Showing 87001 words to 90000 words out of 104857 words

Chapter 30 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7282

mana ita".
Jijjina kanta kawai tayi tace"Ruwa Hamma"ya miƙe domin ɗauko mata ruwan wayarsa da tafa ringing ya ɗaga,na ɗauki goran ruwan na ɓalle murfinsa na fara bata a baki.a hankali take sha ni kuwa duk hankalina yana kan babyn da tun ɗazu take baccinta.
Gani naji ta fara dawo da ruwan baya wucewa idanunta sun kafe wajen guda ta tsaya cak!.


"Yasira!Yasira!!"na faɗa ina ɗan taɓo kafaɗarta ai kuwa sakake ta zame daga kishingiɗewar da tayi.na ɗago hannunta ya sake lamau,nayi jarumtar kai hannuna dai-dai ƙirjinta naji baya bugawa.
Ihu na kurma salati yana biye dashi Habib ya ƙariso ciki da hanzari ,babyn danake ƙoƙarin saketa ya fara karɓa.hannuna na rawa na masa nuni da Yasira"Hamma bata motsi ta tafi ta barmu".
Shima bugun zuciyarta ya fara taɓawa yaji shuru"Hamma ta mutu ko dan Allah karkace min ta mutu".na faɗa ina ƙara ƙarfin kukan danakeyi wanda yasa Hajja da nurse ɗin shigowa.Hajja ta riƙeni dan a lokacin ƙafafuna suna barazanar kasa ɗaukata.
Nurse ɗin tace mu fito mukafito muka zauna a waje,sannan taje ta sanar da likitan suka dawo tare mintuna biyu a tsakani likitan ya fito duk muka isa gareshi.


Dafa ƙafadun Habib yayi"Abokina sai haƙuri Allah ya mata rasuwa ta koma ga mahaliccinta"yana kawowa nan yabar wajen yayin da nurse ɗin ta rufa masa baya.


"Waye ya rasu?"sautin muryan Ummi kenan daya sa dukkaninmu juyowa muka zubawa hanyar shigowa wall ɗin idanu,nan take naji zuciyata ta karaya nakasa gaskata maganar likitan wai ƴar-uwace ta rasu?.
Saurin isa gare Ummi nayi na faɗa jikinta ina sakin wani razanannen kuka a cunkushe,ta ɗago ni"Ke Hibba menene na kuka kuma bayan ta sauƙa lafiya,muje na ganta".har tayi gaba na riƙo hannunta ta fizge taje ta karɓa yarinyar dake hannun Hajja tana jijjigata.
Habib ya iso gareta tare da ɗaura kansa kan ƙafadarta"Ummi Allahn dayafimu son Yasira ya karɓa abunsa".
Hawaye kawai idanunta yake fitarwa tunda ya faɗa mata bata ƙara wani ƙwaƙwaran,motsi ba haka nan ta rungume yarinyar tsam!a jikinta.a duk sanda naji sautin kukan yarinya sai anji kamar ana sukan raina da mashi amanar Yasira ce a gareni wannan yarinyar.
Sayyid kam nan inda yake tsaye ya durƙushe ya haɗa kai da gwiwa,yana nashi kukan na rashin ƴar-uwarsa ɗaya tal!a duniya.Hajja ce ta fara lura da yanayin Ummi akayi saurin sanar da doctor ya dubata yace jininta ne ya hau aka bata gado.
Habib yake sanar da Granny lokacin daya ƙirata inaji,tana faɗa masa gobe zasu ɗauko hanyar katsina ganin jaririya da uwarta,sanda ya sanar da ita kuwa Allah kaɗai yasan irin tashin hankali da kaɗuwar data shiga.Haka nan ma Daddy shikam tunin ya biyo jirgin ƙarfe huɗu ya taho.


Tun zuwarshi Sayyid yake faɗa mishi halin da Ummi take ciki ya shiga ɗakin."Hajiya ita mutuwa halittace ta ubangiji dukam mairai bazai tsallake ba,sannan ita da tafi ba gaggauwa tayi ba mukuma damuke nan ba jinkiri mukayi.kowa lokaci yake jira in tayi kuwa babu tsimi babu dabara sai an tafi,Yasira addu'ar mu take buƙata fiye dakomai ahalin yanzu Allah yajiƙanta ya karɓi shahadar ta".


