Showing 84001 words to 87000 words out of 104857 words
Chapter 29 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt
zamu kwana sai gobe mu wuce dan har ya kama mana ɗaki a GOLLAKA HOTEL ,na dade akan sai mun koma bauchi a ranar dan bana ƙaunar na ƙara koda minti talatine a cikin garin potiskum.
Haka muka ɗauki hanya zuwa ƙarfe tara muka isa cikin bauchi daman Yaya Fawas ya ƙira ya sanar dasu dawowarmu,suna zazzaune a falo muka shigo fuskata duk ta kumbura mahaifiyarsu kawai na gaida na miƙe zan shige ɗaki ko takan Anisa wacce take min tayin abinci banbi ba nayi shigewata zasu biyoni Habib yace suyi haƙuri su barni sai zuwa anjima.
Wanka kawai nayi nazo nayi sallah ina iddarwa na ɗaga hannayena sama" ya Allah kaine mai karɓan addu'a to ya Allah ga baiwarka can bamusan halin da take cikiba wataƙil tana raye ko tana cikin matattu duk bamu sani ba,ya Allah aduk inda take kasa tana cikin aminci ka kareta da kariyarta ka rabata da dukkanin abin ƙi"na shafe addu'ar yayin da wani kukan ya suɓɓuce min har na kwanta wayata tahau ruri banida buƙatar yin magana da kowa a halin yanzu dan haka nama kasheta gabaɗaya.
Washe gari tun asuba su Anisa dasu Mahmud suka shigomin ina haɗa kayana Mahmud yace zai bimu yanata rikice har muka fito tafiya bayan munyi karin kumallo mahaifiyarsu tamin nasiha sosai mai ratsa jikin dan daren jiya Yaya Fawas ya sanar daita abunda da muka riska acikin potiskum.
Habib ya bata kuɗin da ban tsaya ganin yawansu ba tayita zubo masa godiya haɗin da shi mana albarka sannan mukayi sallama dasu muka tafi sundai min alƙwarin kawo min ziyara da zaran sunyi hutun makaranta.
Har muka iso cikin katsina banida wani kuzari a jikina gidan Ummi muka fara nufa muka ɗauko Yasira a nan ma Ummi itama tamin nasiha sosai hadda Daddy dan shima mun sameshi ya dawo a lokacin.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
______________________________
Page 5⃣4⃣
Muna isa gida na wuce part ɗina nayi wanka na fito falo don neman abunda zansa acikin cikina su Habib da Yasira ma suka shigo lokacin danake wanka inajiyo tattaunawar dasuka tsaya yi da Yasira akan Umma shawarar dasuka yanke tamin dai-dai nacewa zasuna zuwa da yaya Fawas da Sayyid kawai potiskum ɗin duk sanda suka ƙara samun wani labarin akan Umma.
Kallo ɗaya na musu na ɗauke kaina nayi kitchen nafara ƙoƙarin kunna gas,har na kusa sauƙar da tean dana ɗaura Yasira ta shigo da tulelen cikinta a gaba sosai cikin ya bayyana duk da cewa watanni uku ne amma ga wanda bai sani ba sai yace yakai wata bakwai.
"Anty yanzu Hamma yake sanar dani har kin kwanta a asibiti dan Allah ki cire komai daga cikin ranki ki miƙa dukkan lamuranki zuwa ga Allah"Furcin Yasira kenan danaji sun ƙara karyar min da zuciya na daɗe inajin irin wannan maganar daba bakin mutane da yawa kowa haka yake faɗa min"haƙuri-haƙuri"ita na runguma badan itaba da yanzu banzo inda nake ba.
"Yasira na daɗe da yakice komi daga raina amma Umma kam banajin zan iya hana zuciyata tinaninta a kowani daƙiƙa"na kai ƙarshen zancena ina sauƙar da tukunyar shayin dana ɗaura domin ta daɗe tana tafasa.
