Showing 66001 words to 69000 words out of 104857 words
Chapter 23 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
kuma abubuwa da yawa".
na ƙariso na zauna ina guntse dariyar dake shirin suɓɓuce min,dan maganar yasira ba ƙaramar dariya ta baniba.ummi ta ɗagota tare da faɗin"kinci gidanku watau faɗa na ma kikayi kewa bani bako?"tayi saurim girgiza mata kaina sai a sannan muka gaishe da ummi ta amsa sannan sayyidd ma mutumina nake masa tsiyar meya kawoshi gida.
ya ɗan gallo min hararar wasa kana yace"kema kin koya sa ido irin na mijin nakin ko,todai sa ido babu kyau ehe".
na saki wata ƙatuwar dariya nace"kaji dashi dai aurar dakai zamuyi mu huta".
yasira tayi caraf ta karɓe zancen tana cewa"wallahi ko budurwa bana tinanin yaya sayyid yana ita".
"ummi ki basu labari an kusa nima a shafa min fatiha"sayyid ya faɗa yana jijjiga ƙafarsa wanda ɗaya ke kan ɗaya.
sai da ummi ta ɗan dara itama sannan tace"todai sayyid ya samo matar aure yanzu ma jiran daddynku akeyi ya dawo asanar dashi".
nan muka shiga zolayarsa a ina ya samota yace babu ruwanmu haka mukata yi,ummi na tambayar mu ina habib mukace mata yayi tafiya.
sai da muka tashi domin yin sallan zuhr sannan nasama damar yin magana da ummi,har ɗakinta na bita tana zaune kan sallayarta tana addu'a sai dana jirata muka shafa addu'ar tare.
sannan nace"ummi daman wata magana nakeson sanar dake"tace"inna jinki hibba"ta faɗa tana naɗe ƙafafunta waje guda.
"ummi cikin kwanakin nan bani da lafiya ina yawan ciwon kai da kuma saka baccin danakeyi,har aman jini inayi shine naje asibiti jiya bayan amin gwaji aka tabbatar min da ina ɗauke da ciwon zuciya,bansanar da kowa ba koda habib bai sani ba domin ina gudun kar yaji ya faɗa wani hali".ina faɗa ina hawaye.salati ummi tasaka sannan ta ɗaura da faɗin"hibba aman jini fa kikace?innalillahi wa inna ilaihirraji'un!gaskiya ya zama dole kisanarwa habib wannan maganar domin ba'a ɓoye ciwo.mussaman ciwon zuciya domin shi yayi sanadiyar rasuwar uwata naga hatsarin dake tattare da ciwon.bawai shan magungunan bane a'a kiyi ƙoƙarin kiga kin cire damuwar dake ranki dan allah hibba".
na sadda kaina ƙasa nace"in sha allah zan sanar dashi amma ba yanzu ba dayake tsaka da samun farin-ciki a rayuwarsa".haɓata ta ɗago tare da faɗin"hibba babu wanda ya cancanci yaji damuwar matarsa sama da mijinta,koda kisan kai kikayi zai nema rufa miki asiri ki ƙarƙafa zuciyarki inya dawo kinema lokacin daya dace ki sanar dashi kinji ƴata?".a sanyaye nace"to ummi zan sanar dashi,sai kuma ɗayar maganar munyi magana da yaya fawas akan jinin dake zuba min yace mu tuntunɓi malamai domin abun yafi kama da sihiri,amma nidai hankali bai kwanta da hakan ba domin a duniya ba tinanin akwai wanda ya damu dani balle rayuwata dahar zaimini sihiri".
"hibba yanzu rayuwa ta sauya ta wuce duk yanda kike tsammani,na jikinka dashi ake haɗa kai wajen cutar dakai kuma zansa a nemo min malamin sai muje ki kwantar da hankalinki kinji,domin hawan jini ba'a fiye son mutum yana daɗa hankalinsa ba".
