Showing 6001 words to 9000 words out of 104857 words

Chapter 3 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7301

ya ɗaura brown ɗin agogo a damtsen hannun sa.




Kansa babu hula yayin da tarin sumar fuskar sa wanda tasha gyara sa sheƙi takeyi,haka nan sun kwanta luf a saman fuskarsa.


Idanunsa sun boye cikin wani farin glass,sai wani ni'imtaccen ƙamshi ne yake tashi daga cikinsa.


A hankali yake tafiya cikin cikakken nutsuwa ya nufo inda muke tsaye.
ƙamshin shine ya bugi hancina, nan take na juya domin ganin Wanda yake tafe da wannan ƙamshin.
Karaf muka haɗa ido dashi,sai a wannan lokacin nasama damar ƙarewa halittar fuskansa kallo.




Round face gareshi skin color ɗinshi black ne amma mai irin kyau ɗin nan ne.Dan kowani mai farin fatan bazai nuna mishi kyan skin ba.


Idanunsa manya ne ma'abota haske,yanada yalwan gashin eyes lid da eyes lashes bakin nashi Dan dai-dai.


Yana da madaidaicin tsayi,lumshe idona nayi yayin da ƙamshin sa ke ƙara tsara ƙofofin hancina.


Da sallama ya ƙariso wajen,a hankali yake motsa dan wannan bakin nasa yana tambayar mai shagon akwa recharge card na airtel?.Da rawan jiki Ma shagon yake cewa e akwai.




Tsaki na saka nacewa shahida wacce ta naga shagalta da kallon wannan guy ɗin"Dan Allah ki karɓa chanjin mu tafi".


Sai a sannan ta ɗauke idon ta daga kallon dake mishi Tace" Malam bamu chanjimu mu tafi".




"Wallahi ba canji, sai dai kuje anjima sai Ku dawo Ku karba".Mai shagon ya faɗa lokacin dayake yagowa wannan guy ɗin recharge card ɗin.


Dafe goshin ta shahida tayi tace"to ai zamuyi amfani da canjin ne yanzu ya za'ayi?".


Sai a lokacin sannan guy ɗin ya ɗago kai daga latsa wayarsa da yakeyi,ya kalle mu murmushi yayi cikin sanyin voice ɗin sa yake cewa mai shagon




"Kaga malam ka basu kuɗin Nasu kawaesai ka haɗa kuɗin card ɗin,da suka saya da nawa zan biya".




Cikin fara'a shahida tace,"Mungode bawan Allah".
Taƙaitaccen murmushi kawai ya saka sannan ya maida kallon sa ga wayarsa ba tare da yace da ita komai ba.


Miƙowa shahida five hundred ɗin ta Mai shagon yayi,karɓa tayi tare da ƙara cewa,"mun gode bawan Allah".




Sai a wannan karon ya ɗago kansa a hankali yana cewa"karki damu amma ita ƙawarta ki bata magana ne?".




Washe baki shahida tayi Shahida tace" La!hibba ai wallahi haka take bata da yawan magana".




Maimaita sunan kawai yakeyi Hibba!Hibba!!"Sunan ya burge ni ni kuma sunana habib bari nabaku complementary card ɗina".




Wani card ya Ciro daga aljihunsa mai ɗauke da sunanan sa da phone numbernsa,ya miƙawa shahida karɓa tayi tare da ƙara yi masa godiya sannan muka bar wajen.


Tsaki shahida tasaka tana faɗin"Wallahi hibba halinki yana bani mamaki ke Sam a rayuwarki bakya sakewa mutane fuska,to a haka wazai ce yanasonki?".


Murmushi nayi kafin nace"Shahida kenan inda ace kinsan irin ƙalubalen dana,fuskanta kafin nazo nan da bazaki min haka ba karatu nazoyi ba sakewa samari fuska ba".




"Amma fara'a ma ai wani abune, ko at list ki nuna mishi godiyanki akan alkhairin daya mana".




A harsale nace,"shahida wai rokansa muka yi ne, ra'ayin kansa ne fa".Shiru shahida tayi dan tasan halina.




