Showing 93001 words to 96000 words out of 104857 words

Chapter 32 - UWATACE SANADI Book Complete by Maimuna Tijjani Iyam.txt

Advertisement

22 Feb 2025

7341

kenan yanayin gaba sannan suka biyo shi.
Habib ne ya shimfiɗa musu tabarmar dake yashe a wajen suka zauna kafin yayi ƙiran Inna,tare muka fito bayan na kwantar da Mu'afsa da Inna ta gama bawa madara tayi bacci.waje muka nema muka zauna kafin muka gaishe da Liman ɗin ya amsa yana gyara zaman babbar rigarsa a jikinsa.Adda Barira ta rarumo Hajara ta fito da ita yayin da warin dake fita daga jikinta ya ɗumame wajen jinginata tayi da jikinta ta zauna domin bata iya zama ita kaɗai.
Tsaf!Liman ɗin ya ƙarewa Hajara kallo kafin yayi gyaran murya ya soma faɗin"naji duk abunda yake faruwa shi lamari irin wannan dole sai ankai zuciya nisa kuma ansa mata haƙuri,dangana da yarda da ƙaddara tabbas na daɗe banji labarin daya rauna zuciyata ba kamar wannan duniya ta zama abun gudu wasun in suna aikata laifi sai kaga kamar basa tunawa da mutuwa alhalin ita ma halitta ce na ubangiji kuma tana kan duk wani mai rai laifin shirka babban laifine a wajen Allah mai girma amma idan aka yi tuba nagartacciya tare da ɗaura niyyar baza'a sake komawa gare ta ba Allah yakan iya yafewa mai aikata ta,sai kuma haƙƙin cutar da wannan baiwar Allahn da kukayi na hana mata nutsuwa a cikin gidan aurenta kuka hanata samun haihu wanda hakan ya jefata cikin tararradin rayuwa kun ɗauki haƙƙinta har sai ta furta da bakinta cewa ta yafe muku domin Allah baya yafe laifin dake tsakanin bawa da bawa har sai shi wanda aka zaluntar ya yafe".
"Wallahi Malam waɗannan mutanen sun cutar damu sun shiga tsakanina da ɗana daya daya rage min a duniya tsakaninmu dasu babu yafiya har duniya ta naɗe"Inna ta faɗa tana fashewa da Kuka har Marinta Hajara tasha sa niyyar yi a gaban Baffa amma baya iya taɓuka komai ashe ba banza an shanye shine.
Habib ne ya soma magana cikin taushin murya"Inna dan Allah kiyi haƙuri kowa yasan sun aikata ba dai-dai ba amma ita afuwa tanada daɗi kuma tana da kyau ko Allah muna masa laifi ya yafe mana".
Sautin kukan Hajara da Adda Barira ya karaɗe dukkan wajen,cikin azaba Hajara ta soma faɗin"Malam ka dubi girman Allah ka yafe min ko zan tarar da mahaliccina cikin salama"tsuke fuskarsa yayi gum!kamar hadirin daya ke gab!da zubar da ruwa tare da cifanta da wani guntun tsaki yana kawar da kansa gefe.


