Showing 72001 words to 75000 words out of 104857 words
Chapter 25 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
kuma ƴan biyun kawu Isma'il Nabiha da Nabila su suka kawo mu ɗakin,sannan suka juyo nidai wanka na faɗa nabar Yasira tana latsa waya.
Acan falo kuwa Habib da babban ɗan Adda Salamatu Aliyu haidar suka fita sashinsa,Goggo Suwaiba ta rakasu da harara kawu Hayatuddeeni data lura da ita yace"lafiya Hajiya?".
Ta taɓe baki"kai dai bari Ɗan-uwa wallahi inna tina wannan abun yana min ciwo fiye da zato".
Goggo Hanne ta kallo ta"meye yake miki ciwon Suwaiba?"
"Hajiya dangin mahaifin Habib sun cuce mu sun ɓoye mana babba al'amari akan auren Habib da wannan matar tasa Hibba take ko Habi,kunsan dai sanin kowa daga cikinku ne irin yanda aka kai ruwa rana kafin auren Zainaba da Abubakar ya yiyu,dan tazo mana da baƙon al'amari na auren bare bayan auren duk cikinmu babu wanda yake zumunci da ita kamar ni nasan dukkan rayuwar datayi a gidan mijinta sannan bayan rasuwarsu babu yanda bamuyi da dangin Abubakar akan su bamu riƙon Habib kodan lalurar dashike ɗauke da ita ba amma suka nuna mana kasawarmu.Munso haɗa shi aure da Batul nan ma suka nuna mana iko akanshi wai ya samu wacce yakeso hakan ya ƙara tuzura da yawa daga cikinmu".
Shuru ya ratsa falon kowa yana jinjina kai alamar gamsuwa da maganganun Goggo Suwaiba.
Adda Hadiza tace"to Suwaiba ai wannan abubuwan cikinmu babu wanda ba akan idonsa ya afku ba tabbas dangin Abubakar sun nuna mana iyakar mu akan ɗan ƴar-uwarmu matuƙa".
Goggo Suwaiba ta ɗaura da faɗin"Duk ba wannan ne matsalar ba a matsayi irin na wannan gidan da mutane suke mana kallon daraja da kima ace jikan wannan gidan yana auren yarinyar datayi zaman kanta,ta guje iyaye da dangina ta zaɓa zaman bariki wanda babu mafaɗi balle mai kwaɓarka".
A hanzarce Goggo Hanne ta tashi daga kishingiɗewar datayi ta ƙurawa Goggo Suwaiba na mujiya kamar yanda duk sauran ƴan uwan nasun sukayi cike dason ƙarin bayani daga bakin Goggo Suwaiba.
"Hajiya bakije auren Habib na farko bane shiyasa baza kusan da wannan al'amarin ba nima ɗin danaje sai ranar auren Hajiya kulu take sanar dani kuma banason aga laifi na ace zan kashewa yaro aurensa akan abunda bai taka kara ya karya ba".
Adda Salamatu ta gwalo idanu"Yo Suwaiba wannan ai sun nuna mana cewa basu ɗauke mu a bakin komi ba,ace auren Uban mu amma su ɓoye mana wannan abun".ta fashe da kukan takaicin dake cinta kawu Isma'il yace"Ai Hajiya ni bana ganin laifin kowa kamar na Zainaba ita ta dage akan sai ta auri Abubakar duk dangi ita ta fara nakasa mana al'adar auren zumuncin da mukeyi a tsakaninmu daya samu asali tun kaka da kakanni,dan haka duk abunda suka mana ita taja mana".
Goggo Hanne data gama sauraron maganganun ƙannen natan ta sauƙe wata ƙatuwar ajiyan zuciya kafin ta sauƙe idanunta akan manyan ƴaƴansu dasuke zaune a falon,tayi gyaran murya kana ta umarce su dasu fice zasu tattauna a tsakaninsu,dan wannan ba lamarin daya shafesu bane dan tun kafin a haifosu suke gwagwarmaya akan auren Zainaba da Abubakar.
