Showing 9001 words to 12000 words out of 104857 words

Chapter 4 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7338

na kar zomon ba rataya aka bani".


Nidai dariya nake ta musu.cikin kwanacin nan muka fara exams sosai na maida hankali ga karatu.


Ana haka habib ya koma katsina gidan ƙanin mahaifinsa suraj,Dan anan katsina ta dikko ɗakin kara manyan companies ɗinsu suke.


Tun daya tafi ya kasa sukuni,kullum sai ya kira wayar hibba yayin da ita kuma bakin ta a baya fasa fadɗa masa,baƙaƙen maganganu.


Nayi tinanin ina tura mishi numbern shahida, zai daina kira na Dan a zato na ya ɗauka wannan layin tane,Dan da shi ta kira at a first time dasukayi waya.sauran mu exams biy malamai suka tafi yajin aiki.


Sosai nayi takaicin haka ma students da dama,duk haka muka fara tattare kayayyakin mu.






____________KATSINA__________




Zaune habeeb yake a office ɗinsa, yana duba wani file dake gabansa.
Ajiyan zuciya ya saka mai ƙarfi tare da dafe ƙirjinsa saboda matsanancin bugun da take masa.


Numfashi ya furzar tare da dafe kansa,tabbas ko shi kansa ba zai iya fasalta irin yanayin da shiga ba saboda wannan yariyar ba.




Wayar sa ce ta fara ringing, ba tare daya duba Wanda ya kira ba ya kara wayar a kunnensa.
Shiru yayi baiyi magana ba,gada dayan gefen Dr bashir ne ke ce"Mutumi na yane?".




Kamar ba zai iya buɗe bakinsa yayi magana ba yace,"normal bashir ya school ɗin naku?".




"Normal abokina mun shiga strike ai gobe ma,students za su watse wallahi". Cewar bashir




Kamar an zabure shi ya miƙe da cewa"Okay nima zan zo damaturun kafin goben".




Bai jira amsar da bashir zai bashi ba ya kashe wayar,key ɗinsa ya ɗauka ya fito daga office ɗin da sauri.




Parking lot ya nufa yayin da drivern sa ya taso da wuri ɗaga masa hannu yayi yana cewa,"No ni kadai zan fita".




A guje ya figi mortar yanufi gida gida,yana isa direct side ɗinsa ya nufa ya faɗa bathroom,a gurguje yayi Wanda ya fito dumping ruwan jikinsa yayi.




Yasaka kayansa brown ɗin shadda sannan ya fito,side ɗin matar uncle suraj(ummi)ya shiga.




Tana zaune a falo da sauri-sauri yake cewa,"Ummi zanje damaturu yanzu".




Juyowa tayi tana fuskantar sa tace," Habib lafiya da yamman nan?".


Cikin ƙoasawa dasan ya tafi ɗin yace,"lafiya kalau ummi akwai wannan company na groundnuts oil ɗin nan, da zamu buɗe,nake son naje naga yanda abubuwan suke tafiya".


Fɗaɗa fara'ar ta ummi tayi kafin ta shiga faɗin"To habib Allah ya kiyaye hanya,ka gaishe min da grannyn inka je".




"To"Kawai yace lokacin da yake, ficewa daga falon yana jin yasira nacewa,"Hamma habib zan rakaka".Amma ko ta kanta baiyi ba ya fice.


A guje yake driving motar,ƙarfe sha ɗaya da wasu mintina ya iso cikin garin damaturu duk da gudun dayake zugawa,bura-bura estate ya nufa inda gidan granny yake.


Yana isowa ya nufi part ɗnsa wanka yayi ya fito yayi sallolin da ake binsa,sannan ya jawo wayarsa jawo dialing numbern da yayi saving da HIBBA ya shiga yi.




Ina zaune a hostel ina harhaɗa kaya na,wayata ta fara ringing na ɗaga,shiru yayi baiyi magana ba.




Nace" hello".Sai a sannan yayi magana yace, "Yakike?"."Lafiya" na amsa dashi.