"Malam Adamu cikin gurare da yawa acikin littafin alqur'ani mai tsarki Allah yayi bayani akan irin tagammashin bayin masu haƙuri,a wata ayar har yana cewa babu wanda zai iya biyan masu haƙuri sai shi a wata ayar kuma yace lalle yana tare da masu haƙuri.wata rana an tambaye Manzon(S A W)cewa menene haƙuri?,sai yace haƙuri shine juriya akan baƙin-ciki,yin raha ga maƙiyi,barin mummunar zato,cire girman kai,karɓan uzuri a inda kasan ba gaskiya,haƙuri a inda kake da ƙarfin ramuwa,yafiya ga wanda ya cecu ka sannan kuma kyautatawa ga wanda ya munana maka wallahi haƙuri babban rabo ce".
Wannan bayanin na Liman ya sanya jikinmu yi sanyi ƙalau kaina dayake tsakakkanin gwiwana ina fidda hawaye masu ɗumi na ɗago"Na yafe miki Anty Hajara,na yafe miki duniya da lahira Allah ya baki lafiya ya tashi kafaɗunki"abinda da yake a cikin zuciya nane bakina ya shiga karantowa ba tare dana shirya ba.Sosai Liman ya saki hamdala na lura Inna sam bataji daɗin furci na ba dan nan da nan ta kuma haɗe rai tana aiko mini da wani irin kallo daya sanya jikina ƙara yin laushi na motso gareta hannuwanta na riƙo cikin muryata da bata fita sosai na fara faɗin"Inna ki yafe musu muma fa muna aikawata Allah laifi kuma da zaran mun roƙi yafiyarsa yake gafarta mana mu a wani dalilin zai sa muƙi karɓan tubansu,haƙiƙa sun cutar damu cuta mafi munin kwatantawa amma haƙurin shi yafi Inna dan Allah ki yafe musu suje da halinsu".
Zazzafar ajiyan zuciya ta sauƙe yayin da idanunta suka fara kawo ruwar ƙwalla ta ƙara matse hannuna cikin nata"Hibba kinga rayuwa iri-iri masifo daga wannan sai wancan babu ɗaga ƙafa kuma duk Hajara ce silar faruwar komai,inada yaƙinin da ta sama dama zata iya kawar dake daga doton duniya gabaɗaya.amma kamar yanda kikace suje da halinsu na yafe musu amma su tattara su bar gidan nan tunda yanzu babu igiyar auren Adamu akanta.dan matuƙar zan cigaba da ganinta zuciya zata iya ɗebata na lahanta ta wataran".
"Alhamdulillah in sha Allahu zakuga sakamakon wannan haƙurin da kukayi,yanzu saura kai Malam Adamu".
Mintuna biyu a tsakani muna sauraron abunda Baffa zai ce kafin yace"Ba komai Malam taje na yafe maka".sosai su Hajara suka ƙara satin wani kukan suna nufo ni Inna tayi saurin dakatar dasu,sannan taja hannuna mukayi ɗakin,nasiha Liman ya ƙara gabatarwa su Hajara kafin ya tafi.yana ƙara tausan zuciyar Baffa dan ya kare akan cewa baza su kwana masa a gida ba sai dai sun fita da daddaren nan sai da Habib da Liman suka roƙe shi sannann ya amince akan asubar fari su tafi.
A gefen Mu'afsa na zauna ina wani irin kuka daya tunkushe mini numfashi waje guda wayata na kallo har yanzu ƙiran Ummi ne ke shigowa.




