Showing 33001 words to 36000 words out of 104857 words
Chapter 12 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
baffa ya shiga faɗin.
"Hibba dan girman Allah da manzonsa in an kaiki ɗakin ki kiyiwa mijin ki biyayya sau da ƙafa,ki riƙe dangin mijinki tamkar ƴan-uwa".
Sosai Baffa kemin nasiha kafin yaya fawas ma ya ɗaura da nashi.
Saida suka kammala sannan baffa ya ɗauko wata alkebba,ya lulluɓa min wanda ta sauƙa min har ƙasa.
Ta da ce alkebba dan hatta ɗinkin ta na hannu ne da mata keyi a wancan lokacin,gyara min zaman alkebban inna tayi.Tana rufe min fuska na dashi sannan ta riƙo hannu na muka fito waje.
Tunin motocin ɗaukar amarya sun hallara,sallama mukayi da irarun ƴan-uwan inna da sukazo sannan muka fito waje hannu na damƙe cikin na yaya fawas.
Da Inna da hajara da kuma wata ƴar ƙanwar inna(shatu),dasu zamu tafi sai kuma yasira.Motar dake tsakiya yaya fawas yasaka ni ƙara damƙe hannunsa nayi yayin da ranar da umma ta rabamu ya dawo min cikin ƙwaƙwalwa ta.
A hankali ya zame hannun shi daga cikin nawa,sai daya sakar min taƙaitaccen murmushi sannan yace"Allah ya bada zaman lafiya ƙanwata".
A Zuciya na amsa sannan ya rufo mufin ƙofar,ta ɗayar ƙofar yasira ta shigo yayin da su inna suka shiga sauran motar.
Muna shiga cikin katsina gidan ummi muka fara zuwa har yanzu kaina na lulluɓe da alkebba,Inna na riƙe dani muka shigo falon ummi wanda yake cike da mutane maƙil.
A ƙasa na zauna yayin da ƴan-uwan mahaifiyar habib mutan ƙasar niger suka shiga feshe ni da turare.
Ummi kuwa tsabar murna ma ta kasa zaune ta kasa tsaye,da an tambaya amaryar habin zatace"gata nan ƴar albarka".
Muna cikin haka habib ya shigo ya sauya shiga izuwa wata farar yadi,Wacce aka iyawa aikin surfani izuwa yanzu kam na lura da cewa yana matuƙar son aikin surfanin.
Ƴan-uwan mahaifiyar sane suka fara tasowa,yayin da wata tsohuwa daga cikin su ta ta kamo hannun sa har izuwa inda nake zaune.
Tafukan hannunsa ta buɗe ta fesa masa turaren sannan ta umarce shi daya haɗa hannunsa da nawa,hakan yayi kafin ya miƙe ya fara min karin ƴan dubu-dubu ina daga zaune.
Tunin gidan ya ɗauki shewa sai fatan zaman lafiya kowa ke mana,sannan aka wuce dani part ɗin habin ɗin su kuwa su inna nan part ɗin ummi sukayi zaman su.
Tun ina sa tsammanin zuwarsu inna part ɗin har na daina,dan a zato na a nan zamu kwana tare dasu.
Wata munguwar gajiya ce ta sauƙar min,da azababben ciwon kan daya sauƙa min lokaci guda sakamakon kukan danayi.
Tashi nayi na faɗa bathroom nayo alwala sannan na fito kayan,akwatin na buɗe na ɗauka hijab nayi salla sannan na koma kan gadon na zauna.
Ina zama suka turo ƙofar,a firgice ta gyara zaman danayi ina ƙara lulluɓe fuska ta da alkebban dake jiki na.
Tare da sayyi da kuma Dr bashir suke sai kuma wani abokinsu ɗaya,zama sukayi kafin Dr bashir yace.
"Amarsu ta ango to a buɗe mana fuskan mana".
Ƙara sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina sakin murmushi muryar habib datayi wa kunnuwa na dirar mikiya ne ya sanya murmushin,danakeyi gushewa yayin danaji zuciya ta tamin wani irin zafi.
