Showing 54001 words to 57000 words out of 104857 words

Chapter 19 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7278

mai kaurin da Ummi ta haɗa mini,ina gama sha zuffa ta karyo min Ummi da daman tasa ƴan aiki su kawo ruwan zafi ta haɗa min ruwan wanka Inna tamini wankan jego kamar yanda akewa ko wacce mai jego.
Sai wajajen ƙarfe goma sannan Daddy,Sayyid,Yaya Fawas,Ummi,Iya,Hajja da kuma Habib da Yasira suka tafi sai dasuka sauƙe Hajja a gida sannan suka wuce gidan Daddy hadda Habib ɗin.
Granny da Inna su suka kwana a wajena,washe gari kuwa tun dana tashi naga nayi wani masifan kumburi kowa yazo sai yayi mamakin irin kumburin danayi.
Likitan yace ba matsala bane kawai rashin jinina ne yayi ƙasa aka ɗaura ni akan magungunar ƙarin jini,bayan an ƙara sakamin roba biyu na jinin wanda Habib yabada ɗaya yaya Fawas ya bada ɗaya dansune jininmu yayi dai-dai danasu.
Kwanana bakwai a asibitin aka sallame ni,kwananmu ɗaya a gidan Daddy muka koma gano tare da Inna da kuma yaya Fawas.
Habib da Sayyid su suka kaimu nan naga ansauya fasalin gidan Baffa an zamanatar dashi Inna ke fesamin ai Habib ne ya ƙara musu gidan ya saye gidaje biyu na makwabtansu ya haɗe ya ƙara musu a nasu.
Ɗakuna manya-manya guda huɗu ne akayi acikin gidan dukka suna kallon juna,sai kuwa wasu biyu da akayisu a waje kamar shaguna,dana shiga ɗakin Inna kuwa ko ɗakin wata amaryan iyakaci dan ya zuba mata sabbin gado da kujeru hadda da labulaye.
Ga simintin dake malale ko'ina a tsakar gidan,duban Inna nayi cike da mamaki nace"Inna duk wannan aikin yaushe akayishi bansani ba?".
"Lokacin dakika sama ciki daya ƙira Adamu ya sanar dashi,bayan kwana biyu kuwa ya turo Sayyid da masu aikin ginin aka fara ya kama mana wani gidan haya anan kusa muka koma kafin a gama"Inna ta faɗa fuskarta cike da alhinin zubewar cikin.


Nima shuru nayi ban ƙara cewa komai ba,ji danayi Baffa na ƙwalamin ƙiran na fito muyi sallama dasu Habib zasu wuce,yasa na fito bayan na zige akwatin kayana da Yasira ta haɗamin na ciro maganin Habib na fito.
A zaure mukayi kiciɓus da Baffa da yaya Fawas suna shigowa na matsa musu suka wuce sannan na fita,da sallama na ƙarisa inda na hangosu suna tsaye da Sayyid.
"Muzamu tafi saikin ƙara warwarewa sannan nadawo na ɗaukeki dan Allah matata ki kula da kanki"cewar Habib.
Ƙasa nayi da idona kana nace"In sha Allah,Allah yakiyaye hanya ga magungunanka kana sha akan lokaci"na ƙare maganar ina miƙa masa ledar maganin ya karɓa sai faman faɗin yake zaiyi missing ɗina.


Na katseshi da cewa "naga yanda ka sauyawa su Inna gida,mun gode Allah ya ƙara buɗi"yace"Amin aduk yiwa kaina Baffa kamar uba yake agaremu".
Nace"Hakane shine ko ka sanar dani sai yanzu nakeji a bakin Inna".


