Showing 21001 words to 24000 words out of 104857 words

Chapter 8 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7289

kulata ba dan ji nayi bakina ya kasa furta komai na shige ɗakin.




Ina shiga na ƙara sakin wani Sabon kuka,anty Amina ta biyo ni ɗakin.




Dafa ni tayi tare da faɗin" hibba lafiya ko kabir ne ya miki wani abun?".




Kai na girgiza mata alamar a'a,tace "to menene?",faɗawa jikinta nayi nacigaba da kuka na itama tana tayani.






Mucin kuka Mai iskar mu, Kafin anty Amina ta ɗagoni daga kwanciya danayi ajikinta.Hawaye fuskana ta fara share min tace "ya isa haka hibba meya saki kuka?".




"Babu komai"na faɗa cikin kukan dayake shirin sarƙe ni.




Miƙewa tayi tana cewa"shikenan hibba tinda bakai naji matsalarki ba,sai ki cigaba da kukan".cikin sauri na riƙo hannun ta.


Nace"anty kiyi hakuri ki zauna".


Zama tayi tana fuskanta na tace "inajinki menene?".


Ajiyan zuciya nasaka yayin da hawayen danake ya tsananta.




"Anty tabbas ki riƙe ni amana zan sanar dake labarin rayuwata,inkiga zaki iya zama dani a haka zanso hakan in kuma bazaki iya ba nagode da taimakon dakika min a rayuwa".




Nan na sanar da ita,komai game dani ita kuka ni kuka ba mai bawa wani haƙuri.Har nagama hawaye bai bar zuba daga idanuna ba.


Anty Amina tayi ƙarfin halin faɗin" tabbas rayuwa cike take da jarabawa kala-kala,ban taɓa jin labarin irin naki ba hibba.Ban taɓajin inda uwa ta aikata irin abinda ummanki ta miki keda ɗan-uwanki ba Allah yajiƙan abbanki".




A zuciya na amsa da amin saboda kukan danakeyi yaci ƙarfina jin abubuwan nakeyi kamar yanzu suke faru,mussamman ranan da Abba ya rasu da kuma ranan damuka rabu da yaya fawas.


Kamo hannuna tayi,tasa cikin nata sannan tace.




"Hibba zan tsaya miki ki cigaba da karatunki,duk dama nima bawani ƙarfi ne dani ba gidan abincin na watace nake tsaye mata akai, amma gobe zanje gidanmu zan sanarwa mahaifiya ta inada dabbobi acan sai na tsayar nabaki kuɗin kiyi amfani dasu ki koma makarantar".






Kuka na saka Mai sauti,nace"anty nagode Allah yasaka da alkhairi".




"Ba komai hibba ai mun zama ɗaya yanzu".cewar anty Amina




Ranan kwana nayi ina kuka washe gari anty Amina ta shirya,zata tafi gidansu dake karamar hukumar daura.




Tare tace zamu je amma sai na tashi da matsanancin ciwon kai,hakan yasa ta tafi ita kaɗai.




Ina kwance a ɗaki ina rawar ɗari balaraba ta banko labulen ɗakin sannan ta shigo tana cewa.


"Nizan fita ki ɗaura min girki sannan kabir yana gida,duk abinda yace kimishiki tabbatar kin mishi".






Ban damu na sanar da ita halin danake ciki ba dan nasan,hakan bazai sa ta basa aikin da tace nayi ba.Dan nasan ko sharafar mutuwa nakeyi sai nayi aikin nan kamar yanda ta saba faɗa min hakan.




A hankali nace" to adawo lafiya".Bata kulani ba illa ficewa datayi daga ɗakin tare dajan wani tsaki mai dogon zango.




Ina kwance naji kabir na ƙwala min ƙira da kyar na tashi na fito ina cewa" kabir lafiya?".




Harara ya watsa min tare da cewa" ki wuce ki ɗaura min ruwan wanka".yana gama faɗin haka ya koma ɗakinsa.




Wuta na haɗa na ɗaura masa ruwan sai daya tafasa sannan,na juye a bukati na nufi ɗakin kabir Kasancewar banɗakin sa acikin ɗakinsa yake.


A ƙofar ɗakin na tsaya ina cewa" ga ruwan wankan".


