Showing 60001 words to 63000 words out of 104857 words

Chapter 21 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7344

na asibiti munyi na gargajiya amma har yanzu bamu dace ba,wataƙil wannan shine ƙaddarata a rayuwa saimu zubawa sarautar Allah ido munga yanda zaiyi dani kuma".
Kamo hannuna tayi sannan ta nunamin kusa da ita tace nadawo na zauna,na tashi na zauna akan gadon tana lallashina tare damin alƙawari bazata zura ido a wulaƙantani ba.
Maganganun Granny suka dawo kunnuwa tamkar dirar mikiyi,na rutse idanuna kukan danakeyi yana tsananta a lokaci guda.


Ummi tace nashiga toilet na wanke fuskata na tashi na shiga,nayi kamar yanda ta umarceni dana fito na tarar da ita tare da Yasira.
"Naji duk tattaunawarku da Granny,bazan hanaki nunawa mijinki soyayya ba kamar yanda ta faɗa miki sai dai bazan laminci wulaƙanci ko kuma cin fuska ga Hibba ba,wallahi duk randa naji to kiyi kuka da kanki dan in ranki yayi dubu sai nabi su,one by one na ɓata su kuma gyaran jikin ma tare za'a muku".
Tana kawowa nan a maganarta ta miƙe ta fice daga ɗakin,nima ƙafata danajisu sun min nauyi na jasu na wuce kan gadon Ummi zan kwanta,muryar Yasira dana tsinkayo ya dakatar dani daga hakan.
"Hibba Wallahi duk maganganun Granny kawai na amsa mata ne amma babu wanda nakeda ƙudurin aikata shi a aikace,na mata uzuri domin tsabar son farin-cikin Hamma shiyake sata makancewa a wasu lokutan dan Allah ki fahimtar da Ummi".
Ta kai ƙarshen maganar tare da takuwa ta riƙo hannuna,a sanyaye nace"Naji zan mata"na zare hannuna daga cikin nata sannan na kwanta.
Koda Habib ya dawo Ummi tace masa yayi magana dani akan lefen daza'aje haɗawa gobe,inda abunda nake buƙata nima sai na faɗa ya amsa mata da to.
Sai yamma lilis na farka a gurguje na faɗa toilet naje canza audugar matan dake jikina sannan nayo alwala,na fita nayi sallan Asr naɗan taɓa karatu kafin Sayyid ya shigo yace Hamma na ƙira na a falo.


Ko cire hijabin danayi sallan banyi ba nabi bayansa muka fito falon,zama nayi yayin da shikuma ya fita.Habib ya sanar dani lefen daza'aje haɗawa gobe.
"Gaskiya lefe zamu haɗa na bugawa a jarida,sake mana bakin aljihu zakayi"na faɗa ina ƙirƙiro murmushin ina yaɓawa a fuskata.
Murmushi yasaka sai da hakwaransa suka bayyana da kuwa kyawawan wushiryar dake tsakanin hakwaran,kana yace"koma menene dai bazai kai naki ba"nayi saurin cewa"A'a kam harma zaifi dan ai yanzu samunka dana da ba ɗaya bane komai za'ayi shi a wadace".


"To shikenan kema ki rubuta naki"


Nace"nikam nahutar dakai aƙarawa amarya".
Tsura min ido yayi har sai dana zargi kaina kona faɗa wani abunda,bai kamata na faɗa bane cikin kalamai na?maganar daya farayi tasa nadawo daga tinanin"Kije dai ki rubuta min duk abinda kike buƙata,daga naira ɗaya har abunda yake naira millayan goma zan miki shi".magana na fara ƙoƙarin yin ya ɗaga min hannun sa alamar bayason jin komai.
Sai dana tashi daga kan kujerar danake na matso gabansa na durƙushe kan gwiyoyina ina cewa"Mun gode Allah yasaka da alkhairi Allah ya ƙara buɗi,Allah yabaka ikon yi mana adalci,Allah yasa mu zame maka mataye na gari sanyi idaniya agareka".