Haɗe hannayensa yayi guri duga alamar neman afuwa har sai sayyid yafara yimana dariya,kafin na rakasu suka shiga motar.
Wasu kuɗi ya miƙo min wanda bazan iya ƙidaye yawansu ba yace na ƙire a hannuna kafin ya ƙara zuwa,na masa godiya sannan suka tada motar har sai da suka ɓacemin daga gani kafin na koma gida ɗakin Inna na wuce nayi kwanciyata dan har izuwa wannan lokacin ban sama tsarki ba.
Sai yamma lilis na farka na fito waje ganin missed call ɗin Habib yasa na shiga dialing nombarsa,katse ƙirar yayi sannan ya ƙira.
Na amsa na gaisheshi tare da tambayarsa sun sauƙa lafiya,ya amsa min da E sosai mukayi hira kafin yabawa Granny wayar mukayi sallama da ita dan itama yau zata koma Damaturu.
Bayan munyi sallama da Habib na fito waje nan na tarar da Inna da Yaya Fawas na jonasu muka cigaba da hirarmu,kwanana uku da dawowa gidan Baffa yaya Fawas ya koma Azare.
Innace tun zuwata gidan Baffa banga koda wulgawar Hajara ba to banyi ƙarya ba,balle kuma tamin jajen abunda ya faru.Inna na tambaya ko bata nan ne?tace min tana nan kawai dai wani baƙin halin yanzu ta dasawa kanta na zama a ɗaki,yayin da Adamu shima yanzu komai za'a faɗa akanta baya gani.
Dariya maganar Inna taso tabani watau Inna mafa irin uwayen miji masu tsaurin nan ne,abinda yaragewa ƙaya zaƙi shine Hajararma ba daga baya ba.
Tun ranar danayi ɓari jini bai bar zuba daga jikina ba tun ina ɗaukar abin kamar wasa har ya fara bani tsoro,satina uku da kwana biyu cur a gano hakan kenan yana nuna nayi wata ɗaya da kwana uku dayin ɓarin.
Inna nasamu da maganar tace min itama abin ya bata mamaki danko haihuwa nayi ya kamata ace jinin ya tsaya zuwa yanzu,dan wasu basayin arba'in ma jinin yake tsaya musu.abin dayafi sanya mini tsoro acikin raina shine yanda jinin yake zuba sosai innace sosai ina nufi sosai bana wasa ba,dan daga safe zba uwa yamma ina ƙarar da pant goma sha uku zuwa sama.
Wasu jiƙe-jiƙen gargajiya Inna ta haɗamin inasha amma babu abunda ya sauya,ganin haka yasa nafara sallolina sannan na ƙira Habib na sanar dashi yace na shirya zaizo yakaini asibiti sannan indaina shan jiƙe-jiƙen itacen gargajiya.


Nasanarwa Inna haka na shirya kayana na fito dasu tsakar gidan ina jiran zuwan Habib,sai ranar na ɗaura idanuna akan Hajara tana zaune ƙofar ɗakinta tana ɓarar gyaɗa wata shewa tasaka hadda da tafa hannu kamin ta aiko min da wani mummunan kallo Inna ta kalleta tace"Allah ya shirya".
Kamar jira takeyi ai kuwa ta miƙa tare da faɗin"Amin Inna ai masu neman shiriyar sunada yawa cikin hadda jikartaki dakike rawar ƙafa akanta,yo waya sanima ko maganin zubda ciki tasha shiyasa jinin ya ɓalle mata za'ayi wata rufa-rufa".


Inna data gama zuwa har wuya tsabar haushi ta ɗaga hannu da niyyar zagawa Hajara mari,Baffa da shigowarsa gidan kenan yayi saurin riƙe hannun Inna data ɗaga.
"Inna dan Allah kiyi haƙuri ki ringa sanyawa zuciyarki salama".cewar Baffa


"Ai daka barta ta maren wallahi dasai naga abunda ya turewa buzu naɗi,dan kuwa zan nuna miki nima inada gata acikin garin nan".