"Inko hakane tabbas dangin Abubakar sun mana zagon ƙasa,ace yarinya tayi rayuwa ba a gaban iyaye ba ai wannan abun dubawa ne ƙwarai da gaske,zan zauna da Habib ɗin naji ta bakinsa inya tabbatar mana da abunda kika faɗa sai munsan matakin dazamu ɗauka"tana kawowa nan a zanceta ta miƙe tare da naɗe dukkan hannayensa a bayanta ta nufi ɗakinta,suma ɗaya nabin ɗaya suka fara fice daga falon suna tafe suna ƙara tattauna maganar.
Ina zauna kan sallaya ina lazimi naji wayata ta fara ruri,na ɗan firgita saboda baccin gajiyan daya fara ɗaukata na ɗaga ina kallon Yasira datake kwance tana bacci hankali kwance sallama nayi ya amsa sannan ya ɗaura da"Ya gajiya dan nasan akwai ta saboda ke daga cikin Katsina zuwa daura ma gajiya kikeyi balle kinyi wannan tafiyar".
Na ɗan tsuke fuska kamar ina gabashi kana nace"kuma gani a zaune ba garau kamar ba wani tafiyar da nayi gajiya ai yanzu tabi jiki".
Ya saki murmushi yace"ko kuma tabi lafiyar gado ba"har na soma magana ya katseni"uhmm ni a wani part kuka sauƙa ne?".
"Tab!ni kuwa ina zan sani ina baƙura wani part ne dai yana kallon na Goggo Hanne"na faɗa ina mimmiƙe ƙafafuna dasuka sanƙare tsabar zama guri ɗaya.
"Part ɗin ƴan matan gidan kenan,ni kuwa gani a ɗakin wannan tuzurun Aliyu Haidar ai wallah......."bai ƙarisa ba naji sauƙar dukan wasan da Aliyun yakai masa,hakan yasani tinanin suna tare kenan.
"Wifey kina ganin zai illatani ko daga faɗin gaskiya?"na ɗan murmusa nace"ai kuwa dayaga taron kanawa da katsinawa dan taron dangi zamu masa".shima ya maido mini da murmushin yana cewa"to dai kaji da kunnenka ko?in kayi zuciya kaima kayi auren". ya saki murmushi yana ɗaura agogonsa yafita cikin uniform ɗinsa na sojojin ƙasar nijar.
Muka cigaba da hirarmu,ƙiran sallan isha'in da'aka farayi ya tilasta mana yin sallama bayan yabawa Aliyun wayan mun gaisa.
Gefena na ajiye wayar na tada sallah,ina iddarwa kuwa nafara jeri addu'o'ina ban damu na tada Yasira ba dan tace min tun kafin zuwarmu tana fashin salla.
Ƙiran Ummi ya shigo wayar Yasira da farko banyi niyyar duba waye ba balle har na ɗaga ƙiran,danaga an cigaba da ƙira ya sani tashi na ɗauka wayar zan tashe ta dana Ummi ce mai ƙira sai kawai na ɗauka muka gaisa tana tambayata ya mun iso lafiya na amsa mata da lafiya kalau sannan na tada Yasira na miƙa mata wayar.
Ina zama Farida dasu Mima suka shigo na ƙara yalwata fuskata da murmushi muka ƙara gaisawa dasu Farida wacce na lura duk tafisu sakin fuska da kuma saurin saɓo haka nan kuma tafi sauran sakin jiki dani tace"Anty duk gajiyarce tasaku zaman ɗaki tun ɗazu muke jiran fitowar ku Hajiya sai aikowa takeyi wai mu fito cin abinci".na murmusa nace"wallahi yanzu nake cewa ina iddar da sallah zan tashe ta mu fito".