Daga ciki naji yana cewa "ki shigo ki kaimin banɗaki".




Ban kawo komai a raina ba na shiga ɗakin, kasancewar irin jan kunnen da balaraba tamin kafin tafita,koma yanzu banason na ƙara jawa anty Amina magana awajen malam habu.




Har kofar banɗakin na ajiye masa bukatin ɗin.Na juya zan fita naji kabir ya riƙo hannuna, firgice duk jikina ya ɗauki rawa na juyo.




Bakina na rawa na furta" kabir meye haka?".na fara ƙoƙarin ture shi daga jikina.




Manna bayana yayi jikin bango ɗakin tare da riƙe dukkanin hanneyana biyu cikin hannunsa ɗaya,yayin dayasa ɗayan hannun nasa ya cire min hijabin dake kaina.




Zani ne ajikina kaɗai ɗaurin ƙirji kaina ko kwali babu,muryata na rawa nake faɗin.


"Dan Allah kabir kayi haƙuri ka barni da mutumcina".




Bai kulani ba illa wani irin kallon daya tsareni dashi da idanunsa da suka rikiɗe suka zama jajir.




Bakina narawa na ƙara cewa"kabir kayi wa girma Allah kayi haƙuri,na haɗa ka da girman allah karka ketamin haddina".




Duk magiyan danake mishi hakan baisa ya barni ba,cillani yayi kan gado yafara nufoni.




Kuka nake ina masa magiya ina ja da baya har na iso ƙarshen gadon,ina waige-waige na hango kwaskon turaren wuta cikin azama na ɗauko kwasko.




Kabir yana yiyowa kaina na buga masa kwaskon a goshinsa,cikin jin azaba yadafe goshin nasa da hannunsa.




Nan take kuwa jini yace salama alaikum ya fara zuba kamar da bakin ƙwarya.


Ɗago kansa yayi yana kalloni da idanusa dasukayi jajir,gashin kaina ya damƙo da ƙarfi ya cillani ƙasa daga kan gadon.




Ɗago ni yayi yafara wankeni da mari hagu da dama,sannan ya hankaɗe ni kaina ya bugu da window glass ɗin windown ya sari hannuna.




Wani ihu nasaka mai ƙarfi saboda azabar danaji.Dai-dai lokacin balaraba ta turo ƙofar ɗakin,daman kabir a buɗe yabarta.




Salati tasaka tare da jefawa kabir,wani irin kallo Mai cike da tuhuma ganin jinin dake ta zubowa daga goshinsa.


Cikin sauri kabir yace"wallahi mama ban mata komai ita ta shigo har cikin ɗakina".




Cikin zafin rai da wani irin hucin ɓacin rai balaraba ta nufo inda nake durƙushe.




Ɗago ni tayi tare da rufeni da duka ta ko'ina dukana takeyi tana faɗin.




"Hibba Allah ya isa tsakani na dake ɗan nawa ƙwalli ɗaya shi kikeson ki lalata min?".




Tana juyawa ta hangi bukatin ruwan zafin dake ajiyen ƙofar banɗakin kabir.




Tureni gefe tayi na faɗi yayin da ita kuma taje ta ɗauko bukatin ruwan zafin.




Ina kwance a ƙasa ina fitar da numfashi sama-sama naji sauƙar ruwan zafin a jikina,wani irin azababben ihu na saka lokacin dana kejin ruwan zafin na ratsa duk ilahirin sasan naman jikina.




"Munafuka daman ki shigo gidan da nufin lalatamin yarone?to Allah yafi ƙarfin ki,ki tashi kibarmin cikin gida kafin na illata ki".




Ƙafafuna na karkarwa na fara ƙoƙarin tashi,hijabina na saka sannan na tashi ina tafiya ina faɗuwa har na fita daga cikin gidan.


Wani irin azaba nakeji acikin jikina ƙafata ko takalmi babu haka nake tafiya.


Ga raɗaɗin da hannuna yake min inda glass ɗin ya yanke ni,idanuna basa ganu min komai sai baƙin duhu.duk gaɓoɓin jikina jinsu nake kamar ana sassara minsu.




Faɗuwa nayi daga nan bansake sanin inda kaina yake ba sai buɗe ido nayi na ganni a gadon asibiti.


