Showing 39001 words to 42000 words out of 104857 words
Chapter 14 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
na fara shirin kwanciya,ta cikin madubi na hango shi yana tsaye bakin ƙofar ɗakin,kamar ko yaushe ya naɗe hannayensa a ƙirjinsa.
Tashi nayi na ƙariso gare shi sai dana ɗaga kaina sama kafin nake kallon fuskar shi nace"Hamma inason naje wajen su Inna,wallahi ina kewarsu daga nan sai ka kaini na gaida Granny".
Murmushi yayi tare da riƙo hannu na muka dawo cikin ɗakin,sai da muka zauna bakin gado sannan yace"To in sha Allah gobe zan kaiki matuƙar hakan zai saki farin-ciki".
"Na gode hamma".
Na faɗa ina ƴar tsalle ta,sannan na tashi naje na ɗauko masa maganinsa da ruwana bashi ya sha.
Mun ɗan taɓa hira kafin kowa yaje ya kwanta.Nikam tsabar zumuɗin da son ganin su baffa na da Inna kasa baccin arziki nayi.Assalatun farko kuwa na tashi,tsaf na gama shiryawa na nufi ɗakin Habib.
Yana zaune dawowarsa daga masallaci kenan."Yanzu nake shirin zuwa na tadaki kiyi salla ashe ma har kin tashi".
Sai da ɗan rusuna sannan na gaishe shi ya amsa,tare da cigaba da faɗin"Ya naganki haka da shirin ki?".
"E na shirya ne".
"Kin shirya zuwa inna kenan?"ya sake jefo min tambaya.
Cikin ƙosawa da mu tafi ɗin nace"Hamma zuwa gano mana".
Dariya ya saka mai sauti sai dayayi mai isharsa sannan yace"Kin duba agogo kuwa ƙarfe bakwai ma fa batayi ba".
"Nidai mu tafi da wuri tunda daga can har gidan granny zamu wuce".Na faɗa ina ninke sallayar daya dawo daga masallacin da ita.
Ganin zai fara wata maganar ya sanya nayi,sauri na faɗa toilet na haɗa masa ruwan wanka na fito sannan na fara ciro masa kayan da zaisa.
Ganin da gaske nake yasa ya shiga wankan bai ɗau lokaci ba ya fito,dumping ruwan jikinsa na masa sannan ya shirya muka fito.Sosai driven yake sheƙa gudu da motar,kafin ƙarfe goma kuwa muka iso cikin gano.
Wani farin-ciki,nishaɗi ko murnar dana kasa bambamce,a cikin ukun nan wane nakeyi naji suka mamaye birnin zuciyata.Tun kafin drivern ya gama dai-dai parking,a ƙofar gidan baffa na fito daga motar da gudu na,na shiga cikin gidan ina ƙwalawa Inna ƙira.
Itama da murnar ta ta fito daga ɗaki nan kuwa na rungume ta,tare da Adda Barira wacce tunda Habib ya ƙira Baffa yake sanar dashi da zuwan namun.
Hajara ta faɗa mata nan gidan tazo dan aiwatar da umarnin malam dan dole sai da taimakon ta,abin zai tafi ba tare da amsama mishkila ba.
Sallamar Habib yasanya Inna raba jikin ta da nawa,sannan ta ɗauko sabuwar tabarmar kaban ta ta shimfiɗa mana.
Sai da muka zazzauna kafin,muka shiga gaida Inna ta amsa tana mai sanya mana albarka.A hankali nakai dubana ga ƙofar ɗakin,Anty hajara wanda tun fitowarsu sukayi cirko-cirko suna tsaye a wajen nace musu.
"Ina kwana nan ku".
Sai a sannan suka dawo daga kallon mu nida Habib,da suka shagala dayi mussamman Adda Barira dan wannan ne karo na farko data fara ganinsa.
"Lafiya kalau mutan katsina"Cewar Adda Barira sannan ta ƙariso,bakin tabarmar ta zauna cikin salo na gwanancewa a munafirci.