UWATACE SANADI


Tsarawa/rubutawa

©Maimunah Tijjani Iyam




________________________________________


Free page




Page 5⃣




Hostel muka wuce,nasa recharge card ɗin da shahida ta saya mana na kira yaya Fawas.
Ringing biyu ya ɗauka cike da so da kuma ƙaunar juna muka gaisa.Nace "ya Umma?".




"Umma lafiyanta kalau yanzu ina shago,inna koma gida da dare zan haɗa Ku Ku gaisa". Cewar yaya Fawas




Ajiyan zuciya na saka kafin nace,"yaya Fawas har yanzu Abba baizo gida ba?".
Shima ajiyan zuciyar ya saka yana cewa,"Hibba har yanzu babu labarin Abba,yau kusan shekara uku kenan har baffa na kira ko yaje wajensu a kano amma suka shaida min bai zoba".




A hankali naji hawaye yana bin fuskana.
Bakina na rawa nace" Yaya Fawas yanzu shikenan ba zamu sake ganin Abba ba kenan na shiga uku nikam yaya Fawas".




Wani kuka Mai ƙarfi na saka tare da kifa, kaina akan pillow ina fitar da numfashi a hankali.
"Hibba ki daina kuka,matuƙar Abba yana numfashi a ciki duniya zai dawo garemu komai daren da daɗewa ki daina kuka kinji ƙanwata kukan ki na ɗaga min hankali"yaya Fawas ya faɗa cike da kulawa.




Cikin dushashewar murya nace "Na daina yaya Fawas na daina kaji yayana".Cikin jin daɗin furci na yace,"yauwa ƙanwata".
Yayin dayake hana hawayen dake cike fal a idonsa zubowa.
Da haka muka cigaba da hirar mu,har sai da aka kira sallar magrib sannan mukayi sallama.


Alwala nayi na gabatar da sallan magriba ina zaune kan sallayata shahida ta shigo tana cewa,"Hibba Dan Allah ina wayarki?".




"Ga tanan meza kiyi da ita?".Matsowa tayi ta ɗauki wayar daga gaba na tana faɗin,"Wani waya zanyi mai muhimmanci wayata kuma ta mutu babu caji".




Ban bata amsa ba, na cigaba da tasbihin da nakeyi yayin da ta koma ta kwanta akan gado tana wayanta.
Suna na naji Shahida tana kira hibba!hibba!! Hibba!!!a harzance na juyo ina faɗin lafiya?.




Ƙarisowa tayi gaba na tare da miƙamin wayan Tace,"Gashi HABIB ne zaku gaisa".




Cike da rashin fahimta nake tambayar ta "waye kuma HABIB?".
Tsaki ta saka kafin tace"Habib mana wannan guy ɗin daya saya mana recharge card ɗazu.




Harara na watsa mata ina cewa"Haba Shahida daga haɗuwa da mutum sau daya shine har zaki kirashi wannan wani irin tusa Kaine?to nidai bazan gaisa da kowa ba".
Inajinsa daga cikin wayar yana cewa, "just leave her alone,kar ki takura mata just extent my greeting to her".




Bansan sanda nasaki wata doguwar tsaki bana,Fizge wayata nayi daga hannun Shahida "Daman wannan shine kiran dazakiyin har kike kiran sa mai muhimmamci?".




Juya idanunta tayi cikin wani nishaɗantaccen murmushi tace"Hibba bazaki gane bane,guy ɗin ya haɗu over nake gaya miki he is very nice and cool".




Cike da takaici nace"Shahida kinyi nisa Allah ya taro ki ".


Ta bangaren Habib kuwa yana kashe wayar ya cilla ta kan bed ɗinsa sannan shima ya kwanta,yana ƙarewa ceiling ɗin bedroom ɗin nasa kallo.




Da ƙarfi ya cije lips ɗinsa tare da shafa sumar fuskarta,sannan ya dafe ƙirjinsa saboda matsanancin bugun da take masa.


Wayarsa ce ta fara ringing gani sunan DR BASHIR ya bayyana cikin screen ɗin wayar yasa shi sakin tsaki sannan ya ture wayar gefe.


