Showing 90001 words to 93000 words out of 104857 words

Chapter 31 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7331

ta shiga faɗin tanason a bata Mu'afsa ta riƙeta a wajenta ƙirjina ya shiga bugun lugudai jikina yayi sanyi ƙalau ina tino furcin Yasira na ƙarshe a gare ni"Amana ce a gare ni Mu'afsa duk yanda zanyi bazan yarda tayi nisa da niba"amsar da zuciyata ta bani kenan na miƙe na koma ɗaki.
Sara da Marwa kawai nakeyi nakai mari nakai bango ƙiran sallan zuhr yasa na faɗa banɗaki ya ɗauro alwala na fito ina shirin tada sallan Nabiha ta shigo da Mu'afsa ta kwantar da ita tayi bacci sautin tashin muryan Habib danaji a falo yasa nazo bakin ƙofar na tsaya ina bada hankalina ga inda zance ke tashi a cikin falon.
"Granny da anyi haƙuri dai domin kafin Allah ya karɓa rayuwar Yasira sai datace ta mallalawa Hibba wannan ƴa data haifa,sannan kuma amana ce ta bar mata da anyi haƙuri an bar mata ta riƙe tunda ma mai sunan ta ce"furcin Habib kenan daya sanya ni saurin gyara tsayiwata ina jiran amsar da Granny data bashi.
"To shikenan daman wai naga tana zuwa makaranta ne shiyasa nace ko za'a bani ita na riƙe".
"Ai Granny tama kusa ƙare makarantar dan yanzu tana ajin ƙarshe"Cewar Ummi daya sani sauƙe wata kyakykyawar ajiyan numfashi ba shiri na ɗaura da Hamdala sannan na dawo na data sallan na daɗe ina yiwa Yasira Addu'a kafin na shafa addu'ar na damo wa Mu'afsa madararta nazo na tada ita na soma bata sai data daina karɓa dan kanta kafin na toɓeta na mata wanka na shiryata cikin wasu kayan marasa nauyi nan kuwa ta koa baccinta na kwantar.Sallamar Anty Amina yasani saurin ɗago kaina daga wayar da muka soma da Yaya Fawas yanzun nan na tashi na tarbo ta kusa da Mu'afsa ta zauna kafin na ƙare wayar muka fara gaisawa tana ta mamakin girman Mu'afsa kamar ba bakwaini ba rurin da wayata ta soma ya sani karata a kunnena daga ɗayan bangaren yace"Matar aljanna ki fito compound ina jiranki".
"To ga Anty Amina ma kuwa tazo"kamar jira yake yii ya koma cewa"yauwa ku fito tare".cike da mamaki na sauƙe wayar daga kunnena ina binta da kallo kafin nace"Anty Amina Habib na miki magana yana compound"
"To"kawai tace muka miƙe duk muka fito bamu iske Ummi da Granny a falo ba haka nan muka fito compound ɗin,cikin garden muka hangosu an sanya kujeru duk suna zazzaune hadda da Daddy muka isa bakina ɗauke da sallama,sallamar daban iya ƙarisawa ba kenan sauran suka maƙe ƙasan maƙoshina jikina ya ɗauki mazari hannuna dayake rawa na ɗaga na fara nuna shi dashi"KA-KA KABIR".ya miƙe a hanzarce yana kallona sanya yake cikin farar jallabiya da ƙaramar hularta kallo ɗaya zaka sama kaga cikakken ɗan ƙwaya koma ince mashayi gaba ɗaya ko ranar da muke gidan Balaraba aka taho dashi ban ganshi ba domin motar Sayyid sula shiga daga nan kuma suka zarce asibiti dashi.
Anty Amina tayi nasarar riƙo hannuna da har yanzu ban ɗauke shi daga nunin dana keyi da Kabir ba Daddy yace mu iso mu zauna kusa da Ummi na zauna Mu'afsa kuwa Sayyid ya karɓe ta.
"Hibba dan Allah ki dubi girman Allah da manzonsa ki yafe min nida Mahaifiyata tabbas mun zalunce ku daga ke har Anty Amina kuma munga sakayya tun anan duniya alƙwarin Allah ne baya barin haƙƙin wanda aka zalunta,a irin sharrin da bamu miki ba har keta miki haddi naso nayi Allah bai bani dama ba amma yau ke kika zama mana gata a duniya kika saka mana da alkhairi wajen ceto rayuwarta dana Mahaifiyata.dan Allah ki yafe min ko hakan zaisa na sadu da ubangijina lafiya"furcin Kabir kenan yana durƙushe kan gwiwoyinsa.
