Showing 12001 words to 15000 words out of 104857 words

Chapter 5 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7298

masarufi GALADIMA'S NIG LIMITED wato ENGINEER SURAJ GALADIMA.


Duk abin da suke faɗa yaya fawas baya fahimtarsu yace.


"To gawarsa fa ko zamu samu mu mishi sutura kamar yanda addini ya tanada?".




Suka ce masa basa bada gawar irin waɗannan mutanan,birne su akeyi tare da sauran yan garkuwar a rami ɗaya.




Lokacin danaji yaya fawas yana sanar da umma wannan labarin,ji nayi tamkar babu rai a cikin jikina.




Tsayawa nayi cak!ba abinda yake motsi a jikina sai ido.


Yayin da numfashi na ya fara barazanan barin gangar jikina,faɗuwa nayi a wajen ba wani gaɓa a jikina Wanda yake motsi.




Cikin wani irin kuka mai bayyanar da tsan-tsan tashin hankali,yaya fawas ya iso inda na faɗi yana jijjigani umma ma sosai take kuka fuskar nan duk ta kumbura.




Tunin gidan mu ya cika da taron mata, har yan daudun umma sunzo,sai kuma maza dasuke waje.




Har yan-uwan Abba sunzo ƙaninsa(baffa) tare da matarsa hajara,sai kuma mahaifiyarsu inna dama suke nan suka ragewa Abba a duniya a matsayin dangi.




Kowa yazo sai ya tambayi gawar Abba, umma takan ce musu a can aka masa jana'iza ba'a kawo gawar gida ba.




Ina kwance da kan cinyar yaya fawas,a ɗakin umma.Dan tunda na faɗi yake riƙe dani ko gaisuwar dasu baffa ke karɓa a ƙofar gida ba jeba shi.




Hannuna yana saƙale a cikin nasa yana murzawa a hankali.Inna na tofin addu'a a cikin ruwa tana shafa min a fuska.




A Hankali na fara buɗe idona dana jisu sumin wani irin nauyi.Ina ƙarewa mutanan wajen kallo,wasu hawaye ne masu matuƙar zafi suka shigo rige-rigen tsiyayowa daga idona.magana ma ya gagare ni.


Tashi nayi daga jikin yaya fawas,na matso kusa da inna na kifa kaina akan cinyarta ina kuka,bubbuga bayana takeyi a hankali da hannayen ta ita ma tana kukan.




Har cikin ranta umma take ɗaurawa alhakin abinda Abba ya aikata,Lokaci daya naji kaina yamin wani irin nauyi,ko idona bana iya buɗewa ga wani azababben zazzabi daya sauƙa a jikina haka na yini cikin wannan halin ina maƙale ajikin inna.




Da dare mutane sun safara watsewa,ina kwance har yanzu a jikin inna.


Izuwa yanzu kam hawayen ma sun kafe sai dai kukan zuci,wayata ce ta hau ringing inaji har kiran ya tsinke aka sake kira a karo na biyu.shima banbi ta kansa ba sai da aka kira a karo na uku.


Sannan inna tace,"wayar wayene wannan aketa kira?".


Muryata har bata fitowa sosai nace"Tawace".




"To ki ɗaga mana".


nace"ki barshi inna ai kiran ma ya katsa".


Ina rufe bakina aka wani Kiran yasake shigowa,ɗauka nayi tare dayin sallama bai amsa sallamar ba Duk dayasan muhimmancinta a addinance.


Illa ajiyan zuciya da ya saka kafin yace,"Hibba for how many days nake kiranki bakya ɗauka?".




UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


_________________________________


Page 1⃣0⃣




Kuka ne ya kubce min,a razane Habib yace,"Hibba lafiya?meya saki kuka?".


Ajiye wayar nayi yayin da na kifa kaina akan gwiwata ina kuka.


"Hello kina jina?"


Shine abinda yake ta maimaitawa a cikin wayar,ganin haka yasa inna ta ɗauki wayar.