Tunda na fara maganar yake amsawa da Amin har nakai Aya,ya taso ya rungumeni yana samin albarka,nayi saurin raba jikina danashi har wani ya ganmu na fice a falo da sauri na inacewa"Bari na ɗauko maka maganin ka".tun kafin yace wani abu har nakai ga barin falon.




UWATACE SANADI


Tsarawa/rubutawa




©Maimunah Tijjani Iyam


__________________________________


Page 4⃣0⃣


Ji nayi an jawoni da ƙarfi har ina neman faɗuwa,na juyo da sauri zan saki ihu Ummi ta toshe min bakina sannan taja hannu na mukayi ɗakinta,kan gado ta cillani sannan ta maida ƙofar ɗakin ta rufeta.
Sai data zauna gefen kafin tace"Karki sake kice bazaki karɓa kayan nan ba,ki zauna ki rubuta duk abunda kike buƙata ki kaisama kinji ko?".
Na gyaɗa mata kaina alamar naji sannan tace inje inkai masa maganin,na ɗauka nafita na bashi yasha tare mu kaci abinci dan ɗazu ba wani cin na ƙirki yayi ba sannan na dawo ɗaki nacigaba da karatuna.
Daren Ranar Daddy ya dawo duk muna falo muna masa sannu da zuwa,suna ƙara tattauna maganar biki shida Granny,Ummi kam yatsina fuska tayi kamar batajin abunda suke faɗin.
Washe gari kuwa ina gama zana jarabawata na dawo gida,Ummi ta tsareni da tambayar cewa ina takardar abubuwan danake buƙata datace na rubutosu tun a daren jiya?nace mata ban rubutaba.
Na miƙo min wani farar takarda tace in Habib ya tambaye na basa,bata jira mezance ba tayi wucewar kitchen domin haɗawa Daddy tea.
Buɗe takardan nayi ina karato abubuwan dasuke rubuce da manyan harrufa,ajikin takardan ɗaya bayan ɗaya.wannan list ɗin zai haura milliyan Biyar da ɗoriya,na maida takardar na rufe ina girmama irin ƙaunar da Ummi kemin a cikin raina.
Da yamma kuwa Habib ya ƙirani yace nabawa Sayyid list ɗin abubuwan danake buƙata,na ɗaukar takardar nabawa Sayyid yakai masa.
Bayan isha'i kuwa Ummi ta kaiwo Yasira tace tayi ƙirana an kawo kayan,na fito tun kafin na ƙariso wasu akwatun masu launin ruwan zuma suka ɗauki hankalina.
Muna fara bubbuɗe kayan Ummi tace mai ruwan zuman shine nawa,mai launin ruwan hoda kuwa shine na Yasira.yawan akwatunan mu ɗaya da ita kuwa nashi bakwai-bakwai sai dai kayan ciki nata yaso yafi nawa yawa amma tsadarsu ma ɗaya.
Nayi godiya na koma ɗaki Yasira kam daman tana ƙirana ta wuce ɗakinta,dan bai kyautu ta tsaya a wajen ba.
Haka abubuwa suka cigaba da gudana gyaran jikina tare Ummi tasa ake mana da Yasira,duk yanda aka tsumata nima haka haka sha'anin biki ya kankama lokacin sauran mu kwana biyar mu gama jarabawa,kwana uku kuwa suka rage ɗaurin auren duk waɗanda muke shiri dasu a makaranta na bawa Lima IV ta raba musu.


Ummi ta saya anko tace nasu Inna ne insun zo,ai kuwa nabada aka ɗinku mata duk da bawani taro za'ayi abikin ba dangine kawai amma gidan ya cika maƙil!ta ko'ina ka wulga mutane ne,ana gobe ɗaurin auren na dawo daga makaranta nasamo Inna tazo Baffa da Yaya Fawas kuwa ɗaurin aure zasuzo.
Ƴan-uwan mahaifiyar Habib ma sunzo kodana nunawa Inna kayan faɗan kishiyar da akamin,ta yaba kyan kayan sosai.
Ranar ɗaurin aure kuwa da asuba Daddy ya taramu ya mana nasiha sosai,ƙarfe goman safe za'a ɗaura auren har ƙarfe tara da wasu mintina ina kwance a uwar ɗakar Ummi.