Kuka nakeyi sosai har ina neman shiɗewa abubuwa da yawa suke dawo mini kamar yanzu suke faruwa mussamman ranar da Kabir yaso mini fyaɗe Balaraba ta kwara mini ruwan zafi tafashashshe a jiki wanda har yanzu tabon bai bar fatar jikina ba yana nan.Granny ta dafo ni"Hibba yayi nadama kuma ya shiryo ki yafe masa domin Allah yana son masu yafiya.
Idanuna suka sauƙa kan Balaraba dake gefe guda tana nata kukan cikin hijabi na zuƙe kukan dana nakeyi ganin Habib ya doso inda nake sunkuya yayi yana min magana wanda ko Ummi dake kusa na bana tinanin data iya jiyo abunda yake furtawa saboda yanda ya sausauta muryarsa"Debbo am tabbas sunyi nadama yafiyarki gare su kan iya zamowa sausauci daga rayuwar ƙunci da sukeyi".
Na yarce ƙwallan dake shimfiɗe saman tudun fuskana"Na yafe mata Kabir daga kai har Mahaifiyarka Allah ya yafe mana gaba ɗaya".Cikin wani kukan ya koma cewa"Anty Amina kema ki yafe mana".


"Na yafe maka Kabir Allah ya jiƙan Malam"Duk aka amsa da Amin Daddy yace nazo alama yamin da hannunsa na kuwa tashi na isa gabansa"Allah ya miki ɗiyata Allah ya albarkace rayuwarki data ƴaƴan da zaki haifa Allah ya shiga cikin lamuranki ya wanzar miki da haske alfarma annabi da alqur'ani"tunda ya fara maganar nake amsa da amin haka ma su Ummi har yake aya.
Sayyid ya miƙawa Kabir Mu'afsa yana faɗa mishi ƴatace,yakarɓe ta yana kallonta da idanunsa dasuke taf!da ƙwalla.ba kunya na miƙe daga gaban Daddy nacewa Kabir"bani ƴata zan shiga ciki"na lura da yanda jikinsa ya ƙara sanyaya ya miƙo min ita yana cewa"Allah ya rayata".
"Amin"na karɓa abata nayi cikin gida nan suka zauna kafin Kabir da Balabara suka tafi Anty Amina ma ko sallama bamuyi ba ta tafi tsawon sauran wunin ranar ban leƙo ko falo ba a ɗaki na ƙarar dashi ina godiya da mahaliccina washe gari su Kawu Isma'il suka zo a ranar zasu koma nijar Daddy yayi ta musu godiya haka suka tafi bayan munyi sallama dasu Farida da Nabiha.
Mu'afsa na hannun Hajja data zo yanzu na barta na wuce ciki lokacin dazan shige ɗaki naji Daddy da Habib da kuma su Ummi da Granny na tattaunawa akan Kabir yanda zasu inganta rayuwarsa tunda ya shiryo ko sana'a ne a sama masa ɗauke kaina nayi nayi shigewata ɗaki ina shiga Yaya Fawas ya ƙirani muka gaisa sannan na sanar dashi abunda ya faru yayita min nasiha sosai akan haƙuri nikam ko yaushe cikinsa nake rayuwa mun daɗe kafin mukayi sallama bayan yabawa su Mahmud mun gaisa.
Ranar da Yasira ta cika kwanaki ashirin da rasuwa ranar da safe Granny da Iya suka koma damaturu da misalin ƙarfe Tara na safe muna zazzaune a falo tare da Sayyid da Ummi,Daddy kuwa tare suka tafi dasu Granny damaturu.Habib ya shigo yanayin daya shiga cikinsa ya sanya dukkanimun jefa masa tambayar lafiya?guri ya nema ya zauna kafin yace"Hibba ki shirya zamuje Gano yanzu"
Cike dason ƙarin bayani muka haɗa baki nida Ummi wajen cewa"lafiya kuwa ko wani abunne ya faru?"
"Ana maka magana kayi shuru wani abunne ya faru?"Ummi ta ƙara faɗa a karo na biyu ya ɗago ya kalleta yace"Baffa ne yace na kaita jikin Anty Hajara ne ya tasha".Ummi ta shiga rafza salati tace na tashi na shiryo yanzu mu tafi na kuwa miƙe ƙirjina na bugun lugudai na saka mayafina sannan na shirya kayan Mu'afsa a jaka tare da madararta na fito na amsheta daga Hannun Sayyid muka tafi Ummi nata mana addu'ar sauƙa lafiya anan ta ƙira Daddy take sanar dashi yace in mun sauƙa Habib ya ƙira shi.