Wani masallaci ne a cikin unguwan suka haɗa kuɗi suka ɗauki nauyin jinya ta.


Ina fita daga gidan su kabir balaraba ta kira malam habu yana isowa,ta fara cewa"malam Amina ta cucemu ta kawo mana annoba cikin gida".




"Balaraba meya faru?" Ya tambaya cikin zaƙuwa dason jin abinda zata faɗa masa.


Nan ta faɗa masa ƙarya da gaskiya wai inason na lalata musu yaro,har neman kashe shi naso nayi na fasa masa goshi.




A take a wajen malam habu,ya kira anty Amina a waya ya mata saki uku sannan suka wuce da kabir asibiti.






____________________HABIB______________




Tun lokacin da drivernsa ya ja motar suka nufi gida, tun acikin motar yaji zuciyarsa ta masa wani nauyi.




Suna isa ya wuce part ɗin ummi, tana zaune tare da yasira wacce yanzu dawowarta daga makaranta.


Driver ya shigo dashi,cikin Sauri ummi ta miƙe tana tambayar ko lafiya?.


Zaunar dashi driven yayi sannan yace "hajiya kirana yayi nazo na ɗauke shi saboda bazai iya driving ba, amma sai naga kamar bashi da lafiya shine na taimaka masa na shigo dashi".




Ummi tace " mun gode".


Sannan ya fita kusa dashi ummi ta zauna tana cewa "sannu habib ina ka ajiye maganinka yasira ta ɗauko ma kasha?".




A galabaice yace"yana bedroom ɗina cikin fridge".


Cikin sauri yasira taje ta ɗauko maganin sannan ta ɗauko masa ruwa yasha.


Yana sha ya sama bacci kallonsa ummi takeyi sosai tabbas yana matuƙar azabtuwa.


Wayar tace ta fara ringing ganin sunana Granny ya bayyana cikin,screen ɗin wayar yasa ta ɗauka tare da kara wayar a kunnenta.


Cike da girmamawa ta gaishe ta amsa tare da cewa" ya jikonki nawa?".


Ajiyan zuciya ummi ta saka kafin tace"Hajiya duk lafiya habib ne dai yanzu ciwon sa ya tashi amma yanzu alhamdulillahi harma ya sama bacci". Ummi ta faɗa tana kallon fuskar habib ɗin.


Salati Granny tasaka kafin tace,"ni daman tun farko banso wannan zuwan nasa da yayi ba,shine dai ya dage sai yazo auren bashir ɗinnan nafiso.Yayi zaman sa acan malesian a cigaba da duba lafiyarsa, yanzu ga irinta nima gobe zan taho katsinan".


UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam


________________________








Page 1⃣6⃣






Tun da Ummi ta sanarwa Daddy, ya taho Sayyid kuwa tunda Yasira ta faɗa masa halin da Hamman nasu yake ciki.




Yace shima zaizo amma Daddy yace "masa yayi zamansa,jikin nasa da sauƙi daman ciwo ne na lokaci guda kuma yanzu da sauƙi".


Nan yadage har sai da Daddy ya barshi nazo.
Granny kam fafur taƙi yadda da maganar da Daddy yake ce mata,na jikin nasa yayi sauƙi.
Sai datazo jikin Habib yayi sauƙi alhamdulillah,suna zaune akan dining sunayin break fast.
Daddy yayi gyaran murya sannan yace" Habib duk ganinka cikin jinya yasa mun mance bamu tambayeka abun daya tayar maka da ciwonka,wai meya faru ne?".


Ajiye spoon ɗin dake hannun sa habib yayi kana a sanyaye yace"Daddy ranan dana fitane naga hibba,da farko na zata gizo tamin kamar yanda kullum hakan take faruwa dani amma dana tambaye mutanen wajen,sai Ku shaida min dasuga lokacin datake barin wajen".




Ummi tace"hakan yana nufin tana cikin nan katsina kenan?".




"To ya kamata naje na sanar da ƴan sandan dana bawa aikin binciko ta,su binciko ko'ina domin tana cikin nan katsina"cewar Daddy.
"Amma Daddy ko photon ta fa bamu dashi taya kenan insun ganta zasu ganeta?".