Martanin Hajara kenan tana karkaɗa ƙudu "Hajara nagodewa Allahn dayayi ni kuma yayi Hibba,gwara ita ai tunda har tasama cikin ya zube keda tun kafin a haifo ta duniya akayi naki auren ai har rana mai kamar tayau ko ɓatan wata acikin gidan nan baki taɓayi ba,in fitsari ya zama abun banza yo kaza tayi mana"cewar Inna tana hucin ɓacin rai.
Kukan mafirci Hajara tasaka tana cewa"Malama kanajinta tana min gorin haihuwa?"tana kawowa nan ta juya fuu tayi ɗakinta yayin da Baffa fa rufa mata baya yana ƙiran sunanta.


Nidai sakeke na tsaya ina kallonsu sannan na shiga laushin zuciyar Inna,muna cikin haka Habib ya ƙira wayata yana cemin yafito ya iso.Inna kam cewa tayi na tafi Allah ya kiyaye danko fitowa batayi sun gaisa da Habib ɗinba haka nan har natafi Baffa bai fitoba.
Nace Habib Inna da Baffa sunje gaisuwar ta'aziya awani ƙauye,sannan muka tafi inata juyayin maganar Hajara acikin raina wani bangare na zuciyata kuwa cike yake da mamakin sauyawar da Baffa yayi.
Tun kafin mubar kano mukaje asibitin Malam Aminu kano bayan munyiwa likitan bayanin matsalar dake tafe damu yace mana babu wani damuwa sannan ya rubuta min wasu magunguna mukaje pharmacy muka saya muka wuce.




UWATACE SANADI


Tsarawa/rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


_____________________________________


Page 3⃣7⃣


Nan yake sanar dani cewa Maryam matar Bashir ta haihu,da haka muka isa koda mukaje ɗaki na wuce nayi kwanciyata nan kuwa baccin gajiya ya kwasheni,Habib daman yana ajiyeni ya wuce office.
Sai yamma na tashi na shiga bathroom na gyara jikina sannan na ɗauro alwala na fito zuhr da Asr na haɗa nayi atare dan banyi zuhr ba.
Ina iddarwa na ƙira Maryam bugu biyu ta ɗauka,muka gaisa sannan na shiga yi mata murnar ansama ƙaruwa.


Inata zolayarta Maman baby boy ina gimtse ƙirar ta turo min ankon dasuka cike na sunar har photon baby boy ɗinmu sak!Dr Bashir kamar kara aka tsaga.
Fitowa nayi naje sasshin Hajja inajin ƙaunar yaron har cikin raina, tana gani na ta washe baki gami da faɗin"Hajiya na leƙa ɗazu ai naga bakya kusa".
Sai dana zauna kan kujerar dana gani yashe a tsakar gidan,sannan na gaisheta ta amsa da fara'arta tana tambayata ya nabaro mutan gano,nace mata lafiya kalau duk suna gaishe ku.
Nan muka cigaba da hirarmu har nake sanarda ita har yanzu jini bai tsaya mini,sai data ƙire haɓa kafin tace"wohoho hajiya ai kuwa dai ki nema magani,dan irin haka ya taɓa faruwa ga ƴar yayata wacce muke uba ɗayada ita,haka itama daga yin ɓari sai datayi wata shidda cur!a cikin jini.Da aka dage da neman magani aka gano ashe mayune sukayi ajiya a mahaifarta"
Gwalo idanu waje nayi ina cewa"Kai lalle tasha wahala,Allah ya shiga tsakaninmu dasu".