"A'a malamai ban fa gane wai ta buɗe muku fuskaba,kuyi abun zakuyi ku tafi"Habib ya faɗa yana ware idonsa akan Dr Bashir.
Dariya dukkaninsu suka yi kafin sayyid yace"Shikenan Hamma zamu tafi tunda daman kowa a gidansa sarki mu kaga tafiyarmu,bazaka ƙara ganin mu ba sai ka neme mu".
"Kyale shi sayyid Yau ai ranar sace"cewar ɗayan abokin nasu ya faɗa yana ajiye ledar dake hannunsa akan site drawer.
Murmushi Habib ya saka sannan ya shiga faɗin"E dai kuyi tafiyar ku,mun gode".
Miƙewa sukayi kusan a tare suna faɗin"To amarya mun bari ki lafiya".
Tashi habib ɗin yayi ya rakasu tamkar na fasa ihu kozan sama rangwamen irin raɗaɗin da zuciya takemin,haka naji hawaye suka fara gosilo a saman kunci wanda nima bansan dalilinsu ba.
A hankali naji ana yaye alkebban dana rufe fuska ta da ita.
Ƙara sunkuyar da kaina ƙasa nayi yayin da yashi kuma ya zauna a bakin gadon,da ido ya tsare ni har sai na fara tsarguwa da kaina.
"Ya isa haka kukan nan fatima ki daina kinji,yanzu ki tashi ki wanke fuskar ki kizo muyi salla mu nunawa Allah godiyar mu a gare shi,daya nuna mana wannan rana a cikin rayuwar mu".
Maimakon na taƙaita kukan saima tsanan tashi danayi.
"Hibba Ya isa nace miki,ki daina kukan nan kodan lafiyar ki"ya faɗa cike da kulawa.
Sai daya tsazaita sannan ya cigaba da cewa"Baki da lafiya ne?,Meyake damun ki?".
Ya faɗa yana ɗaura hannun sa a saman goshi na,sosai jiki na ya ɗau zafi rau.
Sosai yake jera min tambayoyi ɗaya nabin ɗaya na cewa Meyake damu na?.
Ganin irin yanayin daya shiga,sosai naji tausayin sa mussamman da na tino irin cutar da yake ɗauke da ita ta raunin zuciya.
A hankali nake furta"Habib mahaifiya ta na tino yau har anyi bikina amma babu ita cikin mahalalta wajen aure na,Ina kewa ta inason na ganta koda daga nisa ne inason jin muryar ta inason mu zauna da ita muyi magana da ita irin ta ƴa da uwa".
Duk da a wannan lokacin tinanin umma ba shi yafi sanya ni cikin damuwa ba,domin tsanar habib dayake girmama a cikin zuciya ce a wannan lokacin shine babban damuwa ta.
Amma na ɗaukarwa kaina alƙawarin cewa zan bar abin a raina ba tare dana sanar da kowa ba,koda kuwa hakan zai zamto silar salwantar rayuwa ta.
Sai daya sauƙe ajiyan zuciya sannan ya matso kusa da inda nake zaune,hannu na ya riƙo ya sa cikin nasa.
Wasu hawaye masu zafi naji suna rige-rigen fitowa daga ido na,hannu na daya riƙe jinayi tamkar ya watsa min garwashin wuta.
"Fatima ki miƙa dukkan lamuran ki izuwa ga Allah domin kuwa shine sarkin da baya kuskure a cikin lamuran sa,Ki godewa Allah ke kin taso kinsan wacece mahaifiyar ki,kin rayu da ita na tsawon lokaci domin baiwa ce ga duk wanda ya rayu tare da iyayensa biyu uwa da uba".
Sai da yayi shuru na wasu daƙiƙu,Hawayen dasuka ciko masa idanu ya tare su da hannayen saSannan ya ɗaura da faɗin.
