Showing 99001 words to 102000 words out of 104857 words

Chapter 34 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7326

wasu ƙattin maza uku dukkansu sun kwanta dani,bayan wani lokaci cikin dare ya fito ya yasar dani bakin titi wasu samarin mashaya mukayi zina dani a baina jama'a amma babu wanda ya kawo min ɗauki.wani mai mota ya ɗauki ya kaini Lagos ya yar dani a bakin gada anan na fara bara a bakin danger,inason dawowa potiskum amma kona mota bani dashi,ciwo yaci ƙarfina har yakai banayi fitowa barar wata rana mota ta kaɗe ni ya kuma tsere aka kaini asibiti aka tabbatar ina ɗauke da cutar mai karya garkuwar jiki sannan akwai ciki dake maƙale ƙasan marata.tun da aka sanar da wannan batun suma waɗanda suka kawo ni asibitin basu ƙara waiga taba,cikin dare na gudu daga asibitin saboda banda kuɗin dazan biya su,na zubar da cikin ta hanyar ɗirkawa kaina ruwan gishiri.na kuma haɗo ciwon shanyewa ɓarin jiki shine muka haɗo da jikan wannan baiwar Allah daga lagos ya ɗauko ni izuwa nan zamfara ya fara yawo bara dani da sunan mahaifiyarce ni muna buƙatar taimako domin lalurar danake ɗauke da ita,mutane da yawa sun tausaya mana su ɗauki kuɗi su bashi,ya dawo dani cikin wannan ɗaki ya kulle da dare kuwa ya min fyaɗe ta ƙarfi".ta ƙarishe wani tari mai ƙarfi yana sarƙeta kakar Bashari ta fara bata ruwa,a hankali na zame jiki daga na Umma zuciyata tana luguden tara-tara wai daman duk maganar dasu Habib sukayi a waje akan Umma ne?innalillahi wa inna ilaihir raji'un,a gaban mijina da kuma surikata Umma ke irgo mana adadin mazan da sukayi lalalata da ita.haɗuwar ta farko kenan da Umma amma da wannan baƙin labarin kunnuwansu suka fara saurara,na tausaya mana nida Yaya Fawas matuƙar tausayi domin mu ababen tausayi ne.ji danayi kamar ana shigowa cikin gida duk muka baza kunnuwan mu ɗauke da wakar RUSH na mawaƙiya AYRA STAR a bakinsa ta shigo a buge tatil"Jar uban can wani ɗan kutumar uban ne ya buɗe ƙofar ɗakin nan, bana ce kar wanda ya kuskura ko kusan ƙofan nan yazo ba ina Kakan ne Dija mai masa kina inane?".
Duk jikinta baiɗaya ya ɗauki rawa ta fita waje ta same shi tana faɗin"Bashari ne ya dawo".
Wani irin huci yaya Fawas yake fitarwa ya miƙe yabi bayan Kakar Bashari,yana daga tsaye yana yalinsa na wanda yake a shaye Yaya Fawas ya damƙo wuyarsa ya fara kakakin mutuwa ya shiga kai masa duka ta ko'ina yayin da Sayyid ma ya fito ya jona shi sosai suke dukansa.duk muka fito babu abunda Kakar takeyi sai kuka tana faɗin"Dan Allah kar ku kashe min shi,wallahi shi kaɗai nake dashi a duniya duk iyayensa sun rasu maraya ne.ku masa kowani irin hukunci amma dan Allah kar ku rabani dashi".
Ummi ce ta riƙo Yaya Fawas yana janye shi Habib kuwa ya riƙe Sayyid duk da hakan basu daina kaiwa Bashari duka ba.Yaya Fawas da yayi nasaran ƙwace daga riƙon da Ummi ta masa ta zari bukacin ƙarfe dake gefe ya makawa Bashari a goshi,jini ya fara tsiyaya ya ɗaga da niyyar sauƙe masa a karo na biyu kakar tasi saurin shiga tsakaninsa da Bashari kula takeyi sosai tace"inba kashe shi zakayi ba ka barshi haka idan dukan da kuka masa bai ishe ku gani nima ku daka,nasan Bashari ya aikata kuskure babban kuma ya cancanci tsatstsauran hukunci".