Ƙara kira akayi a karo na biyu,sai da ƙiran yakusa tsinkewa sannan ya ɗaga Koda ya ɗaga shiru yayi baiyi magana ba.


"Afuwan mutumi na,wallahi fita ce ta same ni ta gaggawa shiyasa daka zu baka same ni ba".cewar Bashir




A hankali cikin yanayinsa na rashin son yi magana mai tsayi yace"uhmm".
Dr bashir yace "To yanzu yaushe zaka wuce katsina nan?".




" Next tomorrow in sha Allah"ya faɗa yana gyara kwanciyar sa.




"To Dan Allah gobe ka same ni a cikin school wallahi banason ka koma katsinan nan ne Baku haɗu da maryam Ba".


Cikin ƙosawa da sauraron surutun sa Habib yace"okay Allah yakaimu goben and then if u wish ka ƙara ficewar ka nazo ban sameka ba kaga mezai faru".




Yana kawowa nan ya kashe wayar yana sauƙe numfashi,can ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka yayi alwala sannan ya fito ɗaure da towel a waits ɗinsa sai kuma wani ƙarami yana goge kansa dashi.




Doguwar bakar jallabiya yasaka da hular ta,sai ka rantse da allah balarabe ne.
Masallaci ya fito yaje nan ya zauna sai da akayi sallan isha'i sannan ya dawo wani part naga ya shiga Wanda yafi nasa girma.




Da sallama ya shigo cikin palon Wanda aka ƙawata shi da abubuwan more rayuwa,kallo daya zaka yiwa furnitures ɗin dasuke falon Masu launin shuɗi ka tabbatar da an narka kuɗi wajen ƙawata falon.




Wata matace zaune akan lausassun kujerun wacce zata kai kimanin shekaru shitta da biyar a duniya,ta amsa sallamar cike da fara'a.
Kusa da ita ya zauna yana faɗin"Sannu da hutawa Granny".




"Yauwa Babban mutum ga can abincin ka can akan dinning".




Ya tsina fuska yayi yana ƙoƙarin ciro wayar sa daga aljihun sa Yace,"Bashi Granny banajin yunwa sa zuwa anjima zanci".




Ba ta kula shi ba ta miƙe izuwa dinning arean ta zuba mishi abincin a plate,masa ne na farar shinkafa da miyar alayyahu Wanda yaji nama da kifi.
Sannan ta tsiyaya mishi sanyanyan lemon kunnun a'ya a Kofi.




A gabanshi ta dige plate ɗin ta zauna tana cewa" To gashinan oya kacinye mishi gaba ɗaya".


Zaro idanunsa yayi yana faɗin,"Granny ina zankai dukka wannan abincin?".




Ganin bashi da niyyar ci yasa ta fizge wayar sa ta ajiye a gefe.
Da kanta ta dinga bashi abincin sai da tabbatar data cika mishi cikinsa sannan ta kyale shi.


Sun ɗan taɓa hira da ita kafin ya tashi ya tafi part ɗinsa ya kwanta, bayan ya gama jero nafilfilinsa.




WANENE HABIB?




Habib Abubakar Galadima shine cikakken sunansa.
Mahaifinsa alhaji Abubakar sanannan ɗan kasuwa ne bama a iya Nigeria ba gaba ɗaya faɗin Africa sunan sa ya zaga,kusan watace jaha a Nigeria yana company a jahar.


Kasuwanci shine gadon gidansuSu uku ne a wajen mahaifansu Abubakar shine babban su,halima sannan suraj.
Halima tun tana primary school Allah yakarɓi abinsa.
Sun taso cikin kulawar iyayensu alhaji Galadima da Haj.hauwa wacce suke ƙira da Granny.


A bangaren business Abubakar yayi karatum sa shi kuma suraj engeering ya karanta.Bayan kammala karatun sune suka dawo gida Nigeria.




Inda Abubakar ya cigaba da kula da companies ɗin mahaifinsu.A nijer ya haɗu da mahaifiyar Habib ya aure ta Suka dawo Nigeria da zama.




Bayan wani lokacin Allah yayiwa alhaji Galadima rasuwa,sunyi jimami sosai da wannan babban rashin dasukayi.
Nan fa kula da kasuwancin mahaifinsun ya dawo hannun abubakar.
Bayan wani lokaci Suraj ma yayi aure a katsina ya zauna da matarsa,kasancewar acan yake aikinsa.


