Showing 63001 words to 66000 words out of 104857 words
Chapter 22 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
amsa a ladabce,duk dana kusa makara sai dana leƙa sashin Hajja sannan muka wuce,har muka isa ina karatuna.
Ƙarfe sha biyu muka fito lokacin sosai rana ta kwalle,mai buso zafinta ina tsaye ina ƙoƙarin dannawa Malam Habu ƙira na hango shigowar motar Habib,hakan yasani gimtse ƙirar.
Ya faka motar na shiga sannan muka wuce,tun muka fara tafiyar bance ko kanzil ba har muka isa gida part ɗina na wuce na sakewa kaina ruwa sannan nayi sallah,na fito na shiga part ɗin Yasira saboda naga alama masu ganin ɗakin amarya sunzo.
Muka gaigaisa dasu wanda mafi yawansu dangin Ummi ne,Batul na lura wacce tun shigowana falon take bina da kallo tana tseduntawa wasu ƴan mata biyu dasuke zaune kusanta cewa nice matar Hamman.Ɗayar tace"kai!Gaskiya masha Allah gata kyakykyawa da ita ga kuma kyawun hali dan naji anacewa komai na bikin da ita akeyi,bata nuna wani kishi ba".Ɗayar ta kuma cewa"Ai wallahi nikam ma burgeni tayi,kuma fa ba babba bace dan ance Adda Yasiran ma ta girmeta".Batul kam taɓe baki kawai tayi tana sauraronsu daga bisa naga ta ciro wayarsa daga cikin jakar tana latsawa.
Wani sanyin daɗi ya sauƙa min dai-dai ƙalbina,saboda maganganun ƴanmatan sunmin daɗi dai-dai shigowar Maryam falo na sakar maka lausasar murmushi tare da miƙewa na isa gare na karɓa Abbul-khair.
Sannan naja hannunta muka zauna muna gaisawa,Ina tambayarta yaushe zasu tafi tace min gobe.
Har yamma Maryam ta wuni tare dani kafin muka wuce part ɗina,zatayi sallah.
"Kai!ƙawata gaskiya kin burge mutane da yawa a auren nan,jiya bayan tafiyarku bakiji ba yanda aketa yabonki ba.Gaskiya kinyi namijin ƙoƙari yo nikam ai randa akace Bashir zai ƙara aure ai sai dai a tarar da gawarta wallahi dan zuciyata bazata jureba".
Maganganun Maryam kenan danajisu a tsakiyar kaina,lokacin danake buɗe wardrope domin ɗauko mata hijabin dazatayi sallah.takuwa nayi na iso gareta ina ƙara ƙawata fuskana da murmushin danakejin ciwonsa a zuciyata ba tare danasan dalili ba sai dana miƙa mata hijab ɗin nace"Maryam ai zaman aure sai da siyasa da kuma dabara,koni kaina inace banajin kishi acikin raina to nayi ƙarya amma farin-cikin Habib ya fiyemin duniya da abunda ke cikinta.domin shine mutum na farko daya fara nunamin cewa nima mutumce mai ƴanci,shine mutum na farko daya ƙawata min rayuwata da babu abun dana saba dashi face baƙin-ciki,ƙunci da wahalar rayuwa ya sadaukar danashi farin-cikin akan nawa.ya zauna dani ina da lafiya har yanzu danake cikin halin jinya bai canza min ba balle ya jugeni".
"Hmm to Allah yasa ya ɗaure ahaka,dan kinsa wasu mazan da zarar sunyi amarya duk wulaƙancin duniya sai su nema juyeshi akanki".
Sai dana gyarawa Abbul-khair kwanciyarsa kafin nace"Maryam ai amarya kona buzuzune sai anyi mararinta,kuma komai lokaci ne wataran zai wuce matuƙar akayi haƙuri".
"Hakane kuma"ta faɗa tana ƙoƙarin tada kabbara,nima na tashi nayo alwala sannan na tada tawa sallan,ina iddarwa sallamar Batul yana sauƙa a dodon kunne na kulolin abinci suka ajiye wanda aka aiko daga gidan Ummi zasu tafi nace"wannan abincin ai yayi yawa ku maida sauran kula ɗaya ma ta isa".