Amin-amin shine abunda yata fitowa daga bakunan mutanen ɗakin,sannan suka wuce wajen likitan suka karɓawa Ummi sallama.jaririyar datake tsala ihu iya ƙarfin da ubangiji ya bata,datake riƙe a hannun Sayyid sai faman jijjiga yakeyi.
Haka muka fito ina riƙe da Ummi zuciyata tamin nauyi sosai dan jinayi kamar an ajiye min dutsi acikin ƙirjina.


Motar Sayyid muka shiga nida Ummi da kuma Hajja,sai Sayyid ɗin yake driving ɗin motar.Habib da Daddy kuwa sun tsaya tahowa da gawar.
"Hajiya dan Allah kiyi haƙuri,ai haƙuri akeyi kowa yasan mutuwa tanada zafi da raɗaɗi amma dangana ake sawa zuci"furcin Hajja kenan ga Ummi.
Muna isa na ɓalle murfin motar muka fito,muka shiga cikin gidan Sayyid kam lock ya dannawa motar ya ɗaura kansa kan siriyari yana nashi kukan mai tsuma zuciya.har sai dasu Habib suka iso tare da motar asibitin data ɗauko gawar Yasira sannan ya fito.
Part ɗin Habib aka shiga da gawar aka ajiye sannan Daddy yasa aka rufe gabaɗaya part ɗin.tun shigowarmu cikin gidan na wuce ɗakin Yasira yayin da Hajja ta ƙara wanke jaririyar ta saka mata kayan sanyi ta goyeta.
Furcin Yasira na ƙarshe a gareni su suke tamin sowa a kunnuwana,wallahi har yanzu zuciyata ta kasa yarda cewa wai ta rasu bata cikin wannan duniyar.akan gado na zibe ina sakin wani kuka dakai tsaye yake fitowa daga can cikin ƙoƙon raina.
Zuciyana tana min zafi sosai tamkar zata fito daga cikin ƙirjina,ta tada rawar banjo jikina duk ya ɗauro mazari na miƙe jiri na ɗibata na nufi toilet nayi alwala na fito.
Na tada salla ina iddarwa na shiga addu'ar neman gafara ga Yasira,na daɗe kafin na shafa addu'ar tsawon ranan wannan ranar yanda mukaga rana haka mukaga dare.kaina kan cinyar Ummi har akayi ƙiran assalatu.babu abunda jaririnyar tasha har yanzu bayan ruwan zamzam ɗin da Hajja ta bata,sai yanzu da aka kaɗa mata madara tasha sannan aka mata wanka ta koma bacci.




UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________




Page 5⃣6⃣


Ƙarfe taran safe aka gudanar da jana'izan,har an tafi kaita Granny da Iya suka iso ganinta yasa gidan ƙara ruɗewa.nikam tun daren jiya bana iya buɗe koda ƙwayar idona ne sakamakon nauyin dasukamin da kuma azababben ciwon kai daya sauƙa min.
Tabbas duk wanda ya halalci sallan jana'izan ya tafi mamakin irin mutana nan da Yasira tasamo,da kuma yabo daga bakunan mutane,kowa yazo sai ya tambaye abunda ta haifa ta bari Hajja ke gabatar da ita.jaririya kamar ta amma taƙi yarda da kowa daga ni sai Hajja ko Ummi bata yarda da ita.
Suna dawowa daga maƙarbarta Habib,Sayyid da kuma Yaya Fawas daya sama halaltar jana'izan suka shiga.falon yaƙara ruɗewa sosai gaban Ummi ya ƙariso ya tsuguna ya ɗaura kansa jikin ƙafafunta tana sakin kukan daya tukare masa zuciya da sai yanzu ya sama damar fitar dashi.
Sayyid kuwa jikin Granny ya kwanta yayin da Yaya Fawas ya zauna kusa dani,wallahi duk mai ɗauke da ɗigon imani sai ya tausayawa wannan ahalin.
Nima hawayen nake fitarwa da sauri-sauri numfashina na fizga da ƙarfin tsiya Yaya Fawas ya kwanto da kansa dai-dai fuskana"My cute angle ba'a fiye son wannan kukan ga mamaci ba addu'a zakiyi mata Allah ya jiƙanta halinta na ƙwarai ya fita,ya kuma raya abunda ta bari".
Kaina kawai na ɗaga masa amma kuka kam bansan lokacin dazan daina basa,Habib yamin ishara da hannunsa akan nazo na kuwa miƙe na isa gareshi Babyn tana hannuna ya haɗamu dukka ya manna da jikinsa kamar kuwa an kunna mu duk muka fashe da wani kukan.