Daga nan bai sake cewa komai ba,komai bai kashe wayar ba.


Tsaki nasaka nace,"Dan Allah malam in baka da abin fad'a to ni ina da abunyi".




Zaffafar Ajiyan zuciya ya saka sannan yace,"Okay sorry gobe zaku tafi ko?".




Sanyaye na amsa da e,




"Ayya Dan Allah goben before Ku tafi inason magana dake".Ya faɗa yana ƙara sau-sauta muryar sa.


"okay"kawai nace tare da kashe wayata,na cigaba da haɗa kayana.


Ajiye wayar yayi kan bed,sannan shima ya kwanta nan kuwa bacci yayi gaba dashi ko part ɗin granny bai samu ya leka ba.


Washe gari da wuri ya tashi,wanka yayi ya shirya cikin nevy blue ɗin shadda wacce tasha aikin surfani da light blue ɗin zare,hular kansa ma da rantsin blue ajikin sa.


Gyara sumar sa yayi tare da shafa musu mai sannan ya feshe jikinsa da turaren sa na lalatul sahara.




Wayar sa ya ɗauka da key ɗinsa ya fito ta shiga part granny.tare da iya ya same ta ya shigo da sallama a bakinsa,
Suka amsa suna Washe baki granny tace,"A'a Babban mutum yaushe a garin?".




"Sauƙan jiya da dare"ya faɗa yayin dayake zama kusa da ita.Nan ya gaishe su suka amsa da fara'ar su,sannan ya dubi iya yana cewa,




"
Ƴar tsohuwa me kuka jagwalgwala ne yau a gidan?Dan nasan ba wani iya girki kuka yiba".




Dariya suka saka kana iya tace"sinasir ne da miyar kubewa sa kuma kunnun gyaɗa".Yatsina fuska yayi yace,"A kawo min kunnun gyaɗan".


Iya ce ta tashi zata kawo masa yayi saurin cewa,"A'a tsohuwa yi zaman ki bari na ɗauko da kaina".


Ya miƙe ya nufi kitchen ɗin.(iya amintacciyar ma'aikaciyar gidan ce tun yana yaro granny tace masa ita take renon sa kuma tana masa wani irin so mai tarin yawa,kasancewar bata taɓa haihuwa ba.shiyasa shima yake jinta ta daban acikin ransa).




Daga kitchen ɗin ya fito dauke da cup a hannunsa yana shan kunnun,yasha sosai Dan ba ƙarami daɗin kunun yaji ba.


Miƙewa yayi yace"Granny zanje wajen bashir,yanzu zan dawo kiyi min addu'a allah ya bani sa'a".




Bai jira amsar da zasu bashi ba ya fice daga falon.Tun wajen 9:00 na gama shiryawa,ina jiran habib amma har yanzu ana neman 11:00 bai zo ba,har su tima da zubaida sun tafi Shahida kuwa tare zamu tafi da ita.


Lokaci zuwa lokacin nake duba agogon dake ɗaure a hannu na,tare da sakin tsaki da shahida ma ta shanya ni tun ɗazu wai taje sallama da wasu class mate ɗinmu yan Zaria.


Shigowar motarsa na hango yayi parking dai-dai inda nake tsaye tare da kayan mu,Ya fito ya iso inda nake tsaye langwabe kai yayi yace"Afuwan na barki kina jira".




Ban kula shi ba illa ƙara ɗaure fuska danayi."Sai murna ake za'a tafi gida ko?".


Bansan sanda nasaki, dariya mai sauti ba nace, "e mana".Shima sai daya murmusa kafin yace, "may Almighty Allah tackle us this unnecessary strike".




Da amin na amsa mishi dashi,sannan yaɗan fara Jana da hira duk na lura akwai abinda yakeson faɗa amma bansan meyake dakatar dashi ba.

Ƙiran sallan da aka farayi yasa mukayi sallama ya tafi.ƙarisowar shahida ne yasa na dawo da kaina daga kallon motar sa danakeyi har tabar cikin school ɗin.




Hararar ta nayi ina cewa"wai me kika tsaya yine?".


