Showing 75001 words to 78000 words out of 104857 words
Chapter 26 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
wuyana"bari na ɗauko miki magani"tana kawowa nan ta fice.
Na maida kaina cikin gwiwoyina ina lazimi da gaɓoɓin hannuna,naji a rufo ƙofar ɗakin an shigo ban damu na ɗago naga ko waye ba dan nayi zaton Farida ce.
Naji an rungumoni nayi saurin ware idanuna dasuke lumshe,cike da zaƙuwar ganin waye ya shigo min ɗakin.
Idanuna suka tozali da Habib banyi ƙoƙarin rabashi da jikina ba dan kallon cikin idonsa danayi na hangi tsabar tashin hankalin dake cikinta.
"Meyasa zakimin horo mai tsanani irin haka na yarda na amince ki hukuntani ta kowace hanya amma banda wannan".
Nayi maza na haɗiye kukan dake shirin zuwar min nace"hakan shine mafita a garemu dani dakai gabaɗaya domin inaji a jikina an kusa a rabamu rabuwa ta har abada,daman duk wani abunda zai kawo haske a cikin rayuwata sai na fara murnar mallakarsa sai ya suɓɓuce min".
Ya ƙara ƙarfin riƙon daya min yace"babu abunda zai rabamu sai mutuwa na miki wannan alƙawarin,zan zame miki haske acikin rayuwarki zan zame miki ɗan jagora ta yanda zakiyi tafiya ba tare da lalume ba".
Hawayen dasuka fara bin gefen kuncina ya fara share min na tsanya ƙwayar idona cikin nasa"Habib ina gudun ranar da zatazo kaima ka zargini irin wanda ƴan-uwan mahaifiyar kemin a halin yanzu,na gwammaci muyi haƙuri da juna tun kafin zargi ya shiga tsakanin igoyoyin aur..."yayi saurin rufe min baki da tafukan hannyaensa"babu wata ranar makamanciyar irin wannan acikin rayuwarmu,na shaida cewa a budurwa a aure ki sannan ki kawo budurciki izuwa inda yafi cancanta watau gidan mijinki babu abunda zai faru komai zai wuce kinji haba cute Angle ɗin Yaya Fawas kimin murmushi mana".
Bansan sanda taƙaitaccen murmushi ya kubce min na rungumoshi naji numfashinsa dake fuzga da ƙarfi na ɗago inabinsa da kallon tuhuma"Anya kasha maganinka kuwa?".
"Har kina tinanin cewa kina cikin wannan halin zan sama nutsuwar shan magani?"na cizo leɓɓana na ƙasa nace "to bari na ɗauko maka kasha"na wuce cikin akwatin kayana na ɗauko masa daman raba maganin mukeyi wasu a wajensa wasu suna wajena.
Na ɓalla masa yasha sannan muka zauna ya kwantar da kansa akan kafaɗa ta,Farida dataje ɗauko min magani ta turo ƙofar haɗe da sallama na zata zai tashi sai naga ya dake abunsa har ta shigo.
"A'a Hamma daman kana nan ne,kuyi haƙuri na shigo muku a lokacin dabai dace ba"wuf ta fice daga ɗaki ta barni raina cike fal!dakunya shikam ko a jikinsa.na ture kansa daga jikina tare da aika masa siririyar harara"wai kai bakaji kunya bane?".
"Kunyar meye kenan,to me kuma akayi yanzu?".
"Nidai wallahi ka tashi ka tafi kar wani ya ƙara shigowa ya ganka".ya jefomin harara kana yace"sai nagama abunda ya kawo ni tukunna".ya kashe min ido ɗaya daga nan kuma na rasa bakin magana.
Mun dan daɗe dashi kafin ya tafi na kwanta dan banason Farida ta shigo ta tardani idona biyu har yanzun kunyarta nakeji,inajin shigowarta na ƙara rufe idona ta kwanta a gadon tare da kashe wutar ɗakin.
