Showing 30001 words to 33000 words out of 104857 words

Chapter 11 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7343

daura muna isa muka tambaye gidan malam Mahiru mai ɗan kara anan kuwa aka nuna mana.Domin Anty Amina ta taɓa cemin mahaifinta babban malamin addini ne a cikin daura kowa yasan shi.




Muna isa ƙofar gidan Habib yayi parking sannan muka fito nan naji kamar an sauƙe min wani abu mai nauyi,a cikin ƙirji na da sallama muka shiga cikin gidan akan anty Amina idona suka fara sauƙa wacce take zaune a tsakar madaidaicin gidan nasun tana wanke-wanke.


Sallamar damuka shigo da ita yasanya anty Amina ɗagowa tare da amsa salllamar,sakin kwanon siban dake hannun ta tayi yayi da idonunta sukayi tozali da fuska ta.


Miƙewa tayi tana faɗin"Hibba kece".


"Nice anty Amina "na faɗa ina isowa gare ta.


Rungume juna mukayi muna sakin kuka,wanda hakan ya sanya mahaifiyar anty Amina fitowa daga ɗaki ganin mu datayi haka yasata faɗin"Amina lafiya?,Waye waɗannan ɗin?.


"Umma itace Hibba wacce nake baki labarin ta"Anty Amina ta faɗa tana zuƙar majinan kukan daya zo mata.


Salati Umma ta saka tana ƙara jaddada iko irin na illahi,sarkin da ikonsa yake akan komai sannan tace"Baiwar Allah kullum Amina cikin zancen ki take safe da yamma,ko yaushe tinanin ta wani irin hali rayuwarki zaka faɗa?,duk sa'in data ɗaura goshinta a ƙasa da sunan salla kafin tayiwa kanta addu'a to sai ta nema miki tsari daga dukkan abin ƙi".




Tabbas Anty Amina ta zame min tamkar garkuwa a rayuwata ta baya,sannan itace ta fara bani taimako a lokacin danake matuƙar buƙatan hakan,wannan dalilin yasa nima a ko yaushe take cikin addu'ata.
Duƙusawa nayi ƙasa inacewa"Anty Amina nasan nayi miki silar lalacewar auren ki,ban saka miki da irin alkhairin da kika min ba sai dai ma igiyoyin auren ki da a sanadiyata tsinkewar su,ki yafe min anty Aminaa"na ƙarishe maganar take da jan furcin ƙarshen.


Ɗago anty Amina tayi kafin ta shiga faɗin"Hibba ban taɓa sanyawa a raina wai kece kika kashe min auren ba daga ni har iyayena,abinda nasa a raina kuma nake tina shi a ko yaushe shine ƙaddarar bawa ba taɓa tsalle shi,dukkan mu a wannan duniyar kuna rayuwa ne tare da ƙaddararmu.Sannan ba zamu taɓa guje mata ba kamar yanda bazamu iya gujewa inuwar mu ba".




"Anty Amina nagode,ga wanda zan aure wannna kuma ƴar-uwar sace"na ƙarishe maganar tare dayi mata nuni da su Habib da Yasira.


Tabarma ta shimfiɗa mana muka zauna sannan suka shiga gaisawa da Habib.


Muna zaune a wajen mahaifinta anty Amina malam Mahiru ya shigo,sai daya zauna sannna Umma ta shiga masa bayanin komai,jinjina kansa yayi kana yace"Tsarki ya tabbata ga sarkin daya ƙaddara saduwa tsakanin mu dake ".


Sosai malam Mahiru ya mana bayanin yanda malam Habu yayiwa Anty Amina sakin wulakanci a waya tare da jifan ta da zargi kawoni domin na lalata musu rayuwar ɗa.
Nayi kuka sosai da har sai dana rasa hawayen tsiyarwan sannan na shiga kukan zuci,abubuwan dasuka faru tsakani na da Kabir a ranan da Balaraba ta kore ni daga gidan ne,ya fara min yawo cikin ƙwaƙwalwata tamkar yanzu suke faruwa.