"Amin amma kema dai ki dage da neman magani,dan irin haka ba'a zama"cewar Hajja.
Sai dana numfasa kana nace"Nima abin ya soma damuna amma muje asibiti anbani wasu magunguna kuma bazaiyi a haɗa maganin asitibi dana gargajiya a lokaci guda ba".
Taɓa baki Hajja tayi tace "Amin amma magunguna asibitin nan kune dai yaran zamani kuka yarda dasu,amma mukam munfi gane mu sassaƙo itace da kanmu mu haɗa abun mu".
Dariya maganarta taso bani ai kuwa nasaki dariyar har da riƙe ciki,ta miƙe tana cewa cikin harshen fulatanci"Allah ya shiryeki da abun dariya bayamiki kaɗan".
A wajen Hajja na wuni sai da Habib ya dawo sannan na mata sallama na tafi,bayan mungama cin abinci na nuna masa ankon.ranar duk yanda Habib yake cikin matsuwa haka muka sawa ranmu dangana dagani har shi,saboda jinin dayake zuba daga jikina har izuwa yanzu.
Washe gari na leƙa makaranta course mate ɗinmu sukayita min gaje abun ya faru,dan inada jama'a sosai a makaranta duk ba banfiye sakin fuska ba,tare da addu'ar Allah ya kawo wasu masu abarka.
Banɗeba na dawo dan,a ranar zamu je damaturu gobe sunar Maryam ina dawowa na shirya kayana set biyu a cikin ƴar ƙaramar jakata,na fito nayiwa Hajja sallama ta takoni har harabar gidan tana min addu'ar Allah ya kiyaye.


Dai-dai wannan lokacin motar Habib ta shigo,nasa kayana sannan muka ƙarayin sallama da Hajja muka tafi,bayan mun biya ta gidan Ummi.
Gab da ƙiran isha'i muka isa cikin damaturu gidan Granny muka nufa,part ɗinta muka shiga nan kuwa muka sameta tana kishingiɗe tana sauraron tafsirin karatun da akeyi a Africa TV2.
Amsa sallamar damuka shigo da ita tayi tana ƙara ƙawata fuskarta da kyakykyawar murmushin gefen baki,ƙarisowa mukayi muka zauna sannan muka gaishe ta ta amsa tana cewa "kunzo sunan kenan?".Habib yace"E wallahi".


"Hmm ikon Allah kenan kema wataƙil yanzu da cikinki,ya kusa wata bakwai"cewar Granny tana tashi daga kishingiɗewar datayi.Sunkuyar da kaina ƙasa nayi ba tare danace da ita komai ba.tashi tayi tasa aka kawo mana abinci mukaci sannan muka wuce part ɗinmu.
Kamar dai ko yaushe yau ma babu abunda ya shiga tsakani na da Habib,washe gari kuwa muka shirya tafiya suna hadda Granny,a ƙofar gida wajen ƴan raɗin sunan dasuka fara taruwa,Habib ya zauna sai faman yiwa Bashir tsiya yakeyi.
A falo muka iske Maryam ana mata kawlliya,nan na lura da shaddar dake jikinta irin wanda ke jikin Bashir ne anko sukayi,gefenta na zauna bayan na gaida taron matan dana samu a falon.


Rusunawa Maryam tayi tana gaida Granny ta amsa sannan wata dattijuwar mata ta miƙowa Grannyn yaron,ankona Maryam ta tashi ta ɗauko mini wanda nace mata daman ta bayar a ɗinka min.
Ɗinkin doguwar rigace sosai aka ƙawata ɗinki da stone sai sheɗi sukeyi,na shiga ɗaki na saka sannan nima mai kwalliyar taɗan shafa min hoda.
Dai-dai lokacin dana fito naji maroƙa nacewa"Alhamdulillahi yaro yaci suna Abubakar,Allah ya raya sadiqu".


Taɓo maryam dake kusa dani nayi nace"Sunan Abbanki aka saka kona Abban Bashir?"murmusawa tayi kana tace"sunan Abban Habib dai surikinki".
Shaf na manta dasunan mahaifin Habib,Abubakar ne sai danaji ta faɗa na tina.
Granny kam tun dataji bakinta ya kasa rufuwa,sai sawa Bashir Albarka takeyi ba adadi,a waje kuwa koda Bashir ya sanar da Habib cewar Sunan Abbanshi yasaka rungumeshi kawai yayi dan daɗin yaji ya tsirka masa ba kaɗan bane,a ranshi kuwa yana girmama halacci irin na Bashir tabbas duk ɗan halak baya manta alkhairi kome ƙanƙantarsa.