Amma shi Abubakar a damaturu yake tare da mahaifiyar su.
Habib ne ɗansu na farko Wanda yaci sunan kakan sa na wajen uwa, daga shi kuma haihuwar ta tsaya.
Tun haihuwar Habib aka haife shi da wannan cutar ta CARDIOMYOPATHY ma'ana raunin zuciya.




Hakan yasanya tausayin sa a zukatan kowa,tashi ƙaddaran kuma kenan a yanda tazo.
An mishi aiki a zuciyarsa aka bashi wasu magungunan dazasu taimaka wajen saisaita bugun zuciyar tashi.
Sosai ahalin nasan suke kiyaye duk wani abin dazuka san sai ɓata masa rai.


Simple life Habib ke yi dan sanin dayayi masu cuta irin tashi basu fiye tsawon rai a duniya ba,an masa aiki a zuciyar sa tare da jaddawa iyayen nasa suka kasance suna,masu Samar masa da farin-ciki Sosai duk ahalin suke gwada masa ƙauna.


Suraj kuwa ƴaƴansa biyu sayyid Wanda yaci sunan Abubakar,sai kuma Yasira Wanda taci sunan mahaifiyar su.
Habib yana da shekaru huɗu,Allah yayi wa mahaifansa rasuwa,a hanyar dawowarsu daga nijer.


Nan riƙonsa tare da tarbiyar sa suka dawo hannun Granny.
A jami'ar Abubakar Tabawa Ɓalewa ta jahar bauchin yakubu yayi karatun sa fannin kasuwanci,yana dawowa kuwa ya karɓi ragaman kasuwancin family ɗin nasu.




Wannan kenan.




UWATACE SANADI


Tsarawa/rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


________________________________________


Free page




Page 6⃣




Washe gari bamu da lectures ɗin safe sai na ƙarfe goma.
Ina zaune a hostel inna duba hand out,waya ta ta fara ringing, sunan yaya Bashir ne ya bayyana cikin screen ɗin wayar.




Naɗaga wayar tare da sallama ya amsa,sannan na gaishe shi ya amsa min.
"kizo office ɗina akwai sakon da fawas ya aiko miki sai kizo ki karɓa,Dan fita nake son nayi".




" To"kawai na amsa dashi sannan na kashe wayar.
Gyalena na ɗauka milk color na bulluɓa a kafaɗa ta,Shigar atamfa ce a jikina simple ɗinki aka mata bamai taƙurawa ba.
Yaya Fawas da kansa ya ɗinka min ita, an mata adon black stone a jikin ta.




Wayata na ɗauka na fito izuwa office ɗin yaya Bashir,lokacin Dana kusa office ɗin shi kuma yana fito wa da sauri.
"Sorry Hibba ki shiga ki jirani ina zuwa,akwai wani aboki na dazan taro shi yanzu".Dr Bashir ya faɗa lokaci dayake wucewa.




Office ɗin nashiga na zauna ina latsa waya ta.Ta bangaren Habib kuwa Daren jiya dakyar ya samu ya runtsa.


Washe gari kuwa sa wajajen 9:00 na safe ya samu ya farka.
Yana tashi ya faɗa bathroom wanka yayi,as usual ya fito ɗaure da towel a waits ɗinsa da kuma wani ƙarami yana goge sumar kansa dashi yana dumping ruwan jikinsa.
Gaban dressing mirror ya nufa ya fara shafe laulausar fatar sa, da mayuka gyara sumar sa yayi tare da shafa musu mai ai kuwa tunin suka hau sheƙi.


Wata dakakkiyar shada baƙa ya fito da ita wacce aka yiwa aikin surfani,da Golding ɗin zare ɗinkin ya ƙawatu sosai.


Ya saka sannan ya saka hular sa ma baƙa ce da rantsin Golding ajiki sannan ya saka a tsintsiyar hannunsa .
Sannan ya feshe jikinsa da daddaɗan turare,kallon kansa yayi a cikin madubin Wanda kayan daya sa suka ƙara fallasar da sirrin tsan-tsan kyan halittarsa shi kanka yasan yayi kyau ba ƙarya.




