawa na jeresu akan dinning dai-dai lokacin da Habib ɗin ya fito daga ɗaki domin zuwa masallaci,gabatar masa da dabino nayi yaci ina masa sannu da sha ruwa sannan ya fita.
Sai danaga fitarsa sannan na koma ɗakin nayi nawa sallan.Kamar yanda ya saba sai da akayi isha'i sannan ya dawo,Shagwaɓe fuska nayi hadda hawaye na sannan na samu yaci abincin kaɗan jawo ni jikinsa yayi ya rungume,yana sauƙe ajiyan zuciya akai-akai kamar wanda ya shari mungun gudu.


Ranar maƙale a jikinsa muka kwanta,washe gari kuwa da wurwuri muka tashi muka shirya kasancewar a ranar mukeson zuwa gidan Dr Bashir,Afalo muka iske su Granny hadda Iya.


Kusan a tare muka gaida Granny da kuma Iya suka amsa ciikin sakin fuska,sannan muka wuce dinning mukayi breakfast.


"Babban mutum yau baka azumin kenan"cewar Granny wanda hakan yasanya Habib ɗagowa ya kalleni kana yace"E Granny banayi sai ranan alhamis ai".


Kanta kawai ta jinjina muka cigaba da cin abincin,koda muka gama dawowa falo mukayi muka zauna bayan mun zauna ne Granny tace"Babban mutum naji duk abinda ke faruwa tsakanin ka Hibba shiyasa na taraku anan,domin ji daga bakinku shin Hibba menene matsalar ki da kika bar mijin ki cikin wannan ukubar tsawon watanni uku?".


Da dawani irin ƙarfi zuciya ta ke bugawa tamkar zata faso ƙirjina ta fito waje,sadda kaina ƙasa nayi inajin hawayen dake bin gefen kuncina yana sauƙa har izuwa saman wuya na.


"Hibba ke muke sauraro"Granny ta ƙara faɗa a karo na biyu sai a wannan lokacin na ɗago kaina ina kallon Habib,wanda shima ɗin ni yake kallo baki nane ya shiga rawa nace"Hajiya idan nace akwai wani abunda Habib kemin na rashin kyautatawa wanda yasa nake masa haka to nayi ƙarya,ban taɓajin wani abun mai suna sha'awa ba,nima bansan dalili ba zuciya bata nutsuwa aduk lokacin dana ganshi kusa dani ".
Na gwammaci yau in sanarwa Granny komai koda hakan kuwa na nufin za tace Habib ya sake ni,"shi kenan dalilin?"furcin Granny.


Habib ne yayi saurin faɗin"Granny ina zaune lafiya da mata ta,bayan wannan abun bata rageni da komai ba dan Allah mubar maganar nan anan".


Kallon da Granny ta watsa masa ya sashi yin shuru tare da sunkuyar da kansa ƙasa tace"Bada kai nake magana taba kabar ita wacce nayiwa,tambayar ta amsa".
Ahankali nace"Wannan su kenan dalili na amma wallahi band.....".Saurin katse ni tayi ta hanyar faɗin"Kuje keda mijin ki ku nema magani na baku wata biyu,idan har na ƙara fahimtar irin haka na cigaba da faruwa tsakanin ku.To daman munyi magana da Suraj ga nan ƴar-uwar ka Yasira sai mu aura maka ita,ta kula dakai tunda dai ita ta kasa".


Cikin wani irin hanzari Yasira tace"Granny dan Allah kubar Hamma da matar sa"tana kawo wa nan ta fice daga falon.


Habib yace"In sha Allah zamu nemawa kanmu mafita".sai da ta ɗauke kanta kafin tace"Da kuwa kun kyautawa kanku,ni ban taɓajin irin wanga batun ba ".


Iya da tunda ɗazu batace komai ba tace"Amma Hajiya sai na kega kamar yanda Hibban ta bayyana akwai alamu sihiri acikin lamarin".


"Koma dai menene na basu nan da wata biyu in basu nemawa kansu mafita ba,zan zartar da nawa hukuncin"furcin Granny.


Share hawayen dake kai kawo a fuska na nayi kafin nace"Iya bana tinanin sihiri ne domin bayan yaya Fawas da kuma Habib,duk duniya babu wanda ya damu dani balle kuma rayuwa ta domin hatta mahaifiyar da ta ɗauki cikina a jikinta na tsawon watanni tara na rayu cikin mahaifar ta,tayi naƙudata bata damu da ni ba. Balle kuma har ace wani ya damu da rayuwa ta har yamin sihiri".Na ƙarishe maganar ina ƙara fashewa dawani sabon babin kukan.




