Showing 48001 words to 51000 words out of 104857 words
Chapter 17 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
yanzu ya kawo min ke kinaji ko?".Cikin muryana da fara dushashewa nace"naji Baffa ".
Sannan yace inbawa Habib ɗin wayar,Habib ɗinne yayi saurin faɗin"Baffa inajinka".
"Yanzu inaso ka kawo min ita,inkuma kana wani irin ka haɗota da driver suzo".
"Ba koma Baffa yanzu zan kawota in sha Allah"Habib ya faɗa yana kashe wayar.
Nikam runtse idanuna dani yayin danaji kaina ya sara mini da matuƙar ƙarfi,tunda naji yace Hajiya ce ta ƙirashi jiya ta sanar dashi nagane Granny yake nufi.Duk yanda naso haɗiye kukan dake zuwar mini kasa hakan nayi.
Yasira ce keta aikin lallashina tana bani haƙuri,lokacin muna dab da shiga cikin kano muna wudil Habib ya faka motar a gefen titi.
Lokaci guda ya feso iska daga bakinsa wanda har sai danaji titirin iskan a fuskana.Sai daya riƙo hannu na yana gyara zamansa yana fusko ni sosai har inajin bugun zuciyar sa yace"Hibba wannan kukan bashine mafita ba,inason ki matata kuma ina tabbatar miki zan tsaya miki a wani irin yanayi.Zan faɗawa Baffa wannan matsalar mun riga damun shawo kanta".ya ƙarishe maganar cikin son tabbatar mini da abinda ya faɗa ɗin.
Banda na yadda da maganganun Habib ba nayi shuru ina haɗiye kukan danake yi,sai daya miƙo min tissue na goge hawayen daya ɓatamin fuskana sannan ya tada motar muka fara tafiya.
Muna isa cikin gano muka wuce gidan Baffa sai daya dai-daita parking kusa da rumfar almajiran dake kusa da gidan sannan muka fito,Yasira ce gaba sannan Habib ni kuwa ina maƙale jikinsa muka nufa cikin gidan.
Duk suna tsakar gidan hadda Baffa,Inna ce ta amsa sallamar da muka shigo da ita,sannan muka zauna kan yalwataccen tabarman damuka gani shimfiɗe a wajen.
Inna muka gaisher ta amsa sannan muka gaida Baffa,fuskarsa kaɗai na kalla na fahimce yana cikin ƙololuwar ɓacin rai.
Shuru ne ya karaɗe wajen na wasu daƙiƙun da bazasu gaza goma ba kafin Baffa ya shiga faɗin"Hibba watau bakya ganin girman kowa ke ko?".saurin jijjiga kaina nayi alamar a'a sannan ya ɗaura da cewa"Naji duk abinda kike aikatawa kuma wai abun takaici baki da wani dalili,kuma kin tabbatar dacewa lafiya kalau kike wallahi inaso kisani bazan ɗauki rashin mutumci ba Hibba kibi mijinki ki sana aljannar ki sannan ki gyara mu'alamarki tsakaninki dashi".
Daga can ƙasan maƙoshina nace"in sha Allah Baffa "
Sannan Inna ta ɗaura da cewa"Hibbatu menene matsalarki?,mekika nema kika rasa daga wajen mijinki?,bakya tsoron ki shiga fushin ubangijinki?nidai nasihar dazan miki shine kiji tsoron Allah kisani akwai ranar da zaki tsaya a gabansa domin hukunci.In kuma wata matsalarce dake ki fito ki bayyana sai a nema miki magani".
Sai dana jawo gefen mayafina na goge hawayena kana nace"Inna banida matsala sannan banajin alamunta".
Hamdala Inna tashiga yi kafin ta cigaba damin nasiha tana gamawa Baffa ya farayiwa Habib godiya akan irin halin dattakun daya nuna bai yanke ɗanynen hukunci ba.
Anan zamu kwana domin Baffa yanema alfarmar haka daga Habib,shagon dake ƙofar gidan Baffa yasa almajirai suka sharewa Habib.Nikam tashi nayi na shige ɗakin Inna Yasira nabiye dani a baya tare da Inna.
