Showing 42001 words to 45000 words out of 104857 words
Chapter 15 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
bangaren su.
Sannan ya ɗaura da sanar dashi abinda ya faru,ina takure akan tabarma na tisa kwanon dambum tsakin masaran da Hajja ta kawo min.
Malam Idi suka shigo tare da Habib ina ganinsa naji wasu hawaye masu zafi sun shiga kwaranyo min.Gefen tabarmar yazo ya tsuguna tare da faɗin"Meyake faruwa ne duk na ganki haka,nata ƙiran wayanki bakya ɗagawa shiyasa ma na dawo yanzu dan ba kaɗan ba hankali na ya tashi,sai kuma malam idi yake sanar dani cewar wai ƙadangare ne ya shigar miki falo".
"Wallahi Hamma duk inda na duba shinake gani,kuma su Hajja sunce basu ganshi ba".
Na ƙarishe maganar ina tsaida ƙwayar idona dayake cike fal! da sabbin ƙwalla,akansa cikin son tabbatar masa da maganar tawan.
Handkerchief ya ciro daga aljihunsa ya miƙo min,na karɓa na share hawaye na sannan ya riƙo hannun na na miƙe tsaye.
"Malam Idi bari muje na gani da kaina"
Ya faɗa yayin da muke ficewa daga part ɗin nasun,koda muka shiga ba inda habib mai duba ba amma babu wannan ƙadangaren.
Hakan ya ƙara tabbatar min dacewa ni kaɗai kenan nake ganinsa,ranar kota kan abinci bamu biba muka kwanta.
Sosai muka raya mafi yawa daga cikin,dare da nafilfili sannan muka fara karatun alqur'ani.
Ranar Habib a ɗakina ya kwana yana gadina,amma duk da haka na kasa runtsawa.
Haka muka waye gari na kafe kan Habib bazai fita ko'ina ba,Sosai ya shiga lallashi na tare da bani haƙuri akan cewa akwai baƙin da zaiyi daga Morocco,da zaran ya gama dasu zai dawo.
Haka ya tafi sannan na dawo ciki nikam daman ranar bazanje makaranta ba.
Saboda ana training na censors a department ɗin,tun ƙarfe takwas ɗin safe suke farawa zuwa shidan yamma,ko munje ba lectures za'a mana ba.
Ɗakin Habib na shiga na sama wani babban MP nasa memory card ɗin a ciki na kunna karatun qur'ani,na ƙure volume.
Da wuri Habib ya dawo inayin sallan isha'i na kwanta saidai,na kasa baccin haushin karnuka nakeji ta ko'ina a cikin kunnuwana.
Kamar karnukan a cikin ɗakin suke,tashi nayi na zauna ina karatu duk addu'ar datazo bakina.
Habib yana kwance kan sofa,yana bacci har nayi niyyar tashinsa sai kuma na fasa.
Daga jiya zuwa yau baya samun ishashshen bacci,dan sai da asuba yake kwantawa indan na tashi.
Ga kuma wuni dakeyi a office cikin kwanakin nan,alwala na ɗauro nazo na tada salla.
A hankali na farajin na dainajin haushin,ana kan sallayar na kwanta ina fitar da hawaye.
Wai sai yaushe zan sama farin-ciki ne a cikin rayuwa ta?,sai yaushe zan rabu da tarin damuwa da ƙunci?,sai yaushe nima zanyi rayuwa kamar yanda sauran,mutane sukeyi cikin farin-ciki da walwala?.
Da waɗannan tarin tambaboyin dana gaza samun,amsarsu bacci yayi gaba dani.Haka rayuwa taita juyawa yayin da ko yaushe gane-ganen danakeyi suke ƙaruwa,ko Habib inna faɗa masa cemin yake baya ganin komai.
Wai kawai nasa abun a raina nane nima shiyasa nake yawan gani.Cikin kwanakin dabasu gaza bakwai ba,nayi wata mungun rama duk wanda yasanni sai yace na rame.