"Wohoho!ƴarnan yanzu rayuwar nan an daina kiwon dabba na mutum akeyi,wanda baka damu dashiba shikuma komai naka tsule masa ido yake yi".


Sai a sannan Habib yace"Iya ba wani sihiri kamar yanda ta faɗa zuciyar tace bata son gani na kusa da ita shine kawai".Saurin ɗago kaina nayi ina kallon shi meyasa Habib zaimin irin wannan fahimtar?,shi kaɗai nakeda yaƙinin zai fahimce ni?.Ashe shima fahimtar irin tasu Granny yamin na ganni cewa kamar faruwar hakan son raina ne.


UWATACE SANADI


Tsarawa/rubutawa



©Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________




Page 3⃣1⃣




Yana gama faɗin ya tashi yabar falon da kallo nabi bayansa yayin dayake ficewa daga falo,wasu hawayene suka shiga ambaliya saman kunci na Granny ma tashi tayi ta fita ya rage dagani sai Iya a falon.
Ita keta aikin lallashina nima ɗin daga bisani tashi nayi na wuce part ɗinmu,a falo na tarar da Habib yana zaune kusa dashi na tsuguna sai dana tsagaita kukan nawan sannan na shiga faɗin"Habib nasan na cutar dakai amma nima bayin kaina bane wallahi nima ako yaushe,burina na fatarta maka kamar yanda kaima kake ƙoƙarin kwatanta hakan a kaina".


Sai daya sauƙe wani ajiyan zuciya kana yace"Hibba bansan meyasa kike amfani da soyayyar danake miki ba wajen azabtar da zuciyata ba,amma na tabbata kinji abinda Granny ta faɗa zasu rabani dake"ya ƙarishe maganar cikin rauni.
Magana na somayi amma ya dakatar dani ta hanyar faɗin"Kiyi haƙuri komai zaki faɗa yanzu bazan saurare kiba tashi kishiga ciki".


Da gudu na miƙe nayi bedroom ina shiga na zube kan gado,ina sakin wani kukan mai matuƙar ƙarfi wanda nakejinsa yana fitowa kai tsaye daga ƙasan zuciyana.
Sosai nakejin raina yana min zafi yayin da wani tarin mai ƙarfi ya sarƙe ni,tashi nayi zan shiga banɗaki jiri ya ɗebeni ya dawo dani kan gadon dafe kaina nayi inajin yanda yake sarawa.


Ƙara yunƙurawa nayi na tashi hannuna na riƙe da kaina,na nufi banɗaki ina shiga nafara kwara amai sosai nake amayarwa jingina nayi da ƙofar banɗakin saboda jirin danajin yana ƙoƙarin yasar dani ƙasa.wanke fuskana nayi sai a sannan na lura da aman danayi wanda mafi yawansa jini ne.
Kukane ya kubce min nayi saurin toshe bakina ina silalewa ƙasa,sunayen Allah na shiga karantowa wannan wace iriyar rayuwace?,menene yake shirin faruwa dani?.
A hankali naja jikina na fito daga banɗakin bayan na ɗauro alwala hijabina na saka na tada salla,duk jikina ya ɗauki rawa ko sallan ma banyi ta da cikakken nutsuwa ba haka na sallame nan kan sallayan na zibe ina fitar da numfashi ɗaya-ɗaya.


Baccin ma ya gagareni sai ciwon kan daya tsananta gareni har aka kiran zuhr ina kwance a wajen,na tashi nayi sallan sai danayi sallan la'asar sannan na ɗauko maganin Habib na fito falo.
Ban tarar dashi a falon ba hakan yasa na fito na nufi part ɗin Granny acan cikin garden na hange shi,yana zaune kan kujerun cement irin waɗanda ake ginawa ɗina a cikin jami'o'i da suke zube a wajen.
Da sallama na isa gareshi amma tinanin da yayi nisan ciwo a cikinsa yasa baiji zuwata wajensa,sai dana zauna dab dashi ina karkaɗa ledar maganin dake hannuna sannan ya farga da zuwana.


Murmushi na sakar masa a lokaci guda na ɓalla masa maganin na miƙa masa,ya karɓa tare da afasu a bakinsa na miƙa masa ruwan yabi bayansu dashi.
Tashi nayi zan tafi ya tsayar dani ta hanyar cafko hannuna cak!na tsaya ba tare dana waigo ba,tasowa yayi yana ƙara damƙe hannuwana cikin nasa sannan yamin ishara da idonsa hakana mu tafi tare muka jero dashi muka nufa part ɗin Granny.


