Showing 24001 words to 27000 words out of 104857 words

Chapter 9 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7277

shiga bayyanawa Habib yanda suka haɗu dani.


"Tabbas tun ranar dana fara ganin hibba,nayi zargin itace domin a yanda habib ya siffanta ta,aka zana hoton ta kama ce sosai".
Take a wajen Daddy ya kira Granny yasanar mata tayi farin-ciki matuƙa.
Dining area muka wuce muka fara cin abinci spoon ɗin kawai naketa,juyawa a cikin abincin nakasa ci Ummi dake ankare dani tace" Hibba lafiya?".




Murmushi nasaka kafin nace"mmi lafiya kalau".Ina ankare da Habib sai satar kallona yakeyi,amma naƙi yadda mu haɗa ido dashi.
Muna gama cin abincin muka dawo falo yasira tace"Hamma ina tsaraba ta?".
Murmushi ya mata yace,"Ƙanwata tsarabarki nanan ɗauko min akwatin can".
Ya mata nuni da wani pink ɗin akwati taje ta ɗauko ta ajiye a gabansa.
Zungurin kanta Sayyid yayi tare da faɗin"kekam naga ranar dazakiyi hankali,mutumin dayaje jinya ina batun wani tsaraba kuma".


Tuno bakin tayi tana matsowa kusa da Hamma Habib ɗin.Buɗe akwatin yayi ya fara Ciro dogayen rigunan abaya yace"Ƙanwata ga tsarabar ake kaɗai na sayo amma yanzu na fasa baki a wat.........".
Sai kuma yayi shuru tare da sunkuyar dakansa ƙasa yana ɗan Sosa ƙeya.
Cuno baki Yasira ta marairaice fuska kamar mai shirin, yin kuka tana cewa"Ayya Hamma na kayi haƙuri ka bani ".
Murmushi ya saka yayin dayake cigaba da ciro kayan yace"sai kiyi kuma nidai na riga na faɗa miki".
Wasu turarurruka ma'abota tsada Habib ya ciro tare da matsowa kusa da Daddy, ya ladabtar da murya ya shiga faɗin" Daddy ga naka tsaraban".Cike da happy karɓa yana sanya masa albarka.
Ummi kuwa mayafai Habib ya sayo mata ta karɓa cike da farin-ciki,shi kuwa Sayyid wani danƙareren agogo Hamman nasa ya sayo masa.
Sannan ya tura akwatin gaban Yasira wacce tun ɗazu take ta rarraba idanu ganin, Hamma ya kusa gama rabon kayan ita baice ga nata ba.
Wani murmushi mai sauti,ta saka tare da ƙara jawo akwatin gaban ta tana kara duba kayan.Kallo ni tayi tare da faɗin"Anty zoki ga kayan mana".




"A'a basai na ganiba kaya sunyi kyau masha Allah".na faɗa ina sadda kaina ƙasa
Kafeni Habib yayi da ido,ko kiftawa bayayi da sauri-sauri ƙirjinsa ke bugawa.Na ɗauke idona daga cikin nasa,yana ɗago kansa suka haɗa ido da Ummi.


Wata iriyar kunya ce ta lulluɓeshi cikin sauri ya tashi ya nufi upstair yana murmushi.Haka na wuni ranan duk banida kuzari maganar Ummi ce ketamin yawo cikin kwakwalwata"yarinyar dakeso,wacce kayi jinya domin soyayyar ta".
Washe gari ina kitchen ina haɗa breakfast.Habib ya shigo yana sanye da farar jallabiya har ƙasa,a ƙofar kitchen ɗin ya tsaya yana kallona.
Nikuwa sai aikina nakeyi,don bansan akwai mutum awajen ba.Ajikina kawai naji ana kallona,ina juyo wa kuwa muka haɗa ido da sauri na sunkuyar dakaina ƙasa nace"ina kwana".




"Lafiya".


Ya amsa yayin dayake shigowa cikin kitchen ɗin,yana cigaba da cewa" bari na tayaki aikin".