Juye-juye kawai nakeyi ina haɗa zuffa sai numfashin danake fitarwa da ƙarfi duk na yaye bargon dana lulluɓa dashi,firgigi na farka ina haɗa duk wata addu'ar data fara zuwa bakina a wannan lokacin.na juyo na kalli Farida datake baccinta cikin kwanciyar hankali mummunar mafarkin danayi akan Umma ya fara dawo min cikin ƙoƙon kaina na fashe da kuka.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________
Page 4⃣9⃣
Najawo ɗan kwalina na toshe bakina tare da runtse idanuna ina tinano mafarkin danayi,Umma nagani acikin wani mayiwacin hali na jinya duk ta ƙanjame ta bushe kamar ba itaba wacce duk wanda yasanta zai shaideta dason gayu da ƙyale-ƙyale shekarunta kuwa daman ajiye su takeyi a gefe.
Faffaɗan dajine mai cikowar bishiyoyi da manya da ƙananan halittu tana yashe a ƙasa kiyashi da tururuwa suna shiga ta hancinta suna fitowa ta baki da kunnenta,cikin muryarta dabata fitowa sosai tace cemin nida Yaya Fawas mu yafe mata.
Ta maimaita kalmar a gareni yafi sau yanda tela yake taka keken ɗinkinsa,ko ince yafi sau shurin masaƙi yanayin dana hangata shiyafi komai ɗaga min hankali da sanyani fargaba mai tarin yawa yayin dason ganinta ya mamaye ni sai dai ta ina zan fara nemanta?ina zan nufa?waye zan tunkara?.
Tambayoyin dasuka tokare min rai kenan ciwon kan ya dawo min sabo idanuna suka min nauyi sosai duk da banida haske fata amma sai da fuskana tayi jajir.
Na zaro ƙafafuna ƙasa zan sauƙa daga kan gadon,jirin ya maidani na koma na sake yunƙuruwa naji muryar Farida sun sauƙa a kunnuwana"Anty lafiya kuwa?".
Maimakon nabata amsar tambayarta sai na fashe da kuka mai tsuma zuciya da sanya rauni.ta ƙara matsoni tare da faɗin"Suhbanallahi!lafiya kike kuka ko bakida lafiya ne kona ƙira Hamma Habib ne?".
"Babu komai basai kin ƙira kowa ba kawai mafarkine nayi ya tsora tani"na faɗi maganar filla-filla kamar mai koyar magana.
Ta riƙo hannuna tasa cikin nata tare da gyara zaman datayi a bakin katakon gadon ƙiran italian bed"Anty nasan kina cikin wani hali na rashin kwanciyar hankali domin na saurari dukkanin tattaunarwa ku dasu Hajiya tun ba yau Goggo Suwaiba take yawa da wannan maganar acikin dangi tun bayan lokacin dataje bikinku itada Batul da kuma matan kawu Isma'il.babu wanda ya ɗauki abunda muhimmanci sai yanzu dasuka ganki amma kisa a ranki cewa komai muƙaddari ne jarabawa bata ƙarewa a rayuwar mumini mai imani idan kikayi haƙuri zaki ribanto dashi in sha Allah,Hamma yanasonki danko ɗazu na ganewa idona ai wannan ma kaɗai ya isheki godiya wa Allah".
Na sauƙe numfashi"Farida nagode da shawararki amma ke bazaki fahimci irin raɗaɗin da zuciyata take ciki ba,banama ko wacce ɗiya mace fatan tayi irin rayuwata koda kowa maƙiyiyatace domin babu komai a cikinta face ƙunci,baƙin-ciki,rashin hankali da kuma tarin ababen dasuke hana zuciya sukuni su sanya ruwar idaniya zuba ako yaushe".
"Jarabawar mutum takanzo masa ta ko wacce siga kiyi tawakkali,komai lokaci ne dan Allah ki daina wannan kukan kar ya haddasa miki wani ciwon tun ɗazu kike yinsa"ta ƙarishe zance tana share min hawayen dake gudana tsakanin kuncina da kan haɓata.
