Showing 27001 words to 30000 words out of 104857 words
Chapter 10 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
na gaishe ta shima ta amsa sannan ta shiga faɗin"Mun gode sosai kan irin halaccin da kika gwada mana,na amincewa ki auri Habib haƙiƙa kin ceto rayuwarsa a lokacin data dace Allah ya miki albarka".
A sanyaye nace"amin"sannan ta cigaba da cewa"Kuma duk sanda ya ɓata miki kizo gidan kiyi zaman ki abinki".
Dariya Habib yayi sosai kafin yace"Granny tun yanzu zaku fara haɗe min kai?".A hankali nace"nagode nima hajiya sosai allah yasaka muku da mafificin sakayyarku".
Da "amin",ta amsa dashi sannan mukayi sallama na miƙawa Habib wayar shima ɗin sallamar yayi mata sannan muka cigaba da hirar mu.
Har izuwa lokacin da Daddy da baffa suka fito,inna kuwa tanata ƙara jero wa Ummi godiya sai Yasira da Sayyid dasuke bayansu sosai Yasira ta yaba da yanayin garin.Tasowa nayi daga wajen Habib cike da kunya,naso wajen Ummi ina musu addu'ar Allah ya kiyaye hanya hakan nan ma Inna da Baffa ke musu bendir ɗin kuɗi Daddy ya ciro daga aljihun sa ya miƙawa Baffa duk yanda yaso Baffa ga karɓi kuɗin ƙi yayi.Haka suka tafi akan bayan kwana biyu Sayyid zaizo mu koma katsinan tare dashi inna kuwa ta haɗawa Ummi tarkacenta,irin na tsofaffi su bushshen kuɓewa da kalwa Ummi ta karɓa tare dayi mata godiya.
Sai da muka daina ganin motar tasu sannan muka koma cikin gidan,ɗakin Inna nida Yasira muka shiga yayi da Innar ta shiga banɗaki,Baffa ma ɗakin Hajara ya shiga tana tsaye jikin ƙofar ya same ta sai huci takeyi.
"A'a Hajara na zata ai bacci kikeyi,shiyasa ban ganinki ba a waje ashe idonki biyu?"Baffa ya faɗa yana zame babbar rigarsa.
A wulaƙance ta kallo shi tare da faɗin"To mezan zo na muku?,Malam yanzu da hankalin ka ka ɗauki auren Hibba bakawa waɗannan mutanen?,wayasani ma ko dashi wanda aka fake da cewar anzo nema masa auren nata dashi suke yawon taziba.......".
Bata ƙarisa ba sakamaton marin da Baffan ya sauƙe mata a gefen fuskarta,ba zato ba tsammani.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
_______________________________
Page 1⃣9⃣
"Hajara izuwa yanzu kam,bazan jure ba sannan bazan ɗauki duk wani ɓatancin da zaki gandanta hibba dashi ba.A da na kuskuren jefa ta cikin ƙunci amma bazan ƙarayin mai-maita wannan ba"cewar baffa.
Dafe kuncin ta hajara tayi tana faɗin"malam ni ka mara? ".
"E sannan ba ma keba duk wani mahalukin dazai tsaya a gaba na,yana jefar hibba da mummanan kalami to irin hukuncin daya cancance shi kenan".
Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗaki,alwala yayi kafin ya leƙo ɗakin inna yana cewa"ku tashi kuyi salla an kira".
Sannan ya wuce masallaci domin ƙiran sallan la'asar da aka farayi.
A tare muka fito da yasira muna cikin alwalan,hajara ta fito sai data tsaya ta dallo mana wata uwar harara sannan ta fice tare da sakar mana tsaki.ba wanda yace da ita daga uffan muka kammala alwalar muka shige ɗakin inna.
Hajara na fita gidan wata yayar taje wacce itama take aure a cikin ƙauyen ganon,tana zaune a tsakar gida tana tsintar yakuwa haraja ta shigo.
