Showing 57001 words to 60000 words out of 104857 words

Chapter 20 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7307

ya isheni narasa abunda kemin daɗi acikin raina amsar dazan bawa Habib zuciyata ke shiryamin inya sameni da batun aurensa ai ko zamar dadiru mukeyi dashi sai sanar dani.
Sayyid da Ummi ne kawai kemin maganar,Ummi kuwa tana taushar zuciyata ko Granny bata taɓa furtamin ba.
Naji wayata na fara ruri nayi saurin tsaida hawayena,na ɗaga wayar sannan na gaida Ummi ta amsa sannan tace nazo gida tana nema na.
To kawai nace mata sannan na gimtse wayar naja jakata,na tara adaidaita nahau muna isa na biyashi dai-dai lokacin da motar Habib ta iso gidan.


Ko kallon inda yake banyi ba danji nayi zuciyata tana tasafa,meya ɗauke ni daga shi har danginsa?dazai kasa sanar dani batun ƙarin aurensa,da sauri nawuce cikin gidan ina maida hawayen daya ciko min idanu.
Hadda gudunsa ya biyo bayana sannan yasha gabana da sauri yake maganar numfashinsa na fita da sauri-sauri hakan kuwa alamu ne dake nuni da ciwonsa zai motsa.


"Hibba dan Allah ki saurare ni kafin ki shiga inason magana dake".
"Kayi haƙuri Ummi na jirana aciki"ina gama faɗin haka na fara wayar ƙarya inacewa"Ummi gani nan shigowa na iso".
Na raɓa ta gefensa na wuce, duk yanda zuciyata ke girmama tausayinsa matsewa nayi nayi wucewata,hakan da yayi ya ƙara tabbatar min da bai san cewa nasan maganar ƙara auren dazaiyi ba.
Koda dana shiga falo Yasira kawai na iske tare da Sayyid dan shikam har ya riga da yazo domin biki,sallamata dataji yasa tayi saurin miƙewa zatabar falo.
Sallamar daban ƙarisaba kuwa na haɗiye sauran a cikina saboda son furta sunan Yasira da bakina keson yi.
Ai kuwa cak!ta tsayi jin muryata ta daki dodon kunneta,takuwa nayi har gabanta tayi saurin runtse idanunta tana hawaye,riƙo hannunta nayi ina faɗin"Yasira meyasa yanzu kike guduna?duk inda kikasan samu haɗu bakya zama awajen?wannan abun dagani harke harshi Hamma Habib ɗin bayin kanmu bane,haɗin Allah ne ba mai iya canza shi.Sayyid ya sanar dani tun da Granny ta yanke wannan hukunci walwalanki ta gushe kika daina kula kowa kullum cikin kuka kike koshi Habib ɗin bakyaa saurara duk wannan saboda meye Yasira?".


Kamar jira take namata tambayar tayi saurin cewa"Anty wallahi duk yanda naso hana zuciyata ayyana min cewa wannan auren kamar naci amanar kine kasa hakan nakeyi,na tabbata koshi Hamman basona yakeyi ba kawai dai bayanda ya iya ne".
Zaunar da ita nayi nace"Yasira hukuncin Allah ne sai mu karɓe shi hannu bibiyu,bani da shakkar furta cewa Habib yana sonki domin duk cikin ƴan-uwansa ke kikafi kusa dashi,ki kwantar da hankalinki sannan ki saki ranki har ki faɗa fushi ubangiji kiyi biyayya ga umarnin magabatanki".
Kwanciya kawai tayi jikina tana kuka na ɗagota,na share mata hawayenta nace taje tayi wanka taci abinci ta kwanta ta huta ta tashi ta tafi.
Da kallo nabita nan take tausayi halin datake ciki ya dira cikin birnin ƙalbina,maganar da Sayyid ya farayi shiya dawo dani daga tunanin danayi nisan ciwo acikinsa.
"Lalle Hibba kin cika mace mai dattaku madalla da mace saliha mai ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya da nutsuwa".
Sadda kaina ƙasa kawai nayi kafin nayi wata magana,Habib ya turo ƙofar ya shigo kallo ɗaya nayiwa fuskarsa na tabbatar dacewa yayi kuka dan yanda idanunsa su ƙanƙance fatar fuskar tayi jajir.