Banajin kona gwada zan iya tsayiwa akan ƙafafuna nace Farida ta riƙe ni na tashi tayi riƙo da kafaɗata na miƙe na nufi banɗaki.
Raina cike maƙil da mamakin irin zufin tinani irin na Farida na tabbatar na girme ta a shekaru balle kuma na haɗata da Yasira,sai dai tanada girman jiki dan inmuka jera da ita ka iya rantsewa kace yayatace.
Nan nagane cewa shi tinani da sanin ya kamata ba daga shekaru yake ba kwance fuskana na somayi bayan na kawar da tinanin Farida daga raina.
Na tabbatar da inada ciki a wannan lokacin sai ya zube saboda tashin hankalin dana tsinci kaina aciki,na jawo ƙafafuna dasuka min nauyi inaji tamkar basa jikin gangar jikina.
Nan inda na barta na fito na iske Farida ta taso ta kamo hannuna ta zaunar dani,na lumshe idanuna a hankali sannan na waresu akan Farida wacce taketa jera min sannu ɗaya nabin ɗaya nace ta ɗauko min maganin hawan jinina acikin akwatin kayana ta ɗaukomin sannan ta haɗu min da goran ruwa nasha.
"Anty bari naje na sanar da Hajiya ko Hamma Jabir zai dubaki tunda shi likitane koma yana gida yau".
Na buɗe idanuna datunda nasha maganin na maida su na lumshe"A'a Farida ai ciwo ne kawai na lokaci ɗaya daman yana min irin haka lokaci zuwa lokaci har na saba,kar ki ƙira kowa in sha Allah zuwa safe zanji sauƙi".
"Allah yasa" tafaɗa cikin harshen fulanci sannan muka kwanta ina duba agogon wayata daya nuna ƙarfe uku saura mintuna biyar.
Kodana kwanta bacci ya gagari idona yanayin danaga Umma aciki sai dawo min yakeyi har zuciyata inason nayi tozali da Umma inhar na sanyata cikin idona wallahi ko ranar na koma ga mahaliccina na cika burina.
Sanyin da aka fara bushawa na asubahi shiya tashe ni nayi sallah sannan na tada Farida tayi,inta jiwo hayaniyar samarin gidan daga bayan window ɗinmu na tambaya Farida tace min ai a akwai masallaci a cikin gidan sun fito salla ne.
Da safiya nafito daga wanka kenan Yasira ta shigo muka gaisa tana gaya min sunyi waya da Granny tana gaishe ni nace ina amsawa nima zan ƙirata dan mun daɗe bamuyi magana ba.
Tare da Farida muka fito muka bar Yasira a ɗakin,part ɗin Adda Lawisa muka fara shiga dan shi yafi kusa da namu kamar yanda na lura dacewa al'adar gidanne kullum da safe ake shiga kowani part a ɗebi gaisuwa.
Tana zaune da mijinta muka iskesu muka shigo bayan sun mana izini sannan muka bisu da gaisuwa duk suka amsa cikin sakin fuska,mussaman mijinta datun zuwanmu nikam ban gashi cikin gidan ba.
"Alhaji ga matar uban namun fa"Adda Lawisa ta faɗa tana masa nuni dani ya ɗago ya sake kallona "Ayya kice matar tsoho ke yanzu kina yariyarki kika yarda kika auri tsoho"ya faɗa cikin barkonci
Adda Lawisa ta galla masa harara"ai ba auren dole bane ita ta ga tsohon tace tana so".nayi ƙasa da kaina ina murmushi.
Ya miƙe yana cewa Adda Lawisa zai fita,ta kamo hannunsa suka fita tare domin yi masa rakiya amma tace mu jirata.
Na taɓo Farida data toshe kunnuwanta da earpiece "mijin Adda Lawisa akwai shi da zolaya"
"Ai indai Uncle zaid ne kaɗan ma kika gani,daga shi har ita ɗin haka suke soyayya kuwa ko a gaban waye yinta sukeyi shiyasa kullum Hajiya kecewa basuda kunyar fulani".
