Showing 36001 words to 39000 words out of 104857 words
Chapter 13 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
da annurin dake fuska na,nan take naji raina yayi baƙi ƙirin,kamar na fita da guda haka nakeji.
Ina zaune ya shigo miƙewa nayi na iso gareshi tare da karɓan ledan dake hannunsa,Inajin yanda zuciya ta take tsananta bugu.
Rungumo ni yayi muka ƙariso cikin falon,saurin raba jiki na nayi da nashi.
"Bari na kai maka ruwan wanka sannan ka huta"na faɗa murya ta na rawa haka nan ma jiki na.
Ban jira amsa dazai bani ba na juya cikin sauri na wuce bedroom ɗinsa,Bathroom na nufa na haɗa masa ruwan wankan sannan na fito.
Ina fitowa yana shigowa ɗakin kayan jikin sa na fara rage masa.
"Jinki nake a ko'ina a cikin raina shiyasa bazan daina yiwa Abba addu'a ba,Allah yakai haske kabarin sa daya haifo min ke".
"Amin ya Allah"na faɗa ina cire masa safan dake ƙafansa.
Miƙewa yayi ya shiga toilet ɗin,kaya na ciro masa na ajiye masa akan bed ɗinsa sannan na fita.
Sannan na fito na buɗe ledar daya shigo da ita,kaza ce da kuma rufaida yogurt ɗayan ledar kuwa fruit ne.
Kitchen na wuce na zuzzuba komai a mazubin sa sannan na jere su akan dinning.
Waya tace ta fara ringing na ɗaga da sauri ganin sunan yaya fawas,daya bayyana cikin screen ɗin wayar ina murmushi.
Sai da muka gaisa nake tambayar sa yaushe zai zo gida na?.
Sosai yake sakin dariya kafin yace"Haba!ai sai kin shekara tukunna"
"Kai!yaya fawas ai kuwa ni zanzo".
"Kul ban yadda ba kiyi zaman ki a ɗakin ki daga yin auren har zaki fara zuwa gida"ya faɗa yana ɗan ƙara sautin muryarsa.
Fitowar habib ya sani haɗiye maganar,da ke maƙoshi na fuskar shi ɗauke da murmushi ya nufo inda nake zaune.
"Ina habib ɗin fa".
Tambaya da yaya fawas ya jefo min wanda ya sanya ni dawowa daga duniyar tinanin danayi nutso cikin sa.
Miƙewa habib ɗin wayar nayi,ya karɓa tare da karawa a kunnensa ba tare daya tambayan waye ba.
Sosai sukayi hira kafin daga bisani sukayi sallama,dinning area muka nufa mukaci abincin.
Fruit ɗin kawai habib yake sha ni kuwa sosai nake yagar kazar ina bin bayanta sanyanyan rufaida yoguth.
Sai danaji ni nayi ƙatti sannan muka tattare wajen,wata hamma na saka ina lumshe idanu na.
"Bacci ko?".
Gyaɗa kaina nayi yace"to ki tashi muyi salla sai ki kwanta ko?".
Ya faɗa yana riƙo hannu na sai da muka gyara dinning ɗin sannan muka ɗauro alwala muka gabatar da sallan magrib.
Muna zaune akan sallayar aka ƙira isha'i mukayi .
Miƙewa yayi ya kamo hannu na muka nufi ɗaki,wanka na shiga na fito nayi shirin kwanciya.
Sanda mafito yana zaune akan sofa yana aiki a lapton,ɗinsa kayan dasu yasira suka taho min dashi na ɗebo su na nuna masa.
"Masha Allah kaya sunyi kyau"ya faɗa yana guban lapton ɗinsa.
Rufe lapton ɗin nayi na cuno baki ina faɗin.
"Hamma magana fa nake maka kana kallon lapton".
Naɗe hannayen sa yayi a ƙirjin sa yana sakin murmushi yace.
"To shikenan inajin ki ".
Kayan na turo mishi gaban sa inna ce "kaga kayan sunyi kyau ko?"na faɗa ina tsaida idona akan sa.
"To yanzu ke mezakiyi da wannan kwaryan haka da yawa".