"to"kawai nace nan tacigaba da kwantar min da hankali na ƙira yaya fawas nasanar dashi yanda mukayi har nabawa ummi wayar suka ƙara tattauna agame da matsalar tawan.
na fito nabarsu suna maganar sayyid na iske yana shirya dinning table,da mamaki fal!a fuskana nace"mezan gani haka ɗan ɗakina kai ne da shirya dinnig ya kuma".
ya saki murmushi haɗi da farfara idanunsa kana yace"to ai girkin ma ninayi inbaki sani ba,tunda na dawo inake girki a gidan nan"
"lalle kam kace ka fara ɗaukan darasi ne tun kafin ayi auren,ashe amarya ta huta dayin girki"na faɗa ina ƙarisowa dinning ɗin sannan na fara buɗe kulolin na farko dana buɗe fried rice wanda yaji vegetable,na biyu kuwa fried chicken ne sai kuma sallad daya haɗa.
na lumshe idon sakamakon ƙamshin daya ziyarci ƙofofin hanci na.na ɗago na masa thurum up ina cewa"weldone ɗan ɗakina".
kusan a tare da juna ummi da yasira suka fito,kai tsaye dinning ɗin suka wuce yasira tace"meka dafa mana naji ƙamshi haka".
"ɗan ɗaki nane ya mana girki"na faɗa ina buɗe musu kulolin."wannan ɗin wai shi yayi wannan girkin? tab!"ta faɗa tana nuno sayyid da hannu.
ya galla mata harara kana yace"to mekika ɗauke ni,ga ummi ki tambaye ta wayake girki a gidan?".
"sayyid shiyake mana girki yanzu,safe da rana harma dinner yarona yanzu sai dai son barka"furcin ummi kenan wanda ya kawo ƙarshen cece-cucen daya ɓarke tsakanin yasira da sayyid.
muka zauna muka faracin abincin sanin damukayi daddy baya ƙasar,sai da mukacinye tas!munata santi sayyid kuwa sai dariyarmu yakeyi yanajin muna ƙara fasa masa kai.
tare da yasira muka tattare wajen muka dawo falo muka zauna,nan umma ke tambaya karatuna nace mata mun gama exams saura muga result.
na tashi zanyi sallan asr ɗakin yasira na shiga nayi alwala sannan na tada sallan,ina iddarwa wayata ta fara ruri na yalwata murmushin fuskana ganin sunan danayi saving nomban habib dashi ya bayyana ɓaro-ɓaro cikin screen ɗin wayar jigona sunan danayi saving dashi kenan.
na ɗaga ƙiran tare yin sallama ya amsa sannan nace"kamar ka shiga raina yanzu nake tinanin na ƙiraka sai kuma natada sallah,ya hanya an isa lafiya?".ya sakar min murmushi yana cewa"lalle muɗin na dabanne tunda har tinanin dake zuciyoyinmu yakanzo ɗaya".murmushin nima na maida masa kana cewa"an isa lafiya ya gajiya?".
"mun iso lafiya gajiya kam akwai shi sosai".
"todai yanzu kaci abinci,kasha magani sannan ka kwanta ka huta da daddare sai muyi magana".ya amsa min har zai gimtse ƙiran nayi saurin faɗin"ka ƙira yasira kuwa?".inajin yanda ya furzar da iska daga bakinsa yace"a'a ban ƙira taba,ki gaishe ta ".
"a'a bari dai na kai mata"kafin yayi wata kalmar na katse ƙiran na fito falo nan kuwa na tarda yasiran tana kallo,na danna mishi ƙira ya katse ya ƙara ƙira na miƙa mata tare mata bayyanin habib ne sannan nayi wucewata ɗaki dan banason sauraran abunda zasu faɗa.
sai da mukayi sallan isha'i sannan muka fara shirin tafiya ummi tace dare yayi bazanyi driving ba sai dai sayyid yakaimu sai ya dawo a taxi.haka kuwa shiɗin yakai mu sannan ya dawo.