"Haba Habib kai dazaka lallashe ta kuma kai kake haka,addu'arku take buƙata domin yanzu shi kaɗai ne gatan dazaku mata ba wannan kukan ba".


Furcin Daddy kenan yana ƙarisowa cikin falon,yayin da matan dake zazzaune suka fara mishi ta'aziyya yana amsawa.riƙo Habib yayi ya ɗamƙashi a Sayyid yace su fita suyi sannan ya kaishi part ɗinsa ya kwanta,tare da Yaya Fawas suka fita.
Kusa da Ummi ya zauna yana lallashinta duk da ba komai dayake faɗa nake iya tantancewa ba,na miƙe jiri na ɗibata nayi ɗaki sai dana kwantar da Babyn sannan na tashi zan shiga bathroom naji hannunta ya kama jikin hijab ɗina.na juyo na zare a hankali hawaye duk wanke gaban hijab ɗin nashiga toilet na ɗauko alwala na fito na tada sallah.
Ban tashi daga kan sallayanba har aka ƙira Asr nayi ina zaune na shafa addu'a kenan,wata ƙanwar Ummi ta shigo na gaisata ta amsa sannan ta ɗauki Babyn ta fita da ita.ba jimawa Hajja ta shigo da kulolin abinci,ta diresu a gabana ko kallonsu ban yi ba.
"Ga abinci ki daure kici rabonki da abinci tun jiya ai yunwarma sai ta miki illa".


Na sauƙe ajiyan zuciya"Hajja banajin sha'awar komai bazan iya ci ba".


"Hibba daurewa zakiyi ko tea kisa a cikinki".kafin nakai ga bata amsa wayata dake kan gado ta fara ruri,ta miƙo mini nayi saurin ɗaga ganin sunan mai ƙiran.
"Sayyid yaya akayi?"na fara ina kara wayar a kunnena.daga ɗayan bangaren yace "Hibba dan Allah kizo kiga Hamma na kawoshi part ɗinsa amma baya cikin nutsuwa,ke kaɗai zaki iya kwantar masa da hankali a halin dayake ciki yanzu".
Sauƙe wayar nayi daga kunnena ba tare dana furta masa komai ba,na fara ƙoƙarin miƙewa maganar da Hajja ta farayi ya dakatar dani.
"Ina koma zakije?".