Yanda ya shigo falon kai tsaye ya wuce ya zauna,hakan ya tabbatar min dacewa bai lura da akwai mutane a wajen ba yanda numfashinsa yake fita har wani guguu yakeyi.
Sayyid yayi saurin isa gareshi yana tambayarsa lafiya,kansa kawai ya jijjiga masa alamar Babu,na ɗauko maganinsa acikin jakata na tashi na ɗauko masa ruwa dai-dai nan Ummi ta fito daga ɗakinta.
A Sayyid na miƙawa maganin yabashi yasha sannan Ummi ta zauna agefensa tana masa sannu,ya daɗe idanunsa a lumshe kafin ya waresu.
Tare da Sayyid suka je masallaci saboda sallan Asr da aka farayi,muma tashi mukayi mukayi sallan sannan na leƙa ɗakin Yasira naganta tana bacci,tashinta nayi nace tayi sallah tace tana hutun sallah lokacin.
Na fito falo nan na tarar da Ummi a falon na zauna domin maganar da zamuyi maganar data farayi yasamin nutsuwa.


"Hibba mu bamu isa mu dakatar da abinda yake rubutacce acikin littafin rayuwarmu ba,Kiyi haƙuri domin nasan raɗaɗin da kikeji a cikin ranki saboda nima ƴa macece nasan zafin kishi kiyi haƙuri ki tausa zuciyarki".
Murmushi na saka takaitacce nace"Ummi wallahi bakomai bantaɓa riƙonku acikin raina akan wannan aure ba dan nima inzan yiwa kaina adalci,nasan acikin halin da Habib yake ciki yana buƙatar ƙarin aure".
Sosai Ummi taji daɗin maganata sai sanbaɗo min albarka takeyi,muna haka Habbi suka shigo Ummi ta tashi Sayyid yabi bayanta nima barin falon na fara ƙoƙarinyi muryar Habib ta katseni.


"Zauna inason magana dake".


Na dawo na zauna a hankali nake ɗago kaina ina satar kallon fuskarsa."Nasan Ummi ta sanar dake komai har cikin raina bawai na ɓoye miki dawata manufa bane sai dai illa iyaka kawai saboda yanda nake tinanin zaki ɗauki abun,bansan meyasa suka kasa karɓan uzurina a wannan lokacinba?bansan meyasa suka kasa haƙuri harki sama lafiya ba? wasu lokutan zuciyata takance dani ƙaunar dasukemin da tausayin halin dazan iya faɗawa shiyasa su haɗa wannan auren amm...".
Saurin dakatar dashi nayi ta hanyar faɗin"Habib na riga danasan komai tun kafin Ummi ta ƙirani ta sanar dani,ina muka fatan alkhairi dakai da sabuwar Amaryarka".


Cikin wani irin zafin nama ya tashi ya dawo kusa dani yana cewa"Wallahi Hibba babu yanda na iyane amma dazance a dakatar da auren nan,dan ina gudun azabar dazan tarawa kaina domin bazan iya gwatanta adalci a tsakaninku ba".
Da murmushi fal!akan fuskata na ɗago idanuna cikin nasa nace"Habib na fahimce komai kuma ga duk mai hangen nisa zai yabawa namijin ƙoƙarin da iyayenka,sukayi dan ganin sun cetoka daga faɗawa izuwa haram inason na roƙi wata alfarma guda ɗaya tal!a wajenka mijina".


"Inajinki menene?".