Ɗan hararar sa nayi ina cewa"ba ruwanka nidai inason abina".na faɗa ina tattare kayan.
Saurin kamo ni yayi ya manna da jikinsa na fisge,kayan naje na ajiye a store tura ƙofar nayi sannan na jingina a jikin ƙofar.
Da sauri-sauri hawaye dake ambaliya akan kunci na,zuciya ta na bugawa da tsananin ƙarfi.
Dafe goshi na nayi ina karantu duk wata addu'a darazo baki na.
"Ya Allah ka fini sanin kaina ya Allah ka sausauta min wannan tsananin danake ciki,ka nuna min ƙarshen shi ina tsoron ranar da zaka kamani akan laifin kasa bawa habib, hakkinsa na aure dana take a gaban dukkan halittunka Allah ka kawo min sauƙi ".
Na ƙarishe maganar ina sulalewa ƙasa daga jikin ƙofar.
Duk yanda naso kyautatawa habib,tsananin tsanar da zuciya ta ke masa wanda inada tabbacin ko a mizani,aka sashi sai ya rinjaye soyayyar danake masa.
Shike hanani kyautata masa duk da yanda shi yake buri da kuma ƙoƙarin sauya rayuwata izuwa cikin dauwamemman farin-ciki.
Kamar an tsigara min wani abu haka na zabura na tashi wanke,fuskata nayi a kitchen sannan na koma ɗakin.
Yana zaune inda na barshi yana waya da granny,gefensa na zauna ina ƙurawa fuskar shi kallo sosai fuskar tamin baƙi ƙirin a idanu na.
Saurin kawar da kaina gefe nayi,ina ƙoƙarin maida idona ga TVn dake aiki a cikin bedroom ɗin.
Sai daya bani wayar muka gaisa da granny tare da ƙara,roƙo na dana kula da lokutan shan maganin habib ɗin Sannan sukayi sallama ya ajiye wayar.
Sosai yake jana da hira duk yanda zuciya ta take min soya,haka na danne na ke bashi amsa cikin walwala.
Saukar ajiyar zuciyan danakeyi neya tabbatar masa da nayi bacci kan bed, yakaini sai daya min addu'a kamar yanda ya saba sannan ya rufa min blanket.
Shafa goshi na yayi a hankali yake furta"Hibba inason ki so mai tarin yawa".
"Nima haka hamma habib".na faɗa ba tare dana buɗe ido na ba.
Murmushi ya saka sannan ya kashe wutar ɗakin ya fita.
Washe gari da wuri na haɗa mana breakfast,a gurguje habib yaci kasancewar yanada baƙi a office.
Sanda zai fita har da ƴar hawaye ta,sosai ya shiga aikin lallashi na yana cewa"ba daɗewa zaiyi ba zai dawo".
Sai dana mishi rakiya tare da masa addu'o'i sannan ya tafi.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
_Maimunah Tijjani Iyam_
_________________________
Page 2⃣5⃣
Ranar wuni nayi na rasa abinda dake damuna,kamar na fita a guje daga cikin gidan domin zaman gidan ya gundure ni.
Alwala na ɗauro na fara jera salloli,sai dana iddar sannan na ɗauki Al-qur'ani na fara karantawa.
Sosai na farajin sanyi a cikin raina na daɗe ina karatun sai danayi sallan zuhr sannan na tashi na fara haɗa abincin rana.
Simple girki nayi dan na lura Habib ɗin,yafi son abinci marasa nauyi da kuma sauƙin sarrafawa.
Ina gamawa na jere su akan dinning,dai-dai lokacin da waya ta fara ringing.
Sai dana faɗaɗa fara'a ta sannan na ɗaga ƙiran ganin sunan Anty Amina ya bayyana.
Sosai mukayi hira da ita take tambaya ta yanayin zaman namun.
Sai dana sauƙe ajiyan zuciya kafin nace"Anty Amina gashi nan dai wallahi ba abunda ya sauya,sai ma ƙara tsanani dayake yi".