Kurɓan tea ɗin dake gabansa Daddy yayi kafin yace"mama na munje wajensu da Habib, an ƙira Mai zane yana siffantar mishi ita shi kuma yana zana photon ta,to izuwa yanzu dai munada photon ta".




Ajiyan zuciya Granny ta sauƙe wacce daman tun zuwanta bata koma ba tare da faɗin" to Allah ya bayyana ta",dukkanin su suka amsa da amin.
Suna gama cin abincin Daddy ya biya ta station ya sanar dasu sannan ya wuce office.
Saura kwana uku auren Bashir Habib ya shirya tafiya damaturu,Tare da granny da kuma Yasira suka tafi.
Anyi wasu event kafin ɗaurin auren,ana ɗaura auren kuwa Granny tace Habib ya koma malesia.
Hakan nan ya koma sosai Daddy,Granny da Ummi suka masa faɗa akan yawan tinanin dayakeyi,har rubutu Granny tasa a dunga masa yana sha.
Daga can ya cigaba da kula da companies ɗinsu.




_____________________________




Nasha jinya sosai a asibiti tamkar bazanyi rai ba.
Wannan kuɗin da'aka haɗa mina masallaci dashi limamin masallacin ya cigaba da kulawa dani,dan nace musu "ni marainiya ce bansan kowa ba a garin".
A haka aka sallame ni daga asibitin sosai nayiwa liman godiya tare da matar dasuke ta dawainiya dani.


Sun tambaye daga nan ina zanje?,nace "musu zanje wajen dangina".


Fatan alkhairi suka min sannan na tafi,matarsa har da bani dubu biyu wai nasha ruwa a hanya.


Ina tafe ina tinani bansan inda zan nufa ba,bansan sanda hawaye yafara bin fuska naba.


Izuwa yanzu kam nasan na jazawa Anty Amina, bala'i da masifa a rayuwar aurenta watakil ma izuwa yanzu malam Habu ya sake ta.
Wani kuka mai ƙarfi ne ya kubce min WAYYO ALLAH.wai shin tunda muka rabu da Umma ta sake tinanin mu kuwa?.
Ban ankara ba naji mota ta kwashe ni,Wasu maza biyu ne,suka fito daga cikin suna min sannu.


Tare da tambayata"ko naji ciwo?"banji ciwo sosai ba kurjewa ne kawai,a hannuna da kuma ƙafata.
Asibiti muka wuce, akamin dressing wajen dana ɗan ji ciwon.
Ɗayan magidanci ne wanda nake kyautata zaton mahaifin saurayin,dasuke tare ne.
Sukaje zasu kaini gidansu na huta tukun sai sukaini gidanmu,a gate ɗin wani tankamemen gida motar ta tsaya.




Ya dannan horn gateman ya fito ya wangale musu gate motar tashiga.
Cikin parking lot tayi parking fitowa sukayi,nima nafito a hankali ina ƙarewa girman gidan kallo.


Wasu mata biyu na hango sun nufo inda muke tsaye.
Tace"alhaji wannan itace yarinyar da sayyid ke gaya min a waya,kun bige da mota?".




"Itace wallahi".




Ta kalloni cike da tausayawa tare da faɗin "Ayya sannun ko".


A hankali nace"yauwa sannu ina wuni".ta amsa tana cigaba da cewa "YASIRA Ki kaita tayi wanka,tayi salla sannan kikawo ta taci abinci".




Wacce aka kira da Yasira ta amsa da" to Ummi",sannan ta riƙo hannuna muka shiga cikin gidan.
Wani ɗaki muka shiga ta nunamin banɗaki nashiga nayi wanka,Sannan ta bani doguwar rigar material na saka nayi salla.




Sannan muka fito falo ta kawomin abinci naci.
Cikin jimami yYsira tace"yaya Sayyid a ina abin yafaru".Nan ya faɗa mata komai.


Mahaifinsu yace"baiwar Allah a wani unguwa kike mu kaiki gida?".
Kaina na sunkuyar ƙasa nace"ni ba ƴar garin nan bace".
"To inane garinku?".Ummi ta tambaya


Har yanzu kaina na kallon ƙasa nace"ni ƴar potiskum ce na jahar yobe".


