Showing 3001 words to 6000 words out of 104857 words
Chapter 2 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
ummul-khair da fawas Ku tashi kuje Ku kwanta".
Duk jikin mu yayi sanyi muka tashi muka fita bayan munyi wa Abba sai da safe.
Miƙewa Abba yayi tare da faɗin"Juwahir nagaji da abinda kike min a cikin gidan nan,daga rana mai kaman ta yau indai na amsa sunana na matsayin miji a gareki to kin daina wannan sana'ar,sannan kuma bazaki ƙara taramin maza a gida na ba".
Wani shewa umma ta saka kafin tace"Sule gidanka ko gidana? kai ko kunyar faɗa bakayi ba?kuɗin hayan dani nake biyansa".
Cike da takaici Abba yake faɗin "juwahir ni kike gaya haka koda yake bazan yi mamaki ba domin Ku mata kunada saurin manta alkhairi,kin manta lokacin dana auro ki duk da kasancewar dangi na basuyi na'am dake ba juwa".
Cikin matuƙar ɗaga murya wanda ya zamto ɗabi'ar ta,a duk sa'in daza tayi magana tace.
"Na faɗa ma sule nace na faɗa ɗin yo sule da miji irinka a gwara babu,idan ka cika dan halak a cikin iyayenka ka ficemin daga gidana sai sanda ka sama zuciyar neman na kanka sa ka dawo,mu cigaba da zaman yanzu kai idan za'a lissafo maza za'a saka a cikine sule".
Kallon ta kawai Abba yakeyi yama rasa me zaice mata a hankali yace.
"Juwahir duniya ce ta tafi gabaruwa iya jima kije kiyi inkina ganin zai haifar miki da ɗa mai ido".
Ficewa yayi daga daƙin ya shigo daƙin yaya fawas har yayi bacci ya same shi,juyowa yayi ya shigo daƙina inajin shigowar sa amma na rufe idona kamar bai bacci dan duk abinda yake faruwa inajinsu.
Zama yayi gefen lamutsatstsiyar katifa ta kallona yake yi sosai yana shafa kaina yana hawaye yace.
"Mama na Allah ya muku albarka keda ɗan-uwanki inason kasancewa tare daku amma dole zan barku".
Addu'o'i yashiga min yashafa min sannan ya fice daga daƙin.
A hankali nabi bayansa da kallo ina ƙoƙarin fahimtar inda maganganunsa suka dosa,umma na tsaye a ƙofar daƙin ta lokacin da Abba ya fito daga daƙina.
Yatsina fuska tayi kana tace "Dan Allah sule inka tafi karka dawo har anaɗe duniya,inka tafi ma ai ni wahala ka ragemin umma ta gaida aisha a sauƙa tsiya lafiya".
Ficewarsa yayi ba tare da ya kalli ko inda take ba,tsaki tasaka tare da komawarta daƙi.
Tsawon Daren wannan ranan ban runtsa ba kamar yanda ban iya,tsayar da ruwa hawayen da ido ke tsiyarwa ba.
Washe gari da wuri muka yi shirin tafiya makaranta, umma na zaune a ƙofar daƙin ta muka fito as usual tare da yaya fawas hannunmu saƙale cikin na juna.
Durƙusawa muka yi muka gaishe ta amma ko ɗago kai batayi,ta ganmu ba balle tasan da mutum awajen.
Miƙewa nayi na ɗauko mana abincin mu a kitchen cikin sauri mukayi muka gama ci.
"Yaya fawas yau tinda na tashi banga abba".
"Haka ne nima naje daƙin sa da asuba mu tafi masallaci amma da mamakina sai ban ganshi ba,amma karki damu my cute angle akwai kuɗi a wajena sai muyi amfani dashi mu tafi makarantar".
"To yaya na" na faɗa tare da sakin murmushi.
Sallama mukayi a umma muka tafi ƙarfe uku saura muka iso gida bamu sama umma a gida ba amma gidan a buɗe muka same shi.