"Ƴan-uwa rabin jiki,hajara kece tafe da yammacin nan?".
Ƙarisowa hajara tayi ta zauna kafin tace"Adda barira wallahi nike tafe kuma matsalace ta kawo ni".
Ajiye yakuwar dake hannunta adda barira tayi gefen guda kafin tace"to hajara kekuwa wace matsala ce ta ɗago ki cikin wannan sakaliyar yammacin?".
"Wallahi adda kinga yau kawai muka wayi gari inna wannan yariyar da take ƴar wan malam ta dawo,bayan tsawon watannin data shafe bata gidan kuma wai harda wanda zata aura tazo tare da iyayen sa,shine fa daga nacewa malam ni ban yadda da dawowar wannan yariyar ba ya bincike ta shine ya wanke ni da mari nan a kunci na".
Hajara ta faɗa tana gyara zaman akan tabarmar kaban salati adda barira ta shiga yi tare da faɗin.
"Oh ni barira ƴan iska basa ƙarewa a duniya,yanzu shi adamun ne ya mare ki akan wannan maganar?".
"Wallahi kuwa adda ni yanzu ma zuwa nayi ki haɗani da ɗaya daga cikin malaman da kuke hulɗa su,a mallake min shi ta yanda ko kara na ajiye zaiyi shakkar tsallake ta,tunda gashi yanzu tun ba'aje ko'ina ba ya fara mari na".cewar hajara.
Dafa kafaɗarta adda barira tayi sannan ta shiga faɗin"haba!ke kuwa ƴar-uwa sai kace ba jini taba ai ita wacce ya miki abun a dalillin ta,ita za ayiwa bashi ba sawa zamuyi asa mata tsanar shi yaron data kawo zata auren,taji duk duniya babu wanda ta tsana sama dashi sannan daga baya zai mu dawo kan adamun.Yanzu ki tashi kije gida zanzo nima".
Murmushi hajara ta saka kafin tace"yauwa adda ta".
Nan suka cigaba da hirar su,sai da akayi sallar magrib sannan hajara ta komo gida.
Muna zaune a tsakar gida hajara ta shigo kamar bataga mutane ne a wajen ba tasa kai tayi shigewarta ɗakin ta.ranar sosai mukayi hira da inna da kuma baffa.
Washe gari tare da yasira muka gyara gidan tsaf!sannan muka ɗaura girkin shinkafar da baffa ya sayosai da muka gama komai sannan mukayi wanka,muna zaune a ɗakin inna ina karatun jarabawa wanda da zaran mun koma zamu fara.
Inna ta ɗago labulen ɗakin sai data washe baki sannan ta shiga faɗin"ku fito munyi baƙo".
Sai dana rufe littafin sannan muka fito tare da yasira.
Turus nayi ganin yaya fawas zaune a tsakar gidan shida baffa,sai a sannan na tina da cewa daman yau zaizo a hankali naji ɗumin wasu hawaye masu zafi suna bin kunci na.Shima ni ɗin yake ganin bakin sa na rawa ya furta"hibba".
"Yaya fawas".
Yunƙura yayi zai tashi sai kuma ya koma ya zauna,da ƙarfi ya runtse idanun sa hawaye na zubowa kusa dashi na tsuguna ina kamo hannun shi ya fusge.
"Yaya fawas dan Allah ka yafe min kar ka azababtar da zuciya ta ta hanyar yin fushi dani".
Numfashi ya saka mai ƙarfi wanda ya tafiyar da kukan daya ke kafin yace.
"Ummul-khair kin sani cikin wani hali,a ko yaushe zuciya ta kan nuna min kamar na gaza riƙe ki a matsayin amanar da abba ya barni,karki manta ranan da wannan iftila'in ya faɗawa abba abinda yace dani shine "ka kula da ƙanwar ka".wanda hakan ya zamto furcin sa na ƙarshe a gare mu".
Sai daya numfasa sannan ya ɗaura cewa"Ina kika shiga?".
