Showing 96001 words to 99000 words out of 104857 words

Chapter 33 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7349

ƙarin mutum ne da kuma yanda tsoro Allah yayi ƙaracin a zuƙatan al'umma jifa-jifa nake soma bakina acikin hirar tasu.Sayyid yaɗan musguta yana fuskanto Daddy sosai yace"Daddy daman Fadila ƙanwar Yaya Fawas ce mun dai-dai kanmu da kanmu nakeso manya su shiga cikin lamarin a tsaida magana tunda yanzu yana ajin ƙarshen a makarantar sakandiri"yakai ƙarshen zance yana sunkuyar da kansa ƙasa yana ƴar dariya.
"Babu komai zamu tattauna maganar da Granny sannan mu tsaida ranar zuwan namu".cikin saurin Sayyid ya ɗago kansa yana faɗin"Nagode Allah ya ƙara girma da nisan kwana masu albarka".duk muka amsa da amin kafin nace"Ah to lalle yanzu ya kamata a ninka biyayyar da ake min dan na zama surika tun yanzu".
"Ai daga yanzu kin zama babbar Anty,Allah yaja da kwanankin Antynmu"cewar Sayyid maganar sa ta samu dariya sosai Ummi tace"banda lalacewa zamani wai ace yaro dashi ake maganar aurensa mu lokacin mu mijinma bazaki sanshi ba sai bayan an ɗaura an kaiki ɗakinki kuma a hakan ake zaman lafiya".Habib yace"Haka ne kam Ummi ku ai lokacin ku ƴaƴan akwai haƙuri amma gaskiya mukam bazamu yarda da wannan tsarin ba yanzu"Ummi ta kai masa duka a kafaɗarsa yayi saurin gaucewa yana dariya haka nan ma muda Sayyid.Maganar da Daddy ya soma yi ya katse mana hanzarin mu gabaɗaya"Hajiya na manta ban sanar da kuba Habib kawunka Isma'il na nijar yamin magana akan Amina cewa yasano a bashi dama ya shiga cikin manemanta,gobe Hajiya zakuje ki sanar da ita duk yanda kukayi sai ki faɗa min na kuma sanar dashi".
Washe baki har kunne Ummi tayi kana tace"Kai Alhamdulillah lamari yayi daɗi wallahi Allah ya haɗa kansu idan shine mafi alkhairi ga Amina"duk muka haɗa baki wajen furta kalmar amin,na tabbatar idan Anty Amina ta auri kawu Isma'il zata huce takaicin aurenta da Malam Habu gashi daman naji Farida nacewa matarshi mahaifiyar su Nabiha shekara ɗaya kenan da rasuwarta Adda Hanne ta sako shi gaba akan batun ƙarin wani auren Allah ya tabbatar da wannan auren ni kaɗai nayi maganata kuma na amsa abina.nan muka cigaba da hirar har aka ƙira sallan Asr sannan su Daddy suka fita masallaci nida Ummi duk muka wuce ɗaki,sai danayi sallan magrib sannan na fito na haɗa mana dinner na jeresu akan dinning sannan na koma ɗakin Ummi na tarda ita tana wanka a Mu'afsa tagama tana tsantsameta da towel na iso na zaune gefen gadon ina cewa"Ummi wanka kuke yine?"tace"Eh wallahi na bata madarar tane shine na mata wanka nasan babu jimawa zatayi bacci".sai data shirtaya muka fito zaman jiran dawowarsu sannan muka ci abinci mukayiwa juna sai da safe muka kwanta ranar mun taba dare muna waya da Habib sosai wanda hakan yasa naji dul damuwata ta hau.
Sai da akayi sadakan arba'in ɗin Yasira sannan muka koma gida na sanar da Hajja komai ta cika da mamaki tana ƙara gaskata wannan kalmar ta malam bahaushe da yake cewa"Makashinta na tare dakai".zuwar Granny sadakan suka tattauna da Daddy akan maganar turawa nemawa Sayyid auren Fadila,ta kuwa amince domin ta yaba da tarbiyarta.ni nake sanar da Anty Amina magaanar Kawu Isma'il.
"Hibba nifa yanzu wallahi lamarin aure ya fice mini a rai kwata-kwata gwara nayi zamata a gidanmu na iya bautar Allah har lokacina ya iske ni".nace"Anty Amina ai shima auren wani nau'in bautar Allahn nan,dan Allah ki bashi dama wallahi zakiji daɗin zama dashi".ta numfasa kafin tace"to babu komai zamuyi maganar da Abba duk yanda yace hakan za'ayi".naɗan murmusa nace"Yauwa Anty muzo daura musha biki ba"tayi saurin katse ƙiran cike da kunya.