Ban kulashi ba nacigaba da aikin danakeyi.Wuƙa ya dauƙa yafara yanka albasa yana cewa" Hibba I see like kamar bakiji daɗin ganina ba?".
Ajiyan zuciya na saka kafin nace"na isa nace haka kai da gidanku,ince banji daɗin dawowanka ba."
Fuskanto ni yayi sannan a hankali ya shiga faɗin"Nasan jiya kinyi mamakin furcin Ummi ko?".




Kaina na ɗaga masa alamar e,Sannan ya cigaba da faɗin "Hibba" cikin kakkausar murya ya kiran sunan wanda hakan,ya sanyani ɗago kaina na kalle shi sannan na maida idona ƙasa.
"Basan ina sonki ba sai,lokacin dana dena samunki a waya na cigaba da ɓoye hakan a raina har izuwa wani lokaci,yayin da hakan yamin babban lahani a cikin zuciya dalilin hakan iyaye na suka turani malesia.Dawowa ta kenan nazo auren Bashir shine ranan muka haɗu dake duk lokacin dana tinaki sonki ƙara dawowa sabo yake a cikin zuciyana,dan Allah ko sau ɗaya ne ki furtamin kina sona".
Tsare shi nayi da ido hawaye nabin fuskana kamar yanda zuciya ta tasha faɗa min,tabbas yau na ƙara gaskatawa banida wani masoyi a cikin duniyan nan da ya wuce Abbana da yaya Fawas sai kuma Habib.
A hankali nace" Habib wataran zan furta hakan a gareka."
"Meyasa sa wataran?,sai bayan cutar sonki dake addabar zuciyana ta kasheni sannan ki furta, min Hibba meyasa bakya tausayi nane?" Yaƙarishe maganar tare marairaice fuska.
Ɗauke kaina nayi kamar yanda,shima naga ya ɗauke kansa daga gare ni,sannan ya maida hankalinsa kan yankan albasan dayakeyi.
Ajiyan zuciya na sauƙe tare da goge hawayen dake bin fuskana nacigaba da aikina.
Yana cikin yanka albasan wuƙan ya yanki hannunsa,sakin wuƙar yayi ta faɗi ƙasa.
Cikin sauri na iso inda yake sai yarfa hannun yakeyi first aid box na ɗauko masa yayi dressing wajen.




Ɗago kaina nayi ina kallonsa nace" sannu".


Cikin halin ko inkula yace"riƙe sannunki ai daman ba tausayina kikeji ba".yana gama faɗin haka ya fice daga kitchen ɗin.
Da kallo nabi bayansa yayin dayake ficewa daga kitchen ɗin,A haka na gama girkin na jeresu akan dining sannan na koma,ɗakina nayi wanka doguwar rigar material nasaka maroon color sannan na fito falon.
Sayyid na tarar zaune na gaishe shi ya amsa cikin sakin fuska,sannan na zauna tare da ƙurawa tv kallo.
Muna zaune Yasira ta shigo tace "ayya Anty harkin gama break fast ɗin shine baki tasheni na tayakiba?".
" Ba komai Anty Yasira ai naga kina baccine".
Sauƙowar Habib daga upstair,shi ya dakatar da yasira daga maganar dazatayi.
Sanye yake cikin shigar shadda Navy blue, hular Kansa ma da rantsin blue ajikintaSajen fuskarsa ya ƙara kwanciya luf asamar haɓarsa.A hankali yake sauƙowa daga upstair ɗin yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa.
Gaishe shi Yasira da Sayyid sukayi a tsare yake amsa gaisuwar tasu nikam daman mun gaisa a kitchen.
A tare Ummi da Daddy suka fito,dukkaninmu muka gaishe su suka amsa sannan muka wuce dining muka fara break fast.
Tun da muka fara cin abincin babu Wanda yayi magana,sai Habib da yace "Sayyid ka shirya zamuje wajen Granny".




" To Hamma"cewar Sayyid ɗin.