"Zanga Habib ne"na faɗa ina ficewa daga ɗakin na ratsa mutanen dake falon na fita,babu haske ko kaɗan a falon duk bub ɗin a kashe suke dan jiya da aka kawa gawar Daddy yace akashe su,a hankali na tura ƙofar bedroom ɗin na shiga haɗe da sallama.na fara ware kumburarrun idanuwa a ɗakin can kan bed na hangoshi tana kwance ruf!da ciki.
Na saki ƙofar na isa gareshi na fara jijjiga ƙafarsa a hankali ina ƙiran sunansa"Hamma!Hamma!!Hamma!!!?".shuru mai amsa ba wanda hakan ya haifar mini da bugawar zuciya da ƙarfi.na jawoshi yana dafe da ƙirjinsa numfashi na fida da wani ƙara gu-gu-gu haka kakeji.
"Subhannallahi na shigaa uka ya Allah"na furta a riɗime na wuce kan mirro ma ɗauko masa maganinsa sannnn na ɗauko goran ruwan dana gani akan site drawer na bashi maganin yasha.na isashi gaba ina kuka,murmushin ƙarfin hali ya mini yana shafo gefen fuskana.
"Hamma kar ka tabi kabarmu dan Allah kaima,wallahi zuciyata tana dab da tarwatsewa".a hankali yaja jikinsa yazauna ya jingina jikinsa da nawa kallon fuskana yakeyi da hawaye yakets gudana yace"Bazamu rayu tare matata,zamu rayu mu riƙe amanar Yasira".
Kaina na jijjina masa ina mai ƙara tausayinsa tabbas dole yafi kowa jin mutuwar Yasira,a yanda naji Granny na faɗawa wasu mata sanda zan fito tana cewa "tun haihuwar Yasira,Habib ne ya fara ɗaukarta ya kuma hana kowa ita shi yake rainonta har ta girma intana rashin lafiya baya iya matsawa daga kusanta.ranar da aka sata a makaranta shiya kaifa idan yaji kukanta to babu kwanciyar hankali a tattare dashi duk dangi dashi kaɗai take kama,sunyi shaƙuwa sosai duk rashin son maganarsa amma in Yasirace zagewa yake suyi hira,itacs mutum na farko da duk wani abun farin-ciki ko akasinsa ya sameshi yake fara sanarwa.ko Sayyid dayake namiji kuma kusan sa'anni suke basuyi shaƙuwar dasukayi da Yasira ba".
Na sauƙe kyakykyyawar ajiyan zuciya ya ɗago kansa"Muje kuyi sallama da Fawas zai wuce Baffa kam tun ɗazu ma ya wuce".


Nayi riƙo da hannunsa ya sauƙo daga kan bed ɗinmu muka fito,cire harabr gidan yake da maza dan haka muka tsaya daga wajen parking lot ya ƙira Yaya Fawas a waya suka taho tare da Sayyid.
"To my cute angle nizan wuce sai kuma sadakan uku,zamuzo dasu Anisa da Hajiya ".


