Showing 102001 words to 104857 words out of 104857 words

Chapter 35 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7322

Ummi".


"Munje ko kaga yanzu za'a fara walimar"ya riƙo hannuna yana cewa "babu inda zaki".tunda ya furta nasan sai ya aikata nayi raurau da idanu nace"Hamma dan Allah ka fito mu tafi kar Ummi ta fara neman mu".ya saki dariya yana lakuce mini saman kunci na kai masa dukan wasa saboda lip gloss ɗin dake leɓɓana daya lakuce mini.sanda muka fito har an fara gabatar da walimar wanda ya sama halaltar manyan malaman sunna na cikin katsina da kewayenta.Mu'afsa na ganimu ta nufo mu da gudunta Abbinta ya ɗauke ta ya nufi wajen Bashir,ni kuwa na zama kujera kusa da Maryam nazauna.na lura sai murmushi take sakewa ƙasa-ƙasa na galla mata harara nace"faɗi karta kashe ki".
"A'a babu komai tattabau uwayen soyayya".na taɓe baki na maida hankali ga jawabin da malaman suke yi.ƙarfe shida na yamma taro ya watse aka shiga gida ranar kwana mukayi babu runtsawa saboda shirye-shirye ɗaurin auren gobe,Habib sai duka mini ƙira yakeyi akan yana jirana a part ɗinsa har sai da Ummi ta gane ta karɓa wayan ta mishi magana ko kanzil ya kasa ce mata saboda kunyar data mamaye shi.
Washe gari tun asalatun farko muke aiki saboda ɗaurin auren ƙarfe goma ne,da wuri muka kammala komai muka shiga shiryawa sai dana shirya Mu'afsa tsaf!sannan Anty Uwani ƙanwar Ummi tazo ta ɗauke ta nima na shirya cikin wani less ruwan sararain samaniya da mukayi ankonshi nida Ummi,Granny da Mu'afsa sanda na fito naji Ummi nacewa har sun tafi azare ɗaurin auren.
Ana ɗaura kuwa zasu taho da amarya Fadila da kuma Anisa saboda gobe ƴan nijar zasu zo da anyi dinner su ɗauki amaryasu su wuce da ita,hakan ya tino mini da ranar ɗaurin aurena da Habib hakan wata al'adar ne nasu ana ɗaura aure ake ɗaukar amarya.
Zuwa ƙarfe uku masu motocin ɗaukar Amarya suka iso,dukkansu sunyi shigar liffaya iri ɗaya sak sunyi mungun kyau aka fara feshe su da turare sannan aka shiga dasu can ƙuriyar falo,Kawu Isma'il dasu kawu Hayatuddeeni da mahaifin Aliyun haidar ɗin da wasu biyar daban shaidasu ba sukazo amsarwa ɗansu Aliyu haidar auren Amisa.tare da Anty Amina sukazo akan gobe insu Adda Salamatu sun su koma tare.ranar duk yanda Habib yaso mu haɗu gagara hakan yayi sai da Daddy ya shiga yayi ta mim faɗa wai ina gyara auren wasu ni kuma ina wasa da nawa haka na tafi part ɗin Habib na kwana acan.
Washe gari gidan babu masaka tsinke tsabar yawan jama'a da cinkoson motocin,zuwa ƙarfe biyu su Adda Salamatu dukkansu suka iso dasu Nabiha,Nabila dasu Mima a cikin part ɗin Sayyid suka sauƙa dan ba'a nan akayiwa Fadila jere ba a kano zasu zauna wajen aikinsa.
Ƙarfe huɗu aka fara shirya zuwa wajen dinner,ko ya saka ankonsa harsu Nabiha amare kuwa shigar farin less mai ɗigo-ɗigo ruwan golden sukayi aka tsantsaresu da make-up.sai lokaci ango Aliyu haidar ya sama damar isowa da zugan abokansa dukkan su suna cikin unfiorm ɗin sojoji.
