Showing 18001 words to 21000 words out of 104857 words

Chapter 7 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7299

cewa wai ƙaddara ce ta rabota da iyayenta, wayasan abinda ya rabota da iyayen nata".ta ƙarishe maganar tana wani huci.




Ɗagoni anty Amina tayi ta riƙo hannuna tana faɗin"sannu hibba",


A hankali na miƙe idona cike da hawaye nace"anty Balaraba Allah shine shaida na ban taɓa aikata,abinda kike zargina dashi ba sannan bashi ne silar barowata gida ba".


UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam

_____________________________






Page 1⃣3⃣




Taɓe baki Balaraba tayi tare da cewa, "ke akwai abinda zaki faɗa Wanda zan yarda shine, kuma wallahi yau ko sharafar mutuwa kikeyi a cikin gidan nan,sai kin sharewa kabir ɗakinsa."


Cikin zafin rai anty amina ta shiga faɗin" ya isheki haka balaraba ina so kisani daga ke har ɗanki HIBBA ba baiwa na kawo muku ba".




Tana gama faɗin haka taja hannuna muka shiga ɗaki.




Zaunar dani tayi akan kujera tare da riƙo hannuna,dukka biyu tasa cikin nata tace.




"Hibba ina mai baki haƙuri akan irin abubuwan da abokiyar zama take miki ita ɗanta ki cigaba,da haƙuri wataran sai labari".




Cikin kuka daya ci ƙarfi na nace"anty Amina zamana a gidan nan,inaga kamar ina ja miki magana nagode da taimakon da kikamin Allah ya saka miki da alkhairi,amma ni inaga kamar inna tafi rayuwar gidan aurenki zaifi samun kwanciyar hanaki".




Dakatar dani tayi da cewa"hibba ki daina faɗan haka,tun kafin kizo haka nake zaman haƙuri a gidan nan nidai ina mai baki haƙuri" ta ƙarishe maganar tare da sharemin hawayen dake bin fuskana.


Buɗe baki nayi da niyyar yin magana amma anty Amina ta hanani wannan damar.




"Tashi kije kiyi wanka,bari na haɗa miki ruwan zafi ko"anty Amina ta faɗa tana ƙoƙarin tashin daga kan kujerar damuke zaune.


Toilet ta shiga ta haɗamin ruwan zafi sannan ta fito,tana cewa "kije kiyi wankan ko sai kiyi salla kici abinci".




A hankali na tashi duk wata gaɓa a jikina ciwo yakemin na shiga banɗakin,rufe ƙofar nayi na jingina kaina ajikin ƙofar ina wani irin kuka mai raunana zuciyar mai sauraro.




Shin haka daman rayuwar kowacce mace,yake cike da ƙalubale?ko kuma tawace kawai haka?.Allah sarki mutuwa ta tona min asiri,ta rabani da Abba.umma tagaza janmu a jikinta.




A lokuta da yawa ina tinanin,anya umma tun da muka bar gidanta ta taba tinaninmu kuwa?.Dalilin maraici yau gani a inda bansan kowa ba.




Ashe duk macen da bata gaban iyayenta, kallon ƴar iska ake mata kamar dai yanda balaraba take min?.




Nayi kuka sosai sai dana,tausayawa kaina na daina fuskata duk ta kunbura saboda dukan danasha da kuma kukan danayi.


Wankan nayi sannan nayi alwala nafito,anty Amina natarar tazabga tagumi hannu bibiyu.




Cikin nutsuwa nace"Anty lafiya?"


A hankali ta ɗago kanta tare da faɗin"hibba lafiya wani tinani nayi nace ko zamu fara fita shago tare".




"To anty" na faɗa ina barin wajen




Cike da farin cikin amsar Dana bata tace" yauwa hibba kinga duk zaki rage wannan tinane-tinanen da kikeyi".




Wucewa nayi ba tare dana amsa mata ba nayi salla,sannan ta kawomin abinci tunda nasa abincin a gabana na kasaci.akan sallayan na kwanta nan take wani baccin wahala ya ɗaukeni.