Cire uniform ɗina nayi, nayi wanka nayi salla sannan na shirya cikin uniform ɗin islamiya na fito.
Ina fitowa ma yaya fawas ya fito zai tafi shagon da yake zuwa koyan ɗinki,murmushi na jefa masa cike zolaya ina faɗin.
"Allah my yaya irin kyau haka anya ka duba madubi kuwa kaga irin kyan da kayi?".
Na ƙarishe maganar tare da kashe masa ido ɗaya.
Matsuwa yayi ya shafo ƙuncina tare da faɗin.
"Haba!hibba ta kyau ya wuce wanda kikayi a yanzu na tabbatar ko gasar kyau kikaje,a haka babu abinda dazai hanaki ki cinye gasar".
Turo baki nayi tare da kai masa dukan wasa a kafaɗunsa nace.
"A hakanne zanci gasar kyau yaya fawas?".
Na ƙarishe maganar ina duban uniform ɗin jiki na da har canza launi,suka yi daga ainihin kalar su saboda tsabar tsofan dasukayi.
Ganin yanayi na daya sauya yasa yaya fawas cewa "Sosai ma kuwa ƙanwata".
Dariya mukayi sosai kafin muka fito a tare sa daya rakani,har islamiyar sanna ya wuce shagonsu.
ƙarfe Biyar muka tashi daga islamiya sanda na iso gida har izuwa lokacin umma bata dawo ba,uniform ɗina nacire nayi wanka sannan na fito.
Na fito na shiga kitchen na fara dube-dube kozan sama abinda zanci amma babu komai a ciki,fitowa nayi na nufi daƙin umma amma ƙofar daƙin a rufe yake.
Wani nauyayyan ajiyan zuciya na saka na fito ƙofar gida ina jiran dawowar Abba da yaya fawas.
Can na hango ya fawas cikin sauri na isa gareshi tare da karɓan ledan dake hannun sa, cikin sakin fuska yace.
"Ƙanwata umma bata dawo bane naganki a waje?".
Ya tsina fuska nayi nace" e ya fawas bata dawo ba,Abba ma kuma mai dawo ba".
Kallo ni yayi yana murmushi ya riƙo hannuna kafin ya shiga faɗin.
"Karki damu zasu,dawo ai dare ma baiyi ko ummul-khair ɗin abban ta".
Murmushi nasaka ina sunkuyar da kai na ƙasa daya kira ni da yayi da ummul-khair sai naji kamar Abba ne,domin shi kaɗai ne ke ƙira na da wannan sunan.
Da haka muka ƙarisa cikin gidan tabarma na ɗauko na shimfiɗa mana,sannan na shiga kitchen na ɗauko Kofi na juye kunnun da yaya fawas ya taho mana dashi.
Sannan muka fara sha muna hira,muna zaune umma ta shigo tamkar bataga ƴan Adam awajen ba tasa kai zata shiga daƙinta.
Yaya fawas ne yayi saurin cewa" umma sannu da dawowa".
A hankali ta juyo tare da ƙare mana kallo sannan tace.
"Yauwa fawas sannun ku har ka dawo daga, shagon kenan?".
Cikin jin daɗin yanda umma take masa magana yace"E wallahi umma yau da wuri na dawo".
Nima da fara'ata nake faɗin"Umma tun ɗazu da muka dawo daga makaranta muka samu bakyanan".
Cikin sakin fuska tace "wallahi na fita wata unguwa ne hibba ya makarantar taku?".
Cikin nishaɗi na amsa mata da alhamdulillah umma.
"Yauwa maman abbanta Allah ya taimaka" dukkaninmu muka amsa da amin.
Tashi tayi zata shiga ɗakinta cikin sauri, maganar da yaya fawas ya fara ne yasata juyowa.
"Umma wai yau ina Abba yaje ne tun safe baya gidan nan?".
Kamar bazata amsa ba sai data jima a tsaye kafinta dawo ta zauna tare da faɗin.
"Amma fawas ai kasan gidan nan bana sabane ko?".