Ko makaranta daina zuwa nayi,indai ba fita mukayi da Habib ba bana samun nutsuwa,muna dawowa kuwa komai zai cigaba.
Koda Habib ya faɗawa Ummi rubutu tasa aka amso min ina sha sannan tace in daina sauraron kiɗe-kiɗe.
Daddy yace"Yasira tazo ta tayani zama kafin suga abunda Allah zaiyi".
Haka Yasira ta dawo gidan da zama,daga zuwanta da kuma rubutun da Ummi take karɓo min na rage gane-ganen.
Saidai hankali na yakasa kwanciya da Yasira a gidan sosai tasa mana ido.Inna tsoron ranar da zata ganu cewar,ba ɗaki ɗaya muke kwana da Gabib ba.
Haka kullum muna rigata kwanciya duk juyin duniyan nan dazan mata nacewa taje ta kwanta.Murmushi kawai take sakar min tare da faɗin"Anty kuje kuyi kwanciyar ku,niba yanzu zan kwanta ba".
Haka nan zamu tashi mubarta a falon,har sai taje ta kwanta sannan Habib zai koma ɗakinsa.
Ranar na dawo daga makaranta Habib ya ɗauko ni,muna tafe muna hirar mu.Yasira muka iske a falo tana kallo,sannu da zuwa ta mana sannan muka zauna.
Ruwan rubutun da Ummi ta aiko dashi ta ɗauko min nasha sannan na wuce ɗaki na.
Wanka nayi sannan na canza shiga,izuwa wata doguwar rigar material marar nauyu na fito.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Habib daga ɗakinsa,dinning area muka nufa wanda Yasira da jere shi abincin data grika mana.
Sosai naci abinci rabona da abinci tun safe,muna gamaci Habib ya tafi masallaci.
Muma tashi mukayi mukaje mukayi sallan,sai da akayi isha'i sannan Habib ya dawo.Tashi mukayi mukaje muka kwanta,sai dai koda muka shiga ɗaki zama mukayi.Muna jiran Yasira takoma ɗakinta shima ya tafi nashi ɗakin.
Sai wajen sha ɗayan dare sannan ta kashe kallon,tayi ɗakinta sannan Habib ɗin ma yafita bayan yamin sai da safe.
A hankali ya fito daga ɗakin ya shiga nasa dayake ɗan nisa kaɗan da nawa.Yasira wacce tazo ɗaukar wayarta data barsa yana caji a falon taga fitowarsa.
Wayarta ta cire tana ƙarabin ƙofar ɗakin da kallo,tafi minti talatin a wajen tana jiran taga fitowarsa amma bai fito ba.
Komawa ɗakinta tayi tana tinanin to ko wani saɓani muka samu ne?.
Da safe da niyyar yi mana maganar ta tashi,amma ganin mu datayi babu wani sauyi daga yanda muke,ya tabbatar mata da ba wani matsalar da muka samu.
Tare da Habib muka fita ya sauƙe ni a makaranta sannan ya wuce office,sai ƙarfe huɗu muka fito na ƙira Habib na faɗa masa bai ɗau lokaci ba yazo,ya ɗauke ni muka dawo gida.
Muna zazzaune a falon bayan munyi salla munci abinci sosai nakejin bacci amma Yasira ta kasa ta tsare a falon nan.
Ɗan satin datayi a gidan sai naji dukna matso ta tafi.Miƙewa Habib yayi bayan ya amsa ƙiran da aka masa a waya.
"Bari nakai matar malam Idi asibiti bata da lafiya".
Ya faɗa sannan ya fice cikin sauri,fatan samun lafiya muka mata.Sannan nima na tashi zanyi ɗakina,"Anty bari nabiki nima"cewar Yasira.
Ban kulata nayi wucewata tabiyo ni,hira mukeyi sosai muna kallon hotunan bikin mu da Habib.
Sai ƙarfe gowa da wasu mintina,mukaji ƙaran shigowar motar Habib.
"Anty ga mijin ki ya dawo bari na tafi".cewar Yasira ta faɗa tana tattare hotunan.