Phone ɗinsa ya ɗauka da key ɗin motar sa,ya fito ya nufa part ɗin Granny bai iske ta a falon ba.


House maid ɗinta ne kawai suke ta gyare-gyare.
Suna ganinsa Duk suka zube suna gaishe shi cike da girmamawa,kanshi kawai yake gyaɗa musu.
Ɗaya daga cikinsu wacce tafisu manyan ta ya zubawa ido.A hankali yake motsa Dan ƙarami bakinsa yake cewa


"Haba! Iya Bana hanaki Duk wani aikin wahala ba a cikin gidan nan ki bari sauran ma'aikatan suyi mana,saboda haka fa na ƙaru wasu ma'aikatan".


Murmushi tayi wacce ya kira da Iya tana ƙara jaddada nutsuwa da sanin ya kamata irin ta Habib ɗin.




"Babban mutum banason zaman haka ne,shiyasa nace gwara ina Dan motsa jikina".cewar Iya




Langwabar da kai yayi yace,"To iya nidai banason kina wahalar da kanki,ina Granny?"




Ta amsa masa datana ɗaki.Direct upstairs ya nufa inda ɗakin Granny yake.
Tana kan sallaya ta iddar da sallan walaha kenan,ya shigo kusa da ita ya zauna cikin sanyayyiyar voice ɗinsa ya gaishe ta ta amsa.


Kallo ta tsare shi dashi yayin da taga fuskar mahaifinsa ya bayyana akan fuskar tashi.


Turo baki yayi ganin irin kallon datake masa yana cewa,"Tsohuwa wannan kallon fa?to nifa kar ki lashe ni".




Murmushi tayi kafin tace,"ina zuwa haka?"




"Zanje cikin YSU ne wajen Bashir,jiya naje ban same shi ba".


Yana gama faɗar haka ya miƙe zai fita
Muryar Granny ne ya dakatar dashi daga fitan.


" Breakfast ɗin ka fa?"


Yana shirin murda handle ɗin kofar ɗakin yace,"A kaimin part ɗin,sai na dawo zanci".


Har zai fita sai kuma ya juyo da faɗin,
"Yauwa Granny Dan Allah banason iya ta sake wani aiki a cikin gidan nan,Bana jin daɗi inna zo naganta tana wasu aiyukan buda da irin shekarunta".




"Nima ba yanda banyi da ita ba amma ta ƙi dainawa amma karka damu zan ƙara mata magana".cewar Granny




"To"Yace yayin da yake fita daga ɗakin.
Fitowa yayi ya nufi parking lot,wata sabuwar mota dal ƙiran range rover ash color ya shiga,yayin da gate man ya kwangale masa gate ɗin ya fita.




Yana shiga cikin YSU yayi parking mota sa,sannan ya buɗe ƙofar motar ya saƙalo ƙafafunsa wajen,ba tare da ya fito ba.
Wayar sa ya ɗauka ya shiga dialing numbern bashir,ringing ɗaya ya ɗauka yana tambayar yana inane?


yace "gani a parking space".


Kashe wayar yayi dai-dai lokacin daya hangi bashir,ya nufo shi sannan ya fito daga cikin motar.
Da fara'a Dr bashir ya iso,suka rumgume juna suna farin ciki Office ɗin Dr bashir suka nufa.


Yayin da Duk inda suka wuce mutane ke bin habib da kallo,yan mata kuwa kowacce da rawan kanta suka fara tasowa suna gaishe da Dr bashir da kuma habib,Dr bashir ne kawai Mai amsawa.


Har suka isa office ɗin,turo kofar suka yi tare da sallama a bakinsu,nan take naji zuciya ta ta fara bugawa da ƙarfi sallamar na amsa,




Sannan suka ƙarisa shigowa cikin office ɗin.
Dr bashir ya zauna a kujerarsa shi kuwa habib ya zauna a kujerar da take facing ɗina.