Ɗaura kaina nayi kan ƙafarsa ina cewa"yaya fawas zaɓi ne ya ƙare min,a lokacin banda zaɓin daya wuce hakanamma haƙƙin ka danasu baffa bai barni nayi rayuwa cikin farin-cikin ba yaya na ka yafe min".
Sunkuyar dakansa yayi wanda hakan yabawa hawayen dasuka ƙara ciko idonsa damar tsiyayowa sannan yace.
"Na yafe miki my cute angel ki daina kuka kinji,kukan ki na ɗaga min hankali".
"Na daina yayana,na daina ka gani"na faɗa ina share hawayen dake bin fuskar yana sauƙar har izuwa wuya ta.
Sai a sannan yasira ta gaishe shi,ya amsa mata yayin dayake ƙoƙarin tsayar da hawayen sa,inna ce ta mishi bayani wacece ita.
Sannan baffa ya sanar dashi komai daya sani game da habib da kuma ahlinsa,sosai yaya fawas yayi murna sai fatan alkhairi yake min amma baffa yace"ba za'a sanar da mahaifiyar kuba sai tukunnan abubuwan sun ƙara kamkama,dan kar tace wani abun kuma".
Sosai inna tayi na'am da zance baffa haka nan ma yaya fawas,wuni mukayi muna hira da yaya fawas tare mukaci abinci wanda rabon mu dayin hakan tun kafin bayan rabuwa.
Anan yaya fawas ya kwana dan dama tare dashi zamu koma katsina a cewar inna yaje ya gano wajen.kwana nan mu huɗu a gano sannan muka fara shirin komawa domin jarabawar da zamu fara.
Tunda mukazo ba kallon arziki tsakanin mu da hajara,hakan nan zaman lafiya yaƙare tsakanin ta da baffa.
Ranan ana gobe zamu koma katsina muna zaune a tsakar gida muna taya inna tsintar wake,baffa da yaya fawas kuwa sun tafi goma Adda barira ta shigo.
Washe baki inna tayi kafin ta shiga faɗin"lale maraba da zuwa barira kece tafe?".
"E wallahi inna nice tafe hajarar tana nan kuwa?"ta faɗa tana daga tsaye.
"E ki shiga tana daga ciki".
Gaishe ta mukayi a tare nida yasira ta amsa tanabin mu da wani irin kallon dana kasa fassara meyake nufi,mamaki ko al'ajabi.
"Inna wannan ce yarinyar da ake tayi da ita a cikin garin nan ko?,ta sa ƙafa tabar gida tsawon lokaci ba wani makalukin daya sata a idon sa.Oh ni bariratu naga ikon mai mana ruwa da iska,abin mamaki baya ƙarewa a duniya inda ranka kuwa kasha kallo".
Sai data bina da wani irin kallo mai cike da tuhuma,tana jawo kujerar da inna ta miƙo mata ta zauna sannan ta ɗaura da cewa.
"Ke kuwa yarinya duk tsawon wannan lokacin ina kika shiga?,inna kika je?,wajen wa kike zaune?".
A dunƙule ta jefo min tambayoyin tana ƙara kafe idon ta akaina.
Hawayen danake ƙoƙarin hana fitowar sune suka biyo kunci na,yasira da ta lura da hakan ta kamo hannun na tana jijjiga min kanta tare dayi min alamar nabaryin kukan.
Inna ce tayi saurin cewa"Ashsha haba!barira da girman kike biyewa maganar mutan garin nan haba".
Fitowar hajara ne ya katse adda barira daga maganar da tayi niyyar amayar da ita.
"Adda ki shigo mana kika tsaya daga waje"hajara ta faɗa tana daga tsaye ƙofar ɗakin.
"To ai shikenan allah ya kyauta"cewar adda barira yayin datake miƙewa tayi ɗakin hajara.