" Allah ya kiyaye hanya mungode"nayi jarumtar faɗa,duk suka amsa da Amin.
Ranar ma haka ban iya rutsawa ba tare da Babyn muka kwana duk juyin dazanyi sai na kalle fuskarta,da tsan-tsan kama da mahaifiyarta yale malale akai.
Washe gari ina shirya Babyn naji sallaman Maryam ta falo suna gaisawa dasu Ummi da Granny,suna gamawa ta shigo ta kalloni cike da tausayi tana faɗin"Ashe kuma Yasira sa'i yayi,wallahi muna maiduguri Habib yake sanar da Bashir shiyasa bamu sama jana'izan ba yanzu ma ko gida bamuje ba.Allah ya jiƙanta ya kyautata makwancinta".
A sanyaye nace"Amin ya Allah".sannan ta karɓa Babyn tanata faɗan kamanninta da Yasira.
"Kuma gata tufarkalla kamar ba cikin wata bakwai ba".
Nace"uhmm".
Ina zaune akan sallaya na iddar da sallan Zuhr kenan Hajja tashigo take cemin"Inna ta iso"ina ganinta naji zuciyata ta karaya na tina lokutan damuke zuwa wajenta tare da Yasira muci musha ayi raha ayi dariya,ai kuwa na saki kukana na fara binsa wiwi muka rungume juna.sai da mukayi mai ishermu kafin ta rabani da jikinta suka fara gaiswa dasu Granny.
Na neɓa waje na zauna ina zama Anty Amina ta shigo ta'aziyya ta farayiwa Ummi da Granny sannan ta zauna kusa nida Maryam muka gaisheta tana ƙarayi mana gaisuwa,Maryam ta miƙa mata Babyn.
Balaraba da tun da akayi rasuwar take gidan ta taso ta kusan Anty Amina tann mai fashewa dakuka"Amina ki yafe ni kiyafe min alhakinki bazai barni nayi rayuwa cikin farin-ciki ba".itama Anty Aminan kuka takeyi"Balaraba na yafe miki Allah ya yafe maan gabaɗaya ya jiƙan malam".
Amin muka ama dashi yayin da waɗanda basu bansuba suka fara binsu da kallo.sai yamma Anty Amina ta tafi tare da Balaraba suka fita tanuna mata gidan da Habib ya kam mata haya.
Inna kuwa da Maryam ana suka kwana,da asuba bayan munyi salla Inna ke gaya min yanayin jikin Hajara ya tsananta shiya hanata zuwama lokacin da akayi rasuwa dan suna wajen magani,fatan samun lafiya muka mata nida Maryam.
Ranar za'ayi sadakan uku kuma naji Granny nacewa hadda bakwai zaka haɗa,bayan sallan zuhr mutan Nijar su Aliyu haidar,Farida,Kawu Isma'il da kawu Hayatuddeni sai kuma Nabiha da khalifan Adda Lawisa suka zo.
Aka musu tarba suka yiwa Granny da Ummi ta'aziyya.ina zaune a ɗaki dawowa na kenan daga part ɗin Habib nakai masa abinci su Farida suka shigo hadda Kalifa duk suka gaisheni tare da min gaisuwa na amsa sannan na sako hijabina na ɗauka Babyn na fito muka gaisa dasu Kawu Isma'li ya karɓa Babyn ya mata addu'a sannan suka fita wajen maza a waje.
Basu daɗe da fita ba Sayyid ya shigo dasu Anisa,Fadila hadda su Sadiq da Mahmu da kuma Hajiya mahaifiyarsu,aka gaigaisa sannan nayiwa Ummi bayanin ƙanne yaya Fawas ne da mahaifiyarsu.
Hajiya dasu Mahmud da kuma Yaya Fawas a ranar suka koma azare,su Anisa da Fadila kuwa sai anyi suna,Kawu isma'il da Kawu Hayatuddeni ma da kalifa Lagos suka wuce zasuyi sati acan kafin suzo su wuce.
Ranar da Yasira ta cika kwanaki bakwai da rasuwa ranar akayi suna,babu wata gayyata ba iya yamu yamune dangi.muna zazzaune dasu Anisa da Farida a falo Sayyid ya shigo bakinsa har kunne rabon da naga dariyarsa tun Yasira nada rai.Iya ta katse masa hanzari ta hanyar faɗin"Wa aka samu?".
Ya ƙara yalwata fuskarsa yace"FATIMA aka samu sunan HIBBA".
Nayi gaggawan ɗago kaina ina tsaida ƙwayar idona akan Sayyid,ya ɗaga min kansa alamar tabbatar mini da zancensa.


"Kai!Masha Allah amma kuwa Habib ya kyauta wallahi Allah ya raya FATIMA".furcin Iya kenan a karo na biyu.
Su Farida da Maryam sukata murna nikam sakeke na tsaya duk tinanina sunan Ummi ko Granny za'asa.
Ummi ta fito daga ɗaki itama yanzu takejin sunan da aka sa a bakin Daddy ta rungumeni,na saki kukan dana kasa tantancewa na farin-cikine kona akasinsa.
"Ai ba kuka zakiyi ba Hibba,Allah ya rayata ta ɗauko halinki ita kuma Allah ya jiƙanta da rahma".


Furcin Ummi kenan danaji kamar ta karanto abunda ke cikin zuciyana,yau gani ga ƴar Yasira amma babu Yasira.na karɓa Babyn dake hannun Farida suna mata hoto na rungume a jikina a zuci nake faɗin"Allah ya bani ikon riƙe amanar Yasira".
Har Yamma ban sama ganin Habib ba dan yana cikin mutane ga kuma ƴan office,dasuka zo masa gaisuwa.da yammacin Inna ta shirya komawa Gano saboda rashin lafiya Hajara tare da Sayyid suka tafi dan naji yana cewa Ummi zai shiga cikin makaranta za'ayi exams ɗinsa amma a ranar zai dawo.
Sai da dare Habib yashigo Ummi sai sa masa albarka takeyi haka nan ma Granny da Iya,bama kaman Daddy.Dazai fita yace nakai masa Babyn,na karɓeta daga hannun Granny nabi bayansa.


