Showing 81001 words to 84000 words out of 104857 words

Chapter 28 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7342

ɗin muka sanya cikin basket muka nufa part ɗin Yasira.
Basket ɗin dake riƙe a hannunsa yakai kan dinnnig ya ajiye sautin kukan Yasira kunnuwana suka fara jiyomin ƙasa-ƙasa na ƙara ware idanuwa a falo don ganin inda sautin ke fitowa kusan a tare dukkanmu muka nufi ɗakin da ɗan sautinmu har ina ƙoƙarin rigashi shiga.
Bathroom na wuce kai tsaye inda kukan ke fitowa tana nan zaune daɓas!a ƙasa tana rero kukanta na saki salati da sallallami na ɗagota ta wanke fuskarta muka fito falo Habib keta jera mata sannu sannan ya wuce ya ɗauko mata magungunanta.
Kanta yana kan kafaɗata nace"bari na zubo miki abinci inkinci sai kisha maganin"ta girgiza min kai alamar A'a muka haɗa ido da Habib yada kasa zaune balle tsaye yaje ya zubo mata fanke da miyan danayi a plate.
Yana ajiyewa ta miƙe hadda guduta tayi bathroom ta hau kwara amai sai data gama ta fito naje na gyara ɗakin ma gabaɗaya dan komai yayi kaca-kaca,kodana fito suna zaune da Habib yana bata abincin a baki cikin sigar lallami nazo na zaune,har ta cinye sannan na ɓalla mata maganin tasha ta tsura mata ido ta gallo min harara tace"meye kuma?".


"Babynmu nake saurara Allah sarki bawan Allah an barshi da yunwa"tasa dariya Habib yace"nima dai abunda nagani kenan".sannan nida mukaci namo abincin muka fito tare muka shiga sashin Hajja sannan muka fita da Habib ya sauƙe ni a makaranta.
Tun kafin na ƙarisa cikin department ɗinmu Leema Auwal take fesa min result nawa yayi matuƙar kyau nako cika fam!da murna banƙiba a lokacin na tiƙi rawa abuna sai wajajen ƙarfe uku da rabi na baro cikin makarantar inta tararradin Yasira gashi banyi mana girkin rana ba kuma nasan a halin datake ciki bazata iya taɓuka komai ba,adai-daita na tara na koma gida ina isa na sakarwa kaina shower sannan na ɗauro alwala na fito na cazan shiga zuwa wasu marasa nauyi sannan na tada sallah ko addu'ar kirki banyi ba na fito na shiga part ɗin Yasira.
Tana bacci a falon na tattare kwanukan safe nakai kitchen sannan na ɗaura mana na rana yana gamuwa na juyeshi a plate dan sanin danayi Habib bazai dawo da ranaba shiyasa ban sashi cikin girkina ba.
Duk yanda nayi ta kafe akan bazataci ba rakenta na jiya ta ɗauko daga cikin fridge tasha,nan na wuni muna hirarmu ƙiran Habib kuwa sau biyar yan shigowa wayata babu abunda yake tambaya face baby da Uwar baby.
Nan na haɗa mana dinner sai bayan sallan isha'i Habib ya dawo muka fito muka tarboshi munacin abincin nake sanar dashi sakamakon result ɗinna yayi kuwa matuƙar murna har yana cewa shi zai fara sanar da yaya Fawas wannan labarin.
Ranar hira mukayi as one family sai wajen ƙarfe sha biyu sannan na musu sai da safe kasancewar ranar Habib a ɗakinta yake ya rokoni part ɗinna tare damin addu'a kamar yanda ya saba har zai fita na riƙo hannunsa na sakar masa lallaushar murmushi nace"Baban unborn Baby a kwana lafiya"ya maido min da murmushin haɗi da cewa"To matar aljanna abun kuma hadda tsokala"na turo baki nace"babu wani tsokala ai gaskiya ce".


"To shikenan my journalist"ya faɗa tare da shafa saman goshina na rakashi da murmushi yayin dayake ficewa daga ɗakin.
Kashe gari ina gaban mirrio ina ɗaura ɗan kwalina wayarta dake kan gado kusa da jaka da mayafina ta hau ruri nazo na ɗaga muka gaisa da Maryam ina tambayarta Abbul-khair tace min Bashir ya fita dashi sunje gidan Granny.