Yasira na gamayin wayar muka fito na ɗaura hijabin danayi sallan dashi wanda ya sauƙa min har ƙasa dan ko takalmina ba'a hangowa na saka,suka ta min dariya muka fito falon farko damuka fara zuwa shi muka shiga nan kuwa muka tarar da kusan kowa ya hallata a wajen,muka zauna akan babban gardumar daka shimfiɗa.
Bamu ɗau lokaci ba su Habib da wasu samari huɗu suma suka shigo wanda yake a gaba kuma duk yafi sauran jiki na raya a raina ko shine Haidar ɗin,mussaman danaji Adda Suwaila na tsokalar shi dacewa "to ga shugaban gauraye ma ya fito"ƴan matan ƙannen nasan suka saki dariya kallo ɗaya ya watsa musu duk suka shiga taitayinsu.
Addu'ar cin abinci muka gabatar sanna kowa ya maida hankalinsa ga abunda yakeci,babu abunda kakeji sai ƙara cokula.
Muna gamawa nima na shiga sahun masu tattare wajen sannan muka tsabtace shi muka dawo muka zauna na lura da Goggo Hanne da duk motsina take ankare dashi da kuma alamar damuwar dake fuskarta.
Kawu Hayatuddeeni yace"Yanzu kai Aliyu duk ƙanneka sunyi aure ga Habib nan har da mata biyu,amma kai har yanzu kama kasa cire wacce kake son cikin ƙannen nakan"
"kasan yanayin aikin mufa kawu bamu da lokacin kanmu balle kuma na wata,adai ƙaramin lokaci in lokaci yayi zanyi"cewar Aliyu
Wannan karan Adda Hadiza mahaifiyarsa ce ta karɓe zance"Ai su kuma sojojin ce maka akayi basa aure koko meye?kai dai kawai kace baka da niyya ne".
Sadda kansa ƙasa yayi"kuyi haƙuri in sha Allah zanyi in lokaci yayi"yana kawowa nan ya tattari wayoyinsa ya fice.
"Hande min boni ni kuwa anya yaron nan ba aljanu gareshi ba,ace mutum da lafiyarka amma sam bakason zance aure"furcin da Adda Jamila ta rakashi dashi kenan.
Muka tashi muka musu sai da safe sannan muka tafi izuwa makwancinmu,washe gari muka yini da Farida Yasira kam tana can wajen su Nabiha da Mima.bayan mu gamacin abincin dare a ranar kamar jiya kowa ya hallara.
Goggo Hanne ta ɗan musguta kana ta umarce su Farida dasu tashi zasuyi wata maganar da ƴan uwanta tace Habib ya zauna wanda da farko ya miƙe zaibi ayarin su Khalifa ɗan Adda Lawisa ya komo ya zauna.
Damƙo hannuna Farida tayi zamu tafi Goggo Hanne tace nina zauna,na komo na zauna ƙirjina namin dukan tara-tara sau tara.
Kawu Hayatuddeni ne ya fara magana"Habib gaskiyar wani lamari mukeson mu sani shin da gaske ne matarka Hibba tayi zaman kanta kafin ka aureta sannan mahaifiyar ta uwar karuwai ne mahaifinta kuma ƙasurgumin ɗan fashi da makami?".
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un zuciyana ya buga tamkar zai fito daga cikin ƙirjina,na soma sakin hawaye Adda Lawisa ta dafoni haɗi dacewa"Ai ba abun kuka bane,kawai munason mun cewa hakan ne ko kuwa maganarce bamu fahimta ba".
Goggo Hanne ta tsurawa Habib ido tace"Ubana kai muke sauraro".
Na ɗago idanunmu suka gwaraye cikin na juna kansa ya soma jijjiga min wanda na kasa fahimta meyake nufi da hakan, ganin bashi da niyyar buɗe baki yayi magana ya sani cewa"Hajiya hakane kafin aure na da Habib nayi zaman kaina,nayi wata rayuwar da babu iyaye balle ƴan-uwa a kusa dani sannan gaskiya ne mahaifiyata ta kasance magajiyar karuwai amma mahaifina tsautsayi ya faɗa masa ko kuma ince ƙaddara.Tabbas na ƙudurce a raina cewa ko ba daɗe ko ba jima rana irin ta yau za tazo a rayuwata sannan za'a zargeni akan irin rayuwar dana gudanar a baya".na kai ƙarshen zancena tare da sakin kukan dayake fitowa kai tsaye daga ƙoƙon raina.