Sauƙe bokitin Yaya Fawas ƙasa ya faɗi yana hucin ɓacin rai,ban taɓa sanin Yaya Fawas yanada taurin rai irin yau ba koda yake bahaush yace "IDAN ANA DARA FIDDA UWA AKEYI".
"Wallahi wallahi sai ka kwana a hannun ƴan sanda sai ka girbi abunda ka shuka dabba kawai dan ko dabba bazai aikata abunda ka aikata ba,in sha Allah sai kayi wulaƙantaccen ƙarshe".cewar Sayyid ya faɗa yana nashi hucin kwance a ƙasa cikin jini suka bar Bashari numfashinsa na fita ɗai-ɗai ga goshinsa dake fitar jini har yanzu ihun da Ummi ta saka ya sanya mu shigewa wajen Umma a guje as ones.duk jikinta ya ɗauki rawa Habib yace mu fito da ita mu tafi asibiti haka nida Ummi muka ɗauko ka izuwa wajen inda muka faka mota muka shiga da ita nida Ummi.
Sayyid ya jawo Bashari kamar kayan wanki ya saka shi a booth ɗin mota kakar sa sai makiya take masa amma kota kanta bai biba,da mungun gudu muka isa asibitin aka shiga da Ummz yayin da likitoti suka rufu akanta domin jefo rayuwarta,nan ƙiran Daddy ya shigo wayar Ummi lokacin daya ƙira yana tare da Granny"Hajiya wai meyake faruwa,na ƙira wayoyinku dukkan bakwa amsa ƙira,ina fatan an dace?".
Wani numfashi mai nauyi Umma ta fesar kafin ta shiga bayyanawa Daddy duk abubuwan da suka faru,daga shi har Granny babu wanda tausayin Umma bai dirar masa a rai ba.Daddy yace"Yanzu ina Sayyid ɗin yakai shi yaron".
"Ina kyautata zaton afishin ƴan sanda ya wuce dashi tare da Fawas suka tafi".ya kuma cewa ta haɗa shi da likitan asibitin suyi magana,a Habib ta miƙawa wayar ta sanar dashi yanda sukayi da Daddy,ofishin likitan ya nufa bansan mai suka tattaunaba suka fito tare likitan yake sanar da Ummi cewa.sunyi magana da Daddy yace yanzu su mata abunda ya dace zuwa gobe mun taho katsina daga nan kuma zai shirya mana yanda zamuga doctor a ƙasar moscow.
Haka akayi su kayi ƙoƙarin dai-daita numfashinta ta hanyar maƙala mata robar iska.Yaya Fawas da Sayyid kuwa ofinshin ƴan sanda suka miƙa Bashari ga hukuma DPO ɗin division ɗin ya tabbatar musu da doka zaiyi aiki.sai yamma sosai sannan suka dawo asibitin,bayan isha'i haj.Rashida matar aminin Daddy tazo ita da ƴaƴanta mata biyu,Ummi ce take kwatanta mata asibitin awaya har dare ta tsala basu barmu munga Umma ba sai dai mu leƙe ta ta window.
Tsawon dare wannan ranar ban iya tsurawa ba har akayi ƙiran assalatu farkon na tashi sai danayi sallah kafin na tada Ummi ma tayi nayiwa Mu'afsa wanka zuwa ƙarfe bakwai duk mun shirya,nurses suka fito da Umma aka sanya ta cikin motar Habib robar ƙarin ruwan da aka mata yana nan a jikinta.nida Ummi kuwa motar Sayyid muka shiga sai da muka jira dawowarsu daga ofishin ƴan sandan da sukaje shida Yaya Fawas.daren jiya Habib ya ƙara mokawa wajen Kakar Bashari ya kwantar mata da hankali sosai tare da bata tallafin kuɗi.