Batul ta juya tare da faɗin"aw ai daman mun zata akwai ƴan-uwanki ne shiyasa aka aka kawo muku har haka".tana kawowa nan a maganarta ta kwashe kulolin biyun ta juya ta fita.
Da kallo nabita har ta fice daga ɗakin,yayin data buga ƙofar harsai datayi wata ƴar ƙara wanda hakan yasa Abbul-khair firgita daga baccin dayakeyi yana tsala ihu,Maryam ta ɗauke shi tana jijjigashi har ya koma ta kwanta dashi.
Maganganun Batul sai najisu kamar ba'a take min,ƴan-uwa kam nima kaina nasan bandasu wanda har zasu damu da lamaruna balle kuma sha'anin rayuwata,Inna ce kawai sai rabin ɓarin jikina Yaya Fawas.wata ƙatuwar ajiyan zuciya nasauƙe zuciyata na rayamin cewa yanzu kowa a danginsu yasan Labarin rayuwata kenan?,wataƙil har yanda na baro gida saboda auren Nazifi duk sun sani,wata zuciyar tace min tayaya ma bazasu sani ba tunda har ƙaramar yarinyar nan Batul tasani ai kuwa ma yasani.
Nayi saurin kawar da hawayen daya taru acikin ƙuryan idona nacewa Maryam ta sauƙo muci abincin,na zuba mana mukaci tare muna gama ƴan makarantar su Lima Auwal dasu ƴan department ɗimu sukazo suna mim Allah sanya alkhairi dasuka tashi tafiya nabasu savouirners ɗin nayi.
Maryam kam sai datayi sallan magrib sannan Habib sukazo tare da Bashir ya ɗauketa suka tafi.part ɗin Yasira ma babu kowa duk sun watse dan Granny taja musu kunne akan karda wanda ya kwana abar Amarya ta sake da Angonta.
Part ɗina na koma nayi sallah nayi wanka sannan na fara katarun jabarawar dazamu ƙarƙare gobe da yarda mai duka.na daɗe inayi kafin nayi shirin kwanciya naso zuwa part ɗin Yasira amma dana duba lokaci naga har sha ɗaya tayi yasa nayi kwanciyata.
Naje zan rufe ƙofar ɗakin, jiri na ɗibata yana nema dokani da ƙasa tabbas banida lafiya kuma na ƙudurce ziyarta likita gobe,na farajin ana turo ƙofar nayi saurin matsawa ina ƙara ware idona akan ƙofar dan bana tsammanin kowa yanzu.
Habib ne tsaye a ƙofar ya shigo ciki,nakai hannu na nasha hawayen fuskata wanda suka fara zuba ba tare da sanina ba nace"Lafiya naganka anan?".
Ya raɓa tagefe na ya shigo ya riƙo hannuna yace"meyasaki hawaye?"na ƙirƙiro murmushi nace"Abune ya faɗa min a ido,sai kuma baccin danaji wanda shiya haifar min da hawayen,duk amma ba wannan ba kai daya kamata ka kasance da Amaryar ka meya fito dakai?".
Ƙara riƙon dayayiwa hannuna yayi yace"zuciyata ta kasa samun nutsuwa jinake inhar ban ganki ba bazan kwana lafiyaba"nayi saurin katseshi nace"Habib banason ka kasance cikin irin mazajen suke karayin adalci a tsakanin matayensu,Yasirama matarkace kuma tana buƙatarka a halin yanzu kaje ka sauƙe hakkinta dake wuyanka".nakai ƙarshen maganar ina zare hannuna daga cikin nasa.
Magana ya somayi na hanashi wannan damar nace"koma menene gobe zamuyi maganar,gobe zamugama exams kuma inson naje asibiti naga likita dan banajin daɗi".
Ƴar siririyar dariyar wacce ta tsaya iya kan leɓɓansa yayi yana riƙo hannuna na kwanta ya lulluɓamin blanket yace"meyake damuki?".
"Kawai banajin daɗin jikinane sai kuma ciwon kan daya sakoni gaba".