Nan muka jira dawowar Adda muka ɗan taɓa hira da ita sannan muka wuce part ɗin Adda Hadiza,ciki-ciki ta amsa sallamar damuka shigo da ita tana daga kishingiɗe ƴar aikinta na mata tausa sai ƴar autarta Arfat dake wasa a waya.
Muka zauna tare da gaisheta ta amsa fuskar nan babu yabo babu fallasa.
"Ke kuma Farida daman su Mima sun faɗa min kin wani manne mata sai kace chewgum duk inda zata kina biye da ita".Farida tayi rau-rau da ido"Adda shi Hamma Habib ɗinne yace naje ina ɗebe mata kewa kinga wannan ne farkon zuwanta batasan kowa ba ba kaman Adda Yasira bace ita ai mun ɗan saba da ita".
Tsuke fuska tayi tana haɗe girar sama data ƙasa tace"kewa ko?wannan ce za'a nema sai ɗebe mata kewa ɗiyar data tsallake iyayenta tayi rayuwar ita kaɗai,saboda tana ganin cewa ta isa ta kai.to a wancan lokacin ɗin uban waye yake ɗeba mata kewar?ai ita tasan hanyar da sukebi ire-irenta marasa kamun kai wajen ɗebewa kansu kewa".
Zuciyar datake cikin ƙirjina ta duba da mungun ƙarfi yayin da hakan yabama hawayen danake matsewa damar fitowa,meye Adda Hadiza take nufi dani?akan abunda bata da masaniya akansa take jifana da waɗannan munanan zargin?.
Farida ce ta soma magana itama tana matso nata ruwan hawayen"Haba Adda dan Allah kuyi haƙuri mana ai abunda ya wuce ƙoƙari ake wajen mantawa dashi sai a gyara gaba".harara ta cilla mata kana ta ɗauke kanta daga garemu.
Na miƙe idanuna taf!da ƙwaya nace"Adda a huta lafiya"ina kawowa nan na ɗauki hanyar barin falon Farida data taso zata biyo baya na Adda Hadiza ta dakawa tsawa tare da faɗin"ke kuma ina zakije shashasha dawo ki zauna min anan".ba musu Farida ta koma ta zauna.
Kaina ya saramin hawayen danakeyi suka tsananta nazo dai-dai ƙofar fita daga falon naji na bangaje mutum nayi saurin ɗago kaina muka haɗa ido da Aliyu haidar ɗin Adda Hadiza,na ɗauke nawa idon daga cikin nasa Habib ne ke biye dashi shima ya rufo ƙofar ya shigo.
Nayi saurin maida kaina ƙasa sannan na fara ƙoƙarin raɓawa ta gefensu zan fita,amon muryarsa danaji sun sauƙa cikin dodon kunnuwana yasani tsayawa cak ba tare dana waigo ba.
"Lafiya Hibba wani abunne ya faru?"kaina kawai na jijjiga masa alamar A'a na cigaba da tafiyata.
ya kallo Aliyu yana faɗin"bari na bita naji ko menene".har yakai ƙofa Adda Hadiza ta buɗe dukkan muryarta tans faɗin"kar kasake kasa ƙafarka kabar cikin falon nan da sunan binta".
Aliyu ne ya fara magana cikin harshen fullaci wanda yafi zaunawa a bakinsa fiye da hausa"Adda kuka fa takeyi ai a kyautu ya bita yaji dalili ko".
"To ubana zai kaso ka dukan nace bazai jeba ko"tana kawowa nan a zancenta ta koma mazauninta ta zauna.
"Allah yabaki haƙuri"cewar Aliyu suka dawowa sukayi suka zauna cikin falon kawuna a ƙasa.
Ɗaki na wuce naci kukana na godewa rabbana,Mimi tazo ƙirana na fito cin abinci.sai da kowa ya hallara kana muka somacin abincin bayan mun kammala Habib yacewa Goggo Hanne yau zamu tafi zamubi jirgin ƙarfe huɗun yamma.