"Ni ban taso tare da iyaye naba,na rasa su tun inada ƙarancin shekaru na rasa su a lokacin danake da tsananin buƙatar su,rashin iyaye ciwo ne da raɗaɗinsa baya misaltuwa haka nan kalaman baki sunyi kaɗan wajen furta su.Kiyiwa Umma kyakykyawan zato sannan ki dage da Addu'a komai zai dai-daita da izinin Allah yanzu ki tashi kiyi Alwala muyi sallah".
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
Page 2⃣3⃣
Duk da yanda zuciya ta take min soya,ɗaurewa nayi na tashi yayin daya riƙoni har izuwa ƙofar bathroom ɗin dake cikin ɗaki.
Tare muka shiga mukayi alwala,sannan muka fito Salla muka gabatar raka'a biyu sannan muka shiga kirari ga mahaliccin mu kafin muka fara Addu'a.
Nikam ta bangare na addu'a nakeyi Allah ya kawo min ɗauki da sauƙi a cikin damuwar dake damun zuciya ta,Ina tsoron ranan da Allah zai kamani da haƙƙin habib na aure dana tauye,Domin izuwa yanzu tsanar shi na rinjayar soyayyar da zuciya ke masa.
Shikam ta bangare sa sosai yake mai ƙasƙantar dakai ga mahaliccin sa, yana roƙon ubangiji daya bashi damar zamantowa alkhairi ga rayuwar hibba sannan ya dawo mata da farin-cikin data rasa a cikin rayuwar ta.
Muna iddar da sallan ya jiyo inda nake,kaina ya dafa sannan ya shiga min addu'a.
Abincin da ummi ta sa a kawo mana da kyar naci abincin cokali uku nayi, shima kasa ci yayi sai tambayar da na lura baya gajiya dayin ta.
Na tambaya ta lafiya ta nace kaina ke min ciwo,kasa cin abincin yayi yasani gaba yana min sannu.
Alama yamin da hannunsa akan na matso kusa dashi,ba musu na matso jawo ni jikinsa yayi.
Runtse idona nayi da ƙarfi sannan na jawo ɗan kwali na na toshe bakina dashi,saboda kukan danaji yana ƙoƙarin kubce min.
Duk cikin naman jiki na ji nake tamkar yana watsa min tafashashshen ruwan zafi,Haka na ɗaure tare da ƙara runtse idanu na.
Ina sakin ajiyan zuciya akai-akai ganin haka ya sa habib tinanin cewa nayi bacci,zame jikinsa yayi sannan ya gyara min kwanciya ta,ya ɗauko blanket ya lulluɓa min anan wajen.
Baiyi niyyar tashi na na hau gado ba,dan yanda jikina ya ɗau zafi sosai ya zata zazzaɓi ke damu na kuma da kyar na samu bacci.
Sai daya min Addu'a ya shafa min,kafin ya tashi ya shiga bathroom alwala ya ɗauro sannan ya fara gabatar da nafilfili.
Washe gari da matuƙar ciwon kai da kuma zazzaɓin daya sauƙa a jikina tun dare jiya na tashi,magani nasha kodan damuwar da habib ya shiga a dalilin hakan ya sani daurewa na nuna mishi naji sauƙi
Duk da inajin kwana ɗaya danayi a cijin gidan habib matsayin matar sa,duk na nema nutsuwa ta na rasa amma zan zamto masa mace ta kwarai.
Da taimakon sa na shirya cikin shigar laffaya,sannan muka shiga part ɗin ummi.
Ƴan-uwan mahaifiyar dasukazo muka fara gaishewa wata daga cikinsu ne ta shiga faɗin.
"Oh duniya!Allah ya jiƙan zainaba yau ake bikin ɗanta amma bata duniyar rayuwa kenan".
Da Amin dukkaninsu suka amsa dashi,lokaci guda na lura da yanayin habib daya sauya.
Ɗakin da aka bawa su inna muka wuce muka gaishe su sosai inna ta ƙarayi masa nasiha.
Sannan muka wuce part ɗin ummi ita nasihar ta ke mana sosai masu ratsa jiki da ƙwaƙwalwa.