"Inason ka cire duk wani damuwar dake ranka,ka miƙawa Allahn daya tsara wannan auren dukkan lamuranka saboda lafiyarka tanada muhimmamci agare mu gaba ɗaya idan bakason kanka to muna sonka".
Wani ajiyar zuciya ya sauƙe mai ƙarfi yana cewa"Tsarki ya tabbata ga ubangijin daya sanya mace ta gari ta zama silar samun nutsuwa,madalla dake Allah ya miki albarka".
Nace"Amin bari yanzu na tashi na turo maka Yasirar?"na faɗa ina miƙewa.
Da kallo ya tsareni yace"Hibba ke bakii da damuwa akan ƙarin auren dazanyi ko?".
Cikin sauri nace"meka gani"saboda tambayar tasa nasha jinin jikina lokaci ɗaya yanayina ya sauya naji babu abunda nafi buƙata illa nabar falon naje nayi kuka kozanji sau-sauci acikin raina.


"Naga ko irin kishin nan ke bakya nunawa".
Dawowa nayi zauna nace"Kishi wani halittane dake jiki kowani mutum mace kona miji,sai dai akwai waɗanda suke jahiltan abun,Ina matuƙar kishinka sai dai hakan bazaisa na haramta maka abunda ubangiji daya halicceni nida kai ya halalta maka ba amma da inada ikon fayyace maka damuwar dake cikin raina danayi hakan kodan ka sama amsar tambayarka".


Ina kawowa nan a zance na miƙe na nufi ɗakin Yasira,da mamakina na hagota saman gado sai faman rusar kuka takeyi,saurin isa gareta nayi tare da dafa kafaɗunta ina tambayarta lafiya?.
"Hibba daman na gaya miki Hamma baya sona gashi yanzu da bakinsa ya furta miki kawai babu yanda zaiyi ne amma daya dakatar da auren nan".
Tun data fara maganar na gano inda ta dosa kuma hakan yasa na gaskaka hashashen zuciya nacewa taji tattaunawarmu da Habib.
"Yasira bafa sonkine bayayi ba kawai dai abun ne yazo masa ba tare da zato ba.Amma na tabbata babu namijin dazai kalle kyakykyawa kamarki yace wai baya sonki sai dai inbai samu ba".
Murmushi ne ya kuɓuce mata ba tare da zato ba tace"kedai Anty bakya rabo da zolaya".nace"Ai gaskiya ce ba zolaya ba,bakiga duk acikin danginku da Habib kawai kike kama ba?yanzu dai ki tashi kije falo yana jiranki kar kibarmin miji ya jira".
Da farko taso tamin gardama akan cewa ita babu inda zataje,da kyar ta yanda ta saka hijab ɗinta tazaje nace"A haka zakije fuskarki ko ƴar hoda babu".


Kafin tayi wata maganar har na isa gaban mirror na ɗauko hoda na shafa mata,nasa maka lidgloss a leɓɓanta sannan na fesheta da turare bayan na ƙara mata da humra tasaka,sannan ta fito.
Sai danaga fitarta na sauke ajiyan zuciya nan take kuma naji zuciyata tamin wani irin nauyi dana tina wajen Habib zataje zance a matsayin waɗanda suka kusa zama miji da mata.
Kukan dakecin raina na saka yayin danaji jiri na nema ya kadani,kwalban turaren dake hannune ya suɓɓe ya faɗi nan kuwa ya tarwatse ya barbazu akan tiles ɗin dake malele a ɗakin.
Figigi na dawo hayyacina nayi sauri saka key a ƙofar dan kar wani ma yashiga ya sameni cikin halin danake ciki,naja jikina na wuce bathroom ina riƙe da ƙirji dayake min soya.


Ina shiga nafara aman jini hadda gudaji gashi baƙiƙirin dashi sosai nake aman tamkar zan amayar da hanjin cikina,ina gamawa kuwa jikina yahau karkarwa idanuna suka daina gano min komai.
Guri na nema cikin bathroom ɗin na zauna,ina kukan tausayin kaina da kuma irin rayuwar ƙuncin danakeyi.
Da kyar na iya miƙe akan ƙafafuna na wanke fuskata nayi alwala,na fito na share kwalbar data fashen nayi mopping ɗin wajen sannan na tada sallan magrib dake faman ƙira yanzu.
Koda na iddar Addu'ar neman sausaucin halin ƙuncin danake shiga nashiga yi,ina shafa addu'ar na ɗauka wayata na ƙira Baffa bayan mun gaisa shima nasanar dashi batun ƙarin auren Habib ɗin,ya nunamin ma Hajiya Granny ta sanar shi,nace yabawa Inna wayar ai kuwa ya miƙa mata muka gaisa itama na sanar da ita.