Motar Habib Yaya Fawas ya shiga yayin da Sayyid yake jan motar da muke a ciki nida Ummi,tana riƙe da Mu'afsa akan cinyarta nidai gabaɗaya hankali da nutsuwata sunyi ƙaura daga gangan jikina,har mubar cikin jahar Zamfara muna dab da shiga cikin Zaria Sayyid ya amsa wani ƙiran da daga ni har Ummi bamu da masaniyar da wanda yayi ƙiran.
Salatin dayake jerawa ɗaya nabin wani ya sanya Ummi tambayar sa lafiya?,ya faka motar a gefen titi ya juyo ya kalle ni hawaye yana taro masa a ido nace"Sayyid lafiya wai meyake faruwa ne dan Allah ka sanar damu".
Shuru yayi na tsawon mintuna biyar kafin yace"su Hamma ne sukayi accident".
"Innalillahi wa inna ailaihir raji'un a ina sukayi accident?".
"Bansani ba domin nima ƙirana akayi da wayar Yaya Fawas ake sanar dani yanzu".Motsi mai kyau na kasa yinsa bakina ya shiga karkarwa saboda tsananin sun furta abunda yake raina,nayi nasarar jawo numfashi na daya fara nisa da gangan jikina nace"ina fatan ba wanda ya rasa rai"ya ɗaga kansa alamar bai sani ba.aka ƙara ƙiran wayarsa babu jimawa ya katse ƙiran,ya ƙira Daddy ya gaya masa yace shima yanzu aka ƙirashi aka sanar dashi,yace ya airpot yanzu ya sama mana jirgin da zaizo katsina ya biya mana nida Ummi mu dawo shi kuma ya wuce inda akace sunyi accident ɗin.
Haka muka wuce cikin Kaduna muka zarce airpot,Sayyid ya ƙira Daddy ya haɗa shi da Managern wajen sukayi magana.nan da nan aka sama mana jirgin katsina muka shiga sosai Ummi ta tsorita saboda yanda numfashina yake shiɗewa.Muna isa cikin katsina malam Habu yazo ya ɗauke mu a airpot muka wuce gida,Daddy kam daga can Damaturu ya wuce kadunan.
Tunda muka shiga cikin gidan nakasa zama safa da marwa kawai nakeyi nakai mari nakai bango,Ummi ta kalloni da idonunta da suka bayyanar da zallan tausayina tace"Hibba ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu wani mummunan abunda zai faru".nazo kusanta hawaye nabin kuncina nace"Ummi dan Allah inma sun mutu ne a sanar dani wallahi zan ɗauki ƙaddara aduk yanda tazo mini".nakai ƙarshe ina kwanto kaina saman ƙirjinta ta fara lallashina.
Wunin ranar cur daga ni har Ummi bamuda kwanciyar hankali,mu ƙira wayar Sayyid da Daddy yafi sau shurin masaƙi amma basa ɗauka Ummi ta ƙira Granny tace itama tana hanyar zuwa katsinan,yamma sosai Granny ta isi muna zaune a falo kowa da abunda ke ransa mukaji ƙaran shigowar mota duk muka miƙe zumbur muka fito harabar gidan,motoci uku ne suka shigo ɗaga daga ciki motar asibiti ce duk suka faka.ganin Yaya Fawas ya fito daga cikin motar asibitin Habib na biye dashi duk hannayensu da bangeji Habib shikam har goshinsa ga ƙafarsa ɗaya da yake ɗingisata.
Na ruga a guje na isa ga Yaya Fawas cikin kukan dana ɗau lokaci inayinsa nace"Yayana ance kunyi hatsari ina Umma fa?".ya ɗaura kansa a saman kafaɗata tana hawaye na ɗagoshi nace"Dan Allah Yaya Fawas ka taimakawa zuciyata wallahi tana dab!da faso ƙirjina ta fito,ka sanar dani ina Umma".