Murmushi nabita dashi dai-dai lokacin ta Habib ɗin yake shigowa ɗakin,matsa masa tayi sai daya shigo sannan ta fita.
Sai nada tambaye shi jikin Hajjan?,yace da sauƙi hawan jini ke damunta,harma an basu gado.
"Allah ya sauwaƙe".
Da amin ya masa sannna muka ɗan taɓa hira kafin yamin addu'a yafita.Yasira dake tsaye a cikin falo ta naɗe hannayenta,a ƙirjinta yau kam ta ƙudurce a ranta sai ta tabbatar da zargin ta.
"Hamma".
Ta ƙira sunnan shi a hankali ya juyo sai daya bita da wani irin kallo kafin yace"Me kikeyi har yanzu baki kwanta ba?".
Sai data iso dab dashi sannan ta shiga faɗin"Hamma wani irin zama kukeyi da Hibba?,waɗannan abubuwa duk meya kawo su bakwa kwana ɗaki ɗaya,sannan kuma ba wai saɓani kuka samu tsakanin ku ba?".
Dam-dam ƙirjinsa ya bada hannunta ya kamo suka nufi ɗakinta.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
_________________________
Page 2⃣9⃣
Zama tayi akan ɗaya daga cikin kujerun dasuke ɗakin sannan shima ya zauna yana fuskanto ta.
Shuru ne ya tsara ɗakin na wasu mintuna,katse shurun yasira tayi ta hanyar faɗin.
"Hamma inajinka".
Sai daya sauƙe wani nauyayyen ajiyan zuciya sannan ya shiga faɗin"Yasira inason wannan abun yaza mana sirri a tsakanin mu,ko ummi banaso ki sanar da ita balle kuma Sayyid".
"In shaa Allah zan tayaka riƙe wannan sirrin,matuƙar naji dalilanta masu ƙarfi ne".Sai daya gyara zamansa yana mai lanƙweshe ƙafafunsa kafin yace"Tun ranar da aka kawo Hibba cikin gida na,a matsayin mata ta sunna bamu taɓa haɗa gado da ita ba,hasalima kowa a ɗakinsa yake kwana.Ta sanar dani cewa bata saba kwana ɗaki ɗaya da wani ba,hakan yasa na mata uzuri a tinanin abun na ɗan wani lokaci ne sai kuma naga saɓanin tinanina domin tun daga ranar bata sake min maganar ba".
Sai daya numfasa sannan ya ɗaura da cewa"Abun yana damuna sannan ya hanina samun nutsuwa a cikin raina,har na fara tinanin ko batada lafiya ne?,A duk lokacin danayi ƙudirin tattauna maganar da wani makusanci na sai naji kamar an ɗinke min bakina Bashir ne kawai yasan da wannan maganar.Kuma bazan iya tilasta mata ba shiyasa na duƙufa da addu'a kema kuma inason ki tayani".
Hawayen dasuke sintiri akan kunci ta Yasira ta share da bayan hannunta tare da faɗin"Hamma bata saba kwana ɗaki ɗaya da mutum bafa kace?,wannan abun har yakai dalilin daza a amshe shi tabbas ta cutar dakai meyasa bata tinanin zaka iya faɗawa ga halaka?".
Miƙewa tayi da sauri tana cigaba da cewa"Hamma zanje na mata magana domin wannan dalilin nata,bai isa hujja ba".
Saurin riƙo hannun ta Habib yayi yana mata ishara da idonsa,akan ta zauna babu musu ta zauna ɗin.
"Yasira karki ɗauka cewar duk wanda yayi shuru kurma ne,wani yin shurun sa yana jiran lokacin daya dace ne,wani kuma shurun sa domin nazari ne,wanin kuma kawaicinsa shine maganar sa.Na tabbatar in maganar nan ta isa gasu Daddyn soyayyarsu gareni kan iya sawa idanusu su rufe,har su kasa yiwa Hibba adalci cikin hukuncin dazasu yanke".
Kallonshi Yasira take yayin da wasu hawayen ke biyo gefen kuncinta tace.