Goggo Suwaiba ta rafza salati"kun gani ko ashe dai abunda naji babu kuskure acikin sa".
"Ina mahaifiyarki take a halin yanzu"tambayar Goggo Hanne kenan na yarshe hawayena nace"bama tare da ita domin nakai shekaru tara rabon dana sata a idona,ina zaune ne a wajen dangin mahaifina a cikin kano a ƙauyen gano "na gwammaci na sanar dasu komai dan nasan tabbas tambayarta ta gaba shine a ina Habib ya ƙarbo aurena gwara na faɗa mata tun kafin ta tambaya.
"Habib lamari irin wannan yanada sarƙarƙiya kabi ruɗin soyayya kayi zaɓen tumun dare,yarinyar da batayi rayuwa a cikin gidan iyayenta ba kamar yanda duk wata ƴar kirki takeyi, ta zaɓa rayuwar bariki ta gama yawon ta zibar ɗinta akan titi Allah kaɗai yasan adadin mazan datayi tarayya dasu wacce ta siyar da jikinta kai kuma dayake kaine dayyus marar kishin kansa marar hankali da hange nisa ai ko Allah ma yace ka zaɓawa ƴaƴanka uwa ta gari wacce zasuyi alfahari da ita kuma daga tsatso mafi kyawu.ita kuwa wannan menene abun burgewa da sanya shauƙi har ayi marmarin aurenta a kaf!cikin tarihin rayuwarta har wani tarbiyace gareta ita da ta taso acikin karuwai tanbaɗaɗɗo marasa mutumci kuma basa ganin kowa da mutumci hatta iyayen da sukayi silar kawosu duniya.wani tabbaci kake dashi akan cewa itama irin wannan rayuwar data taso taga mahaifiyar tanayi bazai burge taba?shawaran dazan baka ka nutsu ka sake tinani tunda su dangin uban nakan nagan kamar tsoronka sukejine koko meye ni ban sani ba,dasuka kasa nushance dakai wannan babban haɗarin daka tafka sannan kuma abu na ƙarshe kaje asibiti a bincika lafiyarka kar ta goga maka cutarsu ta karuwai cuta mai karya garkuwar jiki".furcin bakin Adda Hadiza kenan takai ƙarshe tana huci.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
________________________________
Page 4⃣8⃣
Kaina yana cikin gwiwoyina tunda ta fara maganar idaniyana suke fidda ruwan hawaye har takai aya,duk maganganunta akan dai-dai suke UWATACE SANADI a yau badan irin rayuwar da Umma ta zaɓawa kanta ba da ban fuskanci wannan ƙalubalen ba a rayuwar aurena.
Habib kam hannayensa kawai yasa yana tare hawayen dayake yi zuciyarsa na masa nauyi sosai yana fizgar numfashinsa.idanuna dasukayi jajir kuma lokaci guda duk suka kumburu kamar zasu faɗo ƙasa na ɗago na sauƙe su kan Adda Hadiza na soma faɗin"Tabbas ban kasance daga cikin mataye da har zasuyi tinanin samun mazajen ƙwarai a rayuwarsu ba,domin duk wanda zaiso neman aurena sai an bashi labarin waye mahaifiyata da kuma abunda yayi silar rasuwar mahaifina UWATACE SANADI bazan zargi kowa ba sannan duk abunda zai faru soyayyarta bazai ragu a cikin wanna ƙirjin nawan ba.ban cancata zama da Habib ba ko ayau ya sakeni bazan daina yi masa fatan alkhairi ba domin shiya tsamo ni daga cikin ƙazantacciyar rayuwata.na kasance ako yaushe zuciyata dana cike da fargabar rana irin ta yau ranar da za'a goran tamin dan Allah mijina dan soyayyarka da annabi muhammadu S W A ka sauwaƙe min hankalin kowa ya huta kaima kasama salam..."