Da yammaci kuwa aka gabatar da ƙwarya-ƙwaryar walima da akayi acikin harabar gidan,Granny kam har izuwa yanzu bakinta yaƙi rufuwa jitakeyi kamar wannan ne farkon takwaran da aka fara sanyawa mijin natan.
Haka taron suna ya watse lafiya aka sanyawa yaron laƙabi ABBUL-KHAIR sunan da za'a ƙiranshi dashi.
A Falon Granny muka yada zango damuka dawo,nan nake tambayar Granny alaƙarsu da Bashir dan izuwa yanzu zuciyata ta fara rayamin suna da wata alaƙa tsakaninsu mai ƙarfi bayan abokatan su da Habib
Sai data saki murmushi wanda yaƙara cika fuskarta da kwarjini kana tace"Babu wata alaƙa tsakaninmu ta nisa kota kusa,Shi Bashir ɗan asalin jahar maiduguri ne almajiranta ya kawoshi cikin damaturu,lokacin tun iyayen Habib sunada rai yake zuwa bara a gidan nan da haka har mukayi sabo dashi a lokacin shekarunsa basu ɗara na Habib ba.haka dai shaƙuwa ya shiga tsakaninsa da Habib har marigayi ya sashi a makaranta bayan ya nema iznin daga malaminsu ya amince,Tun daga lokacin cinsa da shansa,makarantarsa hatta suturansa a gidan nan yakeyinsu tare sukayi sauƙar alqur'ani da Habib kuma sukacigaba da karatunsu har izuwa matakin jami'a har ya sama aikin a YSU,kuma muka cigaba da zumuncinmu dashi harma da danginsa dan auren Habib ma duk sunzo".


Tunda Granny tafara warware mini wannan kundin tarihin tanamin dalla-dalla na sake baki ina binta da kallo,Iya tace"Ai Bashiru kam ba daga nan ba indai kirkine".
Anan mukaci abinci sannan muka wuce part ɗinmu bayan munyi sallah,shirin kwanciya mukayi na lura da Habib dayake cikin matuƙar buƙatuwa amma babu damar yin hakan,haka muka kwanta bayan na tabbatar da yayi bacci na tashi na shiga toilet naci kuka matuƙar kuka har saida numfashina ya fara ƙoƙarin sarƙewa,alwala na ɗauro na fito na iske shi zaune akan gadon ya jingina bayansa a jikin pillow idanunsa har wani ƙanƙancewa sukayi,ya zubosu saitin ƙofar banɗakin.


Saurin kai hannu nayi na share hawayen dake sauƙar har saman tudun wuyana,na wuce zan ɗauka sallaya batare dana ƙara kallon inda yake ba.Har na shimfiɗa sallayan ina faman saka hijab yamin ishara da hannunsa akan nazo.
Sai dana gama saka hijabin na tako a hankali na zaune a gefensa,riƙo hannuna yayi ya gyara zamansa ta yanda yake fuskanta sosai har munajin bugun zuciyar juna.
Mun ɗau tsawon wasu daƙiƙun da basasu gaza gomaba kafin yace"Meyasa kike ɗaurawa kanki damuwa akan abinda,daga ni har ke bamu da iko ko kuma damar sauya shi,KADDARA CE(Littafina mai zuwa in sha Allahu).sai muyi ƙoƙarin karɓarta aduk yanda tazo mana".
Sai daya sau-sauta muryarsa tare ƙara karfin riƙon da yayiwa hannayena dasuke saƙale cikin nasa kana ya ɗaura da faɗin"Matata ban aureki dan ki kasance a cikin kukaba,ban raboki da danginki dan haka ba".
Cikin kukan dayake fizgata nace"Ba yarda da ƙaddarar data same mune banyi ba illa iyaka ina tsoron karna jefaka cikin wani hali".


