Showing 78001 words to 81000 words out of 104857 words
Chapter 27 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
gaskiya"Habib ya gyara zama"inajinka menene faɗi".
"Abunda result ɗinna ya nuna Madam na ɗauki da ƙaramin ciki na tsawo sati huɗu ina kyautata zaton tafiyar da kukayine ya wahalar da ita kasan wasu masu cikin tafiya kaɗan ke wahalar dasu da abun dake cikin cikinsu,sannan cikin inka lura tun daga yanzu ya fara zuwa mata da laulayi sai a kiy....."bai ƙarisa ba sakamakon ƙarƙarfar rungumar da Habib yakai masa.
Yana jero godiya ga rabbul samawati,Yasira dake zaune kusana ta ɗaura kanta saman kafaɗata nima na rungume tsam!a jikina hawaye nabin fuska wanda na kasa bambamcewa na farin-cikine kona akasinsa.
"Habib kabari dai na ƙarisa ko"cewar likitan Habib ya dawo matsuguninsa ya zauna yana aikin jerawa Yasira sannu wacce tayi ƙasa da kanta sabili da kunya.
"A kula da ita sosai sannan kar abarta tanayi aikin ƙarfi kamar ɗaga abu mai nauyi da dai makamantarsu,sannan a kula kar ana ɓata mata rai a lura sosai sannan zan rubuta muku magungunar ƙarin jini sai ku nemesu tana sha dan sunada matuƙar amfani a gareta".ya kawona yana jawo wata farar takarda yafara rubuto magungunan,yana gamawa ya miƙawa Habib ya karɓa tare da ƙarayi masa godiya nima na ɗaura da tawa sannan na riƙo hannun Yasira muka fice.
Cikin pharmacy Habib ya wuce yayin damu kuma muka wue idan yayi parking na buɗe mata ta shiga sannan nima na shiga yana dawowa muka tafi gida,tun a mota na ɗaga waya zan sanar da Ummi Habib ya gargaɗeni akan cewa mu bari sai gobe inmuje gidan sai kowa ya sani.
Muna isa gida muka wuce part ɗin Yasira har cikin bedroom nakaita tare da tambayarta kotanada buƙatar wani abun tace a'a,Habib neya ɓalla mata magungunan tasha.
"Na tayaka murna Habib da Allah ya amshi du'a'ina,na daɗe da sanin kanason ƴaƴa sannan kaima kanason ganin jininka a duniya tun danayi ɓari har yanzu babu labari.sai kuma gashi Allah ya azurtamu dashi Allah ya sauƙeki lafiya".na faɗa ina kai kallona gareta.
"Amin Anty kema ina miki addu'ar samun naki".na riƙo hannunta"bari na barki ki huta ko dan Allah inkina buƙatar wani abun ki sanar dani".kanta ya ɗaga min na miƙe nabar ɗakin ina maida ƙofar ɗakin zan rufe Habib ya riƙe na sakar masa na ɗauki hanyar barin falon.
"Tsaya muyi magana"ya faɗa yana isowa gareni"Naso dake zan fara samun iyali Hibba naso ace kece wacce zaki fara haifa min ƴaƴa amma hakan ma nagodewa Allah kuma kema ina miki fatan samun naki twins zan baki"ya kai ƙarshe yana kashe min ido ɗaya.
Na ciro leɓɓena na ƙasa nace"Hmm Habib wani lokacin abunda muke tsarawa kanmu ba shine alkhairi garemu ba,sanna kuma kaine ma mai bayarwa kenan?".
"kinfa gane abunda nake nufi fa wifey".
Na ɗan saki murmushi taƙaitacce wanda ya tsaya kan leɓɓana nace"kaje matarka tanada buƙatarka a halin yanzu kadaiji abunda likita ya faɗa".ban bashi damar faɗin komai ba na fice daga falo ƙafafuna har suna harɗewa cikin zanina tsabar saurin dana ɗebo.