A hankali yaya fawas daya jinin jikinsa ya amsa da cewa.
"Kiyi haƙuri umma nasan,da haka dama kawai na tambaya ne naga tun safe baya nan".
Sai data turo ɗaurin ɗan kwallin ta irin ɗaurin da akewa laƙabi da ture kaga tsiya,izuwa gaban goshin ta wanda in tayi hakan ƴan daudun ta da sauran tarin,matan datayi silar rabasu da gidan iyayen su.
Suke mata kirari da"Magajiya kinci dubu sai ceto,kinfi ƙarfi yaro walla sai dai baban yaro ƙadangaren bakin tulu kike abarki ki lalata ruwa,a kashe ki a fasa tulu".
Chewgum ɗin dake bakin ta ta tauna da ƙarfi,sai da tayi wata ƴar ƙara kash!.
Sannan ta fara warware mana zare da abawa abinda ya faru a daren jiya,wasu hawaye marasa control ne nayi sun shiga ambaliya daga idona yana sauɗa akan fuskata.
Harara umma ta watsa min tana faɗin.
"Dalla kaji banza marar tinani to dan ya tafi sai me?,Dama meyake tsinana miki a cikin gidan?".
Kuka yaya fawas yake yi sosai muryansa Ƙasa- Ƙasa yake cewa"Haba!umma Meyasa bakya tausayawa halin da muke ciki ne?, umma mufa ƴaƴankine Abba kuma mijinki ne amma Sam k....."
Watsa masa mari umma tayi hagu da dama ta ɗaura da faɗin.
"Shashasha fawas har kai ka isa ka faɗamin abinda ya dace na aikata?.Gida dai nice mai biyan kuɗin hayan nan dan haka duk wanda baiji daɗin hukuncin,dana yi ba to shima sai yabar min gida".
Tana kawowa nan ta miƙe ta shige ɗakinta.
Ɗaura kaina nayi akan cinyoyin yaya fawas tare da sakin wani irin wahalallan kuka,mai cin rai kuka nake da iya ƙarfina ina faɗin.
"Wannan wani irin rayuwa ne yaya fawas?,Meyasa mu kuma ƙaddarar mu take zuwa a haka?,Meyasa Abba zai tafi ya barmu?,Meyasa umma zata mana haka yaya fawas meyasa yaya fawas?".
Ɗago kaina yayi idanunsa taf! da ƙwalla cikin sigar lallashi yake cewa.
"Hibba ƙanwata ki daina kuka kinji,kukan ki na ɗagamin hankali sannan yana karyar min da zuciya naji tamkar bazan iya ba dan Allah ki daina".
Muryana can ƙasa-ƙasa nace" yaya fawas shikenan fa Abba ya tafi kenan?".
Komar da kaina nayi kan cinyarsa na cigaba da kukana,shima yaya fawas hawaye basu daina zuba daga idanunsa ba haka muka kwana a wajen muna kuka.
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
________________________________________
Free page
Page 0⃣4⃣
Washe gari na tashi da matuƙar zazzaɓi ko makaranta bamuje ba,yaya Fawas ya sanar da Umma halin danake ciki,naira hamsin ta bashi wai yaje ya siyo min paracetamol.
Jikinsa sam babu kozari ya karɓa kuɗin cikin sanyin murya yaya Fawas yace "Umma inaso muyi wani magana dake".
Tana daga kwance tace,"menene inajinka Fawas?".
Sai daya sauƙe ajiyan numfashi kafin ya shiga faɗin.
"Umma dan Allah inason nasani ne ke kika haife mu?, kuma wani laifi muka aikata miki a cikin duniyar nan wanda yasa bakya sonmu?".
Cike da mamaki Umma ta juyo tana watsa masa wani irin kallo kafin tace"Fawas kamar ya bani na haifeku ba?banason surutun banza,ka wuce ka je ka sayo mata maganin".
"Amma Umma muka fa ƴaƴanki ne, amma ko kaɗan mu a rayuwar mu,bamusan daɗin uwa ba haba um....."