Sallama tayi habib ya amsa tare da gaishe ta cike da ladabi da girmamawa,sannan inna tace,"Bawan Allah kayi haƙuri hibba yanzu bata cikin hayyacinta,bazata iya magana da kaiba".




"Dan Allah meye faru da ita".








Nan fa inna(baki ba sakata)ta shiga bayyana mishi duk abinda ya faru, sai dai bata sanar dashi irin mutuwar da Abba yayi tadai ce masa abba na ne ya rasu yau.


Wani irin tausayi ne da kuwa abinda shi kansa baisan menene shi ba,suka ƙara shigewa zuciyar habib a lokaci guda,yasan zafi da kuma raɗaɗin maraici domin nasa iyayen bai taso a cikin su ba.




Hawaye yaji suna gudana a fuskarsa,a hankali ya share su yace,"Dan Allah ko zakimin kwatancen gidan?".


Nan inna ta shiga kwatanta mishi gidan,duk da ita ma ba wani sanin potiskum ɗin tayi ba ta'aziya ya mata sannan sukayi sallama.




Washe gari bayan sallan zuhr,ina zaune a tsakar gidanmu yayin da mutane keta zuwa gaisuwa,yaya fawas ya shigo ya kirani gefe muka tsaya sannan yace.




"Hibba kinyi baƙo a waje tare suke da bashir yayan abokina Faisal".




"Ni yaya Fawas ba Wanda mukayi dashi zai zo".




"Kije ki sanarwa inna da Umma zasu shigo su gaisa"cewar yaya Fawas.


GefenUumma na tsuguna ina faɗa mata,ina rufe baki na kuwa sallamar habib ya sauƙa a cikin dodon kunnena,tare yake da yaya bashir da kuma ƙanin yaya bashir ɗin Faisal.




Ɗaya bayan ɗaya suka gaida mutanen wajen, tare dayin ta'aziya wa umma da inna miƙewa sukayi yayin dana bin bayan su muka tsaya daga jikin motar yaya bashir Dan na lura da ita suka zo duk sunmin ya haƙuri.


"Mun gode Allah "sannan suka tafi na amsa dashi.




Wani abin takaici ranar da Abba yacika kwanaki uku da rasuwa a ranan Umma ta cigaba da sana'arta.
Ranan bani ba hatta Inna da Baffa sun sha kuka mai isarsu.
Wasa-wasa Abba ya cika wata biyu cur! da rasuwa, a ranan inna dasu baffa sukace zasu koma umma tace"Ita ta sama miji aurenta zatayi tana gama idda dan haka dani da yaya Fawas kowa zai koma wajen dangin mahaifinsa,saboda mijin da zai aure tan yace bazai riƙe mata ƴaƴanta ba".


Yaya fawas yayi kuka tamkar ransa zai fita a ranan.
Ya roƙi umma data barni na zauna,a wajenta kodan karatu na,amma umma tace"Ai daman,ba ita takeda hakkin kula damu ba dukkanin mu wajen dangin mu zamu koma ni zanbi su inna mukuma kano shikuwa yaya Fawas daman dangin mahaifinsa a azare suke Dan haka shima zai koma can da zama".




Rabuwa da yaya Fawas,jinsa nayi tamkar ƙarshen numfashi na kenan a cikin duniya.
Abba ya tafi tafiyar da ba waiwaye balle dawowa,yanzu kuma ga rabuwa da yaya fawas.
Jinayi komai na rayuwar duniya ya fita a raina,meyasa mu kuma tamu ƙaddarar take zuwa mana a haka?meyasa umma bata tausayin halin da rayuwar mu zai shiga?meyasa Umma bata mana kallon ƴaƴa?.
Tambayoyin dana kasa samawa kaina amsoshin su kenan.
Duk mungama shirya kayanmu nida yaya Fawas muka fito dasu kofar gida, kuka muke tamkar bazamu sake ganin juna ba,riƙo hannuna yaya fawas yayi yace"Hibba ki daina kuka,kukanki na ɗaga min hankali my cute angle ko ina kika tsinci kanki,ki riƙe mutuncinki sannan ki riƙe addininki kinji ƙanwata?".