Nida Habib da Mu'afsa anko farin shadda mukayi aka min ɗingi doguwar riga da adon golden ɗin flower a wuya da hannun riga wanda yayi dai-dai da kalar hular da Habib yasa akanshi,Mu'afsa kuwa ita doguwar rigar aka mata iya gwiwa na raba mata ganshinta gida biyu na kame mata shi da ribbon pink colour,sosai muka ɗauki hankulan mutanan da suka halalta dinner ƴan mata sai shigewa Habib sukeyi na kuwa mannewa abuna.da haka dinner ya tashi bayan anci ansha yaya Fawas ya zubo addu'o'in neman zaman lafiya ga ƙannen nasan,washe gari tun ƙarfe tara aka wuce da Anisa Nijar tare dasu Adda Salamatu da sukazo suka tafi da ƙannen haj jummai da kuma na mahaifinsu sai kuma Anty Amina itama da jaririn cikinta maƙale jikinta.
Da yamma kuwa aka wuce da Fadila gidanta take kano,ranar Sayyid da Ummi suka ƙarayin kukan rasuwar Yasira sosai sai da suka bawa kowa tausayi,yana daga cikin babban burin Yasira son ganin Sayyid yayi aure Allah bai ƙaddaraba har ta rigashi yi.nima sai dana koka mata sosai shiyasa na tsaya tsayin daka wajen ganin komai ya tafi kamar yanda Yasira ta daɗe tana tsarawa.
Duk yanda naso zuwa kai Fadila,Habib hana ni zuwa yayi.Daddy ma ya goya masa baya cikin daren na kwana da zazzaɓi mai zafi ajikina sai kwara amai nakeyi duk jikina babu kuzari,muna gama breakfast Habib ya kaini asibiti aka tabbatar ina ɗauke da jaririn cikina a maƙale a ƙasan mara na,murna wajen Habib ba'a misaltawa muna dawowa sai daya bi kan kowa ya faɗa mishi ko sai faɗin yakeyi daga auren Yaya Fawas sai zuwa suna duk suka sanya ni cikin kunya.
Gidan Daddy muka zauna saboda auren Yaya Fawas sati biyu ne tsakaninsa dana su Sayyid,kulawa ina samunsa bana wasa ba kamar kwai haka Habib yake riritani haka nan Ummi da Daddy,Granny ma ba a barta a baya ba.duk sati Baffa ke aiko min da ruwan rubutu ina sha da wasu ƙarin addu'o'in.lokacin da bikin yaya Fawas ya rage saura kwana biyar Ummi ta hanani ɗaga komai a cikin gidan hatta ruwan wanka haɗa mini takeyi da kanta,washe garin ranar muka wuce azare da Ummi,Granny,Iya hadda Hajja da maryam.
Nan Inna take fesa mini Nazifi ma yazo ɗaurin auren naje mu gaisa,take kwakwalwata ta shiga dawo mini da abubuwan dasuka wakana a da Nazifi ne silar komai.Fadila tazo Anisa ce dai bata zoba,Daddy da Habib da kuma Sayyid da Yaya Fawas da wasu yayun mahaifinsa da kuma Baffa suka ɗunguma nijar karɓawa Yaya Fawas auren Farida.Ƴan ɗaurin aure na watsewa na leƙo zaure na hangi Nazifi tsaye daga waje na nufi da sallamata ya amsa sannan muka shiga maidawa juna gaisu.
"Allah sarki!Hibba Inna ke cemini kinyi aure har inada ƴa kinsa ni tun lokacin da aka neme ki aka rasa,nima na tattara kayana nabar gano".na ƙara rusunar da ƙwayoyin idona nace"E wallahi Nazifi nayi aure har inada yarinyata ɗaya Mu'afsa,kai fa tare da matarka kuka zone?".yasaki murmushi kawai ina sadda kansa ƙasa yace"Har yanzu banyi aure ba wataƙil nan gaba nasone na roƙi yafiyarki domin nasan cewa na taka muhimmiyar rawa wajen jefa rayuwarki cikin ƙunci har shaiɗan yayi galaba akanki kika guji gida".