A cikin satin daya kama su Daddy sukaje nemawa Sayyid auren Fadila a azare,watannin uku aka sanyan da zaran da ƙare makaranta da wata ɗaya kenan,satin sama kusa mutan nijar suka dira a daura neman auren Anty Amina sosai Malam Mahira ya yaba da dattakunsu aka tsaida da lokaci nanda sati uku dan baso ake yaja lokaci ba.a san nan fa Aliyu Haidar ya bayyanar da soyayyarsa da Anisa da duk dangi.


UWATACE SANADI




Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


___________________________


Page 6⃣0⃣


Cikin wannan satin muka fara jarabawar ƙarshe a makaranta,duk da har yanzu mutuwar Anty Hajara bata gama bari raina ba amma na maida hankalina kaf ga karatu zuciyata tana yawan hashasho mini ina gab!da cika burin Abba da Yaya Fawas na zama cikakkiyar ma'aikaciyar aikin jarida.ranar na dawo gida a gajiye dan sai jarabawar ranar ta caza mana kai sosai gashi yamma ta fara kawo kai,a hanyata ta dawowa gida traffif line ya tare ni lokaci zuwa lokaci nake saki siririn tsaki ina jijjija Mu'afsa da duk ta gama yin laushi tsabar gajiya tana kwance a gefena acikin motar.
Kona da iso gida na iske motar Habib a cikin parking space hakan ya tabbatar mini har ya dawo na saɓe Mu'afsa a kafaɗata sannna nayi cikin gidan da sallama ɗauke akan leɓɓana na turo ƙofar falon na shiga yana tsaye a dinning ya amsa sallama kafin na isa gareshi har ya tako gabana ya karɓi Mu'afsa nace"Gorko am girki kayi haka kai daka dawo daga office nasan kuma ka gaji,ai daka bari na dawo na mana"nakai ƙarshe ina shagwaɓe fuska ya shafo kuncina haɗin da cewa"Debbo am ai naga na dawo da wuri ne kuma babu abunda nakeyi shiyasa nace yau dai kaɗai bari na hutar dake na mana girkin"na rusunar da ƙwayar idona ƙasa kana nace"shiyasa ako yaushe bana shakkar bugan ƙirji nace mijina na daban ne ko a cikin ƴan maza".ya riƙo hannuna muka ɗauki hanyar bedroom har mun kai ga ƙofa yace"shiyasa nima ako yaushe idan na rasa wani abu sai naji cewar Allah ya mini gata fiye da duk wani ɗa namiji a duniyar daya azurtani da samu nagartacciyar mata".
na rausayar da kaina cike da kunya sannna na fara yiwa Mu'afsa wanka sannan na shiryata suka fito falo sannna nima na shiga wanka sai danayi sallan magrib sannan na fito na amshi Mu'afsa ya fita masallaci karatun jarabawar da muke dashi gobe na farayi yayin da na ajiye Mu'afsa akan kekenta na koyan zama.
Sai bayan isha'i sannan Habib ya dawo mukaci abincin ina ta yaba daɗin da abincin yayi shi kuwa sai dariya yake mini haka muka kammala muka kimtsa wajen sannna muka dawo falo muka zauna.
"Gaskiya ya kamata na yiwa Ummi magana a samo mana mai raino,ke ki huta ga makaranta ga kuma aikin gida".na gyara zaman Mu'afsa akan cinyoyina tana zuƙar madararta kana nace"Nagode Allah ya saka da alkhairi amma Mu'afsa amana ce a gareni tun ranar data zo duniya,zanzo ace ni nayi dawauniyar ta da kai dan na cika yaƙinin Yasira a gareni".ya riƙoni haɗi da cewa"haka ne Allah ya raya mana ita"na amsa da amin.
Haka na washe gari kafin na tashi Habib ya gama haɗa komai na karin kumallo mukaci kafin na shiga nayiwa Hajja sallama ya sauƙe ni a makaranta.haka rayuwa ta cigaba da juyawa a gareni izuwa yanzu kam zan iya cewa Habib ya maye mini gurbin duk wani abunda na rasa a baya,baya barina nayi ƙunci balle ruwan hawaye ya zuba daga idaniyata.ana cikin haka bikin Anty Amina da kawu Isma'il ya taso,Daddy shi ya ɗauki nauyin yi maka kayan ɗaki gabaɗaya ni kuwa na haɗa mata kayan kitchen sosai da kuɗin da Habib ya bani nayi amfani dashi.