Na ƙarishe maganar ina sharar ƙwallan dasuka ciko min idanu.Itama ajiyar zuciyar ta sauƙe sannan tace"Hibba ki cigaba da addu'a akwai wasu ma zan kawo miki,in sha Allah komai zai wuce tamkar mai komai bai taɓa faru ba.Meye ne bai faru ba a zamanki a gidan malam habu tsohon miji na?,amma ba gashi ba yanzu kamar ba ayi ba".
"Haka ne Anty Amina amma nikam har na fara tinanin ko,inace masa ya sauwaƙe mi....".
Saurin katse ni Anty Amina tayi ta hanyar faɗin"Kul Hibba wannan shine kuskuren daza kiyi mafi muni a rayuwarki,ki dubi irin karamci na iyayen Habib sune sanadiyar cigaba da karatunki,su suka maida ki ga dangin ki sannan suka miki babbar sutura ta hanyar yarjewa ki auri ɗansu."
Sai data numfasa na wasu daƙiƙu kamar mai nazarin wani abu, kafin ta ɗaura da faɗin"Hibba aure shine rufin asirin ko wace ɗiya mace,idan kikace ya saki ki yanzu wani hujja kike dashi dazai zame miki madogara?,Da wani idon zaki fuskanci iyayen ki da kuma Fawas?".
"In sha Allah Anty Amina zanyi yanda kika ce zan koyar da zuciya ta haƙurin zama inuwa ɗaya da Habib".na faɗa yayin danake bawa ƙwallan dasuka ciko min idanu damar zubowa.
Ba kaɗan ba Anty Amina take kwanta min da hankali gami da bani wasu addu'o'in.
Ƙiran sallan Asr da aka farayi yasa mukayi sallama bayan tamin alƙawarin kawo min ziyara,dan lokacin da akayi aure tayi tafiya shiyasa bata sama damar halalta ba.
Sai dana gabatar da sallan,bayan nayi addu'o'in da Anty Amina ta bani na dawo falo.
Wayata na ɗauka na shiga dialing nombar Habib katse ƙiran yayi sannan ya ƙira ni.
"Ranki ya daɗe "ya faɗa cikin muryar da take bayyanar da tsananin gajiyar dake tattare dashi.
Sai dana jefa masa tambaya na ya office ɗin?ya amsa da Alhamdulillah sannan na ɗaura da faɗin"Hamma yaushe zaka dawo?,wallahi nidai tsoro nakeji "na faɗa ina ƙara sausauta murya ta.
"Kinga wallahi yanzu muka fito daga meeting,so innayin sallan magrib zan dawo".
Ɗaukewar da wutar bob ɗin dasuke haska ko'ina na cikin falon sukayi,sakamakon ɗauke wutar nepa da akayi.Kafin kuma sola ta fara nata aikin yasanya ni ɗago kaina ina sauƙe idanu akan bob ɗin kafin nace"To shikenan tunda kace salla zakayi,amma dazaran ka iddar ban yadda a tsaya a ko'ina ba sai gida".
Sai daya murmusa kafin yace"Consider is done ranki ya daɗe".
Nima darawa na yi kafin daga bisani mukayi sallama,Ina zaune akam sallaya na iddar da sallan isha'i kenan naji ƙara shigowar motarsa,saurin shafa addu'ar dana keyi nayi sannan na miƙe tare da cire hijab ɗin dake kaina na cillashi akan bed na fito.
Sanda na fito yana dai-daita parking cikin harabar gidan da ƙwayayen wutar lantarki suke hasko ko'ina kamar ba dare ba.
Ƙarisowa gare shi nayi ya riƙo ni muka shigo cikin gidan,sai na rakashi bathroom ɗinsa yayi wanka sannan muka fito abinco mukaci,sannan muka cigaba da hirar mu.
Ranar duk yanda zuciya ta take ƙara ayyanano min tsanar Habib kawarwa nayi na zage mukayi hirar mu.
Haka rayuwa ta cigaba da juyawa,lokaci na tafiya yayin da duk wani bugun ko wani daƙiƙa na agogo tsanar Habib dake sake hayayyafa a cikin zuciya ta.