Tunda muka hau titi fargabata ta tsananan ta haka nan cikin mu babu wanda yayi magana lokaci zuwa lokaci na lura da yanda Habib yake yarshe gumi duk da air condition ɗin dake aiki a cikin motar,wata zuciyar ta raya min koma Inna ce ta mutu yake ɓoye min yace wai jikin Anty Hajara ne?.tunin hawaye ya fara wanke mini fuska nace"Dan Allah Habib inma Inna ce ta mutu kake ɓoye min ka sanar dani wallahi zan karɓa ƙaddara aduk yanda ta zomin".
"Debbo am kamar dai yanda na gaya miki haka Baffa ya sanar dani".na sauƙe ajiyan zuciya badan na yarda da kalamansa ba.


UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


______________________________




Page 5⃣8⃣


Har muka isa cikin Gano banida kuzari sai tufka da warwara nakeyi a cikin raina zuciyata tana mini sarƙa yana gama daidaita parking na saɓa Mu'afsa a kafaɗata na nufa ƙofar gidan cikin sauri shima ya kashe motar ya biyo bayana buɗe dukkan muryata nayi na kwaɗa sallama tun a zaure Habib yayi nasarar cinmu mini"Hibba ki nutsu mana ki kwantar da hankalinki".
Ban iya bashi amsa ba nasa kai nayi shigewata cikin gidan ganin Inna danayi suna tsaye a ƙofar ɗakin Hajara ita da Baffa ya sani sakin hamdala ina godewa Allah sannan nayi saurin isa gare ta"Inna lafiya kuwa menene yake faruwa?".
"Jikin Hajara ce ya tashi yau dai jikin yafi na kullum tsanani sai dai Allah ya bata damar buɗe baki tayi magana wanda rabonta da magana har lissafin kwanakin ya ɓace min tun ɗazu take ambaton sunan ki tana cewa a ƙira mata ke tana son ganinki".
Duk na gama ratsa nutsuwa ta nace"tana ina yanzu?"dai-dai nan Habib ya shigo su kayi musabaha da Baffa gaisuwar da ya jefawa Inna ta hanata amsa mini tambayar dana mata a farko."Tana ɗakinta"ta faɗa tana min nuni da ɗakin Mu'afsa na miƙa mata saboda naji tana ƙoƙarin sulalewa ƙasa daga riƙon dana mata na shiga ɗakin duk suka rufa min baya.kusa da ita na tsuguna ina kamo hannunta sannan na furta sunan ta duk halittun jikinta ya sauya ina iya jiyo yanda duk gaɓoɓin jikinta suke karkaryewa abunda yafi sanya mini tsoro a zuciyata kenan ta ɗago idanunta da har sun rufe tace"Hibban ce?"nayi saurin amsawa da"e nice Anty Hajara ya jikin".
"Malam a ƙira min Adda Barira a ƙira min Adda tazo".
Da hanzari yafita ya aika yaro yaje ƙiranta bata ɗau wani lokaci mai tsawo ba ta iso a ɗimauce ta faɗa kan Hajara tana sakin kukan daya sanya mana tausayinsu a zuƙatan mu"Adda ba kuka zakiyi ba tabbas yau ne ranar ƙin dillanci Adda ranar da zamu dibi abunda muka daɗe muna shukawa kuma muka ƙarar da rayuwarmu wajen masa ban ruwa,nidai tawa ta ƙare wannan jinyar ta ajali ce Hibba inaso in sanar dake wani ƙulli".Inna ce tayi saurin faɗin"Ashsha haba Barira keda zaki lallasheta kuma kema kike kukan,Hajara ai zafin jinya ba ita take nuni da mutuwa ba ki daina wannan surutan dan Allah".
"Inna na aikata babban laifi a rayuwata wanda innaje dashi gaban Allah bazan sama rahamarsa ba".Shuru ne ya ratsa ɗakin baka jiyo sautin komai dana munsharin da Mu'afsa take yi akan cinyar Inna.