Itama Anty hajarar kujera ta,ɗauko ta zauna tana ta faman washe baki.Ladabtar da murya Habib yayi kafin ya shiga gaishe su suka amsa ba yabo ba fallasa.
"Lafiya kalau yaro,kuna nan dai lafiya ko ina fatan ba wata matsala?"cewar Adda barira.
Ko ni da har yanzu ƙuruciya bai gama bari na ba sai dana sha jinin jiki na,ga duk mai hankali wannan tambayar tana cike da manufofi balle kuma Inna.Dan yanda tayi maganar sai nake tinanin kamar ko ta ganu irin zaman da mukeyi da Habib ɗin ne.
Shigowar Baffa shiya katse Habib daga,maganar da zaiyi.Washe baki Baffa yayi kana yace"Lalle da mutan katsina ta dikko har kun iso?".
"E wallahi Baffa dayake tun a lokacin danake sanar dakai ma zuwan namu a waya har mu taso".
Habib ya faɗa yana miƙewa tare da Ƙarɓan fartanyan dake hannun baffan,ya ajiye gefe guda.Zaman Baffa yayi nan kuwa muka shiga gaishe shi yama amsawa.
Kwaɗon zogala da Inna tayi ta kawo mana,sosai mukaci har muna rige-rigen kai loma nida Habib.Ganin haka yasanya Baffa faɗin"ko a ƙaro muku ne?".
"A'a Baffa sai dai anjima,yanzu kam mun ƙoshi"na faɗa ina suɗar yatsa.
Tashi Habib da Baffa sukayi suka koma ƙofar gida,yayin da muka kafa hirar mu nida Inna lokaci bayan lokaci Hajara take jefa baki a cikin hirar tamu.
Adda barira kam izuwa yanzu na gama fahimtar so take ta kaini ga bango,domin duk tambayar da zata min sai ta sako.
"Yaya zaman ku da Habib ɗin ina fatan kuna zaune kalau ko?".
Murmushi kawai nake sakar mata,ko kaɗan ban yadda nayi maganar zaman dake da Habib da ita ba.
Ƙiran sallan zuhr da aka fara,ya sanya Inna tashi tayi alwala sai data iddar da alwala tata sannna tace"Hibba ki tashi ki ajiye wayar nan,kiyi salla ".ta faɗa tana gyara ɗaurin zanin ta mai launin ruwan ɗaurawa.
"To Inna ta yanzu nima zan tashi nayi ".
Na ƙarishe maganar tare da sakin dariya,dan chart muke da Yasira ta what's app ina gaya mata munzo Inna ta mana wannan shegen kwaɗon zogalan nan natan mai daɗin tsiya.
Ajiye wayar nayi sannan na tashi,na ɗauki butar da inna tayi alwala dashi na zubo ruwa na farayi.
Ina cikin shafar kai Adda barira ta fito daga banɗaki.
"Haba!Hibba dubi kanki,sai kace bana amarya ba duk kitso nan ya tsufa".
Nidai nasan kitsona bai tsufa ba,duk da cewa kuwa tun na biki nane da aka min.Amma ina gyara shi sannan bana wasa da kula da gashi na duk da ba wani gashin kirki gare ni ba,amma ina tattalin abina.
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
________________________
Page 2⃣7⃣
Nikam ma dariya taso ta bani,bance da ita uffan ba na cigaba da alwala ta ina gamawa nayi ɗakin Inna.
"Inna wallahi wannan matar ta cika iyayi da yawa,to ni yanzu ina ruwanta da kitson kaina?".
Na faɗa ina shimfiɗa sallaya Inna tace "Ai Hibbatu da gaskiyar ta har yaushe zaki bar kanki haka ki tsefe shi kafin ku koma sai a miki wani".
Sai dana fuskanto inda take zaune a bakin gado taya saƙar hula nace"Inna muda yanzu zamu tafi,kuma ma to inna tsefe wa zaimin?".
"Hajara mana ai ta iya kitso,duk yawancin makwabtan mu nan suke zuwa ta musu".