"Yaya Fawas ajikin nakejin kamar bazamu sake haɗuwa ba".Hannu yasa yana share min hawayen fuskana.



Kafin ya shiga faɗin"Hibba ki daina faɗin haka in sha Allah zanzo har inda kike my cute angle kinji ki daina kuka".


Muryata har ya dushashe nace" yaya Fawas yanzu karatuna shikenan ya tsaya kenan?".
"Hibba zaki cigaba da karatu domin shine burin Abba, ga kuɗin da Abba ya bani dashi akayi amfani wajen saya abinci da wasu abubuwa dubu talatin ne ya rage gashi yanzu zan baki ki riƙe a wajenki koda zaki buƙaci wani Abu".


"Yaya Fawas ba abin dazan buƙata a yanzu sama da kasancewa tare da kai,amma Umma ta hana hakan yiyuwa"




Muna cikin haka Umma tafito tare dasu Inna,Hajara da kuma Baffa Umma tace"Hibba Fawas sai dai kuyi haƙuri domin ba kuka ba komai zakiyi bazai sa na canza ra'ayi na ba".




Cikin sauri Inna tace"Ashsha ashsha haba Juwa,ki barsu da baƙin cikin da kika sanya su aciki ma ya ishesu basai kin faɗa musu wadannan kalaman ba".




Baffa da duk haushin Umma ya gama cika shi yace"Inna mu tafi".


Ƙarisuwa Inna tayi tare da Ciro hannuna daga cikin na yaya Fawas ta riƙe muka fara tafiya.
Tafiya nake amma bansan inda nake saka ƙafafuna ba,numfashi na sama-sama yake fita har muka isa tasha muka hau motar kano.
Yaya Fawas kuwa inda nabarshi,nan ya tsaya yana wani irin kuka mai tsuma zuciyar Mai sauraro,sai da yayi Mai isharsa sannan shima ya nufi azare.




Ƙauyen gano dake cikin karamar hukumar kano,muka nufa inda su inna suke da zama.
Gidan ƙarami ne Mai ɗauke da ɗakuna biyu,ɗaya na Baffa da matarsa ɗaya kuma na Inna.


A ɗakin Inna na ajiye kaya na saboda anan zan zauna muna isa na kira yaya fawas amma wayarsa a kashe.


Kwana na biyu a gidan na fahimce irin rayuwar gidan nasu.Inna bata isa ta faɗawa Baffa,magana yaji ba yayin da matarsa Hajara take tsula tsiyarta son ranta wa Inna.


Ranan ina shara Habib ya kira wayata,na ɗauka tare dayin sallama ya amsa sallamar tare faɗin"Hibba yanzu Bashir yake gayamin school ɗinku,sunyi resuming daga strike ɗin dasuka tafi.amma yace min ke baki komaba ko lafiya?".




Hawaye suka ciko idona a hankali nace"Banida lafiya ne,amma in sha Allah innaji sauƙi nima zan koma".


A kiɗime yace "Subhanallahi! tun yaushe?".




Bansan sanda bakina ya furta"Tun last week"ba
Cike da nuna damuwar sa yace"To Allah yaƙara lafiya "
"Amin"
Mun Dan taɓa hira har yake sanar dani tsautsayin dayaso ya faɗa ga uncle ɗinsa,na yan garkuwa dasu ka so kamashi.




Na jajanta masa tare da addu'ar Allah ya kiyaye gaba Mun Dan tab'a hira kafin mukayi sallama.


Na cigaba da sharan danakeyi,ina gamawa na nufi ɗakin Hajara sallama nayi aka amsa sannan na shiga.


Baffa na zaune na shigo na zauna can gefe cikin nutsuwa nace,"Baffa sannu da hutawa"


Ba tare daya ɗago ya kalli ni ba yace"Yauwa Mamana".




"Baffa daman mun koma makaranta ne daga hutun da malaman makarantar sukaje shine nima nake son wani sati na koma".