"Wallahi hira muka tsaya yi dasu rukayya sunusi".Shahida ta faɗa tana ɗaukar akwatin ta.


Motor park muka je muka shiga motar potiskum.Dai-dai kiran sallan la'asar muka shigo garin potiskum,ni na biya mana kuɗin motar.




Godiya tayimin sosai sannan kowa ya ɗauki hanyar unguwansu,kasancewar shahida a old army barrack take.


Ina sauƙa daga nafef na hango,yaya fawas yana fito wa daga cikin gida,da Sauri na sallame mai nafef ɗin na sauƙo da akwati na.


A guje naje na isa ga yaya fawas ina cewa,"nayi kewar ka yaya na" riƙo hannu na yace, "Nima haka my cute angle".


Sannan ya ɗauka min akwatina muka shiga cikin gidan.




UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam




Book one free
Book 2 paid @N300


_______________________________




Page 8⃣




Umma na zaune a tsakar gida tana sauraran radio,cike da farin ciki naje na faɗa kan cinyar ta.
Itama fuskar ta ba yabo ba fallasa tace,"Wai ke ummul-khair yaushe zakiyi hankali ne?".




Cikin yanayin zolaya yaya Fawas yace"Umma sai ranan darayi aure zatayi hankali".




Cike dajin kunyar maganan yaya fawas,na miƙe ina cewa bari naje nayi wanka.


Ɗakina na shiga nayi wanka, dama yaya Fawas inna sanar dashi zuwa na ya gyara min ɗakin.


Ina fitowa Tima ta kirani na ɗauka kafin nayi magana tace"mutanan potiskum harkun isa?" "wallahi mun isa".
Mun Dan taɓa hira kafin muyi sallama
Na fito naci abinci sannan muka zauna,da yaya Fawas ina bashi labarin jami'a da yanayin mutanan cikinta,shima yana bani labarin gida bayan tafiya ta.



_________________Habib__________________




Yana isa yayi parking motar sa ya fito ya shiga part ɗinsa.
Direct bathroom ya nufa, ya sakewa kansa ruwa sannan ya ɗauro alwala ya fito.
Doguwar jallabiyar sa fara Sol ya saka ya fito ya tafi masallaci.
Yana dawowa ya koma part ɗinsa,canja shiga yayi izuwa shigar wani maroon ɗin yadi,tsayin rigar dai-dai gwiwarsa key ɗin sa da wayarsa ya ɗauka ya fito ya shiga part ɗin granny.
Tana zaune a falo ta iddar da salla kenan,tana ninke sallayar ya shigo.
Karɓan sallayar yayi ya ninke,sannan ya ajiye shi a muhallinsa Duban sa tayi tace"To har dawo?"






"E granny katsina zan koma",Da mamakin ta take tambayar sa lafiya yaushe ma kazo?.
Langwabar da kai yayi yace,"Granny zan tafi ne akwai akin Dana baro a can ɗin".
"To ka gaishe min da sauran yan uwan naka".Har parking lot ta mishi rakiya sai jero masa addu'o'i takeyi.


Shikuwa ya figii motar sa ya fita,duk ransa babu daɗi,dukan sitiyarin motar yayi tare da furzar da iska daga bakinsa,gefen hanya ya samu yayi parking tare da ɗaura kansa akan sitiyarin motar.




Ransa duk a jagule,a hankali ya furta "ya rabb wani irin al'amari ne yake shirin faruwa da zuciyata?".




Yafi 30min a haka wayarsa da tafa ringing ne ya sashi ya ɗago kansa.a hankali ya kara wayar a kunnensa yace "bashir yane?".


Daga ɗayan bangaren bashir yace,"normal fa mutumina,yanzu Nazo gida granny take cemin kazo har ka koma tace min jiya ka shiga cikin YSU shine ko ka nemeni sannan ma wajen wa kaje a cikin school ɗin?".






Ajiyan zuciya yasaka yace,"bashir I am on my way now if I reach home I Will call you,"


Yana gama faɗin haka ya kashe wayar, sannan ya zaburi motar ya hau titi.