Adda Lawisa tayi saurin kai hannunta ta makemin bakina"kul!waya gaya miki mace tanacewa mijinta ya sake ta haka siddan ba tare da wani dalili ba ai sai ki shiga fushin Allah".
Adda Salamatu tace"ai dakin barta gaskiyan littafin arziki dayace ƴan gidan gadon rama da ƙulu idan suka sama aure a gida farfesu sunfi kowa iya fetsere".Adda Lawisa ta jinjina kai kawai.
"Hajiya hakane tayi rayuwa ba a gaban iyayentaba amma wannan ɗinma da dalili,sannan kuma a cikin gidan Uncle Suraj ta zauna duk tsawon wannan lokacin,idan tanada wani mungun hali ai za'a gani a zaman dasukayi dasu Ummi".Cewar JIGONA mai kareni a ko yaushe.
Goggo Hanne tace mu tashi mu tafi zata ƙara neman mu tare da tambayar Habib yaushe zamu tafi?.yace daman sati ɗaya zamuyi saboda hutun makarantana ya kusa ƙarewa zamu koma.
Da kyar nake jan ƙafafuna na wuce ɗakinmu nayi sa'a kuwa ban tarar da kowa a ciki ba Yasira tana can tare dasu Nabiha.kamar jaka haka na faɗa kan gado ina sakin kukan da hawaye basa fitowa dan sun ƙafe,tabbas duk wata macen datayi rayuwa irin tawa ya zama dole a jefeta da zargi harma fiye da wanda Adda Hadiza kemin a halin yanzu.karo na farko a rayuwata danayi dana sanin auren Habib naji na tsani kaina gabaɗaya badan sanin danayi akan duk wanda ya kashe kansa makomarsa wuta ce ba to wallahi dana rataye kaina na huta da wannan rayuwar.
Habib ne kawai zai iya wankeni daga wannan zargi domin yasan cewa a budurwa ya same ni,ban taɓa riƙe koda farce wani ɗa namiji balle yakaimu ga aikata alfasha,nasan hadda ƙiyayyar dasuke gwada su dangin mahaifin Habib itama ta shafe ni.
Ina jin wayata data soma ringing har ƙiran ya katse aka ƙara kira a karo na biyu shima banbi ta kansa ba,sai ana ukun na yunƙura najawo wayar nakara fashewa da kuka ganin sunan mai ƙiran JIGONA na cilla wayar akan gado na koma na kwanta ina matso ruwan hawayena Naji ƙaran shigowar messega na duba.
"Nasan bakya cikin nutsuwa a yanzu amma dan Allah ki ɗaga ƙirana inason muyi magana ne please wifey dan Allah ki sauyawa halin dazan shiga".
Ina gama karantawa na sauƙe ajiyan zuciya na zubawa emojis ɗin dayasa a ƙarshen message ɗin masu alamar kuka,idanu har na fara maida masa da reply ƙiran Ummi ya shigo wayar na ɗaga tare da mannawa a kunnena na kasa furta koda kalmace.
"Hibba dan Allah kimin magana na ƙira Habib naji shi cikin wani yanayi yamin bayanin komai ki kwantar da hankalinki,karkisa wannan a ranki zan turo miki kuɗi gobe ki shirya kayanki kiyi tahowarki dan bazan juri cin mutumci haka ba daga zuwarku kamar daman jira sukeyi".furcin Ummi kenan dasuka ƙara sanyani tsananta kukana nace"Ummi ni banga laifin kowa daga cikinsu ba domin duk maganansu akan dai-dai take,kowa zaiyi burin samawa ƴaƴansa uwa ta gari kuma mai usuli mafi kyawu da nagarta ,kun nuna min dukkan gata dakuka yarjewa Habib ya aureni sannan baku taɓa min gori ko kuwa nuna tsangwama ba nagode Allah yasaka muku da mafifin sakayyarku amma na fara tinanin na roƙo Habib ya bani takardata".