Afalo muka sameta tana zaune tare da Yasira sallamar da muka shigo dashi shiya sanya Yasira tashi tabar falon cikin sauri tayi ɗakinta.
Zama mukayi muna yiwa Granny barka da hutawa,ta amsa ba tare data dube muba tashi Habib yayi yabi bayan Yasira wanda dalilin hakan naji wani baƙin-ciki ya ziyarci zuciyata.
Furcin Granny ne ya faɗo min arai nacewa datayi wai zasu haɗa Habib da Yasira ƴar-uwarsa aure tunda ni nakasa samar mai da farin-ciki.


Tashi nayi ina maiyiwa Granny sallama na nufi part ɗinmu inajin yanda ƙirjina yamin wani mungun nauyi,ina isa na wuce bedroom bayan na lock ɗin ɗakin na saki kukana.
Sosai nakeyinsa numfashina har yana ƙoƙarin sarƙewa,lokaci ɗaya sai naji duk zaman gidan Grannyn ya gundure ni.tabbas nasan ina yiwa Habib wani irin son dako nima bansan adadinsa ba,haka nan kuma banji zan iya jure ganinsa dawace ƴa mace koda kowa Yasira ce.


Habib kuwa gefen gado ya hango Yasira ta takure tana hawaye,kusa da ita ya zaune yana cusa hannayensa cikin tarin sumar kansa a lokaci guda yana furzar da iska daga bakinsa.
"Kayi haƙuri ka yafemin na kasa riƙe maka sirrinka bada wani nufi na sanarwa Granny ba saidan ina tinanin kamar hakan zai kawo muku mafita a gareku".
Sai daya fuskanto ta kana yace"Ƙanwata bakimin wani laifi ba hasalima taimaka min kikayi na gano abunda ban saniba,ashe ganina ne kusa da ita baso kinga yanzu sai indinga jaye jikina kodan farin-cikinta".


Cikin wani kukan Yasira take faɗin"Hamma kanaji fa cewa sukayi zasu haɗamu aure wallahi Hamma bazan iya zaman kishi da matarka ba".
Taƙaitaccen murmushin gefen baki yasaka kana yace"Bakya sona ne daman ban sani ba?"saurin jijjiga masa kai tayi alamar a'a.Sannan ya ɗaura da faɗin"to kukan nan na menene?".


"Hamma banso ace nazamto silar dazaka sama saɓani tsakaninka da matarka".riƙo hannunta yayi yasa su cikin nasa kafin ya shiga share mata hawayen yana cewa"ki daina wannan kukan banso kinji,ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu abinda zai faru kedai ki tayani da addu'a Allah ya ƙarfafa min zuciyata ta iya jure duk abunda zai faru nan gaba".
Sosai tausayinsa ya ɗarsu a ranta ta share hawayenta ta nuna masa komai ya wuce,sannan suka fito tare basu iske Granny a falon ba dan haka suka fito suka nufa part ɗin mu.


A falo ya zaune yace mata taje ta tasoni muje gidan Bashir ɗin,ina kwance naji ana knocking ƙofar nace"wayene".
A ɗayan bangaren muryar Yasira na tsinkayo tana cewa"Anty daman Hamma ne yace inkin gama shiryawan ki fito ku taje gidan Bashir ɗin".
Runtse ido nayi da ƙarfi ba tare dana buɗesu ba nace"kice masa banjin daɗi bazan iya zuwa ba".
Juyawa tayi taje ta sanar dashi kamar yanda na faɗa masa,bai nuna wata damuwa ko kuma son yayi magana dani ba,ya miƙe ya fice yayin da Yasira ta rufa masa baya.




Tare suka jera har jikin motarsa,ina tsaye cikin window ina hangesu sai danaga ficewar motarsa kafin na dawo na kwanta lamau akan gadon.
Kuka nakeson nayi amma hawayen sunƙi zuwa,cikin haka har aka ƙira sallan magrib na tashi nayi ko bari kan sallayan banyi ba aka ƙira isha'i kasancewar nayi magrib ɗin a makare nayita.
Ina iddar da sallan isha'in naji ƙaran shigowar motar Habib,na zata part ɗinmu zai shigo sai kuma naga akasin haka domin Part ɗin Granny ya nufa.