"Ubana kace sati ɗaya zakuyi yanzu kuma maiya canza maka ra'ayi?".
Yana ɗan sosa ƙeya yana sunkuyar dakai"Goggo wani aiki ne ya tasomin acan ɗin na gaggawa".
"To saika barsu matan nakan ai"cewar Adda Salamatu.
"Adda ai itama Hibbar tana makaranta kuma hutunsu ya kusa ƙarewa"ya faɗa yana kallon Aliyu wanda shiya kitsa masa hakan.Goggo Hanne tace "Allah ya kaiko lafiya yabada ladan zumunci"tsiraru daga ciki suka amsa da Amin.
Muna barin falon muka wuce ɗaki muka fara tattara kayanmu nida Yasira,zuwa ƙarfe biyu kuwa duk muka fito da shirinmu munayi musu bankwana Goggo Hanne tamin ishara da hannunta akan na zo na taho na iso gabanta ta shiga"kowasu iyaye na gari zasu sowa ƴaƴansu samun mataye na gari duk abunda kikaji ko kika gani inason ki barsu anan kar ki tafi dasu a zuciyarki kinji ko?"na ɗaga mata kaina"Madalla"ta furta sannan ta ɗebo wasu liffayu masu kyau da ɗauƙar ido batamu nida Yasira mukayi godiya muka karɓa.
Kowa hankalinsa yana ga Yasira mussamman ƴan matan,Adda Lawisa ce kawai tamin fatan sauƙa lafiya sannan ta karɓi lambar wayarta ita da Farida.
Khalifa ne ya kaimu airpot tare da Farida dasu Nabiha,dai-dai ƙarfe huɗu kuwa jirginmu ya ɗaga daga nijer zuwa najeria.
Muna sauƙa a najeria naji kamar an zaga ƙirjina ana kwashe mini kaso mafi yawa daga cikin damuyoyina,kwana biyu damukayi a nijer har wata ƴar rama nayi ga tinanin Umma daya addabi ruhina,ban samu nutsuwar ƙiran Yaya Fawas mu tattaunaba.
Muna sauƙa Malam habu yazo ɗaukar mu muka tafi gida,da Hajja idauna suka farayin tozali ai kuwa nafito na isa gareta muna musayen gaisuwa a tsakaninmu sannan Habib ma ya fito suka gaisa.
Yasira dana lura kamar bata da lafiya dan duk jikinta babu kuzari ga ƙafafunta dasuka kumbura tsimtim.
Malam Habu ya sauƙo mana da akwatunan mu sannan muka nufi part ɗina gabaɗaya,Yasira ta zauna tana sauƙar da numfashi.
Page 5⃣0⃣
Na zauna kusa da ita"Lafiya kuwa ƴar-uwa kodai gajiyace?"ta dafe goshinta idanunta suna lumshe tace"wallahi Anty duk banajin daɗin jiki nane".
"Ki tashi kiyi wanka sai ki samu ki kwanta"
Ta miƙe muka shiga bedroom ɗina Habib kam daman yana shigowa ya fita zuwa masallaci domin gabatar da sallan magrib.sai dana iddar da sallan isha'i na fito falo naɗan tarkaɗe kujerun da ƙura ya fara sauƙa a jikinsu sannan na wuce kitchen domin ɗaura girki indomie na tafasa mana yana gamowa na juye mana shi a babban plate,sannan na haɗa tea na jeresu a falo na tashi zan koma kitchen na ɗauko cups Habib ya turo ƙofar falon ya shigo sallamar daya shigo da ita ɗauke a bakinsa na amsa ina nufar hanyar kitchen ɗin.
Koda na dawo zaune a saman kujera na sameshi yana latsa wayar salularsa"ina Yasiran naga ke kaɗai kike aikin?".
"Tana ɗaki batajin daɗin jikintane"ma faɗa yayin danake zama ina rufe bakina kuwa tana fitowa nayi saurin miƙewa na isa gareta saboda tangal-tangal ɗin datakeyi har yanzu tana dafe da kanta.