"Babu komai Nazifi Allah yasani ban ƙullace ka a raina ba,Allah ya kawo maka mace ta gari".yace"Amin ki gaida min da mai gidan nakin".har na juya zan tafi Mu'afsa ta rugu wajena da gudu ta rumgume ƙafafuna na ɗagata sama tace"Ammina wannan waye ne shima yaron Hadiya Inna ne?".nace"A'a wannan yaya nane"ta gaishe shi ya amsa yana binta da kallo sosai soyayyar yarinya ya maƙale masa a ruhi.nidai na barshi tsaye nayi wucewa na ciki,ranar na ƙira wayar Habib yafi sau yanda tela yake taka keke amma bai ɗauka ba ƙarshe na haƙura nayi kwanciyata,washe gari aka kawo amaryar yaya Fawas da yamma akayi dinner koda Habib ya shigo gaida Ummi da Inna da safe ko kallon arziki bai mini ba ya fice,har yanzu danake shirin tafiya dinner raina bai sama sukuni ba,ɗinki buba nayi da zanita na lulluɓa mayafina ina riƙe da hannun Mu'afsa na fito a motata muka tafi wajen dinnern dasu Mahmud da Sadiq.
Duk hankali na yana ga Habib a wajen dinnern ina juyowa muka haɗa ido da yaya Fawas yamin ishara da hannunsa akan nazo na tashi na isa gareshi bansan mena tina ba lokaci ɗaya idona suka kawo ruwar ƙwalla suka fara zuba Yaya Fawas ya riƙo hannuna shima hawayen yakeyi yau ranar ɗaurin auren yaya Fawas amma babu ran Umma babu na Abba cikin muryan kukan dayake ƙara zuwar mini nace"Yay Fawas mu kuma haka zamu rayu babu uwa balle uba Allah ya jinƙanku".
"My cute angleb akwai Allah kike raya rayayye a cikin matacce har ya fito duniya tabbas shi zai jiɓanci lamuran mu".daga ni har shi kuka mukeyi sosai Mu'afsa ta tashi tazo wajenmu yaya Fawas ya ɗaukre ta ta fara share masa hawaye tana faɗin"Abbu ka daina kuka kaga ka samin Ammina kuka ko Hadiya Inna ce ta muku bulala".
"Na daina yarinyanta"ya faɗa yana share hawayensa Ummi tazo ta riƙe hannuna muka koma mazauninmu na da Mu'afsa kuwa nan wajen Yaya Fawas da amaryar ta zauna.ƙarfe goma an gama komai nihar har nayi shirin kwanci naga saƙon Habib yana shaida mini gobe da safe zamu wuce katsina,ina gama karantawa na kashe wayar na kwanta raina fal!da tinani.
Washe gari na sanar da Ummi tace na shirya ɗin kawai mu tafi,haka na shirya mukayi ban kwana da yaya Fawas muka tafi muka bar su Ummi anan sukam sai sunyi ƙara kwaba biyu.har muka isa cikin katsina bai tanka mini ba yana ajiye mu a gida ya wuce offics na shiga gyare-gyaren gidan sannan na ɗaura girki nayi wanka koda na fito ana ƙiran magrib nayi ban tashi ba sai danayi isha'i sannan na fito falo saboda ƙaran shigowar motar Habib danaji na tarbo shi tare da gabatar masa da abinci yace ya ƙoshi.
Na tari gabansa ina kuka nace"Habib mena maka kake min wannan hukunci mai tsanani,dan Allah ka fito ka sanar dani".
"Babu komai".nayi saurin cewa"zanfi yarda idan kace mini bazaka faɗa ba akan kace min babu,wallahi wannan hukuncin yayi min tsauri mijina zuciyata tana azabtuwa"ya rungumo ni jikinsa saboda kukan dana saka mai matuƙar sauti muka zauna akan sofa yace"Meye haɗinnki da Nazifi ranar na ganku kuna tsaye kunada wani dangantane dashi na nisa kona kusa,wanda ni ban sani b?".