Nan na sanar dasu ainihin abinda ya faru tsakanin mu da Kabir a ranar,inayi ina ƙwalla haka ma anty Amina,Yasira Umma da kuma Habib daya sunkuyar da kansa yana tare hawayen dasuke shirin zubowa daga idonsa.
A duk cikin rayuwar sa ba halittan dayake girmamawa gamin da darajawa irin mace,wannan dalilin yasa aduk lokacin ya ga wata mace cikin matsala yake mata kallon ƴar-uwa ta jini,kuma yaken shiga lamarin ta mussaman irin waɗannan aka ketawa haddi har sai anmusu adalci.




"Ba komai akwai Allah,kuma akwai ranar tsayuwa a gabansa domin yiwa kowani bawa hukunci dai-dai da abinda ya aikata".cewar malam Mahiru wanda hakan ya dawo da mu daga duniyar tinanin da mukayi nitso a cikin sa.


UWATACE SANADI


_Tsarawa/rubutawa_
©Maimunah Tijjani Iyam


________________________________


Page 2⃣1⃣




Ƙiran sallan zuhr da aka farane ya sanya malam Mahiru da Habib fita masallaci yayin da mu kuma mukayi alwala sannan Anty Amina ta shigar damu ɗakin mukayi salla.
Tunda na iddar da sallan nake zaune kan sallayar,ni kaina bazan iya fasaltar irin tsanar danayiwa Habib ba cikin kwanakin wanda shikuwa kullum burin shi ya kyautata min tare da neman hanyar da zai dawo min da farin-cikin dana daɗe da rasa shi.


Shigowa anty Amina tayi ta dire mana kwanon ɗan-wake a gaban mu,maganar da Yasira tayi ne ya katse anty Amina daga tata maganar datayi niyya fiddawa.


"Anty inso nayi waya da Ummi,naga missed call ɗinta amma ba services".
"Wallahi muna fama da matsalar service a gidan amma da zaran kin fita ƙofar gidan kikayi tafiya kaɗan zaki samo sai kiyi wayarki"cewar anty Amina.


Gyalenta dake kafaɗarta Yasira ta gyara sannan ta fita tana cewa"Anty Hibba bari naje wajen".
Kaina kawai na ɗaga mata sannan ta ƙarasa ficewa.Zama anty Amina tayi kusa dani tana fuskanta na kafin tace"Hibba na kula da fuskan ki tabbas akwai abinda yake damunki menene?".




Nauyayyan ajiyan zuciya na sauƙe sannan nace"Anty Amina wallahi ina cikin matsala babba,bazan ɓoye miki ba wallahi banason wannan auren na Habib domin na gwammace akai mishi gawata ko ganinsa banason yi zaman gidan gabaɗaya ya fice min a rai.Shiyasa na roƙi Ummi ta barni naso nan".
Duk abinda yake raina na fitar daman ba wanda na sama damar yin maganar dashi sai yanzu danake gayawa anty Amina,ko yaya Fawas bamuyi maganar dashi ba.




"Hibba tabbas a yanda kika bani labarin zaman ki da mutanan nan,basu cancancin suzo miki da buƙata ki kasayi musu ba maƙutar kinada damar yin hakan,ni wallahi ma tausayin Habib ɗin nake saboda ciwon dayake ɗauke dashi.Ki dage da addu'a ba abinda ya gagare Allah kita sanar dashi damuwar ki bi'izinillahi komai zai wuce amma kar ki sake koda wasa kiyi wannan maganar da kowa kinji?".




Kaina kawai na gyaɗa mata domin naga Anty Amina bazata fahimci irin saurin da zuciya take iya ba wajen zana min tsanar habib da manyan harrufa a ko'ina a ciki taba.
Shawarwari Anty Amina ta bani sosai tare da wasu addu'o'i,muna haka Yasira ta shigo sannan mukaci abincin.


Mukayi sallan Asr kuwa muka yi shirin bari daura sosai Habib yayiwa malam Mahiru sha tara ta arziki,sai dana karɓa lambar wayar Anty Amina sannan muka tafi.
Tunda muka fara tafiyar zuciya ta take min zafi ɗan wuni da nayi a wajen Anty Amina jina nayi saƙayau kamar ɗaurarran daya masa ƴanci.