Tsawa Umma ta daka masa sai da jikinsa ya ɗau rawa,cikin zafin rai take faɗin" kafice min daga ɗaki Fawas".
Jiki a sanyaye yaya Fawas ya fito daga ɗakin.gefe na yazo ya zauna cike da kulawa yace"Ƙanwata kiyi haƙuri yanzu zanje na siyo miki".
Gyaɗa masa kai kawai nayi sannan ya fice.Haka rayuwa tacigaba da zuwa mana da ƙalubale iri-iri,ga tsangwaman da umma take mana Kullum hau-hawa yakeyi.
Nikam kullum cikin kuka nake,rayuwa duk ta mana zafi gashi bamu da dangi a kusa balle muje wajensu.
Duk dangin Abba a kano suke da zama,ita kuwa Umma duk iyayenta sun rasu inna (kakarta) ma ta Daɗe da rasuwa.
Yaya Fawas kuma dangin mahaifinsa ƴan nijar ne,koda sukazo nigeria a azare suke na jahar bauchi.
Haka muka cigaba da rayuwa abinci ma umma sai jifa-jifa take bamu, ahaka har yaya Fawas ya gama secondary school lokacin ni kuma zan shiga ss 2.
Cikin ikon Allah yasama admission a university of Maiduguri (unimaid),course ɗin daya kasance burinsa cikin ikon Allah shiya samu mass communication.
Nan Umma tace"ita bazata iya cigaba da mana dawainiyar karatun muna,sai dai ɗaya daga cikinmu ya haƙura ta cigaba da biyawa ɗaya".
Yaya Fawas yace "shi ya haƙura zai cigaba da zuwa shagon dayake zuwa koyan ɗinki ni ta cigaba da biya min".
Ranan nayi kuka daya zarce a misalta shi na yadda naka sai naka.Nace" A'a yaya Fawas nina haƙura da karatun kai kayi".
Kamo hannu na yayi yana hawaye yana faɗin"A'a Hibba ke kiyi burin Abba ne,muyi karatu duk da kasancewar Abba ba mahaifina ba amma bai taɓa nuna bambamci tsakani na dake ba,sai yanzu dan bayanan zan shiga tsakanin ki da burinsa my cute angle kiyi karatu ki cikawa Abba burinsa kinji Ummul-khair ɗin Abbanta".
Kallon shi kawai nakeyi ƙwalla nata gudana a saman kunci na, bakina na rawa nace"Nagode yaya Fawas In sha Allah bazan baka kunya ba zan maida hankali ga karatu na".
Shafo fuska na yayi tare da sakin wani murmushi wanda yafi kuka ciwo da raɗaɗi yace "yauwa ƙanwata".
Haka yaya awas ya sadaukar,da burinsa nayin karatu saboda ni nayi.
Burin yaya Fawas ɗaya ne a duniya ya zama dan jarida dan haka,nasa a raina matuƙar ina numfashi a cikin duniya sai na tabbatar da wannan,burin bai mutu ba cikin zuciyar yata Fawas ba.
Lokacin da mukayi jamb mass communication na zaɓa a matsayin course ɗin danake son karanta,a duk choice huɗu na zaɓar institution da jamb ɗin ke bayarwa.
Haka yaya Fawas ya cigaba da zuwa shagon ɗinki,har shima ya gware a sana'ar.
Haka na gama secondary school na cikin ikon Allah na sama admission a yobe state university (YSU),na koma sama course ɗin danake so.
Murna wajen Rabin jikina yaya fawas ba'a magana,dan lokacin tafiyata jami'a tayi,kusan komai yaya Fawas ne ya siyamin hatta sutura sai daya sauya min.Dan yanzu alhamdulilla yana samu sosai a shagonsu.
Ranar dazan tafi tun safe na gama shiri na,na fito da kayayyakina ƙofan gida
Ina tsaye yaya Fawas ya shigo fuskarshi da fara'a yace" A'a ysu student har kin fito"?.