"Ba muda wani dangankata tsakaninum ko ranar ma Inna ce tace naje mu gaisa don tunda yaji auren Fawas yace zaizo ya nema yafiya ta shiyasa har na tsaya dashi amma kayi haƙuru Rajlun amin".ya ɗago kaina tare da tallafo kuncina yace"Babu komai ya wuce matar aljanna kinsan mijin nakine yanada tsananin kishi akanki,banajin akwai namijin daya ɗara ni kishi fa".naɗan murmusa babu shiri yace"taso muje muci abincin ko"na miƙe nabi bayansa shi yayi serving ɗinmu ya kalloni yace"Jibi ne tafiyarmu kuma sai lokacin haihuwarki yayi kusa sannan zamu dawo".Na tausayar da kai nace"Allah ya nuna mana"yace"amin".
Ana gobe zamu tafi su Ummi suka dawo mukaje musu sallama Ummi tace mubar Mu'afsa,Abbunta ya nuna yafison mu tafi ta ita.Granny sai shimfiɗa masa kashedi takeyi da zaran na shiga watan haihuwa ya dawo ni gida.ko gano bamuje ba saboda tafiyar tazo a gaggauce sai waya nake sanar da Baffa ya mana fatan Allah ya tsare hanya,Maryam ma a waya nake sanar da ita.kafin mu tafi Yaya Fawas da Habib hadda Daddy sukaje zamfara domin shari'ar Bashari inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru talatin tare da taran naira dubu ɗari takwas a bisa laifin aikata fyaɗe da kuma zanba cikin aminci.
Saudiya muka bara halalta muka sauƙe farali sannnn muka wuce ƙasar moscow,matuƙa na yaba da tsarin zubin moscow watan mu uku da kwana biyar a moscow muna more rayuwarmu,na murj na ƙarayin haske sosai fatana tana glowing fiye dana da ga wani ƙiban dana narka hak nan ma Mu'afsa har shi kasan Habib ɗin.watan mu biyar a spain muka dawo nijeria saboda naci irin na Granny,tun muna moscow Anty Amina ta haihu da zamu dawo kuwa muka tsaya ta nijar ta sama baby boy ɗinta mai sunan Malam Mahiru haka nan ma Anisa ya ƙarayi kyau sosai kwanan mu uku muka dawo nijeria.
Sayyid da Yaya Fawas da matayensu sukazo ɗaukar mu a airpot muka wuce gidan Ummi ta tarbe mu cike da fara'a kai ya ilahi gaskiya nayi kewar Ummi babu mizanin dazan kwatanta adadinsa.bamu cika sati biyu da dawowa ba na haihu sai dai nasha baƙan wahala sai nada wuni ina naƙuda ban haihu ba ƙarshe ma sai da aka min Cs sannan aka ciro mini tsantalelen yarona na miji mai matuƙar kama da Ummi kamar kara aka tsaga.
Murnan wajen Habib babu kama hannun yaro kasa zaune yayi balle tsaye,dan lokacin da aka shiga dani Cs ji yakeyi kamar nima rasani zaiyi kamar yanda Yasira ta tafi ta barmu ta irin wannan hanyar.tana riƙe da yaron ya hana kowa karɓansa har muka isa gida.
Kullum yana naniƙe damu wataran har sai Granny ta koresa,har daina zuwa office yayi ranar suna kuwa baby yaci sunan Abban -SULEIMAN-.Inna har kuka tayi tsabar murna da farinciki su Fadila da Anisa har Anty Amina sunzo sunan Balabara da Hajja ma haka dasu Adda Suwaila.Maryam ma da ƴaƴanta biyu Diana ƙanwar Abbul-khair.
Ranar sunan Habib ya mallaki min takardun gidade biyu da takardar sabon Companyn sarrafa alkama dayake ginawa dukka.duk muny shigar shadda ash nida Habib da Mu'afsa kowa ya tafi da sha'awar rayuwar aurenmu da Habib a ransa.
Kwana biyu Anisa dasu Adda Suwaila suka koma,Daddy yace su Fadila da Farida ma su koma ɗakunansu.daren ranar Daddy ya ƙirani ya miƙa mini takardun sama min aikin da yayi a wani sabon gidan jarida -MANUNIYA-.na rasa bakin magana tsabar farin-ciki Habib ne kawai yake masa godiya Ummi na tayasa.ranar kasa bacci nayi tsabar murna yau dukkan damuwata ta kau na cika burin -ABBA- na cimma ƙudurin -YAYA FAWAS- yau nice ma'aikaciyar aikin jarida.
-AKKAM-laƙabin da muke ƙiransa kenan sa wani lokacin har rigima mukeyi da Habib akan yanda yake nuna tsallar soyayyar ƙiri-ƙiri ga Akkam nikam nasan har na gama haihuwa bazan haihu wacce zata kai -MU'AFSAT-ba sonta bazai taɓa canzuwa a cikin ƙalbina ba.sai da Akkam ya cika wata uku cif sannan na fara fita aiki.lokacin Mu'afsa ta shiga makarantar Nursery.inna dawo daga aiki na fiyo wajen Ummi na ɗauketa mu tafi gida.