Sai a sannan Baffa ya ɗago ya kalle ni yana faɗin"Hibba kya bari dai abubuwa su dai-dai kafin kizomin da maganar komawa makaranta".


Nace" Baffa makarantar nan shine burin Abba Dan Allah kar ka han......."
Tsawa ya daka min cikin faɗa yake cewa"Wai ke Hibba wace iriyar mara hankali ne?,a halin damuke cikin inna mukaga ƙarfin ɗaukar nauyin karatunki. bayan ba abin da Sulen ya bari sai ɓata mana suna da yayi a gari to karatu dai wanda kikayi a baya Allah ya albarkace shi".




Hawaye tunin sun fara wanke min fuska,na tashi ina fita daga ɗakin ina kuka na shiga ɗakin Inna.
Yaya Fawas da Abba kawai nake tunawa Allah sarki mutuwa Mai tunan asiri.
Wayata na ɗauka na shiga dialing numbern yaya Fawas yana ɗauka kuka nasa Mai ƙarfi nace "Yaya Fawas karatuna Baffa yace banzan cigaba ba".


Da mamaki yaya Fawas yace"Meyasa yace haka?Baki gaya mishi burin Abba bane kiyi karatu?"


" Na faɗa mishi yaya Fawas".




Ajiyan zuciya yaya Fawas ya saka kafin yace"To shikenan my cute angle ki daina kuka na faɗa miki kukanki yana daga min hankali ko,ƙarshen watan nan zanzo sai muyi magana da Baffan ko?".




Cikin sheshshekar kuka nace "to yaya Fawas".
Haka muka cigaba da hirar mu kafin daga bisani mukayi sallama.
Sati na biyu tare da su InnaBrannan baffa ya shigo yace a kirani.Hajara tazo tace min Baffa yana kirana naje na durƙusa a gaban shi nace" Baffa gani".




Gyaran murya yayi kafin ya shiga faɗin"Mama na zamanki a haka bazai yiyuba sabida haka nasamo miki MIJiN AURE aure zan miki".
Wani ras!naji gaba na yana faɗuwa,a kiɗime nace "Baffa aure kuma?"na faɗa maka fa ni karatu zanyi domin shine burin Abba Baffa inna gama sai ayi maganan auren".






"Na dai gaya miki kenan,matuƙar kina ƙaunar ki cigaba da zama a gidan nan to sai kin auri NAZIFI".




Idona fal da hawaye nace, "To ni wallahi bazan auri kowa ba".
Mari baffa ya sauƙe min hagu da dama Yana faɗin "Shashasha to ki kasa kunne ki saurare ni, wallahi ko ubanki ne Sule ya dawo duniya bai isa ya hana aurenki da nazifi ba".
Inna ce ta fito daga ɗakin ta,tana cewa "Adamu dan Allah kabar yarinyar nan haka,ka hana ta cigaba da karatun ma ai ya isa".




"Haba!Inna wai ke ba daman anyiwa yarinyar nan,faɗa sai kita mita to wallahi aure zan mata koda son ranta ko babu".




Hajara ce ta karɓe zancen tana faɗin"Haba!Inna meyasa kike ɗaurewa yarinyar nan gindi ne,in batayi aure ba to mezatayi?".




Ajiyan zuciya Inna ta saka kafin tace"Hibba kiyi haƙuri taso ki shiga ɗaki".




Na tashi na shiga ɗakin Inna na faɗa kan katifa ina kuka Bayan kwana biyu Baffa yace in shirya nazifi zaizo kaina na kallon ƙasa nace"Baffa bana jin daɗi bazan iya fita ba".
Cikin zafin rai yace "Hibba ko mutuwa zakiyi wallahi sai kin auri nazifi".


Da kukana na miƙe na shiga ɗaki naci kukana har na gaji na tausayawa kaina na daina.




UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


______________________________


Katsinawa wannan page din nakune bazan manta da karamcinku ba a rayuwata.




Book 1 free


Book 2 paid @300


______________________________






Page 1⃣1⃣




Gashi wayata ta mutu,balle na kira yaya fawas domin babu wutan nefa a gidan baffa kuma ya hana ni fita ko'ina balle na sama waya nayi kira.