Har taso tafini firgice tace"Hibba in wani laifin kika masa ki sanar min".nace"wallahi Inna ki kwantar da hankali muna zamanmu lafiya kawai dai,Allah ne yakawo lokacin ƙarin auren kisan kana naka ne Allah na nashi".
Tace "Haka ne"nan dai tata bani shawarwari wanda mafi yawansu akan yanda zan ramawa dangin Habib irin halaccin dasuka min ne,dan dana sanar da ita cewa Yasira ce matar dazai aura ɗin sai naji hankalinta yaɗan lafa.
Munayin sallama na buɗe ƙofar ɗakin na fito ina duba hannuna da kwalban ya yankeni da ina tattarewa,da mamakina na tarar da Habib a falo nace"Bakaje sallah bane".


Na lura dukkansu sai a wannan lokacin suka ankara da shigowata falon,ya ɗago kai ya kalleni sannan kuma ya miƙe tare da faɗin"E wallahi yanzu nakeson naje mun tsaya tattaunawa ne hankalina baikai ga lokaci har ya ƙure haka ba".


Kaina kawai na jinjina na wuce kitchen na fara haɗa abincin dare,nan Yasira tazo ta sameni muka farayi tare da ita,duk yanda naso sakin fuskata kasa hakan nayi saida damuwar dake cikin raina ya bayyana akanta.


"Anty gaskiya kinyi dace kekam Hamma yana sonki da yawa"cewar Yasira.
Kaina yana ga yanda albasar danakeyi nace"meyasa kikace haka?".ta rufe tukunyar miyar dake gabanta kana tace"Duk maganarsa sai yasako sunanki a cikin haka ya nuna ako wani lokaci kina cikin tianinsa".
Murmusawa nayi nace"kema ina miki fatan yasoki haka".
Riƙe haɓa tayi tace"Anty kenan wane ni ai sai dai kawai ayi sha'ani amma batun wai Hamma yasoni ai zance ne kawai".


UWATACE SANADI


Tsarawa/rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


_________________________________


Page 3⃣9⃣




Murmushi kawai nasaka muka cigaba da girkin,har muka gama muka jeresu a dinnig dan Ummi batason ƴan aiki akwai wacce take wanke-wanke da mopping amma girki kam Yasira ce keyinsa.
Muna gamawa na wuce ɗakin Yasira tana biye dani a baya,bathroom na faɗa nayo wanka sannan na fito nace Yasira ta bani wata rigar na sauya ta ɗauko min doguwar rigar atamfa nasaka sannan nayi sallan isha'i.
Tare muka fito da Yasira nan muka iske Ummi dasu Sayyid zaune a falon,kai tsaye muka wuce dinning area Ummi tace mu sauƙo da abincin ƙasa tafijin dadin ci anan.sauƙo dasu Yasira tayi na shimfiɗa mana garduma sannan mukayi serving ɗinsu.
Habib dana lura dashi ba wani jin daɗin abincin yakeyiba kawai turawa yakeyi,dan fuskarsa har yanzu tana bayyanar da girman damuwar dake danƙare ƙasan ransa.