Ana haka muka koma makaranta,idan na fita ji nake kamar kar na dawo cikin gidan.
Mota Habib ya saya min sannan ya ɗauko min drivern da zai dinga kaini kafin nima na koya.
Tun ranar da aka kawo ni gidan Habib,bamu taɓa haɗa ɗaki dashi ba har izuwa wannan lokacin.
Sau ɗaya yayi ƙoƙarin aikata hakan bayan mu kwanta sosai nake,sakin kukan duk yanda naso dannesu kasa yin hakan nayi sai da suka fito.
Tashi yayi tare da kunna wutar dake kan site drawer a gefan shi yana cewa"Hibba lafiya?,meya same ki?".
Rasa abin faɗi nayi sai tsananta kukan danake yi danayi,matsuwa yayi tare da kamo hannuna.
"Meya ke damunki,ki sanar dani "ya ƙara tambaya a karo na biyu.
Sauke ajiyan zuciya nake a hankali cikin kuka nake faɗin"Kayi haƙuri Habib wallahi ban iya kwana tare da mutum ba ɗaki ɗaya ba,balle kuma ace gado ɗaya".banida da abunda zan faɗa a wannan lokacin daya wuce haka.Ƙara matse hannuwa na dake riƙe cikin nasa yayi da ƙarfi,sai da hannu na yayi wani ɗan ƙara.
Manyan idanunsa daya ƙara waresu ya kafe ni dasu, sai a sannan naga wauta na ƙarara bai dace a matsayinsa a gare ni ba faɗa masa wannan maganar ba.
Saurin sunkuyar da kaina ƙasa nayi ɗago haɓata yayi da hannunsa.
"Duk wani abunda zai zamto silar wanzar da farin-ciki a fuskar ki,ki sani ina sonsa koda kuwa hakan na nufi nizan cutu"ya faɗa yana ƙara kafe ni da ido.
Wasu hawaye ne suka biyo gefen kunci na,nan baki na ya ɗauki rawa haƙware na har ƙara sukeyi kamar mai rawar ɗari nace"Habib dan Allah ka tayani addu'a Allah ya kawo min sauƙi cikin gaugauwa".
"Ko yaushe kina cikin addu'a na hibba matuƙar ina cigaba da numfashi a goron duniya bazan daina miki addu'a ba".
Ya faɗa yana lumshe idanunsa sa ya buɗe su yayin da yake miƙewa,Magana na fara ƙoƙarin yi amma yayi saurin dakatar dani da faɗin"Ya isa haka bana buƙatar kice komai,kuma wallahi har ga Allah banji haushin ki maganar ki nasan daman dole kiji abun wani irin,saboda rashin sabo".
Kaina kawai na ɗaga masa alamar ina sauraron sa"Ki kwanta yanzu kar gobe ki makara zuwa school ko?".
Ya faɗa yana rufa min blanket ɗin,sai daya min addu'a ya shafa min sannan ya fita.
"Hamma inasonka"na faɗa ina bishin da kallo.
"Nima haka Hibbatuu"
Ya faɗa tare dajan harafin ƙarshen,hakan ya sa na tino da Inna a lokuta da yawa haka take ƙira nada hHibbatu.
Duk yanda naso nayi bacci kasa zuwar min yayi tashi nayi,naci kuka har na godewa rabbana.
Sosai kaina yake sarawa,tashi nayi na ɗauro alwala nazo na fara salla ina iddarwa na fara karatun qur'ani.
Sai wajen ƙarfe uku sannan na samo bacci asuba ma a makare nayi sa.
Sannan na haɗa breakfast nayi wanka,nayi shirin tafiya makaranta na fito.
Har ana neman ƙarfe takwas,Habib bai fito ba ɗakinsa na nufa na tura ƙofar a hankali.
Tare da rangaɗa sallama yana kwance akan sofa daga yanayin,sa na tabbatar da dakyar yasamu baccin.
Matsowa nayi na tsaya kusa da kujeran dayake kwance kallo ɗaya nayiwa fuskarshi na ɗauke kaina tare da runtse idanuna da ƙarfi.