Zazzaɓi na neman rufeni jikina sai karkawa yakeyi daren jiya sam!na kasa runtsawa sai dana keɓe kaina a cikin banɗaki naci kuka sosai inna tari har da jini.bayan nasihar da Daddy ya mana na wuco ɗakin Ummi nayi kwanciyata.
A haka Ummi tasamoni ta bani magani nasha,sannan ta haɗa min ruwan wanka nayi na shirya tace inje in dubo Habib dan har yanzu shima bai fitoba.mayafina kalan atamfar danasaka na ɗaura a kafaɗata na fito na nufi part ɗin Habib.
Tun daga falo nake rabka sallama,jin shuru yasa na kutsa kai izuwa bedroom ɗin na sameshi yana kwance abunsa.
Da mamakina na ƙarisa gareshi ina yaye bargon daya lulluɓa dashi nace"Haba!Ango ya haka anacan mutane duk sun haɗu kai kuma kana nan,ko shiryawa bakayi ba".




Siririn tsaki ya saka yana dafe goshinsa yace"wallahi banajin daɗine,na rasa meka damuna".
Har nakai ƙofar bathroom na haɗa masa ruwan wanka,sannan na ɗauko masa towel na basa ya shiga wankan,na gyare ɗakin tsaf!sannan na buɗe waduruf na ciro masa wasu sabbin kayan dana gansu a sama-sama nake kyautata zaton sune wanda zaisa.
Ina ajiye kayan akan gado ƙira yana shigowa wayarsa lokaci guda yana fitowa daga toilet ɗin,ganin Bashir ne ke ƙirar wayarsa yasa nayi saurin isa gareshi na fara dumping ɗin ruwan jikinsa,na murza masa mai sannan ya zara kayansa.
Na fereshi da turare sannan na riƙo hannunsa muka fito,part ɗin Ummi muka wuce,anan falon muka iske Granny muka rusuna muka gaisheta ta amsa tare da cigaba da cewa"Su Hibba uwar gida,watau shine tun dana sako ƙafata cikin gidanan,ko zuwa gaisheni bakyayi balle kuma kizo muyi hira,saboda kin ƙullace a ranki akan na dage sai mijinki ya ƙara aure ko".


Habib yayi saurin cewa"Haba!Granny dan Allah ki daina wannan maganganun a gaban mutane".


"To ubana"tana faɗa tana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.dai-dai nan aka fito da Amarya Yasira ta shiryo tsaf cikin wani haɗanɗen leshi sai walƙi yakeyi,ƙannen Ummi suke riƙe da ita.
Tashi nayi na kamo hannunta muka ƙariso cikin falon,nan kuwa mai carema ya fara ɗaukar mu bayan mun jera da Habib ɗin.
Ana gamawa Habib ya fita wajen ɗaurin auren,zama nayi ina tinano maganar Granny,dangin miji kenan komai son dasuke maka wataran sai sun nuna maka kai ba kowa bane,bansan sanda na fara hawaye ba sai jinayi Maryam Matar Bashir dako lura da cewa tana cikin falon,ban yi ba ta riƙo hannuna,saurin kawar da hawayen nayi tamin raɗa a kunnena akan bai kamata nayi kuka cikin taro ba.


Sai wasu su ɗauka baƙin-ciki nakeyi da auren,jan hannunta nayi nahau janta da ƙarfi har Abbul-khair yana neman faɗuwa daga hannunta muka nufa ɗakin Ummi.
Muna shiga maryam ta maida ƙofar ta rufe har sai tayi ƙara,gauuu kakeji na zube akan gadon Ummi ina sakin kuka kusa ni Maryam ta zauna bayan ta kwantar da Abbul-khair tafara lallashina.
"Hibba kiyi haƙuri Granny girma yanzu yafara zuwar mata,dole ana mata uzuri domin wasu tsuffin kamar yara sukan koma insukazo irin shekarunta,ki daina wannan kukan karma wani ya shigo ya ganki haka dan Allah"takai ƙarshen magana tana tallafo fuskana na tashi na zauna.