Yana isa cikin katsina direct office ya wuce,yayi locking kansa a office ɗin.




Ƙiran sallan magriba da aka farayi ne,ya tilasta masa fitowa ya tafi masallacin da yake cikin companyn,sai da akayi isha'i sannan ya tafi gida.


Yana isa ya shiga part ɗin Ummi,gefen ta ya zauna yana sauƙe numfashi ƙasa-ƙasa ya ɗaura kansa akan kafaɗarta.




Dubanshi tayi tace,"A'a Habib har ka dawo baka min waya, ka sanar dani ba?".




" Ummi tafiyar ce tazo ba tsammani".ya faɗa yana gyara kwanciyar sa akan kafaɗata.




"To ya ka baro su Granny ɗin?"."Lafiya kalau tana gaishe ku, musamman this parrot".


Ya ƙarishe maganan yana nuna Yasira da take zaune a falon.




Cuno baki Yasira tayi tana cewa"Hamma Habib bana ce zan bika ba ka ƙi kulani".Yace "to school ɗinfa kiyi yaya dashi?".
"Ayya Hamma naga ba daɗewa zamuyiba".Miƙewa yayi tare da faɗin"Ummi akawomin abinci na part ɗin"yana kawowa nan yafita daga falon.




Bazan taɓa manta wata ranan alhamis ba,lokacin kwana na biyu da dawowa daga makaranta tun daga wannan ranan ƘADDARAR RAYUWA TA ta sauya.


Da yamma muna zaune a kofar gida ni da yaya Fawas Muna shan iska,wata farar mota ƙiran Mercedes tayi parking dai-dai kofar gidan mu.


Drivern dake jan motar ne ya fito ya buɗe bayan motar wani mutum ne ya fito,naso ace wannan ranan ta zama mafarki wannan ranan shine sanadin rubuta labari na tamkar a mafarki idanu na suka sauƙa akan fuskar Abba dake fitowa daga cikin motar.




A zabure na miƙe domin tabbatar da abinda idona ya nunamin domin na saba irin wannan mafarkin,Bansan sanda hawaye suka zubo daga idanuna ba.




A guje na nufi inda Abba yake tsaye na rumgume shi ina kuka,yaya Fawas ma zuwa yayi tare da rumgume shi.




Riƙo hannuna Abba yayi muka ƙarisa cikin gidan,Umma tana fitowa daga wanka sukayi ido huɗu da Abba.




Sake bukatin ɗin dake hannunta tayi cike da mamaki gami da jimami da son tabbatar da abinda ta gani tace,"Sule!sule Kaine wannan?".


Abba yace"kwarai kuwa Juwahir nine".
Tabarma na shimfiɗa mana muka zauna yayin da driven Abba ya shigo da wani akwati ya ajiye a gaban Abba sanna ya fita.
Ruwa Umma ta kawowa Abba ta ajiye masa tana cewa tana tafe tana faɗin,"Sule kai kuwa meyayi zafi haka?zaka tafi abinka ko waiwayen mu bakayi ba".




Abba yace"juwa kenan bagashi yanzu na zoba".yaya Fawas ya gyara zaman sa yana ƙara fuskanto Abba yace,"Amma Abba Duk tsawon lokacin nan ina kaje?".




Murmushi Abba yayi tare da buɗe akwatin dake gabansa,ya Ciro waya guda biyu ƙiran iPhone 12pro max ya miƙawa yaya fawas ɗaya sannan nima ya miƙomin ɗayan yana faɗin"Mama na kema ga naki".


A hankali nasa hannu na karɓa ina masa godiya,zannuwa ya Ciro ya mikƙawa Umma har ƙasa Umma ta zube tana masa godiya.


Dubu ɗari ya miƙawa yaya Fawas yace ya riƙe koda wata buƙata Zara tazo Umma ce tayi saurin cewa"Sule kodai arzikin Kane ya dawo?".