Ɗakin granny muka wuce sosai fuskar ta ke bayyanar da farin-cikin dake ƙasan zuciyar ta na ganin mu tare da tayi,Anan mukaci abinci sannan muka zauna tare da ita dakuma yasira data shigo yanzu.
Da kuma matar Dr bashir maryam daman tare suka zo da ita,sosai muke shan hirar mu kamar dama can munsan juna
Nan granny take sanar dani cewa ta faɗawa su Inna ma,da yamma za'a wuce dani gidan habib bazamu zauna anan ba dan dama ya gama gininsa.
Da yamma kuwa da kanta ummi ta shirya ni cikin,shigar laffaya mai tsantsi da granny ta bani.
Falon Daddy muka taro dukkanmu nasiha shima yayi mana,sosai tare da sanya mana albarka da fatan Allah ya bamu zaman lafiya.
Granny da Inna dasu muka tafi gidan dake cikin unguwar Dutsen safa low-cost behind M&M pharmacy a nan cikin katsina ta dikko.
Gidan babba ne sosai dan har yaso yakai na su ummi girma,part biyu ne dasuke kallon juna sai kuma wani ɗaya daga gefe wanda bai kai sauran girma ba.
Ciki muka shiga har cikin ɗaki su granny,suka kaini sosai ɗakin ya ƙawatu da furniture masu launin ruwan toka.
Muna zama habib ya shigo sanye yake cikin shigar manyan kaya kamar kullum,shadda ce fara sol wacce aka ƙawata ɗinkin da ado na zaren golding.
A wuya da kuma hannun rigar,Inna ce ta amsa sallamar daya shigo da ita sannan ya ƙariso ya zauna akan ɗaya daga cikin sofan dake ɗakin.
"Ga matar ka nan babban mutum amana ce da iyayenta suka duba kamala da kuma cancantar ka,suka ɗauke ta suka baka Idan kaci wannan amanar kasani kai da Allah kuma yana kallon ka ko mu ka ɓoye mana".
Sai daya gyara zaman sa kafin ya shiga faɗin.
"In sha Allah baza kuji wani abu marar daɗi ba tsakanin mu da yardan Allah".
"Haka muke fata"cewar inna.
Miƙewa sukayi dasu tafi nan inna take sanar dani gobe suma zasu koma gano.
Sallama mukayi dasu sannan na musu fatan sauƙa lafiya habib ya raka su.
Suna fita na sauƙe kuka mai ƙarfisosai zuciya ta take min suya,kamar na tashi nabi su haka nakeji dan bazan iya zaman gidan ba.
Banji shigowar saba sai jin sauƙar numfashin sa nayi dab dani.
"Ya isa haka Fatima tabbas nasan rabuwa da ƴan-uwa sai dole,amma duk wata ƴa mace da kika gani a cikin gidan aure ta fuskanci rana irin wannan ki daina kukan nan banaso kinji?".
Kaina kawai na gyaɗa masa alamar naji,sosai yake amfani da duk wata kalamar dayasan zai kwantar min da hankali cikin furcinsa.
Ƙiran sallan magrib ya tilasta mishi fita masallaci,nima tashi nayi nayo alwala sannan nayi salla.
Sosai nake tausayin kaina da kuma irin rayuwar da zanyi cikin gidan habib.
Ina zaune akan sallayar aka ƙira isha'i sai danayi sannan na ɗauko qur'ani na fara karantawa ko zanji sanyi cikin raina.
Ina zaune wajen habib ya dawo zama yayi kusa dani,sannan ya jawoni jikinsa muka cigaba da karatun tare.
Sai wajajen ƙarfe goma sannan muka ajiye qur'anin abincin da su granny suka taho mana dashi mukaci sannan muka fara shirin kwanciya.
Ina zaune akan gado na lulluɓe ƙafata da blanket ya fito daga toilet shiryawa yayi cikin kayan bacci,3quarter ce tsayinta dai-dai gwiwarsa da t-shirt marar nauyi.