Tashi nayi batare danace ko kanzil ba,danji nayi bakina gabaɗaya yamin wani irin nauyi,ajiyen zuciya kawai nake sauƙewa ɗaya nabin ɗaya,ganin haka yasa Maryam ta miƙe ta ɗauko min ruwa a fridge nasha ai kuwa na ƙara sakin kukan dayake fitowa kai tsaye daga ƙasan zuciyata ina cewa.
"Maryam wani laifi na aikatawa ubangiji daya hanani farin-ciki a cikin rayuwa,tun daga yarintata har izuwa yanzu nayi tinanin aurena da Habib zai zamto makullin dazanyi amfani dashi wajen buɗe ƙofar farin-ciki a rayuwata ashe ba haka bane.ƙalubale cikinsa yafi komai yawa dai-dai da rana ɗaya ban taɓa samun nutsuwa acikin raina ba,kullum cikin tashin hankali da fargaba abun dazai faru nake, jarabawa kala-kala daga wannan sai wancan tun da aka tsaida maganar auren nan Granny ta canza min komai zan mata bana mata gwaninta.Ummi ce kawai ke fahimtata wallahi akwai damuwa sosai acikin wannan ƙirjin nawa amma banida wanda zan iya zama dashi na buɗe masa sirrikana,sai dai na shiga banɗaki nayi kuka yanzu har aman jini nakeyi,na tabbatar da za'a gwada ni to za'a gano ina ɗauke da ciwon zuciya,wani irin baƙin ƙaddara ne ke bibiyar rayuwata wallahi ina cikin matsala"


Damƙe hannuna cikin nata Maryam tayi tace"Hibba kowani rayuwar aure akwai nasa ƙalubalen,sannan kowacce mace haƙuri takeyi a gidan aurenta ki godiyawa Allah daya miki ni'imar aure yasanyaki cikin bayinsa dasuka rayu ƙarƙashin inuwar aure mata nawa suka rasu ba tare dasunyi aure ba?mata nawa suka rasa ci da sha a gidan aurensu kuma suka cigaba da zaman auren?,Mata nawa suka rayu har suka koma ga mahaliccinsu basuyi aurenba?,Mata nawa suka rasa rayukansu saboda rashin lafiya?.Ke Allah ya azurta ki da lafiya,imani,kuma yayo ki musulma mai imani ya azurtaki da mijin dayake ganin darajarki gami da girmama alaƙar dake tsakaninku ki godewa Allah akan wannan ni'imar".
Kukan danakeyi kawai na tsagaita sosai maganganun Maryam suka ratsani inajin wani sabon imani yana bin zuciya da ruhina,ruwan data kawomin naƙara sha sannan na tashi na shiga toilet na wanke fuskana sannan na Maryam ta gyara min kwalliyan fuskana.
Muka fito sosai na saki raina duk abunda yake raina na damuwa dannesa nayi,nayita walwalata mukaita ɗaukar photo da Habib da Amaryarsa da kuma sauran dangi,sannan na fito wajen su Yaya Fawas da Baffa suka ƙarayi yimin nasiha sosai.
Da yamma kusa jama'a sun fara raguwa,ina zaune a ɗakin da aka sauƙesu Inna ina cire kayana zan shiga wanka Yasira ta shigo Inna tace"Amarya "ƴar dariya Yasira tayi kana ta zauna kusa da Inna kafin tace"Amarya a ina kuwa Inna ai sai dai ayi sha'ani kawai".
Ta dafa kafaɗarta nidai towel na zara na shiga wanka ta,har na fito na iske Inna tana tayiwa Yasira nasiha,Abbul-khair dake wance akan cinyar Inna na ɗauka na fara jijjigashi ya tashi kuma Maryam ta fita.
A cinyata na ajiyeshi nashafa mai,sannan nasaka rigar atamfa ta nafito daga ɗakin na barsu ɗakin Ummi na zauna na tarar dasu tare da dangin mahaifiyar Habib.