Ina shiga na wuce bedroom na kwanta hawaye ne suka ciko min idona na kawar dasu,tare da tambayar kaina meke damuna nidai nasan ba hassada nakeyiwa Yasira da Habib akan samun cikin nan ba.
Na miƙe nayi alwala na gabatar da sallan zuhr sosai nayiwa Umma addu'a sannan na shafa,na jawo wayata na shiga danna nombar Yaya Fawas bugun farko ya ɗauka muka gaisa cikin hawaye na sanar dashi mafarkin danayi da Umma da kuma irin yanayin dana ganta a ciki.
Ba kaɗan ba hankalinsa ya tashi shima sai dai ya danne wajen ganin ya kwantar mini danawa,na sanar dashi zuwa gano dazamuyi shima yace zaizo da haka mukayi sallama.
Na shiga kitchen na haɗa mana abincin rana kodana kammala har ƙarfe uku tayi nayi sallan Asr,inata jiran ko Habib zai shigo amma har izuwa wannan lokacin babu shi babu labarinsa.
Na fito na shiga sashin Hajja tana zaune tana talgen tuwo na isketa muka gaisa sannan najawo kureja na zauna,na kalleta nayi dariya haɗi da cewa"Hajja inada labari mai daɗi amma sai kin biya fa tukunna".
"Faɗi indai baifi ƙarfina ba ai sai nabaki".
Na ƙara sakin wata murmushin kana nace"Yasira ce ke ɗauke da ciki ɗazu munje asibiti likita ya tabbatar mana".
Sai data rufe tukunyar ta juyo yana fuskanta na kafin tace"Amma wallahi na taya Habib murna ƙwarai Allah ya sauƙeta lafiya"ta numfasa kafin nace wani abun a tsakani ta ɗaura"wohoho amma Hibba kinada wata irinyar farar zuciyar daba kowa yakeda ita ba mussamman a wannan zamanin,ace da bakinki koma da murnarki kike sanar da samun cikin kishiyarki".
Na saki wani murmushi mai ciwo"Hajja ban ɗauki Yasira a matsayin kishiya ba hasalima kallon ƴar-uwa ta jini nake mata,Duk wani abunda dazaiyi silar wanzar da farin-ciki a rayuwar Habib inasonshi Hajja bakiga yanda ya ruɗe da murna ba lokacin da likita ke sanar damu tanada juna biyu".na ƙarishe maganar ina sharce ruwan ƙwallen daya taro cikin ƙwayar idona da hannuna.
Ta taso tare da tada kafaɗata"Inada kyakykyawar zuciya na tabbatar Allah bazai barki haka ba kema Allah yabaki naki ita kuma Allah ya sauƙeta lafiya"na amsa da Amin ina miƙewa nace"bari naje na dubota kota tashi daman cewanayi bari nazo na faɗa miki wanna kyakykyawan labarin na karɓa tukwuicina".
"Ai kuwa kin cancanci tukwuici"na fice ina dariya part ɗin Yasira na nufa muka haɗe da Habib a ƙofar bedroom ya fito daga kitchen hannunsa riƙe da kofin tea na tambaye shi tata tashine yace e nashiga ina mata sannu.
Nace abinci ya kammala su fito muci amsar da Habib yabani yaso gigitani dan banyi tsammanin basa.
"Ki kawo mana namu anan kawai dan yanda ƙafafunta ya kumbura banajin zata iya takasu".
Ban ƙara furta komai ba na miƙe nabaro ɗakin naje na haɗa musu abincin nasa cikin basket na aje musu akan dinning nakoma part ɗina.
Abincin na isa a gaba nasa kayin koda spoon ɗaya tun aurena da Habib bamu saba raba kwanon abincin ba,har zuwan Yasira ma tare mukeci yau ce rana ta farko ciki tarihin zaman aurenmu da mukaci abinci daban daban kuma muna cikin gida ɗaya na tashi na kwashe kwanukan nakai kitchen na ajesu raina duk narasa meke min daɗi.