Hajara kam datun shigowar mu batace ko hazal ba ta bimu da kallo yayin damuke shigewa ɗakin Inna ɗaya nabin ɗaya.
Wata dariya mai sauti ta saka yayin datake ƙoƙarin miƙe daga wajen ta fara haɗa wuta,tunda muka shiga ɗaki Inna ta tisani gaba tana ƙaramin wata nasihar tana ƙara nunamin halaccin kan.
Sai da aka ƙira sallan Asr sannan muka fito mukayi alwala mukayi sallah,ina zaune kan sallayar Inna ta shigo da kwaskon turaren wuta a hannunta agabana ta direshi tana cewa"Ɗauki turaren nan kikai ɗakin Habibun".
Miƙewa nayi na ɗauki kwaskon sannan na ɗauko maganinsa a cikin jakata na fito na nufi ɗakin nasa,daga waje na tsaya ina jera sallama ɗaya nabin ɗaya ganin ba a amsa ba yasa na tura ƙofar a hankali na zira ƙafafuna.
Rarraba idanu na shigayi ina nema ta ina zan ganoshi,ba kowa a ɗakin sai dana ƙarisa shigowa na ajiye kwaskon hannuna,sannan na fara bin ɗakin da kallo.
Ƴar katifa ce a ɗakin wanda Baffa yake sauƙan baƙi a cikin sa,sai kuma jakar kayan Habib ɗin wacce muka taho dashi daga gidan Granny.
Ina tsaye naji kamar za a buɗe ƙofar ɗakin nayi sauri gyara tsayiwa tana fuskar ƙofar domin ganin mai shigowar.murmushi ya sakar min yayin dayake baida ƙofar yana rufewa,nima murmushin na maida masa dashi.
Sannan ya ƙarisa shigowa ya riƙo hannuna muka zauna bakin katifar,maganinsa na ɓalla masa na miƙa masa ya karɓa sannan na ɗauko masa jakar ledar pure watern dana gani kusa da kwanon abincin da Inna taba Yasira ta kawo masa.
Sai dayasha maganin sannan nace"yanaga kamar bakaci abincin ba"na faɗa ina jawo kwanon samiran gabana buɗewa nayi naga ko taɓa shi baiyi ba.
"Kinsan banacin green ɗin abubuwa shiyasa banci ba,anjima zan shiga cikin gari wajen Sayyid zanci acan"ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushin daya kasa ɓoyiwa.
Tuwo ne miyar ayyahu abincin sai yanzu ma ninasan me aka dafa dan banci ba,tabbas nasan baya ta'ammali da ire-iren wanga kalolin abincin.
Sai dana maraice fuska kana nace"shine baka sanar dani na maka wani abincin ba".
"Bakomai karki damu banajin yunwar nema shiyasa kikaga hakan"ya faɗa yana lakuto kumatuna.
Daga nan ya fara wuce goma da iri,banyi ƙoƙarin hana shiba saboda alƙawarin dana ɗaukarwa kaina jiya.Haka nan shi kaɗai yake kiɗansa yake rawarsa.Da wani irin kunya na fito daga ɗakin na nufi cikin gidan wani kunyar ne ta ƙara zuwar min lokacin dana shigo naga Inna da Yasira zaune a tsakar gidan suna waya da Ummi.
Cikin sauri nakejan ƙafata na wuce cikin ɗakin Inna,Sannan na fito na ɗibi ruwa a bokatin ƙarfen dake yashe kusa da randa.
Na shiga wanka ina shiga na ajiye bokatin ina durƙushewa a wajen,toshe bakina nayi ina hana sautin kukana fitowa,duk cikin namana jinake kamar ana watsa mini tafashashshen narkarken ruwan dalma,yayin da fatana dukka ya ɗauki zogi.
Jinayi duk na tsani kaina yayin da haushin kaina ya ziyarce ni,amma sai dai ko kaɗan banyi nadamar hukuncin dana yanke ba.
Duk banida kuzari nayi wankan na fito na shige ɗaki,cikin tafiya ta dabata gama dai-daita ba.