Tamkar a mafarki najiyo muryan mijin anty amina,sai zazzaga masifa yake yi,a firgice na tashi na nufi wajen na tsaya daga bayan labulen ɗakin ina jiyo abinda yake faɗa.


Cikin matuƙar bala'i yake cewa"Amina na faɗa miki,tun ranar da yarinyar nan tazo gidan nan kar ta shiga harkan kabiru amma bataji bako?".




"Malam baka fahimce abinda ya faru bane yarinyar nan ba f.....".




Dakatar da ita yayi da cewa" to mezan fahimta ko ita balaraban data gayamin,zata miki ƙarya ne?nidai na faɗa miki ta fita harkan kabiru,dan wallahi in irin haka ya cigaba da faruwa to billahillazi a bakin aurenki".




A firgice anty Amina tace"saki kuma malam meyayi zafi?".




"Komai ma yayi zafi kabiru shi kaɗai nake dashi bazai yiyu ba yarinya tazo har gidan ubansa,tana cin arziki sannan ta nema ta takura mishiba,Ke baki haifamin ba kuma a nema kashe min Wanda nake dashi".




Kukan anty Amina ke dannewa ne ya sama nasarar fitowa"malam,amma kasan ai haihuwa ta Allah ce ko?kuma nima bai manta dani ba".




Tsaki ya sake yayi shigewarsa ɗaki,cikin sauri nima na koma na kwanta,inajin shigowar anty Amina ɗakin na rufe idona kamar mai bacci.


Zama anty Amina tayi tana kuka,inajinta amma na kasa tashi inbata haƙuri.


A hankali nima hawaye suka fara bin kuncina,Matar data taimake ni a lokacin danake matuƙar buƙatar hakan,ta ɗauke nauyin ci da Sha na lokacin da uwata ta gaza yin hakan a gareni,ta zauna dani zama na domin Allah duk da kasancewar bata san labarina.




Yau a ta dalilina,take zubda Ƙwalla,a hankali nace"ya Allah ka bani abinda zan sakawa wannan baiwar taka dashi.




___________ GANO________




Zaune baffa yake,a kofar gida wani Mai mashin yazo ya faka dai-dai kofar gidan.




Yaya fawas ya sauƙo daga mashin ɗin,ya nufo inda baffa ke kishingiɗe.bakinsa ɗauke da sallama.


Durƙusawa yayi ya gaishe da baffa cikin sakin fuska baffa ya amsa tare da cewa"mutan bauchin yakubu yaka baro gidan naku?".




Washe baki yaya fawas yayi kafin yace "baffa duk lafiya suna gaisheku".




"Madallah ka tashi ka shiga ciki kasha ruwa inna ma tana ciki".baffa ya faɗa yana ɓantarar guntun goron sa




Cike da rashin fahimta yaya fawas yace"baffa hibba fa?".


Gyaran zamansa baffa yayi kafin ya shiga faɗin " fawasu yau kusan wata biyu hibba bata cikin gidan nan".




Cike da rashin fahimta yaya fawas ya kuma tambayar sa"Baffa ko ta koma makarantar ne?Dan kullum ina ƙira wayarta,bana samu shiyasa ma nace bari nazo naga ko lafiya?".




Gyaran muryan baffa yayi,tare da bayyanawa yaya fawas duk abinda ya faru.


Wasu hawaye ne suka shiga zubowa daga idanun yaya fawas nan take ya suma a wajen,miƙewa baffa yayi yanata doka salati ya shiga gida ya ɗauko buta ya zuba mishi ruwa.




Dogon ajiyan zuciya yaya fawas yasaka baffa ya riƙeshi yanata jera mishi sannun har suka isa cikin gidan,hajara ta shimfiɗa musu tabarma suka zauna.




Cikin wani irin yanayi Mai matuƙar ban tausayi da wahalar fassarawa,yaya fawas yace.


"Kuma baffa duk an bincika wajen sauran dangi bataje wajensu ba?".


Caraf inna ta amshe zancen da cewa" gashi nan ba yanda banyi dashi akan ya haƙura da maganar nan ba amma yayi burus da maganata ai yanzu kaga abin daka ja mana".