Ban sama zuwa bikin da wuri ba dan har sai da su Ummi suka rigani zuwa saboda jarabawar da mukeyi sosai na maida hankali ga karatu saboda itace ta ƙarshe,sai ranar ɗaurin auren Habib yazo ya ɗauke ni a makaranta Mu'afsat kuwa tun safe damuje wajen Ummi suka tafi dauran da ita kafin na zana jarabawa muma muzo.sosai yake sharara gudu akan titin dan ya sama ɗaurin auren cikin ƙanƙanin lokaci kuwa muka iso a ƙofar gida ya tsaya da ƴan ɗaurin aure suka cika maƙil!ni kuwa na shige ciki bayan mun gaisa da Aliyu Haidar dasu Khalifa wanda suma suka zo ɗaurin auren.
Ɗakin dasu Ummi suke na nufa a gurguje nayi wanka na sauya shiga muka zauna dasu Ummi da Anty Amina har Balaraba tazo dai-dai sauƙowa daga sallan juma'a aka ɗaura auren kuma a lokacin za'a wuce da Amarya maraɗi,iyaye suka fara mata nasiha hadda Ummi ina riƙe da hannunta muka fito waje wajen motocin dasuka zo ɗaura amarya sai da ta shiga motar kafin na ƙara yalwata fara'ar fuskana nace"Allah ya bada zaman lafiya,Allah ya kauda sharri ya kawo ƙazantan ɗaki".can ƙasa ta amsa da amin tana ƙarawa da cewa"saura kuma kar kizo min".
"In sha Allah zaki ganni"nafaɗa ina maida marfin ƙofar ina rufewa.ƙanwar mahaifiyarta dana Malam Mahiru sai kuma Balaraba su kenan suka tafi kai amarya sai da motar ta ɓace mini daga gani kafin ya ɗauki hanyar shige cikin gidan maganan da Aliyu Haidar ya fara min ya sani waigo tare da Habib suka taku inda nake tsaye.
"Kinji mutuminki ko wai ya matsu a aure nashi auren".na saki murmushi kafin nace"Ai kuwa dai zama mu fasa baki shida ko gaisuwa baya zuwar mini,kaga Sayyid ai daya iya allonsa zai kwance yasha".shima taƙaitaccen murmushi ya saka haɗi da cewa"With all respect Antynmu ina miƙo gaisuwa"kafin nayi magana Habib yayi saurin faɗin"Bamaso sai dama kuma ƙora".
Haɗe rai yayi yana watsawa Habib idanunsa na mazan fama yace"Ai bakai a ciki,Antynmu nidai yanzu zan tafi a taya mu da addu'a.
"Allah ya kiyaye hanya Allah ya tsare"duk suka amsa da amin sannnn ya miƙo min Mu'afsa dake hannunsa"Antymu wannan yariyar ta shiga raina fiye da zato wallahi,kodai zaki bani ita ne".na gwalo idanu waje nace"Lalala!wannan kyautar da wuya domin Mu'afsa wani bangare na jikina ne kai dai zan baka Anisa naga salon naka kiwon tukunna".Duk suka murmusa kafin ya ciro ɗaurin kuɗi ƴan dari bibiyu yace a sayawa Mu'afsa Sweet nayi godiya sannan mukayi sallama da Khalifa suka tafi na koma wajen su Ummi a cikin gida.
Sai da mukayi sallan isha'i kafin muka baro daura Mahaifiyar Anty Amina tayi ta yiwa Ummi da Daddy godiya haka nan ma Malam Mahiru musha albarka daga bakinsa,Gidan Daddy duk muka sauƙa a part ɗinsa.
Kwanaki biyu a tsakani da dawowar mu daga daura ranar ina makaranta nabar Mu'afsat wajen Ummi saboda ba daɗewa zanyi ba,mun fito daga exams Hall na ciro wayata daga jakana missed call ɗin Habib huɗu a wayata,Yaya Fawas kuwa shida Ummi biyu na ruɗe zuciya na raya mini ko wano abunne ya kuma faru.nayi saurin faɗawa cikin mota na tada ita na kuwa hau titi sosai nake sharara gudu har na iso ko parking ban gama dai-daitawa ba na fito a falo na iske dukkansu cike da mamaki nace"Yaya Fawas yaushe kazo?".Ummi ce ta amsa min da cewa"An sama labarin Mahaifiyarku ne a can jahar Zamfara shine yanzu zamuje".zuciyata tayi mumunan tsikewa saboda mafarkin danayi akan Umma daren jiya tana cikin mummunan yanayi.