Sai data kalloni da idanunta waɗanda suke bayyanar da zallar tausayina a shimfiɗe acikinsu kana tace"in sha Allah,Allah zai bayyana mana ita cikin aminci".nakai hannu na kawar da ruwan hawayen dasuka ciko mini kwaryan ido nace"Amin".
Tacs ruwan shayin nayi sannan na tambaye Yasira abunda zataci domin na samar mata dashi tace taci a gidan Ummi tea ɗin kawai ya ishe ta.
A jere muka dawo falo muka zauna bayan na kunna mana kayan kallo,muka fara shan tea ɗin.wani lumshe idano Yasira tayi tana sakin hamma kafin tace"wallahi Anty bacci nakeji cikin nan yana sani bacci sosai".
Nakai dubana gareta tabbas cikin nan na wahalar da ita matuƙar ga duk ƙafafunta sun kumbura kamar lale-kabo nace"to ai kuwa ya kamata kije ki kwanta kafin a ƙira sallah"ta fara ƙoƙarin miƙewa ta ɗauki hanyar bathroom ɗina har ta kusa shiga Habib ya fito daga ɗakinsa suka sakarwa juna murmushi sannan ta shige shi kuma ya iso ya zauna.
Banji isowarsa cikin falonba balle zama gab dani da yayi sai jin muryarsa danaji kamar a tsakiyar kaina yana faɗin"Hibba damuwa bashine mafita akan wannan lamarin daya same muba addu'a da miƙa wuya ga Allahn daya ƙaddarta mana hakan shine mafita".na sauƙe nauyayyen ajiyan zuciya hawaye suka ciko idanuwa ya fara share mini su"Hibba ki ƙara haƙuri in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe da iznin Allah"jijjida kaina kawai nayi alamar naji haka yayita bani baki da aikin lallashina yaya Fawas ya ƙirani sosai ya ringa kwantar min da hankali harsu Anisa ya bawa muka gaisa kafin mukayi sallama.
Ranan Habib a ɗakina yake Yasira ta kwana a part ɗinmu a ɗayan ɗakin.
Washe gari tun dana tashi asuba ban zauna ba sai dana gama haɗa mana breakfast nayi shirin tafiya makaranta,har muka fito falo da Habib banga koda kulgawar Yasira ba hakan yasa duk muka ɗunguma izuwa ɗakin,tana ta sharar baccinta hankali kwance muka isketa na wuce toilet na haɗa mata ruwan wanka nasamo Habib har ya tasheta maganganun danaji yana mata yasa naji ba daɗi faɗa yake mata akan tabarni inata aiki ni kaɗai tana nan tana bacci.
Ta tashi ta shiga wanka sannan muka dawo falo jiran fitowarta cikin mintunan da basu gaza ashirin ba ta fito mukayi breakfast sannan nayiwa Yasira sallama muka fita da Habib zai sauƙeni a makaranta.
"Hamma wai ni meye amfanin tawa motar indai kullum kai zakana kaini kuma ka ɗaukoni gashi kuma har koya min kasa anyi"na faɗa yayin dana ke tsaida da ƙwayar idona akan fuskarsa datake cike da yalwar annuri shimfiɗe ta ko'ina.
"Zaiyi amfani ranar da bana kusa amma yanzu danake tare dake nizan kaiki kuma na ɗauko abata"yakai ƙarshen maganar yana buɗe min ƙofar motar nasa kai na shiga ina dariyar maganarsa.shima ya zagayo ya shiga sannan ya data motar muka fita.
A hanya yake sanar dani sunyi magana da Ummi za'a samo min mai aiki dan aikin yafara mim yawa tunda Yasira tayi nauyi bata iya yin komai ga kuma fita makarantar danakeyi.
"Allah sarki Ummina ako yaushe mai tausayinace,Allah ya saka miki da alkhairi".
"Amin"na amsa dashi nayi saurin juyowa ina kallonsa dan ni a tinanina a zuci nayi maganar ya ɗan murmusa yana maida kallonsa kam titi yace"gobe za'a kawota ki ganta".nace "Allah ya kaimu".