Ummi ta kuma cewa" To a ina iyayenki suke?".


"Mahaifina ya rasu mahaifiyata kuma bama tare da ita".na faɗa ina danne ruwan hawayen dake shirin zubo min.


Cike da tausayawa Ummi ke faɗin" Allah sarki baiwar Allah ko sanar damu labarin ki bamu da niyyar cutar dake".
Haka kawai naji zuciyata ta gamsu dana sanar dasu labarin rayuwa ta a karo na farko,anan na sanar dasukomai akaina.


Tun Dana fara sanar dasu Ummi ke hawaye,Yasira kuwa kuka take sosai har da shashsheƙa.


"Innalil lahi wa'inna ilaihir raji'un", mahaifin nasu ya faɗa.


Sannan ya cigaba da cewa"baiwar Allah haƙiƙa labarin rayuwarki yana cike da darrusa masu yawa,amma kinyi kuskure dakika gujewa danginki domin ita mace a gurare uku ya kamata a sane ta gaban iyayenta,ko gidan mijinta inko ba'a same ta a ɗaya daga cikin waɗannan biyun ba to a same ta a kabari.zamu zauna dake tsakani da Allah
bamu da nufin cutar dake ni sunana ALH.SURAJ,ga mata HAJ.AISHA.Sannan ƴaƴanmu Sayyid da Yasira sai kuma yayansu yana malesia".






Ummi ta ɗaura da cewa"meye sunanki".


"Sunana Hibba".






Share hawayen fuskar ta Yasira tayi kafin tace "Ummi nima yanzu na sama ƴar-uwa,daman yaya Sayyid da Hamma sai suyi ta haɗemin kai".




Dariya sukayi kafin alh.suraj wanda naji suna ƙira da Daddy ya ɗora da cewa.


"Zamu zauna dake har izuwa lokacin da kike tinanin danginki,zasu haƙura akan maganar wannan auren da zasu miki sai mu maidaki garesu,ke kuma ki nema yafiyarsu na bujirewa umarninsu dakikayi,kuma in sha Allah za kicigaba da karatun ki".




Cikin zubda ƙwalla na matso na durƙusa a gabansa ina masa godiya.
Ummi tace"yasira ki kaita ki nuna mata ɗakin dazata zauna".




A hankali na Miƙe nabi bayan Yasira,ɗakin dake gefen nata muka shiga tace" Anty ga ɗakin ki sai ki duba inda abin da bai miki ba,sai ki faɗawa Daddy".
Murmushi na saka nace"ɗakin yamin".
"To masha Allah bari na barki ki huta".tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin.




Yasira ta girmeni sosai amma koda wasa bata taɓa kiran suna na kai tsaye ba,sai dai tace min Anty haka nan nima nake Kiran ta da anty.


Haka na cigaba da rayuwa,ƙarsashin kulawar alh.Suraj da iyalansa,babu tsangwama balle kyara.
Sosai na maida hankali na ga karatuna domin shine burin yaya Fawas ne a rayuwa zamantowa ɗan jarida,dan haka na jajurce naga na zamto ƴar jarida.




Nacigaba da karatuna a Alƙalam university lokacin kuwa Yasira ta gama.
Kullum cikin maganar Hamman su sukeyi amma nikam ko a photo ban taɓa ganinsa,sai dai naji lokuta da yawa suna cewa suna matuƙar kama da Yasira.
Sau da yawa insuna waya da Yasira takance min nazo mu gaisa,nace "kibarshi kawa Yasira wataran zamu haɗu".


Bazan taɓa manta wani safiyar ranar litinin ba.
Tun safe muka tashi da shirye-shiryen dawowar Hamman nasun, girki kuwa munyisa babu iyaka.


Ƙarfe biyu Daddy da Sayyid, sukaje airport domin ɗauko sa.
are da Yasira mukayi arranging dinning table ɗin sannan muka wuce ɗakina mukayi wanka.


Ina fitowa daga wankar nawuce gaban dressing mirror, nafara shafe jikina da Mai,sannan na Zara doguwar rigar atamfar da daddy ya mana anko nida Yasira.
Ina ɗaura ɗan kwalina Sayyid ya shigo ɗakin yana cewa"hey ladies Hamma has arrived."
Da gudu Yasira ta fice tabi bayan Sayyid.Ina gama ɗaura ɗan kwalina feshe jikina da turare,sannan na wuce kitchen na ɗauko fruit salad ɗin damuka haɗa.