"Hamma wani adalci kake magana?,ita adalcin ta maka auren wata uku amma k...".
Da wani hanzari ta miƙe"hamma ka barni yanzu naje na mata magana".
Fisge hannunta daya riƙe tayi ,shan gabanta yayi cikin saurin tare da faɗin.
"Nace ki bari ko a hakan ma muna rayuwa cikin farin-ciki da matata sannan inna jiran lokacin daya dace ne muyi maganar da ita".
"Farin-ciki?farin -ciki fa hamma kace meyasa ka zaɓi raya nata farin-cikin,ta hanyar salwantar da naka?".
Sai daya juya mata baya sannan yace"saboda ganinta cikin farin-ciki hakan yakan mantar dani raunin dake cikin zuciya ta ,banason koda da wasa ne naji kin mata wannan maganar sai da safe ki kwanta".Yana gama faɗar haka ya juya zai fita daga ɗakin.
Jida nayi kamar za'a buɗe ƙofar ɗakin ya sanya ni saurin barin wajen na koma ɗakina.Akan gado na faɗa ina sakin wani kuka mai ƙarfi,tun lokacin dasuka fara maganar nake tsaye a ƙofar ɗakin Yasiran inajinsu.
Wayar ta data manta naje kai mata,sai kuma kunne ne suka tsinkayo min wannan maganar.
Tabbas ko nima na yadda da maganar,Yasira nasan ina cutar dashi a zaman mu.
Kukan danakeyi yasa na fara jin zuciya ta tamin,wani irin nauyi idanuna baza ganumin komai.Runtse su nayi inna karanta sunaye mahaliccina,kafin daga bisani na tashi nayo alwala na fara karatun qur'ani.
A hankali nake sauƙe ajiyan zuciya yayin dana farajin sauƙin a cikin raina.
A nan kan sallayan baccin wahala ya ɗauke ni,washe gari kuwa banyi niyyar zuwa makaranta ba hakan ya sa nayi kwanciya nan inda nayi sallan asubahi.Jin zaman mutum danayi dab dani ya sanya ni dawowa daga tinanin,danayi zurfi a cikin sa.
"Lafiya kuwa,tinanin me kikeyi haka?"ya faɗa yana kafe ni da ido.
Sai dana tattaro nutsuwa ta kafin nace"Lafiya kalau kawai banajin daɗin jiki nane".
Ƙara kafe ni da ido yayi kamar mai nazarin wani abun,yanayi na ya nuna masa kamar Yasira tamin maganar.
"Ina kwana an tashi lafiya"na katse shurun daya karaɗe ɗakin.
"Lafiya kalau Hibbatu"ya faɗa yana sakar mini murmushi.
Tare muka fito falo hannun mu sarƙale cikin na juna,Yasira muka iske tana arranging dinning table na iso muka farayi tare.
Kicthen naje ɗauko flask ɗin tea,ganin haka ya sanya Habib saurin faɗin."Kiyiwa Hibba wannan maganar ne?".
"Mezaisa nayi haka tunda ka nunamin bakaso nayi kar ka manta fa hamma sirri ne dayake tsakanin mu".
Ta faɗa tana ajiye plate ɗin dake hannun ta,wanda hakan yayi dai-dai da fitowa ta daga cikin kitchen ɗin.
Cikin nishaɗi mukayi breakfast ɗin muka gama shiryawa nayi muka fita tare da Habib ya ajiye ni a asibiti wajen Hajja.
Yasira kam a gida muka barta dan tace zataje wajen Ummi,a nan asibitin na wuni sannan na wuce gidan Ummi.
Sai bayan isha'i sannan Habib yazo ya ɗauke mu,muka koma.
Haka muka cigaba da zama,koda wasa ban bari Habib ya gane cewa naji tattaunawar sa da Yasira ba.
Cikin kwanakin nan na rasa gane kaina,a lokuta mabambamta nakan shiga banɗaki nayi kuka har na godewa rabbi.Kamar ana huraa min wuta a duk ilahirin jikina,yayin da tsanar kallan fuskan Habib ke ƙara mamaye zuciya ta.In fita makaranta ne kawai nakejin sanyi a raina,haka nan ko na dawo a bangaren Hajja nakeyin zama na.