UWATACE SANADI


Tsarawa/Rubutawa


©Maimunah Tijjani Iyam


_____________________________


Page 5⃣9⃣


Inna ce ta ɗaga ƙiran ko gaisawa ba suyi ba Ummi ta fara zubo mata tambayoyi wani nabin wani"Ina Hibba da Habib ɗin ina fatan dai lafiya ya tafi ya barmu cikin jimami gashi su dukkan basa amsa waya inmun ƙira su".
"Lafiya amma dai ba ƙalau ba"Furcin Inna kenan kafin ta hau warwarewa Ummi sare da abawa akan abunda ya faru zaman ƴan bori Ummi tayi tana sulalewa ƙasa dirsham!kalmar innalillahi wa inna ilaihir raji'un kawai take furtawa wanda hakan yasa Sayyid da Daddy nufo ta karɓan wayan Sayyid yayi yana duba wanda tayi wayan tashi kafin ya kara wayar a kunnunsa"Meyake faruwa ne kun barmu cikin duhu?"Inna ta feɗe masa komai cikin wani irin hucin ɓacin ran ya daya taso masa lokaci guda yake faɗin"Yanzu ina ita Hajarar,ina fatan dai tana hannun hukuma ko?".
Taɓe baki Inna tayi kafin ta shiga labar ta masa Baffa ya riga daya sake ta kuma duk mun yafe mata.
"Wallahi Inna babu wani yafiya bata cancanci hakan ba dan Allah ki riƙe min su zuwa goben zanzo cikin Kanon wallahi sai na musu dukan da ku uwar data haife su inta gansu ba zata shaida su ba".cikin Sauri Daddy ya fizge wayar yana gimtse ƙira bayan yace wa Inna gobe suma zasu ɗauko hanyar kanon,duk abinda Inna take faɗi babu wanda baiji ba domin wayar a handsfree take,wajen Ummi ya fara isa yana lallashinta.
Ina kwance har yanzu kamar matacciya zuciyana na mini soya da raɗaɗi Inna ta shigo ɗakin wayata ta miƙo min haɗi da cewa"Ga Fawas za kuyi magana".da ƙyar na iya wangale ƙwayar idona na tashi daga kwanciyar dana yi na amsa wayar ina manna ta kunnuwa shuru nayi sai kukan danake wanda ya tsananta ba tare dana san dalili ba.
"My cute angle tabbas rayuwar duniya tana cike da ƙalubale kala-kala da kuma jarawaban da baza mu iya kaucewa faruwarsu ba,amma haƙuri da dangana yake sawa rayuwa ta cigaba da gunada tamkar babu abunda ya taɓa wakana.yanda kika yafewa Anty Hajara kinyi matuƙar kyautata ƙanwata Allah ya gubi wannan haƙurin da kikayi ya saka miki da mafificin sakayyarsa".a wahalce na amsa da amin sannan ya ɗaura da faɗin"in sha Allah nima gobe zan zo cikin Kanon,sannan banason kisa wannan damuwar a cikin ranki har ya ɗaga miki ciwon ki kinji my cute angle".sai dana tare hawayen dake shirin gangaro mini kana nace"Yaya Fawas duniya ta fara bani tsoro matuƙa cin amana na babba da yaro kamar baza'a koma ga Allah ba,na daina tsoro ko kuma fargaban komai yanzu a rayuwa domin duk abunda nake tsoron da fargaban rasa su sun faru dani,mun rasa Abba ga matsalar Umma har yanzu bamu san inda take ba ga rasuwar Yasira wallahi Yaya Fawas ji nakeyi kamar na fita nayi hauka ko zanji sanyi a raina".nakai ƙarshe ina toshe bakina saboda ƙarfin kukan danaji yazo mini Inna da tun data kawo min wayar take tsaye ta zauna tana dafa kafaɗarta na ɗaura hannuna saman nata maganar da yaya Fawas ta fara ta sani bashi hankalina"Ba zamu dawwama cikin kukan dan wasu sun cin amanar mu ko kuma dasun baƙan mana ba,Hibba inaji a jikina wahalar mu ta kusa zuba ƙarshe,inaji a jikina mun kusa daina kuka mu rayu cikin walwala da dariya kamar kowa.an tambayi FARIN-CIKI cewa a ina kake rayuwa?amsar daya bayar cike da tabbaci yace"a zuciyar wanda ya yarda da ƙaddarar Allah(SWT) gare shi muyi haƙuri in sha Allah zamu cinye wannan jarabawar.
Daga ni har Inna muka amsa da amin sai daya tambayi Mu'afsa na amsa masa da tana lafiya sannan muka yi sallama,naje na ɗauro alwala na fara jera nafilfili na daɗe a haka kafin na shiga roƙan Allah ya min zaɓi a cikin rayuwarta har na kwanta naji ƙaran shigowar saƙo a wayata ko dana duba Habib ne babu komai a cikin saƙon face kalmomin kwantar da hankali da ɗarsar da nutsuwar zuci ga wanda yake karantawa,wani murumushi mai ciwo nayi sanda na ƙare karanta saƙon ina ƙara kawo Mu'afsa jiki ina rufa mana bargo.


Ban taɓa ganin daren da ya mini tsawo ba kamar wannan baƙin daren a gare ni,juyi kawai nakeyi bacci sam yaƙi ziyarta ta zuciyata banda tufka da warwara babu abunda take saƙa mini,banda bacci ya cika cikakken barawo da bazaiyi nasarar ɗauka ta ba a wannan daren saboda yanda nakai matakin ƙarshe a tashin hankali da rashin nutsuwa a tattare dani.cikin gyangyaɗin daya fara ɗauka ta babu daɗewa nayi jiyo an kurma ihu nayi saurin buɗe idona ƙar!ina ƙara saka kunne tare da sauƙe idona akan Inna da take gefen take munsharin ta,har na koma na kwanta na kuma jin an kurma wani ihu a wannnn ƙaron hadda faɗin"wayyo ni na shiga uku"naji an faɗa.