Koda wasa ban leko ƙofar ɗakin ba koda Inna ta bani abinci inkawa Habib a Yasira nabawa ta kai masa,da wuri na kwanta yayin da baccin wahala ya fara fisgana figiga na tashi ji danayi wayata tahau ruri.
Jawo ta nayi ganin sunan Habib ne yasani ajiye ta gefe guda,ta cigaba da rurinta har ƙiran ya tsinke aka sake ƙira a karo na biyu.
Tisa wayar gaba nayi na haɗe dukka hannayena biyu saman ƙirjina ina kuka kamar wata ƙaramar yarinya.
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 3⃣3⃣
Sai danayi mai ishata kafin na kwanta inajin yadda raina kemin zafi,washe gari haka na yini duk jikin babu kuzari hakanan kuwa tun dana tashi banda wulgawar Anty Hajara ba,Inna naji tana faɗawa Baffa cewa taje gidan Barira ne.
Muna zaune a tsakar gidan munayin karin kumallo Habib ya shigo tare da Sayyid,tashi Yasira tayi ta karɓo ledar dake hannun Sayyid ɗin sannan suka ƙariso suka zauna.
Sai dasuka gaida Baffa da Inna sannan nidabYasira muka gaishe su,tashi Habib yayi yana saka takalminsa sau ciki yana cewa"Hibba ki sameni awaje".
Saurin dawowa nayi daga tinanin da kwakwalwata ta antaya,nabi bayansa da kallo har ya fice daga cikin gidan.Miƙewa Inna tayi ta zubowa Sayyid ɗanwaken ai kuwa kamar jira yakeyi ya naɗe hannun rigarsa yahau ci yana faɗin"Inna kamar kinsa kuwa na daɗe rabona dacin ɗanwake".
Washe baki Inna tayi sannan ta fara cewa"Ai kuwa duk lokacin dakake sha'awar ci,ka garzayo zan maka har sai kaci ka ture".
Sosai Sayyid ya saki dariya mai sauti yace"shiyasa nake ƙaunarki tsohuwar nan duk da kuwa kinƙi kabari".
Wata ƴar gajerar dariya ce ta suɓɓuce min wanda hakan yasa Inna ankara dani tace"A'a Hibbatu har yanzu baki tafi ƙiran da Habib yamiki ba?".
Yatsina fuskana nayi tare dacewa"Inna yanzu zan tashi".Ina kawowa nan na miƙe naje na ɗauka maganinsa sannan na fito na nufi ɗakin nasan.
Can ƙasan maƙoshina nayi sallama sai dana jira aka amsa sannan nasa kai na shiga,yana zaune saman sallaya na ganoshi yana waya da Ummi.
Nesa dashi kaɗan na zauna ina sauraron hiransu da Ummi,duk da ba komai dasuke faɗa nake tantancewa ba.
"Ummi ki kwantar da hankalinki wallahi komai ya wuce ba wata matsala yanzu,ko ita Hibban ma yanzu ta canja".Cewar Habib hakan danaji ya faɗa ya jefani cikin kokwanto akan wani magana sukeyi haka?.
Jin wayar danayi a kunnena yasa naɗan ɗago idanuna na kalleshi sannan nakuma maida dasu ƙasa,ina ƙara manna wayar a kunnena.Sallama nayi tun kafin ta amsa na ɗaura da gaishe ta ta amsa sai datayi jim kafin tace"Naji duk yanda kukayi da Granny kamar yanda in Yasira ce a matsayin dakike bazanji daɗi ace hakan ya faru a zaman aurenta ba,Haka nan ma ke Hibba ki gyara zaman aurenki duk wani mai ƙaunarki bazaiso ace daga auren wata uku har za'a kawo min kishiya ba.Saboda gazawarki.Ki dogara da Allah sannan ki dage da addu'a dakuma tsayiwar dare,zan kuma cigaba da sawa ana amso miki".
Cikin karayar murya nace"In sha Allah Ummi zanyi yanda kikace,nagode Allah ya ƙara ingantaccen lafiya da nisan kwana mai albarka".na ƙarishe maganar inakai dubana ga Habib wanda na lura hankalinsa nakan laptop ɗin dake gabansa.