"Ba matsala goben sai nazo na kaiki ko MY JOURNALIST".na saki dariya mai sauti nace"A'a zanje dakina".
Yamin saida safe sannan yafice daga ɗakin,har cikin raina banajin daɗin abunda Habib yakeyi na kasance a ɗakina ako wani dare cikin kwanakin kwanan Yasira,ya zama dole nayiwa tufkar hanci tun kafin kwarɓar tamu tayi ruwa.
UWATACE SANADI
Tsarawa/rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________
Page 4⃣2⃣
Washe gari na tashi cikin matuƙar annushuwa raina fari tas!,zuciyata tamin ƙal!wanda haka yanada nasaba da tsayiwar daren danayi jiya ina nemawa kaina zaɓin Allah arayuwata.
Bayan na gama haɗa mana breakfast naci nawa,sannan na shirya tafiya school zana exams ɗina a ƙarshe,wanda daga shi zamu shiga ajin ƙarshe a jami'in babu abunda yake damun raina dan inajin na kusa cikawa Yaya Fawas burinsa duk dashima ɗin ya gama NCE ɗin daya jona har ya fara aiki a wata makarantar kuɗi dake azaren,dakuma ƙudurin Abba nason muyi karatu.
Kulolin Abincin nasa cikin basket na nufi part ɗin Yasira,tsit!kamar babu wasu halittun dake zauna cikin part ɗin shurun danayi haka ya tabbatar min dabasu tashi daga bacci ba,na jere musu abincin akan dinning sannan na ciro maganin Habib daga jakata na ajiye akan dinning ɗin da nufin inya fito yagani yasha.
A Tsaitsaye na shiga sashin Hajja muka gaisa sannan,na karɓa key awajen malam Habu yau ni nakeson tuƙa kaina.
Yau duk wanda ya kalleni acikin makarantar yasan nakai ƙololuwa acikin farin-ciki,dan ya kasa ɓoyiwa sai daya shimfiɗa ƙarara akan fuskata.
Muna fitowa daga exams hall ɗin kowa murna yakeyi nagama jarabawar damukayi,sauran mu ganin result daganan kuma mun tafi ajin ƙarshe,naja motar na nufi asibiti.
Na zayyanawa likitan abubuwan dake damuna tace naje amin gwaji tukunnna,nabi nurse ɗin aka min gwajin sannan na dawo ofishin na zauna,bai ɗau lokaci ba nurse ɗin ta shigo ta miƙa mata sakamakon ta fita,likitan ta fara dubawa sannan na ajiye takardan gefe guda ta zuba min na mujiya kana tace"Baiwar Allah abinda sakamako ya nuna shine kina ɗauke da hawan jini kuma jininki ya sauƙa sosai,akwai buƙatar ki maida hankali wajen kula da lafiyarki kuma ki cire damuwar dake ranki dan yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan dake haddasa wannan ciwon,zan ɗauraki akan magani dan Allah sai ki kula ".ta kai ƙarshen maganar tare da fara rubutu ajikin wata takarda.
Tunda ta fara maganar na nema annurin fuskata na rasa,duk farin-cikin danake ciki ya kau yayin da baƙin-ciki ya maye gurbinsa,take naji zuciyata ta karaya na fara hawaye.Likitan ta ɗago kanta tana dubana tace"Subhanallahi!haba ƙanwata ai wannan ba wani abun damuwa bane,matuƙar zaki daina saka damuwa acikin ranki kuma ki kula dashan maganinki zaki rabu da wannan ciwon ki daina kukan ya isa haka".ta faɗa tana miƙo min handkerchief ɗinta nakai hannu na karɓa ina goge hawayena.
"Ya Allah wata irinyar ƙaddarace wannan wanda take bibiyar rayuwata tamkar inuwa,duk inda na shiga saina tarda ita Allah mena aikata arayuwata daka hanani jindaɗi a duniya?duk inda na raɓa babu sauƙi sai ƙunci Allah ka jarabce ni da jarabawa iri-iri daga wannan sai wancan ko yanzu ma acikin jarabawar nake,Ya rabbi samawati ka kawo min sauƙi cikin al'amurana kabani ikon cinye wannan jarabawar".