Part ɗinsa muka shiga muka yada zango a falo ya karɓa Babyn yana ƙarewa fuskanta kallo.
"Hamma nagode nagode kamin abunda bazan iya biyan ka da komai ba a rayuwa,sai dai na dawwama cikin addu'ar nema maka dacewa dakuma gamawa lafiya".
Murmushi ya wurgo mini kana yace"bakiga farin-ciki ba wajen Daddy danace sunanki za'a sa,MU'AFSA nakeson a ɗinga ƙiranta dashi".


"Allah ya raya MU'AFSA"na faɗa ya amsa da Amin.
Muɗan taɓa hira kafin na dawo na barshi da Mu'afsa mukayi kicibus da Anisa tana fitowa nabita da kallo"ina zakije?".
Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta tace"Yaya Aliyu Haidar ne ya aiko Farida ta ƙira ni".sarai na ganewa take nufi amma na basar na kuma cewa"Waye haka?"ta ɗago tace"Yayan su Farida wanda naji kina cewa soja ne".murmushi kawai nayi wanda rabona dashi tun kafin rasuwar Yasira na shige.


UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________




Page 5⃣7⃣


Washe garin sunan tun safe Maryam da Dr Bashir suka koma damaturu,ƙannen Ummi ma duk sun tafi jiya da aka ƙare sunan.ranan Yaya Fawas yazo ɗaukar su Anida da Fadila tun zuwar Yaya Fawas na lura da yanda yake satar kallon Farida dasun haɗa ido sai su sakarwa juna murmushi.haka nan Anisa da Aliyu Haidar,Sayyid ma na lura sai wani shan ƙamshi yakeyiwa Fadila.
Ni kaɗai na saki dariya mai sauti bayan na gama wannan lissafin cikin kwakwalwata,dai-dai lokacin dana gama shirya Mu'afsa na saɓata a ƙafada zan fito.makeken hotonmu nida Yasira da kuma Habib wanda muka ɗauka ranar aurensu dayake maƙale a ɗakin ya dakatar dani daga fitan.
Na ƙurawa hoton idanu rayuwa fa kenan gatanan kamar ka mata magana ta amsa,amma babu daman hakan koma nayi da baya bayan na ciro hoton na zauna ina ƙara binshi da kallo.


"Allah ya jiƙanki Yasira,Allah ya karɓi shahadar ki".


"Amin".
Naji an amsa naji saurin waigowa dan tinanina a zuci nayi maganar,yana tsaye bakin ƙofar ya naɗe hannayensa a bayansa ya rako ya iso gareni,durƙusawa yayi dai-dai fuskana"Banason wannan kukan domin da kinsa yanda zuciyata take raɗaɗi idan naga hawayenki,to dakin tausaya min kin daina"ya ƙarishe yana goge mini hawayen.


"Taso muje ga can su Fawas zasu koma ke suke jira".ya ƙare zancen yana karɓan hoton dake hannuna ya maƙala shi a gurbi shi sannan ya riƙo hannuna muka fito ina riƙe da Mu"afsa.
A harabar gidan muka iskesu suna tsatstsaye ya lanƙwaso da kansa"kinga mutumin ko Aliyu Haidar,kin kusa zama suruka".na saki murmushi ashe bani kaɗai nake zargin soyayya sukeyi da Anisa ba.
Muna isa Yaya Fawas ya karɓa Mu'afsa yana mata wasa sai kwalalo masa dariya takeyi.
"My cute angle ki tayani godiya Habib ya cika alƙawari yadai dage sai na tabbata a Malunta,domin har an saya fili yanzu har anfara gini ".na rausaya kaina nace"Mungode Allah yaƙaraa buɗi".


"Ai naga ka fara neman aurene shiyasa nace nima gwara na zage,kaga sai anyi ga sabuwar makaranta ga sabuwar Amarya ko Farida?".saurin tufe fuskarta tayi da tafukanta tayi ciki da guju muka bita da dariya.
Mukayi sallama dasu Anisa,Ummi ma ta fito sukayi sallama hadda su Granny sannan suka tafi tare da sallahon gaisuwan dana bayarwa akaiwa Mahmud da Sadiq.
Nan nabar Habib sunatayi da Aliyu Haidar,Mu'afsa na hannunsa muka dawo falo tare dasu Ummi anan muka zauna Granny

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login