"Juwahir kinsa ikon Allah yafi gaban komai,shike azirta duk Wanda yaso a lokacin daya so kuma a sanda yaso".yana gama faɗin haka ya miƙe,Cikin sauri nace" Abba ina kuma zakaje?".






"Ummul-khair inason na shiga cikin unguwane mu gaisa da mutane kinsa an Daɗe ba'a haɗu ba".


Har ƙofar gida muka raka shi sannan muka dawo,kowa acikin mu jiran zaman dawowan Abba yake domin amsa mana tambayoyin da suke bakin mu akan dukiyar daya zo da ita.




Muna zaune har aka kira sallan magrib yaya fawas ya fita masallaci,ina iddar da sallah waya ta ta fara ruri na ɗaga.




Mun Dan yi hira da Habib sama-sama Dan ba kowani magana nake bashi amsar,bata sai dai nace masa uhmm da haka mukayi sallama.


Mu na nan zaune har ƙarfe 9:00 na dare Abba bai dawo ba,har bacci ya fara ɗauka na Washe gari duk muka tashi da mamakin,rashin dawowar Abba har makwabtan muka tambaya ko yaje wajen su kamar yanda ya faɗa amma kowa yace bai ganshi ba.




Kullum da sa ran dawowar Abba muke kwana acikin ranm ,har izuwa wata Daren ranan juma'a,yaya Fawas da Umma suna zaune a tsakar gida.




Yaya Fawas kayan mutane yake ta yankawa ita kuwa umma sana'arta takeyi wato dama giya.




Ni kuwa ina ɗaki ina waya da habib, kullum sai ya kirani a kalla sau biyar a yini,yana tambayar lafiya ta tun bana biye masa har na fara sakin jiki dashi.




Sosai mukayi wani shaƙuwa mai ƙarfi da habib,har nakan iya sanya shi a cikin,jerin mutane mafi muhimmanci a gare ni acikin kwanakin nan har yaya Fawas ya fara fahimtar wani Abu.




Sallama mukayi da Habib akan cewa zai shiga wanka inya fito zai kirani.Fitowa nayi waje na zauna kusa da yaya Fawas inna kallon yanda yake yankar kayan.




Ina zama Abba ya faɗo cikin gidan a firgice,cike da tsoro halin da muka ganshi duk muka miƙe muna faɗin lafiya?.




Bai kai ga bamu amsa ba motocin yan sanda suka zagaye gidanmu sannan wasu suka shigo ciki,wani jami'i ne ya ƙarisa kusa da Abba ya daka masa tsawa yana cewa"Be on ur kneel."


Tunin Abba ya durkushe a wajenSannan jami'in yasa masa handcuff a hannun sa,suka ɗauke shi suka fice dashi duk cikin mu babu Wanda Allah ya bashi damar tambayarsu dalilin tafiya da Abba domin mamaki ya gama cikamu.




Wasu hawaye masu zafi naji suna zubowa daga idanuna,wani ƙara na saka mai ƙarfi tare da zubewa a ƙasa ina wani irin kuka mai ban tausayi,durƙusawa yaya fawas yayi a gefena cikin kuka yace,Hibba kanwata ki daina kuka wallahi kukan ki yana ɗaga min hankali".




Muryata can ƙasa nace "Haba!yaya Fawas taya bazan yi kuka ba kana ganin abinda ya faru fa Abba suka kama".






Na ƙara fashewa da wani kukan rumgumo ni yaya Fawas yayi ya riƙe ni gam muka cigaba da kukan mu Umma kuwa sai safa da marwa takeyi.




UWATACE SILA


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


_____________________________






Page 9⃣




Haka muka kwana yanda mukaga rana haka muka ga dare,cikin mu ba Wanda ya runtsa.


Washe gari kuwa tun da sanyi safiya muka tafi police station,abinda ke tafe damu muka bayyana musu suka ce mana ba,nan aka kawo shi ba saboda laifinsa babba ne,damaturu aka wuce dashi tun Daren jiyan.


Umma tace"wa meya aikata ne haka shi kuwa?".


Sai da police ɗin ya zabga mata harara kafin yace"Kinason kice baki San sana'ar mijinki ba,na haɗa kai ga masu GARKUWA DA MUTANE?".