Da haka muka gama cin abincin har compound muka musu rakiya,sai wani cin magani yakeyi ko kallon inda nake baiyiba suka tafi.
Suna isa cikin garin Damaturu direct new bura-bura estate suka nufa gidan Granny.
Wangale musu gate,gateman yayi suka shiga sukayi parking sannan suka fito suka nufi cikin gidan bakinsu dauƙe da sallama.
Ba kowa a falon sai house maid ɗin,Granny tana goge-goge ta rusuna ta gaishe su.




Sayyid yace "Granny fa?"tace "tana ɗaki tana salla".






"To in ta fito,kice mata mun tafi masallaaci".




Da to ta amsa sannan suka juya suka fita.
Masallaci muka nufa saboda ƙiraye ƙirayen sallan la'asar da aka farayi.suna dawowa suka wuco part ɗin Granny tana zaune a falon suka tarda ita.
Cikin farin-ciki ta tarbe su tana faɗin"lale da mutan malesia zance ko katsina".




"Granny yanzu kam sai dai mutan damataru"
Gaishe ta sukayi ta amsa tare da tambayar su mutan gidan,suka amsa mata da duk lafiya.
Dinnig suka wuce ta zuba musu dambu wanda yasha kayan lambu da mai,ga lafiyayyan yaji.sosai sukaci abinci dan ba ƙaramin daɗi ya musu ba.
Suna gama ci suka dawo falo kwanciya sayyid yayi akan ɗaya,daga cikin kujuren falon ai kuwan nan baccin gajiya ya ɗauƙa shi.
Kusa da Granny habib ya zauna tana mata tausa a ƙafarta,kallon shi tayi kafin tace"Babban mutum Suraj ya sanar da ni yanzu haka,kuna tare da wannan yarinyar cikin gidansa sannan ya sanar dani labarin rayuwarta ko wannen mu shaida ne akan irin son dake mata,amma ba musan manufar ka akan hakan ba.Babban mutum nasan halin kane kyautatawa dan girman Allah ka riƙe yarinyar nan da amana sannan kuma ka daraja ta".
Sosai maganganun Granny suka ratsa ƙalbinsa a hankali yake furta.


"In sha Allah Granny zaki same ni mai biyayya da dukkanin umarnin ki".


"Za muyi magana da Suraj ɗin,yanzu kam tunda mun samo maslaha ga matsalar sai a maida ta ga dangin ta mu nema maka auren ta,a yi abun nan hankali kowa ya kwanta"cewar Granny.




Sosai Granny ta masa nasiha sannan ya fita yaje gidan Bashir nan,yake sanar dashi maganar dasu tattauna da Granny ɗin.Sosai Bashir ya masa murna tare da masa fatan alkhairi sai da yayi sallan magrib a can sannan ya dawo.
Part Granny ya wuce nan ya tarda ta,zaune ita da Sayyid zama yayi yana cewa Sayyid."Ka tashi kenan malalaci kawai daga katsina,zuwa damaturu shine duk ka wani gaji haka".


Murmushi Sayyid ya saka kafin yace"Hamma kawai kwantawa nayi na huta shine fa,baccin ya sace ni".
Shima Habib ɗin murmushi ya saka haka nan ma Granny,sosai suka yi hirar su sannan suka ci abincin suka kwanta da gobe da wuri zasu koma zai ajiye Sayyid a kano sannan shi ya wuce katsina.
Washe gari da wuri suka shirya sukaci ɗan waken da Granny tayi musu,nan Habib yake tambayar Iya dan tun jiya dasuka zo bai ganta ba.
Granny tace"tayi wata tafiya ce zuwa ƙauye,ƙanin ta yana aurar da ƴarsa".
Sun sama rakiyan Granny tare da kyawawan addu'o'i ta musu,a kano Habib ya sauƙe Sayyid domin aikin sa daya bari a can ɗin sannan ya wuce katsina.
Koda ya iso office ya fara wucewa sai da tashi sannan ya wuco gida,part ɗin sa ya wuce direct ya nufi bathroom tare da sakewa kansa,ruwa sannan ya yasa kaya mara nauyi sannan ya kwanta nan kuwa baccin gajiya tayi awon gaba dashi.
Sai dab da magrib ya tashi alwala ya ɗauro ya fita izuwa masallaci,nan ya zaune har akayo isha'i sannan ya dawo ya wuce part ɗin Ummi.