Inna da hajara kuwa basu da waya baffa ne kad'ai mai ita,Ina zaune akan sallaya ina roƙo mahaliccina,daya sassauta min tsananin danake ciki.




Bazan zargi umma da laifin jefa rayuwa ta cikin ƙunci ba,amma tabbas UWATACE SANADIn sanadiyar kuka na.
Hajara ta shigo tana cewa,"kizo baffa yana kiranki"Miƙewa nayi nabi bayanta.A hankali kamar mai ciwon baki nace"Baffa gani"




"Kije ki shirya nazifi na jiranki a waje".


Miƙewa nayi jikina a sanyaye na fita wajen sallama kawai,nayi masa naja gefe na tsaya ina masa wani irin kallo mai cike da tsana.
"Ina fatan an sanar dake dalilin zuwana?".Cewar nazifi
Hararan na watsa masa ne ya sanya shi saurin ɗauke idonsa daga kallon daya kemin yacigaba da cewa"Maganar aure ne yakawoni amma bari na fara da gabatar miki da kaina.Sunana nazifi Sana'a ta noma ina noman dankali dawa Masada da kuma barkono sannan ina kiwon tattabaru ina aure k.........".




Tsawa na daka masa ina cewa "Kaga malam kama daina mafarkin aurena Dan bazan taɓa aure mutum irin kaba, gwara ma tun kafin lokaci ya ƙure maka ka janye wannan maganar."




Ban jira amsan dazai bani ba na koma ciki Baffa na tarar zaune a tsakar gida,ko kallonshi ban yiba nasakai zan shige ɗaki naji muryan baffa yana cewa.



"Ya kukayi da nazifin?."




Ya dakatar dani daga shiga ɗakin a dake nace"Baffa ni baimin ba kuma bazan taɓa aurensa".
Mari naji baffa ya sauƙe min ta gefen fuska na sai dana jijiri na ɗebata.
"Billahillazi koda gawarki ne,sai na ɗaurawa nazifi aure da ita kinsa alkhairin da yaron nan kemin kuwa?".


A raina nace ina kuwa zan sani karo na biyu da baffa ya sake maimaita min.
"MATUƘAR KINA ƘAUNAR KI CIGABA DA ZAMA ACIKIN GIDAN NAN SAI KIN AURE NAZIFI,




"Yanzu ke kina tinanin har kina da wani ƴancin akan kanki ne ai hibba ko mai ya faru dake a rayuwarki to babu wanda zakiyi,kuka dashi face MAHAIFIYARKI domin ita ta zaga yi miki abinda uwa take yiwa ƴaƴanta".
A guje na shiga ɗaki ina kuka,kuka nayi na fita hankali naci kuka mai isa ta bamai bani haƙuri saboda inna batanan daman ita ce mai kwantar min hankali.Tashi nayi na zauna tare da share hawaye na,ina kara tino furcin baffa.




"MATUƘAR KINA ƘAUNAR KICIGABA DA ZAMA A CIKIN GIDANNAN SAI KIN AURE NAZIFI AURE ZAN MIKI NA HUTU".


A hankali nace "Baffa zan bar maka gidanka na gwammace nabi dunyia akan na auri nazifi,matuƙar ina numfashi a cikin duniya sai na cika burin Abba sai na cimma ƙudurin yaya fawas na zama yar jarida".




Ina cikin haka inna ta dawo,fara'a na ƙirƙiro na tashi na tarbeta.
Kallo ta tsareni dashi tace "Hibba idonki kamar kuka kikayi ko?".
Wani maraniyar murmushi nasaka tare da karɓan ledan dake hannunta nace,"A 'a inna kaina ne kemin ciwo kawai"




"To Allah ya sauwake" nace "amin".