Murmushi na saka nace"E wallahi yaya fawas umma ma nake jira,ta dawo muyi sallama dan tun ɗazu data fita har yanzu bata dawo ba".
"Haba!ƙanwata kinsan sai dare zata dawo,inki kace zaki tsaya jiranta zaki bata lokacin ki tafi kawai inta dawo sai na faɗa mata kin tafi".
Yaya Fawas ya faɗa yana riƙo hannu na.
Nace " To ya fawas amma Abba fa.....".
Cikin sauri yasa hannun sa ya rufemin baki,yana faɗin"Hibba Abba zai dawo gare mu inajin haka ajikina".
Wata leda ya Ciro daga aljihunsa, ya miƙamin Hannuna na rawa na karɓa na buɓe ledar,sabuwar wayace dal! ƙirar Android, kallon shi nake.
Ina tambayar ta waye? Murmushi ya saka kafin yace"Ƙanwata naki ne kwanan nan muna samu ɗinkuna sosai a shago,shine na tara kuɗin da'ake sallama ta na haɗa da wanda umma ta bayar na biya miki registration sannan na miki wannan siyayyar,shine sauran na saya miki wannan wayar dan inki tafi in dinga jin muryarki my cute angle ko bakya so ne?".
Bansan sanda hawaye suka fara zubomin ba,wayar ta burge ni duk da ba wata mai tsada bace hugging ɗin sa nayi cikin kuka nake cewa.
"Nagode yayana Allah ya ƙara buɗi Allah yasaka maka da gidan aljanna,Yaya Fawas kai kaɗai nake dashi a duniyar nan bayan abba na,ina sonka yayana".
Ɗagoni yayi yana faɗin"Hibba nima inason ki,inki tafi ki kulamin da kanki".
Sausauta muryar shi yayi sannan ya cigaba da cewa"Ki rufamin asiri Dan Allah hibba kiyi abinda ya kaiki makarantar nan kinji my cute angle?".
Yanda yayi maganar sai danaji tausayin sa nace" In sha Allah yaya Fawas bazan baka kunya ba"
"Yauwa ƙanwata sannan banda biyewa samari kiyi abinda yakaiki".
Murmushi nayi nace "Yo a ni yaya fawas ko aure zanyi,to sai wanda ka zaɓar min balle har na fara kula wani ba tare da Sanin ka ba".
Shima murmushin ya maido min saboda yanda nayi maganar cike da shagwaba.
Kuɗi ya Ciro daga aljihun sa 10k ya miƙo min tare da faɗin"Hibba ga wannan ki riƙe a wajenki".
Wasu hawaye ne suka cikomin ido nace "nagode yayana".
Share min hawayen ya farayi da hannun shi yana cewa."Ƙanwata ki daina kuka da kinsa yanda nakeji a zuciya na idan naga hawaye na zuba daga idanun ki,to dakin tausayamin ki daina,inki na haka sai naji kamar na kasa riƙewa Abba ke.Yanzu ki tashi ki tafi har yamma ta miki akwai yayan wani abokina lecturer ne a school ɗin munyi magana dashi zai ringa kulamin dake,ga numbern sa bari nasa miki".
Wayar daya bani ya karɓa ya kunna ta yasamin number sannan shima yasamin nasa numbern daman ya sama min sim a cikin ta
Har motor park yaya Fawas ya rakani sannan ya juyo.
Ina isa cikin ysu na kalli fuskar wayata Wanda ya nuna ƙarfe goma da mintin arba'in.
Lalle kam jami'a(freedom life),jama'a kala-kala kowa sai harkan gabansa yakeyi.
Hostel naƙarisa daman yaya Fawas yagama min komai na registration, nashiga room ɗinmu.
Mu huɗune a room ɗin tima,zubaida sai shahida zubaida ƴar gombe ce tima kuwa ƴar geidam ce shahida ce kawai ƴar potiskum.
Sannan itace department ɗinmu yazo ɗaya da ita,Dan tima chemistry department take zubaida kuwa tana political science department.