Ta faɗa tana tattara zaren a ɗan yatsar ta.Nidai bance uffan ba ko lokacin danake gidan Baffa ko kaina zai dudduge Hajara ba ta taɓa cewa in tsaife zata min ba.
Kawar da tinanin komai nayi a raina,na tada kabbara na farayin salla ta.Inna iddarwa ƙiran Habib yana shigowa waya ta,katse ƙiran nayi sannan na ɗauko maganin sa dake cikin jaka ta,na fita ina cewa"Inna bari yanzu zan dawo sai nayi tsifar".
Ƙofar gida na fito nan kuwa na hango shi zaune cikin mota Baffa kuwa na zaune bisa tabarmar dake shimfiɗe ƙofar gidan tare da wani baƙo.
Sai dana gaishe su sannan na wuce wajen Habib ƙofar motar na buɗe na shiga,ina shiga kuwa drivern ya fita.Magananin na shiga balla masa,sannan na ɗauko goran faro dana hango cikin motar na miƙa masa.
Runtse idanunsa yayi sannan ya saka maganin cikin bakinsa,kafin yabi bayansu da ruwa.
"Nadai lura yanzu kin maida hankalin ki wajen ganin inasha kwayoyin nan,ba tare da miss up ba ko?".
Sai dana murmusa kafin nace"E mana alƙawari fa na ɗaukar wa Granny,so kake inmuje taga ɗan jikallen nata ya rame tace bana kula dashi".
Sai daya ƙara kora ruwar sannan yace"to ai waɗannan maganin basu zasu hanani mutuwa ba in lokaci na yayi".
Sosai gabana ya faɗi kamar faɗuwar aradu,cikin mintunan da basu gaza ɗaya ba idanu na ya kawo ruwar ƙwalla.
"Baza ka mutu ba Habib ka barni da tarin zunubin kasa sauƙe haƙƙin ka dana tauye,inna maka addu'ar tsawon rai ina fatan zuwar ranar dazan sauƙe haƙƙin ka da suka rataya a wuya.Bana son naje gaban Allah da wannan laifi mai girma".
Ina gama faɗin haka na fice daga motar,ko Baffa dayake tambaya ta lafiya ban saurara ba na wuce cikin gidan.
A soro na tsaya na goge hawayen fuska na,sannan na ƙarisa shiga ciki.
A tsakar gidan na iske Inna,Hajara da kuma Adda Barira.Kan tabarmar dana gani shimfiɗe a wajen nakai,mazaunaina na zauna tare da zare hijab ɗin dake kaina.
Nan Inna ta fara min tsifar tana gamawa Hajara ta miƙo min mataji na taje sannan ta fara min kitson.
Runtse idanuna nayi da ƙarfi ina faɗin"wash!kiyi min guda goma".
Saboda zafin kitson dayake ratsa ilahirin kaina,har sai da jijiyoyin kaina suka fito raɗa-raɗa.
Kamar yanda na faɗa guda goman tamin dukka baya.Godiya na mata sannan ta miƙe tayi ɗakinta yayin da Adda Barira ta rufa mata baya.
Nikam a wajen nayi kwanciya ta,riƙe da waya ta ina ƙiran yaya Fawas.
Sai da Hajara ta rufo ƙofar ɗakin,tare da sake labulen sannan taja hannun Adda Barira suka zauna akan ledar data rufe ko'ina acikin ɗakin.
"Adda kinga rabo ko?,ƙarshe dai gashi mun samo gashin kanta".
Hajara ta faɗa tana ɗaga matajin dake riƙe a hannun ta,wanda yake ɗauke da gashin kaina a cikinsa.
Taƙaitaccen murmushin gefen baki Adda Barira ta saka kafin tace"Yo ai daman keki tsaya sanya har kike ganin bazaki iya samowa ba.Ai ƴar-uwa ina tabbatar miki tunda wannan yarinyar ta zamto silar da Adamu ya ɗaura hannunsa akan ki da sunnan duka,abin dabai taɓa faru a cikin tarihin aurenku ba wallahi sai tayi kuka da idonta kai wataran ma sai ta nemi hawayen tsiyayarwan ta rasa,Ke kaɗai kika rage min a duniya babu iyayen mu,babu dangi tsayayyu akan mu,muba ƴaƴa ba ba jikoki ba bazan taɓa iya zuba ido wani ya zamto sanadiyar shigarki damuwa ya kwana lafiya ba".