Sallama mukayi da Ummi sannan na kashe wayar,na ɓalla masa maganin na miƙa masa.
Ba tare daya juyoba yace"yau dai kam kiyi haƙuri mana ki barni na huta,da shan kwayoyin nan"ya faɗa yana shagwabe fuska.
"Cab!kasan Allah kawai ka karɓa kasha ko kuma yanzu in fita waje na nemo mutane,su shigo su danneka na ɗure maka"na faɗa ina ɗan tsuke fuskata.
Dariya yakeyi sosai har yana riƙe ciki sai ya gaji dan kansa kana yace"Ashe kuwa akwai yaƙi,ɗure sai kace wani sabon yaro ɗan yaye".
Nace"ai kuwa kasha kawai shine samun zaman lafiya".
Karɓa yayi yasa abakinsa sannan na miƙa masa ruwa yabi bayansu dashi,tashi nayi zanfi yayi saurin riƙo hannuna yana cewa na zauna tunin idanuna suka kawo ruwar ƙwalla nayi saurin taresu kar ya gani.
Cikin muryata data soma rawa nace"Inna ce tace inzo da wuri zan rakata wani unguwa"ina kawowa nan nayi nasarar raba hannuna danawa na ɗauki hanyar fita daga ɗaki da ƴar sauri na,sai danazo dab da ƙofar ɗakin naji yana faɗin"inkin shiga ki sanar dasu yau zamu wuce".
"Uhmm"nace sannan na fice na nufi cikin gidan,Hajara na hango tana dawowa,muna haɗa ido da ita ta jefomini wani murmushi dana kasa gano manufar yinsa.
Sakeke na tsaya a wajen kamar wawiya,har ta raɓa ta gefena ta shiga cikin gidan.sannan nima na shiga nan inda na barsu Inna na dawo na tardasu.
Yasira tana yanka lemo da abarban dasu Sayyid suka kawo.
Sai dana zauna ina ɗaukar lemon dake dake kan fatanti a gaban Yasira nace"Hamma yace ki shirya anjima zamu wuce".
Tace"To".
Sannan muka cigaba da hirarmu ko lokacin dana shiga banga Hajara awajen ba,wanda nafi kyautata zaton ɗakinta tayi.yaya Fawas na ƙira mukasha hirar mu bayan shima yaƙara ja mini kunne akan na gyara zaman aurena.
Sai damukayi sallan zuhr sannan muka fara shirin tafiya bayan mun sama kyawawan addu'ar sauƙa lafiya,nace"Inna yaushe zaki zo min?".
Sai ta murmusa kan tace"Hibbatu sai kin haihu zanzo".
Dariya nasaka sosai nace"Innata kenan".sannan mukayi sallama muka tafi,har muka shiga mota Baffa bai daina gargaɗina akan kar na sake yaji na ƙarayi wani abu makamanci haka,inkuwa na kuma shida kansa zaisa Habib ɗin ya sakeni,nazo gidan naci uwar abinda zanci.
Da haka dai muka tafi bayan na gama ɗaukar huɗubar Inna da Baffa,sai da muka sauƙe Sayyid a makarantarsu sannan muka wuce.
Muna isa cikin katsina muka wuce gidan Ummi,Habib kam ko shigowa baiyi ba ya wuce office a cewarsa wai yayi baƙi suna jiransa.
Ummi muka samu zaune a falo tana sauraron tafsirin da malam Jabir sani mai hula yakeyi a tashar Albani TV.da sallama muka shigo Yasira najan akwatin kayan mu,da farin-cikin daya kasa ɓoyiwa a saman fuskarta ta miƙe tana amsa sallamar damuka shigo da ita.
Sai da muka zauna sannan muka gaisheta ta amsa tana tambayar mu Granny da kuma su Baffa,muka amsa da lafiya duk suna gaisheki.Nan muka cigaba da hirarmu bayan ta tambaye mu ina Habib.
Yasira ce tabata amsa dacewa"Ya wuce office wai ana jiransa".