Haka muka gama cin abincin muka kimtsa wajen Daddy kam daman naji Ummi nacewa yaje Maiduguri ɗaurin auren ƴar abokinsa,Habib na roƙa akan yabarni na zauna anan har izuwa lokacin da za'ayi bikin tunda yanzu saura kwana tara.
Ya amince a falo suka zauna suna hirarsu banda Habib daya lumshe idanunsa yana zaune kusa da Ummi,tashi nayi nakoma ɗaki na fara karatun jarabawar dazamu fara gobe in Allah yasa muna cikin rayayyu,duk yanda na maida hankali ga karatun kasa fahimtar komai nayi kawai nasa kuka dan a yanzu duk faɗin duniya babu abunda yakeda muhimmamci agareni kuma ya kwashe kaso mafi yawa daga cikin zuciyata,kamar gidan aurena mijina sai kuma karatuna ina basu muhimmanci sosai.
Share ƙwallar dake kai kawo a fuskata nayi tare da kore duk wani tinani daga cikin raina,na fuskanci abinda nake karanta,wayata dana ajiyeta a saman mirro lokacin dazan shiga wanka ta fara ruri,na miƙe na ɗaukota ganin sunan Habib yasanya na dawo na zauna sannan na ɗaga ƙiran tare yin sallama.
Sallamar kawai ya amsa daga nan yayi shuru ba tare daya sake furta ko kalma ɗayaba,sai fitar numfashin juna damuke irgawa.
A hankali ya furta sunana na amsa sannan ya ɗaura da cewa"Bacci nakeji amma na kasa zuciyata tamin nauyi inaji kamar bazan iyaba".
Nayi saurin cewa"Karka saka komai a ranka mijina Allah yana nan kuma babu abunda ya gagari ƙarfin ikonsa a wajensa muke nema".
Ajiyan numfashi ya sauƙe yace"Bacci nakeson nayi ko zanji sauƙi acikin raina amma na kasa hakan".


"Ka tashi kayi alwala,sannan kazo ka kwanta"tun kafin na ƙarisa maganar naji ƙarar buɗe ƙofar bathroom dayayi,ko bai faɗa ba nasan cewa ya tashi domin yin alwalan.
Sai daya kammala alwalar sannan ya kara wayar a kunnesa yace"Nayi alwalar"nace"yanzu kazo ka kwanta a gefenka na dama kayi addu'a,sannan ka kawar da tinanin komai daga cikin ranka ka kama ambaton sunan ubangijinka"
Ƴar siririyar dariya yasaka lokacin dayake jan blanket yana lulluɓe rabin jikinsa dashi yace"Sai kace wani ƙaramin yaro irin wannan bayani dalla-dalla haka".
Nima sai dana murmusa kana nace"Ai bakada bambamci da ƙaramin yaro a wajena".


"Meyasa mata dayawa suke faɗi haka?"yayi saurin jefo min tambayar.


"Mace nayiwa mijinta kallon ƙaramin yaro badan ta raina saba sai dai dan shiɗin abin riritawa kamar dai ƙaramin yaro,miji abun a nunawa sone kamar dai yaron dayake buƙatar soyayya da kulawa.yaro idan yaso abu to mafi yawan lokuta ayi masa sai a kuɓuta daga fitinarsa,to hakama miji idan yaso abu in an masa sai a zauna lafiya"nakai ƙarshen maganar ina duba fuskata cikin mirron.


Wani sanyin daɗi ne yaji ya tsirka masa shuru ya biyo bayan zancena sannan yace"Kin iya shirya zance mai kama zuciyar mai sauraronki,kuma zance irin na hankali wanda akayi amfani da hankali wajen samar dashi".
Godiya na masa saboda irin wannan yaɓon dana samu kana nace"yanzu dai ka kwanta sai nabaka wani labari mai,daɗi har bacci ya ɗauke ka"yace "ya kwanta".
Na gyara zama na shiga bashi tatsuniyar gizo da ƙoƙi,wanda Abba ke mana da daddare ni da Yaya Fawas,a duk lokacin da Umma tafita wajen sana'arta ta barmu a gida mu kaɗai.
Tun dana fara mishi tatsuniyar idanu ke fitar da ruwan hawaye,kewar Abba na ziyartar rai da ruhi na.Jin shurun da Habib yayi ya daina amsawa hakan ya tabbatar min daya sama bacci na kashe wayar ina sauƙe wata ƙatuwar ajiyan zuciya wanda ya tafiyar da kukan danakeyi.
Jidanayi kamar Yasira zata shigo yasa nayi saurin tashi har ina tuntuɓe da dustbin nashiga toilet na wanke fuskata,ina fitowa na same tana saka kayan bacci tamin sai da safe sannan ta kwanta.
Na jawo takarduna na cigaba da karatuna sai wajen ƙarfe sha biyu na kwanta.washe gari na tashi da wuri kasancewar muna jarabawar dazamu ƙarfe takwas,kafin na fito har Yasira ta shirya breakfast tea kawai nasha nayiwa Ummi sallama na fito Habib yakaini a mota na bashi maganinsa ya sha sannan ya sauƙe ni a school ya wuce office.