Ta ƙarishe maganar tana tino irin faɗi tashin dasukayi a rayuwa,da yanda dangi suka wofartar dasu bayan rasuwar iyayensu.
Karɓan matajin dake hannun Hajara tayi,sannan ta cire gashin dayake cikin tare da ɓallo bakin matajin tasa cikin wani ƙyalle ta ƙulle su.
Miƙewa tayi suka fito waje,muna tsaye muna sallama da Inna da kuma Baffa.
Har jikin motar suka mana rakiya hajara da Adda Barira ma ba'a basu a baya ba.
Muna tafiya Adda barira itama sallama tayiwa Inna sannan ta miƙe izuwa gidan malamin.
Yana zaune akan kilisa ta iske shi,zama tayi dan daman ba'a masa sallama inza'a shigo wajen sa.
"Allah gafarta malam ga abubuwan daka buƙata,mun samo su".cewar Adda Barira tana miƙa masa ƙullin.
Ƙullin ya karɓa sannan ya ware gashin ya ɗeba kaɗan a hannunsa ya watsa cikin kwaryan dake gabansa,wanda yake cike da ruwa sannan ya shafa saman ruwan yana faɗin"Matso ki gani wannan itace?".
Matsowa Adda barira tayi ai kuwa hoto nane ya bayyana cikin ruwan,gani nan cikin mota muna tafiya har mun kusa barin cikin ƙauyen gano.
"Kwarai kuwa malam itace".
Sai daya bushe da wata iriyar dariya marar daɗin,sauraro sannan ya shiga ƙulunboton sa da sauran gashin.
Sai daya gama sannan ya buɗe idanunsa,dasuka rikiɗe suka juya kamar garwashin wuta.
Ciki wata iriyar murna mai tsananin, sanyawa duk wani wanda aka yiwa magana da ita firgici da tsoro yace"Daga yau ba ita ba kwanciyar hankali sun raba hanya dashi zata tsane shi fiye da komai a cikin duniya,sannan zamu aika mata da aljani ɗan mama ya hanata samun nutsuwa a cikin gidan".
Sai daya numfasa sannan ya ɗaure fuskarsa,kamar bashi yayi wannan dariya ɗazun nan ba.
Sannan ya ɗauko wasu layu guda biyu ya miƙa mata tare da faɗin.
"Ki sama tsohuwar rijiyar da ruwan cikin ta ya kafe,aka daina amfani da ita ki binne waɗannan layu a bakin rijiyar".
Kamar an sauƙe mata wani abu mai nauyi daga ƙirjin ta,haka Adda Barira taji ranta ya mata fes zuciyar ta ƙal.
Miƙewa tayi tare da ajiye masa kuɗin daya buƙata ta fice sai da ta binne layu sannan ta wuce gidanta.
Yamma sosai muka iso cikin damaturu rabona da garin tun ranar da muka bar YSU.Direct gidan granny muka wuce sosai bakinta ya kasa rufuwa saboda murna,mussamman dataga Habib ɗin kamar hankalinsa yanzu a kwance yake.
Iya kusa ransa inda zata sani tayi saboda tarairayar da take min.Anan muka kwana washe gari kuwa sai da mukayi sallan zuhr kafin muka fara shirin tafiya.
Granny kam cewa tayi ya barni a wajen ta nayi kwana biyu,ya nuna mata bazai yiyuba saboda ina zuwa makaranta.
Haka muka tafi bayan muje gidan Dr bashir matar shi nada tsohon,ciki haihuwa ko yau ko gobe.Sai wajajen ƙarfe goma da wasu mintinu muka isa cikin katsina,a gajiya muka isa gida.
Ina shigowa na wuce ɗakina kayan jikina na rage nayi wanka na kwanta,ko jiran shigowar Habib banyi ba.