A hankali na lumshe idanuna sannan na kwantar da kaina kan seat ɗin motar ina maimaita "Hasbunallahu wa ni'imal wakil".


Habib daya lura da yanayi na yace"Fatima lafiya?".Cikin kwanan kin nan kuma sunan daya tsiri kira dashi kenan.
Kamar ya watsa min wuta haka naji lokacin da na tsinkaye muryar shin ya sauƙa cikin kunne na,sai dana harhaɗo jarumta kafin nace"Lafiya kalau kawai gajiyace".


"Daga cikin katsina zuwa daura shine har kin gaji?,To next tomorow da zamuje damaturu fa sannan mu biya ta wajen su baffa"ya faɗa yana sakar min murmushi.


Shagwabe fuska nayi ina ƙara lumshe idona nace"nidai ba inda zanje sai na huta".


Murmushi ya ƙara sakar min a karo na biyu kafin yace"Haka ne kam tawan ba wanda zai ta kura miki"ya faɗa yana maida ga kallonshi ga titin.


"Allah dai ya nuna mana lokacin bikin nan"Yasira ta faɗa sai a sannan na tino da ita dan tunda muka,shigo motar sai yanzun tayi magana da amin ya amsa mata.
Muna isa gida nida Yasira muka wuce part ɗin Ummi yayin da shi kuma ya wuce part ɗinsa sosai hakan ya min daɗi.Zaune da Daddy muka tardasu muka gaishe su suka amsa mana tare da tambayar mu ya hanya."Alhamdulillah!na amsa musu dashi sannan na tashi zan shiga ɗaki.


Inajin Ummi nacewa"To Hibba hankali ya kwanta yanzu dai ko,kije kin gano ta"murmushi kawai nayi na shige ɗaki.
Anty Amina na ƙira na sanar da ita mun iso lafiya sannan na kira yaya Fawas sosai mukayi hira dashi wanda shikam zancen sa duk akan bikin ne,wanda yanzu saura sati huɗu.


Washe gari kuwa da yamma ina kwance a ɗaki ummi ta aiko ƙirana,a falo na iske ta tare da yasira.




"Hibba zo kiga kayan lefenki ne kafin gobe a wuce dashi gidan granny"ta ƙarishe maganar tana min nuni da akwatinan dake jere jeras a gabanta.


Set uku ne masu launukan maroon,ash da kuma golding,ko wani set guda huɗu ne sai ƙaramar jaka a cikin sa.


Sunkuyar dakaina ƙasa kawai nayi ina cewa"Ummi basai naga ni ba,sunyi Allah ya saka da alkhairi".




Dafa kafaɗata tayi tare da faɗin"Amin hibba Allah ya miki albarka".
A sanyaye nace"amin"sannan na koma ɗaki koda Habib ya dawo ya aiko ƙira na ƙin zuwa nayi,daya matsa kuwa Ummi ce tace ya barni kunya nakeji kar ya matsa min.
Washe gari kuwa Ummi tajeta damaturu tare da kayan lefen a gidan Granny aka ajiye su,sannan suka wuce gano ita da ummi da kuma iya suka kaiwa su Inna lefen kamar yanda al'adar hausawa take dangin ango suke kaiwa lefe gidansu amarya.
Ranan rasa inda zatasa kanta Inna tayi dan tsabar murna,sosai Baffa ya musu tarban azirki.
Koda suka tafi Hajara rasa inda zata sanya kanta tayi dan baƙin-ciki,sam ta kasa zaune ta kasa tsaye.fargaban ta shine kar dai aikin nan baici ba.
Gidan Adda Barira taje ta shaida mata,kwantar mata da hankali Adda Barirar tayi tare da cewa su bari dai suga nanda wani lokaci in ancigaba,dayin batun auren sai su san matakin da zasu ɗauka.