Page 5⃣1⃣
Ina dawowa falon na isa ga wayata wacce keta ruri na ɗaga tare da mannata a kunnuwana nayi sallama daga ɗayan bangaren Maryam ta amsa na tambayeta Abbul-khair tace yana lafiya ta bashi wayar yayita min kwaɓar maganarsa da bana gane komai a cikinsa.
Muɗan taɓa hira da ita sosai kafin mukayi sallama na ajiyewa wayar nayi alwala domin sallan magrib ban tashi daga kan sallayar ba sai danayi Isha'i.ganin abincin rana ma bamu cinyeshi ba yasa ban ɗaura girki ba na fito na nufi part ɗin Yasira ko yanzu ma Habib na nan yau dai na lura ko office baije ba ko masallaci bai fitaba.
Ina zama na sauƙe idanuna akan kulolin abincin rana dana ajiye ko gusar dasu daga inda na aje ba'ayi ba balle nasa rai ko anci na kallo Yasira nace"baku ci abincin bane?"Habib ne ya amsa"wallahi wai bazata iya ciba shigowarki ɗazu tea na haɗa mata shima bata shaba".
"Haba!Yasira ta yaya zaki zauna babu ci bayan kinsa yanzu bake ɗaya bace ki daure kici ko kaɗan ne bari na tashi na zubo miki"ko amsar dazata bani ban jiraba na miƙe na zubo mata abincin sannan na tsiyaya mata zoɓon daaa haɗo abincin dashi na dire mata plate ɗin a gabanta.ganin batada niyya yasa na fara bata da kaina a hankali take taunar abincin kamar ranta bayason tana haɗiye spoon na uku dana bata kuwa ta fara kakagin amai.
Ta miƙe a harzance tayi bathroom yayin da nida Habib muka rufa mata baya sosai take kwara aman duk ta jigata nayi riƙo da kafaɗarta Habib ya wanke mata fuskarta muka fito kwanciya tayi nan take kuwa baccin wahala yayi gaba da ita nacewa Habib bari na gyara banɗakin tsaf!na tsaftace ko'ina na bulbula turare na fito.
Tare muka zauna wajen Yasira raina cike fam!da tausayinsa dan naji ana cewa ciki mai laulayi bashi da daɗin sha'ani balle ita kuma daya fara mata tun da wuri.
Har sha ɗayan muna nan ganin bata farka ba yasa nacewa Habib kawai zan kwana tare da ita.
Washe gari tun danayi sallan asalatu ban zauna ba,tare da Habib muka haɗa breakfast ya shiga wanka ni danayi nawa wankan na tada Yasira ta shiga tayi ina shirin tafiya gano da zamuyi yau ta fito itama ta shirya dan zamu biya ta wajen Ummi.
Ko yanzu ma basa cin komai tayi na lura ko ƙamshin abincin ba wani so takeyi ba dan tunda ta zauna a dinning ɗin hannunta ke rufe da hancinta,da kyar ta iya zuƙar ruwan tea shidai bata amar dashi ba.
Mukayiwa Hajja sallama muka tafi muna isa muka isa Ummi tayiwa Daddy rakiya zai fita muka fito muka kwashi gaisuwa nida Yasira mukayi ciki Habib ya tsaya dasu bansan meyake ce masa ba.
Tare da Ummi suka shigo kalmar Alhamdulillah yaƙi barin bakinta tun kafin su zauna naji Habib nace"Ummi zamu barta anan zamuje gano tun jiya babu abunda tasa a cikinta dan Allah a matsa mata taci".Ummi ta aika masa da hararar daya sanyashi jin kunya ya sunkuyar dakai yana ɗan sosa ƙeya"tashi mu tafi".
Na kamo hannun Yasira nasa cikin nawa kana nace"To ƴar-uwa zamu tafi a kula mana da babyn mu sosai sannan kar a mana huron yunwa dan Allah"na ɗan marairaice murya a ƙarshen zancena.