Sosai na sakin kukan danake dannewa duk mutane irin kallon dasuke min kenan?,meyasa zasu yanke min wannan hukuncin ba tare da bincike ba?,watakil inna jewa umma ma ita ma kallon hakan zata min wacce taje yawon duniya.
"Anty kiyi haƙuri ki daina wannan kukan bashi da amfani,kuma kisan komai kikayi sai mutane sun sama abin suka acikin sa"yasira ta faɗa cikin sigar lallashi.
Sannan inna ta ɗaura da nata"gaskiya ne maganar yasira domin yanzu kisan an daina kiyon dabba sai dai ta mutum".
Share hawaye na nayi sannan nacigaba da gyaran wanken ba tare danace dasu uffan ba.
Domin raɗaɗin da zuciya take ciki kalmomin baki sunyi kaɗan wajen furta shi.
Adda barira na shigowa ɗakin hajara ta mayar da ƙofar langalanga ɗakin ta rufe.
Ƙaran da ƙofar tayi ta sanyani juyo na ganni ƙofar sannan na maida kaina ga aikin danake yi.
"Oh ni bariratu yau idona sun gane min abin mamaki,hajara ki dubi irin suturun da ke jikin wannan yarinyar sannan babu alamar wahala ko yunwa a tattare da ita.Sannan ace ba yawon karuwanci taje ba?".adda barira ta faɗa tana zare hijab ɗin dake kanta.
Sai da hajara ta saki ajiyan zuciyawanda hakan,ke nuni da irin ƙuncin da zuciyar take cikin akan maganar sannan tace.
"Ai adda baki gama komai ba,sai ma kinga yanda malam yake ririta kamar jariri ɗan wata uku".
"Ai kuwa yau komai zaizo ƙarshe"adda barira ta faɗa tana since gefen zanin ta.
Ƙullin magani ta ciro tare da riƙon hannun hajarar tana damƙa mata kullin tana faɗin.
"Kinga wannan kullin shi zaki barbaɗa mata a cikin duk wani,abu nau'in ababen sha kamar kunu da dai sauran su.Bi'izinillahi indai tasha to sai dai a yi wani labarin amma ba wannnan ba domin ita da wannan yaron har abada zuciyar ta zatayi dakon tsanar shi,da duk wani abu daya dangance shi ki fara aiwatar da wannan kafin mu juyo kan shi adamun".
Karɓa hajara tana ƙara damƙe ƙullin cikin hannunta tana faɗin"nagode adda ni daman nasan ba wani matsala tawa dazan kai miki ki kasa magance min ita".
"Haba!ke kuwa ƴar-uwa nayiwa wasu ma balle ke".
Haka suka cigaba da ƙulla mumanan manufofin su,muna zaune inda ta barmu suka fito ni kuwa ina zaune kan dakalin ƙofar ɗakin inna ina waya da habib.
"To inna ni na wuce allah ya bamu alkhairin sa"cewar adda barira.
"To a gaida mutan gidan"inna ta faɗa tana ɗaukar buta zata shiga banɗaki.
Rakata hajara tayi sannan ta dawo "Ana ta abun kenan".
Ta jefo min maganar yayin datake wucewa kusa da inda nake zaune tayi ɗakin ta,tana sakin wani yalwataccen murmushi.
Da kallo nabita ina ƙoƙarin fassara manufofin dake dunƙule cikin wannan dariyar tata,jin Habib yana ƙiran suna na a cikin wayar yasa ni sakin wannan tinanin.
Ko dasu Baffa suka dawo,nan muka zauna muna ta shan hira Yasira sai faɗi takeyi"zarayi missing ɗin kwaɗon zolayan inna".
Da mamaki na naga Hajara ta fito ta zauna cikin mu,abinda da tun zuwan mu banga tayi shibada ita ake ta hirar.
Baffa kuwa sosai ransa ya masa daɗi ganin hajara ta watsar,da komai daga ranta har ta fito ta zauna cikin mu,ana wasa da dariya.