Ina zaune ina karatun exam wanda muke dab da farawa cikin kwanakin nan,ya shigo falon ya zauna gaishe nayi ya amsa cikin sakin fuska yana faɗin"karatu akeyi ne?".


nace "e".Yayin dana fara harhaɗa littattafaina zan koma ɗaki,na cigaba da karatuna muryar sa ce ta dakatar dani yana cewa"Fatima tsaya inason magana dake".




Wani iri naji duk nasan Fatima suna na ne,amma ba kowa ke ƙirana dashi ba.ba tare dana juyo ba nace"inajinka".


UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


______________________________


Page 1⃣8⃣






Tashi yayi ya iso inda nake tsaye,yana fuskanta ta sannan ya naɗe hannayen sa a bayan sa.




"Munyi magana da Granny yau sannan izuwa yanzun na tabbatar da sunyi maganar da Daddy,akan maganar zuwa gidan ku nema min auren ki.Banason na tirsasawa zuciyar ki domin nafi son ta amshe ni cikin daɗin rai shin kina isona?zaki iya aure na?".
Baki nane ya soma rawa na shiga faɗin"Habib idan nace banason ka to nima nasan ƙarya ne,amma yanzu karatuna shine mafi muhimmanci a gare ni ,mu jingine wannan maganar sai zuwa wani lokaci"ina faɗin haka na wuce ɗaki na barshi tsaye a wajen.
Koda na koma ɗakin gagara na karatun yayi,hakan yasa na rufe littafin na lula izuwa duniyar danafi samun nutsuwa a cikin ta wato tinani.Ina zaune a haka Yasira ta shigo tana cewa"Anty kina nan ashe ke muke jira ki fito mu ci abinci.
Tashi nayi nabi bayan ta muka fito tare,muna gama cin abinci muka tattare wajen tare da Yasira,zan shige ɗaki Daddy yace"na zauna ya nason magana dani".dawowa nayi na zauna.
Ajiye jaridar dake hannunsa yayi sannan ya shiga faɗin"Munyi magana da hajiya kuma gobe in sha allah muke son muje gidan ƙanin mahaifinki da kika labarta mana yana zaune a kano,domin nemawa ɗan mu Habib auren ki.Dan haka muke son kimana kwantance duk dacewa ke zamu je".
Wani zazzafar ajiyan zuciya na sauƙe kafin nace"Daddy ina neman alfarma a ɗan jinkirta zuwan har izuwan lokacin da zan kammala karatuna".
"A'a Hibba aure baya hana karatuna,kamar yanda karatun baya hana aure.Na miki wannan alƙawarin zaki cigaba da karatun ki koda bayan auren ki da Habib ne,sannan ni zan kashe miki ko nawa ne har sai kin cimma burin ki"cewar Daddy.


Ummi ce ta ɗaura da cewa"Hibba muna neman alfarmar ki ki taikama mana wajen cero rayuwar Habib amincewar ki muke nema domin baza mu miki dole ba".
Da mai zan sakawa waɗannan bayin allahn,wanda suka bada gudumawa wajen cikar buri na?zuciyata tace kawai ki amshi buƙatar su ki auri Habib hakan zai zamto silar samuwar farin-ciki a zuƙatan su,domin na lura farin-ciki sa shine nasu.




A hankali nace"na amince Ummi,nagode Allah ya saka muku da mafifin sakayyar sa".
Habib da tun ɗazu yake jiran amsar dazan bawa tambayar Ummi,ya sauƙe ajiyan zuciya yana hamdala.
Sosai Daddy da Ummi suke samin albarka,sannan suka shiga tattaunar maganar tafiyar da zamuyi goben.Nidai tashi nayi na koma ɗaki a hankali nake sauƙe numfashi sama-sama yayin da wani kukan da bansan na menene ba ya kufce min.
Ɗan kwalli na na jawo na toshe baki na dashi,ina ƙoƙarin hana sautin kukan nawa fitowa tashi nayi na rufe ƙofar ɗakin sannan na dawo na kwanta na cigaba da kukan.