ranar a part ɗina muka kwana tare da yasira,tun daga lokacin muke kwana tare da izuwa ranar da habib ya dawo.
muna tsaye a harabar gidan muna jiran dawowar tun lokacin daya sanar damu jirginsu ya ɗaga,malam habu ya tafi ɗauko sa.
tun ƙarar motar da mukaji ta tsaya a ƙofar gidan gate man ya wangale masa ya shigo bakunan mu suka kasa rufuwa.tun kan yagama parking muka isa gareshi dukkanmu muka rungume shi cike da murna da farin-cikin ganinsa cikin ƙoshin lafiya,muna laɓe ajikinsa muka shiga cikin gidan.
a falo muka yaɗa zango muna gaishe yana amsawa daki-daki,sannan na miƙe naje na haɗa masa ruwan wanka yaje yayi a kuma ciro masa doguwar jallabiya fara sol!marar nauyi na ajiye masa na fito.
nan na sama yasira tana ƙara arranging dinner na jonata muka cigaba dayi.muka zauna zaman jiranshi bai ɗau lokaci ba yafito.
muka miƙe muka tarboshi sannan yasira ta zuba mishi abincin nikuma nafara bashi sai dana tabbatar dana cika masa ciki sannan na ƙyale shi,na ɗauko masa maganinsa nabashi yasha.
sannan muna muka zuba namu abincin a plate ɗaya muka zuba mukaci tare da yasira.
haka ranar muka wuni cikin walwala har dare muna hira,sai wajajen ƙarfe goma kana habib ya raka yasira part ɗinta ya dawo,dan a lokacin a ɗakina yake.
ina gaban mirro ina shafe jikina da mai yashigo ɗaki,ta cikin madubin na hange shi.
na miƙe na fara gyara mana shimfiɗa har nagama yana tsaye aƙofar ɗakin duk motsin danayi sai ya bini da kallo da haka na gama gyaran.
sannan na ɗaga masa ido ɗaya alamar ko lafiya?baice dani uffan ba ya ƙariso cikin ɗakin ya zauna akan sofa,na takuwa na zauna kusa dashi ina fuskantarsa nace"hamma inason muyi wata magana dakai amma dan allah kamin alƙawarin bazaka sa abun aranka har ya haifar maka wani ciwon ba".sai daya musguta yace"in sha allah faɗi ko menene inajinki"ya faɗa cike da zaƙuwa dason jin menene.
"ranar danaje asibiti ne daman gaskiyar magana ba ulcer ce ke damuna ba,kamar yanda na faɗa maka hawan jini ne ke damuna domin likitan ta tabbatar mini da hakan"nakai ƙarshen maganar ina sakin kuka mai sauti.
a matuƙar razane ya kamo hannuna lokaci guda ya fara share min hawaye ne,kana yace"ki daina wannan kukan banaso"sai dana tsagaita kukan kafin yajefomin tambayar data ƙara karyar mini da zuciya"meyasa kika ɓoye min wannan lamarin shin bakai naji damuwarki bane ?".
"habib na ɓoye maka haka ne domin banason ganinka cikin wani hali,zuciyata bazata jure ba idan nayi la'akarin dacewa yanzu farin-cikinka yafara dawowa domin kana samun komai awajen yasira ba kamar ni ba dana kasa sauƙe hakkinka.ummi tace nasanar dakai domin kai kafi cancanta daka sani akan kowa,kuma munyi magana da yaya fawas dama ummi akan cewa jinin dayake zuba min mu tuntuɓi malamai dan jinnu ma sunasa irin haka".na faɗa cikin kukan daya soma cin ƙarfina.
rungumo ni yayi jikinsa yana bubbuga bayana yace"ya isa haka ki daina kuka in sha allah zaki rabu da wannan ciwon,sannan zamuje wajen malamai ɗin kamar yanda ummi tace".
ajiyan zuciya kawai nake sauƙewa ɗaya nabin ɗaya har bacci yayi nasarar ɗaukata,ganin haka yasanyi kwantar dakai akan ƙafarsa sannan ya lula duniyar tinani.