Washe gari da wuri muka shirya kayan mu muna jiran zuwar Sayyid,muna tsakar gida Yasira sai hoto take ɗauka mana da yaya Fawas da kuma su Inna da Baffa tana faɗin inmun Koma zata bayar a wanke mata su muryar Hajara dana tsinkaya ne ya katseni,daga sheƙa dariyar danake yiwa Yasira.
"Hibba har kun fito kenan?,daman fura ce kingan ta mai kyau na dama miki ita".
Ta ƙarishe maganar tana miƙomin kwaryar furan.
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________
Page 2⃣0⃣
Karɓa nayi sannan nace"Ayya Anty Hajara da baki wahalar dakan ki hakan ba nagode".
Sai data marairaice murya kafin ta shiga faɗin"Haba!Hibba kedai ki sha ko kaɗan ne ai zanji daɗi nima,tunda kuka zo fa ban samu na muku wani abu ba sai wannan".
Inna ce ta amshe zancen tana faɗin"haba!Hajara suda zasuyi tafiya kyabasu fura salon ta kashe mata jiki".
"Haba!ilnna furace fa kawai,kuma kingan ta ba mai yawa bace".
" To ai shikenan"shine iya abinda Inna ta furta.
A hankalin na kurɓa furan sosai tamin daɗi dan haka nake shan ta sosai,kaɗan na rage a cikin kwaryan ina tanɗe baki.
Nan Yasira tace zata sha guntun da wani mungun hanzari Hajara ta karɓa ƙwarya daga hannun Yasira tace"Bari na zubo miki naki ta mussamman".
Sannan ta karɓa ƙwarya taje ta zubo mata tas!Yasira ta shanye.
Sallamar Sayyid ta sa dukkan mu kallo shi yaya Fawas ne ya amsa sallamar,sannan ya sukayi musabaha sayyid ya gaida Baffa da Inna suka amsa tare da yalwata fara'ar dake ɗauke a saman fuskokinsu.
Kayan mu muka fito dasu muka sasu a motar sayyid sannan muka shiga yin ban kwana gasu Baffa.sosai yake mana addu'ar Allah ya tsare mu ya kuma kaimu lafiya haka nan ma Inna da hajara yaya Fawas kam daman dashi zamu tafi Sannan muka tafi.
Muna shiga cikin katsina muka wuce gida a compound muka same su suna jiran isowar mu,cike murna Ummi take mana sannu da zuwa sam bakinta ya kasa rufewa.
Yaya Fawas gaisawa sukayi da Daddy sannan ya gaida Ummi ma musabaha sukayi Habib sannan muka shiga,ko da muka shiga ƙara gaisawa muke tayi mussamman yaya Fawas da Daddy yake ta masa bayanin akan Habib ɗin.
Ɗaki muka shiga da Yasira bayan Ummi tamin umarnin dana kaiwa yaya Fawas kayansa cikin part ɗin Sayyid,wanka mukayi sannan mukayi salla muka fito mukaci abinci,Habib kam tunda muka dawo yakejin kansa cikin wani farin-ciki na mussamman.
Haka muka gama cin abinci muka dawo falo muka cigaba da hirar mu,haka nan kawai naji zuciya ta ta kasa nutsuwa da irin kallon da Habib kemin,miƙewa nayi ina cewa"Ummi ina zuwa"sannan ya wuce ɗaki cikin sauri.
Sai a sannan Daddy yake sanar musu da sunsa bikin nanda wata biyu shi da Baffa sosai Ummi take bayyanar da farin-cikin game da haka.Haka nan ma Sayyid da yaya Fawas, Yasira kam miƙewa tayi da gudu tana nufo ɗakina.
Ina kwance rufda ciki na rungume matashi na,Yasira ta shigo ɗakin kaina ta faɗo tana cewa"Anty nataya ki murna ansa auren ki da Hamma nanda wata biyu".
Ras!naji gabana ya faɗi tureta nayi daga jikin na sannan na juya mata baya"Anty Yasira ki barni na gaji inason na huta".