Hira mukayi sosai Ummi tana ƙara kwantar min da hankali akan maganar auren Yasira da Habib da Granny da Daddy suka ƙudurce yin hakan.
"Wallahi Ummi nifa har yanzu ban ɗauki maganar da gaske ba,gaskiya bazan iya zuwa gidan Hamma a matsayin kishiyar Anty Hibba"cewar Yasira ta faɗa tana ɗan tsuke fuskarta.
Daga ni har Ummi dariya muka ɓarke sai damukayi mai isharmu kafin nace"Haba!ke kuwa Hamman nakine zakice bakyason sa komeye?".na ƙarishe maganar cikin yanayin zolaya ina haɗa mata gira ɗaya.
Pillown kujerar dake kusa da ita ta jefo min tana faɗin"wallahi Anty bazan iya ba".tashi nayi ina dariya ina cigaba da cewa"Amaryar Hamma Amaryar Hamma".
Nan muka fara zagaye falon tana bina da pillow a hannunta.
Ummi da dariyar datake yaƙi barinta ta sarara,sai data tsagaita dariyar kana tace"Allah ya shiryamini ku"tana kawowa nan ta miƙe ta shige ɗakinta.
Haka muka yita zagaye falon muna cikin haka mukaji ƙaran shigowar motar Habib,fitowa mukayi dai-dai lokacin da Habib ɗin yake fitowa daga cikin motar a guje muka nufe shi saurin ɓoyewa a bayansa nayi ina maida numfashi.
Sai daya dawo dani ta gabansa kana yashiga tambayarmu meke faruwa?Yasira ce tayi saurin bashi amsa tana cewa"Hamma cemin take fa wai Amaryarka".ta ƙarishe maganar tana jefo mini pillown hannunta.
Shima dariyar ya saka tare da faɗin"Lalle dole ta fuskanci hukunci tunda tasamini ƙanwa hawaye".
Ya faɗa yana ƙara haɗani da jikinsa muka ƙarisa shiga cikin gidan,sai gwalo nake yiwa Yasira wacce take sharar ƙwalla.
Nida Yasira kitchen muka wuce shikuwa Hamma ya wuce ɗakin Ummi,abincin dare muka haɗa sannan muka jeresu hakan yayi dai-dai da ƙiran sallan magriba da aka farayi.
Sai damukayi sallan isha'i sannan muka dawo falo muka zauna,har izuwa lokacin da Habib da Daddy suka dawo abinci mukaci sannan muka fara shirin tafiya,bayan Daddy yaƙara mana nasiha sosai.
Yasira kam anan muka barta muka dawo,tun daga wannan rana nasakewa Habib jikina duk da yanda nakejin raina yana tafasa kamar rumon farfesu.
Ranan na tashi da matuƙar ciwon kai dana jiki,ta yadda naji bana ƙaunar fito rana ko makaranta banje ba haka nan girki ma banyi ba dan Habib bazai dawo cin abincin rana ba.
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
______________________________________
Page 3⃣4⃣
Dakƴar nake ɗaga hannuna saboda kasalar data sauka min,a dukkan jikina jan jikina nayi zan tashi jirin dake ɗibata ta dawo dani ta warɓa akan gadon.Ƙara yunƙuruwa nayi na tashi ina riƙe da gefen ƙuduna nayi toilet haka nan naji bazan iya alwalar da ruwan sanyi ba,hakan yasa na fito na jona heater sai daya tafasa sannan nacire na koma banɗakin.
Alwalar nayi na fito inajin zazzaɓin dayake saɗɗata,na shimfiɗa sallaya na tada salla koda na iddar tashi nayi na nufi sashin Hajja.
Tana shara na sameta ganina datayi yasata sakin tsintsiyar tana cewa"Hajiya kece a sashin namu bari to na ɗauko miki shimfiɗa".
Ƙarisa shigowa nayi dai-dai lokacin data ɗauko mini tabamar ta shimfiɗa,na haye kai na zauna ina haɗe ƙafafuna wuri guda nace"Hajja aiki kita yine?"na faɗa ina kai kallona da tulin wanke-wanke take jibge a tsakar gidan.