"Hibba sai dai muyi haƙuri Allah ya fimu son Umma shiyasa ya karɓi abunsa".bazan iya tantance muryar waye naji yana faɗin haka ba,a tsakanin Yaya Fawas Habib ko Sayyid.ƙirjina ya buga da tsatsan ƙarfi daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba.
Sai buɗe idona nayi naganni a gadon asibiti maganar rasuwar Umma ya fara mini sowa a kunnuwana,Inna dake zaune kusa dani suna magana da Ummi da Yaya Fawas ta lura da buɗe ido da nayi.ta fara jefo mini sannu babu ƙauƙautawa ganin Yaya Fawas ya sanyi ƙoƙarin tashi daga kwanciyar danayi nace"Yaya Fawas dan Allah ka nuna mini Umma ka kaini wajenta,wallahi inaso inayi mata kallon ƙarshe".ya zauna tare da riƙo hannnuna"My Cute angle haƙuri zamuyi Umma ta amsa ƙiran ubangiji abunda yatafi buƙata daga garemu shine addu'a shi yazamu cigaba da mata".


"Hakane Hibbatu Allah ya jiƙan Juwahir ya yafe mata kurakuranta"cewar Inna cikin maganganun da suka cigaba dayi na fahimce cewar har anyi sadakan uku na rasuwar Umma.wallahi hawaye nakeso su zubo mini amma hakan ya gagara samuwa a gareni sai kukan zuci danakeyi mai tsananin ƙona da yamma aka sallame ni tare da haɗani da wasu magungunan ciwon zuciya muka taho gida,Daddy da Granny muka iske a falo suna zaune muka shigo Granny ta miƙe ta riƙo ni muka ƙariso cikin falon.Mu'afsa dake kwance jikin Daddy daga ganina ta taso cikin tafiyarta dabata daɗe da soma yinsa ta faɗo jikina,Habib ya ɗagota ya ɗauke Daddy yace na matso kusansa na tashi nayi kamar yanda yace.
"Hibba haƙiƙa duk mun shaida cewa mutuwa wata halittace na ubangiji,da duk mai rai bazai tsallake ta ba.rashin uwa rashi ne mai matuƙar zafi da ba'a warkewa daga ciwonsa da wuri sai dai haƙuri da karɓan ƙaddara aduk yanda yazowa mutum babban raboce,Allah ya jiƙanta ya kuma bamu haƙurin rashinta".a sanyaye na amsa da amin hawayen idona ya kafe kaf!ko ɗigon ruwar ƙwalla ban fitar ba Daddy ya ɗaura da cewa"Ki cire komai a ranki mu godewa Allah tinda ya ƙaddara saduwa a tsakaninku har an nema yafiyar juna kafin rai yayi halinsa,yanzu kije kiyi wanka ki fito kici abinci".na miƙe da ƙyar jiri na ɗibata Granny tace"Allah sarki!Allah kaɗai yasan raɗaɗin da take a ciki,kukan zuci takeyi".
Ina shiga ɗaki na mayar da ƙofar na rufe nan na zauna naci kuka na fitar hankali duk da hawayen basa zuwa,nafi awa ɗaya kafin na tashi na shiga bathroom na sakewa kaina ruwa na ɗauro alwala na fito na tara salla a zaune nayi sallan saboda ƙafafuna da suka matuƙar rawa.