Nan ta fara lissafin kalolin event ɗin da za'ayi,ni dai kam bance da ita komai ba dan ji nayi duk raina ya jagule na rasa gane kaina haka na wuni.
Da yamma ina kitchen ina haɗawa Ummi fruit sallad waya ta ta hau ringing,ko ba a faɗa min ba nasa Habib ne ɗagawa nayi na kara a kunne na ba tare da nace komai ba.
"Please inba abinda kikeyi kizo inna jiran cikin garden".Bance mishi komai ba na kashe wayar tare da ajiye ta gefe guda.
Sai da gama abinda nakeyi na kaiwa Ummi fruit sallad ɗin sannan na wuce ɗaki nayi kwanciya ta,wayar tace ta fara ringing tsaki na saka sannan na miƙe na saka hijab ɗin na har ƙasa sannan na fito.
A cikin garden ɗin na hange shi yana zaune kan kujerun plastic da aka shirya su a wajen,da sallama na isa gare shi ya amsa sannan na zauna.Shuru ne ya ratsa wajen ina ɗago kai muka haɗa ido dashi saurin ɗauke nawa idon nayi daga cikin nasa yayin na naji,wata iriyar tsanar ganin fuskar sa ya shige ni tun daga yatsun ƙafata har tsakiyar kaina.
"Amaryan Habib da yaddan allah"ya faɗa yana ƙare kafeni idanu.
Sai dana haɗiye wani yawu mai ɗaci,wanda naji ɗacin sa ya wanzu cikin ko'ina a baki na kafin nace"Angon Hibba",Ba ƙaramin jarumta nayi ba wajen wannan haɗa waɗannan kalaman.
Sosai ya saki murmushi sannan yace"Munyi magana da Granny tace inkun gama jarabawa nakai mata ke ku gaisa".
"To Allah ya nuna mana nima zanso haka".na faɗa ina ƙara takurewa cikin hijabi ta.
"Amin".ya amsa dashi sannan ya cigaba daja na da hira,dauriya kawai nakeyi nake amsa masa amma duk sa'in da sautin muryarsa ta bugi dodon kunne na tsanar shi ne take ninkuwa cikin zuciya.
"Zan shiga ciki kaina yafara min ciwo"na faɗa ina ƙara takurewa.
"Suhbanallahi!Allah ya sauwaƙe muje na baki magani"ya faɗa yana miƙewa.
Tashi nayi muka jera dashi muka shiga cikin gidan maganin ya ɗauko mini nasha sannan ya taraka ni har ƙofar ɗaki,sai daya ga shiga ta sannan ya koma.
Koda na shiga kwanciya nayi yayin da ƙaryan ciwon kan danayi ya zama gaske,domin ji nake tamkar an ajiye min wani abu mai nauyi a tsakiyar kaina.Bansan ta yadda zan fara tunkarar Daddy ba nace masa a fasa wannnan auren domin jinake da a ɗaura wannan auren gwara akai ni kabari.
Kuka na saka mai ƙarfi ta yaya zan butulcewa mutanen dasuka zame mini gata a lokacin dana rasa hakan daga kowa,suka dawo min da farin-cikin dana yanke tsammani dashi,sannan suka bada gudumawa wajen cimma buri na.
Ana cikin haka muka fara jarabawa kullum Habib shike kaini kuma ya dawo dani,a cikin haka yaya Fawas ya koma tare da Sayyid suka tafi wanda shima ya koma makaratan.kamar na bishi haka nakeji amma saboda jarabawar damukeyi nayi shuru.
Cikin haka muka gama jarabawar Ummi na roƙa akan inason naje daura gidan su Anty Amina dan cikin,kwanakin nan sosai nakeyi mungaye mafarkai akan ta.
Tare da Daddy Ummi suka tattauna maganar ya amince min,naje tare da Yasira da Habib haka washe gari muka shirya muka ɗauki hanyar