"Hibba na cuce ki na zalunceki naci amanarki duk saboda son zuciyata na azabtar dake akan laifin da bakiji ba baki gani ba,abun ya faru ne tun daga ranar da kika dawo gidan nan tare da iyayen Habib nayiwa Malam magana akan ban yarda dake ba karuwanci kije kikayi hatta shi Habib ɗin ma wataƙil daruron kine wannan maganar ta fusata shi har ya mare ni abunda bai taɓa haɗa ni dashi ba kenan duka.najewa Adda Barira da maganar ta kuma ɗaura ni akan hanyar data kawo ni izuwa ga nadamar danake ciki yanzu mu muka sa aka cire miki son Habib a cikin ranki kuma aka hanaki jin daɗin zaman gidansa aka haddasa miki ƙiyayyar sa acikin zuciyarki lokacin danajin labarin samun cikin da kikayi sai da mukaga bayansa sannan hankalinmu ya kwanta kuma muka sa aka ɗaure miki mahaifa aka kuma sanya miki zubar jini ako yaushe burin mu rayuwarki ta dawwama cikin ƙunci da baƙin-ciki muka sa aka mallake mana Malam ta yanda duk ko kara na ajiye zaiyi shakkan tsallakewa,hakan ya bani damar tsula tsiya ta son raina sai dai Allah yafimu ƙarfinmu ya bamu nasara akan abubuwa da yawa da muka ƙulla miki bamu sani ba ashe ranar irin ta yau tana nan zuwa Adda Barira kin cuce ni kin cuci rayuwata duk ke kika ɗaura ni akan wannan layin".takai ƙarshe tana matsanancin kuka.
Kasa wani ƙwakwƙwaran motsi nayi tun sanda Hajara ta fara magana nake hawaye har ta ƙarishe ban fasa ba haka nan ma Inna da Adda Barira,Habib da Baffa kuwa kawai dauriya ce da ƙarfin hali irin ta maza amma suma basu ƙi su saki kukan ba.Inna ce tayi ƙarfin halin faɗin"Lalle duniya abar tsoro ce aihun kaji tsoron Allah kaji tsoron mutum mai ƙafa biyu,Hajara ki cuci kanki kin cuci rayuwarki kinci amanar zaman aurenki meye Hibba ta tsare miki a rayuwar duniya?ashe duk wannan abunda dayake samun ta daga wannan sai wancan ashe duk kece sila?".
"Inna sharrin shaiɗan ne da kuma sharrin Adda Barira".
Baffa daya kai ƙololuwar ɓacin rai yace"Hajara kin cuce ni kin haddasa na ɓatawa uwata nayi jayayya da ita a lokuta masu yawa nayi sanadin zubar hawaye daga idaniyar ta wallahi ki cuce ni badan duk wanda ya kashe hukuncinsa shima shine kisa ba,wallahi dasai na kashe ki a cikin ɗakin nan.amma ba komai kije keda Allah zaki ga sakayya gashi nan ma tun kafin ayi nisa kin fara gani na sake ki saki uku ki tattara kibar min gida na".dukkan jikinta ne ya hau jijjiga yayin da wani tari mai ƙarfi ya sarƙeta hawaye sharɓe-sharɓe kwance a saman fuskanta.
"Baffa haƙuri zakayi ba a yanke hukunci ciki fushi mussaman in akayi la'akari da halin da take ciki a yanzu"furci Habib kenan daya sa Baffa saurin faɗin"wannan zan yafewa?ba dai wannan Hajarar ba bakasan irin abubuwan da ta dinga kitsawa bane a cikin gidan nan babu irin abun daba tayi wa Inna a gaban ido na ba amma banida ikon magana".
Rarrafowa Adda Barira tayi ta matso kusa na tare da kamo dukkan hannuna ta ciƙe"Hibba ki gubi girman Allah da ma'aikinsa ki yafe mana ki yafe mana haƙiƙa mun cutar dake aihun".Inna ta miƙe cikin hanzari ta fincike hannuna daga cikin na Adda Barira"Wallahi babu yafiya tsakaninmu daku har abada wannan shari'ar sai muje gaban Allah zamuyi ta domin cuta kam kun cutar damu matuƙa Allah ne kaɗai zai iya mana sakayya"yana kawowa nan ya ɗago ni taja ni muka fice daga ɗakin tana jijjiga Mu'afsa data tashi yanzu,dirsham ta zaunar dani akan gadonta kamar mafarki haka nake ganin duk abubuwan dasuke wakana a halin yanzu kuka nakeso nayi amma ruwan hawayen sun gagara samuwa.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"bakina yayi nasarar furtawa ina jawo numfashi na dayake sarƙewa da ƙarfi mena tsarewa Anty Hajara a duniya mena aikata mata dana cancanci wannan ɓakin ƙiyayyar daga gare ta?a iya sani na ko kallon banzan bai taɓa shiga tsakanina da Adda Barira ba balle har na aikata mata wani mummunan laifin da zatayi ƙudurin ganin bayana ta ko wani hali.yau na ƙara gaskawa cewa bana daga cikin bayin da suke da ƙaddaran jin daɗin rayuwar duniya,figigi na dawo hayyacina sakamakon dafa ni da Inna tayi"ki tashi kiyi sallah".banajin zan iya tsayiwa akan kafafuna a halin danake ciki hakan yasan nace Inna ta ɗagani tayi riƙo da hannuna naje nayi alwalan na dawo a zaune nayi sallan zuhr da Asr dan duk banyi su ba ina zaune kan sallayar aka ƙira magrib nayi sannnn na jawo Mu'afsa jikina wayata ta hau ruri na tsura mata ido har ƙiran ya tsike aka sake ƙira a karo na bakwai kenan dan naga adadin missed ɗin Ummi cikin wayata biyar nata biyu kuma daga Sayyid.kuka na saka mai ƙarfi danake jin ciwonsa sosai acikin ƙalbina mezan cewa Ummi wannna tashin hankalin da muka tarar na tabbatar a wannan lokacin da inada ciki zai iya zubewa saboda matsanancin tashin hankalin danake a ciki.