Ina zama Habib ya shigo suka gaisa da mutanen wajen,idona yakai kan wata matashiyar budurwa danaji an ambace sunanta da Batul naga sai wani shishshigewa Habib takeyi.
"Hamma bakason zumunci wallahi yaushe rabon daka taku ƙasarmu"
Ƴar dariya kawai yayi dan bai cika son shiga cikin taron mataba,kuma baya sakewa a cikinsu.koda ya gaji da suturunta hannuna yaja muka fita daga ɗakin muka wuce part ɗinsa,muna shiga falo ya zara babban rigarsa tare da sakin wata siririyar tsaki na dube shi lokacin danake gyara kwanciyar Abbul-khair a kafaɗata nace"Mijina wacece wannan batul ɗin ban wayeta ba?".
"Ƴar goggo Suwaiba ce ƙanwar mahaifiyata,wai ahakan su kuke suka hada mu aure tun kafin na aureki ".
Murmusawa nayi ina ƴar harararsa nace"Ai kuwa mun rufe ƙofa makullin ma muje fashi rijiya".
Dariya mukayi dukkaninmu sannan mukayi ƴar hira,sai wajen ƙarfe tara sannan mukayi sallama ya taroni har ƙofar part ɗin Ummi.


Washe gari akayi ƴar ƙwarya-ƙwayar walima wanda nina haɗa shi,ƙarfe biyu aka tashi da yamma kuwa Inna dasu Yaya Fawas suka koma na ɗeba mata zannuwa kala biyar acikin kayan da aka min,sannan Ummi ta basu savouiners ɗin bikin.
Nida Sayyid mukayi sickers da kuma memo wanda yake ɗauke da hutonan mu,mu dukka uku Habib na tsakiyar mu,kallo ɗaya zakayiwa photon ka ganu irin kamar dake tsakanin Habib da Yasira,dan ko Sayyid dasuke uwa ɗaya uba ɗaya dashi basuyi kama haka ba.
Dukkansu fararene nice baƙar fata a tsakaninsu,Maryam keta tsokala na wai duk nafisu kyau.
Da daddare kuwa Daddy da Granny suka ƙara yimana nasiha,sannan na riƙo hannun Yasira wacce tayi shigar laffaya muka shiga mota,daga ni sai ita sai Habib dukka muna baya driver najan motar.
Part ɗin dake kallon nawa aciki aka yiwa Yasira jere,ina riƙe da hannunta muka shiga part ɗin nace ta shiga da ƙafan dama tayi yanda na umarce ta kuwa nakaita har cikin bedroom na damƙata a hannun angonta.


UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam




______________________________




Page 4⃣1⃣




Shurune ya karaɗe ɗaki nakawar dashi ta hanyar fara faɗin"Allah mun gode maka daka nuna mana wannnan ranar acikin rayuwarmu,bazan daina gode maka ba Allah daka bawa mijina matace ta gari tazama mallaki a gareshi,kuma mafi kusa dashi daga cikin ƴan-uwansa.Allah ka haɗa kanmu muzamo masa mataye nagari wanda zaiyi alfahari damu".
Habib yace"Amin"a sanyaye kana Yasira ma ta faɗa.


Ganin duk annurin fuskar Habib ta gushe lokaci guda yasa nace"To ango mijin amarya saura kuɗin sayan baki".


"Baza'a yafe min ba?"


Nasaki dariya nace"ina ka taɓa ganin an yafe kuɗin sayan bakin amarya,kawai ka biya don amaryarmu mai tsadace"