Tsoro ya dira a birnin zuciyata ƙiran sallan assalatun farko da aka farayi ya sanya ni dawowa hayyaci na,cikin saurin na fara data Inna sai data tashi ta zauna nace"Inna bakiji ana ihu ba ?"ta hau mirtsika ido kafin ta kai ga furta wani abun muka ƙara jiyo wani ihun haɗe da salati da sallallami.
"Wannan ai Barira ce".Inna ta faɗa duk muka zabura muka fito muka nufa ɗakin Anty Hajara.gefe guda muka hango Adda Barira ta kafe kai da gwiwa taan rusar kuka kamar ƙaramar yarinya wiwi sai rera shi take yi Inna ce ta fara isa gare ta" Barira wai me yake faruwa ne kodai jikin Hajaran ne Allah dai ya nuna mana wayewa gari lafiya ku tattara ku tafi".
Cikin dusashewar muryarta da bata fitowa sosai Adda Barira ta shiga faɗin"Inna Hajara!Inna Hajara!!Inna yar-uwata dai bat........"tsawan da Inna ta daka mata yasa sauran maganganunta maƙalewa a maƙoshinta"wai menene ki fito ki faɗa abunda yake faruwa kita faɗin wai Hajara,to Hajarar me?".
"Inna Hajara ta rasu Hajara ta rasu".ta faɗa tana ƙara sautin kukanta wanda hakan yayi dai-dai da fitowar Baffa da Habib zasu masallaci hayaniyar Inna ta sasu shigowa ɗaki.daga ni har Inna sai yanzu muka lura da Hajara dake wanke ta mimmiƙe ido har sun kakkafe fuskarta ta ƙara duhu da matuƙar muni babu kyawun gani balle in misalta muku yanayin sa.na riga kowa isa gareta na soma jijjiga ta sosai ina ƙiran sunanta da duk muryata amma bata motsa ba balle nasa rai da zan sama amsa,durƙushewa nayi a wajen wani kuka mai matuƙar ƙarfi da ciwo ya karyo mini na buɗe dukkan muryata na shiga fiti dashi wajen wanda duk ɗakin ya ɗauka.har yanzu da Habib yake ɗago ni daga jikinta banbar jijjigata ba ina faɗin"Dan Allah Anty Hajara ki tashi dan Allah ki buɗe idanunki wallahi ni na yafe miki na yafe miki duniya da lahira na yafe miki".kwantar da kaina nayi a kafaɗarsa ina cigaba da rero kukana.
Baffa ya lulluɓa mata wani zanin dake kusa da shimfiɗar tata yana rufe mata idonta da suka ƙafe da hannayensa sannan yace mu fito zasuje masallaci dasu sanar da liman ƙarfe goma za'ayi jana'izan.ina maƙale jikin Habib muka fita wani sabon tashin hankali naji yana ziyartar rai da ruhina da ya kusa tarwatsa su babu shiri har ɗakin Inna ya kaini yanata min nasiha dan tun jiya bamu sama damar zama da shi ba,sai daya ga hankalina ya ɗan lafa sannan ya fita izuwa wajen,wajen Baffa suka nufa masallaci.
Nima na tashi nayo alwala sannan nazo na gabatar da tawa sallan a zaune nayi ta dan jinayi jikina babu ƙarfi bazan iya tsayawa akan ƙafata ba,bayan dogon addu'ar dann shafa na ɗauko wayata nayiwa Yaya Fawas text akan rasuwar Anty Hajara da kuma lokacin da za'ayi jana'izan yana tafiya nayiwa Ummi ma sannan na kashe wayar gabaɗaya na ajiye ta gefe guda,ina zaune a wajen Inna da tun ɗazu ta fita nemo matan da za suyiwa Anty Hajara wanka ta dawo tun kafin ta shigo take faɗin"innalillahi wa inna ilaihir raji'un duniya ina zakije damu"har ta shigo ɗaki bata daina ba nace"Inna lafiya kuwa?".sai data zare zaman hijabin dake wuyanta kafin tace"Wallahi Hibba duniya abar tsoro ce aihun wai yanzu duk matan dake wankan gawa a unguwan nan sun basa su wanki mushiriki ba Hajara ta jazawa kanta bala'in".zuciyata ta shiga lugudan tara-tara inata juyayin yanda wannan maganar ta fita har kowa yaji ta wata zuciyar ta ce min hakan baya rasa nasaba da yanda Adda Bariria ta fita jiya ta ƙira malam Liman da kuma ihu da tayi ta sakewa da asubahin nan.
"Inna yanzu yaya za'ayi kenan?"na jefa mata tambayar ina kafeta da ido"Yaya zamuyi kuwa ai duk wanda yaji abunda Hajara ta aikata dole yayi gudunta kuwa,ni zan wanken ta ai baza'a biyewa halinta ba".ban ƙara cewa komai ba Inna ta ɗauka Mu'afsa tayo mata wanka sanna ta shirya ta na miƙa mata madararta dana gama damawa yanzu ta fara bata.
Su Baffa suka dawo da likkafani dasu turare da sauran abubuwan suka miƙawa Inna,ta karɓa bayan ta sanar dasu yanda suka wanye da masu wankan gawan,bangan Baffa ya nuna wata damuwa ba haka nan suka fice.