"To inna to karatun nata fa?"furcin yaya fawas




Sai da inna ta gyara ɗaurin zaninta kafin tace" Adamu shine silar duk abinda hibba ta aikata sannan ka shirya fuskantar ubangijinka da laifin kasa sauƙe hakkin marainiyar da aka barma".


Sai data numfasa sannan ta ɗaura da cewa"Adamu sanin kan Kane ka ƙuntatawa,rayuwar hibba dakai da matarka".


Ajiyan numfashi baffa yayi cike da nadaman abinda ya aikata yace.


"Inna ban taɓa tinanin hukuncin dana zartar akan hibba,zata iya barinmu saboda wannan ba".


Cikin zubda ƙwalla murya can kasa,yaya fawas ke cewa" baffa baka kyauta min ba,shin baka tinanin halin da hibba zata shigane?,ko baka tausayin tane?,jinin kace fa ita ƴar ɗan-uwanka ce fa".




Dafa kafaɗunsa baffa yayi yana cewa "fawasu ka kwantar da hankalinka in sha Allah duk inda,hibba take tana hannu mai aminci.Daga nan ka wuce wajen mahaifiyar ku ka tambaya ko can hibban taje".




"Baza taje ba baffa kuma ko taje ma umma baza karɓe ta ba".cewar yaya fawas.




Ɗaga hannanyen sa sama yayi,ya shiga faɗin" ya Allah ka tsare min ƴar-uwata aduk inda take acikin duniya,ka amintar da ita cikin amincewar ka dawo mana da ita cikin aminci".




Yana gama faɗin haka,ya kifa kansa akan gwiwowinsa yana wani irin kuka Mai cike da tausayawa.


Miƙewa hajara tayi tana cilla musu harara tayi shigewar ta ɗaki..






______________HABIB_______________




Zaune yake akan kujera a cikin bedroom ɗinsa,na gidan granny sunzo gaishe ta tare dasu ummi,riƙe da wayarsa yana dialing numberna.




Kamar kullum wayar a kashe yajita,dan uncle suraj har a companyn mtn ya bada numbern da zaran ansa layin akan waya zasu sanar dashi.




Cilla wayar yayi kan bed ɗin sannan ya kwantar da kansa,akan hannun kujerar.




Dafe ƙirjinsa yayi saboda bugun da zuciyar sa take masa,da sauri-sauri.


Lokaci guda yaji numfashinsa yana ɗaukewa,tari ne ya sarke shi sosai ƙirjinsa yaƙara dafewa da ƙarfi.




Tari yake yi sosai,har da jini ga numfashin sa daya ke barazanar barin gangar jikinsa,faɗowa yayi daga kan kujerar.




Dai-dai lokacin da ummi ta shigo ɗakin salati,ta saka tana nufo inda yake a ruɗe ɗaura kansa tayi akan cinyarta sannan ta riƙo hannunsa tana murzawa.
ƙwalla nabin fuskarta,ta fara kiran sunansa "Habib!Habib!!Habib!!!".




UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam


________________________






Page 1⃣4⃣




Lumshe idanu sa yayi a hankali muryansa can ƙasa-ƙasa yace"Ummi zan mutu zuciya na ciwo yake min".




Ummi da duk ta rasa nutsuwar ta tace "A'a Habib bazaka mutu ba,ciwo bashine mutuwa ba".
Wani razanan ne ihu tasaka ganin Habib ɗin ya daina motsi,hakan yasa su Granny,Sayyid,Yasira da kuwa iya shigowa.


Dan dama sunzo gidan Granny ne dukkan sunzo gaisheta,Daddy kuwa yayi tafiya Japan.




Asibiti suka wuce dashi GENERAL HOSPITAL dake cikin garin damaturun emergency aka shiga dashi.




Wayarsa dake hannun sayyid ne, ta fara ringing ganin sunan bashir ya bayyana cikin screen ɗin wayar.


Yasashi ɗaga kiran,nan yake sanar dashi halin da habib ɗin yake ciki,tambayarsa yayi"wani asibitine?"sayyid ya gaya masa.