"E wallahi yau ma tashi sam banajin daɗin jikinane kisan jiki da jini".
Na kuma cewa"Wallahi Hajja nima nagaji da zaman kaɗaicin ne nace bari na fito kinsan Yasira ta tafi".
Tashi Hajja tayi ta zubo mini kunnu a babban kofin jug ta direshi gabana,yanda nakejin yanayin jikina yau banaji sha'awar cin komai kai hannuna nayi na taɓa jikin kofin naji shi zafi gau.
Hakan ya tabbatar mini da bata daɗe da sauke shi daga kan wuta ba,ita ta zuba mini kunnun nakai bakina a hankali sanda naji daɗin kunnun ya mamaye ilahirin duk wani kusurwa na bakina.
Yasa na lumshe idona sannan na ware su ina tanɗe leɓena na ƙasa nace"Hajja wannan wani irin kunnu ne?".
Sai data murmusa kafin tace "Kunun aduwa ne".
Kaina na ɗaga inajin daɗin kunun na tsiga mini duk dabasa sugari a cikinsa amma ba kaɗan ba yamini daɗi.
Tashi tayi ta cigaba da shararta yayin da nikuma na zuƙe kununnan tas!sannan na tashi na haɗa wanke-wanken na fara mata.
Nan wajen Hajja na wuni har sai danaji ƙarar shigowar motar Habib sannan na tafi,yana ƙoƙarin fitowa daga cikin motar sanda na iso cikin parking alot ɗin rungumoni jikinsa yayi muka ƙarisa cikin gidan.
Adaddafe na haɗa mana dinner muna gama ci nabi lafiyar gado dan duk wata gaɓa a jikina jinta nake ta sake tsabar gajiyan danayi.
Haka kullum ya shigaba da faruwa dani kasala da rashin son cin abinci dan komai naji sai na amayar dashi,kunnun aduwan da Hajja kemini ne kawai yake iya shiga cikina ya zauna ba tare dana amar dashi ba.
Duk yanda Habib yaso muje asibiti ƙi nayi nace masa ciwo ne na lokaci guda kuma zai daina,yace ko yayiwa Ummi magana Yasira tazo?nace masa A'a.
Ranar tun da Habib ya fita sallan asuba naketa kwara amai a cikin toilet sosai na galabaita,haka ya dawo ya iskeni bayan ya taimaka mini na wanke fuskana muka dawo ɗakin lamau na kwanta a jikinsa ina fidda numfashi ɗai-ɗaiya.
"Hibba ki tashi mu tafi asibiti "bance dashi komai ba na tashi na fara shirya jikina muka fito muna nufa asibiti,koda mukaje bayan nagama zayyanawa likitan ababen dake damuna scanning ya tora ni.
Muna zaune a ofishinsa muna jiran a kawo result ɗin,wata nurse ce ta turo ƙofar ta shigo bayan ta ɗan rusuna ta gaida likitan ta miƙa masa takardan dake hannunta sannan ta fice.
Lalumar gilashinsa likitan yayi ya maƙala a idonasa,sannan ya shiga duba result ɗin zare gilashin ya shigayi a lokaci guda koma yana ƙara yalwata fara'ar dake shimfiɗe akan faffaɗan fuskarsa wacce girma ya fara bayyana akanta,sai daya miƙowa Habib hannu sukayi musabaha sannan yace"congratulation abokina madam tana da juna biyu na tsawon satikai shidda".
A hankali na zare hannuna daga toshe hancina danayi saboda ƙarfin turaren dake ofishin na nema uzura mini,Habib miƙewa yayi nan yayi sujudul shukur yana mai jaddada godiya da ubangijin talikai.
Nikam kunyace taso rufeni dana lura irin kallon da Habib ɗin ke aiko min dashi,tsam!na miƙe na fice daga ofishin ina ta mai-maita kalmar "Alhamdulillah"a cikin zuciyana.
Inajin Habib yana tambayar likitan shawarwa akan yanda za'a kula da cikin,sanda nake ficewa daga cikin ofishin inda mukayi parking na nufa na shiga cikin motar iska mai