Ina iddarwa na shiga zabgawa Umma addu'ar neman rahma,na daɗe kafin nayi shirin kwanciya dan bana sha'awar fita balle zama cikin mutane na fiso na kaɗaita ni kaɗai a halin yanzu.inajin Habib yana knocking a ƙofar ɗaki nayi kamar bazan buɗe ba sannan na tashi na buɗe masa,a bakin gado muka zauna sai daya ƙare mini kallo tsaf!yace"Matar aljanna wannan damuwar ba shi bane mafita,ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah shine sarkin da ikonsa ya game komai yanaji kuma yana ganin duk abunda yake faruwa,dan Allah ki tausaya min ki daina saka damuwa arankii kinji Debbo am".na ɗaga masa kaina alamar naji haka ya cigaba da kwantar min da hankali har nayi salama sannan yace na tashi mu tafi part ɗinsa banyi musu ba yaja hannuna muka tafi Mu'afsa na hannunsa.
Sai da akayi sadakan Bakwai sannan Granny da Inna suka koma,ranar na fita makaranta na amshi jarabawata.lokacin saura kwana biyu mu gama,a wajen Ummi nake barin Mu'afsa dan yanzu watanta bakwai har tana ƙoƙarin tsayawa,ina dawo daga makaranta na biyo tanan da dare Habib yazo ya ɗauke mu.duk na fita hayyacina ga raman dana zuƙa kullum Habib cikin kwantar mini da hankali yakeyi haka ma Daddy da Ummi,cikin haka muka kammala jarabawa sai ranar na tsinci kaina cikin farin-ciki yau na cika burin Yaya Fawas na zamowa MA'AIKACIN JARIDA,na cika ƙudirin Abba nason muyi karatu ko bayan ba ransa.wani daɗin daya darso a birnin ƙalbina ya sani zama akan ɗaya daga cikin kujerun plastis dake cikin makarantar na tsura kaina cikin hijab ina sakin kukan daban dalilinsa ba.tun rasuwar Umma hawaye suka ƙaurace mini sai yau suka zubo mini nayi shi kuwa kamar ba gobe,ƴan department ɗin sai murna sukayi na kammala cikin yarda mai duka.
Sallama nayiwa su Limat Auwal da wasu ƴan department ɗinmu da muke shiri dasu,na ja motata nayi gida dai-dai shigowar motar Daddy isana kenan na fito na jira fitowarsa sannan na isa gareshi na karɓa jakan hannunsa,muka isa falo Sayyid da Habib muka iske suna arranging ɗin dinning suka yiwa Daddy barka da zuwa sannnn Ummi ta fito na miƙa mata jakar na isa ga Mu'afsa dake bacci kan gadonta na yara ina kallon fuskarta"Ayya!ƴar amanata kinata bacci kenan"daga haka na saɓe ta mukayi ɗaki,wanka na farayi na fito nayi sannan Asr a makare sannan na fito falo na taya Ummi fito da kulolin abincin.
Nayi serving ɗinsu sai da muka gama ci muka komo falo Daddy yace"Hibba kun ƙare jarabawa yau ko?"na ɗaga masa kaina"Masha Allah,Allah ya taimaka"duk muka amsa da amin.
"Kyauta ta farko ga JOURNALIST"ya ƙare yana miƙo mini makullan motoci guda biyu na matso na miƙa hannu cikin nutsuwa na karɓa nace"Daddy nagode sosai Allah ya saka da alkhairi Allah ya ƙara girma da nisan"yace"Amin Ƴar albarkata".
Ummi tace"Alhaji motar nan naga ai tanada ita tunda mijinta ya saya mata,ai da wani kaddarar ka sai mata da kuɗin motar dakayi niyyar batan".murmusawa Daddy yayi ya ɗaura da faɗin"Me kikeci na baka na zuwa Hajiya?".ya kai ƙarshe yana ƙara miƙo min wasu takardun daya ciro daga aljihunsa"wannan takardun gidade ne guda biyu da fili ɗaya na mallaka miki shi ko bayan raina".