"Jiya da daddare Habib ya ƙira Bashir yake sanar dashi wai Yasira tana ɗauke da ciki?"na ɗan sunkuyar dakai ina wasa da pattern ɗin daka yiwa ɗinkin doguwar rigar jikina kwalliya dashi nace"E wallahi abubuwa nema suka sha kaina na manta ban sanar dake ba".
Inajin yanda ta tsikar da wani siririn tsaki sannan ta cigaba da faɗin"Hibba wallahi ina tausaya miki halin mazan wannnan zamani sao dai addu'a karfa Habib ya canza miki mussamman ma Granny akan wannan cikin dake jikin Yasira".wani zazzafar iska na furzar daga bakina kana nace"Maryam bazan hana Habib da danginsa ruɓaiya soyayyarsu ga Yasira ba mussamman a wannan lokaci domin ku....."ban kai aya ba ta katseni"kedai kawai Allah ya kyauta shine fatan dazamuyi"na murmushi dan nasan cewa ba haka taso ji daga gareni ba sallama mukayi na ajiye wayar na gama shiryawa zan fito daga ɗaki ƙiran Yaya Fawas ya shigo wayata na maƙala wayar a kunnena ina fitowa falo murna ya fara tayani akan result ɗina sannan ya sanar dani cewa sunyi magana da Habib jibi zamuje potiskum akan maganar Umma.
Da haka mukayi sallama na fito zani part ɗin Yasira ina tafe inajin gabana namin matsanancin bugu na dafe dai-dai ƙirjina sanda na iso ƙofar part ɗin tare da sauƙe ƙatuwar ajiyan zuciya sannan na murɗa handle ɗin na shiga.
Habib ne tsaye yana arranging dinning na ƙarisa gareshi gaishe shi na farayi ya amsa sannan na tsaida idona akan dinning ɗin ina ɗagowa ya kashe mini ido ɗaya sannan ya riƙoni muka dawo falo muka zauna.


Naɗan waiga nace"Yasira bata tashi bane?"yace"ta tashi tana wanka ne shine na fito nace yau dai barina haɗa mana breakfast na hutar dake"nayi ƙasa da kaina nace"Ai kuwa nagode daman yanzu Yaya Fawas ya ƙirani yake sanar dani kunyi magana dashi har jibi zamuje potiskum,mungode sosai mijina yanda kake ƙoƙarin dawo min da farin-cikin da nayi nisa dashi Allah ya kyautata maka,Allah ya shiga cikin lamurank.."sauran maganar suka maƙale a maƙoshina saboda kukan daya zomin ba shiri.
Sai dayaka ƙara matsoni kana yace"Dukkan abunda na miki acikin wannan duniyar ban biyaki irin halallacin dakika min ba Hibba kinsoni sannan kiso duk wani abunda zai sanyani farin-ciki bazaki taɓa gogewa acikin tarihina ba"ya kai ƙarshe yana share min hawayen dake kai koma bisa tudun kuncina.
Yasira ta fito muka gaisha sannan Habib ya zuba mata abinci yabata kamar na jiya taci sosai sannan muma mukaci na mata sallama Habib ya sauƙe ni a makaranta.har ƙarfe biyar sannan na dawo nayi wanka sannan nayi sallan magrib dan an ƙira sai danayi isha'i sannan na shiga part ɗin Yasira tana bacci na isketa na haɗa mana dinner sannan na tada ita tayi wanka na ƙira Habib ya katse ƙiran ya ƙara ƙira na ɗaga haɗi da faɗin"kana inane babynmu fa yunwa yakeji kuma kasan inba kai ka basa ba akwai matsala".


"Gani kusa da gida yanzu zaku ganni".


"Allah ya dawo mana da daddyn unborn baby cikin aminci"yayi dariya sannan na ajiye wayar baifi mintuna goma sha biyarba ya dawo muka tarboshi kamar kullum sannan mukaci abinci nan yake sanar da Yasira tafiyar da zamuyi jibi zai kaita wajen Ummi kafin mu dawo.
Sosai mukayi hira kafin Habib ya rakoni na kwanta,washe gari banje makaranta ba sai ranar da zamu tafi tafiyar safe zamuyi dan zamu tsaya a gano sannan mu wuce azare mu ɗauki yaya Fawas.


Wajen Ummi muka ajiye Yasira,Ummi ta ƙarƙafa mini gwiwa sosai kukan danake dakonsa tun daren jiya na ska da ƙarfi nace"Ni wallahi Ummi yanzu ko gawarta ne inaso nagani wallahi".Ta rungumo ni ta haɗa da jikinta tana bubbuga bayana tace"In sha Allahu ma zaku sameta tana raye da yardan Allah"ta ɗagoni ta mana rakiya ita da Sayyid dan mun sameshi a gidan sannan muka ɗauki hanya ƙarfe goma ta gota muka isa cikin kano muka nufa gano.
Inna ce a tsakar gidan tana tatan kamo muka shiga ta tarbo mu da fara'arta sannan ta shimfiɗa mana tabarma muka zauna muka fara gaisuwa,Baffa ya fito daga banɗaki shima ya zauna muka gaigaisa.