Ummi kuwa kwananta uku a damaturu sannan ta dawo.Haka nan cikin kwanakin nan,da bikin keta matsowa kullum nake cikin kuka duk lallashin da Habib zai min bana kula shi,haka ko kalaman bakin Yasira zasu ƙare wajen tambaya ta abinda ke damun na bana tanka mata.Domin nima kaina zanso sanin abinda ke damun nawan.


Ummi ce wasu lokutan kance dasu daman ko wacce,mace in lokacin bikin ta ya ƙarato takan tsinci kanta cikin fargaba.
Tun ana saura sati biyu bikin Ummi ta sa akemin gyaran jiki sosai fatata ta murjewa ta ƙarayin,haske da kuma kyau.Cikin kwanakin nan kuwa wasan ɓoya mukeyi da Habib dan koda wasa bana yadda mu haɗu dashi.


Ana saura kwana biyar bikin na koma gano tare da Yasira,dan acan za'a ɗaura.Ana ɗaurawa kuwa tare da waɗanda sukazo ɗaurin auren zamu juyo katsina.
Guɗa Inna ta shiga rangaɗawa yayin da muka iso,ƴan-uwa da abokan arziki tunin sun fara cika gidan.Sosai Baffa da Inna sukayi farin-cikin zuwana.
Washe gari kuwa yaya Fawas shima yazo,ranar wuni mukayi Baffa da Inna suna min nasiha haka nan ma Yaya Fawas.


Da kanta Inna tasa aka zanzara min ƙunshi tare da Yasira,ana gobe ɗaurin auren da daddare ina tsakar gida ina waya da Habib Inna da yasira kuwa suna ɗaki.
Hajara ta fito daga banɗaki taɓe baki tayi yayin datake ajiye butar dake hannun ta kafin tace."Oh ni Hajara duniya sam babu tsoron Allah a zuƙatan bayi,daga mutane sun taimaka miki shine kuma bari a aure ɗan gida,yo wayasan irin abinda aka bashi ya sha a kunu da shayi aka mallake shi".




Ajiye wayar nayi ba tare danayiwa Habib sallama ba nace "Anty Hajara wai dani kike wannan maganar?".


Sai ta dallo min harara kafin tace"A akwai wani dazanyi dashi bayan ke".


Lokaci ɗaya naji raina yana mungun tafasa a harzuƙe nake faɗin"To ki buɗe kunnuwanki kiji abinda zan faɗa miki ni Habib baya cikin raina sannan da kike maganar wai na mallake shi,ni ko yanzu banƙi a fasa wannan auren ba baya gaba na balle kuma abin daya mallaka".
Ina gama faɗin haka wuf na juya na wuce ɗaki,na barta tsaye a wajen.
Kodana shigo ɗaki Inna na tarar zaune akan gadon ƙarfenta irin Nada mai rumfa,ta zabga tagumi hannu bibiyu.Yasira kuwa na kwance gefen ta tana bacci.
Kallo ɗaya nayiwa Inna yanayin ta,ya tabbatar min data saurarin maganganun da mukayi da Hajara.


Ɗauke kaina nayi na fara gyara inda zan kwanta muryartace ta katse ni.


"Hibba inason ki tabbatar min da abinda kika faɗawa,Hajara shin da gaske bakya son Habib?".


Gefen ta nazo na ɗauki pillow,ina cewa"Inna karka ki damu kanki fa,amsa ce kawai na bata dai-dai da tambayar data min kuma ai daman hakan takeson ji daga gare ni".na faɗa ina ɗaura kaina akan pillow na.


"To kul Hibba kar na ƙarajin kinyi irin furcin nan,yanzu yanda gidan yake cike da jama'a da wani ya jiki fa ki daina irin haka banaso".


Sai dana murmusa kafin nace"Inna kenan basai a fasa ba".




Cikin sauri tace"A fasa meye ɗin".




"Auren mana".