Yaune karo na farko dana fara ganinsa,da ƙananan kaya sosai kuwa kayan suka amshe shi.
Akan site drawer ya zauna yana fuskanto ni yace.
"Ki kwanta ki huta nasan kin gaji ko gimbiya ta?".
Murmushi nasaka tare da gyaɗa kaina,addu'a yamin ya shafa min sannan na lulluɓa min blanket ɗin.
"Sai da safe fatan nishaɗantaccen bacci".ya faɗa yana kashe wutar ɗakin.
"Allah ya kaimu"
"Amin"ya faɗa yana ficewa daga ɗakin.
Da kallo nabi bayan shi dashi yayin dayake ficewa sannan na sauƙe ajiyan zuciya.
Sosai raina yamin daɗi danaga zai kwana a ɗakin sa,dama tun ɗazu fargaban danakeyi kenan dan bazan iya haɗa shimfiɗa dashi ba.
Washe gari da wuri na tashi na haɗa breakfast sannan nayi wanka,ina tsaye a gaban mirro ina ɗaura ɗan kwalli ya shigo.
Ta cikin madubin da hango shi yana tsaye bakin ƙofar ɗakin ya naɗe hannayen sa a ƙirjinsa.
Juyowa nayi tare da gaishe shi ya amsa yana ƙarisowa inda nake tsaye,riƙo hannu na yayi muka wuce dinning.
Da mamaki shimfiɗe kan fuskarsa yake tambaya na yaushe na tashi na haɗa wannan breakfast ɗin?.
Murmushi kawai nasaka na cigaba da zuba mana abincin,wani lokacin inyana magana na tankamasa ma yakan zama min mayuwacin abu.
Jallof ɗin taliya ne sai dai bansa vegetable sosai ba,kasancewar nasan habib ɗin baya ta'ammalin da duk wani abu green kamar alayyahu da dai-dai makamantarsu saboda lafiyar zuciyar sa.
Sosai mukaci abincin suna ci muna hira cikin nishaɗi.
Ummi ce ta ƙirashi ya ɗauka ladabtar da murya yayi ya gaida ta, ta amsa sannan tace ya bani wayar.
Sai dana gaishe ta ta amsa tare da tambaya ta ya kwanan baƙunta nace.
"Alhamdulilla"
Na faɗa ina ɗagawa habib ido ɗaya irin abun nan dake nuna dako lafiya? Sakamakon kallon danaga ya tsare ni dashi.
Wanda izuwa yanzu na fara karantar hakan na daga cikin ɗabi'arsa,muryar ummi ce ta katse min hanzari.
"Anjima yasira zata kawo min kayan da dangin mahaifiyar habib suka miki".
"To Allah ya kawo ta daman inada faɗa da ita".
Sallama mukayi sannan na miƙawa masa wayar shima ɗin sallamar sukayi.
Muna gamacin abinci ya miƙe tare da faɗin"Akwai wasu abokaina dasukazo a hotel suka sauƙa so innaso naje wajen su kafin su wuce".
Kamar banji saba nayi na miƙe ina tattare kwanonka,izuwa yanzu kam na fara tsorita da irin tsanar da zuciya ta kewa habib ko muryarsa banason ji balle kuma na ganshi kusa da ni.
Riƙo hannu na nayi tare da tsaida idanunsa cikin nawa.
"I'm sorry Tawan wallahi daga nisa sukazo ne shiyasa zanje muyi sallama kafin su tafi,badan haka ba inna tabbatar miki babu abinda zaisa in fita a irin wannan ranar".
"La!ba komai hamma habib na fahimta"na faɗa ina kashi masa ido ɗaya cikin sigar zolaya nayi maganar sannan na raba hannu na dan nasa.
Gwalo idanu waje yayi kafin yace"waye hamman nakin?".
"Kai mana"
Sai daya murmusa kafin yace"zan dawo ai zamu gamu".
Sosai na saki dariya sannan ya fita key ɗin motar dake ajiye akan dinning ɗin na ɗauka nabi bayan sa.