Haka muka isa cikin makarantar muna hirarmu gwanin burgewa har department ɗinmu ya rakoni duk wanda ya gannu zai tabbatar da babu abunda yake damun ranmu illar gangariyar soyayyar da muke gwadawa junanmu.sai da suka gaisa da Limat Auwal sannan mukayi sallama ya tafi.
Ƙarfe biyar saura muka gama lectures,yazo ya ɗaukeni a hanya muka sayi kaza da youthgut muka tafi gida.shi mukaci muka kwanta.
Washe gari ranar banida lectures sai ƙarfe biyu dan haka ina gama aikina nayi kwanciyata tun munayin breakfast Ummi ta ƙira Habib take sanar dashi an kawo ƴar aikin Sayyid zai kawota,dalilin hakan yasa shima ya zauna a gida bai fita office ba.
Cikin baccin danakeyi naji Yasira na tashi na tana ƙiran sunana a hankali,nayi wata shegiyar miƙa na tashi zaune.
"Anty kifito Yaya Sayyid sun zo da ƴar aikin".kaina na ɗaga mata ta fice daga ɗakin ina biye da ita a baya ina faman mirtsike idanuna da bacci yaci ƙarfinsu.
Turus naja na tsaya ƙafafuna suka shiga karkarwa jin zan iya sulalewa a kowani lokaci yasa na jingina bayana da jikin wall ɗin falon ina ware idanuwa akan ƴar aikin da Ummi ta turo cikin son tabbatar da hashashen zuciyana.
Tan durƙushe a ƙasa kusa da kujaran da Yasira takw zaune akai kanta na kallon ƙasa amma hakan bai hana ni kallon fuskarta ba,rabul ɗin idanunta sunyi baƙin dasu alamar taci kuka mai isharsa kafin zuwa yanzu,ta ƙara baƙancewa ta bushe sosai daga sanin danayi mata ada.
Bakina yana mungun karkarwa har ana iya jiyo yanda haƙwarana suke gogan juna,kar-kar sautin dasuke badawa kenan"Balabara"kalmar da nayi nasarar furtawa kenan ina sulale ƙasa na zauna daɓas!ina hawaye.
Sai a sannan ta ɗago idanunta ta miƙe zumbul lokacin da ƙwayar idanunmu suka gwauraye cikinna juna,ta shiga nunoni da yatsa"Hibba"ta faɗa tana fashewa da wani matsanancin kuka.
Yasirace tayo kaina tare da tambayata lafiya,ban iya bata amsa ba sai sautin kukana daya karaɗe ilahirin falon dan da iya ƙarfina nake fidda shi.
"Na gaskata wannan magana ta masu iya magana dasukace alhaki kwoikwoyone kanan sharri ɗan aikene duk yanda yayi nisan kiwo sai ya dawo ga mai shi,Hibba yau kece a cikin wannan daular wacce naso ƙasƙantawa na wulaƙanta na bita da sharri har illataki nayi ta hanyar kwara miki ruwan zafi akan laifin da bakiji ba baki gani ba.tabbas hakkinki keda Amina bazai barmu mu rayu cikin sa'a ba,Kabir ya lalata rayuwarsa da baƙin cikinsa malam ya rasu yanda na ganshi turmi da tabarya da ƴar maƙwantanmu mai shekara sha biyu Allah ya nuna min annabi.son raina yasa na ɓoye faruwar hakan har sai lokacin daya fara nemana yanzu yana can ya haukace sakamakon shaye-shaye banida komai banida kowa sai Allah naga taskon rayuwa abincin bakina ma yana gagarana wani lokacin Kabir ya lakaɗa min ɗan banzan duka sai dai maƙota su shigo su kwaceni".
Takai ƙarshe tana ƙara fashewa da wani sabon kukan,bani ba hatta Yasira da Sayyid sai da suka koka mata inganin sandan Habib ma yake yarshe nashi hawayen.miƙewa nayi jiri na ɗibata na isa gareta muka rungume juna"Hibba ki yafe min,ki yafe min ko Allah zai sausauta min halin rayuwar danake ciki".