Granny keta safa da marwa kofan ɗakin da'aka shiga da Habib,Yasira da Ummi kuwa sai kuka suke iya nata lallashinsu.




Within 15min Bashir ya iso cikin asibitin,Sayyid ya ƙira ya fito ya shigo dashi bangaren da aka kwantar da habib ɗin.




Zama Granny tayi,tana sauƙe ajiyan zuciya kafin ta shiga faɗin"Ban shirya nasaka ba Habib da farko na rasa halima,nasara mijina sannan na rasa dukkanin iyayen ka Habib a lokaci guda.ya Allah ka ɗauki rayuwa domin na tabbatar bazan iya jure rashin Habib ba".
Dafa ta Sayyid yayi yana cewa"haba! Granny inkina faɗin haka mu kuma ai sai ki karyar mana da zuciya, In sha Allah Hamma bazai mutu ba ki daina kuka".ya ƙarishe maganar yana zama kusa da ita
Yana rufe bakinsa likitan dake duba Habib ya fito,cikin sauri suka ƙariso gare shi suna tambayar ya jikin Habib ɗin?.
"Ku kwantar da hankalinku,Gajiya Ku biyo ni office".iya abinda likitan ya faɗa kafin ya wuce office ɗinsa
Binsa sukayi a baya har izuwa cikin office ɗin nasan.
Zama yayi tare dayin gyaran murya sannan ya fara faɗin"Hajiya Habib yana da wata damuwa a cikin ransa ko kuma ince akwai wani abu dayake so wanda bai samu ba,advice ɗin dazan baku a matsayinku na makusantan sa,Ku zauna dashi Ku tattauna ya faɗa muku damuwarsa inba haka ba hajiya I'm sorry to say za'a iya rasa sa gaba ɗaya".




Ajiyan zuciya Mai nauyi Granny ta sauƙe tare da cewa "to doctor ko zamu iya ganinsa?".




"E you can see him amma please kar ayi hayaniya dan hakan zai iya sa jinin sa ya hau".




Fita sukayi suka nufa ɗakin, da aka kwantar da habib ɗin.




Yana kwance yana bacci zama sukayi duk suna kallonsa, fuskar sa kaɗai ta isa mutun ya iya fahimtar girman damunwan dake cikin zuciyarsa.




"Yanzu yakuke ganin za'ayi?" Cewar granny.




Ummi tace " hajiya nidai gaskiya a tinani na,yabar ƙasan nan gaba ɗaya, dan inyaga ya nisanta da ita koyaga ya dena samun wasu labaru akanta hakan zai taimaka wajen rage tinaninta dayakeyi".


Tana rufe bakinta habib yafara buɗe idanunsa a hankali.




Dafe kansa yayi saboda wani irin nauyi daya yi masa,yana faɗin "wash!".




Cike da nuna kulawa Granny tace "sannun babban mutum,inane yake maka ciwo?".




Cikin ƙarfi hali yace"Granny kaina kaina ciwo yakemin".


Ƙara riƙo hannunsa tayi tana murzawa tace "sannu".


Bashir yace" Granny bari naje,na sanarwa doctor ya tashi daman yace inya tashi a sanar dashi".ya na gama faɗin haka ya fice.




Sannan suka dawo tare da doctor ɗin duba shi yayi sannan ya bashi maganinsa ya sha,cikin ƙanƙanin lokacin ya sama bacci.






Sai da dare sayyid ke sanar da daddy halin da habib ɗin yake ciki, faɗa daddy yayi sosai akan me za'a ajiye shi a asibitin 9ja?.




Bayan yanada likitansa na mussamman dayake duba lafiyarsa a malesia.




Tun kafin ya dawo ya gama shirya fitar da habib izuwa malesia.




Haka kuwa akayi yana dawowa,ya ɗauke sa suka tafi malesian tare da sayyid wannan karan hadda granny kwanan su biyar suka dawo.






Amma shi habib ɗin acan suka bari shi daman sugama magana da granny akan zai zauna acan.Na wasu lokaci kafin likitotin sun ƙara tabbatar da samuwar lafiyar zuciyarsa.