Sai da muka zauna Habib ke tambayarta lafiya?tace kanta ke mata ciwo sai kuma ciwon jiki da kumburin da ƙafafunta sukayi,sannu yayi mata akan cewa gobe in Allah ya kaimu zasuje asibiti.
Sosai duk muka maida da hankalinmu ga Yasira muna bata kulawa abincin dataci ma kasa zama yayi a cikinta sai data amar dashi,lokaci ɗaya duk ta galabaita ina riƙe da ita mukayi ɗaki ta kwanta inata jera mata sannu har bacci ya ɗauke ta sauƙar numfashinta kawai nakeji,na gyara mata blanket sannan na fito falo wajen Habib.
"Tasama bacci ne?".nace"E ta kwanta"na kai ƙarshen zancena ina nufar gefen TV na ciro wayata daga cajin danasata lokacin dazan shiga kitchen,sannan na zauna ina danna ƙiran Ummi bugun farko ta ɗaga muka gaisa sannan na shaida mata mun dawo,ta cika da murna kuwa dan daman na lura bason zaman mu acan takeyiba.
Ina datse ƙiran naji hawaye sun ciko idanuna kewar Umma ya ziyarceni,wayar da mukayi da Ummi sai naji inama ace da UWATA nakeyinsa take bani shawarwari kamar yanda Ummi ke bani,take ƙoƙarin yayemin damuwata kamar Ummi,take ɗaukar duk wani lamari nawa da muhimmamci.
"Wifey lafiya kuwa kuka kuma nameye?"Tambayar da Habib ya watsa min wanda hakan ya fargar dani cewa hawayen ya fara zuba min cikin sanyi nace"Umma na tina wallahi zuciyata tana kewarta irin yanda kalaman baki bazasu iya faɗinsa ba,yau da Umma na kusa damu babu wanda zaimun kallon karuwa balle har a zargini akan wata rayuwata"na fashe da kuka har da shiɗewa Habib ya jawoni ƙirjinsa"Hibba dan Allah alfarma ɗaya zan nema a wajenki ki daina saka abu a ranki kinsan fa lalurar dakike tattare da ita,na miki alƙawarin matuƙar Umma na raye a bayan ƙasa kuma acikin wannan duniyar damuke rayu sai na nemo miki ita sai na dawo da ita gareki".
Ajiyan zuciya kawai nake sauƙewa kukan na nema cin ƙarfina nace"nagode Allah yasaka maka da mafifin alkhairinka yanda kake ƙoƙarin faranta min Allah ya faranta maka".
"Amin debbo am"ya faɗa yana shafo gefen ɓarin fuskana.
Mafarkin danayi akan Umma na sanar dashi ya min alƙawarin zai kaini gano dan mu tattauna maganar da Inna da Yaya Fawas.tare dashi muka shiga bedroom dubo Yasira yanayin jikinta yasani cewa ko zata kwana a part ɗina kawai.
Ya amince muka kwana tare da ita shima sai wajen ƙarfe biyu kafin ya tafi ɗayan bedroom ɗin ya kwanta,dan bata sama bacci mai tsawo ba sai a wannan lokacin data fara take farkawa.
Washe gari kuwa da wuri nagawa duk wani aikin gida nasawa Yasira ruwa tayi wanka sannan mukafi asibiti.muna zuwa muka wuce ofishin wani abokin Habib bayan mun gaisa ya sanar dashi lalurar data kawo mu bayan yayiwa Yasiran wasu tambayoyi tana bashi amsa ya ƙira wata nurse yace amata gwajin fitsari aka masa,suka fita tare sun kai mintuna ashirin kafin Yasira ta dawo office ɗin bayan wasu mintuna nurse ɗin ta kawo result ɗin.
Da cikekken nutsuwa yakebin result ɗin daki-daki da kallo yana karantawa ya ƙara fara'ar fuskarsa ya miƙawa Habib hannu sukayi musabaha kana yace"Abokina wannan labarin dazan baka na cancanci tukwuici