hawan jini to meya jawowa hibba irin wannan ciwon?meta nema ta rasa daga gare ni?idan ma akan ɓatan mahaifiyarta take damuwa ai ummi ta zame mata tamkar uwa bada mama ba.tabbas yasan hibba nada matuƙar haƙuri gami da zurfi ciki,aduk lokacin dazata aikata abu takanyi tinanin farin-cikin mutanen dake zagaye da ita.ako ina kuma aban kowani mahaluki zai iya bugun ƙirji yace yayi sa'ar samun nagartacciyar mace abar alfahari ako yaushe.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
________________________________
Page 4⃣4⃣
Washe gari koda na tashi na sama Yasira da Habib sun gama shirya komai na karin kumallo har sun kimtsa ko'ina sai sanyayyan ƙashin turaren dake tashi daga ko wacce kusurwa.
"Anty kin tashi"Maganar Yasira wanda a safiyar wannan ranar shiya fara sauƙa cikin kunnuwana.
"E wallahi yau na makara kadda dai har kin gama girkin?".Sai da taɗan murmusa tace"Hamma ne yayi komai nima kawai ƙarisawa nayi". Na kai dubana ga Habib yadake tsaye yana jera plate a dinning ɗin kamar baya sauraron abunda muke faɗi. Na gaishe shi sai a sannna ya ɗago ya amsa sannan na ƙariso muka gama tare mukaci abinci.
A falo muka zauna domin Habib ya buƙaci tattaunawa da dukkanmu bayan gama cin abincin damu kayi.sai da yayi gyaran murya yana mai ƙara fuskanto mu kana yace"Yasira munaso mu sanar dake wani jarabawar da Allah ya ƙara jarabtar mu dashi na ɗaurawa Hibba cutar hawan jini ga kuma matsalar datake ciki na jinya tun daga ranar da tayi ɓari,mun yanke shawara kamar yanda Ummi ta shawarce mu akan mu tuntuɓi malamai akan matsalar jinin kuma yau zamuje mu sameta domin nemawa kanmu mafita".
Yasira da tunda ya fara maganar tagama ruɗewa tace"Anty muna gida ɗaya dake amma ki kasa sanar dani meyasa".na riƙo hannunta inacewa"Banason na ɗaga miki hankali ne shiyasa ban sanar dake ba amma yanzu ba gashi kinsani ba".
"Allah yabaki lafiya,Allah yasa kaffarane ga zunubanki"ta faɗa cikin kukan dake saɗɗanta.duk muka amsa da Amin kafin muka tafi kowa yaje ya shirya muka fito na ɗauko maganin Habib nabashi yasha tare da tambayata nasha nawa maganin na ammsa masa da e nasha,sannan muka tafi.
Tunda muka hau titin zuciyata ke bugun tara-tara sau tara har muka isa,yana gama parking muka fito sanna muka wuce cikin gidan.
Anan muka tarar da Iya da Granny sunzo,muka gaishesu Yasira na tambayar Iya yaushe sukazo?tace jiya da daddare kuma a ya zasu koma daman sunzo gaisuwar ta'aziyane na wata ƴar-uwan Iya data rasu anan katsinan.
Habib ya sanar da Granny dalilin zuwarmu itama ta amince akan muje wajen malamin,Iya tace"akwai wani maganin gargajiya inhar sihiri ne to cikin kwana bakwai da yardan Allah zai karye ko za'a gwada shi?".
Ummi tace"to Iya sai a gwada mugani ko Allah zaisa mu dace".Habib yace"Mungode iya"
Jikina duk yagama yin sanyi na ƙara da cewa"mungode Allah yasaka da mafifin alkhairi"duk sula amsa da Amin kafin Iya ta shiga lissafo abubuwan da za'a buƙata.ganyen tunfafiya ne guda uku sai kuma nonon shanu mai kyau Ummi tace Sayyid yaje ya sayo nonon shanun ganyen tunfafiyar kuwar almajirai aka bawa naira Dari suka tsinko mana da yawa.