Sosai fuskar shi ta ƙara baƙancewa a idanuna ƙwayar idonsa,da haƙwaransa sune kawai nake ganinsu da haske.
A jikinsa yaji ana kallon sa a hankali ya fara ware idanunsa saurin maida hawayen dasuke shirin zubo min nayi.
"Hamma ka tashi lokaci fa ya ƙure"na ɗaure na faɗa yayin da wani miyau mai ɗaci ya taro min a baki na.
"Subhanallahi!"
Yana faɗa yana ƙoƙarin tashi,tare da sauƙe idanunsa akan agogon dake maƙale cikin wall ɗin bedroom ɗin.
Toilet na shiga na haɗa masa ruwan wanka sannan na fito,towel na basa sannan ya shiga wankan.
Sai danaga shigar sa sannan na saki kukan dayake nuƙurƙusa na cusa kaina nayi cikin gwiwoyi na.
Tabbas nasan ina cutar da Habib amma bayin kaina bane nima.Na kasa tabbatar da yaƙinin da iyayen habib suke dashi akaina,na zan samarwa ɗannasu ɗan gaban goshi farin-ciki.
Jin kamar za'a buɗe ƙofar banɗakin,ya sanyani sauri goge fuska ta.Na fara ciro masa kaya shadda ce nevy blue.
Wacce taji aiki sannan na ciro masa hula da agogo,taimaka masa nayi na shirya sannan muka fito falon.
A gurguje mukayi breakfast ɗin kasancewar inada lectures ƙarfe tara,sai dana bashi maganin sa yasha sannan muka fito.
"Yau fa nizan kaiki school"ya faɗa yayin da muke nufar cikin parking lot ɗin,yana karkaɗa key ɗin dake hannun sa.
Kallo shi nayi tare da sakar masa murmushi sannan nace"A'a Hamma na yafe kar kayi lattin zuwa office".
Sai daya ɗan hararo ni sannan ya shiga faɗin"Aikin me nakeyi dahar zai hanani kaiki school na yau kawai?,to drivern ma tsallamar sa za'a yi,daga yau nizan na kaiki kuma ina ɗauko ki "
"To ranka ya daɗe yanda kake so hakan za'ayi".
"Yauwa dan abin ya fara motsawa"ya faɗa yana buɗe min ƙofar motar.
"Meye kenan?"na jefa masa tambayar tare da tsaida idona akan sa ina jiran amsa ta.
Sai daya juya idanunsa kafin yace"kishi mana".Sosai ya bani dariya yanda ya juya idanun nasan,kamar wata mace.
UWATACE SANADI
Narh
_Maimunah Tijjani Iyam_
______________________
Page 2⃣6⃣
Har muka isa cikin makaranta bamu daina hira ba,ba tare da san rayukan muba mukayi sallama.
A wajen na tsaya ina bin bayan motar da kallo,yayin da yake ficewa daga cikin harabar makarantar.
Nauyayyen ajiyan zuciya na sauƙe ina ma-inama ace farin-ciki zai ɗaure a zaman mu,ina ma ace zamu rayu kamar ko wasu ma'aurata,zanso na zamewa habib abokiyar rayuwa ta ƙwarai incike duk wani giɓin dake cikin zuciyarsa.
Ta yanda bazai nema komai,daga gareni ya rasa ba ko badan soyayyar dake nuna min a aikace ba.Dan ya cancancin hakan daga gare ni.Nasha jin ana faɗar cewa "zuciya nason wanda yake kyautata mata".
Amma narasa gane tawa zuciyar wata iriyar zuciya ce,marar godiyar Allah da duk yanda habib ke kyautata mata hakan ya kasa tasiri wajen canzuwar ta.Bansan sanda na fara hawaye ba sai ji danayi wata ƴar department ɗinmu Limat Auwal ,ta faɗa kafaɗuna tare da faɗin"Fatima suleiman lafiya kike tsaye ana ke ɗaya kina hawaye?,gashi har an kusa shiga lectures".
Saurin ƙirƙiro murmushi nayi na yaɓa a fuskata kafin nace"Lafiya kalau wallahi kawai,yau na tashi banajin daɗin jiki nane".Na ƙarishe maganar ina share ƙwallar da bakin hijabi na.