"Allah ya dubi niyyarku kyakykyawa ya baku sa'a ya datar daku ya sada saduwa tsakaninku da wannan baiwar tasa"cewar Baffa a sanyaye na amsa da amin can ƙasan maƙoshina sannan Inna ma ta ɗaura danata sai naji duk jikina yayi sanyi Baffa da Habib suka fita masallaci saboda ƙiran sallan zuhr da'aka farayi kafin su fita Habib yake cewa Inna suna dawowa zamu tafi.
Na tashi nayi alwala nayi salla a ɗakin Inna ina daga kan sallayan nace"Inna ni kuwa banda Anty Hajara ba tun shigowar mu".hular sanyin yaran da take saƙawa ta ajiye gefe guda sannan tace"Hajara ai jiki yaƙi daɗi ya rikice sosai ba irin maganin da bamuyi ba amma abu yaci tura,malaman asibiti ma cewa suka mu dawo da ita gida acigaba da mata na gargajiya,ki tashi ma kafin ku tafi kije ki dubata tana ɗakinta".
Na miƙe na fito tun kafin nasa kaina cikin ɗaki wani uban wari ya ziyarci ƙofofin hancina,na tura ƙofar tare da zara ƙafafuna ciki tana kwance saman tabarma numfashinta yana fita da ƙarfi sosai duk fatarta ya daddare yayi jajir dashi na tsuguna kusa da shimfiɗar tatan nace"Anty sannu ya jikin?".
Runtse idanuta tayi hawaye na gangarowa tayi azamar ɗamƙo hannuna ta riƙe gam!ta fara ƙoƙarin yin magana harshenta ya cika mata baki babu damar yin wata magana duk tinanina zafin ciwo ke sata haka dan duk jikinta ya ɗau mazari ga maganar da takeson furta min babu damar fitarda.
Na zame daga tsugunan danaji na zauna nace"Anty kiji shuru basai kinci komai ba Allah ya baki lafiya yasa ya zama kaffara ga zunubanki".idanu ta kafeni dashi har yanzu tana hawaye na zare hannuwa daga nata nace"zamu tafi Allah ya ƙara sauƙi"ina kawowa nan na miƙe tsam nima jikina duk ya ɗau rawa ko me takeson faɗa min ni kuwa Allah masani.na fito dai-dai shigowar Baffa da Habib,Inna ta fito mukayi sallama har zaure ta takomu sannan ta koma muka ɗauki hanyar Azare.




Page 5⃣3⃣


Tunda muka hau titi zuciyata da tinanina yake ga Hajara wallahi tausayin halin da idona suka ganta a cikin ya zama babban gurbi cikin ruhina Allah kaɗai yasan azabar datakeji a cikin jikinta gashi bakima ya rufo sai ido kawai.


"Lafiya kuwa kike?"Habib ya jefomin tambaya wanda yasani dawowa cikin hayyacina daga tinanin dana faɗa na ɗan musguta nace"lafiya ƙalau kawai yanayin jikin Anty Hajara ne ya tsaya min arai wallahi tanajin jiki".


"Allah ya bata lafiya nima inzamu dawo zan tsaya in dubata"na jingina kaina jikin kujerar motar ina fidda numfashi ɗaɗɗaya.
Ana ƙiran sallan magrib muka isa cikin garin bauchin yakubu muka ƙira yaya Fawas muka sanar dashi muka masa kwantacen inda muke yazo ya zamemu muna shiga layin gidan dayake farko muka tsaya a ƙofar gidan wasu yaran da bazasu haura shekaru biyar ba suka fito su biyu daga cikin gidan wani matsanancin kaman da na gano a fuskarsu da yaya Fawas yasani tinanin cewa ƙannensa ne wanda suke uba ɗaya dasu.
Muka fito daga cikin motar yaran danaji ya ƙira sunansu da Mahmud da Sadiq suka gaishe mu tare da faɗawa jikin yaya Fawas suna masa oyoyo,jagoranci ya mana har izuwa cikin gidan muka zauna a falo yace bari ya ƙira mana mutanan gidan yabi wata ƙofar dake cikin falo ya fito ai kuwa suka dawo da jama'ar gidan a bayansa.
Daga ni har Habib suka zame daga kan kujerar damuke zaune muka gaida matar babansa da suka fito tare ta ama fuskarta cike da yalwan fara'a sannan tarin ƙannansa suka shiga gaidani da Habib.
"Tsarki ya tabbata ga ubangiji talikai"na faɗa cikin raina tabbas Allah yayiwa dangin yaya Fawas ilhamar kyau gasu farare tas wanke hannu ka taɓa,rabona dasu tun Abba na raye da mukazo ta'aziyyar rasuwar mahaifinsu.