Da wasu idanun zan kalli Inna?,mezan cewa Baffa?,banida ƙwarin gwiwan zan iya haɗa ido da yaya Fawas.watakil ma su zarge ni akan rayuwar dana yi a ba gida ba.
Naso sai na kammala karatuna na zamto cikakkiyar ma'aikaciyar aikin jarida,sannan zan koma musu shiyasa ma ban taɓa yiwa su Ummi maganar son zuwa wajen su Baffa ba.
Kuka nayi sosai har ina ƙoƙarin shiɗewa ganin haka ya sanya ni tashi nayi alwala sannna nazo na fara gabatar da nafila,ina iddarwa na shiga neman sau-saucin ƙuncin da zuciya take ciki a wajen mahaliccina,anan kan sallayar bacci ya kwashe ni.


Washe gari duk muka shirya dan hadda su Ummi da Yasira zamuje Sayyid kuwa zamuje mu ɗauke shi a kanon,tunda muka hau titi nakejin faɗuwar gaba ban san abinda zanje na tarar ba a gano.
Muna isa cikin kano muka wuce,freedom college inda Sayyid ke koyarwa muka ɗauke shi dan daman Daddy ya sanar dashi game da tafiyar.
Muna isa cikin garin gano nafara kwantatawa Daddy gidan Baffa har muka,ƙofar gidan bansan sanda hawaye suka fa bin fuska na ba sai da naji Ummi ta dafa kafaɗata tana cewa"Hibba yanzu ba lokacin daya dace kiyi kuka ba ki share hawayen ki mu shiga".




Share hawaye na nayi sannan muka fito muka shiga cikin gidan dukkanmu har dasu Daddy,Inna muka tarar tana shiƙar wake,sallamar damuka shigo da itane ya sanya ta ɗago kanta tare da sauƙe idonta kan ƙofar shigawa cikin gidan.
Sake kwaryar dake riƙe a hannunta tayi,tana waro idanunta wajen tare son gaskaka abinda ta gani bakinta na rawa ta shiga faɗin"Hibba ce koko mafarkin dana saba neyi ne?".
Nima tunin hawaye suka fara kai kawo a fuskata nace"Inna nice"na ƙarisa wajenta muka rungume juna.
"Hajara fito fito kiga abin al'ajabi"Inna ta faɗa tana ƙara rungumo ni jikinta.
"Haba!Inna wai meye ne kike ta wani kwaɗa min kira haka".Hajara ta faɗa tana fitowa daga ɗaki tare da gyara ɗaurin ɗan kwalin kanta.




"Wa idona ke nuna min kamar Hibba?wato kin gama yawan duniyar nakin shine yau kuma,kika tino inda muke ko bayan kinsa ƙafa kin fice babu wanda ya ƙara saki a kwayar idon sa".Hajara ta faɗa tana tsaida idanunta akaina.
Cikin mu ba wanda ya kula ta,tabarma Innaa ta ɗauko ta shimfiɗa mana muka zauna sannan suka shiga gaisawa dasu ummi.


Inna tace"Hibba waɗannan fa ban shaida su ba".
Kafin na bata amsa Daddy yace"Inna alkhairine ke tafi damu,amma kafin mukai ga sanar dake zanso ganawa da shi ƙanin mahaifin natan".


"Adamu tun farar safiya ya tafi gona,amma yanzu duk inda yake nasan yana hanyar dawowa"cewar Inna.
Tsaki Hajara ta saka sannan ta tashi tayi shigewarta ɗakin bayan ta gama cillo mana harara.
Muna zaune a wajen Naffa ya dawo muna haɗa ido ya saki fartanyan dake saƙale a kafaɗarsa yana cewa"Mamana ke ce koko gizo idanuna kemin?".
Tashi nayi naje na durƙusa a gaban sa hawayen nabin fuska na nace"Baffa nice Baffa na dawo gare ka,ka yafe min na rashin bin umarnin ka nayi".