Ƙarfe tara bata cika ba su Ummi suka iso ta shigo Sayyid da Daddy kuwa suka zauna wajen,wajen su Baffa duk da Baffa yace baza'a yi zaman makokin a gidan sa sai dai suje gidan Adda Barira suyi,itama Adda Bariran tun kafin su Baffa su dawo daga masallaci yazo ya aiko yaro ya kawo mata takardan sakinta uku cur.
Kusan babu tazara mai yawa tsakanin zuwan su Ummi da zuwan Yaya Fawas tare dasu Sadiq da Mahmud suka zo,Ummi da Inna ne suka wanke Hajara tas!suka kuma shiryata sannan aka fito da ita akan mata salla tsirarun mutane ne suka sama damar halaltar sallan jana'izanta kaita makoncinta kuwa daga Baffa,Yaya Fawas sai Daddy da Sayyid sai wasu maƙwatanmu su biyu sai su Sadiq da Mahmud.haka nan cikin gidan babu taro mata da yawa iya yamu yamune sai Kishiyar Adda Barira Larai data zo ko jimawa babu itama tana mana gaisuwa ta tafi abinta.
Sai yamma sannan su Baffa da Daddy suka shigo duk suka tara mu muna ƙara mana nasiha sosai,ana ƙarewa Baffa yace Adda Barira ta fito ta tafi,Daddy yayita bashi baki akan ya bari ayi ko sadakan uku ne sannan ta tafi ya yarda da hakan badan yaso ba sai dan nauyin Daddy dayake ji.
Granny ta ƙirani ta min jaje sosai tare da nata salon nasiha,bayan kwana biyu su Anisa da Fadila da kuma mahaifiyarsu Haj.Jummai suka zo suka mana ta'aziya washe gari kuwa ana sadakan uku suka shirya komawa Azare hadda yaya Fawas muna zazzaune a tsakar gida Adda Barira ta fito a guje Ummi da Haj.Jummai suka riƙota sai fizge-fizge takeyi tana ƙoƙarin keta kayan dake jikinta ganin baza su iya ba yasa su ƙiran Daddy da Baffa suka shigo duk yanda suka so zaunar da ita hakan ya gagara duk ta keta suturar dake jikinta ta figi hanyar waje da gudu.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!Barira ke kuma haukacewa kikayi Allah ya kawo miki sauƙi"furcin Inna kenan dai-dai nan Sayyid da Fadila da suke zance a waje suka shigo suna tambayar lafiya.nan Baffa ya ƙira Liman ya ƙara manaa nasiha mai ratsa zuciya akan cin amana da haɗarurrukanta,wanda ya sanya ni jin komai na rayuwar duniya ya fice mini a rai.
Ranar da Yamma su Yaya Fawas suka koma azare washe gari muma mukeda niyyar wuce katsina sosai na keta kukan daya riƙe mini ƙirji sanda zamu tafi muna sallama da Inna da ƙyar na raba jikina da nata sannan muka tafi,Motar Sayyid muka shiga nida Ummi,Habib kuwa sun rigamu wucewa shida Daddy.Muna isa cikin Katsina muka wuce gidan Daddy Ummi na riƙe da Mu'afsa muka fito daga cikin motar muka nufa cikin gidan kaina danaji yana sara mini da matuƙar ƙarfi na dafe har muka kai ga shiga falo kai na tsaye na wuce ɗakin Yasira na shiga bathroom na sakewa kaina ruwa lumshe idona nayi a hankali ina tinano abubuwa da yawa da suka faru a rayuwata.na daɗe a wannan yanayin kafin na ɗauro towel na fito doguwar rigarta na zata har ƙasa sannan na tada sallan zuhr,ina iddarwa na fito na wuce kitchen zan haɗa mana lunch Habib da Daddy suka shigo ledar dake hannun Habib nayi saurin karɓa ina yiwa Daddy sannu da zuwa ya amsa mini yana yalwata annurin dake saman fuskarsa.
Basu daɗe da shigowa ba Ummi ta fito riƙe da Mu'afsa tana ganinta ta fara sakin dariya tana ƴar tsalle-tsalle na karɓe ta,Ummi na ta mata tsiyar taga uwarta dole ta ƙita.kitchen na wuce na jujjuye abinci da Habib yayi order sannan najesu akan dinner duk muka taso muka zauna zaman ci.juya cokalin kawai nakeyi amma na kasa ci Ummi data lura dani ta jawo plate ɗin gabanta ta fara bani da kanta wani abun dana kasa fasaltar ma'anar sa ya dirar mini a rai inama ace Ummi mahaifiyata yanda take bani kulawa haka.muna gama cin abincin Habib da Sayyid suka tattare wajen Ummi na musu tsiyar sun zaman yan daudu basu da aiki sai aikin mata.Falo muka dawo muka zauna muna hira wanda duk akan cin amana irin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login