"Allah ya shiryeki Hibbatu,ki kwanta kar gobe ki kasa tashi da wuri".
Hmm Tabbas farin-cikin dangina shine abin daya zama abin tattali da riritawa a gare ni.Basan iya tunkarar ɗaya daga cikinsu in sanar dasu zuciya batason Habib ba,na gwammace in rayu cikin baƙin-ciki matuƙar nasu farin-cikin zai cigaba da wanzowa.
Hajara kuwa nan inda na barta nan daɗi ya ishe ta,ɗaki ta koma fuskarta na bayyanar da tsan-tsan farin-cikin da zuciyarta ke ciki.


"Alhamdulillahi madalla da Adda Bariri,wannan farin-cikin danake ciki haka Allah yakaimu gobe in fiddoshi waje".ta faɗa tana rufo ƙofar ɗakin.


"Amin Hajara da alama dai akwai babban abun dakika shirya goben nan?".


Tambayar da baffa ya wurgo mata wanda yasa hanjin cikin ta kaɗawa.
Ya faɗa yana ƙara duban kayan dasuke gaban shi,wanda yaya Fawas ya ɗinka mishi,wanda zai sa ranar ɗaurin auren.


"Ah Ah Malam daman kana ciki ne?,wallahi kasan duk wani masoyin mu yana farin-cikin ganin rana irin ta gobe.Ranar dazaka aurar da Hibba izuwa gidan mutumci,na tabbatar yaya sule zaiyi farin-cikin da hakan".




Sai daya murmusa kafin yace"Haka ne maganar ki Hajara"A takaice ya faɗi maganar.
Washe gari kuwa data kasance ranar juma'a ranar dake mafi daraja da falala daga cikin jerin kwanaki,dai-dai sauƙowa daga sallan juma'a aka ɗaura auren.
Tun ƙiran assalatun farko Hajara ta tafi gidan Adda Barira,duk abinda ya wakana tsakani na da ita ta kwashe ta faɗa mata.


"Adda ni yanzu so nake koda an ɗaura auren ya zamana ta kasa zaman gidan,hankalin ta ya kasa nutsuwa waje ɗaya.Ta yanda da ƙafarta zata baro gidan" Hajara ta faɗa fuskarta na bayyanar da tsatsan ƙiyayyarta gareni.


Shewa Adda Barira ta saka kafin tace"Sha kuruminki ƴar uwa yanda kikeso haka nan za'ayi,kinga yanzu ma tashi zamuyi daga nan mu wuce wajen Malamin nan mu sanar dashi buƙatar mu".




"Yauwa Addata tashi mu tafi,kafin Inna ta farka ta ga bana nan ta tsareni da tambayar ina naje".
Hajara ta faɗa yayin dasuke miƙewa, fitowar kishiyar Adda Barira daga ɗakin tane yasa su tsayawa.


Ɗaga labulen ɗakin tayi ba tare da ta fito gaba ɗaya ba,tana tsaye daga bakin ƙofar tace"Haba!Yaya ita kuwa yariyar nan meta tare muku a doron duniya?,meta aikata muku dahar kuke bibiyar ta da waɗannan munanan sharrukan?,Meye ribar ku indan kuka hana ta zaman gidan auren ta?.Shin bakwa tsoron ranar da Allah zai kamaku da laifin zaluntar wannnan baiwar tasa?.




Tsawa Adda Barira ta daka mata,yasa ta shuru ba tare data ƙarisa maganar data ɗauko ba.


"Laure ki kiyaye ni wallahi wato laɓe kike mana kenan ko?Ina ruwan ki da maganar mu meya shafe ki,muzaki nunawa kin fimu jin tsoron Allah".


"A'a Yaya Allah ya baki haƙuri"cewar laure tare da sakin labulen ta koma ɗaki.


Tsaki Hajara ta saka tare da faɗin"wallahi Adda ke kikayi sake har wannan matar take gaya miki magana son ranta haba!".


"Kyale ta ƴar-uwa zanyi maganinta"cewar Adda ta faɗa tana gyara zaman mayafin ta a kafadarta sannan suka fita.