-BAYAN SHEKARA-


Zaune nake akan ɗaya daga cikin laushashshun kujerun falo masu launin kalar Maroon,haka nan ma kalan dogayen labulen ɗakin carpet mai launin milk dake malale a tsakiyar falon.
Gefe guda kuwa wasu kujerun ne milk colour ga makeken tv plasmaa cikin wall ta can gefe kuwa hotonmu da Habib,Mu'afsa da Akkam ne duk fuskokinmu ɗauke da annuri a manne cikin wall ɗin an gine dashi,daga gefen shi hotona ne nida yasira.a hankali na miƙe ina ƙara damƙe takardan asibitin dake nuna ina ɗauke da ciki na tsawon sati biyu duk na burkice saboda har yanzu ban yaye Akkam ba,tun dawowata daga Office nake dukawa Habib ƙira yana cemin yanzu zai iso,ko ta wajen Ummi ban biya na ɗauko Mu'afsa da Akkam ba.
Inajin ƙaran shigowar motarsa na sakin hawayen dake maƙale a ƙuyar idona,ya isoni cikin sauri"Ummul-kam lafiya kuwa meya faru a asibitin?".yakai ƙarshe yana riƙo hannun ya karɓa takardan sai daya karance tsaf!kafin yace "Alhamdulilah!Allah na gode maka zanga jinina a duniya sosai"na ɗan harare shi ina kai masa duka a kafaɗansa nace"ni wallahi a cire min shi kaga Akkam fa ko shekara baiyi da rabi ba ko yaye sa banyi yanzu kuma ga wani cikin".ya ƙara riƙo hannuna muka zauna"Haba Debbo am ma'aurata nawa suke neman haihuwa ido a rufe Allah bai basu ba,mu kuma Allah ya bamu maimakon mu gode masa sai kice acire miki gaskiya banji daɗi ba kuma ki gaggata tuba zuwaga ubangijinki"na rusunar da kaina ƙasa nace"Na daina!na daina rajlun amin Allah yabamu masu albarka amma Akkam fa yaya zamuyi dashi?".


"Zan ƙira Ummi ya cigaba da zama kawai a wajenta sai ana bashi madara"na jinjina kaina alamar gamsuwa ya ruɗe min hanayensa na faɗa jikinsa.nana wajen ya ƙira Ummi ya sanar da ita Akkam ya zauna a wajenta saboda Hibba nada ciki tsabar kunya yasa Ummi kashe wayar ba tare data gaɓa sauraran sauran zancensa,yakuma ƙiran Inna ya faɗa mata dan tsaban son ƙara kunyata ni har tambayar ta wai meya kamata ina ci ko sha don inganta lafiyar abunda yake cikina nasu na gargajiya.bayan ta gama lissafo min sukayi sallama ya haɗa zai ƙira yaya Fawas ya kwance na turo baki haɗi da faɗin"ni wallahi babu wanda zaka kuma ƙira ya isa haka"yasa dariya yace"Ummul-kam kenan ai abun alkhairi ne ya same mu dole na sanar".


"Ni Abbu Mu'afsa wannan haihuwa babu wanda zan sanar sai dai kawai kowa yazo ya ganni da babyna"ya kuma yin wani dariya muka miƙe muka shiga ɗaki. Ranar haihuwa naci wahala harma fiye dana haihuwar Akkam dan kasa nishi nayi gabaɗaya duk na gama galabaita har an shirya shiga dani tiyata na haihu ƴan biyuna ɗaya mace ɗaƴa namiji,dangi gabaɗaya ya ɗauka dan basu da ƴan biyu da yawa ranar suna yara sukaci sunan -DADDY- da -YASIRA- muna ƙiransu -IKRAM- da -AKRAM-.haka rayuwa ta cigaba da juyawa farin-ciki da zaman lafiya na ƙara wanzuwa a tsakaninmu ana cikin haka Fadila ta haihu ta haiho baby girl ɗinta yariya taci sunan Ummi suna ƙiranta da -AFRIN-sati uku tsakaninta da Farida itama baby girl ta samu aka sanya sunan Inna suka ɓoye mata suna suna ƙiranta da -AJMAL-.Anisa kuwa ciki haihu ko yau ko gobe.


A cikin taƙaitaccen lokacin da Allah ya tsara mini rayuwa a cikinsa,na haɗu da jarabawa kala-kala daban-daban amma na godewa rabbi daya barni da imani na a cikin ko wani hali,har na kawo wannan matsayin a rayuwa Habib ya zama duk wani -HASKE- a rayuwata.




-ALHAMDULILLAH-


Anan na kawo ƙarshen wannan littafin nawan mai suna UWATACE SANADI,ina roƙon Allah duk abunda na rubuta dai-dai a cikinsa ya haɗa mu akan ladan,inda nayi kuskure kuwa ƙarancin ilmi ne,Ya Allah ka tsare mini hannayena wajen rubuta abunda zai zama cutarwa ga al'umman musulmai tare da tarbiyarsu.
Ga me neman wannnn littafin ko wani ƙarin bayani zai iya tuntuɓata ta wannan lambar kamar haka -07038908713-.


Maimunah Tijjani Iyam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login