Washe gari kuwa bamu da lectures sanin hakan yasa nasha bacci na,sai wajen ƙarfe takwas na farka.A gurguje nayi wanka na fito ban shafa komai a fuskana ba na fito na nufi kitchen.
Ganin Habib danayi yana fere dankali yasa na tsaya,sannan nayi saurin cewa"Hamma kaika kanka kake wannan aikin?".
Na faɗa ina ƙarisowa gareshi tare da karɓan wuƙar hannunsa na fara fere dankalin.
Sai daya kama waist ɗinsa,yana sharar zuffar data taru a saman goshin sa sannan ya ce"Yau dai kawai nace bari na mana girkin na hutar dake,sai kuma naga abin na neman gagara nafi 20min ina fere dankalin nan".
Murmushi na sakar masa ina cewa"to ai daman ba aikin ka bane,yanzu dai na hutar dakai bari naje na haɗa maka ruwan wanka,har kayi lattin tafiya office".
Shima murmushin ya maido min dashi tare da faɗin"A'a nima na hutar dake zan haɗa ruwan wankan dakaina".ya faɗa yana ficewa daga kitchen ɗin.
Cikin sauri nagama suya dankalin sannan na haɗa tea,na jeresu a dinning ina tsaye a wajen ya fito.
"100 percent hamma kayi kyau kamar a sace a gudu".
Nafaɗa ina ƙarisowa cikin falo domin ɗauko masa maganinsa,sai dana ɗauko sannan na dawo dinning area ɗin.
"To ai ni bazan satu ba"ya faɗa yana jawo min kujera sai dana zauna na ɓalla masa maganin na miƙa masa da ruwa yasha.
Muna gama yin breakfast ɗin muka tattare wajen tare,sannan na masa rakiya har wajen motarsa.
Da mugun sauri drivern ya taso ganin fitowar habib ɗin,sai daya gaida mu sannan ya karɓa jakar habib ɗin dake hannu na.
"Jiya dana dawo malam Idi mai gadi yake sanar dani matar ka ta haihu har yau suna shine baka sanar dani ba".
Cewar Habib yana nuna kansa da key ɗin motar dake riƙe a hannunsa.
Ƙoƙarin magana driven ya fara ya katse shi,ta hanyar zara hannunsa a aljihu ya miƙa masa wasu kuɗaɗe da bazasu gaza dubu ɗari ba.
"Ga wannan kayi hidimar suna dasu, sannan ka koma gida sai jibi sannan ka dawo aikin,iyalanka suna buƙatar kularwa a halin yanzu".
Sosai drivern yake godiya yana ƙara ɗurƙushewa a wajen,ɗaga masa hannu habib yayi alamar ya tafi.
Addu'o'i na shiga masa sannan ya tafi,na juya na koma a falo na tsaya na kunna kallo.
A hankali kunnuwa na suka fara jiyomin kamar ana ƙiran suna na a cikin bedroom ɗin Habib,wanda kuma na riga nasan cewa ni kaɗai ce a cikin gidan sai su malam idi dasuke waje.
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
____________________________
Page 2⃣8⃣
Rage volume ɗin kallon danakeyi,nayi sannan na kasa kunne kozan ƙaraji amma banji komai ba.Miƙewa nayi na ajiye remote ɗin dake hannuna,na nufi kitchen zan ɗauko ruwa.
Sosai gaba na ya faɗi ji danayi a wannan karan an ƙiran sunan nawan da ƙarfi kuma muryar yarace.
Tunin jikina ya ɗauki rawa duk da yanda zuciya ta take bugu hakan,bai hanani dakatawa daga hanyar ɗakin Habib dana nufa ba.
Sai dana runtse ido na da ƙarfi,baki na na rawa na shiga karantu bismillah sannan na buɗe ƙofar ɗakin.
Wayam babu kowa kuma babu alamun ma wani ya shiga ɗakin,Sai dana lalleƙa har cikin bathroom amma babu kowa.
Dawowa falon nayi na wuce na ɗauko ruwar na dawo hannunane,ya shiga karkarwa tunin na sake kofin tangaran ɗin dake hannun na ya faɗi ƙasa ya tarwatse.