UWATACE SANADI


Tsarawa/rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________


Page 2⃣2⃣






Gidan malamin suka wuce suka zayyana musu buƙatarsu bayan Adda Barira ta aje masa kuɗin aikin dana yankan daya ce za'ayi.
Sosai ya basu tabbacin cewa ita da zaman gidan aure lafiya sai dai da wani,ɗa namijin amma ba Habib ba sai taji ta gwammace ta shiga duniya akan ta zauna a gidan sa.
Sosai suka masa godiya sannansuka tafi gidan ta,Adda Barira ta wuce akan cewa zatazo anjima sannan Hajara ta wuco gida.




Hakan nan ji zuciya ta,ta kasa sukuni tun da Habib ya ƙira ni yake shaida min nazama mallakinsa.
Cikin wani tsadadden atamfa na shirya mai launin shuɗi,ɗinkin doguwar riga ne daya sauƙa min har ƙasa yayin da aka ƙawata ɗinkin da adon stones masu ɗaukar hankali.
Tare dasu Sayyid da sukazo ɗaurin auren Ummi ta haɗo su da mai make-up.
Sosai kwalliyar ta zauna a fuska na,sannan ta ɗaura min ɗan-kwali sannan na yafa gyale na daya kasance fari marar nauyi da kuma kauri haka nan kuma bashi da duhu.
Yasira kuwa anko ta saka wanda harsu Inna ma sunyi shi,ko dana fito nan gidan ya ɗauki guɗa ta ko'ina.
Yasira ce tashiga yiwa Inna magana a kunne,bansan meta faɗa mata ba sai gani nayi Habib ya shigo Sayyid na biye dashi a baya.Tare da tarin zugar abokansu.


Wata guɗar aka sake rangaɗawa,wata tsohuwa na faɗin"Ga angon ga angon".
Gaishe su sukayi sannan suka miƙe zasu fita bayan Sayyid ya sanar da Inna cewa yanzu za'a wuce da amarya.
Dam!zuciya ta ta bada,duk da Ummi ta sanar dani daman da zarar an ɗaura zamu taho,amma ban zata abin zaizo min a haka ba.
Bansan sanda hawaye suka fara bin fuska na ba,sai jin Habib nayi dab da inda nake tsaye yana share min hawayen.
Kamar ana watsa min tafashashshen ruwan dalma,haka nakeji a duk inda hannun Habib ya sauƙa a fuska na.


"Ki daina wannnan kukan fati na banaso kinji ko?"ya faɗa cikin raɗa,kaina kawai na ɗaga masa alamar naji.


Nan kuwa abokansa suka fara hasko mu,da kemarurin wayoyinsu suna mana hoto.
Sai a sannan na tino a inda nake,saurin matsawa gefe nayi ina sunkuyar da kaina ƙasa cike da kunya.


Shi kam ko a jikinsa fita yayi yana ɗan sosa ƙeya.
Yayin dasu Sayyid suka rufa masa baya ɗaki na koma na faɗa kan gadon ƙarfen Inna ina kuka,shigowa Inna tayi tare da zama dab dani tana faɗin"Hibba ba yanzu ne lokacin daya dace kiyi kuka ba,ki share hawayen ki inna da kyakykyawan zato akan Habib zai riƙe ki bisa amana".


"Inna nima banida tantanma akan Habib Inna,kukan danake Inna wai yau ake ɗaurin aurena amma mahaifiyata bata damu da tazo ba balle sanin yanda za'a gudanar da bikin".Na ƙarishe maganar ina cusa kaina a cikin pillow.


Ajiyan zuciya Inna ta sauƙe kafin tace"Hibba Fawas yaje sanar da mahaifiyar ku,amma ya samo ta tashi daga gidan kuma ba wanda yasan inda ta koma, ba wanda za'a tambaya cikin unguwan domin daman ba zaman mutunci sukayi ba".




Cak!kukan danake yi ya tsaya yayin da zuciya ta min nauyi sosai.
Numfashi na dayake sarkewa yasa ni tashi na zauna Inna ce ta fara ƙoƙarin yi magana,Amma na katse ta ta hanyar faɗin"Inna shikenan basai kinci komai ".


Ina rufe baki na Baffa da yaya Fawas suka shigo ɗaki sai da suka zauna kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login