Sai ƙarfe goma muka fito nahau adai-daita na dawo gida ko jiran Habib ban tsaya yiba dan Ummi ta ƙirani Granny har ta iso,haka nan naji na nema nutsuwata da walwalata na rasa,zip ɗin jakata na zuge nacirowa mai adai-daitar kuɗinsa sannan na shiga cikin gidan.
Gidana na fara zuwa na ɗebo kayana sannan nayiwa Hajja bayanin ƙarin auren Habib ɗin,ta cika da mamaki nidai haka naja akwatina na taho na barta na wuce gidan Ummi.


Falon Ummi na shiga na tarar da Granny ta tisa Yasira a gaba,sai faɗa take mata akan tabi mijinta sau da ƙafa da zarar an ɗaura auren,kar ta tsaya ganina a matsayin wani abun har hakan ya hanata nunawa mijinta soyayyarta gareshi,hannuna yana kan handle ɗin ƙofar amma maganganun Granny dasuke tashi daga cikin falon ya hanashi tura ƙofar nashiga.
Jida nayi an dafa allon kafaɗuna yasani nayi saurin juyowa ganin Ummi,yasa nafara saurin share hawayen fuskata da gefen mayafina.
"Mun shiga"ta faɗa tana jan hannuna ta gaban Granny muka ratsa zamu shige ɗaki bayan na gaisheta ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa.
Ɗakin Ummi muka wuce tace min anan zan zauna ba'a ɗakin Yasira ba,sannan ta shiga bani haƙurin akan maganganun Granny na nuna mata ni banma ji abunda suke tattaunawa ba.


Rage kayan jikin nayi na shiga toilet na haɗa ruwa nayi wanka na fito,kukan dayake shirin fito mini naketa ƙoƙoarin dannewa,domin yanzu na farga na gane kuka bazai min maganin ciwon dake cikin ƙalbina ba.sai dai zai sausauta min wani daga cikin bangaren ƙuncin danake ciki.
Domin kuka ba rauni bane wani yare ne na zuciya wanda baki,yayi kaɗan wajen furtashi ko kuma fasalta shi.
Kaɗan-kaɗan na shafa mai a jikina nasa kayana nayi sallah,Ummi da tun fitowa take zaune saman gadonta tace nazo na tashi na zaune gefen ƙafarta a ƙasa.


Sai data numfasa kana tace"Allah yasani har cikin ƙololuwar raina banason,wannan haɗin auren kawai dai Hajiya ce ta kafe akan hakan amma bazan jure ana miki cin mutumci akan idona saboda wannan ƙaddarar ta faɗa miki ba,wallahi bazan iya ba domin ko ba komai nima uwace kuma na haifa inke ƴatace bazanso ba".
Tabbas inhar za'a bani alƙalami da tawada na rubutu jerin masoyana a rayuwar duniya,Ummi na daga cikin mutane mafi soyuwa a rayuwata.ƙarayin ƙasa nayi da kaina nace"Ummi idan Allah ya ƙaddatar akwai zama,a tsakaninsu babu yanda zamu iya nidai addu'ata Allah yasa wannan auren ya zamto silar samuwar farin- cikin Habib".


"Hakane amma kema ya zama dole in dage da gyaraki har Allah ya kawo mana sauƙi,dan bazaki zauna ba haka ba".
Kukan danake hana fitowarsu sune suka fito da matuƙar sauti har sai da Ummi ta razana nace"Ummi munyi maganin nan ba sau ɗaya ba,ba sau biyu ba munyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login