Dam-dam ƙirji na ya bada wani jiri naji yana ɗebata nan take na faɗi awajen sumammiya.


Cike da tashin hankali yaya Fawas ya riƙoni,yana kiran sunana Umma tace,"To Dan Allah bawan Allah inmukaje damaturun zamu zama ganisa".


Yace mata bashi da tabbacin zamu sama ganinsu Dan daga damaturun abuja za'a wuce dasu.




Salati umma ta saka,tana faɗin"Sule ka cucemu ka cuci kanka sule mai ya kaika wannan aikin?.




Wani police ne Wanda babu tsausayawa acikin ƙwallar idonsa ya dakawa yaya fawas tsawa,Yana cewa"Ku fice mana daga nan mutanan banza kawai".




Ɗauka na yaya Fawas yayi nuka fito,muka nema nafef mukayi gida.tunin labari ya baza unguwarmu masu zagi nayi masu tsausaya mana suma nayi.




Buɗe idona nayi a hankali,ina ƙarewa wajen kallo a zabure na tashi ina faɗin Abba!Abba!!Abba!!!.yaya Fawas ne ya kamoni ganin bana cikin hayyacina kuka yake matsananci yace, "Hibba kiyi hakuri abba zai dawo".






A hankali na kwantar da kaina a ƙirjinsa ina kuka,haka muka yini muka kwana Abu ɗaya.




Tabbas naga tashin hankali Umma matuƙar awannan lokacin tabbas tsakanin miji da mata sai Allah.




Nikam ba abinda yake sake sani kukan zuci,kamar ina tuna umma ce ta kori Abba daga gida har, shaiɗan ya rinjaye shi ya aikata wanna aika-aikan.




Tabbas UWATACE SANADIn duk wani ƙuncin rayuwa dana shiga,itace silar zubar hawaye na.




Washe gari muka ƙara komawa police station ɗin,cikin rawar murya Umma tace,"Dan Allah bawan Allah ka sanar damu shin zamu iya ganinsa inmukaje damaturun?".






Cikin zallar masifa yace,"wai Ku wasu irin mutane ne? nan fa aka sanar daku laifin wannan mutumin, to wallahi laifin,da mutumin nan ya aikata kuma cire rai da dawowarsa baza ku gani ba Dan wallahikashe su za'ayi".




Salati Umma ta saka tana faɗin"Na shiga uku ni juwahir naga abun da ya isheni.




Ni kuwa wani jiri ne naji yana ɗebata,da ƙyar na iya tsayawa akan ƙafafuna,riƙoni yaya fawas yayi idanunsa taf da ƙwalla yace,"Umma muje gida".




Muna isa gida na wuce ɗakina na kwanta,wani nauyi naji zuciya tamin da sauri-sauru take bugawa tamkar zata fito daga cikin ƙirjina.




Inajin wayata tana ringing nasan habib ne,sai dai bana cikin yanayin da zan iya ɗaukar waya a yanzu.Haka muka shafe kwanaki biyar cikin wannan tashin hankalin.






A cikin rana ta shida, wani makwabcin mu ya shaida mana,da yankewa su Abba hukuncin kisa ta hanyar harbewa da bingida,kuma har an zartar musu da hukuncin.




Har video yanuna mana a wayarsa, gasu nan kafin a kashe su suna fitowa daga kotu yan jaridu sai tambayoyi suke musu.




Su goma sha ɗaya ne dukkaninsu matasa ne da bazasu ɗara shekaru ashirin da biyar ba a duniya,Abba ne kawai dattijo a cikinsu.




Yana gama sanar da mu umma tace yaya fawas yaje police station,Dan tabbatar da gaskiyar wannan videon.


Can ɗin ma da yaje suka bayyana masa da kotu ta yanke musu da hukuncin kisa kuma,har anzarta da hukuncin akansu.




Dan acikin Wanda suke da plan ɗin yin garkuwa dashi har da ƙwararran engineer ɗin nan masu kamfanin kayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login