Haka muka shirya zamuje duba Granny bata da lafiya,tunda muka hau titi nakejin bugun zuciya ta,na tsanar ta gaba sai faɗuwa yakeyi.Koda muka isa sai da Yasira ta taɓa ni tare da faɗin"Anty mun iso fa".
Sannan na dawo izuwa duniyar zahiri daga tinanin dana faɗa.
A falo muka iske Granny da iya suna zaune,da sallama muka shigo ɗauke a bakin mu.
Nan take annuri ya bayyana akan fuskokin su,kusa da granny yasira ta zauna tana faɗawa jikin ta.
Shi kuwa habib gefen iya ya zauna,daga can gefe kaɗan na zauna ina gaishe su.
Suka amsa sannan muka yiwa granny ya jiki,dukkan mu sosai yanayin jikin naka da sauƙi.
Sannan granny tamin ishara da hannun ta akan na matso kusan ta,ba musu na matso ina mai sunkuyar da kaina ƙas.
"Babban mutum ya naga duk rame ko baka da lafiya ne? "cewar granny.
Sosa ƙeya ya farayi yana ƙara sadda kansa ƙasa kafin yace"granny lafiya ta kalau akwai kwana nan aiki ne sukamin yawa" .
"Hibba yana shan magungunan sa kuwa,dan nasan halin babban mutum business ɗinsa shine akan komai harma da lafiyar sa".
Sai dana ƙarƙayo murmushin dole na yaɓa a fuskata,da fargaba da tsoro ya gama bayyana nace."Hajiya yana sha kuma ciwon nasan ma ya daɗe bai tashi ba".
Hamdala tayi sannan iya ta kawo mana abinci,mukaci sosai ranar na wuni cikin nishaɗi.Part ɗin Habib anan muka sauƙa sai da muka sha hira da su iya kafin kowa yayi shirin kwanciya.
Sai da safe muka yiwa Granny da iya sannan na wuce part ɗin Habib,shi kuwa Granny ya raka ɗakin ta,daman lokacin dayake inba tada lafiya haka yake mata.
Nikam ina shiga nayi wanka sannan na kwanta inajin shigowar Habib na rufe ido na kamar mai bacci.
Shima shirin kwanciyar yayi na zata a ɗayan bedroom ɗin zai kwana sai kuma naga tsaɓanin hakan.
Ƙara rufe idona nayi da ƙarfi,inajin yanda hawaye suke gosilo a saman kunci na,sai dai ban bari ya gane kuka nake ba.
Haka nan na kwana ban runtsa ba,jiki na gaba ɗaya ya ɗau kerma ko yaya na rufe idona wannan ƙadangaren nan nake gani yau kuma
Washe gari da wuri na tashi na shirya,sannan na tada Habib tare muka fito muka nufa sashin Granny.Tana zaune a ɗakin ta muka iske ta,tana sauraron labaran safe dake haskawa a tashar NTA.
Kusa da ita muka zauna a tare muka gaishe ta ta amsa,sannan muka ɗaura da tambayar ta ya jikin ta amsa mana,da da sauƙi.Tashi nayi ina cewa"Granny bari naje wajen iya".
"To nima yanzu zanje wajen natan"cewar Granny.Fita nayi na nufi ɗakin iya na basu waje dan su tattauna,dan na fuskanta granny nason ta gana dashi na sirri.
Dan duk wanda yaga habib ɗin dole ya tambaye shi,lafiyar sa dan ba kaɗan ba yayi wata rama a cikin kwanakin nan.
"Granny kinsha magani kuwa?".
"A'a yanzu nakeson na tashi nasha".
Cewar granny tana gyara zaman ɗan siririn farin,gilashin dake zaune saman karan hancin ta.Tashi yayi ya ɗauko mata maganin sannan ya ɗauko goran ruwa,ɓalla mata maganin yayi sannan ya miƙa mata.