Ganin haka ya sanyani komawa saman gadon na kwanta,figigi ta farka daga baccin daya fara fizgana sakamakon ji danayi kamar ana ƙoƙarin buɗe ƙofar.
Yana gama kiciniyar buɗe ƙofar ya shigo yayin dayake zara sifiya key ɗin daya buɗe ƙofar dashi a aljihunsa.
Gefen gadon ya zaune nisa dani kaɗan yace"tashi inason magana dake".tashi nayi jikina duk ba ƙwari kamar sabuwar haihuwar kazar da ruwan sama ya lakaɗa mata duka.
"Hibba su Granny nason aiwatar da ƙudurinsu nason haɗani aure da Yasira,banga laifinsu ba domin nasan ƙaunarsu gareni shiya jawo hakan.Tun kafin aurenmu yaje ko'ina kinason wargaza farin-cikin dake cikinsa meyasa?,nasan kinsan cewa hakan yana iyasa a kashe aure ko?meyasa kika aikata hakan ga raunanniyar zuciyar da batasan komai ba face soyayyar ki?".


Ya ƙarishe maganar yana ɗan sausauta muryarsa,sai dana haɗiye kukan dake shirin fito min cikin muryar datake bayyanar da raunin da zuciyata take ciki nace"Habib tabbas nasan na cancanci kowani irin hukunci daga gareka harma daga danginka,amma inaso kasani banyi kaina bane kamar yanda na faɗa maka jiya wallahi na rasa abinda kemin daɗi acikin duniyar nan,babu ranar danake fargaba irin ranar da Allah zai kamani da wannan laifin a gaban dukkan halittunsa.Bazan hanaka yin aurenka domin tabbas inayi hakan na tabbata azzaluma,kuma na tauye maka hakki.....".


Saurin kai hannunsa yayi ya toshe min bakina kana yace"ki daina faɗi haka in sha Allah inama fatan komai ya dai-daita basai ankai ga ƙarin auren ba,munyi magana da Bashir akwai wani malamin daya sani yana bada magani game da irin lalurarmu in sha Allah zai taimaka mana".
Hannunsa yakai saman wuyana zafi gau,magani ya ɗauko yabani nasha sannan muka kwanta ranar na ƙudurce zan bawa Habib dukkanin hakkinsa dana daɗe ina tauye su koda kuwa hakan na nufin ƙarshen numfashin dazanyi a rayuwata.
Ranar farin-ciki wurin Habib baya misaltuwa dan abinda bai taɓa tsammani bane ya faru,dan a hirar dasuka da Bashir har suna tinanin wai ko aljani ne ya aure ni.


UWATACE SANADI


Tsarawa/rubutawa




©Maimunah Tijjani Iyam


_________________________________


Page ɗin jiya ansama mistake wajen rubutun shine page 31 wannan kuma 32.


__________________________________


Page 3⃣2⃣




Haka nan washe gari na tashi da matuƙar ciwon kai ga kuma wata iriyar kunyar Habib ɗin da yayi dabaibayiwa zuciyata.
A ranar kuma shirya komawa katsina tare da Yasira har ƙasan zuciyata nake murnan komawar dazamuyi,muna gama kalaci mukayi shirin tafiya muna tsaye cikin harabar gidan Granny da Iya suka fito fatan sauƙa lafiya suka mana,Iya ta bani wasu addu'o'in.
Bayan ta jani gefe ta faɗamin wasu abubuwan dazan nayi domin ɗauke hankalin Habib ɗin,domin nasan har yanzu yana fushi dani dannewa kawai yakeyi.


Tunda muka baro cikin damaturu na lumshe idanuna ban boɗesu sai lokacin danaji Habib yana bubbuga kujerar motar dana jingina kaina aciki.Ware idanuna nayi wanda najisu har wani zafi-zafi sukemin sakamakon ciwon kan daya tsananta a gareni.
Na tsaida idona akan fuskarsa jidanayi ya ambaci sunan Baffa yasa ƙirjina dukan tara-tara,inajin Baffa yana cewa"Kabawa Hibban wayan".tunin nafara ruwan ƙwalla ina jijjiga masa kaina alamar yace bana kusa.


Shima hakan yaso ya faɗa masa amma ganin yanda Baffa yake surfa masifa yace"ki karɓa kawai"ya faɗa yana ɗan sausauta muryasa ta yadda Baffa bazai jiyo shiba.
Ganin banida niyyar karɓa yasa shi sanya wayar a handsfree,sannan yace"Baffa gatanan tana jinka".


"Wato duk abinda nake faɗa miki Hibba bakyajinsa ko?,ashe irin zaman dakukeyi da Habib kenan?,yanzu badan Hajiya jiya taƙirani ta sanar dani ba da haka zaki cigaba da cutar da wannan bawan Allahn ko?.Nace dashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login