Wani ƙaton ƙadangare na gani akan kujerar falon inda na tashi ,irin masu jajayan kai ɗin nan.
A guje na fice daga falon na nufi bangaren malam Idi mai gadi ina ƙwala masa ƙira.
Tare da matarsa Hajja suka fito,kusan a tare suke tambaya na lafiya?.
"Malam Idi dan Allah ƙadangare ne ya shigo min falo,ka fitar min shi".na faɗa ina waigen falon.
"To".
Kawai yace sannan ya nufi hanyar falon bai daɗe ba ya dawo yana faɗin"Hajiya nifa banga komai ba wallahi,na duba ko'ina a cikin falo".
Sai dana dai-daita numfashi na dayake fizga tsabar kaɗuwar danayi sannan nace"Yana nan akan kujerar farko kana shiga zaka ganshi".
"Wallahi Hajiya babu komai sai dai muje dake ki nuna min".
Gaba yayi muka bishi a baya nida hajja muka nufi falon.Rarraba idanu na shiga ina duba inda naga ƙandagaren tabbas anan na barshi amma kuma yanzu babu ko alamarsa.
"Hajiya to kindai gani,gaskiya nan kam babu wani abun".cewar Hajja
Muryarta ne ya tsinkayo ni daga duniyar tinanin dana lula,figigi nayi ina cewa"to shikenan amma nidai tabbas na ganshi".
Fita sukayi sannan na rufe ƙofar na koma bathroom ɗina sai dana ɗauro alwala sannan na kwanta bayan na kunna karatun alqur'ani a wayata.
Sai wajen ƙarfe biyu sannan na tashi,salla nayi sannan na wuce kitchen na haɗa tea kawai nakeda sha'awar sha.
Dan ba girki zanyi ba kasancewar Habib sai yamma sai dawo,ina buɗe ƙofar kitchen ɗin idanu na suka sauƙa akan wannan ƙadangaren,yana gefen gas yayin dayake fuskanto ƙofar kitchen ɗin.
Saurin maida ƙofar nayi na rufe inajin yanda ƙirjina yake dukan tara-tara.
"Innalillahi wa'inna alaihirraji'un".
Kawai bakina yake iya furtawa,shi na cigaba da nanatawa har na tsawon wasu minti na.
Nayi jihadi na buɗe ƙofar a hankali na shiga ware idanuna,ina sauƙesu dai-dai inda na ganshi yanzu wayam babu shi.
Da wani mungun hazari na fice daga kitchen ɗin,ɗan madaidaicin part ɗin malam Idi mai gadi na kuma nufa.
Nan na iske matar shi Hajja tana wanke-wanke,gani na datayi cikin wannan yanayin yasata miƙewa tare da faɗin.
"Hajiya lafiya".
Ta ƙarishe maganar tare da nauraye hannuwan ta,da ruwar ɗaurayar wanke-wanken natan.
"Wallahi tallahi na ƙara ganinsa wai hajja bakwa ganin sa ne ni kaɗai nake ganinsa kenan?".
Na faɗa ina sakin wani kuka mai matuƙar ƙarfi,ƙarisowa gareni tayi tasa hannu tana goge min hawayen dake sintiri a samar fuskana kafin tace"Kidaina wannan kukan Hibba,bari Malam ya dawo sai yaje ya ƙara dubawa kozai gansa".
Kaina kawai na gyaɗa mata ina wucewa naje na fara mata wanke-wanken hawayen dake gudana a idona basu daina ba,kamar yanda nima banyi wani ƙoƙarin hanasu zubowa ba.
Dan a wannan lokacin,ina tinanin su kaɗai ne zasu sani naji sauƙi daga irin raɗaɗin da zuciya take ciki.
A nan part ɗin su Hajja na wuni koda malam Idi ya dawo Hajja,ta sanar dashi dayaje ya duba baiga komai ba.Sai gabda magrib Habib ya dawo,malam Idi dayaje buɗe masa gate nan yake sanar dashi ina