Sai dana haɗiye kukan dayake shirin suɓɓuce min kana nace"na yafe miki Anty Balaraba ban taɓa riƙeki a raina ba".
"Nagode Allah ya saka miki da allahairi"ta faɗa tana ƙara riƙon datamin a jikinta,na ɗago kaina tare da riƙon hannunta muka ƙariso tsakiyar falon inda su Sayyid ke tsaye nace"Habib wannan itace kishiyar Anty Amina mahaifiyar Kabir,su suka fara bani taimakon farkon shigowata katsina suka bani matsuguni acikin gidansu bazan taɓa mantawa dasuba a tarihin rayuwata"na fashe da wani kukan zuciyata na tino mini irin rayuwar danayi tare dasu na ƙunci da wahala.
"Tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai,wanda ya tsara faruwa komai tabbas Allah baya bari hakkin wani mussamman wanda aka zalunta".
Muryar Sayyid kenan dana tsinkayo sun bugi dodon kunnuwana,muka zazzauna sannnn Habib ya fara nashi jawabin"Duk abunda ya faru ya wuce sai dai muyi fatan Allah ya tsare na gaba ya kuma rabamu da mummunan ƙaddara.yanzu Kabir ɗin yana ina?".
Cikin kukan daya gama cin ƙarfinta tace"yana nan acikin unguwa yanabin bola".
Nan wajen Sayyid ya ƙira Ummi ya sanar da ita ta kuwa cika da al'ajabi,Yasira ta kawo mata abinci taci sai da nutsuwarta ya dai-daita sannan Habib yace muje unguwartasu ganin Kabir da farko na nuna bazani ba amma daga baya na shirya mukaje hadda Yasira.
Unguwarsu tada tun can baya itace basu canza ba,muna isa ƙofar gidan naji wani kuka ya zomin ranar farko da Anty Amina ta kawoni gidan ya dawo min cikin kwakwalwata da kuma tarin abubuwan dana riska cikin gidan.
Wasu samari akasa suka kamo Kabir suka kawoshi inda muke sai fizge-fizge yakeyi,hauka tuburan babu kama hannun yaro.aka sashi cikin motar da Sayyid yazo da ita.
"In sha Allah zanyi duk mai yiyuwa wajen ganin ya sama lafiya,ga wannan ki riƙe a hannunki sannan duk lokacin da kikeda buƙatar wani abun zaiki iya zuwa gida ki sanar dani"ya ƙarsihe yann miƙa mata bendir ɗin kuɗi ƴan dubu-dubun daya ciro daga aljihunsa.
Hannunta na rawa ta karɓa tana ƙara fashewa da wani kukan har shiɗewa takeyi,yau Hibbace a gabanta wacce taso ƙasƙantarwa ta tozartata yau ita ta zame mana gata kuma majingina,wacce ta ɗaurawa tsana da ƙiyayya babu laifin tsaye balle na zaune yau itace ta zamto mata mai share hawaye a gareta.
"Allah kenan me yanda yaso".
Kalmar data furta kenan tana ƙara neman yafiyata a karo ba adadi,na ƙara jaddada mata na yafe mata sannan muka tafi akan Sayyid zai kawo mata saƙo.
Dukkanmu gidan Ummi muka nufa muka ƙara sanar da ita abun daya faru da kuma Kabir da za'akai asibit domin duba lafiyar ƙwaƙwalwarsa.
"Hibba kinga lamarin Allah ko,tabbas alƙawarin Allah tabbatacceni duk wanda ya rungumi haƙuri haƙiƙa ya rungumi babban nasara a rayuwa yau dalilin haƙurinki ya jawo miki ɗaukaka".