Ban kuma furta wata kalmar ba Daddy yace"Hibba ki kwantar da hankalinki in sha Allah zakuje ku sameta cikin aminci kuma ga Hajiya ma da ita zaku tafi da Sayyid nima gobe zanje Damaturu na sanar da Granny,a cigaba da addu'a.maganar jarabawar da kukeyi kuma zansa a zana miki har ku dawo".
Kaina kawai na jinjina sannna muka fito daga falo nida Ummi muka shiga motar Sayyid.Habib da Yaya Fawas kuwa suna mota ɗaya sosai ya kwantar mini da hankali tare da mana fatan sauƙa lafiya bayan ya ƙara jaddarawa Sayyid cewa da zaran mun isa ya ƙira shi ya faɗa masa.haka muka ɗauki hanyar jahar ZAMFARA tunda muka fara tafiyar na nema nutsuwata na rasa ko abincin da Sayyid ya tsaya ya sayo mana kasa ci nayi rabunmu da Umma shekara goma kenan da ƴan kai yau gani hadda aure da ƴa.
Kukan zuci nake yi mai matuƙar raɗaɗi da ƙuna sai yamma sosai muka isa cikin jahar zamfara gidan wani aminin Daddy muka sauƙa nan matar nada kirki aihun dan ta tausaya mana matuƙa muka kwana sannan da safe muka fara shirin nufar ƙaramar hukumar ƙauran Namoda nan akaji labarin Umma,tsakanin jiya da wayewar safiyar yau na fahimci akwai abunda Habib da Yaya Fawas suke ɓoye mini to menene shi?tambayar dana watsawa kai kenan kenan dana kasa karantar amsarsa a fuskokin Habib da Ummi.da wuri muka isa cikin ƙauran namoda muka zarce wata unguwa mai yawan cunkoso da yalwar halittu birjin da Sayyid yaja ya sani ɗauke kaina ƙarewa yanayin unguwar kallon dana keyi Ummi ta faɗa surfa masa faɗan yayi duƙi da ita a hankali duk muka fito ina goye da Mu'afsat.koda da kuskure Habib bai yarda muka haɗa ido ba haka nan suka wuce daga nida Ummi muna biye dasu.tsukakkene gida ne mara yalwan fili wata dattijuwa muka iske tana dama koko a ƙofar ɗaki sallamar da muka shigo da ita ya sanyata watso ƙwayoyin idonta akanmu sannan ta amsa dana binmu da kallon rashin sani muka ƙariso muka zauna akan tabarma dake yashe kusa da ita.
"Bayin Allah ban shaida ku ba daya ke idon tsofa ba gani nake dasu sosai ba,Allah dai yasa ba wani masifar Bashari ya ɗauko min ba".
Habib ya ɗan musguta kana yace"Baaba daman shi Basharin muke nema Allah yasa yana nan".
Sai data zame daga zaman datayi kan dakalin ƙofar ɗaki izuwa bakin tabarmar sannna ta shiga faɗin"Bashari baya nan amma bana raba ɗayan biyu yana can wajen shaye-shayensa sai anjima kuma zai dawo ya ɗauki wannan matar dayazo ya jibge mana a gida ya tafi yawon bara da ita".
Cike da wani irin hanzari Yaya Fawas yace"Ina matar yanzu zamu iya ganinta"
sai datayi nisa kafin tace"ya gargaɗe ni akan ko ɓako nayi kar na sake na sanar dashi zaman matar nan a cikin gidan nan,amma inkun tabbata cewa cikinku.babu ɗan sanda zan nuna muku ita".sai a sannan Sayyis yace"Meyasa mu zaki nuna mana ita bayan kince ya hafa miki sharaɗi akan hakan?".


"Ɗan nan saboda nagaji da ganin yanda yake yaudarar mutane da sunan cewa mahaifiyarshi ce suna buƙatar taimako,har yake yaudarar masu raunin zuciya akan hakan sau ɗaya ya lamince min na bata abinci kullum tana ɗaki,ranar daya shawo giyar har fyaɗe yana mata.Bashari maraya ne dukkan iyayensa suna ƙasa kakarsa ce ta bangaren Uwa amma baya ganina da kima dan Allah ku ceci rayuwar baiwar Allahn nan ku fitar da ita daga cikin gidan nan".sakake na tsaya ina bin bakin wannan matar da kallo muda mukazo neman Umma kuma mezai kawo mu nan,wacece wannan matar da suke magana akanta meye haɗin tafiyarmu zuwa Zamfara da ita?.maganar Ummi ta dawo dani daga wannan tinani na ƙwaƙwalwata"Dan Allah ko zaki fito mana da ita muganta".
"Bazata iya fitowa ba domin ko tsayiwa akan ƙafafunta bata iyawa balle har ta taka su,sai dai ku taso mu shiga ɗakin tare".