Tun daga cikin ɗakin nake jiyo yanda Adda Barira keyiwa Inna magiya da ban haƙuri amma Inna ta kafe akan babu yafiya tsakaninmu dasu har gaban abada tana ƙara jaddada kafin asuba su kwashe kayan Hajara su bar gidan tun kafin ta tara musu mutane,sautin kukan da Hajara take yi daga cikin ɗakinta ya sanya ni rutse kumburarrun idananu,kamar rago za'a yanka shi irin kakakin da yake yi babu bambamci koda ɗan taƙi da irin sautin dayake fita na kukan Hajara."Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wayyo ni Allah na,Allah mun tuba Allah mun tuba Inna ku tausaya mana Hajara zata mutu".furcin Adda Barira kenan tana zubewa akan gwiwonyinta tana riƙo ƙafar Inna,saurin tureta gefe tayi tana faɗin"Ai bakuga komai ba ma badai haƙƙin marainiya kuka ɗaukarwa kanku wallahi sai kunga sakayya".tana kawowa nan wuf!ta banko labulen ɗakin ta shigo tana hushin ɓacin rai madarar Mu'afsa ta haɗa ta soma bata.tashi Adda Barira tayi tana mai cigaba da kukan da takeyi ta fice daga gidan,gidan limamin unguwar ta nufa kai tsaye ta shaida masa abunda yake faruwa bata ɓoye masa komai ba dan a yanzu mafita ɗaya ce garesu YAFIYAR HIBBA.Furcin Hajara suka fara dawo mata cikin kunnuwanta"Adda kije ki roƙar mana yafiyar su wallahi ana min azaba acikin jikina ki roƙesu su yafe mana koda za'a sausauta min azabar danake ji acikin naman jikina Adda inna koma ga Allah da wannan laifin ina tausayin makomata".kuka mai tsanani ta fashe dashi"na cuce ki Hajara na cuce ki na ɗaura ki akan hanya marar ɓullewa da sanda kikazo min da wannan maganar na miki nasiha da haka bata kasance gare mu kaico na ni Barira".
"Lalle duniya abar tsoro ce babu shagallalle face wanda ya biyewa ruɗun ta har ta ruɗe shi,kun aikata babban zunubin da Allah maɗaukakin sarki ya haramta su na haɗa shi da wani abin halitta muje gidan na meke faru".
Miƙe tayi tana gaba yana biye da ita har suka iso gidan Habib da Baffa suka iske suna ƙoƙarin shiga gidan wanda dawowar daga masallaci kenan,ganin Liman ɗin ya sa Baffa isa gareshi yana bashi hannu sukayi musabaha sannan Habib.wani mummunar kallo da Baffa ya aika mata yasa saurin rusunar da ƙwayar idonta ƙasa a yanda yakejin tsanar ta ko wuƙa zai iya caka mata ba tare da nadama ba.maganar da Liman ɗin ya soma yi yasa shi ɗauke idonsa daga gare ta"Wannan baiwar Allah ta taso ƙafa da ƙafa tazo ta same ni akan matsalar dak faruwa yanzu a cikin gidanka,shiyasa nazo domin gyara lamarin".
"Mu shiga daga ciki amma wallahi kamar yanda na faɗa a abaya zaman aure ya ƙare tsakani na da Hajara kuma sai munyi shari'a a kotun Allah kotun da babu alkali kuma ba'a karɓan rashawa ko cin hanci".furcin Baffa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login