Furcin Ummi kenan sannan ta ɗaura da nasiha a garemu tare da buga misali da rayuwata,anan muka wuni Habib da Sayyid kuwa tun zuwarmu suka fita wani asibitin kuɗi aka kai Kabir domin duba lafiyarsa.komai Habib ne ya ɗauki nauyinsa likitan ya musu hanya aka fita dashi Cairo.
Har gida Balaraba tazo ta ƙarayiwa Ummi da Habib godiya,ranan dana ƙira Anty Amina nake sanar da ita ba ƙaramin kuka tayiba domin komai rashin imanin mutum yaga rayuwar da Balaraba takeyi sai ya zubar mata da kwalla.
Bazan taɓa manta wannan ranar ba a kaf!cikin rayuwata muna zaune da Yasira a part ɗin mum gama lissafin watannin cikinta kenan wata bakwai da sati biyu,ta tashi ta shiga bedroom ɗinma zatayi sallah.ganin ta daɗe bata fito ba yasa nabi bayanta tana zaune a cikin toilet ɗin tun shigowata nakejiyo nishinta.
Na saki salati ganin jinin dayake bin ƙafafunta na rarumota jikina muka fito ɗaki,ɗamƙo hannuna tayi tasa cikin nata zuffa na tsatstsafo daga kowani sassan jikinta"Anty cikin nan bazan haife shi ba mutuwa zanyi, ki yafe min inna taɓa ɓata miki acikin zamanmu ki roƙa min Ummi itama ta yafe min Hamm......"bata ƙarisa ba sakamakon numshinta data jawo da ƙarfi sai kuma ta sake dukkan jikinta.
UWATACE SANADI
Tsarawa/Rubutawa
©Maimunah Tijjani Iyam
______________________________
Page 5⃣5⃣
Kuka nasaka mai matuƙar sauti na gama ruɗewa na fara jijjita ina faɗin"Yasira ki tashi dan Allah kar kimin haka ki buɗe idanunki ki kalle ni".shine abunda naketa maimaitawa kafin na miƙe kamar an tsira mini wani abun na koma falo na ciro wayata dake caji nashiga dannawa Habib ƙira,ƙiran farko bai ɗagaba sai a ta biyu ya ɗaga.
"Hamma dan Allah kazo gida Yasirace ke naƙuda ka hanzanta"ban jira abunda zai ceba na zame wayar daga kunnewa na ruga ɗakin da duguna na rungumota jikina jini duk ya malale ɗakin,kuka nakeyi sosai naji an buɗo ƙofar ɗakin an shigo na miƙe kuwa da saurina a zatona Habib ne.
Hajja ce ta shigo shaf!na manta da zamanta acikin gidan,na isa gareta da saurina"Hajja ki duba min Yasira ta daina motsi".
"Yanzu Habib ya ƙira Malam yake sanar dashi wai nazo na dubata shima yana hanya yaƙiraki bakya ɗagawa"ta faɗa muna ƙarisowa cikin ɗakin.
Ɗaukarta mukayi muka kwantar akan gado Hajja ta fara danna cikin a hankali,ina zaune gefe babu abunda nakeyi sai ƙwalla, jikina ya ɗauki rawa kamar ana jona mini wutar lantarki.
Ƙaran shigowar motar Habib yasa Hajja cewa mu fito da ita kawai akaita asibiti,muka fito da ita a ƙofar shigowa falo mukayi kicibus da Habib duk muka mufa inda yayi parking muka saka a motar muka nufa asibit hadda Hajja.
Har muka isa asibitin bata motsa ko ƴar yatsanta ba balle musa rai da zata buɗe idanunta,muna isa nurses suka ɗauko gado suka ɗaurata akai aka shiga da ita emergency.