Wasu ƙannensa mata suka jani ɗaki nayi sallolin dasuke kaina Wacce tafi ɗayar surutu tace"Anty ko yaushe in yaya Fawas zashi gano sai munje masa zamuje sai yaƙi"na kallota nayi murmushi ina dan jan carbin dake maƙale a yatsata nace"gaskiya Yaya Fawas bai kyauta ba amma kuma ba gashi yanzu nazo ba".natayi saurin cewa"Ai ko lokacin da kikayi ɓarima munso zuwa sai kuma lokacin muna makaranta".


"Ke daikam Anisa bazaki barta ta huta ba kincika da surutai"wacce aka ƙira da Anisa ta tsuke fuska tace"Kai Fadila akwai ki da ƙarawa abu gishiri yanzu har wani surutu nayi".
Mahaifiyarsu ta shigo ta samemu tace mu fito muci abinci muka fito su Habib ma sun dawo tare mukaci abinci ana raha ana hira.
Raba dare mukayi muna hira da ƙannen Yaya Fawas haka nan kawai naji yaran sun shige mini rai sosai bansani ba kodan matuƙar kaman dasukeyi da yaya Fawas ne oho.
Washe gari kuwa tun ƙarfe takwas muka gama shirin wucewa Potiskum mukayi sallama da ƙannen yaya Fawas da mahaifiyarsu sannan muka wuce tare da yaya Fawas.
Bamu sama isowa potiskum da wuri ba saboda lalacewar da motar tana mana a hanya.Yaya Fawas naga yayi waya da wani sannan kuma muka nufi wata unguwan da ake ƙira da ƘODAWA.


Muka faka muka fito muna jiran isowar wannan mutumin dasukayi waya da yaya Fawas wanda bansan wanene ba, zafin ranan da ake bushawa ya dakeni bugun zuciyata ya tsananta sai naga duk garin ya sauya min rabona da garin potiskum tun ranar da Abba ya rasu nabi su Inna izuwa gano.
Sallamar da mutumin yazo da ita ta dawo dani hayyacina sukayi musbaha da Habib da kuma Yaya Fawas sannan na gaishe shi ya amsa yayi gaba muna binsa a baya na lura a buge ma yake yana tafiya tana tangaɗi.
Wani gida muka shiga mai yalwan jama'a sai da muka shiga na gane inda muzo gidan KARUWAI ne kowa yana sabgar gabansa duk babu mai suturar mutumci a jikinsa.ya nuna mana wani ɗaki yace mu shiga muka shiga wata dattijuwar macece zaune a ɗakin tana daga kishingiɗe tana sauraron radio muka gaishe ta ta amsa a daƙile sannan na zubawa wanda ya shigo damu na mujina.


"Allah ya taimake uwarmu maganin kukanmu,ai waɗannan sune baƙin danake gaya miki cewa zasuzo neman magajiya uwar tantirai haj.Juwahir"ta tashi daga kishingiɗewar datayi tace"ina ƴaƴan natan suke a cikinku?".duk mukayi shuru kamar ruwa ya cinye mu Habib ne yayi ƙarfin halin cewa"dukkan mu ƴaƴanta ne dan Allah idan kinada labarin inda ta koma da zama shi muke buƙata".
Tun shigowarmu ɗakin na gane matar a kallo ɗaya danayiwa fuskarta,Umma tasha aikena wajenta sai dai a wancan lokacin ba'a wannan gidan take ba nayi mamaki ma dabata shaida muba.


"To nidai banace da takamenmen inda ta koma da zama ba dan tunda ta ɗaura aure tabi mijinta suka koma can garin arnan nan a kudu shekara ɗaya daya wuce nasama labarin cewa shi mijin data auren ɗan shan jinine ya rufeta a ɗaki yanata gallaza masa ita kuwa ko wayarta ka ƙira bata shiga.sai haj.Luba mai babban harka tace ta ganota a Lagos tana bara bakin danger wannan shine abunda nadanasi ko nace labarin danaji akanta".
Kusan suma nayi a inda nake zaune a cikin ɗakin da wari tabar sigari ya gauraye ko'ina Yaya Fawas ya shaƙo kwalarta idanunsa sun firfito yace"Wallahi ƙarya kikeyi wallahi ƙaryane ba Umma bace aka baki wannan labarin akanta".
Habib da wannan matashin daya shigo damune sukayi nasarar ɓamɓare hannun yaya Fawas daga jikinta.
Da rarrafe na matso kusa dashi na ɗaura kaina dayake sarawa akan cinyarsa ina kuka haka nan ma shima kukan yakeyi.