A tare ta watsa su a bakin ta,sannan yasa mata goran ruwan a bakin ta."Babban mutum inason kuwa muyi wata magana dakai"ta faɗa tana cire goran ruwan daga bakin ta.
Sai daya gyara zaman sa yana ƙara fuskan inda take zaune sannan yace"To granny inajinki".Murmushi ta saka yayin datake miƙewa tace"to jirani in shiga bathroom na fito".
Kansa kawai ya ɗaga mata sannan ta wuce bathroom ɗin.Wayar sa data fara ringing ya ɗaga"Angon Hibba yane?"cewar Bashir.
Sai daya shafa sumar sa kafin yace"normal na shigo damaturu fa".
"Ya maka kyau ai shine koka leƙo inda nake,ya Hibban ina fatan dai yanzu komai ya dai-daita ?".
Sai daya furzar da wani zazzafan iska daga bakinsa shuru yayi ba tare daya ce komai ba.
Ganin shurun yayi yawa ya sanya bashir faɗin"Mutumi na yadai".
Sai a sannan yace"bashir wallahi har yanzu ba abunda ya sauya,babban tashin hankali na ma yanzu yasira ta fahimce komai ina gudun ta sanarwa su daddy".
Ya ƙarishe maganar yana miƙewa tsaye windown ɗakin ya nufa ya fara yaye labulen.Shima bashir ɗin sai daya numfasa kafin yace"Habib sanarwa su daddy fa shine mafita,domin ta nan ne za'aji dalilin ta na aikata haka tunda har yanzu bata baka wani gamsheshshen hujja ba".
"Bashir zan cigaba da roƙon Allah ya bani ikon jurewa har,izuwa lokacin da komai zai zamto dai-dai.Cikin kwanakin nan na lura kamar zaman gidan ma ba daɗinsa takeji ba a cikin ni da ita na kasa bambamce waye marar lafiy........".
Cak ya tsaye juyowan dazaiyi idanun sa suka sauƙa akan Granny,dake tsaye bakin bathroom ta naɗe dukka hannayen ta a ƙirjin ta da dukkan alamu ta daɗe a wajen.
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________
Page 3⃣0⃣
Saurin katse ƙiran yayi yana maida wayar aljihunsa sai daya dai-daita nutsuwar sa kafin yace"Granny kin fito".Bata kula shi ba illa ƙarisowada tayi bakin gadon ta zauna tana aika masa da wani irin kallo mai cike da tuhuma.
"Habib wai meyake faruwa ne tsakanin ka da Hibba?".
"Granny ba komai fa muna zaune lafiya da Hibba me kika gani?"yafaɗa yana zama kusa da ita.Sosai ta kafe shi da idanu tana cewa"Habib duk tattaunawar ku da Bashir ba wanda banji ba,ka faɗa min gaskiya meyake faruwa?".
Ƙara matsowa yayi kusa da ita tare da riƙo hannun ta kafin yace"Granny ki yarda dani babu wata matsala tsakani na da mata ta"ya ƙarishe maganar yana sakar mata murmushi.
Kallonshi kawai takeyi cikin son tabbatar da maganar sa nacewa babu wata matsalan"tashi kaje".Ta faɗa tana ɗauke idonta daga kansa.
Tashi yayi jiki a matuƙar sanyaye ya fice,a falo ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun yana lumshe idanunsa da ba komai a cikinsu face bacci da kuma tsan-tsan gajiya.Daren jiya yanda yaga rana haka nan yaga dare ji yayi kamar bazai iya jurewa ba dalilin haka yau yasanya shi tashi da azumi domin kare kansa daga faɗawa izuwa halaka.
Tare da Iya muka gama haɗa abincin karin kumallon sannan muka fara kaisu dinnnig,ciki-ciki nayi sallama ganinsa danayi akan kujera ya lumshe idanunsa saurin mayar da hawayen daya taro min a ido nayi,yayin danaji wani kibiyar tausayin kaina ya karbi ƙalbina.
Ko tantama