Har jikin motar na rakashi tare dayi masa kyawawan,addu'ar sauƙa lafiya sannan yaja motar ya tafi.
Sai da naga ficewar motarsa daga gidan sannan na sauƙe wata zaffafar ajiyar zuciya,yayin da wani nishaɗi ya sauƙa min lokaci guda ciki na dawo.
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________
Page 2⃣4⃣
A falo na tsaya ina ƙarewa falon kallon,furnitures set biyu ne a ciki da masu launin shuɗi da kuma golding.
Sai makeken Tv plasma dake manne cikin wall ɗin falon.
Lokaci guda idanu na suka sauƙa akan hotunan mu na bikin dake ajiye gefen Tvn sai kuma wasu da aka kafesu a cikin wall.
Matsowa nayi ina bin hotuna da kallo wasun ma bansan lokacin da aka ɗauke su ba.
Waya ta data fara ringing ne,tasani barin cikin falon na wuce dinning.
A hankali na ɗaga kiran tare da kara wayar a kunne na daga ɗayan bangaren habib yace.
"I forget to tell you i love you,shine na ƙira na faɗa miki".
Wasu zuffa ne suka keto min lokacin guda bakina na mungun rawa nace"me too"na faɗa ina dai-dai nutsuwa ta.
Sosai nakejin sautin dariyarsa kafin yace"ki kula min da kanki kinji".
"Uhmm kaima haka".
Ban jira amsar dazai bani ba na kashe wayar,dawowa falon nayi na kwanta akan ɗaya daya cikin kujerun ina lumshe ido na.
Bansan sanda na fara hawaye ba sai jin ɗuminsu nayi sunabin kunci na,Arazane na tashi jin ana bubuga hannun kujerar danake kwance akai.
Ganin Yasira yasa na watsa mata harara ina ƙoƙoarin tashi na zauna tare da share hawayen dake fuskana.
"Anty lafiya kike hawaye,ina shi hamma Habib ɗin?".
Yasira ta faɗa tana bina da wani kallon tuhuma.Ban kulata na fara gaishe da mata biyu da sukazo tare wanda suke ƴan-uwan mahaifiyar Habib,amsawa sukayi suma suna ƙara tambaya ta dalilin hawaye dasu gani a fuska na.
"Ba komai wallahi,wani abu ne ya shigar min cikin ido"na faɗa ina miƙewa domin ɗauko musu abin sha.
Yasira kam nomban Habib ɗin,tashiga dialing ringing biyu kuwa ya ɗauko.
Nan ta sanar dashi halin dasuka zo suka same ni,da mamakin ta sai taji ya saki dariya sannan yace.
"Wai ba dan na fita ne wajen wasu abokaina da sukazo daga malesia yau zasu koma shine nakega dalilin wannan kukan".
Murmushi ta saka kafin tace"Au hamma kace kukan daɗi take?".
Shima murmushin ya maido mata dashi sannan sukayi sallama,ina shigowa falon hannu na ɗauke da tray.
Kallo ni tayi yayin da take maida wayar cikin jakar ta tace.
"Anty lalle hamma na shagwaɓa ki da yawa dan ya fita shine kike kuka".
Sai da na galla mata harara sannan nace"Anyi ɗin"na faɗa ina juya idanu na.
Anan suka wuni yasira take sanar dani su inna tun asubar fari suka tafi.
Sai yamma sosai sannan suka tafi,bayan na musu rakiya sannan na dawo falon ina duba kayan dasu zo min dashi.
Zannuwa ne da kwaraye wanda aka ƙawatasu da launuka,da zane masu ɗaukar hankali irin dai na ƴan mutan niger.
Sai kuma kwaskon turaren wuta,suma sun ƙawatu da zanuka da kuma turaren wutan.
Sosai kayan suka burgeni duk da ba wani yawa gare su ba,amma naji daɗin wannan kyautar tasu gare ni.
Ƙaran shigowar motar habib danaji ne ya kawar