Jidanayi likitan ta fara bani haƙuri tare da nunamin na ƙarfafa kaina,hakan ya tabbatar min da cewa a fili nayi maganar ba'a zuci ba kamar yanda na zata.
Takardar result ɗin kawai na ɗauka na gyara zaman jakata saman kafaɗata,nace"Nagode"sannan na fita daga office ɗin ta tsaidani ta miƙo min takardar maganin data rubuta min tana ƙara bani wasu shawarwari sannan nafito daga office ɗin,pharmacy na wuce nasayi maganin sannan na dawo mota.
Na jingina kaina ajikin kujerar ina fidda hawaye,na daɗe acikin wannan halin kafin na figi motar nayi gida,ina isa na wuce part ɗina kai tsaye bedroom na wuce na ɓoye maganin acikin kayana sannan nayi alwala nayi sallan zuhr ina iddarwa na ɗaga hannayena saman ina nema sauƙi agun sarkin da babu kamarsa.
Sai dana shafa addu'ar sannan na zare hijabin na fito na shiga part ɗin Yasira tana zaune tana kallo na isketa,tamin sannu da zuwa na amsa ina tambayarta Habib yaga maganinsa kuwa akan dinning dana ajiye?tace yagani harma yasha kafin ya fita,nayi hamdala sannan na zauna muka cigaba da kallon tare.
Sai damukayi sallan Asr sannan muka shiga kitchen domin ɗaura girki,an zuba kayan abinci sosai a store ɗinta anan mukayi girkin sannan muka jeresu a dinning na wuce part ɗina domin nayi wanka,wankan nayi sannan nasaka doguwar rigata anko sunnan Abbul-khair na wuce wajen kayana na ɓalla maganin nasha.
Sannan na mayar dasu gurbinsu na ajiye,dan banason kowa yagansu koda Habib ne kuwa balle Yasira shiyasa banyi niyyar sanar dasu ina ɗauke da wannan ciwon ba.
Shigowar Habib naji yasa nafito da saurina na tarbe shi ina masa sannu da zuwa,bai daɗe da shigowa ba Yasira ma ta shigo muka zauna zaman hira,Habib na tambayata jarabawar ƙarshe inata basu labarin irn murnan dasu ƴan department ɗinmu sukayi,wasu har tsere mashin sukayi.
"Ya asibitin kinje?"ras!naji mummunar faɗuwar gaba na harhaɗo jarumta nace"E naje daman ulcer ce keson kamani kuma an bani magani".cike da kulawa yake faɗin"Allah ya sauwaƙe gaskiya ya kamata kina bawa kanki kulawa,kamar yanda kike kulawa damu acikin gidan nan".
Yasira da ɗaura danata zancen"Anty gaskiya Hamma ya faɗa".nace"in sha Allah zan kiyaye kodan farin-cikinku dakuka kasance abu mafi soyiwa a gareni".suka saki dariya Habib yana ƙarasama mana albarka.kafin muje part ɗinta mukaci abinci na musu sai da safe,sannan Habib ya rakoni kamar kullum.
Sosai na raya daren da salllolin dare da kuma karatun alqur'ani,washe gari ina iddar da sallan asuba kuwa na danna nomban yaya Fawas sai da kiran ya kusa tsinkewa sannan na ɗaga tun kafin mu gaisa ya dara jefo min tambayar "Lafiya naga kiranki a wannan lokacin?".
"Lafiya kalau Yaya Fawas inaso nasanar dake wani abune"yayi saurin yace"Inajinki my cute angle menene"ya kai ƙarshen maganar cike da zaƙuwa.