Har jikin mota tayi mana rakiya sai da muka fice daga cikin gidan sannan ta koma ina hangenta ta cikin madubin motar.
"Gorko am idan Allah ya sauƙi Yasira lafiya tunda ta kammala karatunta mezai hana a nema mata aiki tunda kaga nima inna gama ba zama zanyi ba aikin zan nema"lokacin mun iso dai-dai hanyar da zata rabomu da cikin katsina nayi maganar ya kalloni fuskar nan fal annushi a shimfiɗe yace"To yanda kika tsara haka za'ayi Matar Aljannah".
Na saki murmushin jindaɗi har muka isa cikin gano muna hirarmu gwanin burgewa dai-dai sanda muka nufa unguwar Baffa na ciro wayata daga cikin jakata nace"bari na ƙira naji lafiyar babynmu"yasa dariya"lalle wannan babyn dan gata ne"nayi fari da idanuna nace"sosai ma kuwa ai Allah dai ya kawoshi lafiya".shigowar ƙiran Yaya Fawas cikin wayata yasani katse ƙiran dazan soma na daɗa yace min ya iso nace muna gamu a kusa.A
A ƙofar gida na hangi Yaya Fawas na fito da saurina na isa gareshi na ware manyan idanuna nace"Yaya Fawas kaha yanda kayi wani ƙiɓa kuwa ga wani hasken daka ƙarayi".
"Haba my cute sai dai in idonkine ba ni bawani ƙiban danayi"Habib ya iso haɗi da cewa"ai dai kuwa kayi ƙiba kodai nima idon nawan ne"muka saki dariya sannan sukayi musabaha suka gaisa nidai na barosu a wajen na shigo cikin gidan tun daga zaure nake jiyo banbamin Inna ina sako kaina ciki kuwa najita na faɗin"Aikin banzan aikin wofi an fake da jinyar da bata taka kara ta karyaba duk an ɓata mana gida da ƙazanta".ina zaro ƙafata na kusayin tuntunɓe da marfin tukunya wanda yasa Inna waigowa"Ah Hibba kuke tafe".na ƙara ware idanuna inabin tsakar gidan da kallo kwanukan wanke-wanke ne jimgim a watse ta ko'ina kai kace sunyi wata baronsu da wanke-wanke ga wasu kayan wankin da aka gibjesu gefe guda wasu an farayi wasu kuwa ko jiƙasu ba aiba.na tattare ƙasan zanina na shigo saboda ruwan dake kwance maƙil a tsakar gidan kamar ayi ƙiyo wanda nake alaƙanta hakan ga fanfon danaga yaketa tsuba shi ɗaya.
"Inna lafiya kamar ba mutane acikin gidan?"na faɗa ina ƙarƙaɗe ƙasan zanina.ta taɓe baki tana gyara ɗaurin ɗankwalinta dake neman sulewa daga kanta tace"Wallahi tafiyar kwana uku rak!nayi shine Hajara ta maida gidan nan haka nima ɗazu dawowata Adamu yake sanar dani zuwanmu nace bari na ɗan tattare tsakar gidan".
"Bata da lafiya ne?"na kuma jefa mata wani tambayar ta kuma taɓe baki kana tace"wai ba gatacan kwance a ɗaki".
Na jinjina kaina sannan na rusuna na gaida Inna ta amsa na kai Mayafi da jakana ɗaki na fito muka hau tattare gidan muka saka komai a matsuguninsa na kama kwankwosona ina faɗin"wash bayana"Inna ta kalloni haɗi da cewa"Sannu sai kizo kiyi sallah ki huta kafin su shigo"na zari buta nayi banɗaki sannan na fito na fara alwalar na kammala saura wanke ƙafar hagu data ragemin Hajara ta fito daga ɗaki tsabar firgicin dana shiga lokaci guda yasani tsakin butan ina ƙara binta da kallo.