Na rasa bakin godiya tsabar murna kawai nasa kuka Habib ya rusunar da murya yace"Daddy mum gode Allah ya ƙara arziki"duk suka amshe da amin.Sayyid sai murna yake min yana faɗin ya masa motar da zaina aƙa inzashi azare wajen Fadila,Daddy yace kar na sake na bawa kowa motata don ni ya saya bayason ganin kowa a tare da ita.sai da aka fara ƙiran sallan magrib sannan suka fita masallaci,na shiga ɗaki na ƙira yay Fawas na sanar dashi shima ya cika da murna yana ƙara jinjina karamci irin na dangin Habib,sai ƙarfe tara muka bar gidan.
Mun raya wannan dare da sunna nida Habib fiye da sauran dararen rayuwar aurenmu da suka shuɗe,washe gari da yamma Sayyid ya haɗa mini walimar murnar gama makaranta ana gidan Daddy har yaya Fawas da Inna haka nan ma Balaraba da Kabir,koda da wasa ban sakar masa fuskaba balle ya sama damar shige min dan har yanzu inajin zafin abunda Kabir yamin a rayuwa.aka taro ya watse kowa ya tafi da murna da sha'awar rayuwarmu nida Habib a raina nake cewa basu san gwagwarmayar da akayi ba kafin ak iso nan.a wajen taron Habib ya gabatar mini da ticket ɗin zuwa ƙasashe uku daya mana na farko saudiyya na biyu Moscow sai kuma spain da zaran an gama bikin su Sayyid zamu ɗaga.
Bikin Sayyid da Aliyu haidar za'a farayi dan Yaya Fawas yace sai an farayin na ƙannen nasan tukunan Anisa da Fadila,Daddy shi ya ɗauki nauyi yiwa Anisa da Fadila harma da Farida kayan ɗaki kaf!nida Ummi da Inna da kuma Granny mukaje dubai muka sayo musu furnitures na kece raina dukka kayan iri ɗaya,Ummi kuwa ta lodo musu kayan kitchen sosai anan aka haɗa lefen Sayyid dana yaya Fawas.kwanan mu takwas sannan muka dawo,harkan biki ya kankama ganda-ganda.
Inna da Hajiya Jummai da kuma Ummi suka kai kayan ledan Yaya Fawas ga Amaryarsa Farida a ƙasan nijar cikin Maraɗi.kwana huɗu tsakani aka kawo na Anisa lokacin su Granny da wasu ƙannen Ummi hadda Hajja sun tafi kai na Fadila duk suka haɗu a can azare ɗin.kowani shawara Daddy zaiyi sai yayi ta dani haka nanma Ummi da Granny,Tun ana sauran sati biyu Maryam tazo da tsohon cikinta nayita yi mata tsiya.ana saura kwana biyu muka shirya walima washe garin ɗaurin aure kuma in an kawo amarya ayi dinning Anisa ma anan za'a kawota kafin a wuce da ita Nijar ɗin.
A cikin harabar gidan aka shirya waliman,ina zaune a ɗaki ina murza hoda a fuskata Mu'afsa na zaune gefena tana game acikin wayata,Habib ya shigo na ɗago na kalle tare da amsa sallamar daya shigo da ita wajen Mu'afsa ya fara isa cikin magananta da bai gama nuna ba tace"Abbi tun ɗazu Ammina take nemanka aka ce mata ba'a ganka ba"ta kai ƙarshe tana ware masa hannayenta muka saka dariya sosai yariyar zata jawo mini ruwa ɗazune nake tambayar Ummi saboda wasu ƴan office ɗinsu da sukazo har zasu tafi basu gaisa ba take cemin ita ma tun safe bata sanya shi a idonta,shine Mu'afsa ta riƙe zancen cikin kanta yariya sai shegen wayo kamar wata babba alhalin ko shekara biyu bata cika ba.
An ankara ba nayi ya rungumo ni ta baya tana kallona ta cikin madubin yace"Menen tun ɗazu kike nemana kodai inkiyi missing mijinki a kusa dake ne?"na jaye jikina yace"To Mu'afsan ta fita na aiketa wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login