Sai dana tare ruwan hawayen dasuka ciko kurmin idanuna sannan nace"Yaya Fawas jiya naje asibiti bayan amin gwaji aka tabbatar min da ina ɗauke da Hawan jini,wallahi zuciya takusa tarwatsewa Yayana wannan wata iriyar rayuwace na gaji da ita wallahi na tsani duniyar gabaɗaya da abunda yake cikinta,ga wannan ƙaddarar data sameni tun lokacin danayi ɓari har izuwa yanzu da muke wannan maganar kullum cikin jini nake,wannan shine dalilin dayasa iyayen Habib suka haɗa aurensa da ƴar-uwarsa,wallahi ina cikin damuwa zuciyata tana min nauyi yanzu tinanin Umma ya uzura min sosai Yaya Fawas ka kusa rasani inajin hakan a jikina".na ƙarishe maganar ina kifa kaina akan pillow.
Kusan mintuna biyu a tsakani kafin Yaya Fawas yace"Hibba ƙanwata kowa da irin ƙaddararsa a rayuwa mukuma haka Allah ya ƙaddara mana ya bamu Umma uwar dabata damu damu ba,balle taji damuwarmu acikin ranta.Sai dai a hakan mafa mufin dubun mutane gata domin wasu ko fuskar iyayensu basu sani ba,basu taɓa rayuwa dasu ba.Akwai wani abokina Imam shi kuwa ƙaddararsu mahaifiyarsu mahaukaciya ce,hauka takeyi tuburar har tsirara tana yawo akan titi kinga gwara mu ki kwantar da hankalinki ki daina kukan sai muyi magana ko?".
Nace"To"sannan na ɗago kaina daga kan pillow nafara share hawayena.
"Tabbas wannan babban lamarine amma kin sanar da Habib kina ɗauke da wannan ciwon?"a sanyaye nace"ban sanar dashi ba kuma na ƙudurce bazan faɗawa kowa ba face kai,ko Inna ban sanarwa ba".
"My cute angle ba'a ɓoye ciwo domin dole wataran zai bayyana kansa,amma meye dalilinki na ɓoye hakan?".
"Bazan iya sanar da Habib ba domin yanzu farin-ciki yafara wanzuwa acikin rayuwarsa,sanar dashi wannan lamarin zai ɗaga masa hankali fiye da tunani dan yana da sa abu aransa".sai daya numfasa kana yace"Ki sanar da Ummi na tabbatar zata nemo mana mafita,sannan maganar jinin nan gaskiya ya kamata mu tuntuɓi malamai don yafi kama da sihiri".
Sai dana zuƙe majinan kukan dayazo mini kana nace"in sha Allah zanyi hakan zan sanar da ita".
Sosai Yaya Fawas ya cigaba da kwantar min da hankali,har sai danaji raina yafara samun nutsuwa sannan mukayi sallama kan zan ƙira na sanar dashi yanda mukayi da Ummi.
Tashi nayi na zare hijab ɗin danayi sallan dashi,na fito kitchen na wuce na haɗa mana breakfast sannan na dawo nayi wanka nafito falon ina zama Habib da Yasira suna turo ƙofar falon suka shigo,na miƙe tare da gaida Habib ya amsa sannan muka gaisa da Yasira.
Ganin akwatinsa a hannun Yasira yasani faɗin"tafiya zakayi ne naganka da kaya"na ƙarishe ina tsaida idona akan akwatin.
"Wallahi zanje Adamawa ne akwai mutane dasuke samar mana da gyaɗa acan,zamu gana dasu zan iya kaiwa kwana biyu zuwa uku haka".Tsuke fuska nayi nace"yaushe aka shirya tafiya ni ko sani banyi ba,to Allah yakaika lafiya yakuma tsare ka".ina kawowa nan na nufi dinning.
Banyi zatoba kawai naji ya rungumoni ta baya nafara kiciniyar raba jikinsa danawa,amma na kasa muryarsa ta bugi dodon kunnena yana cewa"Haba wifey wallahi jiya da daddare ne suka ƙirani,kuma tafiyar tanada muhimmanci shiyasa zanje dakaina".
Nasarar zare jikina nayi daga riƙo dayayi min nace"To Allah ya kiyaye dan Allah inkaje ka kula dashan maganinka akan lokaci".ya gyaɗa min kai alamar zaiyi hakan.