Sa yamma muka fito zamuje cafterian dake cikin school ɗin,makarantar babba ne sosai Dan nasha kallo.
Tare muka fito dasu tima,indomie mukayi order cikin nishaɗi muka faraci inka ganmu zaka rantse mun jima da nisanin juna.
Cikin haka yaya Fawas ya kirani hira mukayi sosa kafin mukayi sallama.
Hostel muka wuce damuka gama Dan a lokacin bamu fara lectures ba.
Sai da mukayi kwana uku da zuwa sannan muka fara lectures.
Ranar da wuri muka shirya nida shahida muka fito,dan munada lectures ɗin 8:00 to 10:00am sannan zamu fito daga lectures ɗin.
Sosai na maida hankali ga lectures ɗin, lecturer ɗin macece hakan nan kawai naji ta burge ni muna fitowa.
Wayata na ciro daga cikin jaka ta na shiga dialing numbern lecturern da yaya fawas ya bani.
Sai da kiran ya kusa tsinkewa sannan ya ɗaga,gaishe shi nayi ban masa wani dogon bayanin ni wacece ba,yace ya ganeni dama sunyi maganar da yaya fawas ya kwantamin office ɗin sa yace nazo.
Tare da shahida mukaje sai damukayi knocking sannan ya bamu iznin shigowa,yana duba wasu takardu sanda muka shigo.
Zama muka yi har ya gama sannan ya dago ya kallemu,sunan sane ajiye kan teburinsa DR.BASHIR MUHAMMAD AUWAL.
Gaishe muka karayi ya amsa sannan yace "Hibba ko?"
"E itace".
Sannan ya cigaba da cewa"Muyi magana da fawas so duk da ni ƴan a chemistry department,nakewa lectures amma duk abinda ya shige miki duhu ki sanar dani in sha Allah zan yi iya ƙoƙarina".
A nitse nace "nagode".
Cikin yanayinsa na barkwanci Dana karanta yace "sunana bashir".
Taƙaiceccen murmushi nayi kafin nace,"To nagode yaya bashir".
Sannan muka fita,Haka rayuwa ta cigaba da tafiya nidai karatu na nasa a gaba baji ba ƙwauƙwautawa.
A lokuta dama ina tuna furcin ya fawas"HIBBA DAN ALLAH Ki RUFAMIN ASIRI KIYI ABINDA YA KAI KI".
Sam samari basa gabana Dan Bana ma sakar musu fuskar da har zasu min magana,kullum su tima cewa suke.
"Wallahi ke hibba har yanzu baki waye ba".
Bana damuwa da abinda suke faɗi dama wasu daga cikin course mate ɗin mu da suka ganin kamar,girman kai ke sakani yin haka.
Na tabbatar dasun san irin ƙalubalen dana fuskan ta kafin su ganni a cikin wannan jami'ar,da bazan sumin wannan maganar ba.
Bazan taɓa manta wani safiyar asabar ba,tin daga wannan ranar ƙaddarar rayuwa ta sauya.
Ina kwance a hostel shahida tace inrakata ta sayo recharge card doguwar rigar abaya ce ajikina.
Gyalen rigar nayi rolling akaina muka fito,muna tafe muna hira har muka isa wajen.
5 hundred shahida ta Ciro daga Jakarta ta mik'awa Mai shagon tace,"Gashi a bamu card na mtn na Dari bibiyu".
Kallonta nayi nace"Kedawa na ɗari bibiyu?A'a wallahi shahida kibar kuɗin ki karki ɗaurawa kanki wata wahala".
"Haba Hibba babu wata wahala,kedai sai dai inkin Rena ne to".Shahida ta faɗa,Murmushi na saka kafin nace,"To nagode".
Wata mota ce tazo ta wuce ta gefenmu, tayi parking cikin parking space aka tanada cikin compound ɗin school.
Buɗe ƙofar motar akayi tare da sauƙo da ƙafafunsa waje sannan shima ya fito
Milk ɗin shadda ne ajikinsa,tsayin rigar dai-dai gwiwar sa