Na ɗaura akan tray sannan na nufi falo bakina ɗauke da sallama,Ummi ce ta amsa sallamar sannan cikin farin,-cikin daya kasa buyiwa a saman fuskan ta tace"To Hibba yau dai ga ɗan nawa kingan shi nan".




UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


_____________________________


Page 1⃣7⃣




Ɗauko kaina nayi ina satar kallonsa yana zaune agefen yasira ya lumshe idanunsa,yayin da yasira keta gabza masa surutu.


A firgice na saki trayn dake hannuna ya faɗi ƙasa nan take ya tarwatse.


Sayyid yace" Hibba lafiya?".A hankali Habib ya buɗe idanunsa dan ganin meyake faruwa.
Lokaci daya muka haɗa ido a razane shima ya miƙe tsaye baki na rawa ya shiga faɗin "HIBBA".




Hawaye nabin fuskata yana wanke hodar dana shafa nace "Habib".
Miƙewa Ummi tayi daga inda take zaune tana cewa" Habib daman kasan Hibba ne?".
Wasu hawayen farin-ciki,ne suka fara zubowa daga idon habib yace"Ummi itace fa".
Sayyid cikin zaƙuwa yace"hamma itace Wa?".




"Hibbata Sayyid itace".
Cike da al'ajabi dukkaninsu suka kallo ni ummi kuwa da murna da mamaki ya gama,cika fuskar ta tace"Habib kana nufin Hibba itace yarinyar dakake so?,wacce kayi jinya a sanadin soyayyarta?".




" Ummi itace".




Rungumoni Ummi tayi tana jero godiya ga Allah"Alhamdulillah Allah yakawo mana,sauƙin jinyar Habib har gida".shi kawai take mai-maitawa.
Runguma Habib ɗin sayyid yayi,yana faɗin na tayaka murna hamma.
Kallo ya tsareni dashi yana sakin ajiyan zuciya,dafe ƙirjinsa yayi da sauri tare da runtse idonsa da ƙarfi.
Ummi ta ke duban sa tace" habib lafiya?".
Ƙara dafe ƙirjinsa yayi da ƙarfi yana cewa"Ummi zuciya na yamin nauyi".
Cike da nuna kulawa dukkaninsu suke,masa sannu zaunar dashi Sayyid yayi ya kwanta akan kujeran tare da ɗaura Kansa akan cinyar Ummi.
Yasira na zaune akasa kusa da kujerar dayake kwance akai ta riƙe hannunsa.
Sayyid kuwa yana zaune a gefen Ummi sai sannu suke jera masa,cike da kulawa Ummi take kallon sa tare da faɗin" Habib anya kana shan maganinka kuwa?".




Cikin sanyin voice ɗinsa,marar hayaniya yace"Ummi ina sha".
"To yanzu ina maganin?".


"Yana cikin akwatina".yabata amsa
Akwatin na gefena inda nake tsaye Ummi tace"na buɗe na ɗauko masa maganin".Na buɗe na ɗauko sannan na ɗauko masa ruwa.Na miƙawa Ummi dakanta ta bashi maganin yasha.Tashi yayi ya zauna tare da ɗaura Kansa akan,kafaɗun Ummi yana kallona yana sakin murmushi ƙasa-ƙasa.
Dai-dai lokacin da Daddy ya saƙo daga upstairs sanye da farar jallabiya,Dan tunda suka dauko Habib daga airport ya shige bedroom ɗinsa sai yanzu ya fito.
Tun kafin ya zauna,Yasira tace"Daddy I have a gist for you".




"To inajinki auta ta".


"Daddy Anty itace wacce Hamma yakeso ɗinnan".cewar Yasira wacce bakin ta ya kasa rufuwa tsabar farin-ciki.
Zaro idanu Daddy yayi yana cewa"hajiya wai maganan Dasira haka yake?".
"Kwarai kuwa", Ummi ta faɗa tana shafo kan habib ɗin dake kwance akan kafaɗar ta.Godiya Daddy ya farayiwa Allah, kafin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login