Kallon da take bina dashi,ya tabbatar damin da bata yadda da abin dana faɗa mata ba.Gaba nayi na ɗauki hanyar dazai sadani,da department ɗinmu ina cewa"Kinga kizo mu tafi,kinsa halin lecturer ɗin nan inya rigamu shiga ba barin mu zaiyi mu shiga ba".
Biyo baya na tayi da ɗan saurin ta kasancewar duk makarantar ba wanda baisan halin prof A.S karumi ba,matuƙar ya rigaka shiga class to saidai kayi zaman ka a gindin bishiya dan bazaka shiga ba.
Ƙarfe sha biyu muka fito,masallaci mukaje mukayi sallama sannan muka saya abinci mukaci.Sannan muka koma lectures wanda muke dashi ƙarfe biyu,sai ƙarfe huɗu sannan muka fito.
Habib na ƙira na sanar dashi baifi mintuna goma sha biyar ba yazo.Gidan Ummi muka nufa ya sauƙe ni kan zai dawo anjima ya ɗauke ni,A falon ummi na tarar da duk mutanen gidan hadda daddy.
Cike da farin-ciki suke amsa gaisuwar tawa,yasira kam kamar ranar ta fara gani na tana maƙale gefe na tana faɗa min yanda tayi missing ɗina.Nan muka zauna muka sha hirar mu,hadda sayyid dan shima yazo gida lokacin.
Sai bayan magrib sannan habib yazo,muna zaune nan a falon ya shigo da sallamarsa ummi ta amsa.
"Ango mijin amarya sai yau aka tino damu"Sayyid ya faɗa yana duban wayarsa.
Ɗauke kansa yayi kamar baiji abinda ya faɗa ba,ya ƙariso ya zauna ya gaida Daddy da Ummi,sannan yasira da Sayyid ma suka shiga gaishe shi.
Amsawa yayi tare da yiwa Yasira ishara da hannunsa akan tazo nan kuwa ta dawo kusa dashi ta zauna."Kai kuma meka dawo yi?,Sayyid kana wasa da aikin nakan nan fa"cewar Habib.
Ajiye wayarsa da yake latsawa tun ɗazu Sayyid yayi sannan yace"Haba!Hamma ni shikenan kuma bazan so gida ba,haba satina nawa acan Hamma ka dubi fa duk yanda na rame".
"Kai dai kam,Sayyid sai shiriyar Allah yanzu ne lokacin dayafi dacewa ace ka ƙire aikinka da muhimmanci".
Daddy ne yayi saurin amshe zancen ta hanyar faɗin"Gaskiya ne abinda Habib ya faɗa,ni na rasa me kake zuwayi gidan nan yanzu yaushe ka tafi har ka dawo,suma makarantar dasuke barinka kakeyin son ranka".
"Yanzu dani ne da ya fara cewa ni malalaciya ce kullum sai zaman gida"Yasira ta fada tana watsa masa idanunta.
Miƙewa Sayyid yayi tare da shurin Yasira da ƙafa,sannan ya zauna kusa da Ummi tare da kwantar da kansa akan cinyar ta.
"Ummi kinajin su ko wai hadda wannan parrot mouth ɗin ma duk sun saku ni gaba,Dan Allah inbanzo na ganku ba ina zanje".ya ƙarishe maganar tare da shagwaɓe fuska.
Ummi tace"Haka ne Sayyid duk ka kyale su ko yaushe kazo zan buɗe maka ƙofa".
Dariya muka saka sosai,nikam hadda riƙe ciki sai da mukayi sallan isha'i anan mukaci abinci sannan mukayi azamar tafiya.Kamar nace masa ni ana zan kwana,sai kuma naga kamar hakan dazanyi zan cutar dashi da yawa kuma zaisa su ummi suyi zargin wani abun.
Haka muka tafi bayan Yasira ta mana alƙawarin zuwa tunda muka fara tafiyar bance uffan ba shi kaɗai yake ta surutunsa.
Muna isa kowa na wuce ɗaki wanka nayi sannan