"To nawane?"furcin Habib sai dana ɗaga kaina kamar mai tinanin wani abun kafin nace"duk kuɗin dake jikinka ayanzu shi zaka bayar shine farashi,ba a ƙidaye ba balle kace anmaka tsada".
Yayi murmushi sannan ya ciro ɗaurin ƴan dubu ɗai-ɗai daga aljihunsa,guda uku ya miƙo min na karɓa ina miƙe tare da musu sai da safe.
Habib ya kallo Yasira wacce fuskarta ke lulluɓe yace"bari na rakata".kafin tace wani abun har kai ƙofar ɗakin ya biyoni a baya.
A falo muka tsaya inacewa nidai ya koma zan tafi abuna ni ɗaya,yaƙi haka ya rakoni part ɗina har cikin bedroom hannuna yaja muka shiga banɗaki nayo alwala sannan na kwanta ya rufa mini blanket,yamin addu'a ya toni dashi.
Sai da safe mukayiwa juna sannan ya miƙe zai kashe min wutar ɗakin,har kai ƙofar ya jiyo tare da faɗin"ki rufe idanunki dan banason kiga fitana".
Na ɗaga masa kaina alamar naji,sannan na rufe idanuna kamar yandaya umarce ni ya fita daga ɗakin wani kuka mara control ne suka suɓɓuce min tun inayi daga kwance har na miƙe na zauna na jingina bayana ajikin gadon.


Jinayi wani ƙululun baƙinciki ya ziyarce dana tina wai yau Habib ne zai kwana da wata maccen a shimfiɗa ɗaya,abun danafi so da ƙauna acikin rayuwata na sadaukar danawa farin-cikin saboda ɗaurewar nasa.na rasa nutsuwar zuci na duk dan na raya murmushin dake saman fuskarsa.
Sautin kukan dana keyi ne ya ƙaru sosai duk ɗakin ya ɗauka,nasoma ajiyan zuciya ɗaya nabin ɗaya.
Ban iya runtsawa ba tsawon daren wannan ranar,wanda a tarihin rayuwata wannan daren yana ɗaya daga cikin darare huɗu dabazan mance dasu ba,na ɗaya dare aurin aurena da Habib na biyu daren da ya kwana da fushina acikin ransa lokacin da Granny ta ganu irin zaman damukeyi,na uku daren ranar danayi ɓari,sai kuma wannan daren danajin tamkar ƙarshen farin-cikin dazanyi kenan a iya sauran kwanakin dasuka ragemin a duniya.
Ƙiran assalatun farko kuwa kamar acikin kunnuwana limamin ya ƙira,dan idona kar!lokacin na miƙe nayi alwala sannan nayi sallatul fajr nakuma sallan asubahin.na daɗe akan sallayan ina karatu duk wasu addu'o'in neman sauƙi dana iya.


Sai wajen ƙarfe shida nabar ɗaki na wuce kitchen nafara haɗa breakfast,na soya irish potatoe da egg sannan na haɗa tea najeresu akan dinning,sanda na gama har bakwai ta wuce na shiga bathroom da sauri nayi wanka sannan na shirya saboda jarabawar da zamuyi ƙarfe tara na dawo falon.
Ganin su Habib basu fitoba yasa nafara karatun exam ɗin danake dashi,har takwas tayi da wasu mintuna kafin na rufe handout ɗin danake karantawan.
Na sauƙe wata ƙatuwar ajiyen zuciya ina tsaida kallon akan agogon bangon dake maƙale jikin wall ɗin falon,har na ɗaga wayata zan ƙira Habib sai kuma na fasa na wuce nayi nawa breakfast ɗin sannan na saka hijab ɗina na fito.


A cikin harabar gidan na hango Habib da Yasira suna nufo nawa part ɗin,suna tafe suna nishaɗi fuskokinsu ɗauke da annashuwa,take zuciyata ta tayo min cewa sun more daren amarcin su,nayi saurin kawar da wannan tinanin na isa garesu kafin su iso na gaishe da Habib ɗin ya amsa,sannan Yasira ta gaidani a taƙaice na amsa datare da ƙarawa da "an tashi lafiya abincinku nakan dinning nizan tafi school".


"Subhanallahi!na manta gaba ɗaya da jarabawar da zaki zana yau,dana fito tun ɗazu na kaiki ai"cewar Habib fuska cike da damuna nace"ba komai malam Habu zai kaini".
Ban jira amsar dazai maido min da itaba,nayo saurin barin wajen ina amsawa Yasira Allah ya bada sa'a datamin da Amin.
Habib ya ƙira malam Habu yace ya kaini makaranta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login