Iya ta wanke ganyen tunfafiyar tasa a tukunya tare da nonon shanun yayita tafasfasa,sannan ta sauƙar daya huce aka juye shi acikin wani tsaftataccen bokati tace da safe kafin naci komai nafara shansa.
Granny tace Habib yabarni nayi kwana biyu a gidan saboda maganin danake sha,haka kuwa ya barni suka tafi da Yasira duk safiyar Allah wannan ruwan maganin shike fara sauƙa a maƙoshi ne.Na ƙira Yaya Fawas nagaya masa halin da ake ciki yace incigaba da shan maganin har muga abunda Allah zaiyi.
A rana na uku danayi ina shan maganin da safe Habib da Yasira sukazo,duk muna zaune a falo ana gaisawa Iya ta kawomin ruwan maganin na karɓa nasha inajin yanda yake sauƙa yanabin maƙoƙarona izuwa cikin ciki.naji jikina yaɗauki rawa zuffa ta shiga karyo mini daga kowace kusuurwa jikina take nafara kwara mai a wajen.Duk sukayo kaina suna min sannu sosai nake aman tamkar zan amaryar da hanjin ciki ga aman kore shar!dashi tun inayi daga zaune Iya da Ummi suna riƙe dani har na durƙushe inayi daga kwance.
Suka ɗauke ni suka kaini ɗaki banɗaki suka shiga dani dana na galabaita sosai,ƙafafuna ma jansu kawai nakeyi dan jinsu nayi kamar a jikina sukeba.suka gyara min jikina sannan suka kwantar dani a gado ai kuwa banfi minti uku ba bacci ya tafi dani.dai-dai anan Habib ya shiga ɗaki gani na a kwance yasashi tambayar Iya ko lafiya?.
Cikin tsantsan murna daya saka ɓoyiwa akan fuskarta da tsofa suka fara bayyana tace"Ai babban mutum sai dai mu godewa Rabbi domin sauƙi yasamu,tana tashi daga wannan baccin daman cikin biyune dole tayi ɗaya kode amai ko kuma zawo".
Yasira da mamakin furcin Iya ya gama cikata tace"Hakan yana nufin kenan sihiri aka mata?to waye yayi mata hakan alhalin ita kowa nufinshi takeyi da alkhairi babu abunda ke zuciyarta face imani da tausayi".
"Ai Yasira yanzu rayuwar duniya ta lalace lamarin sai dai muce innalillahi wa inna alaihir raji'un,kufito mu barta har zuwa lokacin dazata farka"furcin bakin Granny kenan,kamar jikinsu babu laka duk haka suka fara ficewa daga ɗakin Habib yace zai zauna tare dani har na farka.
Zazzafar ajiyar numfashi yayi lokacin da duk suka gama fice daga ɗakin,maganganun Yasira na dawo masa cikin kunnensa tabbas abun yakai ayi mamakinsa sihiri wa yayiwa Hibba hakan?kuma meye dalilinsa na aikata hakan a gareta?.
A iya zaman dasuka yasan bata da abokin faɗa balle ace har sunyi gaba da wani.da wannan tinanin ya iso gaban gadon ya zauna akan kafet ɗin dake yashe kusa da gadon akan gwiwoyinsa ya zube ya kamo hannuna yana ƙarewa fuskata kallo.ya zama dole ya gano wanda ya aikata hakan domin inbaiyi hakan ba zuciyarsa bazata rayu cikin salama ba.
Bazan iya ƙidaye awannin danayi ina bacci ba,sai lokacin dana buɗe ƙiran sallan magrib shine abunda yafara sauƙar mini cikin kunne.na fara ƙoƙarin tashi a hankali duk jikina ciwo yake min akan sallaya na hango Habib ya idar da sallah yana addu'a ganin na fara tashi yasashi fasha addu'ar da sauri ya nufoni.