Innalillahi wa'inna alaihirraji'un"na furta can ƙasan maƙoshina haka daman ake haihuwa?kowacce mace sai data ɗanɗana wannna azabar ta naƙuda?,koki sauƙa lafiya koki sauƙa a lahira.wallahi sai naji wani sabon ƙaunar Umma ya ƙara dasuwa cikin rai da ruhina.indai sai data ɗanɗana wannan azabar ta haihomu ta cancanci komai daga garemu.nishin naƙudarma kaɗai wani abune haka muka tsaga jikinta muka fito kowa na mata san barka bayan mum rayu tsawon wata tara acikin mahaifanta ta jure nauyin ciki ajikinta ta cigaba da ɗauniya damu batare da nuna gazawa ba tabbas uwa ta cancanci dukkan sadaukarwa.
Fitowar likitan daga emergency room ɗin yasani kawar da wannan tinanin na bada hankalina ga abunda yake faɗin.
"Ta zubar da jini sosai tana buƙatar jini sannan kuma bazata iya haihuwa da kanta ba dole sai an mata CS dan abunda yake cikinta baya motsi zaka bini office domin kasa hannun akan takardun".
"A ɗauki nawa jinin asa mata"abunda bakina yayi gaggawan faɗa kenan.
Likitan ya kalloni"bamu fiye ɗaukar jinin mace ba amma kije lab a gwara inyayi dai-dai danata tukunna".
Nabi bayan nurse ɗin muka nufa lap Habib kuma suka wuce office da likitan,jininmu yayi dai-dai aka ɗauki leda ɗaya daga jinina sauran ukun kuwa aka saya dan,Habib a jininsu baizo ɗaya ba.
Har ancike takardan cs ɗin daza amata za'a shiga da ita Habib yace zaije ya sanar da su Ummi,Hajja tace ya bari sai ta haihu lafiya tukunna kar ya tada musu da hankali.
Muna zaune aka fito da ita an sanya mata kayan tiyata a jikinta,hadda hula jikin da ledar jinin aka shiga da ita.na saki kuka mai ƙarfi sai da duk mutanen wajen hankulansu ya dawo gareni.
"Hibba ba kuka take buƙata a yanzu ba addu'armu tafi buƙata shi zamu mata".kwantar da kaina kawai nayi a ƙirjinsa ina fidda hawaye shima ɗin ƙarfin haline kawai.
Mintuna goma a tsakani nurse ɗin ta fito da sarsarfa ta iso garemu tana faɗin"Ta sauƙa tun kafin ayi cs ɗin ta sama baby girl".bansan sanda na miƙe na rungumota jikinaba ina hamdala.Habib kuwa hadda sujudul shukr Hajja tace"kaga yanzu sai ka sanar dasu ƴarsu ta haihu lafiya".
Ya dannawa Sayyid ƙira ya sanar dashi sannan ya ƙira Granny itama ya faɗa mata,murna gurin Ummi da Granny ba'a magana,ta shirya Sayyid zai kawota asibitin.
Muna Zaune aka fito da Yasira aka wuce da ita ɗakin hutu,ita kuwa babyn suka shiryata suka miƙo min ita,tsam!na rungumeta a jikina ina sakin ajiyan zuciya.nurse ɗin ta koma fitowa tace"Hibba da Habib su shiga tanason ganinku".
Har rige-rigen shiga mukeyi tana kwance tana ƙarewa ceiling ɗin ɗakin kallo,har yanzu ledar jinin na jikinta.
Kusa da ita na zauna Habib kuwa yaja kujera ya zauna kusan gadon,babyn na miƙa mata ta karɓa tana ƙarewa fuskarta kallo.
"Anty ga amanar wannan yarinya zan baki,ki tarbiyartar da ita tamkar ƴar dakika haifa a cikinki nima muka fatan zaman lafiya mai ɗaurewa keda Hamma.Hamma ga ƴata nan kazama shaida na mallakawa Hibba ita ko Ummi ban yarda abata ita ba".
"Haba ƴar-uwa wannan wani irin magana ne in sha Allah babu abunda zai faru"na faɗa ina karɓan babyn daga hannunta.
Riƙo hannunta Habib yayi yana murzawa a hankali yana faɗin"Babu abunda zai faru Allah ya baki lafiya ita kuma Allah ya raya