"Hibba karda wahalar gidan miji yasaki ki gujewa bautar Allah ki sani shi aure ibadane kuma bauta kikeyi.duk abu mai muhimmanci ba'a samunsa cikin sauƙi ko jindaɗi sai ansha wahala duk duniya babu wanda ya kamata kibi sau da ƙafa kamar mijinki idan aka cire Allah da manzonsa,zaman aure sai an daure kuma sai an haɗa da haƙuri.yanzu kidan kikace ya sake ki shin kinsan waye zaiki kuma aura ne?,shin kinsa wani irin zama zakuyi dashi?,shin kina da tabbacin zaki dawwama cikin jindaɗi ba tare da jarabawa ba?.Hibba babu komai a cikin wannan rayuwar face ƙalubalen da zakita haɗuwa dashi,shifa ɗan-Adam ba zai taɓa zama cikin farin-ciki da jindaɗi ba".
Tabbas banyi kuskuren bawa Ummi wani bangare mai girma acikin raina ba,domin ta cancanci hakan daga gareni kalamanta suka sanyaya mini ruhina nafara sauƙe numfashi a hankali kana nace"Nagode sosai Ummi Allah yaƙara lafiya da nisan kwana dan Allah ki tayani da addu'a Allah ya kawo min haske cikin rayuwata".
Inajin yanda ta sauƙe numfashi tace"in sha Allah Habib zai zamto duk wani haske a rayuwar ki".
"Ina fatan haka Ummina".sosai tayita kawo min misalai da ƙissan matan annabawa hadda ƙissan ƴar ma'aiki Nana Faɗima alaihissalam a gidan aurenta tasha wahala sai naji to waye mani ɗin dabazan sha wahala agidan aure ba tunda mai matsayi irin nata yasha balle ni.
Mun daɗe muna waya da Ummi kafin mukayi sallama nayi niyyar ƙiran Yaya Fawas amma nafasa dan banason naɗaga masa hankali acikin wannan daren.
Na tashi na nufi banɗaki na ɗauko alawa nafito na sama wayata tana ruri na duba naga Habib ke ƙira bakin gadon na zauna na zuwa wayar idano ina rafzar kuka kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta.
Har ƙiran ya tsinke na kasa ɗagawa mussamman dana tinu cewa zaman aurenmu dashi yakusa zuwa ƙarshe.
Furcin Adda Hadiza suka soma dawo min cikin ƙwayar kaina"Shawaran dazan baka shine kaje asibiti a duba lafiyarka kar tasa maka cutarsu ta karuwai,cuta mai karya garkuwar jiki".kaina ya sara mini da matuƙar ƙarfi na durƙushe a wajen ina kuka na daɗe cikin wannan yanayin kafin nayi ƙarfin halin miƙewa ina riƙe da kaina da nakejinsa tamkar an ajiye min wani abu mai nauyin gaske saboda azabar ciwon dayake min.
Na rarimo hijabina nasaka na tada sallar ina iddarwa Yasira dasu Farida suka shigo ɗakin nabisu da ido har suka ƙariso suka zauna,Yasira tace"Anty nazo na miki sai da safe ne zan kwana a ɗakin su Mima".
Na sunkuyar da kaina nace"to atashi lafiya Allah ya bamu alkhairin sa".
Ta amsa da Amin yayin datake jan hannun Nabiha suka fice,saura Farida ita kaɗai.
"Anty kamar bakida lafiya duk jikin ki babu kuzari ko gajiyar ce har yanzu?"na ƙirƙoro murmushin daya tsaya iyakan leɓɓana nace"Babu komai Farida kawai yanayin ƙasar takuce kamar bata karɓe ni zazzaɓi nakeji".
Ta taso ta dawo kusa na tare da ɗaura hannunta saman