Dama can ba fara bace amma ta ƙarayin baƙi sosai ga fatan jikinta dayake daddarewa kamar bayan kunkuru duk ta bushe ta ƙare sai idanu da haƙwara.
Ko kulani batayi ba tayi abunda yafito da ita ta koma ɗaki,na ƙarisa alwalar na shiga ɗaki jikina har rawar mazari yakeyi.
"Inna meyasa ba'a kaita asibiti ta sama kulawar jami'an lafiya ba gaskiya nikam ban taɓa ganin mai irin wannan cutar ba"na faɗa cike da jimami.
Cikin halin ko in kula Inna tace"ai daman shi alhaki kwuikuyone kuma ai hausawa sunce sharri ɗan aike ne idan ka aikeshi to sai ya dawo maka ai daman duk wanda yace zai wulaƙanta sunnar ma'aiki ya taɓe wallahi"duk da ban fahimci inda maganganun Inna suka dosaba amma ban sake cewa komai game da maganar ba na tada sallana ita kuma tafita dubo abincin damuka ɗaura.
Ina iddarwa najiyo sallamar su Baffa sun shigo Yaya Fawas ya shimfiɗa musu tabarma Inna ta zubo musu abinci tana tambayar Habib cewa ina Sayyid yace yana cikin makaranta.
Sannan muna ta zubo mana namu abincin tashigo mana dashi ɗaki,munaci nake sanar da ita ƙaruwar damuka samu na cikin dake jikin Yasira tayi murna sosai muna gamawa kuwa Baffa yayi ƙirana na fito sannan muka fara tattauna abunda ya taramu.sosai Baffa yayi farin-ciki yana ƙarawa da cewa"Daman nima inada ƙudurin zama daku akan hakan lokaci yayi da zaku nemi uwarku domin bahaushe yace ba'a canzawa tuwo suna kai kuma Habib Allah ya maka albarka Allah ya tsare bayanka".duk muka amsa da amin sannan Yaya Fawas ya bashi wasu bayanai akan Umma garinsu da sauran abubuwa.
Nidai abunda nasani shine bayan rasuwar Abba,Umma ta ɗaura wani auren bamu taɓa kallon wanda ta aurenba daga ni har yaya Fawas.yace bazai riƙe mata ƴaƴanta ba duk da wanna kalmar ta malam bahaushe dayake cewa maso uwa yaso ɗanta amma Umma ta zaɓeshi sama damu damuka tsaga jikinta muka fito.
Wasu hawaye masu matuƙar ƙona suka shiga gangarowa daga idanuwa har izuwa saman tudun kuncina suna sauƙe zuwa wuyana.
"Ashsha Hibbatu wannan ai ba abun kuka bane banda abunki ai mafita ake nema"furcin Inna kenanna sauƙe ajiyan numfashi ina cigaba da sauraron Baffa dayake yiwa Habib bayani tiryan-tiryan.
"Nidai nawa shawarar itace a fara duba gidajen karuwai da ƴan daudu tukunna ko Allah zaisa a dace a ganota acan"furcin Inna kenan daya tokare mini rai na sanƙare awajen ina ɗago ido muka haɗa da Yaya Fawas na lura shima kukan yakeson yayi na matso gabansa ai kuwa muka saki kukanmu muna tausayin rayuwar da muka taso acikinta.
"Ya isa haka my cute angle"ya faɗa yana kawar da hawayen fuskana.
Sai dana tsagaita kukan sannan muka fito zamu tafi Habi ke tambayar Yaya Fawas a wacce makaranta yake koyarwa ya sanar dashi.
"Sai mu buɗe maka wata ƙaramar makaranta kana kula da ita kaga idan Allah ya kawo mana ƴan dagwai-dagwai sai mukawo makasu kana koyar mana dasu ko?"su biyun suka saki dariya Yaya Fawas yace"Ai kuwa kaga bayan koyar dasu dazanyi hadda toyar masa zan koya musu"suka ƙara tuntsirewa da wata dariyar nidai jinsu kawai nakeyi nayiwa Habib godiya akan makarantar dayace zai ginawa yaya Fawas.