Tare da tallafar kafaɗata ya jingina ni acikin pillow lumshe idanuna nayi wasu sirarun hawaye nabiyo gefen kuncina.
"Ba kuka zakiyaba Hibba kamata yayi ki godewa Allah daya kawo mana sauƙi kuma mafita ga lalurarki".
Muryan Habib kenan dana tsinkayo su a tsakar kaina,nayi saurin ware idanuna ina tsaidasu akan fuskarshi ko ranar dana fara ganinsa a office ɗin Yaya Bashir ban masa irin kallon nan ba.
"Ki tashi kiyi sallolin dake kanki"ya kuma faɗa yana riƙe da hannuna,namiƙe na shiga bathroom.wasu tinanin nika suketa ziyartar kwakwalwata marasa kan gado,da haka nafara wanke fuskana sannan na zare kayana domin ina buƙatar na watsa ruwa ajikina.
Pant ɗin dake jikina kodana cireshi naga jinin ya tsaya cak!na shiga hamdala ina ƙara godiya ga ubangiji tsabar murna har ƙwalla sai danayi.
A gurguje nayi wanka tsarki sannan na ƙarayin wani wankan nayi na fito,ban iske Habib a ɗakinba wanda nake zaton ko yafita masallacine dan sallan magrib ma a ɗakin naga yayi.
Ko mai ban tsaya murzawaba na saka kayana na ɗaura long hijab ɗina asaman sa na tada kabbara,sai da nayi duk sallolin dake kaina sannan nayi isha'i sosai nayi addu'o'i acikin sujjadata ta ƙarshe.sannan nayi sallama ina gamawa na shafa addu'ar na jawo wayata na danna ƙiran Yaya Fawas yana ɗauko ko gaisuwa ba muyiba na fara sanar dashi Allah ya kawo min sauƙi ina labarta masa ina hawayen farin-ciki.
Shima haka nan murna ta gama cikasa ba abunda yake faɗi illah kalmar ALHAMDULILLAH,har mukayi sallama akan zai ƙira su Baffa ya sanar dasu dan Inna ba ƙaramin damuwa ta shiga ba.
Ko zare hijabin kaina banyi ba na fito falo,nan na tarar da kowa hadda Daddy wanda ko dawowarsa banji ba,na ƙariso cikin falon ina gaida da Daddy ya amsa fuskarsa cike da ni'ima.Ummi ce ta fara faɗin"Hibba yanzu yaya kike jin yanayin jikin nakin?"na sadda kaina ƙasa nace"Ummi Alhamdulillah banajin komai hatta jinin ma ya tsaya".
Duk suka haɗa baki wajen furta Alhamdulillah haƙiƙa Allah shine abun godiya.
Yasira ta nufo ni tare da faɗawa jikina na rungumeta ina kukan murnan daya zomin,Ummi ta ɗagota daga jikina tare da cewa"Meye na kuka kuma ku kuwa?ai godiya zaku yiwa Allah daya kawo mana ƙarshen wannan masifa data samemu gabaɗaya".Granny ta ɗaura da faɗin"Haka ne kam sai dai mu godewa Rabbi,haƙiƙa Allah gwamin hikima ne".
Na kai hannu na sharce hawayen fuskana,Habib tun ɗazu dayayi sujjada har yanzun bai ɗago ba.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________
Page 4⃣5⃣
Dukda kunnuwa na basa jiyo mini abunda yake faɗi cikin sujjadar amma na tabbatar godiya kawai yakeyi wa ubangiji daya nuna mana wannan ranar muna masu rayayyu.
Ummi dake nake zaune ɗan nesa da ita,ta dafa kafaɗata nayi figigi na ɗauke idona dasuka ƙara kawo ruwar hawaye daga kan Habib.
Na sunkuyar da kaina ƙasa sai a sannan Habib ya ɗago yana ƙara jere godiyarsa ga Allah sarkin da ikonsa yake akan komai da kowa tare dukkaninmu muka shafa addu'ar sannan ya taso ya zauna a