Watansa uku acan bikin bashir ya taso da ƙyar granny ta amimce masa yazo.




________________________________________






Ina kwance a ɗaki anty Amina ta fita,unguwa naji balaraba na ƙwala min kira.




Na fito nace"gani".


Wasu tulin kayan wanki ta nunamin,tana cewa.




"Ga kayan kabir nan yanzu ki wanke masa sannan inki gama kizo,zan aikeki kasuwa kimin cefa ne".




"Anty balaraba waɗannan kayan,ai bazan iya wanke su ayau ba Sai dai na raba su yau nayi,gobe ma nayi". na faɗa ina ƙarewa yawan kayan kallo.






Harara ta ɓalla min tana faɗin"ke zan sharara miki mari fa,ki kiyaye ni fa,a yau zaki wanke kayan nan gabaɗaya".


Nauyayyen ajiyan zuciya na sauƙe, kayan na ɗauka na fara wankin.




Tun safe har bayan la'asar ban gama ba gashi saboda anty Amina bata nan,ko abinci banci ba dama itace mai bani kuma yau bata nan.




Haka na wanke kayan tas!ko sannu balaraba batamin ba balle tace min madalla.




Ina shara anty Amina ta dawo,nabar sharan naje na karɓi ledan dake hannun ta ina mata sannu da zuwa.




Cikin fara'a take amsa min,sannan muka nufa ɗaki.


Tsawa balaraba ta daka min tana cewa "munafuka inazakije?baki gama min aikin dana saki ba?".




Jikina na rawa nace"anty balaraba innayi salla zan fito na ƙarisa".




"Yimin shuru wato kinga ta dawo ko shine zaku shige ɗaki kuyi sana'ar taku ta gulma ko?".cewar balaraba




Ajiyan zuciya anty Amina ta sauƙe kafin tace"hibba shigo ɗaki kiyi salla,sannan kici abinci dan nasa tun safe baki ciba".




Cikin ɗaga murya anty balaraba tace,"Yo daman wa kika ajiye acikin gidan dazai bata abinci?".




Ba mu kulata ba,muka shige ɗaki anty Amina ta bani abincin data sayo min a hanya.




Naci sannan nayi salla,na fito na ƙarisa aikin.na zaune kan sallaya bacci ya ɗauke ni.




Washe gari anty Amina ta tashi da ciwon kai,don haka ko shago bata fita ba.




Kamar kullum ina tashi na fara wanke-wanke nayi shara sannan na wanke banɗaki.


Ina gamawa zan shiga ɗaki kabir yana fitowa daga ɗakinsa,wani harara ya cilla min mai cike da tsana lokacin da muka haɗa ido dashi.




Ƙofar ɗakin balaraba ya nufa,yana faɗin"mama!mama!!mama!!!".




Fitowa tayi tare da malam habu tace"lafiya kabir?".


Marairaice murya yayi kana yace" mama dan Allah kiga wani irin wankin da yarinyar nan tamin duk basu fita ba salon kawai ta dafarmin da kaya".




Kamar jira malam habu yakeyi ai kuwa ya rufeni da faɗa tare da cewa" ki ɗauki kayan nan yanzu ki kara wanke su.




Wasu hawaye masu zafi suka shiga rige-rigen fitowa daga idanuna,kayan na kwatsa na fara wankesu, inayi ina hawaye har kiran sallan azahar ban gama ba.




Fitowa anty Amina tayi tace "hibba kibar wankin nan ki tashi kije kiyi salla sannan kici abinci".




Miƙewa nayi naje nayi alwala sannan nayi salla,Anty amina ta ɗebo min abinci inasa abincin a gabana naji muryar balaraba sai ashariya takeyi.




Tana cewa "malam fito,kagane min ikon Mai sama yanzu na sauƙe abinci wani yazo ya ɗeba".




Malam habu yana fitowa yafara kiran anty Amina, tana fitowa ya hau ta da masifa.




Ta inda ya shiga bata nan yake fita ba,cikin sanyin murya anty amina tace "ayya malam a hibba fa na ɗebawa,naga tun safe take aiki acikin gidan nan kuma ban fita ba balle insayo mata shiyasa na ɗeba mata".