Muzgutawa yayi yana shafo kaina kafin yace"babu abinda zai faru da yarda illahu,kedai ki tabbatar kina shan magungunanki akan ƙaƙida,sannan ai ni yanzu ba abin tausayi bane domin zuciyata tayi ƙarkon da zata iya jure koma menene shi farinciki ko akasin sa".
Kwantar da kaina nayi ajikinsa lokaci guda naji duk damuwata sun kau,inajin wani farin-ciki na ratsa jini da jijiyoyin jikina.
Tashi mukayi tare yashiga bathroom yayi alwala sannan,ya fito mukayi sallan tare kana muka kwanta.
Washe gari muje kasuwa da Granny da Iya muka haɗu kayan takwara sosai,sannan muka wuce gidan Bashir muka kai danginsa mutan maiduguri sai sanya albarka sukeyi.
Sannan muka dawo gida muka fara shirin komawa katsina saboda jarabawar da zamu fara cikin satin nan,muka tafi tare da addu'ar Granny da Iya agaremu,sai dai koda wasa ban bari Granny ta fahimce inada matsala ba,dan ina sallata tunda nayi tambaya a wajen wani malami yace mini ya halalta nayi salla,dan jinin ya zama jinin ciwo sai dai na nema magani ba haka kawai zan zauna ba, ko Ummi bata sani ba kuma banajin Habib ɗinma ya sanar musu.


Sha ɗayan dare ta gota muka shigo cikin katsina,a gajiye na shigo gida na watsa ruwa sannan nabi lafiyar gado.
Washe gari Habib ya sauƙe ni a makarantan,wuni nayi cur!a cikin makarantar saboda akwai test ɗin da akayi bana nan sai dana tsaya nayi clearing ɗinsu kafi na dawo gida,sai dana leƙa sashin Hajja na tarar ma batanan sannan na shiga ciki.


Haka Abubuwa suka cigaba da tafiya wasa-wasa har na shanye magungunar da aka ɗorani akai,tashin hankalina yafi na baya dana zaune na lissafa nayi wata uku da ƴan kwanakin dayin wannan ɓarin amma har yanzu jini bai tsayaba.
Muka ƙara komawa asibitin likitan ya shawarce mu damu gwada na gargajiya,dan yafi zaton aljanune suka haddasa mini faruwar hakan,ba'ason raina ba Habib ya sanar da Ummi dan anema min magani,sosai ta dage wajen ganin tayi hakan nasha magunguna jiƙe-jiƙe bazasu irgu ba amma babu abunda ya sauya.hatta Inna ma bata fasa aiko min dasu maganinba haka nan ma Hajja tanayi nata ƙoƙarin da kuma Anty Amina.
Ko da maƙiyin mune yaga Habib sai ya zubar masa da ƙwalla saboda halin daya shiga,ga wani uban ramar dayayi har kwanciya yayi a asibiti saboda cikin mara.ganin hakan Granny tace a ɗaura aurensu da Yasira kafin ni kuma Allah ya kawo min sauƙi.
Ranar nayi kuka na fitar hankali domin inason Habib so matuƙa,na ƙira Yaya Fawas na faɗa masa lallashina yayi sosai tare sa shawartata akan na cigaba da addu'a in wannan auren alkairine Allah ya tabbatar da alkhairin dake cikinsa.
Satikai biyu aka sanya biki duk wani labarin bikin a wajen Sayyid nakejinsa,dan har yanzu Habib ɗin bai faɗa min komai ba,wanda zuciyata take hashasho min nauyi maganar ta masa wajen furtawa,haka nan ma Yasira konaje gidan bata yarda mu haɗu.


UWATACE SANADI




Tsarawa/rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam




___________________________________________




Page 3⃣8⃣




Ranar ina makaranta munfito daga lecture na zauna akan kujerun dake cikin makarantar,abin duniya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login