Ina juyowa idanuna suka sauƙa akan Yasira wacce ta ɗauke kanta daga garemu,ta maida shi ga kallom TVn dake aiki acikin falon.kunya ta lulluɓe ni na cillawa Habib wata uwar harara watau yasan tana wajen yamin haka,da watace ai da mun kwashi ƴan kallo danma Yasira duk halayan Ummi ta ɗebo na haƙuri da kawaici.
Jawo hannunta nayi muka wuce dinning ɗin,na fara zuba mana abinci kota kansa banbi ba sai dana gama na jayo nawa gabana nace"ki zubawa mijinki abinci"ta gwalo idanu waje tace"Anty ki cika ladanki kawai ki zuba masa".
"Ai kema inason ki sama ladanne shiyasa nace ki zuba masa da kanki"ta cuno baki sannan ta tashi ta zuba masa yace"ba komai nasan zaman dazan nayi daku yanzu,tunda haɗe min kai zakuyi".nida Yasira a tare muka bushe da dariya mai sauti.
Da haka muka gamacin abinci mukayiwa Habib takiya har harabar gidan,sai daya bi kan dukka ma'aikatan gidan ya sanar dasu zaiyi tafiya ya basu amanar iyalinsa suka masa tare da masa addu'o'i.
Nan nake sanar dashi zamuje gidan Ummi yau tun kafin na ƙarisa Yasira ta saki shewa haɗi da tsalle tana cewa"Yau zanga Ummina zanga Ummina".
Farin-cikin danagani akan fuskarta haka nan naji zuciyata karaya,tinanin Umma yafara dawo min cikin kwakwkwalwa ta,idan kaga mun cikin farin-ciki da walwala to ranar Umma bata gidan kodai tayi tafiya ko kuma tana wajen sana'ar ta,da zaran ta dawo duk walwalar mu take gushewa.
Acikin zuciyata nake ayyano irin farin-cikin Yasira take ciki dan taji zamuje ganin Ummi,sai dai nakasa samun mizanin dazan kwatanta shi,daman haka ake kasancewa cikin irin wannan farin-cikin idan ɗa yaji an ambaci sunar mahaifiyarsa?na jefawa kaina tambayar inama zan iya dawo da hannun agogo baya inama zan iya dawo da rayuwar damukayi abaya duk dacewa babu komai acikinta illa ƙunci da baƙin-ciki amma inason kasancewa da Umma koda na daƙiƙa ɗaya ne.
Dafa kafaɗata da Habib yayi yasa nadawo daga cikin tinanin danayi nisan kiwo acikinsa,yafara tambayata lafiya nace masa lafiya kalau kawai dai ni yamin alƙwarin zaina shan maganinsa akan lokaci dan shine babban matsalata,dan intashine zai iya kwana uku bai shaba.
Shafo kaina yayi yace"in sha Allah zansha koda na kawar da damuwar dake kan fuskarki".na saki murmushi tare da godiya sannan nashiga yi masa addu'o'in neman tsari da kariya.
Yasira taso sukayi bankwana sannan Malam Habu ya wuce kaishi airport ina tsaye a harabar gidan har sai danaga ficewar motar sannan na koma part ɗina,Yasira ma tayi nata domin shiryawa sai dana sha magani na sannan na fara shiri.
Cikin mintuna dabasu haura arba'in na na shirya na fiti part ɗin Yasira na wuce ganin har yanzu bata fitoba na sameta ta baza kaya akan bed ɗinta tanacan gefen ta buga tagumin.na tambaye ta lafiya?wai ta rasa kayan dazata sa.
Murmushi kawai nayi araina nace ƴaƴan masu kuɗine kena akwai sakalci,sannan na zaɓo mata wata doguwar riga ɗinki buba iya gwiwa da strength siket ta saka yamata ɗas!kuwa dayake datana da jiki.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani iyam
_______________________________
page 4⃣3⃣
ni nayi driving ɗinmu har gidan ummi ina gama dai-daita parking muka fito yasira har kusa tuntuɓe tayi tsabar sauri datakeyi wajen shiga gidan.
a falo muka iske ummi da sayyid,yasira ta faɗa kan ummi tana faɗin"nayi kewarki ummi wallahi sosai faɗanki da