Zabga mata mari malam habu yayi hagu da dama,sannan ya ɗaura da jaddada mata cewa.


"Shin Amina ban faɗa miki nauyin ci da shan yarinyar nan yana kanki ba tun lokacin dakika kawo ta?,maza-maza ki wuce ki dawo da abincin nan".




Ina zaune a inda anty Amina tabarni ta shigo ta ɗauki abincin, daman ko hannu na ban saba.




Sannan ta dawo tace"hibba kiyi haƙuri,bari na baki ɗari biyu kije ki sayo wani abincin".




"A'a anty kibar shi ma banajin yunwar".




Bata kulani ba ta ɗauko kuɗin ta miƙomin ban mata musu ba na karɓa na fita.




Ina tafe ina hawaye wannan wani irin rayuwa ce?,komai ya faru dani UWATACE SANADIn zubar hawaye na.




Ina cikin tafiya wani Mai mota yayo kaina,kafin na kauce masa har ya iso gareni.




Fitowa yayi daga cikin motar yayo kaina cike da faɗa ya fara zagina.




Wata macece zaune agaban motar wacce bazan iya faɗin matarsa ce ko ƙanwarsa ba,ta fito tana ƙoƙarin hana shi zagi na.Ni kuwa ina tsaye na kasa ko motsi sai hawaye danakeyi.




Wani mummunan kallo ya jefomin yace "dallah dube ta fa ko haƙuri bata iya badawa ba".hannu ya ɗaga niyyar sauƙe min mari.




Cikin sauri na runtse idona,jin banji sauƙar Marin ba yasa na buɗe idona.




Wani mutum ne ya kama masa hannun daya ɗaga da niyyar mari na.




Ɗago kaina nayi da niyyar, gani ko wanene caf" idanuna suka sauƙa akan fuskan HABIB.




Zaro idanu nayi bakina narawa nake furta" habib".


Kallo ya tsareni da shi a hankali lips ɗinsa suka motsa tare da furta"HIBBA kece".


Juyawa yayi yana bawa Mai motan haƙuri, ni kuwa cikin sauri na tsara ta cikin mutanan dasuka fara tarowa a wajen na bar wajen.


UWATACE SANADI




Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam




_________________________


Page 1⃣5⃣








Bayan wani shagon aski,na tsaya ina hangen habib sai bawa Mai motan haƙuri yakeyi.


Yana gama bashi haƙurin ya juyo inda yabarni tsaye sai dai,bai ganin awajen ba waige-waige ya farayi.


Tambayar mutanen wajen ya shiga yi ko akwai wanda yaga fita ta daga wajen?.


wani yace masa "ai ta daɗe da barin nan dama tare kuke ne?".




Da sauri-sauri zuciyarsa ke bugawa,tamkar zata fito daga cikin ƙirjinsa jingina bayansa yayi a jikin motarsa.




Sannan ya fara zamewa a hankali har yakai ƙasa ya zauna.




"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!".


Ya furtawa a hankali badan mutumin daya shaida masa yaga wucewa ta ba,tabbas da zaice gizo idanunsa ke masa.




Wayarsa ya ciro daga cikin aljihunsa ya ƙira drivern sa,ya faɗa masa inda yake yace yazo ya ɗauke sa,dan a yanda yake jin kansa yanzu bazai iya driving ba.




Ina tsaye bayan shagon naga tafiyar habib, wasu hawaye masu zafi suka fara bin kuncina.




Tabbas bayan Abba da yaya fawas,banida wani masoyi kuma jigo kamar habib,amma bazan iya bayyana masa kaina a halin danake ciki yanzu ba.




Da kyar nake ɗaga kafata har na isa gida kabir na iske a ƙofar gidan sai daya dallo min harara sannan yace.


"Ke kuma lafiya zaki dawowa mutane gida kina kuka?".




Ban kulashi ba nayi wuceta cikin gidan,anty Amina tana tsakar gida tana haɗa murhu na wuceta zan shiga ɗaki.






Muryar tace ta dakatar dani tana faɗin "hibba lafiya meya faru?".


Ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login