Ummi ta riƙo hannuna bayan ta amsh Mu'afsa ta damƙata ga Sayyid duk mukabi bayan wannan dattijuwar,a ƙofar ɗakin muka tsaya tashiga waiwaigen dutsin da zata ɓalle kwaɗon da aka garƙamawa ƙofar,Habib ya ɗauko wani dutsi ya shiga ɓalle kwaɗon sannan ya cire shi ya yar gefe guda duk muka ɗuru cikin ɗakin nikam fargaba da kuma tsoro sun kwashe kaso mafi girman yawan a zuciyata.yayin da bangare guda kuwa nake cike da tsagwaron mamaki.
Sautin kukan da yaya Fawas ya fara fitarwa a hankali ya sani kai gubana ga matar dake shimfiɗe akan fasheshshen simitin ɗakin,gefenta ɗaya ya janye bata motsa shi gabaɗaya ga ƙanjame ko wani mai cutar sidan ya fita kyawub gani,fatar jikinta duk ta nannaɗe wuri guda halittun jikinta sun sauya matuƙa inka ganta zakace yariyace ƴar shekara tara saboda yanda ta kuma ƙanƙancewa jiri ya shiga ɗebata na fizgo numfashina da ƙarfin gaske nace"UMMA"na nufota a matuƙar gigice cak!na ɗage yaya Fawas daga kusanta ko nima bansan inada wannan ƙarfin ba sai yau,na ɗagota daga cikin wannan yashin ɗaki na rungume a ƙirjinaYaya Fawas ya zare babban rigarsa,ya rufa mata a jikinta da babu komai dangin sutura.ɗimin hawayen dake sauƙa ajikina yana ratsa ni duk ɗakin kuka mukeyi har kakar Bashari,na ɗago ta daga jikina ina share mata hawayen da take yi"Umma ki daina kuka ga munan munzo kinga Hibba ce ga kuma Yaya Fawas"na kai ƙarshe ina janyo hannun Yaya Fawas na haɗɗ da nata na riƙe na daɗe banga hawaye a fuskar Yaya Fawas ba ko sanda Abba ya rasu baiyi irin wannan kukan ba.
Ganin yanda numshina ke fita da wani irin ƙarfi da kuma ƙara yasa Ummi isowa gareni ganinta kusa dani yasani tsananta kukana nace"Ummi kinga Umma ce a cikin wannan ƙaramin yanayin daman na daɗe ina mafarki da ita cikin mummunan yanayi"nakai ƙarshe ina kwanto da kaina jikin Ummi ta fara bubbuga bayana cikin sigar lallashi hawaye na zuba mata.
"R-R-Ruwa-a-a"Umma ta faɗa dalla-dalla,kakar Bashari ta fita da saur i ta dawo da kofin ruwan a hannunta ta fara bata,na ɗago na karɓa ruwan na fara bata da kaina dan gani nayi kamar bata sanya mata a bakinta,"Mukai ta asibiti a duba ta"cewar Habib.
"Yaro ku barni!ku barni!!,ko yanzu na mutu na mutu cikin farin-ciki naga ƴaƴana"wannan maganar ya ƙara sanya mu sakin wani kukan.ta mana alama nida Yaya Fawas akan muzo muka matso kusanta sosai ta shiga faɗin"Ban kasance irin uwar da ƴaƴanta zasuyi alfahari da ita ba,ban kasance cikin matan da mazajensu suke alfahari da samun su ba.ban ciba ci rayuwata tun lokacin ƙuruciya ba har girma ya zo min.na cece ku dana kasa baku tarbiya kamar kowacce uwa na kasa janku a jiki kamar ko wasu ƴaƴa.nayi nadamar yakice ku daga jiki danayi nayi nadama yanda na galzawa rayuwar Sule da abunda ya tafi na bari.sai danaga sakayya tun anan gidan duniya Allah ya nuna min iyakata,bayan aurena da Cindu sabon mijin dana aure duk da ba musulmi bane akan bai hanani aure sa ba muka tattata muka koma can garinsu Edo a nan na gane ɗan ƙungiyar shan jini ne na nemi ya bani takardata ya hanina daga ƙarshe ya kulle ni a ɗaki babu ci babu sha ko ranaa bana gani.wata rana nayi nasarar fice daga gidan cikin duhuwar dare nayi tafiya na tsawon lokaci da ƙafata.amma sai daya cin mini ya ɗaureni ya bamar gidan ranar ya duke ni kamar bazai barni da numfashina ba ya maida ni ɗakin ya kulle duk wayewar safiya sai y kawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login