Nuni yamin da hannunsa kan na tashi daga durƙushewar danayi sannan yace"Hibba na yafe miki nima ki yafe min ƙuntatawa zuciyar danayi nasan nine silar komai daya faru dake,kaico! na dana gaza fahimta ƙuncin dana jefa zuciyar marainiya a ciki".




"Baffa na yafe maka",riƙo hannuna yayi kuka zauna akan tabarman sannan suka gaida dasu Daddy.
Nan Daddy ya shiga labarta masa yanda haɗuwar mu dasu ta kasance,har kuma da irin alaƙar dasuke son ƙullawa da dangin su.Sosai Baffa da Inna suka tausayawa irin rayuwar danayi a gidan Anty Amina.
Nan wajen suka tsaida magana akan yanda aure zai kasance suka sanya watanni biyu,Inna ce ke sanar da ni bayan bari na gida yaya Fawas yazo.Nayi kuka sosai lokacin da Inna ke faɗa min irin mawuyacin hali daya shiga.
Baffa na roƙa nace ya kira shi yace masa yana neman sa,amma kar yace masa na dawo hakan kuwa akayi a wajen Baffa ya kira yana sanar dashi yanason ganinsa gobe.
Sosai Inna da Baffa suka yaba da kamalar Habib da kuma halin dattaku irin na iyayen sa.Sai yamma sosai su Daddy sukayi shirin komawa amma nida Tasira zamu zauna muyi kwana biyu a wajen su Inna.
Muna zaune a ɗakin Inna nida Yasira munacin kwaɗon zogalen da Inna ta mana,Sayyid ya shigo ɗakin tare da faɗin"Hibba kije Hamma Habib yana kiran ki yana ƙofar gida".
Hijab ɗin na saka na fito shi kuwa Sayyid ya zauna ya faracin kwaɗon shima,a tsakar gidan na tarar da Inna da Ummi sunata firar su kamar dama can sun sa juna.
Yana zaune akan benci na hango shi na ƙarisa na zauna nisa dashi,wata leda dake kusa dashi ya miƙo min yana cewa"gashi waya ce ki riƙe a hannun ki dan kwana biyun daza kuyi a wajen su Baffa indinga samunki".
Kaina na kallon ƙasa ina wasa da yatsun hannuna waɗanda suka sha jan lalle wanda Ummi tasa aka mana kafin tahowar mu,nace"A'a nagode ka bashi bana buƙatar sa".
Tun farko zuwa na gidan su Habib Ummi ta saya min waya,amma na ajiye ta bana amfani da ita dan banda ma wanda zan ƙira da ita.
Ajiye min ledar yayi kusa dani sannan yace"gashi nan dai na ajiye miki,kuma nasa miki sim aciki na kuma samiki lambobin su Ummi da Sayyid a cik.....".
Saurin ɗago kaina nayi ina kallon shi wanda hakan ya sanya shi kasa ƙarisa maganar daya ɗauko.
Yaya Fawas na tino lokacin da ya sayo min waya ranar dazan tafi jami'a,irin kalmaman Habib ya furta min yana cewa"ya samin sim a cikin wayar kuma yasa lambarsa".
Saurin mayar da hawayen dasuka ciko idona nayi nace"nagode allah yasaka da alkhairi".
Sai daya saki taƙaitaccen murmushi kafin yace"amin ".
Wayarsa ce ta fara ruri ya ɗaga da sauri ganin sunan Granny ya bayyana cikin screen ɗin wayar.




Sai suka gaisa sannan take tambayar sa sun "iso lafiya?"don ta kira Daddy bai ɗaga ba"lafiya kalau Granny"ya amsa mata dashi.
Nidai maida hankalina nayi akan wayar da Habib ɗin ya sayo min,suka cigaba da hirarsu ban ankara ba naji ya miƙo min wayar yace "ga Granny zaku gaisa".




A hankali na karɓi wayar na kara a kunne na duk kunya ta rufe ni,sallama nayi ta amsa sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login