Sannan muka tafi sai da muka tsaya a gefen titi Habib ya lallashi ne sannnn muka ɗau hanya muna isa cikin Katsina magariba ta goso kai ya ajiyeni a gidan Ummi sannan ya wuce masallaci.na shiga Ummi na tambayata ya hanya na amsa data da Alhamdulillah sannan na shiga nayi sallah hadda isha'i na haɗa sannan na fito na same Ummi a kitchen na tayata muka gama girkin ban tambayeta ina Yasira ba saboda dana shiga ɗaki nakanga tana bacci.
Habib yana dawowa ya fara da tambayar Yasira Ummi tace tana ɗaki tana bacci da kyar tasha tea sannan ta sama wannnn baccin,mukaci abincin Daddy kuwa yayi tafiya damaturu wajen Granny muna gamawa muka fara shirin tafiya na taso Yasira Ummi tamana rakiya muka tafi.
A hanya Yasira taga mai saida rake tace tanaso muka tsaya ya sayo mata,ɗaya tasha tace ya isheta tans riƙe da sauran har muka isa gida.
Part ɗin Yasira dukkaninmu muka nufa tayi kwanta tayi shirin kwanciya,na haɗa mata fruit sallad takasaci sai da Habib ya karɓa yabashi da kansa sannan tasamo taɗan taɓa kafin ta kwanta.
"Tazama bacci muje mu kwanta ko"na faɗa ina miƙewa da mamakina naji yace"kije matar Aljanna zanzo na sameki"tunda naji yace haka ban ƙara gigin cewa komai ba nayi gaba.
Bathroom ɗina na wuce na shiga toilet na watsa ruwa na fito narasa abunda kemini rai acikin wannan duniyar ina zaune kar na gama karatun al-qur'anin danakeyi Habib bai shigo ba har ƙarfe sha ɗaya ta gota.
Page 5⃣2⃣
Cire rai nayi da dawowarsa duk danasan cewa yau a ɗakina yake yau nayi kwanciyata ina ƙarewa rufin ɗakin kallo naji hawaye fal!a idona.
Cikin bacci daya fara zuwar min naji shigowar Habib na ƙara ƙamƙame idanuwa wutar ɗakin ya fara kunnawa haske ya gauraye ɗaki gabaɗaya wanka yafara shiga sannan yayi shirin kwanciya,ya kwanta"nasan idonki biyu ki tashi"nayi burus nacigaba da kwanciyata.
"Bata samu bacci bane shiyasa na daɗe"sai a sannan na iya buɗe bakina na furta"Uhmm".zai riƙoni na zame "tun dawowar mu nakeson musama lokaci naƙara baki haƙuri akan abunda ya faru a nijer".
Na musguta har yanzu na bashi baya nace"ba komai ya wuce kuma ai tun lokacin da hakan ya faru ka bani haƙuri kuma har raina ban riƙesu ba".
Ya shafo goshina"Allah ya miki albarka Matar aljanna".
"Gobe Zamu koma makaranta in Allah ya kaimu".
"Allah ya kaimu innaga result mai kyau akwai kyauta"na murmusa irin murmushin gefen baki ɗinnan kana nace"Nagode".
Haka tsawon wannan daren nakasa sakar jikina hasalima shi yayi kiɗansa kuma ya taka rawarsa,Washe gari na tashi da wuri na gama aikina na cikin gida na tsaftace ko'ina na haɗa mana breakfast sannan nayi shirin tafiya makaranta fitowata daga wanka yayi dai-dai da shigowar Habib ɗakin yana ɗaura maɓallin hannun rigarsa.
Mukasa sakarwa juna murmushi na shirya cikin ɗinkin riga da zani na atamfa mai ruwan goro,breakfast