"A'a nifa bazaku maida min da gida kamar na mutuwa ba tunda na sanar daku abunda nasani ma ban siraba to ku fice min daga gida banda ikon jalla ma ta yaya za'ace wai Juwahir ne ta haifa waɗannan ƴaƴan masu nutsuwa da kamewa Allah ne kaɗai yasan adadin yawan ƴaƴa matan da Juwahir tayi silar rabo su da gidan iyayensu ta jefasu a rayuwar bariki Mahaifiyarku tun a nan gidan duniya sai ta fuskanta abunda ta shuka sai tayi mutuwar da ko uwar data haifeta ne bazata shaida ta ba".Furcin Ladi ƴar caras zuciyata ta buga da matuƙar ƙarfi naji ƙirjina kamar an ajiye min wani abu mai nauyin gaske.
Yaya Fawas ne ya riƙo hannuna muka fice daga ɗaki ina laɓe lamau a jikinsa duk jikina ya sake,Habib yana biye damu a baya.
"Bari naje na karɓi kuɗin sallama na ai ba aikin banzan na muku ba"cewar wannan matashin ya kai ƙarshe yana ficewa daga ɗakin ya biyo mu a baya.
Bayan motan na shiga na kwanta akan kujerar ina sauraran yanda bugun zuciyata ke tashi.A jikin motar suka tsaya Habib yace"Bawan Allah yaya sunanka".yaja da baya yana binsa da wani kallo da riƙiɗaɗɗun idanunsa da ƙwaya tasa suka canza launi yace"Sunana Lawan bani kuɗina kawai na wuce".
"Bazan baka ba domin kona baka nasan ƙwayoyi zaka saya dasu,meyasa kana matashi mai jini a jika wanda yanzu ne lokacin daya kamata ka nutsu wajen gina rayuwarka ta inganta sai kuma ka bige da shaye-shaye kanada iyaye shin bakason suyi alfahari da kai koda na rana ɗaya ne a matsayin ɗa na gari a garesu?".
Tabar sigarin dayake zuƙa ya cire daga bakinsa yana tsaida idanunsa akan Habib kana yace"Iyaye?iyaye fa kace,iyayen da tun ina cikin zanin goyo suka yar dani akan titi babu tausayi balle tinanin rayuwa ko mutuwata,tun lokacin dana buɗi ido naganni acikin wannan gidan kuma wannan matar ta zame mini uwa wallahi tun lokacin da naji mutane na faɗar ta yanda aka sameni an jefar dani a wulaƙance ina kuka naji ban ƙaunar ganin iyayena ko kaɗan"Hawayen dasuka fara taruwa a idonsa ya kawar"bani kuɗina kawai malam na wuce".
Buɗe motar Habib yayi ya cire masa kuɗin ya basa tare da complementary card ɗinsa yace duk sanda ya shiga katsina ya nemesa sannan muka tafi.
Tunda na ɗaura haƙarƙarina na kwanta ban sake sanin inda kaina yake ba,dan jinayi bana fahimtar duk zance dasukeyi haka nan idanunsa basa ganu min komai sai duhu bakina yayi nauyi bana iya furta koda kalma ce.
Sai buɗe ido nayi na ganni a gadon asibiti Habib na zaune gefen gadon ya dafe goshinsa da alama dai tinani yakeyi,Yaya Fawas kuwa yana tsaye jikin window yana jeƙan wajen.kaina ya sara da ƙarfi nayi ƙoƙari haɗa kalmomin bakina nace"Ummaa".
Hakan yasa duk suka nufo ni suna min sannu gani Yaya Fawas ya sani sakin kuka"Wallahi Yaya Fawas nikam na yafewa Umma in tana raye a duniya zan cigaba da addu'ar Allah ya sada fuskokinmu da alheri inkuma bata raye zan cigaba da nema mata gafara wajen Allah".


"Kiyi shuru ya isa haka my cute angle kinga ba isheshshen lafiyace dake ba"
Na kuwa yi shurun ina zuƙar majinar kukan daya zo min,suka fita zuwa masallaci domin gabatar da sallan zuhr nurse ta shigo ta cire min robar ruwan da aka samin domin ya ƙare na shiga cikin banɗaki dake cikin ɗakin nayi alwala na fito nayi sallah.
Zuwa yamma aka sallame mu Habib yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login