Tunda ya shigo office ɗin zuciyar sa take bugawa,muna haɗa ido kuwa bugawar zuciyar tashi ta tsananta.
Kallo na yake yi da sexy eyes ɗinsa masu kashewa mutum jiki.




Dr bashir yace,"Sorry hibba na barki kinata jira".




Sunkuyar da kaina nayi saboda izuwa yanzu na fara tsorita da irin kallon da yakemin nace,"La ba komai yaya bashir".


"Bari na ɗauko miki saƙon na bari a mota".Dr bashir ya faɗa yayin dayake ficewa daga office ɗin.


Kamar na ƙwala ihu naji da yaya bashir ya fita,ya barni dashi.


Na daure nace"To yaya bashir"Sannan ya fita yana cewa.


"Abokina sorry fa bari na ɗauko mata saƙo".Yana kawowa nan ya fita.


Kamar jira yake yi yaya bashir ya fita yayi magana,cikin sanyayyiyar voice ɗinsa da na ji ta,tun daga toe ɗin na har cikin head ɗina Yace ,"Sannunki".


Ba tare Dana dago na kalle shi nace,"Yauwa sannu".


Kallona ya cigaba dayi hakan, ya ƙara tsorita ne.cike da tuhuma na ɗago kaina nace,"malam lafiya irin wannan kallon?".




Murmushi yayi Wanda sai da fararen haƙwaransa suka bayyana.


"HIBBA ko? Shine jiya gaisawa ma muyi a wayar shahida kika ƙi ko?".




Cike da faɗa na ke cewa"Meye haɗina da kai da har zamu gaisa".




" Amma ai ke musulmacce addinmu ne ya haɗa mu".




Harara na watsa mishi na cigaba da kallon wayata.
Shigowar yaya bashir,ya dakatar dashi daga maganar daya yi niyya.




Ledodi yaya bashir ya shigo dashi ya ajiye a gaba yana cewa,"Yauwa hibba ga saƙon naki".


Godiya nashi sannan na ɗauki ledar zan fita.Ina ɗaga ledar ta tsinke nan kuwa kayan ciki suka zubo ƙasa,kayan tea ne da abubuwan da dan makaranta kan iya buƙata na yau da kullum.




Kamar na fasa ihu haka na fara tattare kayan,A hankali ya miƙe daga inda yake zaune ya fara tattrare kayan shima.


Wata Leda yaya bashir ya miɗomin na zuba kayan aciki na fita.


Hostel na wuce raina Duk baya min daɗi,Ina isa na ƙira yaya fawas ina mishi godiya har umma yabawa wayar muka gaisa da ita sama-sama.duk da bawani magana mukayi da ita sosai amma naji daɗi rabo na dajin muryan ta tun bayan zuwa na school.




Hira mukayi sosai da yaya fawas nan yake faɗamin shima zai jona FCE potiskum dan yanzu alhamdulilla yana samu sosai a sana'ar sa na ɗinki,fatan alkhairi na mishi sannan mukayi sallama.




UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam




______________________________




Free page




Page 7⃣




kallo yabi bayana dashi har na fice daga cikin office ɗin,kallon shi Dr bashir yayi tare da sakin murmushi,sannan ya kawar da kansa gefe.
Dan hararan shi habib yayi yace, "Wai meye ne haka malam?".




"To ai kai zan tambaya habib".Ajiyan zuciya habib yasaka kana yace"kaga malam ka tashi mu tafi inda zamuje,tun kafin na canja ra'ayi kuma".




Cikin sauri Dr bashir ya mik'e suka fita.Ina zaune a hostel shahida,ta shigo Dan harararta nayi tare da gyara kwanciya ta, sannan nace,"ɗazu naga mutuminki a office d'in yaya bashir".




Washe baki tayi tace "Ayya my Prince,kin tinamin ma bari na kira shi".


Tima dake zaune tana cin abinci,tace "wai ke shahida wanene wannan habib d'in?".


Juya idanunta shahida tayi Wanda izuwa yanzu,na tabbatar haka tana yin shine a Duk lokacin da take cikin farin ciki.




"ina ruwanki yar sa ido". Cewar shahida


Taƙaitaccen murmushi Tima ya saka kafin tace,"To Allah ya ki hakuri bani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login