Kwana nayi ina tufka da warwara a cikin raina,ko yaya fawas bazan Sanar mishi zan bar gidan baffa ba domin nasan shakka babu ba zai goyi bayana ba akan hakan ba.
To ma ina zan nufa inna bar gidan baffa?,wanake dashi dazan nufe shi da matsalolina a halin yanzu?umma ce ta fara faɗu min a raina.
Amma nasan ko hauka nakeyi basan nufi wajen umma ba domin baza ta karɓe ni ba.Wata zuciyar tace min to ki shiga duniya mana.
Haka na kwana ban runtsaba,washe gari kuwa na shiga tinanin hanyar dazan bi na fita koda Ƙofar gida ne domin baffa ya hana ni fita ko'ina.
Muna zaune da inna ina tsince mata wake,hajara ta fito daga ɗaki tana ta jaraba.Cewar wai gidan ba ruwa ga shi baffa ya fice abinsa ba tare daya nemo yaron dazai ɗeboba.




Cikin hanzari nace"Bari naje na ɗebo ruwan".
Inna tace "A'a hibba kar kijawa kanki abin magana,adamu yazo yata miki faɗa ki bari ya dawo ya nemo Wanda zai ɗebo ruwan da kansa".
"To inna ki barta ta ɗebo mana daman,aikin metakeyi a cikin gidan".hajara ta faɗa tana wurgo min wata uwar harara.
Cikin sanyin murya inna tace "To hibba kije amma Dan Allah karki daɗe"


"To"


Kawai nace, hijab ɗinna na ɗauka da waya ta sannan na ɗauki bokatin ɗebon ruwan na fita.
Ina fita na ajiye bokatin a kofar gida,na nufi tashi duk daba wani sanin garin nayi ba.
A ƙafa na ƙarisa tashan wani shagon saida wayoyi na hango a gefen tashar
Na shiga na saida waya tavsannan na dawo cikin tasha.
Ajiyan zuciya nasaka yayin da hawaye ke zubowa daga idona,ina zan nufa yanzu?wanake dashi dazan je wajen sa?inama-inama ace innaje wajen umma zata fahimci irin raɗaɗin danake ji a cikin raina ta karɓe ni?.
Share hawaye na nayi dai-dai lokacin da wani mutum ya ƙariso Inda nake tsaye yana cewa "Hajiya KATSINA ne?".




Lokacin ɗaya naji bakina yace "E",ba tare da yayi shawara da zuciya ta ba.
"To bismilla ga can motar a can"
Na shiga motar daman mutum ɗaya ya rage motar ta cika ina shiga kuwa direban ya ja motar.
Tinda muka hau titi nake kuka har muka isa cikin katsina ta dikko ɗakin kara kunya gare Ku badai tsoro ba.
Tabbas mutanen katsina sunmin karan da bazan taɓa mantawa dashi ba a tarihin rayuwa ta.
Yaron Motan ne ya shiga tattaran kuɗin motan,yana isowa na zara daga cikin kuɗin waya ta dana sayar na bashi.
Sannan na fita daga cikin motar,ina ƙarewa wajen kallo a duk cikin rayuwa ta ban taɓa ko mafarki zuwa katsina ba,sai gashi yau a dalilin maraici nazo.




Mahaifiyata ta kasa janmu a jikinta ta riƙe mu duk daɗi Duk wahala,yayin da dangin uba suka Gaza Samar min da kwanciyar hankali.




Haƙiƙa maraici cuta ne musamman na uba.Furcin baffa na tino"MATUƘAR KINA ƘAUNAR KI CIGABA DA ZAMA A CIKIN GIDAN NAN TO SAI KIN AURE NAZIFI".




A hankali nace yayin da hawaye kebin fuskana "Baffa nabar maka gidan ka".




Sannan wani kuka Mai ƙarfi ya kubce min nan na zauna cikin tashar naci kuka mai isa ta.


________________________________________


Inna tana zaune har tagama tsintar waken bani ba alamata tace"Hajara ko zakije ki dubo hibba ne kar,adamu ya dawo bai sameta a gida ba kinsan faɗansa".




Harara Hajara ta cilla mata kafin tace"Kiji min inna da wata iriyar magana,hibban ƙaramar yarinya ce da inta fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login